Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai hawaye kawai, gaskia ya tausayawa
sumy ba kadan ba, duk laifin hajiya hadiza ne, da yanxu
sumy na gida agabanshi hankalinta kwance. Yana taba
sumy hakuri akan karta damu jarabawa ce ta ubangiji,
komin wuya akwai dadi, ya ajiye masu shopping din
daya masu sa’annan ya masu sallama zai koma kano,
karshen shekara zai dawo ya dauketa, ya dauko
makudan kudi yabasu suna ta godiya.. Daddy kam yayi
niyyan kwana biyu, amma bazai iya jure ganin sumy
halin da take ciki ba, shi kanshi daurewa kawai yake
amma ranshi a bace yake, aka ya tattara ya koma kano,
Hajiya hadiza na hakimce a parlour a zaune tana jiran
shigowan daddy gidan, dan ta kwarara mai buhun
bala’in data saba akan yaje ganin yar tsintuwo bada
izinin taba…. Yana shigowa ta gane muryanshi da
sallaman da yayi bata ma damu da yanayin shi ba, ta hau
zaginshi damai rashin kunya ta ko ina, daddy kam kasa
magana yayi ma saboda bakin ciki ta riga tamai yawa,
nan take shikam ya yanki jiki ya fadi sai jin faduwan
mutum tayi tim akasa…..:oops::oops: Ta kwallawa samira
(yar aiki) kira maza ta fito Alhaji ba lafiya, samira ta fito
da gudunta tana hajiya, alhaji ne ya fadi da alama ma rai
yayi halinsa. Hajiya a rude tace “samira kiramin wayar
shehu nasan baiyi nisa ba,kirashi mukai alhaji asibiti…..
Baba shehu da sauri ya iso gida,suka sa alhaji a mota sai
asibiti likitoci sun yi iya kokarinsu, amma rai yayi halinsa
(kulli nafsin za’ikatul mauti), abun tausayi hajiya da baba
shehu sai kuka suke yau sunyi babban rashi. Doctor
yasamu baba shehu da hajiya ya tambaya su ya akayi
suka bari har zuciyan alhaji ya buga alhalin sunsan yana
da ciwon zuciya, hajiya tayi tsuru tsuru bata ce komai ba
illa kukan da take tayi dan tasan tabbas itace silan ciwon
zuciyan alhaji, yanxu gashi ya tafi ya barta, kuka kawai
take tana nadaman abunbuwa data shuka mai……..
Nima kasa rubutu nayi saboda mutuwan daddy ba
karamin girgizani yayi ba…… Rip *Xarah Bêê*
*Dedicated to Bady social* ~Luv u all~ KURSUM By
~Xarah Bukar Page ~ *Kano* Mutuwa daddy ba karamin
girgiza jama’a tayi ba, mutane da dama sun sanshi da
halin kwarai da taimakawa talakawa, Sam ba ha’inci ko
xalinci a lamarin sa……mutane sai shigowa ta’aziya suke,
baba shehu na daga waje yana amsan gaisuwa… Hajiya
kuka kawai take dakyar take ma iya amsa gaisuwan da
ake mata, hajiya mario ce tadawo gefen ta tana kara
bata baki akan tayi hakuri addu’a ya kamata tamai bawai
kuka ba. Zainab ma tayi rashin daddy ba kadan, dan
daddy ne kadai yake kwabarta da mata nasiha sosai
game da yanda tadau rayuwa da zafi, yau gashi tayi
babban rashi. Tana kaunar shi tamkar shiya haife ta.. Har
gida yazid yaje yama xee ta’aziya, ya tausaya mata sosai
dan yasan yadda suka shaku da daddy ba kadan ba, wani
irin sonta ya karaji a zuciyan shi….har dakin hajiya yaje
ya mata gaisuwa, ta amsa ba yabo ba fallasa dan yanxu
tadan rage kukan nata, dazai wuce ta bashi sako ya kaiwa
mairo tare da shi mai Albarka. ……..yazid kam yana jin
haushin yadda hajiya ke cewa umman sa mairo sai kace
a kauye Ina laifin maryam ma…… Bauchi Yan makaranta
kam sai shirye shiryen xana jarabawa shiga ajin karshe
ake babu wasa kowa ya dukufa da karatu, sumy kam ciki
ya shiga wata tara, haihuwa ko yau ko gobe, “Sam bata
da labarin mahaifinta ya rasu wata bakwai da suka wuce.
Kursum da gimbiya kadai suka San da rasu war shi, sunki
sanar matane akan lalular da take tare shi. Sun fiso saita
haihu sannan su gaya mata….. Bayan kwana biyu, sumy
ta tashi da nakuda mai tsanani, da gudu kursum ta kira
gimbiya sukai rushing dinta zuwa hospital , Allah yasa
haihuwan taxo mata da sauki ta haife kakkyawan baby
gal wanda babu bambamci da ubanta kaman an tsaga
kara an karya…washe gari likita ya sallamo su suka
dawo… Ranan suna ba wani bidiri akai ba, duk da
gimbiya ta gayyato mutanan ta, yarinya kam taci suna
hanifa son kowa kin wanda ya rasa. Sumy kam sai
murna take, ba karamin son hanifa take ba, dan yanxu
tama daina jin haushi mijinta asalima ta yafe mai duk
abunda ya mata…tana fatan Allah ya hada hanifa da
ubanta wata ran. Kursum ce ta shigo daki ta kwantar da
hanifa da tayi bacci, tace akwai abunda nakeson
gayamaki sumy amma kiyi hakuri bamu gayamaki ba
tun lokacin saboda cikin ki, Allah ya yayiwa daddy
rasuwa tun wata takwas da suka wuce…. Innalillahi wai
inna’ilaihi raji’un kawai sumy take furtawa, kuka take na
tashin hankali shikenan daddy ya tafi ya barta yanxu
bata da wani gata, yanxu ya zata koma gida da zama, dan
bata manta da azabar da tsanar da hajiya ke mata ba tun
tana karama, hawaye kawai take tana Allah yaji kanka da
rahma daddy……Kursum kam tashi tayi tabar dakin dan
bazata iya ganin kawarta cikin yanayin da
takeba…….itama tasan tayi rashin daddy ba kadan ba,
dan shine ya mamaye mata gurbin uban da bata dashi.
*kano* Gaba daya family din daddy sun hallara a
parlour din gidan tare da lawyer (alkali) sa dan karanto
will (wasiha) da alhaji ya bari kafin ya rasu…… Baba
shehu kam sai murna yake dan yasan dole yasamu abu
mai tsoka, dan tun rasuwar daddy ya maida kanshi
managing director din oil company dinsa. Mommy da
xee suma suna zaune suna jiran barrister yafara bayani..
Barrister shu’aibu ya fara da addu’an sannan ya fara
bayani yace tun lokacin da alhaji yakamu da ciwon
zuciyan yasan bazai dade ba, shiyasa yazo ya sameni ya
bani takardar nan, acewarsa duk ranar da baya duniya
yanaso acika masa burinsa dake rubuce anan……
barrister ya Bude yafara bayani kaman haka Ni Alhaji
Tanimu Bawa na damkawa ya’ta sumayya dukiyata kashi
hamsin acikin kashi Dari, sannan na bata matsayin
managing director na oil company dina da kuma gidan
da muke ciki duk na mallaka mata su. Acikin kashi
hamsin daya rage na bawa hajiya hadiza kashi ashiri,
kashi goma na bawa Zainab, kashi goma na bawa shehu
sai sauran kashi goma akai masallaci da gidan marayu.
Ina fatan iyalaina zasu cikamin burina , sannan banyi
haka danna matawa wani ko wata rai ba…..bissalam
Barrister ya gama karantawa sannan ya mikawa mommy
takardar, yace alhaji yamai xancen nan da shekera daya
atura driver yaje ya yaje ya dauko sumy daga
makaranta, mommy tace to insha Allahu xaai haka,
barrister yamasu sallama yatashi ya tafi. Baba shehu
kam fuskan nan babu annuri ko kadan, wato haka alhaji
zai sakamai duk irin kokarin dayama company dinsa
shine zai bashi 10% kawai acikin uban dukiya daya tare,
kuma harda ba yar’sa director din company din, yarinya
karama da komai bata sani ba, “Yayi murmushin
mugunta da tunanin halaka yarinya kafin ma ta shigo
gidan nan.. Hajiya kam bata damu da abunda tasamu ba
asalima abun duniya bai dameta ba, takai cinta daya
shine yadda alhaji ya bawa sumy komai daya mallaka
alhalin bama yar’sa bace ta jini, zata bar sumy ta zauna a
gidan amma tayi alkawarin making life dinta miserable.
Zee sai murna take, dan batama yi expecting samun
wani abu ba, tunanin ta daya shine Wacece sumy ya
take, itadai tasan sumy diyar alhaji da mommy ce amma
bata taba ganinta ba. *Bayan shekara daya* Sun gama
exams sai shirye shiryen tafiya suke, kursum dake wasa
da hanifa tace sis yanxu kina ganin idan nabi ki gidanku
ba matsala , nidai ina tsoro kar hajiya tamin wulakanci ta
kore ni, dan yanda kike ban labarin halinta na rashin
kirki nasan tana iya wa. Sumy tace karki damu nasan
yanxu ta canza tunda shekaru sun ja, kuma makauniya
ce ba lailai bane tasan kina gidan ba…… An turo driver
daga gida daukan su, sai sallama suke da kawayen su da
sauran malaman makaranta , suka shiga har office din
gimbiya hafsatu sukai mata sallama ta dauko wani dan
karamin box ta bude taciro wani hadadden pink
diamond da take ajiye dashi wajen shekaru goma sha
takwas da suka wuce ta damka wa kursum a hannu, tace
yaudai na cika alkawarin, kursum tace wanna na miye
kuma, gimbiya tace matar data kowa kine tun kina
jiririya tace in baki idan kin tashi tafiya kya iya siyarwa ki
samu na rike kanki, Kursum tai mata godiya sosai suka
fice, sun iske driver na jiran su, suka shiga mota… koda
suka shigo cikin gari sun tsaya suka shiga gidan Inna
sadiya (mai kitson su) suka gaishe ta sosai ta amsa da
fara’arta dama tasan da zuwan su, sumy ta mika mata
hanifa, Inna ta amshe ta sai wasa take mata tace karku
damu zan rike muku ita har kudawo daukan ta dama
nagaji da xaman kadaice. ….. Kursum tace Inna
mungode sosai, da munyi settling zamu zo mu dauke ta
yanxu ki rubuta mana number wayan ki yadda idan mun
isa gida zamu kira, dan yanxu ba waya ahannun mu,
“Suka bata kudi masu yawa wanda zai ishe su kafin su
dawo, suka kama hanya sai kanon dabo… amota sumy
sai kukan rabuwa take da hanifa, tabbas tasan barin
hanifa wajan Inna shine daidai dan tasan hajiya bazata
taba yadda da cewan tayi aure harta haihuwa ba, shiyasa
ma tabar ta hannun Inna kafin tasamu yi mata bayani.
…… Sun shigo kano kenan, sumy tace gaskia yaka mata
kindan gyara fuskan ki kodan kwalli ne kisa a ido,
kursum tace kinsan ni bana kwalliya asalima ko kayan
kwalliya ban dashi, sumy ta mika mata handbag dinta
tace bude kidau powder ki sha fa, Daidai lokacin da
kursum ta amshi jakar sumy wata katuwar motar petur
dake tafe ta bangaje motar su, kofan side din da kursum
ke zauna ya Bude ta fado kan titi rike da jakar sumy, sai
birgema take harta buge da wani katon dutse, sumy da
driver kam suna cikin mota dake kamawa da wuta sai
gangarawa motar take cikin daji harta bugu da wani
katon bishiya tayi exploding baammm kawai kake ji.
… :oops::oops::oops::oops: *Xarah Bêê* *Dedicated to
Bady social* ~Luv u all~ KURSUM By ~Xarah Bukar Page
~ Kursum ta farka taganta a gadon asibiti, duk jikinta ya
duk jikinta ya
kurje ga farin bandage da aka daura mata a kai dan
tsayar da jinin dake zuba, sai kuka da ihu take tana Kiran
sunan sumy. Da gudu wanda ya tsince ta a hanya ya
kawota asibiti yaje ya kira doctor malik yana gayamai
patient din ta tashi amma kaman bata hayyacinta…
Doctor ya shiga yana mata magana, amma ita kam ihu
kawai take tana Kiran sumy, ya tsira mata allurar bacci
ya fito. Yace Bala daka tsince ta babu waya ahannunta ko
wani abu dazai sa musan family dinta ko inda take zama,
Bala yace gaskia babu sai dai ko jakarta xaa duba, dan
koda na ganta akwai karamar jaka tare da ita, ya mikawa
doctor malik jakar, suka zazzage jakar daga kayan
kwalliya sai wani wallet mai kyau suka bude, pictures din
daddy kuda biyu Dana kursum ne aciki sai wani karamin
littafi an rubuta sumayya tanimu bawa. Doctor malik
yace ai wanan hoton alhaji ne, kuma ba shakka wanna
yarinyar yar’sa ce amma to ina taje harta samu accident,
ya kalli Bala yace mungode sosai da taimakon da kayi,
nasan family din yarinyan kuma yanxu zan kirasu awaya
suzo su dauketa, nine family doctor din su. Bala ma
yamai godiya sannan ya wuce. Doctor malik ya kira
mummy yamata bayanin komai, tace tabbas yar’ta ce
dan dama tun wajen kwana biyu daya wuce akaje dauko
ta daga makaranta, amma sukaji shiru basu iso gida ba,
an duba hanya an gano motarsu tayi hatsari ta kone sai
gawan mutum biyu akone kawai aka gani, kuma ance
mana tare suke da kawarta daga makaranta, doctor yace
kawar ce ta rasu da driver kenan, dan yanxu haka sumy
na nan kuma jikinta yayi sauki sai dan ciwon da baza’a
rasa ba, tayi mai godiya sosai tace zata turo baba shehu
yaxo ya dawo da sumy gida.. Kursum ta tashi sai dai ba
ihu yanxu sai kuka kawai take, doctor ya shigo yana
gayamata ai kawarta da sukai accident tare ta rasu dan
haka yanxu ta shirya kanta dan kanin mamanta yazo
daukanta suje gida, ya dauko wallet da pictures din
yabata hade da jakan gabadaya sannan ya bata
magunguna wanda zata sha, yace sumy ki tabata kinsha
maganin nan saboda your body is still weak, tace to
nagode sosai doctor, Kursum kam hankalinta duk ya
tashi shikenan sumy ta rasu yanxu ya zata yi , gashi
kuma ana tunanin itace sumy alhalin kuma sumy ce ta
rasu ba kursum ba, amma kuma dole ne ta tsaya a
matsayin itace sumy kodan ta samo wa hanifa gata da
yancin ta. Ta fito ta iske baba shehu na jiran ta, dukda
batasan shi ba saida tace kawu ina wuni, ya bita da
kallon banza sannan ya amsa a kwasale yayi gaba
abunshi tana binshi a abaya, a zuciyan ta tace tab wato
family dinnan babu sauki, lailai zata daura damara dasu
dan kuwa baza tai tolerating ko wana nonsense ba. Suna
isa gidan yayi parking mota suka fito, masha Allahu
kawai take fada dan kuwa bata taba ganin katon gida mai
kyau kaman wannan ba, wani tausayin sumy taji, Allah
yaji kanki kawata kuma insha Allahu hanifa sai ta samu
gatan xaman gidan nan Daram. … Hajiya da xee suna
zaune a parlour suna jiran isowan su sumy, baba shehu
yafara turo kofa sai kursum abaya, tana karasowa cikin
palon xee da mum suka tashi tsaye afirgice suna kallon
ta……. Nima afirgice nayar da biron rubutuna dan na
tsorata da yanayin mom, ita da bata gani miyasata firgita
haka..:oops::oops: *Xarah Bêê* *Dedicated to Bady
social* ~Luv u all~ kursum 36 to 50 Posted by XARAH
ABUBAKAR on NOVEMBER 13, 2016 KURSUM By ~Xarah
Bukar Page ~ Kursum ta dukusa har kasa ta gaishe su,
hajiya kam hankalinta bai tare da ita, mamaki kawai take
yadda sumy ta zama kekkyawan budurwa dan koda
tasan ta abaya ba wani kyau garetaba sai fari kawai
…….abangaren xee kuwa faduwan gabanta sai karuwa
yake, yaudai duk takama da kyawuta taga Wace ta fita
kyau da komai, wani irin tsanar kursum taji azuciyanta.
…….:evil::evil: Hajiya amsa adakile, ta kwallawa samira
kira, taxo da sauri tana gani hajiya, tace kikai sumy can
gidan baya kusa da dakin masu aiki sai ta zabi dakin data
ke so, samira tace toh. Kursum da haushi hajiya ya
isheta ta, ta karaso cikin palon ta xauna tace tunda gidan
ubana ne babu wanda ya isa yasani xama dakin masu
aiki, dan haka nima a main house zan zauna, ta tambayi
samira ina dakuna suke da kuma wana dakine yafi kyau
da girma a gidan, tace antee dakuna asama suke kuma
dakin daddy yafi kyau da girma tunda ya rasu babu
wanda ya shiga, kursum ta mike tsaye ta karewa hajiya
da xee kallon sannan tace samira kaini dakin daddy dan
yanxu yaxama nawa in ga wanda ya isa ya hanani…:?
Hajiya kaman tafasa ihu dan takaici, lailai yarinyan nan
wato ba kyau kadai takara ba harda baki tayi, yazama
dole insa mata ido saboda….. Da daddare Abba da
umma ke zauna a parlour sai hira suke suna darawa,
umma tace gaskia yakama in leka hajiya mun dade
bamu haduba aiki yamin yawa. Abba ya kalleta yace wai
ke bana hanaki shiga harkar hadiza ba, kinsan sarai
banason matan nan saboda Sam bata da mutunci, kowa
yasan itace sanadiya mutuwan mijinta , umma tace haba
alhaji ya za ai kace haka, lokacin mijinta ne yayi……. bata
ida magana na ba yazid ya shigo da sallaman sa, sanye
yake da uniform dinsa na pilot wanda ya kara fito da
ainuhin kyau shi, ya fada kan kujera yana wai na gaji,
umma ta kalle shi tace my son hope dai you are okay,
banason ganinka da stress , Abba yayi tsaki yace wlh
maryam ke kike kara sangarta yaron nan, idan baije aiki
ba so kike yana xaman gida ko me, shida wataran zaiyi
aure ya kula da iyalansa……yauwa nama tuna shehu
yazo min da batun diyar shi Zainab dinnan kwana kin
baya, kun dade kuna soyyaya amma baka ma xancen
aurenta kuma ma dai at your age ya kamata ace kafara
tunanin fara iyali. Yazid ya tamke fuska, yace gaskia abba
ni ban shirya aure ba dukda inason xee, koda zanyi aure
sai nan da shekera daya, ya tashi a fusace ya wuce dakin
shi. Abba ya kalli umma yace kinga halin son dinki ko ,
tace karka takura mai tunda yace ba yanxu ba, ni xee
dince ma banaso ya aure Sam bata da kamun kai, yace
to ina ruwanki bashi ya gani yanaso ba kuma ni banga
rashin kumun kan taba, babanta abokina ne kuma yana
da kirki sosai, umma dai shiru tayi bata ce komai.
*************************** Bayan kwana biyu
jikin kursum ya warware ta samu sauki sosai tayi fresh ta
kara kyau, sai dai zaman kadaice da take babu mai shiga
harkanta a gidan sai samira kawai dan ita ke kawo mata
abinci har daki, tayi tsaki ta kwallawa samira kira, taxo
da saurin ta tace antee kina bukatan wani abu ne,
kursum tace babu komai tambayan ki zanyi wai babu
masu shigowa gidan nan ne, naga tunda na zo banji an
shigo ba, gida sai kace kurkuku……samira ta gyara zama
tace antee ai indai gidan nan ne ana wata biyu babu
wanda ya shigo, yaya yazid kadai ke xuwa wataran
umman shi takan zo wajan hajiya dan kawarta ce sosai,
kursum ta nisa tace Waye kuma yaya yazid wajan wa
yake zuwa, samira tace ai saurayin antee Zee ne kuma
suna son junan su sosai bare ma antee zee tana iya
mutuwa akanshi, kursum ta bata rai tace tashi ki fita ban
tambayi ki wannan ba, sumsum ta tashi ta fice da
saurinta……ita ko wani farin ciki taji ta maimaita sunan
yaya yazid, gaskia sunan ya mata dadi. ..
:mrgreen::mrgreen: Da yamma barrister shu’aibu yazo
har gidan ya damkawa kursum takardun gidan da komai
data mallaka amatsayin itace sumy, sannan yace mata ta
shirya gobe zata fara aiki acompany din babanta
amatsayin managing director, tamai godiya sosai ya
masu sallama ya fice. Hajiya dake gefe sai hararan
kursum take ta eye glass dinta (oho dai batasan kina
yiba)…… Baba shehu ma ya cika yayi fam , ya kalli
kursum yace yanxu sumy abunda ya kamata shine
kibarmin komai a hannun na tunda na dade in charge,
xan naima maki admission ki shiga university tunda iya
kacinki secondary skull kuma baki da experience na
managing babban company, kursum shiru kawai tayi
batace komai ba ta haura sama abunta. …. Baba shehu
yayi murmushin samun nasara da alaman yarinyar ta
yadda da Zancen shi….:mrgreen::mrgreen: Washe gari
da safe kursum ta shirya cikin hadadden pink and white
suit mai shegen kyau na kardashian collection tayi
rolling kanta da karamin pink veil mai kyau, ta dauki
handbag karamin mai kyan gaske mai tambari versace
tarike a hannu, tabi stairs tana sauka atsanake hankalinta
kwance, ji tayi an bangajeta har tana naima fadowa kasa,
tana daga kai tayi ido hudu da xee, da ganinta kasan she
is high danko kayan jikinta bana kirki bane, xee tace ke
dabbar ina ce ko bakiga ina hawowa bane, banza
bakauya taja tsaki ta wuce, kursum kasa cewa komai tayi
ta wuce abunta tana mamakin hali irin na xee ta tabbata
daga club take kuma till dawn tayi, dan samira ta taba
gayamata xee bata fiya kwana agida ba, bata da aiki sai
clubbing, kuma baba shehu da hajiya suna sane amma
babu mai kwabarta…. Allah ya shiryeta kawai tace ta
karasa waje ta shiga hadaddeyar motar ta kirar 2016
Buick Cascada……….driver yaja ta sai company. Babban
Company ne mai huge twenty-story office building, all
curved glass and steel, an architect’s utilitarian fantasy,
with Tanimu bawa oil & investment written discreetly in
steel over the glass front doors. Tana shiga officials din
suka karaso suna gaishe ta tare da mata congrat as the
new MD , ta amsa da fara’arta tana masu godiya, Mr
dabo ya karaso gabanta yace madam am your PA let me
excort u to ur office, ta bishi har office din amma sai tayi
mamakin :oops::oops: ganin office karami kaman gidan
kaji, ta juyo tace Mr dabo how comes ina MD zaa bani
karamin office haka, yace madam kiyi hakuri ba laifin
mu bane, kawunki yace abaki nan tunda ba wani sanin
kan aikin kikayi ba, kursum tace lailai ma baba shehu
wato itace ta dace danan, aikuwa zanyi maganin shi….
..tace Mr dabo kaini office din baba shehu yace toh…
Suna shiga taga office dinshi tankameme kaman aljarnar
duniya komai na office din ya burgeta tace Mr dabo nan
nake so as my office ka kwashe tarkacen kawo ka canza
mai wani office sannan kuma ka kawo min file din ko
wana employee zan fara aiki na, yace to angama madam
Ya fice. … Kursum zauna kan office chair tana swivel din
kanta, sumy kawai take tunanin, Allah sarki kawata da
yanxu kice anan bani ba, Allah yaji kanki insha Allahu zan
rike maki hanifa tamkar nina haifeta… Banko wan kofan
da akayi ne ya firgita ta, baba shehu ne fuskar nan
tamke, babu annuri ko kadan, yace “I won’t let you
disrespect me, I’ve been working day, noon, and night
for this company, busting my hump since before you
were born.” who are you to throw me out of my office?
Kursum ta mike tsaye ta karemai kallon sannan tace, the
early bird doesn’t always catch the worm, Warming a
seat in this company doesn’t mean you’re working, baba
shehu daya gama kulewa ya nunata da yatsa yace, how
dare you, you snot- nosed brat! Kinsan dawa kike
magana kuwa, ta kara kare mai kallo tace, I dare because
I’m the heir to my father’s company. From now on, I’m
going to monitor the performance of every employee;
including you. No, not including, but beginning with
you. If you don’t like it, the door is wide open enough.
Understand? or should I draw you a picture?” Baba
shehu kasa cewa komai Cox kalamanta ba karamin
girgiza shi yayi ba, sai yanxu ya tabbatar kawar da
yarinyan nan will not b easy, amma dole ne ya naima
mafita kafin taza ma doom dinshi Hmmmm *Xarah
Bêê* *Dedicated to Bady social* ~Luv u all~ KURSUM By
~Xarah B Page ~ Zaune yake a office dinsa yana waya da
xee tana ta zuba mai shagwaba kaman tana gabanshi, ta
turo baki tace baby kace zaka zo Jiya baka zo ba I
couldn’t sleep Cox I was thinking of u kuma your fone
was off, ta kara shagwabe fuska, yace am sorry dear I
was kinda busy ne xanzo anjima, kar kiyi fushi kinsan I
love you alot……….Abba ne ya shigo office din yasamu
kujera ya zauna jiran ya gama wayan, yazid yace baby
xan kiraki later, tace toh my love, kisses & hugs dear ……
Abba yace miye amfanin love dinnan da bai da future,
ance kayi aure kace you are not ready, kudai yaran
zamani halinku sai ku, yayi murmushi yace abba abar
xancen auran nan plz, nace muku am not ready, abba
yace kai ka sani yanxu dai ga document din shares din
mu na Tanimu bawa oil & investment company, Ina so
gobe ka kaiwa new MD na company din tasa hannu, ya
dire mai document din ya fice abunshi , yazid ya bude
yana dubawa yace abba kenan wato dan aikin nan ma
bazai tura wani ba dole dai ni zai aika……..:evil::evil::evil:
Hajiya ce zaune a falo rike da sandar ta, tasha bakin glass
dinta, tunanin kawai take yadda za ta fidda sumy daga
gidan dan Sam bata yarda da ita ba, tana suspecting
akwai abunda take boye masu, tasha leka dan karamin
ramin dake jikin kofan dakin ta, ta ganta rike da wani
hoto tana kuka tana cewa ki yafeni hakan da nayi shine
kadai mafita, hajiya ta tashi da saurin ta haura sama, ita
dai tana son sanin wana mafita sumy take nufi, ta bude
dakin kursum ta shiga ta fara bude bude da binciken
amma bata ga komai ba, side drawer na gadon taxo
budewo ta ji muryan samira abakin kofa tana cewa
Antee kin dawo ne, da sauri ta maida glass dinta ta fito
daga dakin, samira tace hajiya kece aciki ashe, ko
kallonta bata yi ba ta bi gefe ta wuce tana dafa bango
dan karta fadi…….. Samira mamaki ne ya cika ta, matar
da bata gani miye na shiga dakin daba nata ba kuma da
alama ma bincike take, ikon Allah
kenan…..:oops::oops::oops: Kursum zaune a office tana
hada files waje daya dan yamma tayi zata wuce gida, ta
kira Mr dabo tace mai ya kwashe duka files din ta gama
dubasu sannan tamai sallama ta wuce parking lot
tasamu driver na jiranta a mota, ta shiga ya ja…. Sun
hau kan babban titi driver ya hango hold up sosai, babu
alaman motoci na motsi, yace madam hold up dinnan
yayi yawa amma akwai wani one way gaba kadan, bari
inbi damu tanan, kursum tace toh duk yadda kayi ta
cigaba da kallon sabuwar wayar da ta siya dazu kirar
iphone 3G king’s Button… Daidai lokacin da driver ya
danno kan motar, dai dai lokacin da shima ya karyo
kwana sai ji kake kiiiiiiiiiii……..ko wannan su yaja birki,
kiris ya rage suyi accident.. Sanye yake da uniform dinsa
na pilot yasha kyau da alama shima daga aiki yake ya fito
fuska tamke, tun kafin ya karaso driver ya fito da sauri
yazo yana bashi hakuri, amma ina shi kam baisan hakuri
ba sai zazzaga masifa yake yace kai wawan ina ne, koka
taba ganin inda akabi one way, hanyar da ake fita shine
kake shirin shiga tunda baka da hankali, driver dai sa
hakuri yake bashi…. Tana daga mota take jin hayaniyan
su, wato driver na bashi hakuri shi ko guy din kara
harzuka yake, lailai ko zata yi maganin shi, ta bude kofar
motar ta fito da tafiyar ta mai daukan hankali ta karaso
ta bayan shi tace Mr man ko Kaine devil himself sai haka,
ana baka hakuri kana kara harzuka, toh karka hakura
idan titin taka ce sai mu gani, taja uban tsaki, ya juyo a
fusace fuskan nan ba annuri, ya kare mata kallo tas yace
ni kike gayawa wai maganar banza , ita ko hankalinta bai
ma jikinta dan ba karamin tsorata tayi ba, tabbas babu
tantama wannan shine wanda sumy ta aura ya yaudare
ta ya gudu, sau daya ta taba ganin shi amma bazata taba
manta wa da fuskan shi ba, ba

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment