Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawai na tsinci kaina da kasa bata amsar tambayartata,komai yasa oho.
"Shin dolene sai kaje,kasan fah babu kyau hakan bai dace ba,inda zakaje ka tarwatsa suma sunada iyalai,ko ya kabamu zai ishemu basai ka ɗebo da yawa ba wanda ba naka ba"
Matsawa kusada ita nayi na miƙa mata makullin hannuna,har a zuciyata nasan zancenta gaskiya ne,amma bashine abinda zuciyata takeso ba.
"Ki kulada inna,akwai number Tunga a ciki,ki ƙirashi in kuna son wani abun,aikin dazanje wannan karon yanada hatsari,dan haka idan ban dawo ba harkika gama karatunki,to kiyi rayuwarki yadda ya dace tun farko takasance"
Hannuna naji ta riƙe tareda makullin,jijjiga kai take wannan karon ta kasa cewa komai,shin yaushe kusanci yashiga tsakanina da itah bansani ba..
Zare hannuna nayi tareda yin hanyar waje ina saƙale da zakata. Can ƙasa ƙasa najiyo ƙaramar muryarta ina shirin fita daga gidan.
"Ka kulada kanka,zamu jiraka harka dawo"
Runtse idona nayi,bantaba jin irin wannan yanayin idan zan bar gidaba sai yau,wanne irin abune yake shirin faruwa danine. Koma menene kawar dashi nayi na maida hankalina ga aikin dayake gabana,wannan ne aikina na ƙarshe daga nan zan zama shugaba a bangarena,zasu bani kayan aiki da komai danake buƙata.
Kaman koyaushe baƙar motar da take ɗaukata ce ta tsayah,ina shiga kuwa taja zuwa cikin dajin.
Kwananmu uku muna training da shirye shiryen yanda wanann harin zai kasance,tun daga sannan na gane wannan dabanne da sauran aikin danayi da ƙungiyar.
Sai a kwana na ukun aka taramu domin faɗamana abinda zamu je yi.Kuma yauɗinne zamu tafi.
Mu tarane kaman yanda suka faɗa a tsakiyar filin.
Don 2 Ne a zauna kan kujera,kaman koyaushe sanye yake da suit baƙaƙe,yafara manyanta amma kana ganinsa kaga tantiri,ya runa gashin kansa gefe gefe fari,sai tsakiyar kuma ja.
"Barka da wannan lokaci ya gwarazan jarumanmu,a yau zamu faɗamuku menene abin harinmu a wannan aikin,sannan in mun gama bayani zaku hau jirgi zuwa babban sansaninmu na garin abuja.
Munason Sace Bayanan Nuclear da za'a kawo ƙasarnan a ranar 23 ga watannan,wato nanda sati biyu kenan.Wannan kundin yanada matuƙar muhimmanci,kuma za'a kawoshi cikin tsaro sosai. Zaku sake samun horo a wajen babban member ɗinmu na can,shine mai kulada harkar hacking da gano mai ke Iya zuwa ya dawo. Kuma shine zaija ragamar shirin a can,ku naku aikin shine abin abinda yace.
Ina fatan kun fahimta"
Dukka a tare aka bashi amsa bandani,dan haka kawai bansan meyasa ba yake bani haushi,kuma nake jinsa kaman na sanshi.
"Wannan aikin yanada hatsarin gaske,wanda ya samu nasarar dawowa za'a bashi maƙudan kuɗaɗe,sannan a lokacinne zaku haɗu da Don1 kafin kuma shugaban ƙungiyar,wannan shugabana ne zai faɗamuku mai zakuyi ya haɗaku da shugaban wannan ƙungiyar"
Hmmm dama nasan za'a rina,aikin gamu kashemu zasu turamu,bakomai dama kasada gaba muka bata ba bayaba,sannan zuciyata bata rayamin tsayawa daga haka tunda na riga na fara.
Ƙarar sauƙar helicoper muka faraji,hakan yasa muka shirya domin tafiyah.


Layi muka yi zuwa wajen jirage guda biyu wanda suke ta diri,toh satar ma a jirgi za'a je kenan,kai kaga sata mai aji.
Announcement aka fara bayarwa bayan mun shiga cikin jirgin.
"Daga nan zamu tafi secret domain ne dayake cikin abuja,anan zamu zauna na tsawon sati guda mu Shirya komai kafin target ɗinmu ya iso"
Yana gama faɗan hakan aka rufe ƙofar jirgin muka tashi sama,belt naja na saka a kunkumina,abinne yabani mamaki,taya akayi nasan inda belt ɗin yake,sannan na gefena sai diriricewa suke suna rirriƙe duk inda hannunsu yakai lokacin da jirgin zai tashi,amma ni banji komai ba,ji nake kaman na saba ma da shiga jirgin,mai yake faruwa ne?.
Tafiyah muke tayi a saman,har muka iso inda jirgin zai sauƙa.wani gidane daga waje iya rufune,amma muna shiga naga ashe a can ƙasa aka yi ginin.
Wajen ya ƙawatu matuƙa,idan ba naga lokacin da muka shigo ba,bazan taba yarda cewar a ƙasa wajen yake ba,gashi tarau tarau duk da hasken da wajen yayi kaman da rana.
Dukkanmu kowa ɗakinsa daban aka bashi da kuma duk wasu abubuwa dazai buƙata,sanann duk safiya zamu dunga fitah training da yanda zamu tsira idan jamian tsaro sun taremu. Nidai banajin abinda suke cewa ina sai zuwa gobe,tunda suka nunamin ɗakina nashiga nayi wanka,wai goje zayyi wankan arziƙi kenan bana sabulu ɗan yanka ba.
Nafaɗa a raina ina murmushi,tsuke fuska nayi tareda ɗan ja da baya a gaban madubin ina kallon fuskata,wai ba dole ma a dunga gudu idan an ganni,haka Sumaimah take kallona ashe??.
Kaya Nagani a cikin ƙaramar drawer,bayan nasaka ina fitowa naga dukka sauran suma irin nawane kayansu.
Bayani aka farayi yanda tsarin sace abun zai kasance,sai koyon harbi da kuma juriya. Shi mukayi ta koya har ranar 23 ga watan tazo ta.
Tofah abin yazo inji mai tsoron wanka,cikin daren yau zamu kai farmaki babban gidan tsaron a nan abujan mu ɗauko bayanan wanda yake a wajen da aka killace shi.
Bindigogi aka bamu manyan manya cikeda bullet ɗinsu,kai dolema wannan ƙungiyar tanada saka hannu wani babba,in ba haka ba taya zasu samu irin waɗannan makaman haka.
Ta wata ƙofa muka shiga ta sirri wacce tabi ta cikin ƙasa,har muka shiga cikin ginin a haka.
Nidai abinma kaman film haka naganshi.
Tafiyah muke babu wata matsala a nawa rukunin da nake ja har muka isa ɗakin da bayanan suke ciki.
An ce mana bayanai ne,amma ni ban yadda da hakan ba,in bayanai meyasa baza'a turo ta na'urar sadarwa ba. Sannan kuma abin yayi matuƙar bani mamaki,ganin har mukai ga ɗakin da akwatin yake amma kuma babu kowa a cikin ginin.
Hasalima ƙofar da abun yake a buɗe take.
Wani abokin tafiyarmu ne ya tafi gafa gafa zai ɗauki akwatin,har zan hanashi sai naji ɗakin yafara wata ƙara,wutar wajen takoma ja mai walwali,shikuma wanda yaje kusada akwatin dake shoking ya daskararshi..
Ƙarar taku na tahowar jami'an tsaro mukaji,ga ƙofar ta kulle baza'a fitaba saidai a shigo.
Munanan mutane da yawa cikin kaya na sojoji suka fara shigowa,suna harbi muma munayi,kafin wani lokaci anyi raga raga da ɗakin,sojojin da mutanen mu sun ji rauni wasu kuma sun mutu.
Idona ne ya kai kan akwatin,wanda a garin harbi aka jajjage na'urar rezar wajen.
Cikin zafin nama na fizgeshi nayi wani window da gudu,wajen kusan hawa uku ne,ina faɗawa nafara gudu,naji alamar faɗowar wani ya biyoni,duk da buguwar danayi amma bna tsayaba na cigaba da gudun.
Munyi ƴar tafiya kafin naji ya bangajeni. Akwatinne ya faɗi gefe muka fara faɗa nidashi,yanada ƙarfi sosai da alama sojane mai zafin nama.
Saidai nima na nunamasa nawa zafin damtsen,ganin nafara cin galaba akansa yasa nafara dan sararawa, Hular kansa na yage,saurayine fari,na shagala da kallon fuskartasa wacce takemin kamada ta wani naji wani zafi ya ziyarci cikina. A hankali nakai idona wajen,inda ya cokamin wata wuƙa a ciki,hakan bai isheshi ba saida ya jata yayimin mummunan rauni,dishi nake gani a haka ya samu nasarar cire min nima hulata,zaro ido kawai naga yayi yana shirin magana,kafin yace wani abun wata mata sanye da baƙaƙen kaya ta buga masa ƙasan bindiga akansa. Tare ni dashi muka zube a wajen,na saddakar tawa ta ƙare kawai. Ina jin lokacin da jinina yake fita daga jikina.
Buɗe idona nayi naganni a cikin wani kogo wanda yayimin kama da wanda nasani,wato na garinmu.
To waye ya kawoni nan wajen? Nayiwa kaina wannan tambayar.Yunƙurawa nayi zan tashi,wani azababben raɗaɗi ya jiyarci inda sojan ya soka min wuƙa. Kai sai yanzu ma na tuna kenan komai ya faru a gaske kenan.
Idona nakai kan cikinnawa wanda aka naɗeminshi da farin bandeji,gefe kuma audugane wanda akayi ta goge jinin wajen.
Koƙartawa nayi na zauna ina haki na wahala,wata takarda nagani na gefena an naɗeta an ajiye.
Ɗauka nayi duk da dishi dishin danake gani nafara karantawa.

.....Nasan zakayi mamakin ganin kana abuja amma lokaci guda ka dawo garinku,nice na kawoka,amma ba lallai sai kasan ni wacece ba,duk da niɗin nasanka......kayi ƙoƙarin komawa gidanka kayi jinya ka warke,ta hakane zaka samu damar kulada wannan akwatin da kayi nasarar ɗaukowa,shiɗin abune mai muhimmanci ga ƙasarka da kai kanka a matsayinka na.........
Wajen bai ƙarisa karantuwa ba ta yage shi,da alama wacce ta rubuta ɗin ta faɗi matsayina,amma kuma saita sanja shawara ta yage wajen.
Waiwayawa nayi da idon inda akwatin yake.Ban mantaba shine wanda nake shirin saida raina akansa.
A kwance nake ina tunani,na,rasama mai zanyi.
Cikin dauriyah na miƙe tsaye,hannu nasaka na ɗauki akwatin,amma ko kaɗan na gagara ƙara ko taku ɗaya daga wanda nayi.
Komawa nayi na zauna,wata dabara ce ta faɗomin. Rigata na fara lalumewa,anan naga wayata a cikin kayannawa,number Tunga nayi ta ƙira amma a kashe,tun inayi harna gaji.
Number Sumaimah na ƙira,tana ringing amma ba'a ɗagawa,saida nayi kaman sau uku kafinnaji ta ɗaga.
Shin meyasa na nemeta a ɗaya daga cikin waɗanda zasu taimakeni lokacin danake neman taimako? Koma dai menene naji daɗi dana sametan.




Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan
09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan
09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please*SANADIN CACA*


Mallakar SADI-SAKHNA


PROFICIENT WRITER ASSOCIATION



*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[26]


[Sumaimah a mahangar gani]

A galabice na shigo gidan,na dawo daga makaranta,kai neman ilimi kam akwai wuyah.
Uniform na fara cirewa sai naji wayar da goje tabani tana ƙara,tunda ya tafi bai taba ƙiraba,iyah Tunga kawai na taba ƙira yakawo mana kananzir.
Ɗauka nayi naga two missed call,goje?? Ni nayi zaton Tunga ne ma ya ƙira.
Tunda ya tafi hadda cewa sati biyu zayyi,abu ana shirin yin wata amma bai dawo,mai kuma zai ƙira yace. Dama yana raye kalau kenan.
Ɗagawa nayi tareda yin sallama a hankali,yanayin dana ji muryarsa ne yasakani maida hankali kan abin zai ce,idan ba kunnena ne ya samu matsala ba toh nishi naji yana yi.
"Hello Sumaimah kin....ajinahh?"
"Ehh ina jinka mai yasameka,wata matsalarce ta faru?"
"Kinga ki tsaya ki saurareni,kinsan wannann dutsen mai kogo na bayan gari?"
"Ehh ....eh nasani"
"Toh kizo ki sameni a wajen,ki tahomin da abinci da kuma kaya,yawwa sannan ki je chemist zan turo miki sunan wasu magunguna ki tahomin dasu,sannan karki sanar da inna komai"
Daga haka ya kashe wayar,wani bugawa kirjina yayi,yayinda kaina yafara lissafomin abubuwa da dama,shin mai ya sameshi yake cikin kogo,shida yayi tafiya..
Kayan na cire a gurguje na nufi inda abincin mu yake. Ɗiba nayi a kula na saka a kwando da,hijabi na zura na fita daga gidan da sauri..
Akan hanya chemist ɗin yake,magungunan daya faɗamin nasiya,harda auduga,plaster da kuma bandaji acikin abinda ya turo ɗin, ciwo yaji,shine abinda yafara zuwa kaina lokacin dana siya abubuwan.
Pure water na siyah a ɗaya shagon,daga nan na nufi inda yayi min kwatance.
Da ɗan tazara wajen da cikin gari,dan haka saida na taka kafin na isa..
Ina shiga wajen na sameshi a kwance akan kayansa,gefensa kuma akwatine da tarin auduga duk jini a jikinsu,idonsa a rufe yake yana kallon saman kogon,inda bashi yayi kwatance ba zan iya cewa bashine bane,don babu wannan gashin fuskar dana sanshi dashi,sannan yayi fari ya rame kaman bashi ba..
Numfashi yake fitarwa hankali ma wahala. Ban lokacin dana isa wajensa ba da sauri,bayan na ajiye kwandon danazo dashi..
Tsugunnawa nayi a gabansa ina ƙare masa Kallo,fuskata ɗauke da damuwa ƙarara,na tunanin shin wanne irin mummunan abune yasameshi haka,sannan kuma yaushe?
Buɗe shanyayyun idanuwansa yayi ya ɗora akaina masu kama dana majinyaci.
Nima kallonnasa nake da nawa idanuwan wanda suka cika da ƙwallah,fatar bakina nakeson na buɗe nayi masa tambaya,amma sai rawa suke sun kasa bani haɗin kai.
Hannunsa ya ɗakko zai kawo wajen fuskata,amma abinka da dama tsoronsa nake,saina ɗan ja da baya.
Murmushi yayi tareda rufe ido a hankali yakuma buɗewa,dimple ne ya lotsa a gefen kumatunsa,dama yanada wannan abin a fuskarsa,amma ba wanda yasani saboda gashin fuskarsa,yanzu daya aske sainaga kaman wani mutum daban aka ajiyemin. Ashe farace fuskartasa kamar jikinsa,saidai bakinsa yayi duhu bakaman sauran fatar jikinsa ba,saboda shaye shayen dayake.
"Duk da ina cikin wannan halin amma tsorona kikeji,shin mai zan iya yimiki a yanayin danake uhm?"
Tari ya fara yana runtse ido,ban san lokacin dana tallafo kansa zuwa jikina,dama gani Allah yayini banson naga mutum a halin jinya. Bare irin wannan,tsayawa yayi da tarin tareda saqala hannayensa ya riƙo kunkumina gam,wanda nasan ciwon dayake jine yasakashi yin hakan,a nanne nima na kulada bandejin dayake cikinsa wanda yayi jajur dashi da jini.
"Sannu sannu,wayyo please ka tsaya barinaje na ƙira mai chemist ɗinnan,wataƙila zasu iya taimakawa"
Ƙoƙarin zare jikina nayi domin na tafi,amma sai naji yasake ƙanƙameni sosai.. Magana yafara cikin gajiyayyar murya.
"Ahahh kada ki ƙiramin kowa,banason kowa yasan halinda nake ciki....kin kawomin abinda na buƙata?"
"Ehh dukka na taho dasu"
"Uhm barina dashi ki gyaramin wajen,jikina ba ƙarfi bazan iya dakai na ba"
"Niiii ban ban....iya ba bazan iya gyara wannan ciwon ba"
"Uhmm zaki iyah mana ko baki iya ba zannunamiki yanda zakiyi,ba wani abune mai wuya ba,taya zaki ƙira kanki matar goje idan kina tsoro uhmm?"
Nidai kurmiya na koma da zancennasa. Saboda kallonsa nake kaman bashi ba.
Tallafah masa nayi ya jingina da jikin dutsen,jikinsa har rawa yakeyi saboda zafin ciwo.
A hakan kuma yasaka hannu ya sunce ɗaurin ciwon,wanda matar data kawoshi wajen tayi masa.
Lokacin da yagama suncewar saida na rufe idona saboda yanda wajen yayi jawur kaman ɗanyen nama.
"Ohh bazaki iya gani ba,taya kuma zaki iya wankemin idan kika kasa gani?"
"Ya akayi ka samu wannan ciwon haka,a wajen satar ne koh"
Nafaɗa cikeda jin haushin yana satar,koda yake yaudarar kaina nake,zaman danayi dashine a wannan watannin nafara manta waye shi.
"Uhm a wajenne wani soja ya soka min wuƙa,ina faɗuwa dana bude ido nasamu kaina a wajennan tareda abinda muka je sata ɗin. Sannan ba sata ce wacce kika sani ba,abune na sirri da mutanena ma basu sani ba,shiyasa nace miki kada ki faɗawa kowa ina wajennan ,saidai in yayi yawane ki faɗawa Tunga kinji"
Ɗaga kaina nayi tareda fitowa masa da abubuwan dayace na kawoɗin,naga yanda yake maganar na fahimci lamarin mai tsaurine.
Kaman yanda yafaɗa shine yake nunamin yanda zanyi har muka gama rufe ciwonnasa,gumi kuwa ya haɗashi shirkif saboda wahala.
"Gashi sai wahala kakeji,da baka jeba da haka bata faruba"
"Uhm to hakane,amma ni nasamu da sauƙima,tunda abokan aikina kusan duk sun mutu,wanda sukeda rai ma suna hannun ƴan sanda. Wannan akwatin in zaki tafi gida ki tafi dashi ki boyemin,zan kaiwa ƙungiya idan na warke"
"Kace tacemaka yanada muhimmanci,amma meyasa zaka kaiwa barayi,bayan kasan hakan yanada hatsari,dan Allah karka sake komawa wajensu,duk da cewar kaima........uhm ....amma dai kafisu kasaka hakan a ransu"
"Me kikeson fada kika fasa,nima bana kirki bane koh?"
"Ahah nidai bance ba amma dan Allah karka koma,inna bataso"
Hannunsa yasaka na dama ya ballamin akan goshina,nima sai a sannan nakulada yanda na zage inata surutu.."
"Ya karatunki,daga gani dawowarki kenan bakici abinci ba..ɗebomin naji ko zan iya ci"
Ɗan murmushi nayi ina shafa goshinnawa,kafin na ɗebo abincin. Miƙamasa plate ɗin nayi amma naga ya kafeni da ido yaƙi ƙarba..
Har na fara tunanin ko bayason jallof ɗin taliyar,saikuma naga ya buɗemin baki,wato so yake na ciyar dashi kenan.
Ɗiba nayi a cokalin cikeda kunya nakai bakinsa,ba kunya kuwa shi ya karba yafara ci. Shuru wajen yayi sai numfashinmu kawai,baici da yawa ba ya min alamar ya ƙoshi.
"Naƙoshi bani ruwa,sannan ki cinye sauran,dan naga yunwa kikeji"
Ikon Allah tun ɗazu yake cewa yunwa nakeji,yaushe yafara kulada ni haka?.
Maganin dana taho dasu na miƙa masa ya balla,kafin na bashi ruwa ya kora dasu.
Bayan mun gama cin abincin alwala nayi na sallahr la'asar nazo na shimfiɗa ɗankwalina,yana kallona harna idar da sallahr,Addu'o'i nayi kafin na juyo na kalleshi..
"Amma tsawon wannne lokaci kayi a kwance"
Ɗaga min kafaɗa yayi tareda cewa.
"Bansani ba,kawai dai abinda nasani shine ranar 23 ga watana march ne aka sokeni da wuƙa"
Zaro ido nayi tareda rarrafowa kusada shi,kenan satinsa guda a sume?
"Sati guda kenan kayi a kwance,dan yau talatinne ga wata"
"Uhm zai iya yiyuwa,kuma da alama wadda takawoni nan wajen har asibiti suka kawoni"
Yafaɗa yana nunamin hannunsa,inda aka saka masa canular,kaman ma yau aka cireta a jikinsa,kuma wajen akwai takun sawun takalmin mace,harda robobin lemo da ledar cakes.
"Amma wacece haka in tana cikin tawagarku meyasa ta ajiye maka akwatinnan,inaga bataso ka kaiwa kungiyar nan taku"
Dan haka kawai naji banaso ya koma wajensu.
"Hhhhh da alama bakyaso na koma aikina,amma ke ruwanki ne,dan kinga bana iya komai shiyasa har umarni kike bani ko"
"Ahah ba haka bane kayi haƙuri"
Koƙarin tashi nake shirinyi daga wajen,sai kuma naga ya kamo hannuna gam ya riƙe,idonsa ya rufe yana jijjiga kan cikin sauri.
"Ciwon kaina wayyo kaina yana shirin tsagewa ahhhh,bansha wiwi ba,kibani wiwi ɗina......."
Tambayata yake,amma da alama kuma badani yakeba,sambatune kawai na ciwo.
Hannayena na saka a gefe da gefen kannasa na riƙe,Addu'o'i nafara karantowa na neman sauƙi,hannunsa yasaka yana ƙoƙarin ture hannuna,tareda ƙara sautin ƙarar dayakeyi. Yayinda nikuma na riƙe gamm na dawo yi ma a fili,kasancewar jikinsa babu alamar ƙarfi yasa ya kasa ture hannunnawa.
Can bayan kaman wasu mintuna naga yatsaya da jijjiga kan,ina dubawa naga yafara bacci daga zaunen,gyara shimfiɗin danaga anyi masa da kayansa nayi,tareda kwantar dashi a wajen.
Tashi nayi na tsaya ina kallonsa,daga yanda yake maganar kaman daman ya san da ciwon kan kuma ya daɗe yanayi.
Dannima na sha ganinsa a ɗakinsa ya riƙe kai,kenan shiyasa yake shaye shayen. Har yanzu na gagara fahimtar sa,kowacce rana sainaga wani abu sabo dan gane dashi.
Kayan abincin na ɗauka domin komawa gida,zanje na dawo kada inna inna taka bananan.
Karare na gona na ɗakko nayi ta jerawa saida na rufe wajen tass kafin na tafi.
Ina shiga gidan muka haɗa ido da inna,tun kafin nayi magana ta jefomin tambaya..
"Kekuma daga ina haka kikadawo,ɗazu naji motsinki ina tashikuma na bakyanan"
To anan gizo yake saƙar ,shin mai zan faɗawa inna,gashi yace kada na kuskura tasani.Wata dabara ce ta faɗomin.
"Umm uhm inna dama wata ƴar ajinmu ce a islamiyya batada lafiyah,kuma ba ƴar garinnan bace zuwa sukayi,shine to na kai mata abinci.....sannan inaso na zauna mata kafin ta warke,tunda bakowa wajenta"
"To ikon Allah,dama rashinnaka a garinnan ba daɗi,kin kyauta sosai saki faɗawa shi mijinnaki a waya"
"Ehh na tura masa message yace ba matsala,yace yana gaisheki ma wajen aikinnasu ne ba a kiran waya ne"
"To shikenan ba matsala ina amsawa,zan shiga anguwa anyi matar ɗan marka ta haihu"
"To saikin dawo inna a gaisheta"
Daga nan tabar zancen,dan dama ita macece da bata matsamaka sai tasan mai kake,musamman idan tasan abu kake boye mata.
Kuɗin na ɗauka a cikin wanda Tunga ya kawomana. Kasuwa na tafi na siyo hanta da kuma alayyahu,dama duk wani abunda nake buƙata.
Farfesunta nayi masa da ɗan romo na juye a kula,saikuma shayi dana haɗa na zuba a flask.
Wanka nayi lokacin rana ta kusa faɗuwa.
Pillow na ɗauka da sallaya sai butah,a cikin jakar da aka kawomana kayannan na saka su,saikuma kwandon kayan abincin.
Lokacin dana ɗauki hanyar wajen ba sawun mutane sosai,Allah ya taimakeni dana ɗebi ƴan kallo an ganni da kaya nayi bayan gari.
Yanda na rufe wajen haka naje na sameshi,saida na ture kararen kafin na shiga.
A kwance yake yanda na tafi na barshi yanata bacci,da alama maganin dayasha akwai mai saka bacci a ciki.
Ban tsasheshi ba,dana ajiye kayan hannuna wajen na fara gyarawa. Na ɗebe dattin da wanda suka kawoshi wajen suka zubar,da kuma audugar da sukayi ta goge ciwon dasu,harda wanda muka cire muma ɗazu.
Shimfiɗa sallayar nayi gefe,kasancewar wajen rairayine,awakin mutanene masu kwana a jeji suke shiga wajen da daddare,kokuma almajirai idan suka iyo itace su tsaya su huta.





Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan
09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan
09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please*SANADIN CACA*


Mallakar SADI-SAKHNA


PROFICIENT WRITER ASSOCIATION



*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[27]



Basan ya tashi ba saida naji maganarsa tukunna.
"Yaushe kika dawo?"
Cikin magagin bacci yake maganar.
"Uhm ban daɗe ba sosai,sannu ya jikinnaka"
"Da sauƙi kawai zance,miƙomin ruwa nasha,bakina bushewa yakeyi akai akai"
Ruwan na ɗauko na bashi,lokaci guda ya zuqe guda biyu,Wannan wanne irin shan ruwane haka,na faɗa a raina.
"Ga abinci yakamata kaci"
"Mts banajin yunwa, bar abinci nan,ki ƙiramin Tunga kice ya kawomin ajiyata danayi a jeji"
"Ba abinci bane haka,nayine saboda ina tunanin ko jikinka yana buƙata,sannan a halinda kake ciki bai kamata ka zauna da yunwa ba"
Ganin bai sake cemin komai bane yasa na jawo kular dana zo da itan,farfesun hantar na tura masa gabansa,na manta banzo da plate ba..
Matsawa kusada shi nayi ina bashi a baki,daga yanda yake karba ma tabbatar yanayimasa daɗi sosai,dan saida ya kusa cinyeshi tass.
Kofi na ɗakko bayan yagama na zuba masa shayi shima mai zafi.
"Yaushe kika waɗannan abubuwan haka?"
"Lokacin dana koma gidane,saidai kayi haƙuri na fita zuwa kasuwa da kaina,dama inason na faɗamaka saikuma na manta."
"Uhm bakomai nagode da kulawarki,bani maganin can nasake sha naga har dare yafara"
Bayan na miƙomasa yasha ruwa na zuba a buta nima nayi alwala nai sallahr magriba,kaman ɗazu yana kallona har na gama.
Sake zuba wani ruwan nayi nazo inda yake,kallon tambaya yakemin ganin na miƙamasa hannu yabani nasa hannun.
"Kawo hannunka alwala zanyi maka,yakamata ka rama sallolin da ake binka,tunda ka ɗan samu sauƙi"
"Taya kike tunanin zan iya sallah a haka?"
"Indai kana cikin hankalinka to zaka iya yin sallah,domin a kowanne yanayi mutum yake ba'a ɗauke masa sallah,saidai idan baya cikin hankalinsa. Ance idan bazaka iya a tsaye ba ka jingina,in shima bazayyi ba ka zauna,in ya gagara ka kwanta ka kalli gabas,in shima bazayyiyu ba toh zaka iya yi a duk yanda ka tsinci kanka.
To haka ma wajen yin alwala,in jikinka bazai ɗauki ruwa ba saikayi taimama da ƙasa,idan itama bazaka iya da ita ba to saika shafi jikin gini mai tsarki kayi dashi.
Toh a wannan bayanin kaga kai zaka iya yin alwala kuma kayi sallah a zaune"
Bayan gama bayanin bai ce komai ba,amma ya miƙomin hannayensa na fara yimasa alwalar. Cikin nutsuwa nake yimasa alwalar har na gama tsaff.
Rigar dana zo da itah na taimaka masa yasaka,yanda bazata shafi ciwon ba,kafin na juyashi ya kalli gabass,magriba yafarayi wacce ake binsa kafin ya fara da rama sallahr asuba tun sanda aka jimasa ciwo.
Daki daki yake bin sallahr ina zaune ina kallonsa,daga baya daya gaji sai na koma ta baynasa ina tallafamasa. Muna daɗe a haka har akayi sallahr isha ya tsaya da ramakon yayi,ganin yana haki yagaji yasa ya tsaya dayi sai ya huta tukunna.
A bayansa nake ya jingina dani,saiji nayi ya kwanto akan cinyata,kallon fuskata yakeyi,yayinda nima na sunkuya ina kallonnasa,mun daɗe a haka idonmu a sarƙafe dana juna,saida naji hannunsa akan fuskata kafin na dawo zahiri..
Magana yafara a cikin wata murya da banyi tunanin yanada itaba.
"A ɗan zamana dake kin taka wata rawa a rayuwata,ko yaushe cikin juyewa kike da narasa taya zan misaltashi. A lokacin danake son naga kin sake dani saiki ɗankware jikinki,lokacin danazo yimiki barazana kuma saiki dake,idan nayi laushi kuma sai zama jaruma,a yau kaɗai kinyimin abinda ban taba tunani ba,kin zamemin hannun a sanda na rasa nawa,kin zamemin ƙafa da tawa taƙi aiki,kin zauna dani a wannan dokar dajin da babu kowa a ciki saini kaɗai.
Tun farkon da mahaifinki yabani ke a matsayin fansar kuɗina naga rashin dacewarsa nayin hakan,shiyasa na nesanta kaina dake,a tunanina hakan zaisa kiyi rayuwarki yanda kikeso,naƙi shiga rayuwarki saboda nasan nida ke bamu dace ba ko kaɗan,amma sai naga duk wannan koƙarin danake yatafi a banza,ke koyaushe so kike ki cusa rayuwarki cikin tawa.
Wannan ƙasa da kan da kike idan kina gabana,da kuma neman izinina a duk wani lamari na rayuwarki shine yayi babban tasiri wajen karya zuciyata,har tasaka na ajiye komai na ɗauki nauyinki batareda nasani ba. Saboda tunda nake babu wanda yazo da kansa yanemi izinina akan abu,saidai na bashi dakaina in kika ɗauke Tunga.
Sannan tun kina zuwa inda nake ina jin kin takuramin,har yazamo idan banganki ba sai zuciyata tayi ta kewarki. Sumaimah bansan mai kikayimin a rayuwata ba amma dai shigarki kinyi nasarar share wani a fili a ciki kin mamayeshi yazamo naki. Ciwon kan dana tashi a rayuwata bansan lokacin dana faraba,bai taba dainawa ba indai ba shaye shaye nayi ba sai yau,kuma dama yakan tashi ne idan na bijirewa umarnin da zuciyata tabani,saikashi yau kin karanta min wani abu naji ya tafi batareda nasha komai ba"
Tunda yafara magana ban ɗauke idona ba daga kan fuskarsa,shin anya kuwa gojen danasanine yake waɗannan kalaman,meyasa yau ɗaya naga wata nutsuwa a tattare dashi,babu wannan zazzare idon da kuma cije cijen baki..wannan gashin daya maidashi dodo duk babu shi. Kar a ji haushina idan nace yayimin kyau fiyeda mutane dayawa a garinnamu.
Hannuna nasaka akan nasa wanda yake kan fuskata,tareda sakin wani murmushi da bansan ma'anarsa..
"Duk abinda kake faɗan nayi aikata a rayuwarka banice nabaka wannan matsayinba,Allah ne dakansa yabaka a matsayinka na mijina,ni kawai umarnin da aka bani na nayi maka biyayya,kada nayi wani abun batareda saninka ko kuma yardarka ba,sannan na kyautata maka na kasance sassanyar inuwar dazaka

Please Login or Register in order to submit comment