Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ma rahamane a rayuwa,haka aka gama Lecture daman ranar daya zamuyi,ana gama nakama hanyar hostel.



Kasa nike tafiya dayake Makarantar batai cikar nan ba sosai,ba mutane da yawa,ina cikin tafiya naga ansha gabana da mota,kaucewa nayi naga anfito cikin motar ankara shan gabana wasu samari ne guda biyu suka sakani tsakiya wai lallai in shiga cikin mota ko su kasheni nikam naki shiga gani nayi an zuge glass din motar JJ ne zaune cikin suite yafitoni yayi da hannu alamun inje naki zuwa,wani ya daka mani tsawa har saida cikina ya kada, dan dole naje natsaya bakin motar.


"Shigo."
Yace cikeda gadara nikam naki shiga kallona kawai yake yace.
"Bakya daukar wayana miyasa.?"
Ban ra'ayin magana dakai shiyasa."
Nace batareda nuna tsoro ba."
Okay ki dinga daukar wayana kinajina inba haka zakiyi nadama duk wani mostinki a tafin hannuna yake koda kina gida na kyalekine dan ki huta,bacin haka dana nagama cika burikana akanki kinajina.?"
Shiru nayi,badake nikeba."
Naji, "zaki iya tafiya."


Haka natafi raina na mani zafi da kuna harna isa daki ina nanata maganar shi wai indauki wayar shi,a zahiri nace sai kace Yusuf Caranci bazan dagaba kayi duk abinda zakayi dan iska.



*******Haka rayuwa ta kasance mani a Jami'a duk barazanar duniya JJ yaimani nikam naki yarda kuma ban nuna tsoron sa a gaban idon sa dakewa nikeyi duk da kuwa inajin tsoron.


Akwai wata rana shike garemu,kuma naje class dinshi yana mana Lecture a first sit nike zaune yanzun nadaina takura kaina in koma baya mazewa nike,kuma in muka hada ido yanda yaiman kur da ido nima bana janye nawa saidai shi zai janye yaci gaba da Lecture dinshi amman ina neman tsarin Allah da kaidin shi,ana cikin Lecture ya tadani tsaye,mikewa nayi yafara antayo mani Questions kamar yanda yaimani a farko wasu inbashi amsa wasu ince ban sani ba,ai tunda nace bansani ba yafara bala'i.

"U re very stupid daman kwanyar ki Empty take ashe?this is simple Questions amman kince baki sani ba,muddin baki bani wannan amsar ba i will give u a suprise.!"


Wani kallan tara saura kwata nai mashi nace,I say i dont know,ka koya mana sai insan shi mana."


"Ke are u mad kinsan abinda kike fada kuwa an kawoni dan in maku Lecturing ko kuwa ance maki ni am ur teacher? I come to guide u, bawai na koya maku ba,kin baro koyawa tun a secondary school dan haka give me a answer."

Sai dumi yafara tashi kasa kasa kowa yana fadin abinda yazo ranshi.
"Keep Quit.!"
Yace a fusace
Tsit akayi yace.
"Am wating for u."
Sir i dont know i swear."
Kuma nasani saida na samu banzan Question nace bansani ba,kuma shima din yasan karya nike wani mugun kallo ya aikaman sannan yace.


"Good zakisan ni bana wasa -30 in ur scores promise."
Baki daya aka hau salati nan fa akafara Caranci kibashi amsar nan 30marks ba wasa bace Amina."
Kowa da abinda yake cewa ni kaina gabana ya yanke ya fadi amman na dake nace sam ban sani ba."


Haka na zauna jikina sanyaye kallan kallo mukema juna ya watso mani killer smile dinshi ni kuma na watsa mashi kallan banza yana mani kallan biri ina mashi kallan ayaba harya gama yafita.


Kamar jira wasuma bansan sun san sunana ba,akazo haba Amina taya kinsan abu zakiki fada 30 marks fa kikai losing kije ki bashi hakuri ni wlh muje inrakaki muna neman Mark din da tsada zaki tsaya kina wasa dashi bakida hankali gaskia.


Canfa naji wasu nacewa hakanan suke zargina akwai alaka tsakanina da Dr JJ da akwai bazai tsaneni har haka ba.


Hakanan nasamu jin dadi araina nace kwara da akai haka kenan yanszun Course Mate dina zasu fara trusting dina alhmdullh.
Azahiri na kalli Maimuna wadda tace zata rakani nace.
"Shikenan muje sai in bashi hakuri nagode da kaunarki agareni."
Ameen tace.
Mikewa mukayi Maryam tace.


"Hehhhe waimu za'aima bariki ,dan ku goge mana hadda ashema tsana wannan wani logic ne sukai using dan su samu aduhu mudaina zargin akwai alaka a tsakanin su daga baya su zagaye suna cutarmu kuma yana dura mata uban Marks.

Nan fa wasu suka hayayyako ma Maryam suna cewa
Miye haka Maryam wai miyasa kin tsani Caranci ne ,haba shifa zato zunubine inda zai bata Marks tun a result din last semester zamu gani amman kina gani C ta wuce Course dinshi C dinma 50 da kyal tasha kidaina haka wannan fa ba rayuwa bace."


Cewar Yunus duk da tana kawar shi.
Nanfa wasu na goya mata baya wasu kuma na kareni,raina ya baci idanuna sun sauya bansan sadda nazo gaban taba nace.

"Kiji tsoron Allah Maryam kinata yiman wulakanci da gaya mani mugayen maganganu son ranka,kina yawan tozartani a class dayawa Course Mate dina sun tsaneni saboda zakin bakin ki wajen aibatani,miye laifina da zaku tsaneni wane irin bakin jinine dani dahar kowa ya tsaneni har haka minayi maki Maryam? shin duk wannan tsanar da kukai mani Bakin Jinina Yajaman kenan?shikenan nagode amman dan Allah kirabu dani haka na aibatu kibarni inji da abunda ke damuna mana ki rabu dani saidai kisani nabarki da wanda mahudar rana da faduwar ta take hannun shi Maryam keda da duk magoya bayanki.!"


Ina gama fadar haka naja hannun Maimuna ina kwalla muka fita,zuwa wajen shi bansan yanda suka karataba saidai inajiyo hayaniyar su.


Muna zuwa gaban office dinshi naji gabana ya fadi wanda na rasa dalili duk da inada hope ganin bani kadai zan shigaba knocking mukayi shiru,na kalli Maimuna nace.
"Inaga bai nan yazanyi.?"
Kikira shi mana.!"
Shiru nayi wata zuciyar tace muddin kika nuna kinada number shi tabbas zargin da ake maki gaskiane kenan.
"Banda numbar shi."
Okay bari inbaki saiki kira shi."
Fiddo wayarta tayi ta fiddo numbar shi Doctor Junaid tasa.
Aaa Maimuna ki kirashi da wayarki banda credit a tawa wayar."

Okay shikenan."
Dailing tayi akuwa tashiga saidai tayi 2miscall ana ukku ya daga da sauri ta daura mani a kunnena jikin ta nabari nima din samun kaina nayi da tsorata.


Wake magana.!"
"Amina Caranci."
Na bashi amsa
Wow Beauty how are u?"
Ban amsa ba nace
Sir ina bakin office dinka baka nan."
No ina ciki coming in."
Okay.
Na mika mata wayar yana ciki mu shiga."
A sanyaye na kama handle din nashiga ciki dayake nike gaba sai zabga murmushi yake mai ma'anoni ganin Maimuna bayana yasa shi tsuke fuska kamar mai aljanu,nima kama kaina nayi na fuske,sallama ciki ciki ya amsa mukayi tsaye kuma baice mu zauna ba yace.
"Lafiya.?"
Dan satar kallan Maimuna nayi tana mani nuni da inyi magana nace."
I apologise to u sir pls forgive me.!"
Da akai mifa?"
"Ƙin baka amsa danayi wlh bansani ba dan Allah kada ka taba mani Marks dina na rokeka."

Sai lokacin yayi smile yace.
"Banda wannan lokacin daman kinsan akan shine zakizo mani office.?"
Sorry sir kaimata hakuri dan Allah bazata kumaba."
"Kazaure ki rabu da ita tana bukatar warning."
Nan fa Maimuna ta zaƙe sai bashi hakuri take nikam saidai kallan da muke jefama juna na ki/ka san sauran maganar shi ta katse mani tunanina.


"Kazaure naji zan yafe mata amman sai zuwa gobe tazo ta sameni na duba inga yuyuwar hakan.?"
Thank you sir."
Cewar Maimuna,juyawa mukayi zamu fita tace ke baki masa godiya,tasa kai tafita.
Juyowa nayi nace Thank you sir."
Jinjina yai mani ba babban hannun sa da haka mukaci gaba da daukar Lectures har muka tashi 6pm nanfa yan Course dinmu suka nemeni yafiya ta banda Maryam dako ajikin ta.

Washe gari kuwa kamar yanda yace zai yafe mani haka Maimuna da Humaira suka takura mani har bakin Department suka rokoni saida sukaga nashiga ciki sannan suka koma inda muke daukar Lecture.
Knocking ynayi kamar mai duba naji yace.
Caranci come in."
Jikina a mace na shiga saidai na danne mamakina.
"U re wellcome my world."
Tsuke fuska nayi nace.
"Nadawo kace zaka yafe mani."
Have a sit beauty."
Zama nayi yana murmushi yace.
"U think nai maki mainus ne dan wani abu,wannan wani sabon salon ne domin na fahimci Students dina sun fara gano akwai wata a kasa, shiyasa naga sunfara samana ido na bullo ta wannan hanyar dan in wargaza masu dan karamin tunanin su,kuma nasan definitely za'a samu wadda zata rokoki danki bani hakuri, saiga shi kuwa tun tafiyar batai nisaba sun fada tarkona ya kikaga wannan tsarin nawa Beauty.?"
Killer smile ya kuma saki mai kashe mani duk wani hope.


Daurewa nayi na tattaro jarumtata nace.
"Nice idea Dr JJ kamar kasan nima zuwan da nayi da Maimuna kenan nabi ra'ayinta dan in dakile tunanin su akaina,kai kana zatan zan biyo 30marks ne in saida maka Pride dina?bari kaji koda 100marks dina ka amshe banjin komai domin kuwa kimata da darajata ta fiyemani komai JJ."


Keep Quite are u in ur sense? Ko kin haukace ni zakina gayama wannan zancen? Ina wasa dake.!?"
Ai kwara wasa kila nafi ganin kimarka akan wannan salon wasan dan haka kajini da kyau JJ ba barazanar da zatayi tasiri agareni kwarama ka aje wannan kudirin naka tunkan dare yai maki ni Caranci nafi karfin wulakanci.!"
A fusace yayo kaina zai mareni sai kuma ya fasa yace.



"Duk iskancina ban bugun mace bare in mari wannan kyakkyawar fuskar mai sakamani nutsuwa saidai kisani duk wayon amarya sai andandani zumar ta Amina."
Shikenan muzuba mugani wakeda nasara nida kai JJ."
Well zaki iya fitar mani office."
Yanzun kuwa."
Natafi harna rike handle yace.
"In lessthan two weeks nagama aikata komai agareki kijira lokaci."
Gabana ya fadi na boye hakan a fuskata nace Allah yakaimu."


Na rufe office din harda buga kofar nayi, Nan Dr Salim zai shiga office din saida yabini da ido,ko kallan kwarai ban mashi ba natafi,saidai ina tsoron al'amarin JJ kuma nasan indan ina nuna mashi tsoro hakan zaisa yai saurin nasara akaina wannan kenan......




_Yar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Pls
❣️


*BAKIN JININA YAJAMAN😭*


*NA*

_Yar Mutan Kankia❣️_

*_TRUE LIFE STORY!_*

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

_*DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI.*_


S2/E19&20

*Bonos Page💕*

_Goron Juma'a ga dukkan Masoyana Allah yabar kauna._
*AMINA CARANCI na miko dimbin godiya*



*Caranci""""""*



Tunda Dada taima Anty Hafsat fada saita sauya salon takonta duk abinda zatayi sai tazo har gida tayi shawara da Mama,tun daga kayan kitchen haka take zuwa taji mi za'asiya kusan kullin tana gidan mu su kashe su rufe da mama.


Akwai wata rana ne tazo gidan mu,ayam ta iske Mama dakin ta,zaunawa sukayi suna fira rabi da kwata duk akan yanda za'ayi bikin Umaima ne.

Kwatsam saiga Zulai mai adashe ta shigo hannun ta dauke da kudi wuri na gugar wuri har dubu dari biyu(#200),tazo kawoma Mama zubinta dayake tinda aka samani rana Mama ta shiga adashe dan yimin siyayyar da uwa kema yarta koda aka fasa bata daina ba,acewar ta tanaji maganin tashi nakama ka.
Koda Zulai tashigo ganin Anty bai hanata ba fiddo kudin ba aganin ta ai yayar Mama ce.
Mikoma Mama kudin tayi tace.
"Khadija ga kwasarki nan ki lissafi kiga in sun cika."
Murmushi Mama tayi tace.
"Haba Zulai ai nasan bazaki bani kudi da gintsirmi ba."


Aaa aaa aisu kudi yan lissafine inke baki iya lissafawa nibani in ɗirgesu tas.
Tunkan Mama tayi magana Anty ta anshesu tafara lissafawa da karfi har takai karshe.


Jinjina kai tayi tace.
"Angaisheki Khadijatul Kubra,wuri na gugar wuri na dubu 200 gaskia kinyi kokari Allah yasa albarka."
Ameen,cewar Mama.


mikamata kudin tayi Mama taba Zulai ladar adashe tace bazata karba ba,ita haka take adashen ta,dan dole Mama ta hakura ta aje kudin.


Godiya taima Zulai ta tafi ai kamar jira Anty take gyara zama tayi tariko hannun Mama tace.
"Allah nagode maka daka rufama yar uwata asiri nasan nawa asirin ne ya rufu Khadija,yanda Allah yatai makeki ki taimaka mani dan Allah kibani aran kudin nan kinga yau saura wata ɗaya bikin Umaima kuma duk abinda uwa kema yarta ko taro ban ajeba ki aromani su insai kayan kitchen dan Allah Khadija."


Tayi maganar cikin karayar zuciya ta wani marairace abar tausayi.
"Anty kinga kudin nan shigowar su kenan,kibari ko Baban su Amina ne idan yazo ya gani sai insan abinda zanbaki a ciki."


Haba Khadija idan baki rufamani asiriba wazai mani duk duniyar nan,yanzun ina kike tunanin zan samu kudin da zamma yar taki kaya?ko sokike azageni ace ban mata komai,koda yake kudai za'a zaga badai niba."
Kamar zatayi kuka tayi maganar.

Mama zatayi magana kenan kanin su Kawu Ali ya shigo shima zama yayi suka gaisa maimakon Anty Hafsat ta amsa saita fara kalar kuka tana.
"Aliyu katayani rokon alfarma Khadija ta aro mani kudin nan ayima Umaima kayan kitchen kada asirina ya tonu dan Allah."


"Keko Anty taya daga ganin kudi zakice ta baki,baki ganin ko akwai abinda zatayi dasu."
Dakata Ali indai kasan bazaka taimaka mani ba kai shiru da bakin ka ai ance ciwon ya'mace na mace ne."


"Shikenan bansan harkar kudi su,shiga tsakanin ku har zumincin ku yasamu rauni,amman ke Anty Khadija saiki bata in kinada halin hakan."
Karaf tace
Tanama da hali ana gama biki idan nasamu kudi zan bata."


"Aaa Anty Hafsat ai zakima samu bikifa kawai dai ana gama biki ki lissafa kudin ta kibata kawai fakat."

To Dan iya naji,kinji Khadija ana gamawa zan dawo maki da kudin ki."
"Shikenan Anty zan baki Dubu dari da Hamsin cikin kudin."

Aaa gaskia kibani duka domin nasan duk wani kayan kitchen zasu isa inyi mata sai inji da kayan kore kuma kinga nan ma aijidali ne."
Aaa Anty kibarta tabaki yanda tace dagani tanada tata bukatar."

Eh Ali inada ita daso nayi ranar asabar din nan inje kano insiyoma Amina kayan kitchen in aje mata har lokacin da zatayi aure ba gara ba zago kaji planing dina."

Anty ce tace.
"Keko Khadija inake ina wannan dogon burin yarinyar dako saurayi bata dashi amman harkin fara wannan dogon burin.?"

"Anty kenan da abin dariya kike naga auren nan lokacine kuma ai ita ajiya maganin wata rana ce."
Cewar Mama

"Hakane kibari ta baki abinda tai niya Anty."
Aliyu in baka iya fadin alkhairi ka kakkabe rigarka ka kara gaba nidai kibani kudin nan Khadija nan da wata ɗaya ana gama biki nadawo maki dasu saikiyi abinda kike bukata dasu."


Nauyayyar ajiyar zuciya Mama ta shide ta mikama kawu Ali ya lissafa ya mikama Mama taba Anty da hannun ta itama ta kara lissafawa da haka tace sun cika Kawu ya zama shaida nan akayi yar fira ta tafi gida wannan kenan.



*****_Amina Pov_


Zuwa yanzun ba kadan na iya takuna ba shi kanshi Dr JJ idan agaban Mutane ne sai ya wulakantani amman kuma bai fasa yimani barazana ba musamman ta waya ko text messages saidai bantaba mashi replay ba nakan karanta.


Yau bamu dashi muna zaune Class ana mana Lecture Dr Salim yake gaya mana sumptoms na Tuberclusis,sosai muke ganewa saidai akwai inda yaimana karen tsaye muka gaza ganewa amman Yunus ya gane sai suka koma daga shi sai Dr suke Class din ana tashi kowa yace ba inda Yunus zaije sai yayi mana turtorial nan fa akahau akafara yai mana daldala sosai muke ganewa harya gama.


Yana gamawa,su Humaira da Surajo suke inmasu turturial din Course din Dr JJ,da nace banyi suka matsa mani duk da bansaba magana gaban maza ba amman haka nai masu nagama kowa ya fahimta sosai.
Bamu,mukabar Class dinba sai 4pm,muka koma hostel.


Haka muka dingayi da yan Course dinmu duk sanda akayi Lecture ba'a ganeba sai wanda ya iya,yai mana turtorial, a hankali nafara samun kaunar su da kulawa suka daina yimani habaici da kananun maganganu hatta gandilar tasu Maryam itama ta kyaleni,kusan kullin munatare ina mata turtorial itama wanda ban saniba tana koya mani,ba kadan hankalina ya kwantaba karatu nike bil hakki da gaskia.
Haka rayuwa ta kasance a Hostel ma nayi kawaye da Course mate dinmu da wanda ba Course dina ba.

Tsakanina da Ahmad kuwa waya muke sosai wanda zan iya kiranta da soyayya domin ni kaina inna samu lokaci nakan kirashi,Ya Taufiq kuwa ba laifi muna waya dashi saidai duk friday saina mashi happy Juma'at harya saba in bamma shiba yakan kira yace na yada shi,wannan dalilin yasa ban yarda in manta domin bansan jin kalmar na yada shi da yake fadamin.


Bayan sati biyu Anty Aisha matar Ya Tariq ta haihu,kuma twins ta haifa saidai mace da namiji ne,da asuba tun karfe shidda na iske kiran Ya Taufiq har saida na tsorota na dauka wani abun ne ya same shi,binshi nayi zuciya na halbawa yana dagawa yace.

"Haba baby wane irin bacci kike harka.?"
Ayyah Yayana ba bacci nikeba naje study room ne."
" good albishirin ki."
Sai lokacin na sauke ajiyar zuciya nace goro."
Fari ko Ja.?"
Fari kyal mai kyau kamar kyakkyawar fuskar Yayana."
Wani kunya naji domin bansan haka nace ba saida nagama fada,shima shiru yayi na sakkanni yace.
"Woow really.?"
Eh Yayana."
Dagske ni Kyakkyawane?(handsome)?"
Sosaima kuwa Yayana kanada kyau, gaka da kyakkyawar zuciya mai alkhairi wane albishir ne fada mani."
Ajiyar zuciya ya shide yace.
"Mrs Tariq ta haihu yau da asuba ana gayaman nace kawata zan fara sanar mawa."

Murmushi nayi nace alhmdullh Congratulation yayana an girma an zama Daddy."
Uhumm yarinyar nan kinga makwancina da yawa daman can ban girma ba kenan.?"
Dariya nayi naci gaba dacewa.
"Ai da'ace kayi aure sannan zaka girma amman yanzun tunda Ya Tariq ya daga darajar ka zamuna kiran ka Dady amman na wucin gadi har sai kayi naka ya'yan."
Na ida maganar ina dariyata dan banji komai ba.
Minal?"
Naji yakira sunana cikin wani irin yanayi."
Na'am nace still ina smile a fuskata kamar yana kallona."
Cigaba dacewa yayi.
"Ki kasance dani sai in zama cikakkken mutun kuma akirani da Daddy kamar yanda kike mani fata,Matata tana nan a kusa dani, saidai nike jiranta saboda matsayinta ba ita ke jirana ba,kanwata ina kaunarki so na hakika wanda ban tunanin zamma wata makamancin shi baby na."


Murmushi nayi nace.
Gaskia ko wacece wannan tayi dacen samun masoyi kamar Yayana tayi zarra a cikin mata,zanso insan wadda ka zabo yayana wacece ita.?"

Duk da naji haushi ganin ya daina sona,ba kamar yanda Fatash ta gaya mani ba ashe ya zabi wata yanzun."

Idan kece wadda na zabafa zaki zauna dani a matsayin mijin ki?."
Kaina naji ya sara mani na gaza magana.
"Uhmm kikayi shiru."
Yaya eh amman....
Ya isa tawan maida hankalin ki wajen karatu komai lokacine saidai kisani kina raina a kullin gobe zanzo Kaduna zan biyo in daukeku kuje kuga Babies dina ko.?"

Ya Taufiq kadauko mana su a photo mana basai munje ba."
Aaa that's mean bakiji dadin zuwan babies din ba kenan."

Aaa ba haka bane,saidai iyakata gidan Ya Tariq bazanje gun Mum ba."
Saboda me.?"
Saboda Mami kuma Baba bazai bari ba,shiyasa."

Okay nagane bakomai sai nazo."
Allah yakawoka lafiya Yayana."
Ameen Minal bye."
Okay bye."


******Washe gari kuwa muna tashi mukayi wanka muka shirya nida Fatash,saida na kira Mama nagaya mata zamuje gidan Ya Tariq domin ina shakkar tambayar Baba.


Toh nidai bance kijeba duk da naji Babanki na waya da Mum tace zakuje ganin yara keda Fatima amman bansan ya amince ba ko bai amince ba amman ki tambayi shi kiji ta bakin shi.


To Mama bari inji.
Ina kiran Baba lokacin yana wajen aiki yace.
"Har kuntafi Kadunar.?"
A daburce nace Aa Baba daman so nike in tambayi izinin ka."

Dakyau Mamana kije saidai iyakarki gidan Hassan bance kije gidansu Fatima ba kinajina."

Toh Baba insha Alalh."
Ya karatun naki.?"
Ahmdullh.
Masha Allah,Allah yaimaki albarka yabaki sa'a."
Ameen ya rabbi."
Kikula da kanki ina aiki sai anjima.
Insha Allahu,Allah yataimaka Babana."
Ameen ya'ta.
Da haka mukayi sallama da Baba.


Anayin la'asar Ya Taufiq ya iso shida driver dinshi duk da kaki a jikin su,basu jimaba muka fito baya muka shiga nida Fatash sai ya kasance munsa Ya Taufiq a tsakiyar mu,gaida shi mukayi ba yabo ba fallasa ya amsa yana murmushi.


Haka muka dauki hanya muna fita a bakin titi muka iske wasu motocin na sojoji a wajen makaranta sunkai hudu gaba sukayi muna tsakiyar su sai Kd.


Ba'a wani jimaba sai gamu mun iso kaduna within an hour.
Direct gidan Ya Tariq muka nufa a malali,muna zuwa motar mu kadai ta shige cikin katafaren gidan su sauran sukajira a waje.
Bude door Fatash tayi ta fita,nima zanfita wani Soja ya bude mana kofa ina fita shima ya sauko,mukayi cikin gidan.


Wani irin masifaffan falo ya iso wanda yaji royal chairs kirar Turkish,saidai ba kowa a falon ,gaba mukayi wani falon wanda shi kuma yakeda kujeru Ledar chairs,nan kuwa dangin Anty Aisha Manga, muka iske suna firar su,gaisawa mukayi dasu,sannan muka shiga wani corridor sannan muka shiga wani falon mai dauke da kujeru hadaddun gaske nan muka iske Ya Tariq muna shiga ya taso ya rungume Ya Taufiq yana.

"Wellcome back Daddy ur kids missing u."
Missing them more bro,suna ina.?"
Sake rungume juna sukayi kotamu basuyi sai muka bige da kallan su.


Ya Tariq ya shiga wani daki sai gashi bada jimawa ba ya fito dauke da namijin a hannun shi Anty Aisha na binshi da macen da sauri ya karba sai Murmushi yake yace.
"Alhmdullh wellcome to the world Laftanal General Major Sarki Mukhtar Hassan Mukhtar ina alfahari dakai ɗana."
Kafa kunnen shi yayi yai masu addu'oi da alama harda huduba.
Jinayi Ya Tariq yace
Masha Allah,Allah yaraya Major bisa sunna."
Ameen duk mukace.
Miko mani yayi na ansa.
Sake karbar macen yayi yace.
"Uwata takaina Hajia Maryam Adam Caranci u re wellcome in this Special family my daughter, i proud of you."
Itama addu'a yai mata da huduba.
Mikama Fatash namijin nayi na amshi nacen hannun Ya Taufiq nace Allah yaraya mana Aira."

Shima murmushin yayi yace woow nice nick name Aira."
Duka mukayi dariya harda Anty Aisha.
"Hassan ina san magana dakai but nagaji anjima zandawo after isha prayer."
Toh Daddy Allah ya huta gajiya."
Ameen,kallan mu yayi yace.
"Ku zauna nan zaku kwana gobe sai ku koma school kafin suna,indawo sai musan mi za'a shirya na sunan,Mrs Tariq gift dinki dana babies dina nanan anjima zan kawo maku."
To Daddyn Major."
Dariya yayi suka tafi shida Ya Tariq zai mashi rakiya.

Kallan mu Anty Aisha tayi tace.



_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Pls
❣️


*BAKIN JININA YAJAMAN😭*


*NA*

_Yar Mutan Kankia❣️_

*_TRUE LIFE STORY!_*

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

_*DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI.*_


S2/E21&22


Editing❌


"Kai Major badai son ya'ya ba,kullin sai yaji lafiyar mu yaudai gashi Allah ya kawosu duniyar cikin aminci."

Dariya mukayi nace,

Aikuwa Ya Taufiq yana son yara musamman su Amna,mi za'acema Hassan din?"
"Major mana tunda shi ya gaji Abba."
Cewar Fatash.
Aikuwa haka za'ayi Allah yaraya."
Ameen muka amsa baki ɗaya,mai aikinta ce tajere mana abinci a dining daki mukaje mukayi sallah sannan muka fito zuwa dining din,mukayi Lunch.

********A wajen su Mama kuwa sosai Anty Hafsat ke janta jiki,tana mata wani irin mutunci na musamman danko kayan kitchen saida taje da Mama sabon gari suka siyo abunda suke bukata harda zannuwan gado masu kyau american bedsheet saida ta yomata sannan suka dawo gida.

Idan tazo gidan mu har dare take komawa gida kullin planing dinsu yanda zasuyi bikin cikin rufin asirin Allah.

Lallai kam dan uwanka shine mai rufa maka asiri akoda yaushe haka Mama ta hadama Anty gudummuwar da zataba yayar tata,har Baba saida yabada tashi gudunmuwar Mama Dubu hamsin tahada mata da man olgwa da buhun filawa da suger takai mata tace tayima amarya gara kudi kuma takara tayi hidima,Baba kuwa dubu ashirin Yabata.

Mum ma haka ta aikama ta da sakon dubu talatin haka Mama takai mata dubu dari cas daga bangarenta banda kayan gara da takaimata.
Koda yake baka biki da dan uwanka komai zakayi kaima zumunta.

Ba kadan Mama tasaki jiki da Anty suka koma kamar da suka hada kansu kamar da kowa yanata sha'awar su.

Hakama yan dakin su Mama suka hada gudunmuwar su suka kai mata duk da haka saida Mama ta kara bada tata gudunmuwar aka kai mata.
Saijin dadi takeyi ta rungumi yan uwanta sukaita shirin bikin Umaima.

Kowa yana iya kokarin shi ganin sun rufawa yayar su asiri,gudun dariyar mahassada.



*******Daddare kuwa Ya Taufiq ya dawo cikin kananan kaya English Wears sosai suka amshe shi tunda ya shigo idanuna suka kasa daina kallan Ya Taufiq don ba kadan yai mani kyau zan iya cewa baitaba yimani kyau irin nayauba saidai hakan yanada nasaba da farin cikin daya kasance ciki,zan iya cewa haryafi Ya Tariq zumudi dajin dadin haihuwar tunda yazo yakama Hassan ya rungume sai cewa little Major sai tsokanar shi dangin Aisha sukeyi har mamaki sukeyi yanda yake Smile a fuskar shi.

Shima kallona yake kasa kasa yana sakar mani smile yinayi kamar bangan shiba dayake nima material nasaka Ash color nida Fatash iri daya muka saka.
Satar kallan shi nayi idanun mu suka hade cikin na juna tare muka sakar ma junan mu murmushi mai kayatarwa wani irin shock naji har cikin zuciya ta,wanda bantaba jin irin shiba,tunda nike da Ya Taufiq.
Mikewa nayi natafi daki zan shiga kenan yakirani,dawowa nayi nazauna kusa da Anty Aisha na zauna.

Kallona yayi yace.
"Ina zaki bayan nace zamuyi zama baki dayan mu ina Fatima."
Tana daki bari inkirata.
"Aaa tsaya bari inkirata a waya."
Kiranta yayi bada jimawa tafito ta zauna kusa dani yace.
"Mi kuke ganin zamu shirya da sunan nan.?"

Shiru mukayi kowa ya shiga nazari can nace.
"Ina ganin asa ayo Order din abinci,ayi Masa,Alkubus Pride rice,jallof rice,cus-cus sai kuma tuwo."

Uhummm,Fatash saura ke.?"
Am togather with Minal saidai bansan tuwo gaskia sai kuma snacks."

Yah cewar Tariq ayi donot,samosa,meat peat,springrolls.
Ya kuka gani.?"
Eh yayi gaskia dan zaifiyin kyau."
Uhmm naji naku Mrs Taufiq why are u silence?"

"Ai Mrs Taufiq tagama magana komai ta lissafa hakan

Please Login or Register in order to submit comment