Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kusa da
ita ta riko hannun ta , tana mamakin abunda ya firgita
hajiya da jininta ya hau sosai, duk sai taji tausayin hajiya
ya kamata, batasan lokaci da ta fara zubda hawaye ba ,
burinta kawai Allah ya sada ta da maihaifiyar ta wataran
koda amafarki ne. Digan hawayen da hajiya taji ahannu
ta yasa tafara motsi tana kokarin bude ido, ahankali
harta bude idonta, ta kalli kursum dake kuka, afirgice ta
tashi ta ruko hannun kursum tace “Kursum ashe baki
mutu ba” Agigice kursum ta dago ta kalle
ta………..:oops::oops::oops::oops: Rudani, tashin hankali,
faduwar gaba, lokaci guda ta shiga:oops: *Xarah Bêê*
KURSUM By ~ Xarah Bukar page Hankali tashe Tace
“hajiya nice sumayya ba kursum ba, amma sam hajiya
batasan inda kanta yake ba, ihu sunan kursum kawai
take, doctor ne ya shigo dakin da sauri jin ihu ta, ya tsira
mata allurar bacci. Ya kalli kursum yace”wace mai sunan
da hajiya ke kira? “Tace nima dai doctor bansani ba,ko
adangi banji mai sunan ba, “ya nisa yace tabbas mai
sunan tana da alaka da shock din da hajiya tashiga,
amma karki damu idan ta tashi she will be normal, “tace
toh dr mungode, ya fice. Itama taja kujera ta zauna tayi
tagumi, tunanin ta daya wace kursum din da hajiya ke
ambata, dan tunda take da sumy bata taba mata xance
wata kursum ba. Ranta abace ta iso gidan aminiyar ta
tana kuka, meerah dake baje afalo daga ita sai bom
short da bra ga uban giya agabanta, ” ta ajiye cigarette
din hannunta, ta karasao wanjenta dasauri,”tace zee mi
aka miki? Miya faru? Kukan mi kike? Zee takara fashewa
da kuka tace “girlfriend wai yau ni ya yazid ya mara akan
wata shegia yarinya, “meerah ta kwalala ido waje, tace
babe gayamin wace yar iska ce yanxu in maki
maganinta, “zee ta gyara zama ta zayyane mata komai
akan sumy, “meerah tayi kwafa tace lailai galfrnd, akan
small brat dinnan duk kika birkeci, yanxu abunda
zamuyi shine gobe muje har school din da aka jefar da
ita a bauchi mu binciki past dinta, dan na tabbata she
will have some dirty secret da take boyewa,” zee tace
nima dai I dnt trust her, dole mu samo abunda zamuyi
using against her, “meerah ta zuba giya a cup ta mika
mata,tace just drink diz banason ganinki haka plz, chill
up babe akwai casu anjima, ” ta amsa tayi murmushi, ita
dai tana son meerah sosai cox she is always there 4 her.
*wace ce meerah* Asali sunanta Amirat oyekola,
haifaffiyar garin lagos ce, sun hadu da zee a lagos state
university inda department dinsu guda, ganin zee yar
masu kudi ce marar wayo yasa ta shishige mata har suka
zama best friends, duk wata harka ta shaye shaye da
clubbing saida ta koya mata, taso tasa zee a harkar bin
maza amma taki yadda. Sun kare degree ta tattara tabiyo
zee kano har gidansu, acewarta ta gaji da talaucin
iyayenta, “haka tayita harkar kawo samari gidan, daga
karshe hajiya ta koreta tabar gidan, wani daga cikin
samarinta suka kama mata gidan da take yanxu.
*cigaban labari* suna zauna a parlour suna hira “yace
umma barin leka huzaifa kwana biu bamu huda ba, tayi
murmushi tace a daren nan, gayamin gaskia dai kodai
gurin sumy zaka, dannan lura da kallon dakake mata
dazu, ya sosa keya, “Allah umma wajen huzaifa zani
kuma yarinyan nan babu komai tsakani na da ita,”tace to
son saika dawo, “kaima dai yakamata kayi auren, ga
abokinka ya dade da aure shiyasa ma ya rage zuwa
nan,”yayi dariya yace umma karki damu very soon
xanyi, ya fice. Zaune suke suna cin abinci sukaji knocking
din kofa,ta tashi da sauri ta zura hijab taje ta bude,”tace
ya yazid yau kaine a gidanmu sannanu da zuwa, “yayi
dariya yace amarya bakya laifi, ya karasa ciki, huzaifa
yace “aina dauka yauma baza ka zoba aiki yama yawa,
yazid yace toh gashi nazo kuma dama yunwa nake ji,
nazo adaidai, “huzaif yace to ai xama zakayi mu baje,
“salma dai dariya kawai take dan tasan basa wasa da
abinci. sun gama Ci suka hau hira, huzaifa ya yace
“angon zee wai yaushe xamu kawo maka itane, yazid ya
bata rai yace “zee ko matsala, banma gayama ba
hajiyarsu ba lafiya tana asibiti, huzaifa yace kace suruka
dai ba lafiya, “yazid ya kaimai duka yace nifa bance maka
zan auri zee ba, “Salma tace gaskia ya yazid zamu biya
gobe mu dubota duk da bana shiri da xee, “huzaifa yace
kodan darajan amintakar su da umma yakamata muje,
“yazid yace to Allah ya kaimu goben, xan biyo sai mu
wuce, ya musu sallama dare yayi ya wuce. samira ta
kawo masu komai da zasu bukata, wajen 10pm doctor
mallik ya shigo dubata, “ta tashi jikin da sauki, ya kalli
kursum yace,”data farka ba tace komai ba? “tace eh, ya
mika mata magunguna, yace wanna joltan valsartan 160
mg na hawan jini ne, zata na sha sau daya a rana, Aspirin
cardio 100mg zai taimaka wajen narkar da jini daya hau
kanta shima sau daya zata sha, ku tabbata tasha su, “tace
toh Dr nida kaina zanna bata, “yace jikin nata yayi sauki
gobe xan sallame ku, “tace Allah kaimu ya fice. tashi tayi
ta ninke kayan sallarta ta ejiye gefe, ta karaso gaban
hajiya dake Zaune tayi tagumi, “tace hajiya sannu kina
bukatan wani abu?? tace taimaka min in watsa ruwa
kawai. “ta rike hajiya har toilet ta watsa ruwa tayi alwala
ta fito tafara sallolin.. *washe gari* Duk sun hallara a
asibiti umma na zaune kusa da hajiya suna xantawa kasa
kasa, kursum na gefe tana hada musu kayansu waje
daya, shi kuwa oga yazid ya kame kan kujera yana waya
ya zuba mata idanu,”da sauri ya tashi yace umma barin
je in shigo dasu huzaifa suna waje” tace to my son,” ta
kalli hajiya tace bakwa hira da sumy ne ?? naga tunda
mukazo tana gefe tayi shuru, hajiya taya tsine fuska tace
“ina ruwana da ita” umma tace haba hadiza tunda kin
rasa yarki Ai ya kamata kija sumy ajiki tamkar ke kika
haifeta, tsaki hajiya tayi tace nifa banason ta, xan jata
ajiki kawai dan inji labari kursum daga bakinta. yazid ya
shigo tare da huzaifa da salma, suka gaishe da umma da
hajiya, umma tace angama amarcin kenan tana zolayan
salma amarya, huzaifa yana dariya yace kakus (sunan
dayake Kiran hajiya) an tabo file kenan, ya jiki ? hajiya ta
harare shi ta tace” nagaya ma ban tsufa ba har yanxu am
16 kana cemin kakus, gaba dayan su saida suka dara, sai
sannan suka lura da kursum dake dariya daga gefe,
huzaifa ya kalleta yace yammata daga ina ? tayi banza
dashi, “yace umma ina kuka samo yarinya mai kama da
kakus, yazid yayi caraf yace ai yarta ce, zai sake magana
hajiya ta wullo mai harara, ba shiri yayi shuru, “salma
tace nikam nasamu kawa, takarasa wajen kursum, tace
kawata bakya magana ne? kursum tayi murmushi tace
“inayi mana yakike ? ni sunana sumayya, “salma tace
gaskia naji dadi saninki dama banda kowa agarin nan,
kursum tace u are welcm nima am happy to meet u.
………huzaifa na gefe yana waya, yazid ya karaso wajen
su ya zauna, ya kashewa kursum ido yace “my witch anyi
sabuwar kawa an manta dani koh ?? ta bata rai ta
murguda baki tace ina ruwana dakai, u are my enemy
not a friend, yayi dariya yace bakisan enemies na zama
best frnds ba, “salma dai bunsu tayi da Ido, “huzaifa ya
gama yace”umma nizan wuce ana naima na a office,
tace to son kayi kokari ma, ya kalli hajiya yace kakus get
well soon, “salma ki zauna tare da kawarki later zanzo in
dauke ki, tace toh , yabi kursum da kallo ya fice, yazid
daya lura da abokin shi, yatashi fuska a daure yace
umma sallaman sai yaushe ne? nafara gajiya da zaman
asibiti, “hajiya tayi caraf tace kaga yaro da rigima, ai
tunda bagaka zee ba dole ka damemu, idan ka gaji kaje
waje ka zauna mana, “a fusace ya fice yayi waje dan
yasan halin hajiya, “umma tace kwantar da hankalin ki,
keda baki da lafiya miye na tada jijiyar wuya, ” kursum
dake jinsu bata ji dadin abunda hajiya tace ba, kaman ta
fita ta bishi amma ba dama… Baba shehu ne ya shigo da
takardar sallaman hajiya, yace su zo su wuce ya sauke su
gida, kursum da salma suka kwashi kaya, umma ta
taimakawa hajiya ta mike suka fice, “yana zaune cikin
mota, umma tashigo tace muje koh, yace su hajiya fa ?
tace suna motan shehu, muje gidan “yace toh umma.
sun iso gidan, samira ta fito da sauri ta gaishe su ta
kwashi kaya tayi ciki dasu, kursum da salma suka shigar
da hajiya, baba shehu ya juya ya koma office. “umma
tace son bazaka shiga gidan bane, “yace umma barin
jiraki anan kawai banason shiga ga mitar hajiya ga kuma
zee da rigima nasan tana ciki, “tayi dariya tace yau kuma
zee ake boyewa, to barin shiga agurguje in fito, ta wuce
shi kuma ya karasa garden ya zauna. ……. Sauri suke ta
karaso gida ta canxa kaya su wuce bauchi , tun sassafe
su kayi niyya tafiya, till dawn party din da sukayi yasa su
bacci har rana, meerah tace galfrnd kiyi parking a waje
kawai ki shiga ki canxa kaya ki fito mu wuce kar muyi
dare, ” zee tace karki damu babe bazan jima ma,”
meerah tace yauwa karki manta da kudaden dazaki
kwaso, tace toh hajiya da umma na sama adaki suna
xantawa, kursum da salma suna parlour suna hira,
“samira ta sauko tace antee sumy umma na Kiran ki,
kursum ta tashi da sauri ta haura sama, ta shiga dakin da
sallamanta, umma ta amsa da fara’arta tace yauwa sumy
yayanku na waje ki kaimai ruwa yasha,”tace toh ta fice,
taje kitchen ta dauko bottle water ta fita haraban gidan,
can ta hango shi shinkide kan kujera, ta karaso, “idon shi
rufe da alama bacci yake, tayi murmushin mugunta ta
bude roban ruwa zata tsiyaya mai a fuska, “karaf taji ya
rike mata hannu gam saida ta tsorata, ya mike tsaye
yana kallonta,”tayi karfin halin cewa miye haka na
rikemin hannu, yace ai yau bazan sake kiba saikin
gayamin dalilin dayasa kike cemin am ur enemy, “tayi
shuru batace komai ba. Agurguje tayi parking awaje, ta
shigo gidan da saurin ta, gabanta saida ya fadi hangosu
tare rike da hannu ta, wani irin bakin ciki ya mamaye
zuciyan ta, wato yarinyan nan bazata fita harkar
saurayina ba, lailai kuwa I have to destroy her once n 4
all, ta karasa parlour da sauri dan karsu ganta, bata
ankara ba taji salma tace “zee daga ina haka ? saurin mi
kike ?? “ta juyo a fusace tace I don’t owe u any
explanation, dan kina matar abokin yazid dat doesn’t
give u d right to interfere in my life, taja uban tsaki ta
wuce, salma kam bataji haushi ba, tasa ba da cin
mutuncin ta, dan farkon haduwan suma ce mata tayi
she is 2 local tayi harka da ita. hmm ko dakin hajiya bata
shiga ba ta wuce dakin baba shehu ta kwashi kudade
masu yawa da papers na address din makarantar sumy,
ta wuce dakinta tasa wasu matsatsun english wears
marasa mutunci, ta sauko koh kallon salma batai ba ta
fice, “salma tace Allah ya shirya, gaskia dai ya yazid baiyi
saan mace ba. koda ta fito suna nan tare, saidai yanxu
zaune suke da alama hira suke, tayi kwafa ta wuce waje,
taja mota sai bauchi, meerah na magana ko kollanta
batai ba, sharara gudu kawai take. kinyi shuru baki ce
komai ba, tace to ya yazid me kakeso ince, nidai kawai I
don’t like u datx all, yayi dariya yace karya kike nasan
kina sona, ta bata rai ta tashi zata tafi, yace my witch
karki tafi zauna in baki labarin rayuwata, “ta kara tamke
fuska ta zauna tace ina jinka, “yace kinsan dai no one is
perfect koh ? ta girgiza kai alaman eh ,”yace ni nan da
kike ganina nayi making alot of mistakes arayuwana
wanda har yau am still regretting, “akwai wata yarinya
dukda na manta sunanta, but I will never forget her
smiling face, ya gyara zama zai cigaba da magana umma
ta fito tace mai su tafi , ya tashi ya killi kursum yace next
time idan mun hadu zan karasa miki, “jikinta a sanyaye
ta bishi da ido tace toh, ya wuce, tayi shiru tana tunanin,
wato ya yazid bai manta da sumy ba, amma meyasa bai
dawo gareta ba ko sau daya ba ?? jiki ba kwari ta shiga
ciki, salma tace ke kuwa daga kai ruwa kin makale,
kursum tace aiko ban dade ba, “muje dakina muyi hira
zaman parlour ya isheni, suka wuce daki, salma ta dale
gado tace “anya sumy ya yazid ba sonki yake ba,
“kursum tace haba dai, aini ko sona yake bazan yadda
ba, saboda he is really good at playing women’s heart,
“salma ta kwalalo ido tace dama kinsan shine ,”da sauri
tace a’a, salma tace au nayi mamaki ne, dan ya huzaifa
ya taba gayamin ya yaudari mata ba kadan ba amma
yanxu kam ya daina, mata basa gabanshi.”kursum ta
sauke ajiyan zuciyan, aranta tace Allah yasa dagaske ya
shiryu. Sun iso bauchi around 6pm direct makarantar
suka wuce, suna zuwa har office din gimbiya Hafsatu aka
gaisu, gimbiya na zaune rai abace sai hada tarkacen ta
take waje daya, suka shigo da fara’arsu suka ja kujera
suka zauna, ta kalle su tace kuna bukatan wani abune
yan mata ? zee tayi shiru, meerah tace mu yan garin nan
ne, dama cigiyar kawarmu muke, munaso kidan bamu
details akanta na zamanta a makarantar nan. gimbiya ta
nisa tace miye sunanta ? zee tace sumayya tanimu bawa,
“gimbiya ta kare masu kallo aranta tace karya suke, dan
sumy bata da wasu frnds sai kursum, kuma daga gani
yan bariki ne, kila sunji labarin dukiyar da ubanta ya
mutu ya bar mata shiyasa suke naiman ta suci arziki, toh
Basu isa ba nice xanci arzikin nan. Tace yammata sai dai
kuyi hakuri record dinmu confidential ne bama fitar
dashi, “zee zata fara roko meerah ta tabo ta tayi shuru,
meerah ta bude jakar xee ta fiddo da makudan kudi ta
tura su gaban gimbiya tace ko nawa kike so zamu kara
miki ki gayamana abu akanta kawai, “gimbiya tace lailai
yau na hadu dayan duniya, ta masu kallon banxa tace ku
fice mun daga office kafin insa ayi waje daku, Meerah
tace toh xamu tafi, ta dauki paper ta rubuta mata
contact dinsu incase in ta canxa mind din gayamasu
wani abu, suka fice. gimbiya taja tsaki ta dauki paper
tasa a dust bin, ta kwashe kudin tasa a jakar ta, “dama
naiman kudi take ido rufe, saboda gwamnati tayi seizing
licences dinta na makarantar akan zarginta da ake na
saida dalibai,” tayi murmushi tace sumy amfanin ki yazo
rayuwata, ta binciko file din sumy ta kwashe address din
gidan su…….ta kyalkyale da dariya tace gobe sai Kanon
Dabo :oops::oops::oops::oops:Hmmm tashin Hankali
kursum get ready gimbiya na hanya. *Xarah Bêê*
*Dedicated to bady social* ~Luv u all~ [05/09 12:52
pm] xarah bukar : KURSUM By ~Xarah Bukar Page Dadaddare huzaifa yazo daukan salma, har bakin mota
kursum ta rokata,suna ta hira da dariya kaman dama
sunsan juna”ta gaida shi ya amsa da fara’a sa yana
tsokanar ta da autar kakus (hajiya),tayi dariya tamasu
sallama ta koma ciki…….. Bayan kwana biyu jikin hajiya
yayi sauki, “kursum ta shigo dakin rike da magani da
ruwa, tace hajiya lokacin shan magani yayi “ta ya mutse
fuska tace maganin sai dacin tsiya a dole kawai nake sha,
tayi murmushi ta zauna tabata maganin da ruwa tasha
sannan ta gyara mata kwanciya, zata fita hajiya tace
Sumy kawarki da kukayi accident, ta rasu iyayanta sun
sani kuwa? Dam gaban kursum ya fadi, ta dawo ta zaune
tace Ai marainiya ce bata da kowa, dama gidannan zamu
zo, “jikin hajiya yayi sanyi,da gangan dama ta tambaye ta
Dan taji labarin yar’ta ,ta nisa tace Allah yaji kanta amma
ya akai tayi surviving a skull din tunda kince bata da
kowa “kursum dake sharar kwalla tace abun tausayi ko
kayan sawa gimbiya bata siyamata saidai Sumy ta bata
akayanta,excursion ma baa zuwa da ita,tunda bata da
kudin biya,” hajiya tace wace Sumy CE ke bata kaya?
Kursum data gano kuskuren magananta tace ni mana
Nike bata kayan. Ran hajiya ya gama baci, aranta tace
wato diamonds din da akaba gimbiya cinyesu tayi,alhalin
ko wana diamond worth 2.5 million ne ,shine ko kayan
sawa bata iya siyawa yar’ta, wani irin tsanar gimbiya
taji……”ta kalli kursum tace ke tashi ki ficemin daga daki
,”kursum tace daga hira kuma sai kora kaman nayi laifi
,ta tashi sum sum ta fice, tana mamakin halin hajiya
wataran ayi hirar arziki wata ran kuwa ba mutunci…
Kina ganin akwai Hope kuwa,kwana biyu da dawowan
mu amma shuru matan nan bata Kira ba, “meerah tace
haba zee duk kin tada hankalin ki, idan ma bata kira ba
zamu samo wani mafita, zee tace ai dole in damu dan
yanda nake ganin taketaken ya yazid zai iya rabuwa dani
ya komawa Sumy, meerah taja tsaki tace karfa ki manta
tun farko dama baice yana sonki ba,kece kika makale
mai, so don’t be surprise idan ya rabu dake, zee ta bata
rai tace koda na makale mai aiya kulani, kuma yanxu
Gidan su zani coz nasan he is still angry with me ko calls
dina bai picking ,ko kallon meerah batai ba ta suri
Jakarta ta fice……… Zaune suke a dinning suna lunch,
Umma tace “son hurry up ka wuce airport saura 1hour
flight din abbanka yayi landing, banaso ya jiraka, “yace
toh umma ina gamawa xan wuce,” bugun kofa sukaji
anayi da karfi, umma ta kwallawa hajara (mai aiki) kira
taje ta bude,”tana budewa zee ta ban gajeta ta shigo ciki
tana kwalla wa ya yazid kira batama lura dasu ba, umma
ta bata rai, azuciyan ta tace dama nasan sai crazy girl
dinnan, dan haushi fasa cin abinci tayi ta tashi zata wuce,
“yazid yace umma baki ci komai ba ? Tayi banxa dashi,
sai sannan zee ta lura dasu,ta karaso da sauri tace baby
ashe kana nan shine kayi shuru,ta kalli umma tace
sannu,” umma ta balla mata harara ta wuce. Taja kujera
ta zauna ta tace “baby miyasa mom dinka ke treating
dina lyk nobody kaman ba future in-law taba, “ya tamke
fuska yace” Ai baki taba gaishe taba iyaka cinki sannu,
sannu ko ba gaisuwa bace, ta turo baki tace “nifa ko
babana bana gaisarwa balle ita, bata isa ba, yazid daya
gama fusata ya mike tsaya yace uwartawa CE bata isa
ba ? hankali kwance tace Yes, ” Rai abace yace ban taba
sani u are crazy ba saiyau ya dauki car keys zai fice, tayi
saurin riko hannun shi ta rungumo shi ta baya tace yes
am crazing in love with you, “a fusace ya tureta,ya kalle
ta yace diz is not love,u are only obsessed with me,
infact nida ke it over……what ta fada a firgice tace are u
breaking up wit me? Yace yes,ko juyowa baiba ya fice
abunshi. Duniyar gaba daya tai mata zafi, kuka take
rusawa ta shiga fasa plate da cups dake kan dinning
,tabbas tasan saboda Sumy ya rabu da ita,amma tayi
alkawarin bazai taba samun taba cox sai tayi destroying
life dinta, sai zage zage take kaman tababbiya. Umma
dake daki ta fito da sauri jin fashe fashen yayi yawa,
ganin zee na displaying madness yasa ta kira hajara tayi
waje da ita…..zee tace basai anyi waje dani ba, nasan
hanya, kuma nasan makircin kine yasa ya yazid ya rabu
dani, “Allah ya shiryeki kawai umma ta iya ce mata, taja
tsaki tabar gidan. Office din baba Shehu ta wuce, yana
zaune yana waya ta banko kofa ta shigo tana kuka, ba
shiri ya ajiye wayan ya karaso gabanta yace zainab kukan
mi kike ? Ina kika shiga kwana biyu ban ganki ba ?” Cikin
kuka ta tsara mai komai har zuwan su bauchi, baba
Shehu yayi dariya yace halina dake u ar alwyz crazing
bakya Abu da tunani, “ta bata rai tace Baba ka daina
cemin am crazing ina da hankali, I don’t knw y mutane
ke cemin banda hankali, yayi shuru yana tunani, koda ya
auri jamila (maman zee) tana da mental illness harta
rasu, shiyasa sumtymz zee take abu kaman mai hauka,
ya nisa yace ,” am sorry auta ta….ta kyalkyale da dariya
tace to baba yanxu miye mafita, yace karki damu zan
tura private detective dazai binciko miki komai akan ta,
tun daga ranar da aka kaita school din, abunda kikeso
kenan koh ?da fara’arta tace eh, yace toh yanxu abu biu
zakiyi idan kinaso komai ya tafi daidai, da sauri tace me ?
Yace dole ki nunawa yazid kin hakura dashi sannan
kuma kija Sumy ajiki yadda bazata gane abunda kike
shirin yiba, ta kwalalo ido waje tace”gaskia baba bazan
iya, yace toh ke kikasani tashi ki tafi,”ta ma rairace fuska
tace na yadda xanyi, yace toh ki wuce gidan kafin in zo
tace OK ta fice da murnan ta…… Shima sai murmushi
yake dan perfect tym yake jira ya kawar da Sumy once n
4 all. Washe gari, hajiya na zaune a parlour tana cin
abinci, zee na kallon TV, kursum ta sauko zata wuce
office kusan kwana biu bata jeba, ta gaishe da hajiya ,”ta
amsa a yatsine ne ,zee dake gefe tace my sis har zaki
tafi,kursum da taji maganan bambarakwai,tace eh ta
masu sallama ta fice. Zata shiga mota taji hayaniya
abakin gate, ta karasa wajan da sauri, mai gadi daya
hango tana zuwa, ya kalli matar dake tsaye da Da niki
nikin akwatuna, yace yauwa ga madam Sumy nan zuwa
kwayi magana dan bazan bari ki shiga gidan nan
ba,”gimbiya tayi shewa tace gidan nan shiga daram. Tana
leka waje sukayi ido hudu da gimbiya hafsatu,dam
gabanta ya fadi ,gimbiya data gama tsorata tace baki
mutu ba dama…….. Da sauri kursum taja ta gefe ta tace
mi ya kawo ki gidan nan, gimbiya tace aike xan tambaya
kin mutu miya kawoki nan,INA Sumy ? Kursum tace ai
Sumy CE ta rasu bani ba, yanxu haka yan gidan sun
dauka nice Sumy, long story ne idan mun zauna xan baki
labari ,”ta bude Jakarta ta zaro makudan kudi ta mikawa
gimbiya tace ga wannan ki koma bauchi yanxu nan,
zamuyi waya……gimbiya ta kece da dariya tace Ai baki
isa ba, babu inda zani, kursum tace koki tafi ko in kira
securities su fitar dake daga nan, “ta kara kecewa da
dariya tace ai ke zabi ya ragewa, ko ki barni in zauna a
gidan ko kuma inje in tona miki asiri,kinga dagani harke
mun rasa , balle ke da baki da wajan zuwa. Kursum data
gama kulewa tace Baza ki zauna a gidan ba, kiyi abunda
zakiyi. Gimbiya tace toh zakiga Abunda zanyi kuwa, ta
bangaje maigadi ta shige gidan da gudunta, Agigice
kursum ta bita tana cewa tsaya!! Tsaya!! Muyi magana,
amma ina…..gimbiya tayi nisa batajin kira, harta karaso
bankin parlour ta tura kofa ta shiga…….. Tashin sense
:oops::oops: *Xarah Bukar* *Dedicated to Bady social*
~Luv u all~ kursum 56 to 58 Posted by XARAH
ABUBAKAR on NOVEMBER 13, 2016 [06/09 10:53 AM]
Xarah Bukar : KURSUM by ~ Xarah Bukar Page Hankali
kwance ta tura kofan ta shiga da sallaman ta, hajiya ta
amsa tace waye ? Zee ta juya taga gimbiya, tace baiwar
Allah aida baki zoba kin kiramu ta waya, sai sannan
gimbiya ta gane zee, itace marar kunyan nan da sukazo
naiman labarin sumy, taja tsaki tace bansanki ba kuma
ba wajan ki nazo ba, hajiya tace zee kinsanta tane ? Zee
tayi shuru, hajiya tace bakuwa gurunwa kikazo ? Caraf
kursum ta shigo tace gurina tazo, kuma a gidan nan zata
zauna, hajiya tace bazata zauna ba, Ai nan ba hotel bane
daza ki kawota, gimbiya tace haba hajiya nice fa gimbiya
makarantar da Sumy tayi harta girma, yadda na kulan
miki da ita bai kamata ki Kore niba, “ran hajiya ya gama
bacci, wani irin tsanar gimbiya taji a zuciyar ta,aranta
tace wato matar nan itace ta maida min kursum abun
tausayi ko kaya bata siya mata. Ta nisa tace koda kike
riketa aiba kyauta bane kudi aka baki, na baki minti biyar
ki ficemin daga gida….. Gimbiya ta kalli kursum tamata
signal kotasa baki ko kuma ta tona, ” kursum tayi Gyaran
murya tace gaskia hajiya saidai kiyi hakuri, dole gimbiya
ta zauna agidan nan, tunda gidana ne, “hajiya data gama
fusata tace to na yadda ta zauna amma ba nan tare
damu ba, ki kaita can bangaran masu aiki ta zauna,
kursum zata kara magana hajiya ta daka mata hannu
tace nagama magana, ta dogara Sandar ta tahau ra
sama…….kursum tace nizan wuce office ta fice,da sauri
gimbiya tabi ta tace amma dai hajiyar nan bata da
mutunci, kursum tace karki CE haka dan kuwa bata da
matsala, kiyi hakuri ki zauna a part din masu aiki kafin
insamo mafita, idan kika Kama kanki zakiji dadin zama
da ita, makauniya ce ba gani take ba,gimbiya tace kina
nufin duk kwalliyan datayi da uban dauri da bakin glass
din bata gani ? Tace kwarai kuwa,tun wajan shekaru 18
da suka wuce tasamu matsalan ido, gimbiya tace
shikenan ki tura masu aikin su gyaramin dakin, kursum
tace toh kayan ki ma xansa ashigo dasu, xan wuce aiki
saina dawo. Gimbiya ta koma parlour ta zauna, zee ta
kalle ta taja tsaki tace ashe bakin ku Da ita shiyasa kika ki
bamu details akanta, gimbaya tace yarinya ni kike jawa
tsaki ? Zee tace eh mana ke wace CE ? Gimbiya ta mike
taje har gabanta ta kama mata kunne gam tace idan kina
takama ke yar bariki toh ni sunana na biyu bariki, ki
kiyaye ni danni ba tsarar wasanki bace,kina jina ? Zafin
da taji yasa Ba shiri tace eh naji kisake mun kunne, saida
taga kunnen yayi jajir sannan ta saki ta koma kan kujera
ta baje, “da sauri zee ta tashi tace muguwa ta gudu
sama……….. Agurguje plz…….. Kursum ta koma bakin
aiki, takan kiran inna taji ya hanifa, tsakanin ta da yazid
sai wasa buya bata barin su hadu dan ta tabbatar ta
kamu da son shi. tsoranta daya bai wuce kar asirinta ya
tonu ba. Hajiya ta warware sosai, bata shiga harkan
kowa a gidan kullum tana makale adaki, kursum tana
shigowa gaisheta ta bata magani. Yazid ya kanzo

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment