Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gidan
ganin kursum, amma sai dai yasha zama a parlour bata
fitowa, idan yagaji ya tafi…. Zee kuwa basu da aiki ita da
meerah sai clubbing da shaye shaye, takan yi kwana biu
bata kwana gida ba, ta fita harkan yazid ko sun hadu
bata kulashi, dukda sonshi na nan daram azuciyar ta, har
dakin kursum take shiga tayi ta janta da hira kaman
gaske. Baba Shehu na nan da kudirin sa, burinsa ya
kawar da Sumy,amma ya rasa yazeyi. Gimbiya hafsatu
ko yaushe tana main house abaje a parlour bata da aiki
sai tsegumi, kowa haushin ta yake ji agidan, tunda taga
Baba Shehu take shishige mai, ita adole tasamu mijin
aure, shi ko kallon bata ishe shi ba….. Bayan sati biyu
Umma ce taxo gidan tayi knocking kofa, gimbiya dake
kallon TV taja tsaki ta tashi taje budewa, ta bude suka
gaisa da umma, umma tace amma ke bakuwa ce koh?
gimbiya ta Kare mata kallo tace wata sabon gani hajiya
maryam ai bazan taba mantawa da fuskan kiba, umma
ta kwalalo ido waje tace ina kika sannni nikam bansan
kiba……gimbiya ta kece da dariya tace Ai dole kimanta
ni, 18 years ago kika kawo min kursum tana jaririya
kokin mata ne? Umma ta bata rai tace banganeki bane,
me kikeyi a gidan nan ? Tace zama nazoyi mana Ai Sumy
daliba tace, umma tace toh yanxu babu komai tsakani
na dake, tunda kursum ta rasu, karki kara gani na kice
kin sanni, gimbiya tace haba hajiya miya yayi zafi haka,
ki bari muyi zumunci mana,” tayi banza da ita ta wuce
sama dakin hajiya. Gimbiya tace lailai matan nan,aiko
saina juyo xancen da zakuyi, sadaf taje bakin kofan
dakin ta kasa kunne… Hajiya tace ashe zaki zo, na dauka
kokin mata dani, umma tayi dariya tace yanxu ma
agurguje nazo Alhaji na gari Shiyasa kika jini shuru ,ya
karfin jiki ? Hajia tace da sauki sosai, Ina son dinki kwana
biu baizo ba…….umma tace indai yazid ne anjima kina
iya ganin shi, ta duba agogo, nizan wuce office sai munyi
waya,”tayi sallama da hajiya ta fice. Gimbiya dake labe ta
bar wajan da sauri, aranta tace oh kakkyawan yaron nan
dake zuwa wajan kursum ashe danta ne, ta kwalalo ido
waje, idan umma ce uwarsa kenan yazid da kursum are
siblings basu sani ba, ta koma bakin kofan ta tura
ahankali tashi ga dakin, hajiya na zaune kan gado tana
kallan pictures din daddy tana sharar kwalla, bata ankara
ba sai ganin gimbiya tayi gabanta, arazane tace miya
shigo dake nan, gimbiya data cika da mamaki tace keda
kike makauniya hw cms kike kallon picxx, hajiya duk ta
kideme,da sauri tadau glass dinta ta maida, munafuka
fice min daki kafin insa ayi waje dake, “tayi shewa tace ai
ina fita xan tara kowa a parlour ingaya masu Karya kike
4 d past 18yrs, kina gani kuru kuru,” afusace hajiya tace
Fadi price din da kikeso in baki kiyi shuru da bakinki,
gimbiya tace banason kudi idan kikamin abu biyu toh ur
secret is safe wit me, tace mai kikeso ? Na farko inaso
indawo main house da xama nagaji da zama part din
masu aiki, na biyu kisa Shehu ya aure ni, ” hajiya taja
tsaki, na yadda dana farkon, amma na biyu I don’t tink
zai yuyu, bazan ma kanina auran dole ba,balle ke yar
bariki wace tayi aure wajan shida ta kasa zama, gimbiya
data gama kulewa tace toh naji ,xan baki time kisan
yadda kikai ya aure ni, ta fice afusace kalaman hajiya sun
bata haushi. Agajiye ta dawo daga office tayi sallan
magrib ta fada gado, ta dauki wayanta taga 10 missed
calls da sauri ta tashi zaune ganin number inna sadiya, ta
buga ringing daya Inna ta dauka, jin kukan hanifa yasa
kursum ta gigice, tace Inna miya sameta ? Kukan mi
take? Inna tace wlh zazzabi ke damunta tun jiya munje
asibiti amma ba sauki har yanxu shiyasa ma nake
kiranki,” hankali tashe kursum tace inna dare yayi balle
inzo, Ki cigaba da lallashin ta, gobe da sassafe zanzo in
dauke ta, Inna tace toh sai kinzo, sukayi sallama. Tunani
take yadda zata dawo da hanifa gidan, bata da wani
mafita ,da sauri ta tashi ta sauka kasa, suna kan dinning
suna cin abinci ,zee sai wani bata rai take ganin gimbiya
zaune dasu tana wurga loma, ta kalli baba Shehu tace
waimi matar nan keyi anan ? Hajiya tayi caraf tace ke
bana son rashin kunya, kici abinci……..kursum ta karaso
ta zauna tace baba xan tafi bauchi gobe, ya kalleta lafiya
dai ko ? Tace eh, inaso kasamo mun driver dazai kaini
kasan ban kware sosai ba, “zee tace sister y not inkai ki,
baba Shehu ya watsa mata harara, bazaki kaita ba, ya
kalleta kursum yace karki damu zan shirya miki driver
dazai kaiki gobe wajan 8am, tace toh nagode baba,
hajiya ni xanyi tafiya gobe xanma doctor malik magana
ya turo nurse dazata na baki maganin ki, ” hajiya taja ta
tsaki tace shekara zakiyi kenan ? tace a’a agoben xan
dawo xanyi dare dai, tace to asauka kalau ta mike ta
wuce Daki, Baba shehu ma ya tashi ya fishi, zee data
gama kulewa tayi wurgi da glass cup din dake hannuta ta
fice daga gidan…..gimbiya ta kalli kursum, amma zainab
dinnan is crazy koh ? yauwa mi zaikai ki bauchi? kursum
tace hmm hanifa xan dauko bata da lafiya,” gimbiya tace
tashin hankali idan kika dauko ta mi zaki cewa masu
gidan, yarki zakice ko wa? Tayi banza da ita ta tashi ta
wuce…. Wajan karfe dayan dare, tana parlour tana
kallon TV, taji motsi kaman ana saukowa kasa, da sauri
ta kashe wutan ta labe bayan kujera, taji yana waya
“yace bala kajira ni bakin gate gani nan zuwa ya fice
waje, gimbiya dake labe tace shehu wazai gani a
darannan, sadaf ta bishi ahankali har waje, baba shehu
yace bala nasan zaka iya aikin shiyasa na samoka, gobe
karfe 8am zakazo ka kaita bauchi, bala yace angama duk
yadda kace haka zaai, “yace yauwa ashe ka gane, kasheta
zakayi idan kunyi nisa ka jefar da gawar ta yadda babu
Wanda zai gani, sannan kai kuma ka bace kabar gari, ya
fiddo makudan kudi Ya damka mai, bala ya karba yace
angama, sai nazo goben, sukayi sallama ya koma ciki da
sauri. Gimbiya dake labe tana jinsu saida ta girgiza,
mamaki kawai take kowa da hidden agenda dinshi a
gidan, hajiya mai karyan maganta, zee d crazy gal, ga
umma da yar’ta amma bata saniba, shehu da nashi
makircin, kursum dake using identity din dead Sumy, ta
tabbata yazid yana da nashi unknw secret din, Wat a
mysterious family. Tayi kwafa ta koma ciki, tunani kawai
take yadda zatayi saving kursum in 7hours, cox idan ta
bari aka kasheta barin gidan nan yakamata dole. *Xarah
Bukar* *Dedicated to Bady social* ~luv u all~ [08/09
12:20 am] Xarah bukar : KURSUM by ~ Xarah Bukar Page
Tun 7am ta shirya tama hajiya sallama “ta fito haraban
gidan jiran driver. “Gimbiya sai kai komo take a daki tun
bayan sallan asubah, ta leka waje ta hango kursum tsaye
bakin mota tana jiran bala,” can dabara ta fado mata, da
sauri ta fice ta shiga dakin baba shehu ahankali, da
alama yana toilet, sadaf ta karasa bakin gadon ta dau
wayarshi ta ta binciko contact din bala driver,” ta tura
mai msg “` “change of plans kazo by 10am”“` tana
turawa tayi deleting ta kashe wayan ta ajiye ta fice da
sauri, ta sauke ajiyan zuciya, atleast zata samu tym din
samu mafita. “Yana fitowa ya shirya da sauri yadau
wayoyin sa ya fice, ” kursum dake tsaya ta karaso ta
gaida shi, baba kasan 8am zan wuce, gashi 7.45 har
yanxu baizo ba, “yace karki damu bala baya wasa da
aikin sa zaizo Yanxun nan, ” toh baba Allah yasa karya
bata min tym, sukayi sallama baba shehu ya wuce office,
aranshi sai murna yake , yarinya zaman ki yazo karshe a
duniya. “Sai leke take ta window ta rasa mafita, ta sauko
sum sum ta karasa wajan kursum dake tsaye rai abace,
“tace anya bazaki hakura da tafiyan ba naga har 9 yayi
driver bai iso ba, ” kursum ta kalleta tace haba gimbiya
kinsan hanifa amana tace dole in dauko ta, gashi layin
baba shehu off bansan yadda xanyi ba, “gimbiya tayi
shuru tama rasa me zatace, fatan ta kawai kar bala yazo
dan 30mins ya rage goma ta cika… “Hankali kwance yake
driving har ya iso gidan, ya kudiri niyya yau saiya ganta
koda zata makale adaki, kusan 3weeks kenan yana
bibiyanta…. Suna tsaye yashigo, dukta daburce ganin shi,
zata koma ciki da gudu gimbiya ta riketa tsam, Ai babu
guduwa da zakiyi in har kinason ganin hanif dole ki
rokeshi ya kaiki, kursum ta bata rai banason haka,
bakisan banaso in hadu dashi ba, gimbiya tayi shewa,
tace ahab ai nasan kina sonshi kina kaiwa kasuwa, taja ta
har wajan shi ta bude motan ta turata ciki, ” yazid dake
kokarin fitowa daga motan saida ya tsorata,Sam bai lura
dasu ba sai ganin gimbiya yayi ta turo ta…. “ya tamke
fuska, miya haka ? zaki ji mata ciwo ne ? Ta washe baki
tace ai nasan wajan ta kazo, sai ka kaita Inda zata, ta kalli
kursum da tayi kicin kicin fuska a murtuke, sai ki
gayamai inda zaki ta rufe motan ta koma ciki…… “Yaja
mota suka kama hanya, ya kalle ta yayi murmushi, my
witch ina zan kaiki ? Kaman tayi banza dashi, sai kuma
tace ” bauchi zaka kaini… “Ya kalleta, hop all is well. tayi
banza dashi Ya cigaba da sharara gudu, can yace miya sa
kike guduna ? “Banason ganin ka ne” Ya murmusa yace Y
“i hate yhu” Kinsan I hate lies, nasan u Luv me” I dunno y
kike cewa u hate me, gashi ni am deeply inluv wit u kina
bani tough time….. “Tace hmmm I don’t biliv, infact I
don’t trust yhu. Am serious, u can trust me yace mata.
Tayi murmushi, last tym da muka hadu baka karasa min
labarin yarinyar nan da kuka hadu a bauchi ba, kace ka
manta sunanta, kasan inda take yanxu ??? ” ya sauke
ajiyan zuciya, matata CE just 4 a nyt, na aureta da kwana
daya nasake ta, wat tace “kana nufin u wia once married
n divorced ?? ” eh, dat was d biggest mistake da nayi
arayuwata, koda na saketa na tafi nakara komawa in
dawo da ita, amma it waz 2 late aka cemin ta sake aure
tabar nigeria.. Kursum dake sharar kwalla a boye, aranta
tana mamaki waya cemai Sumy ta sake aure, ta nisa tace
eyya iyayen ta suka gayama ta sake aure kenan ? “Yace
a’a, bata da kowa agarin ma, wani jamilu dana tura
naiman aurenta a makarantar su shina turo ya
bincikomin ita, koda yaje director din tace mai ai tayi
aure bata kasar…. ” ya kalli kursum dake zubda hawaye,
ya ciro hankie dinshi ya mika ta, kukan mi kike, “ta karba
tace it a pity, umma tasan da faruwar haka ? Yace e
tasani na gayama ta komai, tare ma muka so zuwa
naiman yarinyar, amma she was so busy, ” I hop duk
inda take yanxu zata yafemun. “tace am sure ta
yafemaka. Kinsan tane, hw are u sure she has 4given
me ? ” nayi guessing ne kawai tace mai….aranta
mamakin hali gimbiya take, wato ita tayi karyan cewa
sumy tayi aure tabar kasar, wat a cruel woman, aiko
tana komawa zata fadi gaskia, inyaso daga ita har
gimbayan sabar gidan. “Ta dau wayanta ta kira inna, suka
gaisa, ya jikin hanifa ” Inna tace da sauki sosai yanxu
bacci ma take, inna nima Ina hanya, tace toh kursum
Allah ya kawoki lapia, sai kinzo, sukayi sallama. “Ya
kalleta yace wace ce Hanifa ???? Ta fuske tace ya’ta CE,
Wat yaja birki da karfi, kina da aure dama ? tace banda
shi asali ma ban taba yiba, amma inada Ya’ yar shekara
daya, dauko ta xanyi bata da lapia, ” yayi shuru bai ce
komai ba, yasan dai she is decent ,hw cms take da Ya’ ba
aure, Afusace ya tada mota ya dunga sharara gudu
kaman xai tashi sama, ni phatee mai dauko rahoto saida
na tsorata, wanga sheka gudu kaman ba
gobe:oops::oops: Tana baje a parlour (as usual) tana
taunar cingam kaman wata yar gidan mangwaro, zee
dake kan dinning tana cin abinci ta ja tsaki tace
tsohuwar banza haka zaki kare munafuka, “gimbiya ta
nuna ta da yatse, ni kike zagi ? Zee tace kwarai kuwa
mayya, ta tashi afusace ta kama zee tana duka, ihu take
bazan kara ba ki kyaleni, ba mafita ta dankara mata cizo
ba shiri gimbiya ta sake ta, da gudu tabar wajen. ”
gimbiya tayi kwafa, shegian yarinya nakusa zama uwarki,
ubanki ya shigo hannu na dole ya aureni ko yanaso ko
baya so *Xarah Bukar* *Dedicated to Bady social* ~luv
u all~ KURSUM by ~ Xarah bukar page Babu wanda yace
uffan har suka iso garin bauchi, direct gidan inna sadiya
suka zarce, “yayi parking yace karki dade cox bana nyt
driving, ” baza ka shigo ku gaisa da inna ba? no need, jux
hurry up ki fito mu wuce, xan shiga masallaci Toh kawai
tace ta shige gidan. Inna na tsakar gida tana wanki taji
sallaman ta, ta amsa tace amma dai kinyi saurin isowa
“Kursum tace eh wlh inna ya kuke? lapia lau, taja ta suka
shiga daki, hanifa na kwance tana Bacci, yanxu kam
xaxxabin ya sauka sosai, saidai bata son cin abinci inji
inna ” kursum ta nisa tace ai rashin cin abincin nata nada
muna, ina isa gida zan kaita asibiti, “inna tace barin kawo
maki naci da sha Kidai barshi wlh, muda muke sauri
sallah kadai xanyi in wuce, inna tace irin sauri haka, bara
na zubo maki ruwa a buta. “Bayan tayi sallah, sukayi
sallama da inna tare da bata makudan kudi ta kula da
kanta, tadau hanifa suka fice, inna sai zuba godiya ake.
“tsaye yake bakin mota yana waya da umma ” son kace
tana da ya’ marar lapia ? Haka dai tace min. Okay don’t
bother asking her anytn, irinsu nasan situation dinsu,
kuna isowa kano ka kaita asibiti, xanzo insa meku “Yace
toh. Hey ka gama wayan can we go ya juyo yaganta
zaune cikin mota, wen kika fito ko motsin kin ban jiba ”
nayi kusan 10mins anan ai, “yayi murmushi ya shiga
mota, ya kalli hanifa dake bacci jinkinta yace ur baby is
cute tnx kawai tace, suka Kama hanya Baba shehu zaune
a office, ya kalli agogo yasan by diz tym she is already
dead, wayashi ya dauka zai kira bala driver, yay mamaki
matuka gannin wayan nashi kashe, yasan dai baya kashe
waya, da sauri ya kunne ya kira bala, bugu daya ya dauka
” ina fatan dai ka cika aiki? Bala yace wana aiki kuma,
naje gidan around 10 wata Mata tacemin ai kace anfasa
tafiyan sai gobe, nayi kokarin kiran ka layin kashe “ya
tamke fuska, kaida nacema 8am maiya kawo ka 10,
kuma wace tacema anfasa tafiyan? bala yace ka turomin
msg inxo by 10am, ni bansan matar ba, amma daganin
ta yar gari ce. Afusace ya tsinke call din ya dauki car keys
dinshi yayi waje, yasan babu tantama gimbiya ce ta
ruguza mai plans dinshi, amma hw cms tasan komai,
lailai ko sai ya koya mata hankali. Tana zaune kan
dinning ta hada varieties of abinci sai wurga loma take,
ya banko kofa ya shigo, saida ta tsorata ta mike tsaya,
shehu lapia ? Ko sauraron ta bai yiba, ya cafko wuyan ta
ya shake, bana hanaki shiga tsabga taba ” gimbiya dake
kakarin shedewa tace kashe ni zakayi kenan kaman
yadda ka tura akasheta, ” ba shiri ya tsake ta ya wurga
mata harara, bangane me kike nufi ba tayi shewa, shehu
karka raina min yawo, ta fito da wayatan ta kunna mai
zancen su da tayi recording, “yayi tsuru tsuru, toh mai
zakiyi dashi? “ta kece da dariya, police station zan kai
yanxu kuwa, ” haba hafsatu mi yayi zafi haka kiyi hakuri
mana….ta balla mai harara, aurena ko prison sai ka zabi
daya “Ya kwalalo ido waje, are u trying to blackmail me.
za tayi magana hajiya ta sauko, lafiya nake jin hayaniya?
gimbiya tayi caraf tace ba komai dama zancen auran mu
muke da shehu, ta kalle shi koh shehu ? ” yayi banza da
ita ya wuce abunshi. Ta kalli hajiya,nagama part dina sai
ki san yadda zakiyi ayi auran cikin sati daya, “hajiya ta
balla mata harara, matsiya ciya ai dama nasan zuwanki
ba alheri bane, ” ta washe baki, karfa ki zageni kinsan
nasan komai, “takaici duk ya isheta tama rasa mizata ce.
Karfe takwas na dare suka iso kano, suka wuce asibiti, ”
Dr aesherh dangusau ce on duty, da sauri ta tarbesu
sanin tasan dazuwan su, suna zaune a office dinta ta
gama duba hanifa ta kalle su, babyn ba wani serious
sickness take ba, dou rashin appetite ke hana ta cin
abinci, ta dau pen da paper, “ta mata prescribing
paracetamol syrup na pain relieve, da Oral rehydration
salt na restoring body fluid & electrolytes lost due to
dehydration, idan tasha zataji dama sosai tace ” ta mika
mai paper ya karba tace baby dinnan sam bata kama da
mamanta, kamar ku da ita yayi yawa, “nan gaban
kursum ya buga, sai yanxu ta kara tabbatar wa da kaman
yayi yawa” shiko yazid ko acikin shi, dan baiga kaman
komai ba. Suka fito zuwa pharmacy sukayi kicibis da
umma ta shigo, “kursum tayi murmushi ta gaida ta
aladabce, ta amsa da fara’arta ta amshi hanifa, ” yazid
yace umma barin barku anan inje amso magani, tace
OK. Taja ta suka samu guri suka zauna, ta kalle kursum
tace sumy kinsan na dauke ki tamkar nina haifeki, “yazid
ya gayamin komai yanxu gayamin waye uban hanifa ?
tayi narai narai da ido, aranta tace danki ne
ubanta……..afili tarasa mi zatace kawai ta fashe da kuka,
” jikin umma yayi sanyi matuka, kar kiyi kuka kinji, am
sure kina da kamun kai, saidai ko u are a victim of rape..
“kursum tayi shuru batace komai ba illa sharar kwalla da
take, “umma tace kirki damu haka Allah ya kaddara, so if
u nid any1 to talk to kina iya xuwa kisame ni, kinji ? ” toh
umma nagode sosai da kulawarki, aranta tace da umma
ce mahaifiyar ta da nayi sa’ar uwa.” ya dawo rike da
maganin, ya amshi hanifa yace muje koh suka mike zasu
wuce umma taja shi gefe, my son plz karka ce xaka rabu
sumy, yanxu yakamta mu taimake ta, kasan yan gidansu
ba sonta suke ba, ‘karki damu umma no matter wat ina
tare da ita, I will 4ever luv her till eternity. tayi
murmushi, tnx my son, tayi sallama da kursum ta wuce
gida. shima yaja mota suka bar asibiti. tana zaune a
parlour nurse ta shigo tace hajiya lokacin shan magani
yayi, “ta yatsine fuska ke nifa karki takura ni da magani,
da safe ma nasha. nurse tace kiyi hakuri, aiki na in kula
da lafiyar ki, idan baki sha ba abakin aiki na, zee dake
kallon tv taja tsaki ta mike, kun cika min kunne da
surutu, “hajiya tace baa dole saiki tafi daki kiyi kallo.
“turo wan kofan ne yasata tsayawa chak, ganin su tare ga
kursum rike da yarinya, ta bata rai, ku kuma da ga ina
adaran nan ? ko kallanta basuyi ba suka karasa wajan
hajiya suka gaida ta, “ta amsa ayatsine ganinsu da yar
yarinya da bazata wuce 1year ba, aranta tace Allah kadai
yasan ina suka samota, “tayi gyaran murya, ina jin
motsin yara, yazid kazo da baby ne ?? “kursum tayi caraf
tace eh ya’ta dama ita naje dauko wa a bauchi. Daga zee
har hajiya sai da suka tsorata, lokaci guda suka ce badai
shegiya bace. tayi banza dasu, yazid yace ba shegiya bace
zee data gama kulewa tace kaine ubanta kenan “yace
bani bane amma daga yau nazama ubanta. hajiya tace
zainab kiramin gimbiya in ji daga bakinta, dan bazan
yadda da shegia agidan nan ba…… Dam gaban kursum
ya buga, Allah yasa kar gimbiya ta kufsa mata…. *Xarah
Bukar* *Dedicated to Bady Social* ~luv u all~ kursum
59 to 63 Posted by XARAH ABUBAKAR on NOVEMBER 13,
2016 KURSUM by ~ Xarah Bukar Page Hankali kwance ta
shigo palon, ganin kursum rike da hanifa yasa tasha jinin
cikinta, aranta tace oooh family drama dinsu baya
karewa. “hajiya lafia kika naima na ? Ta wurga mata
harara, gayamin zakiyi ya akai sumy tayi ciki harta haihu
bani da labari ? ” gimbiya ta kwashe da dariya, abu mai
sauki ai ita zaki tambaya bani ba, “zee tayi caraf tace
dama bakin ku daya, kun gama karuwanci ku tare ai dole
ki rufa mata asiri, Hajiya ta daka mata tsawa, ke banson
hauka anan, tunda sunki magana kawai tadau shegiar
yar’ta ta maida ta inda ta dauko ta. “Yazid da takaici ya
ishe shi yace babu inda xata , infact aurenta xanyi sai
inga mai ce wa yar’mu shegia, ” daga kursum har zee
saida suka girgiza jin kalaman sa Xee ta fashe ihu, baby
akan karuwa zaka gujeni, toh wlh baka isaba, ke kuma
kin gama iskanci a duniya shine zaki lake mai dan
matsiyaciyar yarki tasamu uba ,”kursum data gama
fusata ta nunata da yatsa, kince min karuwa nayi shuru,
don’t u dare insult my daughter…. “zee ta yi kwafa tace
na zaga din shegia, du your worst….tass din kakkyawa
marin da taji a kuncin ta yasa ta mut lokaci daya, ” ya
wurga mata harara, kara zakinta kiga abunda zan miki,
marar hankali kawai, yaja hannun kursum suka hau
sama. Zee dake hawaye ta kalli hajiya tace ki taimaka kar
ya aureta yabar ni , “hajiya taja tsaki, indai zai aureta
aina ji dadi, barinta gidan nan shine farin cikina, gimbiya
tayi shewa, buki bidiri aure biyu zaai kenan, ” akule zee ta
kalleta, ke kuma yar bariki wazai kwashe ki ? “tayi fari da
ido, ashe baki da labari toh ubanki ne zai kwashe ni, aure
nan da kwana uku, ” haushi da takaici ya hana ta
magana, ta suri Jakarta ta fice daga gidan. Har dakinta ya
shigo da ita, ta kwantar da hanifa, ta kifa kai kan gado
tana zubda hawaye, “yana tsaye yana kallonta, tausayi da
tsananin sonta yaci gaba da ratsa shi, ya yarfe hannuwa
gami da durkusawa a gabanta, ” kukan nan naki na
breaking heart dina, atleast say sumtim ko zanji dadi. “Ta
dago idonta da ya sauya launi tana dubansa, ta kwantar
da kai tace ya yazid I don’t deserve ur love saboda ni ba
wace kake tunani bace, ” yayi murmushi, ai nasan u wia
adopted, hajiya ba mom dinki, kar kiyi tunanin kozan
ki’ke dan baki da asali, “ta kalleshi da mamaki, aranta
tace nikam ba haka nake nufi ba, inason gayama wace ce
ni amma ina tsoron karka gujeni, ” afili ta nisa tace yaya
just go I need some space, ya kalleta okay I’ll but
promise me u won’t cry again, “tace yes I promise “ok
gud nyt ” ya sauko yama hajiya sai da safe ya fice daga
gidan. gimbiya tayi murmushi mugunta, yanxu inta auri
shehu tazama queen of d house, shiyasa baza ta gayawa
kursum cewa yazid yayanta ne ba, gwanda ta aure shi
tabar mata gidan….hmm( wa’iyazubillah gimbiya kiji
tsoron Allah, dukda munsan basu hada jiniba bai kamata
kice haka ba ). ************************ Tana
bacci taji an daka mata duka, firgigit ta tashi tana
murtsuka ido,”miye haka zaki dakeni? “Meerah tace nayi
mamakin ganin kine, yaushe kika zo ? Zee ta gyara
kwanciya, ke nifa jiya da daddare na shigo, tension
yamin yawa datx y nazo ke kuma as usual bakya nan,
Meerah ta kwalalo ido, galfrnd wana tension, gayamin
miya Sameki, “humm ta nisa, ta fyade mata biri har
wutsiya ” meerah tace anya cousin sis dinki ba jazz tama
ya yazid ba, ta gama yawon duniya harda shegia gareta
but still he is willing 2 marry her, “zee tace babu wani
jazz, dama yana dason yara, ni yanxu bansan ya xanyi
ba, ga p.D yace mu bashi nan da sati biu, ” meerah tace
karki damu muna da hope ai nasan detective zai samo
komai akanta, ita kuma gimbiya ki shareta naga alama
matar ba mutunci. “aiko dai, ni bansan hw cms baba ya
yadda da aurenta ba, koda yake datz his problem not
mine. Abba yayi doguwa ajiyar zuciya ya kalli umma
yace narasa miyasa kike son yazid ya aure yarinyan nan
alhalin kuma har ciki shege tayi, ” ta bata rai, haba alhaji
karka ce haka, kowa arayuwa yana da nasa laifin dan ya
aureta aiba haram bane, “ya nisa yace toh shi kenan
xanje wajan shehu naima mai auranta, amma kisani duk
abunda ya faru nan gaba babu ruwana, ” umma tayi
murmushi, babu abunda zai faru sai alheri, yace toh
nidai nagama magana, yadau hulansa ya fice. Tun daga
wannan ranar wata irin soyayya suke gudanarwa mai
cike da kauna, wani lokaci abin yakan baiwa kursum
mamaki, shin dama zuciya takan iya son abunda ta tsana
da fari ,domin ko taki ko taso ayanxu tasan dan zaman
da tayi da yazid takamu da sonshi, dan ba karamin kula
da hanifa yake ba…… Salma ce tazo gidan, suka gaisa da
samira dake rike da hanifa, “samira Ina kike samu pretty
gal ? ” tayi dariya tace ai diyar Antee sumy ce, “salma
data cika da mamaki tace sumy na daki ? Tace eh tana
nan. ” ta shigo dakin, kursum dake zauna tana shafa mai
tayi dariya, kawata yanxu nake shirin calling dinki, salma
tayi yake, nima kasuwa zani shine nabiyo, yau baki je
office ba, “eh kwana biu bana zuwa, dayake ya’ta bata jin
dadi. Salma tace wai dagaske yar’ kice , nidai ban yadda
ba, sam baku kama, ” kursum ta sauke ajiyan zuciya, ta
tashi ta rufe kofan dakin da mukulli, taja hannu salma
suka zauna kan gado, tace kawata yau xan gayamaki
sirrin rayuwata, ta tsara mata komai tun daga ranar da
mahaifiyar ta tayar da ita har izuwa yau, “ba karamin
tausaya mata tai ba tace Allah yaji kan sumy, ni aganina
it better ki gayawa yazid gaskia yasan cewa shine uban
hanifa, ” kursum ta nisa, inason gayamai ina tsoro karya
gujeni, “salma tace karki ji tsoro, ba karamin sonki yake
ba am

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment