Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiri ta saita kanta, ta
wurga mai harara tace kwarai kuwa dakai nake kai din
banza Waye kai da bazaka hakura ba, Driver mu tafi plz
karya hakura din yana iya kwana anan tunda hanyar tasa
ce, ta juya ta barshi nan tsaya yana mamaki karfin hali
irin nata, lailai ko sai ya koyawa mata hankali, ya ga
ubanwa ya tsaya mata da har ta isa ta gayamai magana,
yayi kwafa yaja motar sa yabar wajen. Suna cikin mota
tana tunani iri iri, gaskia dole ta naimo Mr devil kodan ta
koyamai hankali, wato hankalin shi kwance har wani
kyau yakara, kibiyar tsanar shi ce ta soki zuciyar ta, tayi
murmushin mugunta afili tace count down to my
revenge has ended, it’s time for pay back Mr devil……
Driver yace madam mun iso fah naga kinata magana ke
ka dai, tace ahh ba komai barin sauka saika gyara
parking, yace toh. Ta turo kofar parlour da sallaman ta,
hajiya da xee na zaune ko kallo bata ishe su ba, tana
gaishe su ko amsawa basuyi ba suka bita da harara, ta
haura sama abunta…. Xee da taci uban kwalliya da wasu
matsasu kayan dake jikinta, ta kalli hajiya tace ni wlh na
tsani yarinyan nan ga shegen kyau kamar aljana, ni
wataran kina min kama da ita ma, hajiya taja tsaki tace
ke daina hadani da mayya ni kaina na fiki tsanar ta, na
gayamaki tsinto ta Alhaji yayi a titi, ko jini ban hada da
ita ba……..zata kara magana hajiya ta tsayar da ita, tace
surutun ki ya isheni haka, ba kince saurayin ki zai zo ba,
toh sai kiyi zaman jiran shi ai, nikam na tafi daki……xee
tace haba hajiya ki tsaya ku gaisa mana, tace nikam
bacci zanyi ta haura sama abunta. Tun komawar shi
gida, sallah kawai ya iya gabatarwa, ya rasa inda zaisa
kanshi yaji dadi, abunda ya faru dazu gani yake tamkar a
mafarki, wai yau shine little witch (sunan daya laka
mata ) tama rashin M, lailai ko saiya making life dinta
miserable sai tayi dana sanin cin zarafi da ta mai, wani
irin tsanar ta yake ji, ya mike ya naushi bango a fili yace
Game on little witch……….:evil::evil::evil: Hmmmm
tashin hankali Masu karatu muje xuwa….. (Dedicated to
Bady social KURSUM by ~ Xarah Bukar Page ~ Tana shiga
dakin ta ganshi a hargitsi da alaman an shigo an mata
bincike, ta kwallawa samira kira, taxo da saurinta tana
antee har kin dawo kenan, kursum tace waya shigo min
daki naga komai ba daidai ba, samira ta sosa keya tace
Antee nima bansani ba amma dai naga hajiya ta fito
daga dakin dazu…. Kursum tace hajiya kuma, ita da bata
gani miya shigo da ita dakina, tayi shiru can dai tace
tashi ki tafi zan naime ki anjima, samira ta tashi ta
wuce….. Ta tashi ta gyara dakin ta kimtsa komai daidai ,
sannan ta bude side drawer ta dauko picture dinta ita da
sumy da pink diamond dinta wanda su kadai ta tsira
dasu ranar da sukayi accident da yake cikin aljihun
trouser dinta tasa su, ta kalli pic din tana hawaye,
rayuwarta da kawarta kawai take tunawa, tayi missing
dinta sosai , yanxu tunanin ta daya shine yadda zata
dauko hanifa daga Bauchi, ta tashi ta dauko wani
karamin book din sumy inda Inna sadiya ta rubuta masu
number ta akan in sun iso zasu kira ta, da sauri ta
kwashe lambar tayi dialling………ringing daya biyu Inna
sadiya ta dauka da sallaman ta, kursum tace Inna ina
wuni ya gida, ya hanifa, nasan baki gane mai magana ba
kursum ce…..Damm gaban Inna ya fadi gaba daya ta
gigice dan bata taba tunanin kara jin muryar kursum ba,
tace kursum dama baki mutu ba , aini dana je aiki
makaranta gimbiya ke cemin ai kunyi hatsari kin rasu,
kursum tace eh wlh munyi hatsari amma sumy ce ta
rasu bani ba. Inna tace Allah yaji kanta, yanxu hanifa ta
zama marainiya, kursum nace haba Inna kar kice haka,
nice uwar hanifa yanxu bazan taba bari tayi maraici ba,
insha Allahu dana samu lokaci xanzo in dauke ta, Inna
tace to babu damuwa sai kinzo, gatanan kuwa tayi bubul
da ita, kursum tayi murmushi tace Inna karki gayawa
gimbiya ban mutu ba, kibarta amatsayin ni na rasu ba
sumy ba, Inna tace toh duk yadda kikace, sukayi sallama
ta ajiye wayan….. Driving yake hankali kwance, fuskar shi
ba yabo ba fallasa, yasan rigimar zee idan baije wajen
taba zai sha mita, ya iso gidan mai gadi ya bude mai gate
ya shigo ciki…… xee data cika tayi fam a parlour, sai tsaki
take ja, wajen awa hudu kenan tana jirashi ta kira layin
shi switch off, ranta duk abace:evil::evil::evil: taji karar
doorbell , ta kira samira taje ta duba waye, ta bude ta
ganshi tsaye yana mata murmushin, tace yaya yazid
sannu da zuwa ashe Kaine, yace yauwa samira ya karaso
ciki, tana jin muryar shi ta tashi da sauri tana kukan
shagwaba taje ta rungume shi. yace haba zee kukan mi
kike haka, ta kara fashewa da kuka tace ba Kaine kaki
zuwa ba tun dazu nake jiranka, yace baby kiyi hakuri
yanxu nazo ai forgive me ? Kinji baby na yakara
rungumeta tsam yana shafa bayanta, ita ko sai sauke
ajiyar zuciya taje.. Basu ankara ba sai ji sukayi ana tafa
masu lokacin guda suka saki juna suka juyo suna kallon
ta, sanye take da black jeans da yellow top, sauko wanta
kenan zata je kitchen ta naima wa kanta abun ci ta gansu
makale da juna kaman ba gobe…. ta masu kallon up &
down, tagane guy din sarai shine Mr devil wanda suka
samu clash dazu, tace lovers of the year duk iskanci da
kukeyi awaje bai ishe ku ba har sai anxo ana nuna hali a
gida:?:?, shi kam yazid kasa magana yayi dan mamakin
ganinta yake for d second time kuma a gidan nan, ta
karaso gabanshi ta nuna shi da yatsa tace shameless
man haka dai zaka kare da bin mata, dan iska kawai, xee
data bata rai jin kalaman da kursum take gaya masu
yasata karasowa da niyyan wanketa da mari amma ina
kafin takai mata marin kursum ta rike mata hannu gam
tace don’t you dare sis, jikina yafi karfin duka, kuma am
advicing you to stay away from diz man cox he is just
using you for his own selfish reasons, tayi tsaki ta wurgar
mata da hannun ta wuce kitchen abunta….. yazid yace
baby ina kuka samo witch dinnan ne, I hate her with
passion, she is rude, zee tace diyar daddy da hajiya ce,
shegiyar yarinya, mayya, Yar titi, agidan marayu daddy
yasa mota, tana school ne sai yanxu ta dawo gida ……:?
