Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akan soyayayarmu har istihara yasa mukayi,kuma cikin ikon Allah sai muka kara samun nutsuwa da junan mu sosai.


Yau kam da Husna niketa waya wasa wasa bai wuce sati daya bikin ta,sai tsara yanda zamuyi hidimar mu, mukeyi kusan kullin ina waya da Abdallah, itama taje Camp anyi posting dinta kano can zatayi service dinta,komai ya tafi cikin tsari,inajin dadi inna tuna kawata zatai aure ta hutama ranta kuma mai sonta zata aura.

Yau litinin natashi da wani irin matsiyacin ciwon ciki da kai,ba abinda nike kyarawa sai uban amai kamar yan cikina zasu fito tun safe nike abu daya.

Idan Fatash tace zata gayama Ya Taufiq sai in hanata aganina zan samu sassauci akan tilas takira Ya Tariq lokacin anci sa'a ya shigo Zaria bai jimaba yazo Makarantar mu ya daukemu nida Fatash sai Kaduna dan kuwa bansan inda kaina yakeba hospital dinsu yakaini aka tafi dani Emergency daura mani ruwa akayi da allurar tsaida amai,direct aka sake shi yana karewa aka saman wani a hankali tareda allurar bacci sai magunguna.

Bacci yai awan gaba dani Fatash ketare dani sai matar Ya Tariq sosai suke bani kulawa dare yayi sukabar ni da Fatima zata kula dani dayake hospital din ta kudice komai a tsare yake.


Washe gari da safe naji dama dama ajikina a ranar Mum da Mami sai Abba sukazo ganina tunda sukazo Mami ke aika mani kallan tsana nidai kaina kasa a hankali na gaidasu suka amsa.

Sannu ya'ta ya jikin naki.?"
Da sauki Abba."
Allah yabaki lafiya kinji Amin dago."
Ameen.
Suka amsa,sawa yayi aka fiddo mani abinci da ice cream da kanshi ya matsa saida naci sunjima a sibitin.
Mum tabani Baba muka gaisa yaimani ya jiki haka nagaisa harda kannena sai Mama ita mun gaisa.


Karfe sha biyu suka mike zasu tafi dai dai Ya Taufiq ya shigo jikin shi sanye da kaƙi sai soldiers biyu a bayan shi.

Mikewa Abba yai yana welcoming din shi,tinda ya shigo idanun shi kaina ko keftawa baiyi."
Sannu Minal ya jikin.?"
Da sauki."
Nace mashi.
Major Taufiq."
Yes Sir."

"Yaka mata ka koma gida ka huta idan gari yai sanyi saika dawo tinda dawowar ka kenan

Ƙamewa yayi yana sarama mahaifin nashi sannan yace.
Thank you sir."
Baki dayan su suka tafi Mum nakara taba jikina ban zazzabi sannan suka fita dawowa ya Taufiq yayi a hankali yace.

"Mizan tahoma queen dina dashi."
Bakomai kazo da wuri."
Okay bye,Fatash take care for her."
Okay sir."


Da haka ya fita niko najidadi ice cream din da Abba yasa aka bani dan bakina yafara samun test dako nayi losing Apatite dina


Bacci yai gaba dani mai dadin gaske harna samu kwanciyar hankali ganin Baba yasan ina Kaduna bai faɗa ba hakan yasa nai bacci mai rai da lafiya.


Ban farkaba sai 3pm,da salati na tashi jikin garas Ya Tariq ne ya shigo yakara dubani sannan yaba Fatima magani yace innaci abinci tabani insha.

Fita yayi ya koma office.
Tashi nayi nafada wanka sosai naji dadin wankan ko man shafawa ban safa ba,na zira doguwar riga purple na koma na zauna kadan kadan Fatash ke mani fira.

Wayana yai ringing nadaga Husna ce taimani ya jiki tana tareda Abdullah muka gaisa ina aje wayar Ya Taufiq ya shigo cikin kananan kaya junse sai purple t-shart mai ratsin baki ajiki,murmushi fal a fuskar shi.

"My Queen ya jikin naki.?"
Am fine Prince ya aiki."
Alhmdullh"

Ohni Fatima ba'ajin kunyar yar kanwar taku,anfara QueenPrince ni bari in koma falo wannan abu har haka amman fa kunyi maching Allah ya cika maku burin ku."

Ameen muka amsa.
Fatima Sarki Mukhtar Munzali tawa ina jidake kanwata."
Cewar Ya Taufiq.
Dariya tayi tace,me too bro.
Da haka tafita.

Dawowa yayi kusa dani ya zauna bisa Sofa ya kalleni yace.

"Baby mike maki ciwo pls tell me.?"
A sanyaye ya tambayeni nikam idona kanshi sai karajin son shi nikeyi na ratsani duka sassan jikina.

Jin shirun yai yawa hakan yasa yai waving face dina.
Babyna wannan kallan fa ban kyauta ba ko.?"

Yace mani.
Girgiza kaina nayi nace.
"Ina tsoron kada Qaddara ta rabamu bayan nasaba dakai kuma kaine farin cikina in hakan takasance tabbas bansan ya zanyi da raina ba ina kaunar ka Yayana."

Ki daina fadan haka Minal insha Allah kece uwar ya'yana inaji ajikina bazan taba barin kiba domin kece Qaddarata tare zamuita rayuwa,nayi istihara naji alkhairi ajikina da jinina ina sonki Minal ina kaunarki,kece kika koya mani sakewa da mutane akan kisaki jiki dani nakoyawa kaina sabo dake har magana da mutane duk dan ke,kisa aranki Taufiq nakine Minal."


Ajiyar zuciya na sauke inajin dadi lallai nayi dacen masoyi.
Sallama mukaji, anyi Tariq ne ya shigo yana murmushi yace.

Mrs Taufiq our special couples,Allah ya cika maku burin ku na alkhairi.
Gaskia Littile Major nasan yaga kannen sa yaka mata aima Aira kanwa."

Dariya mukayi ina sadda kaina kasa
Ameen muka amsa.
Soon cewar Ya Taufiq.
Doctor Tariq Mukhtar yaushe za'a sallame Princes dita.?"

Yanzun nan kuwa Arth,Major Taufiq Mukhtar zan sallameta Allah yakara lafiya."

Ameen ya rabbi.
Bada jimawaba ya sallemu hada kaya Fatash tayi takai mota Ya Taufiq ya daukemu zuwa gidan su,shi kuma Ya Tariq yai gidan shi malali.

Muna shiga compound din gidan su Ya Taufiq,yai parking motar shi kamani Fatash tayi muka shiga side din Mum falor muka isketa tareda Aisha.
Oyoyo sukai mana Mum ta taroni muka zauna,sannu yajikin naki ya'ta."

Da sauki Mum."
Ba inda ke maki ciwo ko?"
Eh babu naji sauki.
Allah yakara afuwa, Fatima kamata kuje daki tayi wanka kotaji kwarin jikin ta."
Toh Mum."
Kamani tayi mukayi sama,inajin Ya Taufiq naima Mum sallama shima yai part dinshi.


Ina shiga daki ta kunna heter ban jimaba na shiga birthroom na sakarma kaina ruwa ajiyar zuciya na sauke najima sannan na fito daure da towel a jikina zama nayi bisa stool nafara shafa lotion.

Minal ya kikejin jikin hope kinsamu kwari sosai."
Alhamdulillah ba inda ke mani ciwo gaskia.
Allah yakara afuwa,ya kyauta gaba."
Ameen ya Allah
Miko mani doguwar riga tayi ta atamfa na saka ko turare ban sakaba nahau bisa gado na kwanta nafara jin bacci bansan sanda ya daukeni ba,saida yamma likis na mike karfe biyar na yamma wanke bakina nayi inajin wata irin yunwa har cikina na kuiwa.

Fatash akwai abinci yunwa nikeji."
Aaa ana dai hadawa babu,muje ƙasa in sama maki abinda zaki fara tabawa."

Ban mata musuba nabita gyalen after dress na gyalama kaina,muka shida kasa Mum da Ya Tariq sai Aisha sunata fira gaidasu nayi sukai mani ya jiki,da sauki nace masu.

Itako Fatash shiga tayi kitchen ta dawo mani da cake sai coffee a cup ansa nayi nafara sha kadan kadan.

Aminatu kada ki cika cikin ki akwai dinner kibari kici abu mai dan nauyi nauyi kinji ya'ta."
Toh Mum.

Ina cikin shan tea din naji Aisha tace.
Yaya kayi kyau kamar wani ango."

Dago kaina nayi naga Ya Taufiq sanye cikin light brown din yardi yana murmushi.
"Ko auta kiyima yayan ki addu'a kinji komi lokacine."
Allah yasa ka auri Anty Minal
nidai ina sonta."
tayi maganar sai jin dadi takeyi.

Nidai kaina kasa saidai Murmushi danayi.
Ameen autas Allah yaraya mana ke."
Ameen duk suka amsa shiko Ya Taufiq sai jin dadi yake zama yayi akahau fira baki dayan mu,saidai duk na takura har aka kira sallar magrib sukayi masallaci mu kuma mukayi daki mukayi sallah.

Muna gamawa muka sauko kasa nida Fatima direct dining muka wuce Mum da auta sai ya Taufiq da Ya Tariq kowa ya zauna muma zaman mukayi pride rice sai tuwon shinkafa da miyar kubewa taji kifi,tuwo nace inaso Mum ta zuba mani nafaraci ahankali ji nike kamar kowa ni yake kallo,sallama Abba yayi muka amsa mashi shima zama yayi center chair hakanan sai naji duk wani nauyi da kunya yaka mani sannu da fitowa Abba."
Duk sukai mashi
yawwa yace dasu shima tuwo aka samashi.

Ya'ta ya karfin jikin naki.?"
Da sauki.
Kin tabbata ba inda ke maki ciwo kifada mani kinji daka ki boye mani komai ya'ta."

Bakomai Abba na warke."
Allah yakara afuwa,kici abinci sosai kada ki zauna da yunwa bakyau marar lafiya na wasa da abinci."

Insha Allah."
Ciganba da cin abinci mukayi ba mai magana a cikin mu,saidai a takure nike tsikarar abincin dana dago kaina sai inga idanun Ya Taufiq akaina saifaman satar kallona yake tare muka sakarma juna murmushi.

Major ya aikin naka on tuesday akwai meeting ko.?"
Yes sir."
I have been there insha Allah kila mu wuce tare ko.?"
Insha Allah."
Fatima wazai maidaku school.?"
Inji Abba
Usama zai maidamu."

Aaa kisa Nuhu yakaiku zamuyi tafiya da Usama ,amman nayi tunanin sai jibi zaku koma."
Cewar Ya Taufiq.
Aaa akwai abubuwan da zamuyi.
Cewar Fatash

Nidai bance komai ba sai faman juya abinci nike duk na gaza sakewa inci abinci gashi kuma ina so inci.
"By 12 kazama ready saimu wuce insha Allah."
Allah yasa."
Mikewa Abba yayi yace.
Ya'ta kisaki jikin ki nanfa gidan kune kidaina jin kunya kinji."
Toh Abba nagode Allah yakara girma.
Ameen."


Fita yayi Mum tabishi shima Ya Tariq falor ya koma harya gama cin abincin shi,dagani sai Fatash sai kuma Ya Taufiq.
"Gimbiyata ki saki jikin kici abinci pls kunyar Mum kikeji ko Abba ko kuwa Ya Tariq.?"

Murmushi nayi nace.
"Kasa mani ido taya zanci abinci."
Dariya yayi mai sauti yace.
Sorry prince nadaina sa maki ido bari inkoma wajen dan uwana aci abinci lafiya tawan."

Tafiya yayi falor sai lokacin nafara cin tuwona bilhakki da gaskia harna koshi,ina gamawa mukayi masu sallama zamu koma bedroom dinmu.

Mrs Taufiq har zaku wuce ba fira."
Cewar Ya Tariq
Nagajine yaya zan kwanta."
Yaka mata saida safe.
Allah yakaimu."


Wani kallo na watsawa Ya Taufiq ya saki baki yana mamakina yasan ba baccin da zanyi.
"Haba Ya Tariq biyeta zakai kenan yanzun za'ayi isha'i fa shine zatace bacci takeji."
Yai maganar duk ya damu.

Calm down Hussein kasan patient ce pls tana bukatar hutu."

"Alrighit Allah yakaimu.
Juyawa mukayi zamu tafi na fakaici idon su naima Ya Taufiq gwalo nahaye sama ina dariya,kwafa yayi yana nuna kanshi ɗaga kaina nayi nace eh da haka na fada daki abuna inajin dadi.

Saida muka taba fira da Fatash harta bani waya muka gaisa da Bash yai mani ya karfin jiki sannan nayi addu'ar bacci,da wuri na kwanta,wannan kenan.




_Yar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Pls
❣️



*BAKIN JININA YAJAMAN😭*


*NA*

_Yar Mutan Kankia❣️_

*_TRUE LIFE STORY!_*

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

_*DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI.*_


S2/E45&46


Washe gari da safe ina tashi wanka kawai nayi ina son in koma makaranta akwai abunda zanyi kafin monday mu shiga asibiti zamuyi theater Dr Tahir.


Mum ce ta sauko cikin kayan alfarma fuskarta cikeda annuri gaisheta mukayi tace,zataje gidan yinin biki bazata jimaba.

Sai kindawo mukace,nida Fatash muka rakasu a mota da kanta ta tuka ita da autarta suka tafi.
Muna dawowa mukaita fira da Husna a waya sai dariya muke mata wai ita amarya muna zolayar ta.
Ya Taufiq ne yashigo misalin karfe hudu da kwata lokacin rana tafara karyewa yau cikin kananan kaya yake saidai riga da wando duk iri daya ne.


Zama yayi tunda muka gaisa bai kuma cewa komai ba,kamar ma bai kusa damu haka ya koma,araina ko nace yan miskilancin sun motsa.


Yaya muje garden pls inasan mike kafata."
Cewar Fatash dake rokon sa kamar zai kaita wani shopping basarwa yayi yana chat abun shi.

Minal tashi muje."
Ba inda zataje,ke kije mana."
"Pls Ya Taufiq kabari mutafi mana."
Alright kuje.

Kaifa bazakaje ba."na samu kaina da tambayar shi ba zata.
Muje saiku bani jisting."
Murmushi nayi muka tafi har garden dinsu mai yalwa da kyau,ga kayan marmari su mango,guiva,cashew,Banana,pawpaw sai iccen dabino da abun daba arasaba,daga can gefe kuma swimfool ne gwanin birgewa zama mukayi nida Fatima ke labari wani yajimu yabamu amsa a takaice wani kuma baijin mu da alama yana abu mai mahimmanci a wayar.

waya aka kirata,ina kallan tana satar kallan Yayan nata ganin bai kallan ta,ta daga mani hannu, tayi cikin Apartment dinsu.

Nima latsa wayata nafara wajen 15mint yace.
"Fatima dauko mani juice cikin gida."
Shiru yaji hakan yasa ya dago,badake nike ba.."
Bata nan ta shiga gida nace,bari in kawo maka."

Aaaa Minal zauna bani labari."
Dan shiru nayi,sai kuma nafara bashi labarin yanda zamu tsara bikin Asma'u,murmushi kawai yake yana sai kuma me zakuyi?
Niko sai lissafi nike yana cewa ba kyau bidi'a muyi walima kadai zaifi.
A raina ina cewa kamar bikin Husna ai infara rawa sai nasha magani kila.


Kice zakisha horo kenan."
Dariya nayi ina rufe fuskata ganin yajini.
Waike sarkin kunya ko Minal,ina sonki tawan i love u with all my heart."


Wani irin uban salati mukaji anyi mai razanarwa baki dayan mu,muka waiga dan naji tsoro,Mami muka gani ta daura hannuwa bisa kai tana ihu.

Taufiq mizan gani a ido na soyayya har cikin gidan nan bayan uban ka ya haramta maka auren yarinyar nan wato har yanzun baka fita harkar Amina ba ko.?"
Dafe kanshi yayi yanda take magana kamar zata fasa wajen da tsananin karfi,daga karshe saiya toshe kunnen shi.

Wato ga mahaukaciya kasamu shine zaka toshe mani kunne?kaida uban naka wlh baka ba Amina saidai in mutuwa nayi,yanda Samir yarasa kaima ka rasa."

Enough Mami is over nagaji da bala'in nan naki miyasa kikeson saman ciwon kai,kuma Amina in dai ban aure taba Allah ne bai nufaba,kuma nafada nakara fada Amina nike so."

Jar uba,Hussein ni kake kara maimaitawa wannan kalmar bari kagani yau zakasha mamaki,ke kuma kika tsareni da mugayen idanun ki kamar na mujiya mayya kwalelen ki baki ba Hussein.!"

Waya ta dauko tayi kira ba a ɗaga ba,tafiya tayi sai sababi takeyi tana tsine mani albarka.
A dimauce nace.
Ya Taufiq nabani wlh guduwa zanyi mi Abba zaice nashiga ukkuna.
Kwalla nafara,ina neman guduwa,ji nayi ya riko hannu ya dawo dani,ranshi yagama baci idanun shi sun kada jajir,dagacan muka hango Mami tagama zigo Abba shima kuwa ranshi a bace.
Da sauri na kwace hannuna ina jin kaina kamar zaibar jikina.


Abba na isowa ya daga hannu zai shararama Ya Taufiq mari sai kuma yafasa yace.
"Kai har kayi girman da zan saka doka ka take Taufiq?harkayi kwarin da zakayi soyayya da abinda na hanaka a gidana waye kai mikake takama dashi!?"


"Alhaji abin takaici har ikirari yake waishi yana
sonta kuma saiya aureta."
Aiko da natsine mashi albarka wlh bazaka aureta ba,tunda abin nashi iskanci ne nidakai muzuba mugani.!"
Jikin Ya Taufiq na rawa yace.
"Abba kasan mi kake fadi baki fa kake kokarin yi mani."
Kwarai kuwa tinda baka da anfani muddin zaka dinga jayayya da umurnina."


Jin saukar leda mukayi ƙasa Mum ce jikin ta sai rawa yake tana salati.
Harta iso wajen mu.
Alhaji ɗanka zakaima baki,akan wannan lamarin inalillahi wa'inna ilahirraji'un,nashiga ukku ni Maryama."

Kaɗan kika gani ki gargadi ɗanki akan maganar auren Amina wlh bazai aure taba,matsawar nine uban shi.!"
Wasu kwalla Ya Taufiq ke fitarwa domin idanin shi sun koma kamar garwa shi.

"Abba dan Allah kasamani albarka a lamarin nan kaimani lamani banjin zan iya auren wata inba Amina ba narokeka.!"
"Shut up Hussein zan saba maka,kaida ita har abada,ke kuma kijini daga yau kar inkara ganin keyarki gidana bake ba Taufiq."

Mum na kuka tace.
Alhaji kaji tsoron Allah yar kanina cefa akan mi zaka raba zumuncin dake tsakanin su,dan kawai kakasa gane hanya mai kyau nasan koma minene bayin kanka bane wlh akwai lokaci."

Wani wawan mari Abba ya akama Mum saida ta saki kara,da sauri Ya Taufiq ya tarato jikin shi,cikin tashin hankali.
Nuna Mum da yatsa yayi yana warner ta yace.
"Wlh kikara saka bakin ki aharkar nan bakin aurenki alqawali.!"


Ke kuma hada kayan ki kibar mani gidana bake ba ɗana,yanda Samir ya rasa wlh shima bazai aureki ba,ya zama darasi a gare shi."
Kukan da nike yaci karfina tafiya nike har ina ganin juwa kaina na sarawa ina hango ta yanda zan rayuwa batareda Ya Taufiq ba,miyasa nabari son shi yai tasiri a zuciya ta,inalillahi wa'inna ilahirraji'un,tawa tasameni wace irin Qaddara ce ke tunkaroni batareda na shiryaba.!"

Tafiya nike bansan minake yiba,saidai naganni cikin side din Mum jikkata kawai naja na fito,inda nabar su Ya Taufiq sai Fatash dake kuka ko motsi sun kasa saima,alwashi da Mami keyi tana taya Abba ruwan bala'i kana ganin shi tabbas kasan bai cikin hayyacin shi yanda yake gitta rai akan abinda Allah kadai yasan yanda al'amarin yake.

Hanyar gate na nufa ina kuka,Ya Taufiq ne yayo wajena da zummar tsaidani.
"Kada ka kuskara ka isa wajen ta Taufiq nagaya maka.!"
Inji Abba tsaye yayi muna kallan kallo kauda kaina nayi na fita,tafiya mai nisan gaske nayi,saiga Usama zai dawo gida ban lura dashi ba,ya tsaya yana tambayata ko lafiya.
"Kaini makaranta Usama.!"
Ina Fatimar take,mike faruwa Aminatu?"

"Bakomai Emergency ne ya taso mani yanzun nan ina sauri.
Muje yace dani.
Ina ganin ya daga waya bansan waya kiraba naji yace.
Ok Sir."


Da haka muka tafi Zaria,ina zargin kaina da kaina anya wannan kiyayyar ta lafiya ce?anya ba *Bakin Jinina Yajaman ba?* miyasa mutane keman haka?,Abba dake girmamani yadawo wani iri kamar bashi ba,mike faruwa dani!miyasa Abba zai dage sai yarabamu bayan munsaba da juna bayan shidin shine farin cikina,kuma shine hasken rayuwata,inalillahi wannan itace *Qaddarata* lallai kam bako shakka haka Allah yaso,kuma komai Lokacine! fatana Allah yasa kada Baba yaji abinda yafaru nasan idan yaji tabbas lamarin zaifi ta'azzara daman da kyal yabari aka wuce dani Kaduna daban lafiya inko yaji tabbas zai kara nisantani da Ya Taufiq.

Tafiya muke gani nike bamu sauri ko alama,munkai awa daya da kusan rabi sai naga kamar munkai awa ukku,har muka iso ya saukeni sallama nai mashi na shige ciki jikina a matukar mace.


****Washe gari Fatash tadawo itama kana ganin ta kasan tana cikin damuwa mai tarin yawa,ko maganar kwarai ta gaza kadan kadan tayi tagumi kamar wadda akace tarasa iyayen ta,ganin damuwarta nasan zarce tawa na tattaro jarumtata,wani irin tausan ta naji nace.

Fatima kiyi hakuri nasan nidin Qaddarar kuce nashigo rayuwar ku natar watsa maku duk wani farin cikin ku,dan Allah kuyafe mani."
Ajiyar zuciya ta shide tace.
Tabbas Amina ke Qaddarar muce amman ta Ya Taufiq! ɗan uwana nason ki,saidai Qaddara itace zata rabaku,kiyima Abba uzuri wlh ko shakka banayi bai cikin hayyacin shi,nasan hakanan bazai iya wulakanta kiba Amina.!"

Hakane ni ban kullaci shi da komai ba,natsorata kinji abinda yake ikirari akan Ya Taufiq baki zai masafa! Kuma akaina haba Fatash yazama dole mu hakura da junan mu.!"

Kuka ya kamani nafara shi inajin raina na suya,kuka nike sosai batai yunkurin hanani ba saida nayi mai isata sannan na goge kwallana,kowa yai shiru sai can tace.
"Kunemi zabin Allah shine zabi Amina,Allah yakawo mana mafitar wannan al'amari,dan Allah kidaina damuwa Minal."
Shikenan Allah yasa mudace."da ameen ta amsa.


********Caranci.

Tunda Anty ta karbi kudin Mama akaima Umaima aure harta haihu biyu ba alamun zancen kudin idan Mama ta gwada yimata magana saitaita bala'i tana ai bashi hanjine Allah yabata ikon biya,dan dole Mama tasama sarautar Allah ido.

Bayan kwana biyu a wajen Umaima ba dadi zama itada miji ga jinjirin ciki ga bala'i nayau daban na gobe daban, har yaji saida tayi,haka sukaita nuƙu nuƙu basu san kowa yasani,suke kidin su suna rawar su haka ta koma.

Zama yai zama ba dadi lamarin dan dole ta dawo gida harda takardar saki daya,ga kwaiwai tana fama dashi(Laulayi).
Haka Anty tazo gida tana kuka tana komai tagayama Mama halin da ake ciki amman batai mata korafi ba,haka taje gidan iyayen mijin Umaima aka sasanta da kyal,harda korafi wai ɗansu yagaji da halin uwar yarinya tana shiga sabgogin gidan su.


Saida Mama taita basu hakuri sannan suka amince aka maido Umaima dakin ta.
Zama yai zama daga baya suka samu kan mijin sai sukace daman ai harda sa hannu kuma wa'anda sukasa hannun har auren yaki dadi,sunje sun sasanta gashi zama yai armashi saidai dan baki ciki ya mutu.


Haka labarin ya dawoma Mama bataji dadi ba sam.
"Kinga Mubara mubar wannan zancen Allah da zuciya yake amfani ni ba abinda zance Allah dai ya kauda fitina."
Abinda Mama kefada kenan amman kana ganin ta kasan alamarin nasata jin zafi aranta.

Haka rayuwa ta koma lokacin nadawo hutu ina komawa shine Final Year dina dan har Project nafara Ya Tariq yabani Sample din nashi inayi saboda Course dinmu iri dayane kuma akabani Project Topic dinmu sun kama dana juna shiyasa komai yazo mani cikin sauki.
A ranar dazan koma Makaranta Baba ketai mani wa'azi yana mani nasihohi

Amina kada kibiyema soyayya ki guji shiga inda ba'ason ki kada kifada cikin hatsari ki tsaya matsayinki,kada ki shiga inda ba'a bukatar ki,yanzun kinga kin girma Final Year kike zaki iya kula samari amman sai kin duba,kina sara kina kula da bakin gatarin ki Allah yai maki albarka."

Ameen Baba insha Allahu.
Haka naita Parking dina saidai maganganun shi da yaimani yana hakaito mani Ya Taufiq domin shida Mum kadai ke bukatata kodai Baba hannun ka mai sanda yake mani,to ta yaya?bayan baisan ina soyayya da Ya Taufiq ba yasan dai mun hakura da juna tinda mahaifin shi baiso da haka na kauda zancen araina.

Salatin da mukaji an rabkane yasa muka fito waje ba shiri Anty Hafsat keta burgima kasa tana salati tana.
"Na shiga ukkuna ni Hafsatu ansakar mani Yar tawa,Khadija kina ina fito kije ki gayra abinda kika 6ata ansaki Umaima ga tsohon ciki na bani na shiga ukku."

Banda kyarma ba abinda Mama keyi tana salati rungomo yar uwar tata tayi tana bata hakuri duk ta gama kidimewa itama.

Idan na fahimta kamar Mama bata fahimci zancen Anty Hafsat ba sosai tsabar firgita,kamar ya taje ta gyara abinda tabata mi hakan ke nufi?

Da kyal ta kwantar mata da hankali ta maidata gida tana basu baki harda Umaimar.
Sannan ta dawo gida ni kuma naima Husna ban kwana bikin ta saura yan watanni ayi shi,da tuni anyi an daga shi sakamakon ciwon da mahaifin Abdallah din yasha fama dashi kuma shine babba a gidansu kusan dawainiyar gidan nasu tana wuyan shi,shiyasa aka kara bikin sosai.


Itama Husna ga ciwonta daya motsa(Jinni) saida akaita magani an kwashi watanni sannan ta samu lafiya hakan yasa bikin ya dade da sawa.
Na koma makaranta inaci gaba da rayuwata Danko Taufiq nida kaina naja baya dashi gudun abinda zaije ya dawo,wasa wasa samester dinmu tai nisa hakama Project yana tafiya kan tsari.

Haka rayuwa ta kasance har nagama first semester,mun dawo gida dana koma Second Semester daga ita nayi Graduate saidai mufara su Intership da Service.

*Nasan zakuce ina maku sauri akwai gabar da nikeso mukai domin dauko wani sabon topic dan cigaba da labarin yanda ya kamata nagode da addu'oin ku😍*

Bikin Husna ya matso sosai baifi wata biyu ba saina kanwar Umaima shima baifi wata daya da sati biyu,tsayawa gaya maku cikimillan da akaiyi da Anty akan samun mijin Hauwa'u sai kuyi mamaki,har cewa tayi Mama tasa mata hannu dan ya'yan ta nada farin jini batasan ai auren dan taga ni ina da bakin jini,maganganu ba dadin ji da sauraro amman ta kyaleta saidai kudin Mama ta hana tun ina Year one zamuje two akai bikin Umaima gata da ya'ya har ukku,amman ta hana kudi tace inda karfi azo a kwata,ƴan uwansu sunyi magana hatta Dada amman tahana,dole tasa Mama tace a barta kada akara zancen.
Yanzun bikin Jidda ne ya tashi kuma ba kunya tadawo gidan mu tana zuruftu nidai nawa ido.

Haka na koma wata Second Semester na ida project dina har bikin yazo saura sati aiko nace ban zuwa domin saura sati biyu bikin Husna kuma shi zanje wannan kenan.....





_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Pls
❣️



*BAKIN JININA YAJAMAN😭*


*NA*

_Yar Mutan Kankia❣️_

*_TRUE LIFE STORY!_*

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

_*DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI.*_


S2/E47&48




Shirin bikin Husna mukeyi ba kama hannun yaro hatta dunkunan da zamu saka nida Fatash mun dinka abun mu,yau zamu tafi Caranci Usama yazo daukar mu,har gida yakaimu.

Muna isa mukahau shirin biki tun daga kudin Setting da abincin da za'aci duk mun hada komai anraba aikin abinci.
Amarya kuwa bakaramin kyau tayi ba,sai gyara ake mata gidan mu tadawo Mama tadage da yimata gyara,mai dilka aka dauko ta musamman tahau gyaran Husna.
Itako Mama bata kano bata Caranci yau sukaje jere duk wasu kayan Husna Mama ta tarasu wasu ita tasiya wasu kuwa Mamar su Husna dayake komai biyu suke siya mana suna ajewa(tanadi) kafin lokacin bikin mu yayi,gashi Allah yakawoma Asma'u nata lokacin.


Washe gari mukaje akai mana hanna bakaramin kyau yai mana ba,dayake inada yalwar gashi sai wash and set kawai nayi na daure shi.
Itako Husna iya gyaruwa tasha harta gaji da gyaruwa jikin ta har glowing yakeyi.

Ya Taufiq kuwa har gudumuwa yaba kawar tawa,kusan kullin muna waya saida ba kamar daba nadanja jikina dashi gudun abin daka iya zuwa ya dawo.
Ina zauna falo nida Husna sai Fatash,Anty Hafsat ta shigo gaidata mukayi.
"Ina Mamar ki."
Ta tambaya,bata nan mukace.


"Wato ke Amina dan rainin hankali da tsabar bakin ciki,ayi bikin Jidda bakizo ba sai bikin kawa ko?tsabar kedin kin kware a hassada,to ta Allah bataki ba kuma aure anyi angama tana dakin miji,keko kina zaune tsabar bakin jini,ina amfanin mugun hali.!"
Kallan juna mukayi nida Fatash saina samu kaina da rashin jin dadi ganin gaban Fatima take kananun maganganu.
"Kiyi hakuri Anty zanje gidan ta."
"Aaa bamu bukata kawai kije ki kashe mata aure,tasamu ta shiga daga ciki so kike tadawo tazama ke,aaa shazaman kashe wandan ki yan matan Jami'a."

Uhmmm kawai nace,wayata tahau ruri na daga Ya Taufiq ne,daki nashiga ina jinta tana zagina wai inyisu gani in tusa na hura wuta.
Ina dagawa na gaidashi.
Baby,mikikeyi

Please Login or Register in order to submit comment