Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tai mani yasani danne kukana naji maganar Ya Taufiq har kokon zuciya ta.


Daki nashiga nahau kuka ina tunanin kodai ya daina sona kwata kwata.
Ranar haka na wuni a daki sai kuka nike ba carry over tasani kukaba halin ko in kula da Ya Taufiq ya nuna mani,ba wanda nagaya mawa nayi C.O da 4.0 nagama semester najima inajin ba dadi musamman hushin da Ya Taufiq keyi dani.


Wasa wasa nafara shirin tafiya school haka nagama kimtsa komai nawa washe gari na koma makaranta.
Saida nayi kwana ukku sannan Fatash ta dawo,sadda zamuyi sati Lecture ya kama gadan gadan,saidai tinda nai C.O a Course din Dr JJ yan course mate dina suka debe duk wani zargi da suke mani yau JJ ke garemu kowa ya kama kanshi musamman ni,saidai abin mamaki bashi yazo ba,kuma a ƙa'ida bai daina daukar mu sai mun shiga final year amman sai mukaga Prof Sharif shiya daukemu, koda ya fita a Course din Dr Salim shima wata tazo Dr Mandiya kowa yai mamaki rumor kuwa an yada wasu nacewa an kore shi wasu nacewa transfer yayi nidai koma ina yayi damuwar shice daman bansan ko ganin shi inakarayi a rayuwata ta duniya.

Bayan kwana biyu yai mai text message.

```Amina Caranci kina ganin burin ki ya cika keda dan uwanki ko?yasa an koreni daga school an mani demotion sannan anmani transfer a inda bai kai nan ba,duk ta dalilin ki harkika jama Salim,wlh saina baki mamaki saina hanaki zaman lafiya da sukuni daga ke har Taufiq din da Dr JJ kuke magana.```

Ina gama karantawa na adana shi a Email dina da abubuwan daya turomni duk nasasu a Mail dina domin nafara tsorata da barazanar dayake mani,da haka nai blocking number din shi.

Sosai nayi concentrating akan karatuna nafara samun nutsuwa zuwa yanzun ba wadda nike good time da ita irin Maryam sai Humaira domin sun kara tabbatar da kokarina daga Yunus saini a class dinmu tangan muke tafiya kowa yasan yanda karatun Medicine yake, zuwa yanzun duk kusan rabi da kwatar yan Course dinmu duk sunyi reciting wasu kuma sunbar school din a year 5 dinmu kaf matanmu da mazanmu bamu wuce mu talatin cif saboda zazzaga da rairaya da muke sha,aiko munsan muna karatu musamman da nasamu cikakkar natsuwa ta.

Wasa wasa Ya Taufiq yai mani waje ya ajeni gefe saidai in suna waya da Fatash shima din baicewa ta gaidani saidai innice nace ta gaida shi zai amsa a dakile.
Haka rayuwa ta kasane gwanin dadi da walwala.

Bayan wata ukku aikin mu yafi yawa a sibiti kullin muna theater da sauran department matanity,Minor theater da sauran sassa na asibiti sai gwaji ake mana tareda manyan Doctors tun level 3 muke watanni a cikin asibiti amman yanzun ankara linka mana sosai akai.

Haka abubuwa sukai taja bayan sati biyu Ahmad yakai wata yana magiyar ganina amman naki amincewa hardai yasamu nayarda koda yazo asibiti ya sameni munsha fira sannan ya maidoni hostel fitowa mukayi muka tsaya jikin motar shi kana ganin mu kasan mun shaku musamman yanda mukema juna smile,hankalin mu nakan junan mu muryar dana tsinkaya cikin kunnuwa yasani suman tsaye har shi saida ya razana a dimauce na jiyo jikina na kyarma kamar mazari ganin Baba daya fito daga motar shi tsaye yai holding hannayen shi fuskar shi ba alamun wasa acikin ta,tabbas nashiga rudu marar misaltuwa tsayawa baiyana maku bata lokacine,atare nida Ahmad muka isa bakin motar shi muka gaidashi sannan na koma gefe duk na raina gaskia ta,maida kallan shi yayi gun Ahmad yace.
"Bakaine kataba zuwa gida neman izini,nace kabari tagama karatu ba.?"
Eh Baba nine."

"Ya akai kabiyota har makaranta.?"
Shiru yayi yafara kame kame yace.
"Kayk hakuri Baba kuskurene."

"Aaa ba wani hakurin da zaka bani domin dagani kun shaƙu koma ince kun sasanta kanku kafin tai maka izini kazo neman auren ta,tunda naganema idanuna ina umurtar ka daka turo iyayen ka cikin satin nan asa maku rana kanajina.?"

Daram haka naji kirjina ya buga har saida na dafa mota jin juwa na neman kadani kasa na dake.
Ahankali Ahmad ya dago kai ya kalli Baba domin yanda yaji maganar shi ya tabbata ya fusata,kuma yana ganin kamar zai mani auren dole ne."
"To Baba nagode Allah yakara girma."
Ameen.


Ko kallona baiba ya koma motar shi,ganin haka yasa Ahmad yatafi ko magana bai gigin sake yi mani ba,niko idanuna har sun ciko da kwalla nasan wannan karan ko zan mutu sai Baba ya aura mani Ahmad tunda nace JJ karya yake bani na tura shiba,a hankali na isa bakin kofar motar nashiga ina kuka mai tsuma rai saidai ko kallo ban ishi Baba,bare insa ran zai tausaya mani,ya janye hukuncin shi akaina,kallo ɗaya yai mani ya kauda yace.

Ya karatun ki.?"
Alhmdullh nace ina goge kwallan idanuna,kudi ya miko mani.
"Keda Fatima ga kayanan a boot dauka ina sauri."
'Baba dan Allah kayi hakuri ka yafemani dan Allah natuba."

"Nayafe maki,ai ban taba fushi dake ba kuma ban fatar ranar da zanyi fushi dake Mamana,ni kaina bansan abinda zai faruba,tashi kije Allah yai maki albarka."
Ameen Baba nagode Allah yasaka da alkhairi."

Fita nayi ya bude mani boot na kwashi kaya natafi saida yaga shigata hostel yaja mota yatafi.
Jiki mace nakoma daki duk banjin dadi arayuwata ba abinda nake tsoro da shakka irin shirun Baba musamman idan kai mashi laifi har kwara yaimaka fada yafi maka sauki daya shareka.

Ba Fatash sakon nayi tayi godiya harta fara sababi wai ban kirata sun gaisa ba nace sauri yake ko minti goma baiba,saidai ban bata labarin abinda yacema Ahmad ba gudun kada ta gayama Ya Taufiq hankalin shi yatashi.

Haka naita rayuwa sukuku dani ga shakkun abinda ka iya zuwa da dawo ga tunanin Ya Taufiq ya gujeni haka na zauna banda wani hope a tare dani.


Bayan sati ɗaya kuwa Husna takirani tace ansa mani rana da Ahmad wata ukku,tunkan ta ida magana na saki wayar kasa na kwalla uban ihu mai razanarwa har saida Fatash dake bacci ta farka a dimauce tayo kaina tafara tambayata saidai nagaza furta uffan.
jin anata hello hello kawata kidaina kuka mana hakan yasa ta daga taji Husna ce.
"Mike faruwa Asma'u mi akai mata.?"

"Ansa mata rana shine take kuka."
Kamar ruwa yaci Fatash tai shiru kanta na bugawa da kyal tace.
"Dawa aka sa mata ranar.?"
"Ahmad mana."
Kashe wayar tayi ga mamakina itama kwallan suka fara ziraro mata kallona tayi rai bace tace.


"Amina Yusuf mi yayana yai maki kika tsane shi?mi yasa bakima Ya Taufiq adalci ne?duk yanda yake sonki ashe zuwan da Ahmad yayi dan ku sasanta kanku asaka maku biki da shi,gaskia Minal bakida tausayi na fahimci so kike ki kasara mani rayuwar dan uwa bayan ya sakan kance kece tashi rayuwar kin bani mamaki."


Fatima wlh blh ban son Ahmad ki yarda dani Ya Taufiq nikeso kema shedace."

Idan Ya Taufiq kikeso taya har za'asa maki rana da Ahmad nayi imani da Allah Kawu baitaba maki auren dole duk zafin shi."
Shiru nayi sai kuma nace.

"Eh Fatima kinyi gaskia ranar da Baba yakawo mani ziyarar bazata,nan ya ganni da Ahmad shine yace ya tura iyayen shi,a ranar saida nabashi hakuri na dauka ya janye kudurin shi,shiyasa ban fada makiba,kinji dalili amman kinsan Ya Taufiq nikeso kema shaidace ya jima yanaso yazo ina hana shi ashe tsautsayi yasa shi zuwa wajena."

Naji abinda kikace amman daman can kina son shi ko yayane tunda kike kulashi a waya,kuma abinda Baba zai gani da ace baki son shi aida baki bari yazo har Makarantar nan ba,nidai bakomai kisani duk abinda yafaru da dan uwana wlh Amina dake zan koke!ya nanike maki yanzun Ya Tariq yayansa Ukku,Ya Samir nada biyu amman shi Ya Taufiq yaki aure yace saike ke kuma baki da buri saina son kiga kin tarwatsa mashi rayuwa akanki ya gaza yima mahaifin mu biyayya! dan kawai ya rayu dake Amina gaskia bansan ya zan kwatanta maki bakin cikin da nikeji ba nagaji da matsalolin nan.!"
Tashi tayi tabar dakin tana kuka,nima kukan nike kamar zautatta.

Wayata tahau ruri Ya Taufiq ne zuciya ta,ta tsinke tausan shi yakara kamani dagawa nayi nakasa magana sai kukan zucin da nikeyi.
"Dagske ne ansa maki rana Minal.?"
Yanda yai maganar yakai kololuwa ga ɗimauta
"Haka naji Ya Taufiq."
Auren dole za'ai maki.?"
Ya jefo mani tambayar
Shiru nayi,narasa mizance mashi kukan ya kubce mani harda shasheka nike dan kuka."

"Enough yes/no,nace auren dole za'ai maki.?"
Nidai banda bakin bashi wannan amsar saina kara karfin kukana kashe wayar shi yayi,kwantawa nayi ina jin inama mutuwa nayi sake kirana yayi bayan 30mint ina dagawa yace.

"Dakyau ashe kinada saurayi bayan ni,Amina daman baki sona ashe nagode tabbas kin mani halacci wlh bazan taba ganin laifin Baba ba,domin yaudarar shi kikayi kamar yanda kikai mani ai yasan baki kula samari dole ya yanke wannan hukuncin nagode maki Allah yahaɗa kowa da rabon shi,nima Allah yabani hakuri da danganar rashin ki,kuma ya bani mai sona.!"

Kashe wayar yayi ihu nasaka kamar an mani mutuwa wanda a wajena kusan hakane domin rashin Ya Taufiq a taredani daidai yake da datsewar numfashina,koda Fatash ta shigo wani karamin kit naga ta zuba kaya a ciki tabar mani dakin lokacin ban iya magana bare inji ina zataje nidai nasan tawa ta kare.

Wasa wasa nafi sati ba Fatash bare alamun ta niko ban zuwa ko ina sai ciwo da nike fama dashi kiran duniya naima Ya Taufiq bai dagaba kuka nike ina kiran Allah ka kawo mani dauki

Ga gida daga Mama har Baba na wanda yace ansa mani rana,baccin Husna nasan halin Baba shi zai hana Mama gaya mani baiki ina dawo a ranar yakaini gidan mijiba koma mizanyi inyi damuwata ce.

Haka na zauna itama Fatash din bata daga wayata gaskia nashiga damuwa,narasa wane Bakin Jini ke gareni da duniya tai mani atishawar kare yanzun ba mai sona sai Husna duk masoyana sunkini dagani saini inalillahi ya zanyi.

Rayuwa banda banbaci da maiyinta gidan yari gani nayi lamarin ba mai karewa bane bayan sati ukku na shirya zuwa gida ko Baba bangaya mawa ba domin shirun nashi yakara gigitani.

Ranar asabar na isa Caranci ina zuwa gida na iske Baba kuwa yanacin abinci dukawa nayi na gaida shi,kallo daya yaimani ya amsa ya kauda kai,karfin hali nayi na wuce daki na'aje kayana ko Mama ta sauya mani sama sama ta karbeni haka na zauna gida har kusan kwana ukku ba wanda yace mani uffan bare atambayi dalilin dawowata gida saima akayi kamar ba'asan da zamana a gidan ba.

Hakan ba karamin zafi yai mani arainba cijewa kawai nike saidai kukan zuci daya zama abokin firata zuciya tab da kaunar Ya Taufiq,nasan duk inda yake a halin yanzun ya fini shiga damuwa.

Ina zaune ni kadai dakina wata dubara ta fado mani arai dauko wayata nayi nakira Ahmad yana dagawa nace.

"Ahmad kazo kacema Baba baka sona kafasa aurena wlh Ahmad kakuskura ka aureni sainayi ajalinka na tsaneka kuma ban kaunarka a rayuwata nadai gaya maka.!"

Am am Amina dan Allah kirufa mani asiri ina son da kike mani ya tafi ki tausaya mani.!"

"Dakata Ahmad inaga .
nagaya maka wanda nikeso ko? Sai!nace maka kaine zan aura.?"

"Amman Amina nace maki allura cikin ruwa kuma Allah yasa dani za'ayi kiyi mani lamani dan Allah ina sonki."

Ni kuma bansan ka Ahmad ka kyaleni ai kaga yanda komai ya faru agaban idanka wlh ka aureni saina zame maka bala'i da jidali kama san da wannan Ahmad."
Amina tsaya dan Allah kiji wata magana na rokeki....

Kashe wayata nayi,kiran duniya yai mani naki dagawa tunda akace ansa mana rana daman na yanke alakar waya dashi kwata kwata,haka kullin yakirani ban picking,nima in kira Ya Taufiq bai picking,ikon Allah wannan shine akekira son maso wani kenan,aganina yanzun Ya Taufiq bai sona nike rawata ina kidina,wannan kenan........




_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Pls
❣️



*BAKIN JININA YAJAMAN😭*


*NA*

_Yar Mutan Kankia❣️_

*_TRUE LIFE STORY!_*

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

_*DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI.*_


S2/E41&42



A Kaduna kuwa tunda Ya Taufiq yaji labarin sa ranata ya susuce ko aikin daina zuwa yayi ba yanda Abba baida shiba yaki zuwa ciwo ya kwantar dashi gashi bai magana da kowa sai Fatash ko Mum bai cema komai akan lamarin itama ta wallafawa Allah, ko Baba bataima maganar sa ranata ba tasan Allah shine mai komai.

Itako Mami banda jin dadi ba abinda take har cewa take ai daman nace kaida Amina har abada yanda Samir yarasa kaima ka rasata Hussein.

Bata ita yake ba zuwa lokacin zan iya cewa ta ranshi yake saboda cutar so ba karamin guba bane.

Rayuwa ba dadi daga Ya Taufiq harni dake tsaka mai wuya.
Ranar danai kwana shidda Mama ta kirani.

Ina zuwa nagaidata dukawa nayi zuciya ta bugawa nasan koma minene sakone daga Baba domin kwayar idona tayi kadan in sake tunkarar Baba da wannan maganar bayan nayi breaking trust din dayake mani.

"Aminatu ko kin gama karatu ne.?"
Aaa Mama ban gama ba sai next year."
Allah yabada sa'a,yaka mata gobe kikoma makaranta duk abinda kikeyi."

Toh Mama aiman lamani zuwa jibi.
Allah yakaimu.
Tashi tayi ta shige dakin ta.

Agidan su Husna kuwa aikowa Mama akai za'akawo kayansa ranar ta yau bayan la'asar daman tagaya mani saina dauki abin wasa,saida naga Mama ta tafi na yarda,itako gidan mu ta gudo,ta zauna sai lamarin kawar tawa ya birgeni ganin zata auri wanda takeso zabin ranta,sosai na boye damuwata natayata murna kamar yanda take supporting dina akoda yaushe,ranar yini tayi suna soyewa da Abdul,nima nai waya dashi natayasu murna saida magrib Mama ta dawo gida,tareda Husna mukaje ganin kaya alhmdullh komai yaji yai kyau sosai.
An tsaida wata hudu rak April,alissafi anyi nawa da wata daya za'ai nata.

Kowa da abinda yake cewa aminai zasuyi aure lokaci guda itako saijin dadi take nikam saidai inyi yake wanda tafi kuka zafi.

A wajen Anty Hafsat wannan sa ranar da akai mani ba karamin haukatata taiba duk ta rude kullin da kallar abinda zata cema Mama,wai kada ta yarda ance yaron dan iskane."

Mama tace ko a gidan giya aka ganshi zasu bashi aurena ai kowa yana zunubi kuma Allah ya yafe mashi."

Jin abinda Mama tace ya fusata Anty Hafsat,niko awajena banda wata damuwa daman ba son auren nike ba.

Saida ta kusa fita gidan ta waigo tace.
Nabaki shawara amman kika ƙibi ko Khadija?to ayi auren ingani.!"

Ta tafi tana bugo kofa.
Allah shi kyauta shine abinda Mama ta iya cewa.
Nikam Uhmm nayi kasan makoshina.


Washe gari kuwa naji shiru ba alamun zuwan Ahmad sake kiran shi nayi da dogon message na tashin hankali na aika mashi dashi,zaune nike inajiran replay dinshi.


Da yamma likis ina daki kwance naji murna Zainab tana oyoyo Ya Taufiq sannu da zuwa,a firgice na mike nasa mafarki nike nayo waje aikodai Masoyina ne,kana ganin shi kasan yana cikin damuwa yakara haske sosai,kallo daya yai mani ya kauda kai,gaida shi nayi,ina kwana."
Lafiya lau."

Yace dani,Mama ke mashi maraba da zuwa saiga Baba ya shigo kama hannun Ya Taufiq yayi sukayi Sitrum dinshi tare suka zauna bisa tree seater nikam kamar munafuka na lafe jikin taga ko numfashi bansan yin mai karfi naji Ya Taufiq yace.


Baba dan Allah kataimaki rayuwa ta,kabani auren Amina nayi yanda zanyi nagaza hakura da ita,kai dan uwan mahaifiya tane nasan zakaji tausaina in laifi naimaka ka yafeni natuba.!"

Hussein wlh baka taba yimani laifin Komai ba a duk duniya inda wanda nikeso ya mallaki Aminatu bayan kaine,karfa kamanta kai jinina ne akan mi zan ƙiƙa,abu daya ya hanani baka Amina matsalar mahaifin ka,in yau zaice kazo ka aureta yasa albarka mi zai hanani baka Amina amman muddin hakan bai faruba,na rokeka karka kara yi mani maganar Amina bansan fushin zuciya yasa nai aikin dana nasani domin kai jinina ne."

Jinjina kai Taufiq yayi alamun gamuswa.
Ya za'ayi dasa wannan ranar.?"
Ya Taufiq ya tambayi Baba a raunane.


"Tananan daram saidai in su suka fasa amman ni Yusuf bazan saba alqawali ba,wannan shine adalci."
Ajiyar zuciya ya shide haka Baba yaita kwantar mashi da hankali.

Nikam na kosa ace inzo ingaisa da Ya Taufiq amman shiru bai nemeni ba,saida yamma yatafi ko sallama baimin ba sainaji ba dadi a raina

Jin abinda Baba yace muddin basu sukace sun fasa ba bazai fasa aura mani Ahmad ba hakan yasa nakira shi waya aiko wata yayar shi ta daga sai naki magana,Ahmad din na wanka akira zuwa anjima.
wani dadi ya kamani nai sauri na rubuta mashi text message kamar haka.


_Ahmad Idris ina kara jaddadamaka kayi gaggawar zuwa gidan mu kai da iyayen ka kucema mahaifina kun fasa aurena inba hakaba kasa aranka ni zanyi ajalin ka,nace natsane ka! Ya Taufiq nikeso waike wane marar zuciya ne karabu dani ban sonka!_

Wani ajiyar zuciya na shide ganin sakon nawa ya tafi,saboda soyayyar Ya Taufiq ta rufe mani ido namanta da shima Ahmad din masoyine na gaskia kuma mai sona dan Allah amman nidai nafison Ya Taufiq araina.

Washe nagama shirin komawa makaranta sai diminiya nike inajiran inji zuwan su Ahmad gidan mu.

Danko Baba tun ranar danazo nagaida shi ya amsa bai kuma tankani ba,ko kudi Mama yaba tabani.
aiko karfe biyu daidai akaima Baba sallama koda ya fita yaga iyayen Ahmad ne dashi sukazo har falon shi yai masu iso,suka gaisa sosai kanin Baban shi yace.

Alhaji kayi hakuri da maganar da mukazo maka da ita,hakika munasan Aminatu hakama ɗan mu,saidai matsalolin da muka fuskanta yasa mun yake shawarar fasa aure nan tsakanin ta da Ahmad.

Tabbas fadar tashin hankalin da Baba ya tsinci kanshi a ciki bai misaltuwa,cijewa kawai yayi yace.
"Naji abinda kukace nasan hakanan bazakuce kun fasaba ko miye dalilin ku.?"

Eh Alhaji munada dalili yarinya dai bata son Ahmad wannan shine dalili."
Aa Alhaji isiyaku ban tunanin Amina zataki Ahmad hakanan,bayan sun saba da juna."
"Hakane amman ga shaidar mu nan kagani.
Mikawa Baba wayar yayi yaga text iri iri na rashin mutunci da hauka duk naima Ahmad mamaki yagama kashe Baba.

Dan dole yafara basu hakuri dan ya gilgiza.
Bakomai Alhaji mudai da azo ayi aikin dana sani kwara mun hakura Allah ya hada kowa da rabon shi."

Ameen cewar Baba inaji yana kiran Ahmad aka fara dauko kayan sa ranar su daman ya hana kowa yataba komai a ciki har boot aka kai masu nidai ta window nike hangen su kana ganin Ahmad kasan yashiga damuwa har kwalla yake.

Nikam jikina na kyarma dan murna naima Ya Taufiq text nagaya mashi saijin dadi nike nasan yanzun nasamu damar auren masoyina nasan zuwa yanzun Abba zai yarda muyi aure.

Abin mamaki Baba na dawowa daga rakiyar iyayen Ahmad kirana yayi jikina na bari nazo dukawa nayi kallona yayi yana girgiza kai gami da murmushi wanda shi kadai yasan abinda yake nufi yace.

"Kin makara tashi Ahmad ya rakaki ki koma makaranta kuma kidage da karatu Allah yai maki albarka."
Ameen Baba."
Ina zumudi na mike na fiddo kayana natafi makaranta,wannan kenan.


******Bayan kwana biyu da fasa bikina da Ahmad,hankali yafara kwanciya duk da ba wani waya nike da ya Taufiq ba,itama Fatash har yanzun bata dawo ba,kuma itama din ba daukar kirana take ba,sai naji ba dadi.

Zaman kuraman da nikeyine yasa na mike nafara gyaramana kayan mu,ina cikin aiki naga kiran Fatash wani irin dadi naji ya mamaye ni,da sauri na daga bakina dauke da sallama.

Idan Ya Taufiq ya mutu saiki zuba ruwa kasa kisha Minal."
Dit ta kashe wayar a rikici na dinga kiranta taki dauka kiran Ya Tariq nayi yana dagawa naji muryan shi ta sauya hankalina ya tashi muryata na rawa nace.

"Yaya miyasamu Ya Taufiq.?"
Bai lafiya."
Inalillahi wa'inna ilahirraji'un,tun yaushe.?"
Kinga Amina ki kwantar da hankalin ki yaji sauki."

Can naji Fatash nacewa Aa yaya bawani yaji sauki duk karfin halin shi takai shi da karin ruwa ai inmuka rasa shi,hankalin ki saiya kwanta."

Wlh bahaka bane,amfasa bikina da Ahmad tun ranar na turo mashi sako.
Dan Allah Fatima kidaina yanke mani hukunci."

Mum kinji anfasa bikin Minal da Ahmad."
Eh nasani."
Mamaki sosai kowa yayi harni dake fatan inji muryar Ya Taufiq da alama wayar na speaker ne.
"Miyasa baki sanar mana ba.?"
Cewar Tariq.

"Ba anfanin hakan koda na gaya maku kowa yasan mahaifin ku bazai bari Hussein ya auri Aminatu ba niko banga dalilin da zaisa aita abu daya ba,nasama sarautar Allah ido a cikin lamarin nan Allah ya kyauta."
Kowa shiru yayi sai kukan da nike kasa kasa marar sauti,nima da haka na yanke kiran inajin ba dadi a cikin zuciya ta.


Bayan kwana biyu Fatima ta dawo makaranta,ba laifi ta saki jikinta dani,nima haka cikin kulawa na kalleta nace.

"Ya jikin ya Taufiq.?"

Nauyayyar ajiyar zuciya ta shide tace.
Uhmm Minal kin zama Qaddarar Ya Taufiq kullin kara sonki yake,da sauki tunda yau yaje company kwangila."
Sihirtattar ajiyar zuciya na shide.

Alhmdullah Fatash dan Allah kidaina juyaman baya kisani nima ina cikin wani irin hali na Qaddara tana tunkaroni ni kaina ina cikin taraddadi a raina,ina son Ya Taufiq kowa ya shaida."

hmmm kawata nasani amman kisani wlh Abba shine cikas wannan karan ma daya kara mashi zancen kinji yanda yaita gitta rai yana bai aurenki kuma Mami itace ke zugashi wannan matar batai ba wlh.!"

Toh Allah yai mana gata amman inaji a jikina Fatash Bakin Jinina Yajaman duk wannan abubuwan da nike fuskanta."
Ba wani bakin jini jarabawa ce kuma haka Allah yaso."
"Hakane kawata Allah yaimana jagoranci."
Ameen.
Nan mukayi shiru sai kuma tace.

Wai kin kai project topic dinki.?"
Aaa banyi ba,amman inasan innemo sai inkai aimam prove."

Aikam kinsan yan pharmacy har an masu nasu,mu kuwa grp project zamuyi."
Cewar Fatima.
Aiko kunji dadi saura mu kenan.
Labari mukai tayi duk kan project kowa yana kawo idea har yamma.



******_CARANCI_


Tunda aka fasa bikina da Ahmad sai yama didin yan unguwa ya ninku fiye dana baya ,kowa yana cewa ai yai bincike angano ni yar isakace shiyasa angon yace yafasa a ranar suka kwashe kayan su.

Wasu nacewa ai wani mai kudi nasamu shiyasa naki Ahmad saboda yafishi wadata
Kowa da abinda yake fada wasu naganin ai Jami'a tasa idanuna sun bude ban ganin kowa da kima shiyasa na raina iyayena har akafasa bikin.

Haka ɗumi yaita yawo cikin gari,har dumin yafara fusata Baba harya fara shawarar mubar garin baki daya,dan shi mutin ne wanda bai iya fushi ba zaman shi zai iya haddasa komai,amman Mum tai mashi waya ta hana shi zuwa ko'ina ba yanda ya iya dole ya hakura.

Yauma Anty Hafsat da kawar ta sukazo sai ba Mama labarin haushi take akan ɗumin da ake cikin gari,rai bace Mama tahau faɗa tana cewa.....




_Yar Matane Kankia ce❣️_



Share
Pls
❣️



*BAKIN JININA YAJAMAN😭*


*NA*

_Yar Mutan Kankia❣️_

*_TRUE LIFE STORY!_*

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

_*DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI.*_


S2/E43&44



"Kin isheni Anty Hafsat wai Aminatu ba Allah ya halicce taba,kuma shi ya tsara mata yanda zatayi rayuwa,waike miyasa kika tsani Amina ne,kifito fili kice baki kaunata nida zuriya ta,bawai kina wannan maganganun ba!"

Lallai Khadija kin isa nikikewa masifa akan yarki ke har kinsan dadin ya'ya kenan ko?ai bani na kashe zomon ba rataya aka bani kuma inba tarin bakin jini dake dawainiya da yar taki ba,mike damunta,malama kiyi biyayya abaki maganin farin jini.
kwananan zakiji bikin su Aisha kanne sai aure suke suna barin ta zaune a gida tsabar bakin jini irin nata.!"

Mama tagama kulewa tace.
"Naji Bakin Jinin ta yaza mata ke mai farin jini kirike abinki bani bukatar kosai a bakin ɗan garuwa,wlh kin kaini bango kuma Amina zatayi aure da yardar Allah."


"To ai tayi auren mugani a haka za'aita sa rana ana kwancewa sai kuyita rashin arzikin ku."

Mama kamar tayi kuka haka takeji aranta tace.

"Aikuwa zaki gani Hafsat indai auren Amina ne insha Allah komai lokacine,kuma komai yana tafiya yanda Allah yaso karki manta da wannan,sannan indai kunsan maganar nan zata kawoku gidana kufita bansan zancen banza."
Cewar Baba ranshi yagama sosuwa.
"Kaima Yusuf kabiyema matar taka daman taya zakuso zancen banza kunkai yarinya Jami'a ta gantalle tagama lalacewa dole zakuce haka,Allah ya tsareni inkai ya'ta Jami'a."

Ameen dan baki yarda da ya'yan naki bane,shiyasa kike cewa haka niko Yusuf na yarda da ya'ta ko karshen duniya be zan iya kai Aminatu ta nemi ilimi dan haka maza barman gidana"
Fita sukai sunata sababi da zage zage.

Hakuri Mama tafara ba Baba dan bataji dadiba da yaga abubuwan da yayar ta keyi daman bata taba gaya mashi sai yanzun daya ganema idanun shi.
Bakomai yace ya shige dakin shi.


*Noted:-* ```abinda mutane ke jahilta kenan a wannan zamanin da yawa mutane naganin Jami'a itace ke lalata masu tarbiyar yara kuma ba haka bane hausawa nacewa kowane tsuntsu kukan gidan su ya sani kedai uwa dage kibawa yar ki tarbiya saiki barma Allah ikon shi,Allah yasa mutane su gane dan yarinya tayi Jami'a bashi ke nuna ta zama gantalalla yar iska ba,shiriya ta Allah,Allah yasa mudace```



Bayan kwana biyu komai ya lafa ba laifi mundawo yin waya da Ya Taufiq saidai nice nakasa sakewa dashi sai nike ganin kamar yana mani kallan mayaudariya shiko bai nuna mani komai,soyayyar mu,mukeyi duk da nasan Abba ya hanashi aurena amman bai nuna mani ba kullin karamani kwarin guiwa yake

Please Login or Register in order to submit comment