ya nisa yace baby barin wuce kawai, am not in a good
mood, tace haba yaya daga zuwan ka zaka tafi, indai
akan abunda ta fada ne kayi hakuri zan mata magana ,
yace sorry zee but I have to go, ya mata peck a cheeks ya
wuce rai abace:evil: kursum da take hango su ta kitchen
ta kara mata rai, ko miye na mata peck kuma in ba
iskanci ba, zuciyar ta namata zafi …… (su kursum da
karfin hali, mutum da budurwa shi karya soye ) *Xarah
Bêê* kursum 51 to 52 Posted by XARAH ABUBAKAR on
NOVEMBER 13, 2016 KURSUM by ~ Xarah Bukar page
Abincin ma kasa Ci tayi dan haushi, ta fito zata wuce
dakinta zee ta finciko ta, tace ke yar titi ki fita daga ido
na, ke har kina da bakin Kiran mutum dan iska, wayasan
iskanci da kikayi a makarantar da aka jefar dake, ina baki
last warning ki fita daga rayuwa ta…… kursum bata ce
mata komai ba illa gyara rigarta da tayi ta wuce abunta,
zee tayi kwafa tace lailai ma yarinyan nan, ya zama dole
in binciki past dinta, xanje har makarantar da aka riketa
in samu wani abu akan rayuwarta. … umma ce zaune a
daki tana duba new designs dinta a laptop, yayi sallama
ya karaso ya fada kan gado, tace my son daga ina haka a
darennan, naga ma ranka abace, hop all is well ? yace ba
komai dama wajan zee naje, nan take umma ta bata rai,
ita dai bata kaunar zee ko kadan, dan farin cikin son
dinta take nuna tana sonsu tare, ya nisa yace umma
dama hajiya hadiza nada ya’ budurwa ?? Dam gaban
umma yafadi dan tasan tabbas hadiza nada diya kuma
yanxu ta isa zama budurwa, tace my son hajiya bata da
diya tun wajan haihuwa yar’ta ta rasu, nasan dai alhaji
yayi adopting yar yarinyar daga gidan marayu, zaman su
yaki dadi da hajiya shine yakai ta wani boarding skull….
yazid yace ta dawo ai, ita nagani a gidan dazu, yarinyar
sai rashin kunya da raina mutane, umma tayi dariya tace
haba son daga ganin yarinya sai aibata ta, Allah umma
dagaske nake sau biyu muna haduwa tana min fitsara,
sam bana sonta:?:? umma dai dariya kawai take yadda ya
dage shi baya sonta, sai kace ance ya so ta, tace son
abbanka ya wuce England dazu, yayi trying line dinka
switch off, yace eh wlh I was so busy ne, zan kira shi
gobe, tace to yace dai karka manta gobe ka kai ayi
signing document din daya baka dazu, yace toh umma
barin je in kwanta good nyt, okay nyt my son. ********
sauri take ta wuce office dan yau ta makara kuma suna
da meeting, harta fito daga daki ta kara komawa da
sauri, ta bude side drawer ta dauko pink diamond dinta,
tayi murmushi, ta san koba komai tana da abunda
uwarta ta ajiye mata, ta saka pink diamond din jikin
chain din wuyanta, ta fito tayi kicibis da hajiya abakin
kofa amakale tace hajiya ina kwana, mai kikeyi abakin
kofana ? kina son wani abune ?? lokaci guda take jero
mata tambayoyi, hajiya data gigice ganin diamond din
wuyanta yasata fara kame kame, tace daban kwana ba
zaki ganin, shegiyar yarinya toh wuce wa xanyi ta wuce
fuuuu har tana naiman faduwa, kursum dake tsaye tana
mamakin hajiya, anya matan nan bata gani kuwa, ta rufo
dakin ta wuce. hajiya ce a daki sai sake sake take da
tunani iri iri, ina yarinyar nan tasamu diamond din nan,
nasan ni kadai keda irinshi kuma na bayar dashi dadewa,
wayarta ta dauko tayi dialling line din mairo dan tasan
ita kadai ce zata bata amsar komai, ringing daya umma
ta dauka, kafin ma su gaisa hajiya tace mairo kizo gida
inason ganinki, ina son muyi magana akan abunda ya
faru shekara goma sha takwas da suka wuce…… Dam
gaban umma ya fadi, :oops::oops::oops:dama tasan zaa
rina. *Xarah Bêê* *Dedicated to bady social* KURSUM
by ~ Xarah Bukarêê page Tana isa boardroom ta wuce,
“suka fara meeting, dama ita kawai ake jira, “baba shehu
sai zuba bayani yake, ita dai bata gane komai ba har aka
gama, ta koma office dinta. baba shehu ne yashigo office
din, sai wani fara’a yake kaman dagaske, “kursum tace
baba da kanka, ayda ka turo wani, yace “nida ya’ta ai
dole inzo gaisheki da kaina, ya mika mata check din
makudan kudi tayi signing, ta karba ta duba tace “baba
kudin sunyi yawa, me xaai dasu ? “ya sosa keya yace
dama wasu sabbin machines na company mukeso
importing dan wanda muke dasu sun fara lalace wa. tace
toh shikenan amma dai xan rage kudin sunyi yawa, tayi
signing ta mika mai, bai ji dadin abunda tayi ba ya amsa
ya fice rai abace, ita dai kursum bata yadda da fara’arsa
ba kwanan nan sabanin da idan ta gaishe shi sai harara
da zargi yake wurgo mata. zaune yake a office yana duba
takardun dake gabanshi, can ya hango papers din shares
dinsu da abba ya bashi yakai T. b oil & investment
company asa hannu, da sauri ya mike ya kwashe papers
din tare da car keys dinshi ya fice Da sauri yake driving
har ya iso company din, ya tambayi daya daga cikin
workers din inda office din MD yake, suka kai shi office
din Mr dabo, da sauri mr dabo ya tashi ya gaishe shi dan
yasan family dinsu ne major share holders din company
din, “Yazid ya bashi hannu suka gaisa dan ya sanshi sosai
mutumun abba ne, “yace mr dabo ashe kaine new MD
din, dabo yayi dariya yace ai bankai matsayin nan ba,
nine dai personal assistant din new MD din, barin
gayamata tayi bako, da sauri ya fice ya dawo yace kana
iya ganinta yanxu, “Yazid yace okay thanks….. Hankalin ta
kwance sai buga game take abunta, yayi knocking kofa,
ko dagowa batayi ba tace come in, yana karaso ciki ya
ganta yaji mugun takaici, dama witch dinnan itace MD
din, lailai ko yau idan tamai fitsara bazai barta ba, bai
ankara ba yaji tace can I help you ? ya kara kallonta wato
ko dagowa baza tai ba game dinta kawai take, lailai ko
zanyi maganinta. …… Papers din hannun sa ya watso
mata a fuska, da sauri ta dago suka ido, sai da gabanta ya
fadi dan ba karamin kwarjini ya mata ba, ta harare shi,
ta daure tace “miye haka zaka watso min papers, have u
lost your manners ? ya bata rai, “yace aiki kika zoyi ko
game, ko an gayamiki wasan yara ake anan, ta murguda
baki tace “bansani ba ina ruwanka, dariya ma ta bashi,
yace “signing zakiyi akan papers din” ta yamutsa fuska
tace na miye , harara ya wurga mata yace baki iya karatu
bane, “ta hada papers din waje daya ta karanta ta kalle
shi tace “ashe kuna da shares a company dina” yayi
banza da ita , tayi murmushi ta tashi ta karaso gaban shi
ta ajiye mai papers din tace ” banda pen ( biro) balle inyi
signing, kana iya komawa da papers din, next time idan
xaka zo saika hado da pen ta zauna taci gaba da game
dinta… Bai ji haushi abunda tace ba, ya tashi yadau
papers din yai murmushi ya kalle ta yace” I have nothing
to say amma keda kanki zaki ne me papers din, ya fice
daga office din. Mr dabo ne yashigo office din da saurin
sa yace madam lafiya dai koh, naga bakonki ya fita a
fusace, ta yatsine fuska ta gayamai abunda ya faru, yace
“madam ai kinyi kuskure babban saboda sune major
share holders din company dinnan, idan suka kwashe
shares dinsu company dinnan zai zama bankrupt kuma
zaiyi affecting oda share holders, “kursum da hankalinta
ya tashi tace mr dabo yanxu ya xaai kenan dan papers
din na hannu shi, “yace abu mai sauki tashi zakiyi muje
har office dinshi ki bashi hakuri ya baki papers din, “tace
to muje ” handbag dinta ta dauka da sauri suka fice…
umma ce ta shigo parlour gidan da sallaman ta, shiru
babu wanda ya amsa “can ta hango zee zaune tana
kallon tv da alama batasan ma ta shigo ba, ta karasa ciki
tace baki ji ina sallama bane , ta juyo ta kalle ta aya tsine
tace banji bane sorry, umma tare kuke da yaya yazid ?
umma tayi banza da tambayan tace ina hajiya ? zee tace
bansani ba amma ki dubata sama, ta cigaba da kallon tv
abunta. …..Umma tayi kwafa ta haura sama, tana
takaicin hali irin na zee, sam batayi sa’ar suruka ba.
hajiya ce zaune a daki sai kuka take tana dana sanin jefar
da yar’ta datayi, babban tashin hankalinta shine rashin
gayawa daddy cewan yar’su bata mutu ba harya rasu,
kuka kawai take tana dana sanin bakin halin data shuka a
rayuwarta, “da sauri umma ta karaso wajanta tana
hadiza lafiya, meke damunki ? hajiya tayi shiru tana
tunanin yadda zata gayawa umma ta ga pink diamond
dinta awuyan sumy, saboda kowa yasan makauniya ce,
ta nisa tace “shekarun baya da suka wuce nayi niyyan
jefar da ya’ta, amma kika dauketa kika kaita inda zaa
raineta harta girma, “ta kara fashewa da kuka tace mairo
ina ya’ta kursum take ? kina da labarinta kuwa ?? umma
ta gyara zama tace “hadiza ni bansan inda yarki take ba,
makarantar dana kaita munyi dasu idan takai shekara
sha takwas zasu sallameta, kuma yanxu ko ta cika sha
takwas dan gimbiyar makarantar ta kirani ta gayamin
tacika alkawarin dake kanta na bawa yarinyar diamond
din da kika ajiye mata. … agigice hajiya ta kalle ta, tace
mairo ki taimakeni ki kiramin gimbiyar awaya, ko zata
San inda ya’ta taje ranar da suka sallameta, umma tace
to barin kirata muje, dan nima tunda nakai yarki
makarantar ban yanke zumunci da gimbiyar ba, dan
nasan wataran zaki nima yarki….. Tasa masu call din a
speaker, ringing daya biyu Gimbaya hafsatu ta dauka da
fara’arta, suka gaisa da umma, “umma tace dama zancen
kursum ne, ko kina da labarin inda take yanxu, gimbiya
ta nisa tace “ai kursum Allah yayi mata rasuwa tun
lokacin da muka sallame ta, kawarta tabi suje gidansu a
kano shine sukayi hatsari a hanya, ita ta rasu amma
kawar bata rasuba, “Dam gaban hajiya ya fadi, shikenan
yar’ta ta rasu” umma tace gimbaya ya sunan kawarta ?
tace sumayya tanimu bawa sunan ta, umma tace nagode
sosai gimbiya sukai sallama. Rudani, tashin hankali,
lokaci guda hajiya ta shige su, ta kalli umma da jajayan
idonta da suka rine tsaban kuka tace “babu tantama
sumayya gidan nan ce kawarta, tare sukayi accident
kursum ta rasu, kuka kawai take tana salati , taga samu
taga rashi, “umma sai bata baki take tana kwantar mata
da hankali, amma ina kuka take , bata ankara ba sai gani
tayi hajiya ta fadi kasa sumammiya.
:oops::oops::oops::oops::oops::oops: Xarah Bêê kursum
53 to 55 Posted by XARAH ABUBAKAR on NOVEMBER 13,
2016 Kursum by ~ Xarah Bukar page Umma ta tashi ta
dibo ruwa ta yayyafa mata, amma shiru hajiya bata tashi
ba, a gigice ta fito ta kwalla wa zee kira, zee tazo da
saurinta tana “umma lafiya kuwa?? tace ba lafiya ba
maza kira doctor malik, hajiya ba lafiya, “da sauri zee
tayi kiran layin doctor tana gayamai abunda ya faru,
“doctor yace ni yanxu am very bixy , zan turo
ambulance yanxu akawo ta asibiti, “zee tace toh dr.
muna jira. Ba’a fi minti biyar ba, ambulance yazo suka
wuce asibiti gaba daya, direct emergency aka wuce da
ita, umma da zee na daga waje hankalinsu duk atashe,
umma tace zainab kin gayawa shehu muna asibiti
kuwa? , tace eh yanxu na kira shi yana hanya zuwa ma,
“umma tace tun dazu nake trying line din yazid ban
samu ba, gwada kira min shi ko zaki samu, “zee tace
nima dai tun dazu nake trying line dinshi ban samu ba,
amma barin je office dinshi inji ko lafiya, umma tace toh
ki gayamai ina naiman sa yanxu nan, tace to ta wuce.
Zaune yake a office yana sipping coffee, yana danna
laptop dinshi hankali kwance, ya dauka papers din ya
kare masu kallon, yayi murmushi ya ejiye su gefe,
secretary dinshi suzzie ta shigo, “tace sir a lady is here to
see you, “yace owkay tell her to come in” suzzie ta fita
tace madam u can go in, kursum tace tnx, ta juyo ta kalli
Mr dabo “tace karna batama lokaci, kana iya komawa
office, idan nagama zan naimi taxi indawo, yace toh
madam sai kinzo, ya wuce. Ta turo kofan tashigo, wani
irin kamshi mai dadi da sanyi suka mamaye ta, offfice
din mai girman gaske dan har yamafi nata, dago wa yayi
ya kalleta yayi murmushi ya cigaba da abunda yakeyi, “ta
karaso tace mai sannu taja kujera zata zauna, ya dakatar
da ita yace “baa zaman min a kujera saida izini ni na,
kuma miya kawo ki nan?? Tayi shiru ta koma gefe ta
tsaya, “tace humm mm dama papers dinnan zaka bani
inyi signing” yayi banza da ita kaman beji abunda tace
ba. Har kusan minti biyar baice komai ba kuma bataga
alaman zaice ba, ga tsayuwar ta isheta daurewa kawai
take, “kashe laptop din yayi ya tashi ya dibi wasu files, ya
kalleta yace kina iya zaman a couch din can kiyi game
din da kikasaba, ni yanxu ina da important meeting da
zanyi attending” bai jira abunda zata ceba ya fice. Ba
yadda ta iya dole ta jira shi, ta bude jakanta ta dauko
wayanta ta fara game, har kusan 30mins bai dawo ba,
gashi ta gaji da game din, ta kwanta ta fara bacci abunta,
“bayan awa daya ya shigo ya cigaba da aikin gaban shi,
yama manta da wata a office din, can ya dago zai dauki
wasu files ya hango ta kwance kan couch tana bacci da
alama ma sanyi Ac yamata yawa dukta takure waje daya,
ya dauki papers din ya taso zuwa wajenta da niyyan ya
tashe ta, ya tsugunno setin fuskan ta yana kallonta,
yaune na farko daya kare mata kallo, ya ciro wayan shi
yayi snapping dinta, ta gyara kwanciya veil din kanta ya
zamo kasa, gashin kanta ya zubo ya rufe mata
kakkyawan fuskan ta, da sauri yasa hannu ya matsar da
gashin gefe, karaf ta tashi sukayi ido hudu dashi, ya
tsakar mata lausassar murmushi, “ta lumshe ido tana
kallonsa wani irin sanyi take ji azuciyar ta, dakyar ta
mike, ta Harare shi “tace miye haka zaka tabani? ? Dariya
ma ta bashi, ya mika mata papers din yace kiyi abunda
kika ga dama dasu, ta bata rai ta amsa ta ciro pen a
jakarta tayi signing ta mika mai, ta tashi tace sai anjima,
yace “babu ko godiya, tayi banzan dashi ta wuce zata
fice, takasa bude kofa, ta danna lock din yaki budewa, ta
juyo ta kalle shi a fusace tace “nakasa bude kofan, yayi
dariya ya taso yace d door is open kece dai yar kauye
baki iya budewa ba, yasa hannu xai bude kenan aka
bango kofan daga waje kursum ta fada jikin shi a
tsorace:oops::oops::oops: Zee dana gama kulewa ganin
kursum jikin masoyinta yasan ta kara
fusata:evil::evil:,tace yaya yazid dama shegian yarinyan
nan ce a office dinka tun dazu, shine secretary dinka ta
zauna dani office dinta tun dazu akan cewa kana da
important visitor, gajiya nayi da jira shiyasa nayi
deciding in shigo kawai, ta fashe da kuka Ya yazid kasa
magana ma yayi dan haushi, dan dama haka take shigo
mai office duk lokacin data ga dama,”kursum ta karaso
wajenta da sauri tace “kiyi hakuri, wlh ba abunda kike
tunani bane, aiki ne yakawo ni nan ba komai ba” zee ta
Harare ta tace karya kike munafuka dama daga ganinki
ke yar bariki ce, mayya yar titiiiii…….bata ida magana ba
ya yazid ya wanketa da mari saida taga wuta , tace baby
ni ka mara? Yace namareki din, ba sister dinki bace
atleast respect her for once, “kursum dai tana gefe bata
ce masu komai, zee tana kuka tace baby dan ina sonka
dayawa shiyasa kakemin wulakanci, ta kalli kursum tace
ke kuma hajiya na asibiti ba lafiya kinzo nan kina cin
amana, toh baki isa ba kuma sai na koya miki hankali ta
fice , da sauri itama kursum ta bita tana kwalla mata
kira. Yana nan tsaya yaji wayar shi na ringing ya duba
yaga umma,da sauri ya dauka suka gaisa, tace my son I
hav been trying ur line bai xuwa, kana ina ne? “Yace ina
office umma, tace to kazo ka sameni a asibitin dr malik
yanxun nan, hajiya hadiza ce ba lafiya, yace toh ganinan
umma, ya ajiye wayan da sauri yadau mukullin mota ya
fice. Har bakin mota ta biyota tana zee kiyi hakuri mana,
ki taimaka ki kaini asibitin banzo da mota ba, zee tayi
banza da ita ta shige mota abunta taja a fusace:evil::evil:
Haka ta karaso bakin titi kozata samu taxi, shiru dai bata
samu ba ga wani irin ciwon kai dake damunta, tana tsaye
wata hadaddiyar jeep kirar classic 2020 taxo gabanta,
yayi wining glass din motan, yace little witch shigo in
kaiki, tayi banza dashi, yayita mata horn taki kulashi, da
daga dai zai kara mata ciwon kai tayuwo tace ya yazid
miye haka, nace bazan shigo ba ka wuce kawai, “yace
asibiti zani wajen hajiya kema nasan can zaki je, kizo in
maki lift dan bazaki samu taxi anan ba, ta tsaya tunani,
ita dai bataso zee ta kara ganin su tare, haka dai ta
hakura ta shigan motan. Har suka iso asibitin babu
wanda ya yiwa wani magana, ta fito da sauri zata wuce
ciki, yace ke kinsan inda aka kwantar da ita ne? Tace a’a,
“yace to saiki jirani ai tunda ni nasan wajen, duk sai taji
kunya, haka suka jero har inda umma ke zaune, ya
karaso gabanta yace umma lafiya dai ko? Tace eh
hajiyan ta farfado, yanxu bacci take ma, shehu yana
wajen doctor jin meke damunta, kursum dake bayanshi
ta karaso ta gaida umma da mata godiya sosai akan
kokarin datayi na kawo mamanta asibiti, umma dai sai
kallonta take dan batasanta ba, tace my son ina kasamo
pretty girl dinnan, yazid yayi dariya yace ai sumayya ce
diyar hajiya, na rage mata hanya ne,”umma tace ikon
Allah dama ni ban taba ganinta ba, ya kike sumayya?
Kursum akunya ce ta amsa tace lafiya kalau, umma dai
sai murmushi take, ji take kaman tasan ta, wani irin son
yarinyan taji har cikin zuciyan ta.:mrgreen::mrgreen:
Baba shehu ne ya fito yasame su yake gayamasu ai jinin
hajiya ne yahau sosai dalilin firgeta da tayi, dan yanxu
haka ta farfado amma har yanxu tana tare da shock,”ya
kalli umma yace haijya mairo bata gayamaki abunda ke
damunta ba kafin ta suma, umma tayi shiru batace
komai, baba shehu yace toh Allah ya bata lafiya shine
kawai fatan mu, yanxu dai doctor yace mutum daya zai
zauna da ita, inya so gobe mazo mu ganinta, ya kalli
kursum yace ke kizauna da ita harta tashi, hajiya mairo
kuna iya tafiya tunda sai gobe za’a iya ganinta, “umma
tace to shikenan bari mu wuce, gobe saimu dawo, my
son let go, ta kalli kursum tace sumayya ki kula da
mamanki sosai kinji, tace toh umma zan kula da ita
sosai. baba shehu yace zan turo samira ta kawo muku
abunda zaku bukata,tace toh”ya wuce abun shi. Har sun
wuce ya yazid ya dawo da sauri yace Karki zauna kina
game, akula da marar lafiya dai, ta murguda mai baki
tace ina ruwanka toh:?:?…… yayi dariya yace zanyi
maganin tsiwan nan naki, ya fice da sauri…… Ta tura
kofan dakin ahankali, ta karaso gaban gadon da take
kwance ga ruwan drip an daura mata, ta zauna

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment