Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

BAKIN JININA YAJAM S2 na YAR MUTAN KANKIA



*BAKIN JININA YAJAMAN😭*


*NA*

_Yar Mutan Kankia❣️_

*_TRUE LIFE STORY!_*

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

_*DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI.*_


*Godiya ta tabbata ga Allah daya sake ara mana lokaci mai tsada da dimbin daraja inda zamuci gaba da labarin rayuwar Amina,yanda muka gama ALQALAMI Season One lafiya Allah yamu ikon gama BAKIN JININA YAJAMAN Season two ameen.*

_Naga sakonin ku dafatan alkhairin da kuka dinga yiman,Amina Caranci nagodiya Allah yabar zumunci._

*Muje zuwa🤸🏻‍♀️*

S2/E1&2


Na shiga tashin hankali tareda kalubale na rayuwa narasa duk wani farin cikina da sukunina kullin ina cikin zullumi da fargaba musamman halin dana tsinci kaina a Jami'a ga tarin fargaba marar misaltuwa a gefe guda kuma ga challanges na dangi da yan unguwa kowa da abunda yake faɗa akaina bayan kowa yasan yankema mutun hukunci akan abinda baka da ilimi akanshi haramunne,lallai nasan komai yake faruwa dani yana cikin Qaddarata amman ya zanyi bayan nasan koma minene yanada sila da *BAKIN JININA YAJAMAN!*

_Amina Caranci kenan wadda take cikin wani yanayi na rayuwa._

*Muje zuwa domin cigaba da labarin gadan gadyayi


_Cigaban Labari*******_


Fatash ta fito a cikin motar Ya Taufiq kallan dayake jifana dashi kadai yasa na sha jinin jikina hakan yasa a hankali nafara takawa zuwa inda motar shi take a tsaye kaina kasa nike tafiya saida na kusa isowa bakin motar ya figi motar shi har kura nadan tashi yai tafiyar shi wani irin mummunan faduwar gabane ya riskeni narasa dalilin jin hakan take na shiga damuwa.


musamman hudubar dayake yawan yi mani ta dawo mani cikin kwakwalwata jinayi duk ban lafiya,karfin hali kawai nayi jin Fatash ta kamo hannuna muka juya zamu koma hostel.

Amina pls kitsaya ki saurareni cewar Ahmad dan harna manta dayana wajen.
Cak na tsaya saidai ko kallan shi banba,saima wani irin haushin shi da naji ina blaming dinshi akan abinda ya faru.


"Amina ki saurari abinda nafada maki karkimin haka."
Daga mashi hannu nayi najiyo raina a dagule nace.
"Dan Allah Ahmad ka sauraramin kabarni da abinda yake damuna na rokeka kafita rayuwa karkayi gigin shigowa a cikinta dan baka da wani muhalli da zan iya baka,kabarni dan Allah karatu ke gabana ba wata soyayya ba."

Ina gama fadar haka na fisgi hannun Fatima muka tafi daki ji nike kamar inyi kuka,musamman da Ya Taufiq yatafi a fusace kuma nasan hakan ya nada nasaba na ganina da wani bayan alqawalin da nai mashi bazan kula samari ba,duk da Ya Taufiq yace yana sona amman nasan tunda har aka fasa sa ranar mu,zai hakura da sona,saboda hakan yake yimana fada kada mu kula samari mu dage akan karatu,sai gashi tunkan tafiya tai nisa ya ganni da saurayi.



"Haba Minal akan mi zaki zauna kina dogon tunani kin tisa abinci gaba kina kallo kuma kinki yin magana."


Hmmm Fatash kenan dan Allah kibari bakisan yanda nikeji bane,tunkan karatuna yai nisa nafara samun matsala ga wannan Ahmad din da Ya Taufiq ya ganni dashi na tabbata zaiga ban dauki maganar da mahimmanci ba kenan."


Aaa sam bakisan Ya Taufiq bane ko maganar da wahala yai maki ita saidai zai baki shawara,kuma tunda kince baki son shi ai komai ya wuce."


"Allah yasa,amman abin na damuna."
Da haka mukaci gaba dacin abinci amman saidai badan yai mani dadi ba,hankalina kaf yana wajen Ya Taufiq fatana Allah yasa kada yaiman maganar Ahmad dan bansan mi zance mashi ba,saurin cire hannuna nayi a cikin abinci tuna maganar Dr JJ ya zanyi dashi.



Kaina ya sara mani hakan yasa naje na kwanta da tunani iri iri araina,ko bacci na kasa jin ana kiran sallah natashi nai alwallah natada sallah.



****** Lecture Theater zaune muke bisa Chairs kowa yazo da wuri muna jiran shigowar Dr JJ dayake shike garemu kuma ka'ida idan kayi late bazaka shiga ba,ya iya disga mutun wannan dalilin yasa kowa ke shayin ya rigashi shigowa Class,zaune muke na kifar da kaina kasa inata nazari abubuwa sun mani yawa,domin bansan sadda Dr JJ ya shigo ba,kowa yai shiru annatsu harya fara lecture,saida ya duba gaba kamar yanda yasan nan nike yawan zama amman ba alamuna,saboda koda na shigo second to the last sit na zauna, dan bansan muna yawan hada ido dashi inyana mana lecture musamman dayace yana sona,shiyasa na koma baya na zauna.



Rufe idanuna nayi kamar mai bacci,fuskata ta tana kallan ƙasa na hada hannyena bisa desk na daura kaina saman hannuna nayi zurfi a tunani bansan mi akeyiba,jin ta kusa dani tana bubbugani a hankali hakan yasa na dago in kallan ta,murmushi tadan yimani,ganin ba wani abu tace mani ba hakan yasa na sake kifar da kaina kasa.


"Baiwar Allah Dr JJ na magana."
Wani abu naji ya keta cikin kunnena a hankali nafara ɗago da kaina jin hall din yai tsit kamar an mutu ga idanun kowa akaina hatta shi dake saman step yai holding hannayen shi.

Stand up."
Shine abinda yace mani,mikewa nayi duk na tsargu.
What are u doing?" sorry sir."
Abinda nace mashi kenan ina kara maida kaina ƙasa.
I say mikikeyi."
Nothing Sir."
Get out of my Class."
Jikina yai sanyi gashi ya hade rai,ganin idanun mutane akaina hakan yasa na dauki jikkata na fita duk nashiga damuwa dan bansan mi zaije ya dawo ba, nasan zaiyi tunanin saboda shi na koma last sit na zauna.


Ban wani batama kaina lokaci ba,na tafi hostel saidai Fatima bata dawo ba,abinci nafara kokarin girka mana.



******Baba Pov

"Maman Amina kinsan abin nan yana damuna yana ci mani tuwo a kwarya,musamman kananun maganganun mutane akan Mamana nagaji da al'amarin nan."


Ajiyar zuciya Mama ta sauke tace.
"Haba Alhaji hakuri shine zamuci gaba dayi kowa yasan wacece Amina baccin wannan kadararrar sa ranar da akai mata ai da bata shiga cikin wannan gutsiri tsomar ta mutane ba."

"Ni duk ba wannan ba dazun Hafizu ke mani magana wai yaji wasu samari nacewa wani saurayi yazo yana neman makarantar da take karatu, kowa yasan dagani saurayin tane,amman ni nasan ya'ta bata da wani saurayi kuma Taufiq aiba bako bane tunda yasan inda take karatu al'amarin ya dameni baki ɗaya."



Ba dadi amman haka Allah yaso komai zai zama labari,ni kaina kan wannan Jami'ar da tafi karkaso kaji kowa da kalar zancen da yakeyi sai kace kanta farau,koda yake kusan dai a cikin mata nan kusa damu ita kamar zan iya cewa tafara shiyasa abin ya zama zunubi Allah dai ya kyauta ya tsare mana ita da kariyar shi."


Ameen wannan itace addu'a ni nayarda da ya'ta kuma nasan wacece Amina Allah dai yai mata albarka."

Ameen ya rabbi.


*Fiction*

Taufiq ne cikin sashen shi yarasa mike mashi dadi musamman dayaga Amina tareda wani ,hakan ya taba mashi zuciya sosai shi kanshi har mamakin kanshi yakeyi tambayoyi yafara jefoma kanshi.


Miyasa Minal zatai mani haka? Waye shi,mi yake nema wajen ta?ya zatayi da karatun ta idan harta fara soyayya? Can kuma wata zuciyar tace miye ruwan ka tunda tana ganin wannan rayuwar itace dai dai da ita,karabu da itaTaufiq kaima kaje ga yan mata nan kala kala kanema ka aura,akan mi zaka tsaya batama kanka lokaci akan kankanuwar yarinya waddama ba sonka take ba,da bakinta tace bata sonka gashi Abba yace baka aurenta mizaisa ka damu kanka,ga dan uwanka can da matar shi sai kai,haba Taufiq kafarka daga baccin daka lula kullin fa kara shekaru kakeyi Hussein!

Can kuma ya girgiza kai kamar wani zautacce a zahiri ya furta.
Never bazan iya rabuwa da Minal ba itace zabina ina sonki so na hakika dake na shirya rayuwa Minal in kinga ban aureki ba kilan Allah baisa zan aure ba a rayuwata ba amman kece farin cikina Minal dan Allah kada ki kula kowa kiyi karatu Aminatu."


Ya ida maganar yana kallan picture dinta yana karajin sonta a cikin zuciyar shi.



Amina Pov


Tunda Dr JJ ya koreni Class dinshi duk ranar da yakeda Class idan har yari gani shigowa ina zuwa zai korani,idan kuma ya iskeni ciki koda ina gaba zaune yana fara lecture zaiyi sending out dina waje tun ban damuwa harna fara,domin kowa yasan indai yafara tsanar mutun shikenan bai kara daga maka kafa sunsa tun korar dayai mani ta farko ce tajawo mani wannan tsanar daga gare shi,ni kuma nasan dalilin sa nayi mani hakan.


Gashi course din shi babban ne yana dauke da 4 credit unit kuma kowa na shakkar course din wasa wasa ankai sati ukku bai barina ina attending lecture din shi,gashi next week zai mana test kuma duk banda attendence dinshi rabi da kwata,ba kadan hankalina ya tashi ba daurewa kawai nike ina karatu saboda ya bada handout.


Kullin hankalina da tunanina nakan test din da zamuyi ta Dr JJ wanda kowane dan course din mu ya maida hankalin shi kanta.


Ranar Monday a ranar zamuyi test din tunda muka tashi da wuri nacema Fatash zanje Class domin yau mukeda Dr JJ domin haka kawai muke cewama Course din nashi da kace Dr JJ kowa yasan abinda kake nufi addu'a taimani tace ita yau bata da komai hutawa kawai zatayi.
Murmushi nai mata nace damani wlh bokon nan ba dadi karfin hali kawai nikeyi.




Fita nayi zuwa school area akan hanyata nasamu Commercial motor na hau har gaban Department suka ajeni na karasa ciki,kai tsaye theater na nufa aiko rabi da kwata duk anzo banfi minti da goma da zamaba saiga Super Visors sun fara zuwa,ciki duk ya duri ruwa saboda first test dinmu ce a University,musamman yanda ake zuzzuta mana lecturer din da rashin mutuncin shi ga ya iya setling Questions,suna shigowa kowa ya nutsu haka suka gama setting arrangement dinmu jiran shigowar shi kawai ake yana shigowa ya tsaya daga baya aka fara raba Question Paper saida kowa ya samu sannan ya tafi dayan hall din saboda watsamu sukayi wara wara akai mana,duk da bawani karatun kwarai naiba amman dana duba Question din sai naga nasan wasu harda tambayar da yaimani a class ya dawo da ita ban wata wata ba,nafara answering hankalina kwance duk da akwai apply Question sai nafara amsa wadda nasani,ina cikin answering naji an fizge mani Paper saboda a Fullscape muke test.



A firgice na dago zuciya ta na bugawa naga Dr JJ yana mani wani killer smile dukar da kaina nayi nace.
"Sorry sir dan Allah kabani in ida pls."
"Get out."
Hankalina yai bala'in tashi kaina ya kulle ganin first test dita zanfara da kora kuma babban Course irin wannan wanda kusan shike rike da GP dinmu.
Bansan na duka ba nafara bashi hakuri har idanuna sun kaɗa,haka lecturers din suka fara bashi hakuri ganin yanda na rude na fita tunanina amman ya kafe saina fita karshe cewa yayi.

"Idan nayi counting one to three i swear i will give u a Carry Over (CO)."
Jiki mace na mike ina kwalla a gabana ya yaga mani paper din ya watso mani ita,bisa step naje na dauki jakata natafi ina kwalla,jikina yai masifar sanyi har banganin gabana tafiya kawai nike bisa titi bansan mike damuna ba hankalina bai jikina ga ciwon kai wanda tsananin damuwa harya zame mani jiki tsallaka titi nazoyi naji ana banka mani uban Horn na tashin hankali,har saida mota ta kusa gogata,a rude na dawo duniyar damuwa ganin wasu har sun aza hannun su,bisa kai alamun sallallami sukeyi dan dayawa an dauka motar tabi ta ruwan cikina,ni kaina jikina banda mazari ba abinda yakeyi na watsar da jikkata sai wayata dake yashe ƙasa ni kaina kasan nike zaune dabas banda rawar gabbai ba, abinda nikeyi kaina keta juyaman ina ganin mutane kashi kashi,suna juyawa bansan na aza hannaye na bisa kunnena ba na saki uwar kara mai rudarwa ina jijjiga kaina.


Shiko Driver din yai zaune yakasa fitowa duk tsoro ya kama shi ganin naki tashi wadda ke gaban motar ta fito tana sannu baiwar Allah tashi,Allah ya auna mana arziki,shima sai yanzun yajawo kafa ya fito ran shi abace yace.....






_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Pls
❣️


*BAKIN JININA YAJAMAN😭*


*NA*

_Yar Mutan Kankia❣️_

*_TRUE LIFE STORY!_*

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

_*DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI.*_


S2/E3&4



"Wane irin sakarci ne wannan bayan kin hayema mota,Allah ya soni ban takeki ba,shine zakizo ki mana zaune akan titi, dallah malama kitashi bani wuri stupid.!"


Kaina na dago ina kallan shi ko keftawa banyi sai kwalla da suka samu damar cigaba da zirara bisa idona maganganun shi suka bani mamakia,sai yanzun juwar tasamu damar lafa mani,wato baima tambayar lafiya ta shine zai fara yimani bala'i.



Haba yaya bai kamata kai mata fadaba ai barka zamuyi ma juna tunda bataji ciwo ba,kamani tayi ta dagani ta miko mani jikkata da wayata harta dan fashe.


ina sakala takalmina nai saurin cire kafa saboda zugin da tai mani banjin zan iy takata sosai,godiya nai mata najuya ina tafiya a hankali tace,in shigo su rage mani hanya maganar Ya Taufiq ta fado mani arai yai mana kashedin hawa lift shiyasa naki yarda da kyal tasamu na amince har hostel suka kawoni sannan na sauka na tafi,ina dingisawa a hankali,ji nayi anrikoni kanwar shi tace dan Allah ya sunanki."
Amin Yusuf.
Ni kuma Zainab Sule Garko."
Bari inrakaki dakin ki naga kin razana bakida kwari sosai.



Ban mata musuba muka tafi a hankali nike jef kafata duk tai mani tsami muna tafiya tace.
" dan Allah Amina kiyi hakuri akan abinda Ya Hafiz ya fada maki saurin fushine dashi kinji."
Bakomai nace mata har muka shigo room dinmu,yanda nike tafiya hkan yasa Fatash tashi da sauri ta taroni,lafiya Minal miyasame ki.?"
A rude take tambayar mu,Zainab tai mata bayani tace
"Ai an auna arziki Allah ya kyauta gaba,level one kuke.
Eh muka ce mata."
Nima 100level nike ina karantar Pharmacy."
Kufa ni nace mata Medicine Fatash Enginearing."
Nan tai mana bankwana tace a gari take zaune.


Tafiya tayi nikam kamar jira nahau kuka ina cewa
Nabani Fatash kwanana ya kare ya zanyi."
Haba Minal kidaina kuka tunda abin yazo da sauki dan Allah.!"


"Ba wannan ba Dr JJ ya hanani yin test dinsa kuma over 40 zaiyita zanyi making wannan uban mark din da narasa mi nai masa da har ya tsane ni haka,dan Allah minene mafita ya zanyi ya tsaneni bai sona ni kadai yakema haka,wlh Fatima nafara zargin Bakin Jini gareni,inba hakaba akan mi zai hukuntani ta hanyar tsanata banci ban sha mashi ba kuma....



Kukan yaci karfina naita kuka tana lallashina tace.
"Ni banga wani bakin jinin da zakice shi yaja maki ba,kawai dai kije ki bashi hakuri zuwa gobe kiji mi kikai mashi insha Allah zai maki make up dinta kidaina kuka.

"Shiru nayi ina tuna yanda nayi dashi a office din shi gashi har an shiga wata ɗaya bankara bi kota kanshiba yanzun taya zanfara yi mashi maganar,nasan da whala ya hakura,ajiyar zuciya kawai na sauke ina gayama Allah kukana.


Saidai still kwalla nike tun Fatash nabani hakuri harta gaji ta kira Taufiq tagaya mashi na samu accident,inajin yanda yaketa jera salati yana fadin garin yaya hakan ya faru? tai mashi bayani da yace tabani wayar sai kuma naji yace wait ina zuwa i will call you.
Katse kiran tayi nace.
"Akan mi zaki gaya mashi bayan kinsan shima yanajin haushina dan Allah Fatima wlh da baki gaya mashi ba,in ya kiraki mizance mashi nidai kibari nasan zuwa nan da gobe kila in iya taka kafata sosai,da baki ɗaga mashi hankali ba."

Kedai kibari nasan zai samo maki magani shiyasa na gaya mashi sannu,kije kiyi wanka.

Mikewa nayi ina dafa bango na cire kayana nayo wanka na sauya wasu kayan sannan na kwanta,sainaji kwarin jikina saidai inata sake saken yanda zan shawo matsalar dake shirin kunno mani kai a rayuwa ta.
Bansan nayi bacci ba dan nakwshi gajiya sosai.



Mami Pov


Tunda ta shigo gidan su Amina ko sallamar kirki babu itada wasu samari saidai kana ganinsu kasan kannen tane,akayi sa'a Mama suka iske zaune a falo karar saukar kafat aja anjefo shi tsakar daki tif,hakan yasa ta mike tana mamakin ganin Mami sai huci take.



"Lafiya kike bina da idanu ai nasa kinsan da zuwana bayan kun nace sai kunci dukiyar mu, akanmi zaki nuna mamakin ganina a fuskar ki kayane ko gasu nadawo maku dasu? kamar yanda mayyar Yayar mijin naki ta kitsama Alhaji yasa na maido hankalin ku ya kwanta sai kuyi yanda kukeso, indai sunana Mufida Shehu, yarki Amina tayi aure ingani,ai duk wanda yaci tuwo dani wlh miya yasha miyar ma baisha taba eheh,wuce muje Tasi'u.!"


Tsaya Mufida,kike maganar indai aurene ya'ta tayi kigani ko?kisa a ranki tayi tagama koda ba ya'yan kuba,ai Allah yabata masu santa kuma wa'ɗannan tambadaɗɗun kayan naku basu muke jiraba shiyasa aka aika maku da tsiyata kunku tunda wuri saboda maitanci da son hada iri da yarmu shiyasa kika kara dawowa dasu,to ya'ta tafi karfin ki,kuma aure saitayi kuma sai kingani da izinin lillahi."


"Ni daku muzuba mugani saina zame maku kadangaren bakin tulu,dani kuke maganar kuma Amina ita dajin dadin duniya saida taga anayi.

tunda nike bantaba neman abu narasa ba amman akan yarku saida ɗana ya susuce sannan kuka hanashi yanda yarasa kowama ya rasa kuma tayi auren ingani matsiyata."

ta Allah bataki ba Mufida ya'ta tafi karfin ki da izinin Allah."

Da haka tabar gidan,aiko duk jikin Mama yai sanyi batasan tafara kwalla ba tin kalaman Mufida suna bata mamaki har sun fara bata tsoro, koda Baba ya dawo ya iske kaya tagaya mashi itace ta maidosu baiji dadiba hakan yasa ya kira Alhaji Sarki yana dagawa yace.

"Aslm Alhaji barka da yamma ya iyali."
Alhmdullah.
Daman nadawo gida na iske kaya ankuma dawowa dasu dan Allah kayi hakuri bada wata manufa na maidosu ba hakan shine kwanciyar hankalina."
Hakuri Alhaji yahauba Baba sannan sukayi sallama.


Kiyi hakuri Khadija nasan yanda zamuyi da kayan nan nai alqawalin zuri'ata bazasu cisuba kodan gorin da akaimana akansu da zargin da suka jefamu a ciki dan haka zan siyar dasu komai kenan zan gaya maki manufata.


Toh Baban Zainab amman kaji abinda Hajia Mufida ke cewa akan Amina lamarin yana bani tsoro fa."

Haba dan Allah bansan sakarci ai bata isa taimata abinda Allah bai kaddara mata ba,komai yasamu Amina kisa aranki Qaddarar tace kun fiye canfe canfe wlh."


Haka Baba ya gama gwasale zancen sannan ya dibe kayan ya fita dasu daga gidan baki ɗaya.



Amina Pov.


Bayan la'asar wajen karfe shidda saiga kiran Ya Taufiq ya shigo a cikin wayata raban daya kirawoni yakai wata ɗaya tun ranar daya ganni da Ahmad yatafi ko dubamu bai kara zuwaba bare yai waya dani hatta Fatash bai waya da itaba,saida ta kirashi tace nasamu accident.


Dagawa nayi jikina sanyaye bayan na nunama Fatash kiran da yake mani murmushi kawai naga taimani sallama dauke a bakina.
Amsawa yayi a kausashe duk lokacin da zaimani wannan muryar nakan rasa sukuni ina shiga dauwa domin tana razanani.
Kufito bakin gate inajiran ku."
Kashe wayar shi yayi kallan ta nayi nace yana jiran mu a waje."
Toh tace,ta tashi tana saka kaya jikin ta,nikam da doguwar rigar atamfa a jikina veil dina kawai na yafa mukafita,tsayawa mukayi neman motar shi, kiran mu yayi ina dagawa yace.


"White Matrix car ina ciki".
Sai a lokacin muka kai kallan mu a motar sabuwa dal da ita,sai daukar ido take araina na yaba da tsarin motar lokacin tana sabuwar shigowa,muna zuwa duk muka zauna baya,gaida shi mukayi.


Banza yai mana ta mirrow yake kallan mu,dan bugoni Fatash tayi tai mani nuni inzauna gaba, komawa nayi na zauna,ina rufe marfin kofa yaja muka tafi jinayi jikina yai sanyi itako Fatash sai aikin danna wayar ta takeyi niko tsoro ya kamani ina tunanin ina zai kaimu musamman dana ga munbar makaranta,mun shiga cikin gari,tsoro Allah tsorona kada wanda ya sanni ya ganni yasanarwa Baba anganni cikin wata mota,sarai ya gane a tsora ce nike yanda yaga na takure amman yayi kamar bai ganni ba.


"karkata motar shi yayi zuwa wani Cleanic muna shiga already sunyi waya Xray akai mani a kafata aka bani photon ba abinda yasamu kafar tawa sannan mukaje gun likita akai mani check up ya rubuta mani magunguna bayan yai mani tambayoyi ina bashi amsa har da ciwon kai nace inayi daga nan muka biya pharmacy ya sai mani maganguna,muka hau mota ya wuce damu wani super market ya siyomana su biscuit da lemuna sai kayan tea da bredi,sai Youghourt katuwar jarka,haka aka samana a boot mukayi school har bakin gate ya tsaya yace.


"Fatima kwasar maku kayan kai maku daki."
Toh tace fita tayi ta fara dauka ta tafi daki.
Nima fita zanyi intayata dauka.
"Anshi.
Ledar magunguna ya miko mani ansa nayi nace, nagode Allah yakara arziki.
Jinjina kanshi yayi zan fita yace.
"Minal."
Dawowa nayi na zauna,Na'am nace.
"Kin tabbata ba inda ke maki ciwo.?"
Eh babu naji sauki."
"Masha Allah,ki dinga kula da kanki kinji.?"
Eh insha Allah zan kula."
Da aka bigeki da mota waya dawo dake Hostel.?"
Yai mani tambayar yana kallan wayar shi."

Shi ya dawo dani."
Kallona yayi yace.
Bance banda shiga motar kowa ba.?"

Yaya ai harda kanwar shi itace ta tai maka mani ta dagani shine tace bari sukaini time din ban iya tafiya sosai."
Kallan kafar tawa yayi tadanyi hushi kadan ya kauda kanshi yace.
"Sorry Allah ya baki lafiya,ku kara kula banda yawo ko hawan lift.

Ina fatan kingane wuce kije,ina sauri."
Tom kagaida mani da Mum."
Okay ita kadai kikasani kenan baki gaida ɗan uwana ko.?"


"Aaa harda Ya Tariq da Anty Aisha."
Tom zasuji kuma kice da unborn baby na."
Murmushi nayi ganin farin ciki fal aranshi sai smile yake dagani yanaji da cikin matar Tariq dan fuskar shi ta nuna hakan."
Ina gaida shi Allah ya kawo mana shi lfy."
Ameen ya hayyu ya qayyum."
Lekowa Fatash tayi tace.
"Wato fira kukeyi kuka barni da jidar kaya ko wlh wannan son kaine.!"
Sorry kawata muje in dauka."
Bayan duk ba kwashe su ni kadai ai shikenan."

Rigimammar Abba ko ina sai an nuna hali baki gani itadin patient ce ki tausaya mata mana."
Tom Yaya ai nagama kwashewa, bakomai."


sai anjiman ku,adage da karatu."
da haka yaja motar shi ya tafi,muma hostel muka shige.


******"Ki kula da addu'a Amina karki saki jikin ki,kuma sai kin yawaita azkar."
Cewar Mama da muke waya da ita tun dazun hankalin ta ya gaza

Please Login or Register in order to submit comment