Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanzun.?"
bakomai amman anjima zamuje kamu bayan isha'i."
"Well amman inasan ganin kwalliyar biki,aiman pic,zanzo daurin aure insha Allah."
Badamuwa zan maka sai kazo,,
"Babyna i miss u,,
miss u too bye.

Fitowa nayi naga harta tafi tashi mukayi mukahau shiri,mai make-up tazo daga katsina muka daukota suka shiga daki tafarama amarya make-up.
Ranar bamu muka gama shiri ba sai karfe takwas na dare munyi kyau sosai cikin material dinmu pink mai touching purple a jiki.

Ango Abdallah saida sukazo kamu da mukayi a katsina wani katafaren gidane na Cousin din shi akaima decoration ya hadu nan mukayi harda iyaye,anyi kamu iya kamu.

Husna tahadu cikin maroon din material dinta doguwar riga sosai ya fiddo da ainihin kyawun aminiyar tawa.
Anyi raye raye yan uwa da abokan arziki,akagama aka yanka cake,kowa yaji dadi sanda akagama 10pm shiyasa akace mu kwana gidan Yayan Abdallah.

Nan muka kwana da safe wajen karfe shaɗaya aka mai damu gida.
Ranar ake daurin auren Asma'u.
Tinda gari ya waye sai nikejin kaina wani iri kamar bani ba,duk jikina yai sanyi,wani irin kewar aminiyar tawa duk ta lulubeni,zaune nike saidai kana ganina ina cikin damuwa.

Anko dinmu muka saka na atamfa light blue mai ratsin pink ajiki.
Anty Habba takirani kanwar Mamar Husna ina zuwa tace zan raka kawar tawa gidan kakannin ta,jan Fatash nayi muka shiga mota mukaje.
Karfe biyu dai dai aka daura ma Asma'u aure da angon ta Abdallah.
Dubban mutane sun shaida,wani irin dadi ya lulubeni.

Domin kafin a daura auren tasha surutai itama wasu nacewa anfasa wasu nacewa dagawa akayi,ba wanda yai la'akari da dalilin dagawar saboda lafiyan tane,da kuma ciwon mahaifin shi.
Jinayi wani abu har kokon raina na murna, da kewa bansan ina zansa abinda nikeji ba.

Koda mukaje gidan su Iyah grandma din Husna hudu ba iyayenta sukai mata mai saka nutsuwa da kashe sassan jiki nidai ina jikin aminyar tawa sai kuka take,nima idanuna tab da kwalla,bawai hudubar bace ke neman sani kuka ba,kewarta ce ke damuna.

tun ina dakewa har kukan yaci karfina,haka mukaita kuka nidake ba Husna hakuri sai aka hau bamu tare,dan harnafita kukan kaina har ciwo yake.
Da kyal nasamu kukan nawa ya tsagaita nan muka dawo zuwa gidan setting Mate dinmu kuwa duk sunzo,aka hau hidima gwanin dadi haka na boye ina kuka,Rukayya ta ganni nan fa suka hau zolayata wai zan rabu da aminiya ta muna kuka,batasu nike ba.
Ya Taufiq ya kirani waya dauka bayi muryata a sarke na dauka tareda sallama.
Minal mi akai miki naji muryar ki haka.?"
Bakomai.
Kizo gida ina jiran ki."

Tashi nayi na wanke fuskata naje gun Husna na rada mata zanje gun Ya Taufiq.
Saikin dawo ta fada itama murya a sanyaye.
Ina zuwa na iske shi falon Baba,gaida shi nayi kallo daya yai mani ya maida bisa wayar shi.
"A ranar murnar zakizo kina kuka,haba Baby na kuka ba naki bane.
Jinjina kaina kawai nayi na goge kwallan da suka taho mani.
"Wace mota zakibi kai amarya ko insa Usama yakaiku.?"

"Aaa zamubi ta amare kabar shi."
Minal.?"
Na'am.
Ina mai kara baki hakuri akan abubuwan dake faruwa tsakanin mu,abinda nikeso dake mu yawaita addu'a in akwai alkhairi atsakanina dake Allah ya tabbatar mana dashi kinji kanwata."

Eh naji zan dage insha Allah.
Yawwa ko kefa yiman murmushi mana pls.
Murmushin nai mashi,ina karajin son shi a cikin zuciya ta.
Good girl."
Wai ya Project kin gama.?"
Eh nagama yanzun on Wanesday zamu fara Exam."
Allah yabada sa'a.

Duba agogon azurfa dake hannun shi yayi yace.
Bari in wuce yamma nayi gobe zanje Lagos Seminar."
Okay Allah ya tsare hanya yabada sa'a.
"My my Queentake care ku kula kinji banda yawo idan akakai amarya kigayama Fatima."

Tom Yayana,ka kula da kanka kazama makaho idan kafita kazama kurma wajen sauraron kowa Allah yakare mani kai my Prince."
Ameen Princes,zan zama kurma,makaho,bebe banganin kowa saike banji amon kowa sai naki Allah ya mallaka manike Aminatu."
Ameen.

tare muka fito inajin sukuni a raina har ya shiga mota driver yaja shi,na koma wajen Husna raina fayau,Ahmad ya rufo gidan shida Zainab suka shige gidan su Husna.

Sai la'asar aka fara shirin kai amarya,Abdallah ne yakirani yabani motar kawayen amarya guda hudu,saida na tabbatar kowa ya shiga sannan na shiga mota daya nida Fatash sai Rukayya da Hauwa'u,har motar mu zata tashi Baban su Husna ya fiddoni ya mai dani motar amarya,sannan muka tafi kanon dabo,inajin wani farin ciki araina tareda kewar kawata.


Har muka isa cikin kwaryar birnin Kano,Zoo Road motocin suka kusa kai cikin wani kamilallan gida mai kyawun gaske nagani na fada,alhmdullh yanda kawata tayi dacen miji haka ta dace da gidan tsara,kowa sai sam barka yake,a falo muka zazzauna kan dankara dankaran kujerunta masu taushi da laushi gwanin burgewa.

Ina isa Ya Taufiq ya kirani waya yai mani barka da sauka,nan muka taba fira.
Da Mama akazo sai kannen Mamar su Husna da dangin Baban sai kanwar kakar su.

Ba awani bari mun fita waje ba,kowa ya zauna bamu jimaba aka kawo abincin saukar amarya,kowa yaci masha Allah.

Washe gari da karfe biyu akayi walima shadda mukasa nida Fatash anko mukayi,munyi kyau,tunda aka gama walima Husna ke kuka niko dai nasama raina bazan kuma kukan ba.

Kirana tayi tasani agaba sai kallona take tana kuka,zuciya ta kuwa neman karaya take cijewa nayi.

"Amaryar Abdallah yadai na zamar maki Cele ko.?"
Rungume ni tayi taita kuka kamar wadda za'a kashe.
Haba Husna kidaina kuka ki godema Allah kinji."

"Minal Allah yai maki zabin miji nagari,inama ninafara ganin aurenki kawata Ya Allah kada kasheni saika nuna mani auren Amina wannan shine cikar burina a rayuwata."
Ameen mutanen wajen duk suka amsa,nidai ina kallan ta,riko hannun ta nayi.

"Husna indai wannan Allah zai cika maki burinki Allah yabaki zaman lafiya kawata da zuriya dayyiba zanyi kewarki kewa wadda bansan ya zansata ba,ina Caranci amman kisani zuciya ta tana Kano Inatareda ke kawata."
Hawayen da nike dannewa ne suka silalo mani haka mukaita kuka kawayen mu nabamu hakuri wasu na goge kwalla.

Allah yasani jinike inama in mutu inuwa daya da Husna gashi zan gama makaranta wazata zama abokiyar shawarata wazai share hawayena idan Challanges sun mani yawa,Ya Allah kazama gatana😭


Ke Aminatu kitashi kin tisa mani Ya' gaba kina sata kuka,maza mike."
Cewar Mama,jiki a mace na mike tarikeni kam da kyal aka fiddani dakin sai kuka take,nima fita nayi ina kukan ga mamakina Usama nagani tsaye bakin mota,sai Fatash gefen shi.

Ba'ajimaba yan walima kowa ya fito daman already mun gyara mata gidan ta,anbar dangin su na kano zasu ida gyara mata komai,mantuwa nayi na koma bag dina na dauko naciro wani dan box na mikata,nace gashi zobe da yan hannune sai sarka,amman kisa zoben ingani."
Budewa tayi duk ta dame kwalliyar ta tsabar kuka ta ciro ta sakala,ta kalleni.

Idan kika kalla zakiji kin rage kewata kidaina kuka Husna."
Murmushi kawai tayi na juya natafi inajin wani iri araina.
Bamu jimaba Abdallah yazo wajen motar mu,kauda kaina nayi bayan kallo daya danai masa.

Ke Minal ba amana wannan kuka har haka so kike ki rudamani amaryata ko.?"
"Uhmm Abdallah kaji tsoron Allah ga Asma'u amana na baka bata dakowa sai kai karabata da duk wasu masoyanta dan Allah kayi hakuri da duk wani hali na Husna ka riketa amana dan darajar alqur'ani.!"

Bakida matsala aminyar Husna wannan kauna badan aure yazama doleba tabbas da Abdallah bai raba kuba,amman ai anatare kema Allah ya nuna mana naki bikin cikin aminci."

Ameen cewar Fatash."
Nagode sai wani Lokaci."
Muka shiga mota Ahmad ke gaba saini da Zainab da Hauwa'u da Fatash ne abaya muka nufi gida ina kewar kawata a cikin zuciya ta!


Kowa ya dawo gida cikin aminci yan biki an watse alhmdullh ranar monday muka koma makaranta dan cigaba da jarabawar mu.

Munfara Exam gadan gadan abun mu,bamuda wata mastala duk munyi rigunan graduate abun mu, munyi Ash and black kowa da sunan shi mun tanaje ta zuwa ranar da zamuyi final paper mu saka,itama Fatash maroon sukayi sai baki ajiki masha Allah.

Banda wata damuwa sai yar fargabar idan nagama karatu wane kalubale zan fuskanta a rayuwata aure aiki ko kuma ba ko daya.

Gashi dai in maganar aure ne banda wanda zan fidda Ya Taufiq ne akwai kalubale a tarayyar mu,Ahmad kuwa tuni na binne babin soyayyar shi a halin yanzun banda kowa daman ance bakin jinina yajman inje Anty Hafsat da ire iren su
Take naji Graduation din ya fita araina saboda challanges dake jirana awaje.

Exam dinmu tayi nisa saura ukku mugama anata programs na gamawa masu party nayi yan aluta na casun su da yan S.U.G
Kowa da abinda yasha mashi kai a haka har jibi zan final Paper na ,danko Fatash yau tagama tata jarabawar murna ba abin faduwa bace nita zauna jira in kammala.


A Caranci Mami ce zaune a falon Baba tanata tata rashin mutuncin ta,tana cewa........




_Yar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Pls
❣️


*BAKIN JININA YAJAMAN😭*


*NA*

_Yar Mutan Kankia❣️_

*_TRUE LIFE STORY!_*

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

_*DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI.*_


S2/E49&50


End😭


_Na sadaukar da wannan book din ga yan *Bakin Jinina Yajaman fans 3* kuyi yanda kukeso dashi_

➿➿➿


"Alhaji Yusuf naga lamarin nan ba abinda da zamu zubawa ido bane tunda naga kai abin kamar bai shafeka ba,ace yaron nan yana soyayya mai zafi da Amina,abin bakin ciki nama har Makarantar su yake binta! Kuma kai shaida ne uban Taufiq yace baison yaron nan da yarka,amman sun naniƙema Juna,koda taje jinya karkaso kaji yanda suke masayar kalaman soyayya atsakanin su,har uban shi yai fushi,dan haka ina kara jaddadama kaima yarki kashedi tarabu da Hussein tunda batare aka haifedu,kada asoma kuma zan kara maimaita maka da babbar murya kajama yarka kunne tarabu da Hussein tinda shi yana ganin yakawo karfi kamar yafi karfin nashi uban.!"

Kallan mamaki kawai Baba kemata yana jinjina kai.

"Karki damu komai ke faruwa ina sane niba yaro bane,dakike maganar Alhaji Mukhtar baisan Amina da ɗansa ainima Yusuf bansan Hussein da ya'ta itama fa haifa akai bawai sakaka takeba,dan haka na haneki da zuwar mani gida da wannan zancen indai Taufiq da Amina ne basu ba auren juna alqawali saidai abunda gaibu ta haifar wannan kuma banda iko."


"Aiko kaima kanka hisabi dan wannan auren har abada basu ba mallakar juna dan haka kaga tafiyata Amina ta rabu da Taufiq ina dalilin bala'i yarinya tanace sai kace mayyana wlh saidai in mutuwa nayi amman basu taba mallakar juna."

Fita tayi ta tafi sai sababi takeyi.
murmushin takaici Baba yayi bai kuma cewa komai ba

*******
Ina zaune natisa book agaba ina karatun final paper dita,wadda zanyi nan da kwana biyu aka daga mana ita sai nan da kwana huɗu zamuyi ta,kiran Baba naga ya shigo a wayata,cikeda nishadi na daga da sallama abakina,naji yace.

Maza kizo gida yau dinnan inason ganinki."
Kashe kiran yayi mikewa nayi inajin kirjina na bugawa kamar zai fado kasa hakanan naji kiran da Baba yai mani kamar bana lafiya bane.

"Minal lafiya miya faru."
Gida zani Fatash Baba kemani kiran gaggawa."
"nalillahi wa'inna ilahirraji'un Allah yasa lafiya kawata,tashi muje nima nakasa samun nutsuwa."
Handbag kawai na dauka muka tafi sai Caranci.


Tinda muka tunkaro unguwar mu naji bugun kirjina ya tsanan ta,musamman dana saka kafata cikin gidan mu.
Ido hudu nayi da Baba a cikin falon shi tareda Mama kana ganin ta kasan ta shiga tashin hankali bayyananne.
Da salllama bakin mu,dukawa nayi muka gaidasu nace,Baba gani.

Kin kwaso kayan ki ko.?"
"Ai Baba sai litinin zan gama nan da kwana hudu."
Nace kirjina na bugawa da sauri da sauri.
"Ai kindawo kenan dan bake ba komawa makarantar nan."


Inalillahi muka dauka baki dayan mu, ina dafe kirjina kuka nafara ina bashi hakuri.
"Baba dan Allah karufa mani asiri kaga shekarun dana kwasa ina karatun nan dan Allah kabari ingama badan hali naba minayi."

Afusace Baba yayo kaina yace.

"Ke dan ubanki ni zaki zubdawa kima da daraja daman karatun dana turaki ashe soyayya kikaje yi bayan kamaki da Ahmad danayi ashe keda Taufiq har soyayyar ku tayi nisa Aminatu?kisa aranki keda gama makaranta har abada.!"
Jikina yahau kyakkyarwa ko magana nagaza Mama da kannena kuka sukeyi sosai.
Baba kai mata hakuri kabari ta ida dan Allah kuma wlh...
Cewar Fatash wadda itama harta fara kukan

Yiman shiru kema waya saka da bakin ki.?
Ke kuma kisa aranki bake ba gama karatu,daman akan karatun ki ansha goranta mani ashe gaskia ne ake gaya mani kin dauka zan kaiki Jami'a ban bibiyar al'amuran ki ko kin dauka haka zan sakeki sakakai bayan kedin amanace agareni Allah yabani kinma kanki bake ba kowama makarantar.
Haka nakamaki kina soyayya da Ahmad,kika turo mani Junaid akan yazo neman aurenki kikace baki san shiba,kikazo kika fasa auren Ahmad bayan sa ranar ku,duk dan kicimani mutunci ashe saboda soyayyar Hussein kika ƙishi,yanda uban shi yaki ki,nima bazan lamunce ba ki auri Taufiq ba bake bashi har abada.!"

Kuka nike sosai mai tsuma zuciya har ganina yara ragewa nahau yi mashi magiya.
"Baba dan darajar Allah karufaman asiri kabari nagama karatuna,natuba bazan karaba.!"

"Yiman shiru munafuka kin barar da furarki a wajena ban kara yarda dake,na aminta dake kin ha'ince koda kikaje Kaduna jinya angaya maki bansan soyayya kuke yiba,ni zaki cima zarafi,dani kike batun wlh zaki gane kuran ki."

Kuka kawai nike ga radadin rabani da Ya Taufiq ga bala'in dana tunkara na datse karatuna wanda baifi 4days ingama hada karatuna na medicine ba.

Kaina naji ya buga manai bansan na daura hannuna bisa kai na kurma uban ihun da bansan nayiba ji nike kamar zan haukace da zaucewa.
Fatash ta rungumoni tana bani hakuri itama kukan take sosai,ranar tazama bakar rana agareni bansan ya zanyiba.

Har gari ya waye ban iyacin komai ba,ga kiran yan Course Mate dinmu da suketa yimani wai inzo muyi turtorials saidai nace masu banda lafiya.

Rayuwa taimani kunci na tabbata banda sa'ar rayuwa challanges sun mani yawa a cikin zuciya ta,da misalin karfe goma na safe Fatash ta shirya ta tafi gida asusuce ganin irin tashin hankalin dana shiga.

Tana komawa ta iske Tariq da Taufiq a sashen Mum,itama kana ganinta tana cikin tashin hankali,domin gidan ya rude mata Mami da Abba sai bala'i suke akan soyayyar Amina da Taufiq,ka rantse kace mayya zai aura.
Yanda sukaga yanayin Fatima ya daga masu hankali zama tayi ba kwari,a jikinta.

"Graduate ina smiling din ya tafi kike fushi.
Ya Tariq ke mata wannan tambayar ,kuka ta saki mai tsuma rai kowa yana mata kallan tuhuma.
"Fatima mike faruwa kiyi magana.
Mum ta tambayeta hankali atashe.
"Mum Komai yagama lalacewa abubuwa sun tabarbare."
A dimauce Mum ta riketa tana cewa.
"Ke yimani bayani zaki daga mani hankali inaji da tension dina.!"

"Ya Taufiq dan Allah ka hakura da Amina wlh Baba Yusuf ya cireta daga makaranta dan kawai ya gano kuna soyayya yace ita da karasa bokonta har abada kuma bakai bata.!"

A razane Taufiq ya mike har yana rike kirjin shi,ba rabasu bane ya daga mashi hankaliba karatunta wanda ya dade yana tsumayin sa,ya tanadama gifts duk dan cika mata burin ta.

Agigice yake girgiza kanshi cikeda ɗimauta.
"Aaa Fatima ki tabbatar mani da karya kikeyi Amina zata cika burinta zata gama karatunta kice karyane Fatima."

Wlh Allah Ya Hussein rayuwar Amina ta tsaya komai ya lalace Qaddara ta riga fata,Haka Allah Yaso,ka tsaneta kodan cikar burin ta dan Allah kada kubari karatunta ya datse.!"
Bazan iya tsanar Aminatu ba wlh ina sonta koda zan rasa raina na tabbata Amina tana cikin Qaddarata!"
Dole karabu da ita koda zaka mutu Hussein....


******Caranci.

Kuka nike sosai nadaina cin komai wayata Baba ya amshe banda wanda zai share hawayena,kewar Husna ta addabeni a raina,hawayena sunata ambaliya nasan da tananan tabbas tana ajikina tana sharen hawayena banda mahaifiya ta bamai cewa in daina kuka,dan Baba ya fita shirgina.

Ganin kukan nawa bamai karewa bane hakan yasa naje dakina,biro na dauko na rubuta wasika,nakira Ahmad kanina, cikin sirri nace yakaima Baban su Asma'u hannun shi da nashi
Haka akayi kuwa ina zaune sai jiran tsammani nike amman shiru ba alamun Baban su Husna zaizo gidan mu,nidai nasan tawa takare haka Allah yaso.

Duk kwana daya da zanyi daidai yake da bugun numfashina ganin Exam dina ta karshe zata zama waste agareni.

Zazzabi mai zafi ya rufeni ko allura Baba kinyi mani yayi magani kadai Mama tabani,damuwa kuwa nasan ta, tun ina kankanuwa ta bare yanzun da nike shekaru 25 a duniya.

Wasa wasa saura kwana biyu muyi Exam kasa hakura nayi,naje wajen Baba yana tsakar gida zaune gaidashi nayi bai amsani ba,ya kauda kai gefe.

Dukawa nayi na hade hannayena ina kuka nace.
"Baba natuba kayafe mani dan Allah karufa mani asiri kabarni na ida jarabawa ta,naji zan hakura da Ya.....

Kika ida kiran sunan shi agabana saina karyaki tashi kibani waje nagaya maki keda ida karatu sai alahira in anayi mutuniyar banza,barima kiji nida kaina zan zaba maki miji in maki aure ni zakima dibar albarka da Yusuf kike magana nidake aga waya haifi wani."

"Baba kaine wlh kaine ka haifeni kowa ya shaida hakan, kataimaka mani dan Allah badan halina ba.!"

Kuka nakara saki mai sauti.
"daman ke har wani halin kwarai ke gareki tinda har kika iya ha'inta ta ina uban ki,baki da abinda zakiyi dan burgeni Amina,kinyi breaking trust dinki a cikin zuciya ta,tashi kibani wuri kuma bake ba Taufiq!."

Da gudu nayi daki ina kuka mai sosa rai,ina kiran inalillahi wa'inna ilahirraji'un!


*****Bakai ba Amina dole karabu da ita saidai indai kai ba ɗana bane."
Cewar Major daya shigo falorn Mum,shida Mami sai Samir.
Da idanu suka bisu dashi musamman Fatima dake ji kamar zata mutu.

Zubewa kasa Taufiq yayi duk ya shiga matsananciyar damuwa yace.
"Abba miyasa katsaneni miyasa ka kasa yimani uzuri,kaman ta kaunar Amina Qaddarata ce,ada banso kowace ya'mace ba kullin addu'arka kaganni na fidda mata bazato ba tsammani a fiddo Amina miye laifinta da zaka tsaneta Abba.!"

Saboda dan uwanka ita yafara so,sannan kaima kace ita kake so,bayan nagaya maka hukuncina amman kayi kunnen shaggu da maganta ka dauka wasa nike!"
Taufiq yana kasa bisa guiwar shi ya rike hannun mahaifin nashi yace.

"Kasa mani albarka Abba kai mahaifin nane kuma da tausayi akasan uba akan dan'sa dan Allah kacika mani burina in auri Amina.!"

"Kaji zancen banza yarinyar nan saidai in tsafeka tayi, Allah Alhaji idan ka amince zata zamar mana fitina a cikin gidan nan,banga alkhairi a jikin yar nan ba,kumafa Samir aka hana nidai raina bai kwantaba karka bari ya auri yarinyar nan.
Cewar Mami ta ida maganar cikeda tuggu.

"Koba kice ba Mufida ba Taufiq ba Amina bazata zama ya' acikin ya'yana ba wannan alqawali ne!"

Mikewa Taufiq yayi yana fesar da iska mai zafi yayi side dinshi,nan sukaita bala'i musamman Mami.
Sudai su Mum nasu ido



******Ina kwance bisa gadon dakin mu kamar marainiya nayi zurfi a tunani gashi gobe karfe hudu na yamma yan Course Mate dinmu zasu zana Final Exam lallai ta tabbata bani a ciki,harna dangana nazubama sarautar Allah ido,can na tsinkayo muryar Baban su Husna a kidime na mike nayo waje dukawa nayi na gaidashi a mutunce,kallan tausayi ya bini dashi,Baba ya leko fuska sake yace ya shigo Sitrum dinshi suka shiga nikam nagaza tashi daga inda nike,dagani har Mama sai muka fara labe danjin dame yazo musamman ni danasan na aika mashi da later.

"Haba Alhaji Yusuf kasan mika akaita kuwa?anya inrai yabaci hankali na gushewa?yarinyar ka tasha wahalar karatunta zakazo ka datse shi,kada kabiyema son zuciya mana,dan Allah kabari yarinyar nan ta ida karatun ta,dan wlh labari ya karade unguwa kowa da abinda yake cewa har cewa akai korota akayi kaimata adalci kabari ta ida dan Allah."
Hmmm Baba yaja da karfi har cikina na katsawa tsorona kada ya ki hakura.

Alhaji banso ka shigo zancen ba yarinyar nan batajin magana soyayya take da Taufiq bayan kai shaidane mahaifin sa da kanshi ya yanke alakar auren su amman ta nace mashi,kayi hakuri kabarta duniya ta koya mata hankali.!"

Aaa kai kasan darajar ilimin nan kodan al'umma kabarta ta ida daman likitoci mata sun mana kadan kabarta kuma kasa mata albarka dan Allah Alhaji Yusuf."

Shiru yayi harna cire rai zai hakura kuma sai yayi magana yace.

"Ko a lahira wani nacin arzikin wani to kasani Amina arzikin ka taci aiko Yayata kagako ban ketare zancen ta tayi juyin duniya naki yarda amman darajar kana makwafcina kuma aminina na aminta zata ida.!"
Bansan na saki kukan farin ciki ba.

Inajin Baba nacewa.
"Labe kike mana ko Aminatu,miyasa bakijin magana."

Shigowa nayi dakin guiwowina biyu ina hawaye.
"Baba nagode dalilin ka ya yafe mani Allah yakara girma."
Ameen dan haka kikiyaye kuma ki rabu da wannan yaron tunda mahaifin ki baiso."
Toh insha Allah,Baba nagode da kayafe mani Allah yasaka da alkhairi."

"Rike godiyarki saidai kazama shaida kema kijini da kyau.
Khadija,Na'am cewar Mama shigowa tayi ta zauna,tace gani.

Kema kizama shaida ba Amina ba Hussein,sannan tana gama karatun nan ko bautar kasa batayi zan aurar da ita."

To Alhaji munji amman kada kada kaima yarka auren dole."
Inji Baban Husna

"Ai Bakin Alqalami ya bushe domin kuwa harna gama magana tuni da mijin da zai aureta yasan da zancen.!"

Shiru kowa yayi musamman ni dake ganin taya zan iya rayuwa ba Ya Taufiq! Wane kalar miji Baba zai aura mani? Shin yana sona? Kodai sadaka Baba zaiyi dani? Wace irin rayuwa nike fuskanta!kuma wane babin rayuwar zan bude? daga wannan sai wancen nikuma a haka rayuwata ta zomani wace kalar Qaddara ke kusantoni, kowa da kalar tasa.

Ameen cewar Baban Husna,sallama yaima Baba yai mashi rakiya nidai na kasa kuka nakasa magana saidai ido,da kyal na babbaka nafara shirin wanka so nike gobe karfe shidda nabar gida inje dan insamu Jarabawa.


*******rike yake da kayan shi na Soja(kaki) ya iso gaban mahaifin nashi dake tareda matan mashi yana kara shaida masu zabin matar dayaima Taufiq yar aminin shi cikin wata daya zai aura mashi ita,kuma yakara jaddada masu ba Taufiq ba Amina.

Zubewa yayi bisa guiwar sa idanin shi rau kamar wuta yace.
"Kayafe mani Abba nagaza yimaka biyayya akan Amina,narasa sukuni zuciya tagaza halbawa kamar takowa na zama sakarai sususu,wanda yagaza mallakar zuciyar shi,ina mai kara baka hakuri na yanke shawarar aje aikin office da nikeyi,domin banda wani hope akai Abba kayi hakuri narasa control dina aikin Soja bai kamaci Hussein Mukhtar ba,domin Major Taufiq Sarki Mukhtar tuni ya dade ba 6acewa wannan wanine bawan zuciyar shi,Abba kayafe mani!"
Ya ida maganar yana aje belt dinshi da sauran uniform.

Kallan shi kawai Major Sarki yakeyi yana fesar da numfashi mai zafi yace.
"Akan mace zaka aje aikin ka? Akan mace zaka juyama uban ka baya ka gaza yi mani biyayya? Duk akan mace? Lallai kam Hussein din dana sani ada ya jima da mutuwa,Hussein dina jarumine kuma gwarzo mai dakakkar zuciya,da kwarjini ba bawan mace bane asalima matan basu gaban shi,wannan shine suffofin Hussein dina,amman wannan wanda ke gabana raggone musamman a bangaren zuciyar shi yazama bawan ta,dan haka yanda kagani haka za'ai Hussein!
Saidai inaso kowa ya shaida ba Taufiq ba Aminatu har abada,ba aikiba ko ubanmi zaka aje damuwar ka!sannan ni Mukhtar naimaka mata koda zaka mutu Khairat itace matar danai maka yar Aminina Mas'ud kowa ya zama shaida.

Mun shaida cewar Mami

"Maganar aje aiki kuwa ni Major Mukhtar Sarki Munzali na umurceka da kaje ka rubuto resign later kamar yanda doka ta umurta, ba'a aje aiki a gida,saboda a gida ubanka nike a office kuwa shugaban ka nike fatan ka hankalta.!"

Naji Abba insha Allah zan rubuto nagode."

Ya fice abinshi baidamu da maganar auren da akace za'ai mashi ba,ko me Taufiq ya taka?


******nagama shiri karfe takwas na safe kalaci atsaye nayi shi domin raban da cikina yaci abinci na kwana biyu saiya zamana hannu baka hannu kwarya nikeyi shiga nayi dakin Baba ganin duk yan uwana suna ciki harda Mama zama nayi ina duba wayata wadda yabani ita jiya da daddare ganin takwas da rabi,baki dayan mu,muka maida kallan mu akofa sakamakon sallama da muka tsinkaya musamman ni dake neman kwarewa,haduwar idanun mu cikin na juna nida Ya Taufiq ida shigowa yayi ciki ba shiri naaje kwanan hannuna kallo daya Baba yai mashi ya kauda kai,gaban shi Ya Taufiq ya zube yana hada hannayen shi sifar ban hakuri,kirjina ke halbawa da karfi kamar zai faso rigata ya fado,muryar shi na rawa ya kalli Baba ya.......


_*BAKIN JININA YAJAMAN* kenan wanda yazo maku da salo mai taba zuciya ga rikitarwa,sai mun hadu a cikin *QADDARATA* season three danjin yanda wannan kullaliyar zata kasance._

Kash abubuwa da dama dama waɗan da bakuyi zatoba duk zaizo maku a cikin *Qaddarata* ,shine wace irin Qaddarace wannan kuma taya zatazo da wani salo take tafe?

_Kudai kuci gaba da kasancewa da Jameey danjin yanda komai zai wakana._


*Naga sakon ninku da fatan alkhairi nagode Allah yabar kauna da zumunci ni Amina Caranci ina maku fatan alkhairi*

*Noted:-* ```Naga ƙorafe ƙorafen ku,ina kara baku hakuri nasan kuna ganin abubuwa iri iri a cikin wannan labarin kusani ba yanda zanyi domin haka labarin yazo kuma kowa da kalar tashi Qaddarar fatan zaku fahimceni🙏🏻```

_Banso na batawa kowaba kusani akwai

Please Login or Register in order to submit comment