Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mubar gidanann,baba ma ki faɗamasa kar ya dawo gidannan mu tafi gida gaji,mu koma gida kawai"
"Ke dallah kimin bayanin mai yafaru ne wai,mai kikayiwa hajiyanne,naga ɗazu ta fita daga gidan ma bata nan"
"Eh ta tafi amma komai ta manta saita dawo,shine.....shine.... Tasameni nida alhaji akan gadonta toh. Toh saita yanki jiki tafaɗi,kuma dama tanada hawan jini.......wlh gaji inaga ta mutu,idan ta mutu wannan sojan ɗan uwannata bazai ƙyalemu ba sam,kizo mukoma gida wlh kafin su kashemu"
Sakin hannun Atika gaji tayi ta faɗa akan gado yaraff mai kunnenta yake jiyo mata haka.
"Atika mai kikace wai...hajiyah ta kamaki da mijinta a kan gadonta,idan ma iskanci zakiyi kiyi mana,amma taya daƙiƙancinki zaisa ki bari ta kamaku,ni ai mai farinciki ce idan har yaga yana sonki zai aureki,amma kafin komai ya tabbata shikenan kin zawo mana asarar wannan arziƙi da muka fara lasa. Taya kike ganin zasu barmu mu fita daga gidannan iyee batareda sun lahanta muba"
"Gaji bama wannnan ba,ƙanwarta wannan fatin itama ta ganmu,kuma shi sojan yana waje shiya dawo dasu ɗaukar wani abu a mota"

"Meeee kikkka ceeee shikkenan tafaru ta ƙare,wlh bazan faɗawa malam ba,dolene shima ya dawo ya karbi nasa luguden,ban isa shansa nikaɗai ba aradu. Ke kuma bari a gama yimana na nan kema mu tsira na baki naki...........


Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan
09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION


*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[05]


Ture atika gaji tayi daga bakin ƙofar ɗakin tana leƙawa,cikin ƙanƙanin lokaci ta haɗa gumi shirkif,banda zagin ƴar tata babu abinda take na aika aikar data jawo musu.
A kan idonta sojan ya fito da hajiya a hannunsa,fati tana binsu tana kuka,shikuma mai gidan ya biyosu cikeda kunya da sanyin jiki.
Har sunzo fita daga gidan wasu sojoji guda biyu suka iso bakin ƙofar gidan,magana suke da ƙanin hajiyan na wani lokaci kafin suka fita daga gidan a mota.
Shima alhajin mota ya ɗauka yabisu a baya.
Kenan gadinsu zayyi kada su fita a gidan komai.
Duk abinda yafaru akan idon gaji itada atika,a tunaninsu idan suka bar gidan suma zasu fice,saidai da alama ba haka bane,dan sojojin a bakin ƙofar gidan suka tsaya suna jajjagawa.
Suna cikin haka har yamma tayi liƙis hankalinsu ya gagara kwanciyah,ba halinda matar gidanne ya damesu ba illah su halin dazasu shiga.
"Hmmm mlm audu har yanzu bai dawo ba,kaddai yasan mai yafaru ya gudu ya barmu a ciki,tukunna ma mai yasa zasu hanamu fita toh daga gidan"
Kallon uwar tata atika tayi tareda cewa.
"Yanzu haka fatinnan ce tafaɗawa sojojinnan karsu barmu mu fita,dan daman tun a ɗakin ɗazu tace saita ɗaiɗaita rayuwata nida iyayena,dama ta tsaneni"
"Laaahaulah wala ƙuwwata shik........"
Bata gama salatin ba aka banko ƙofah,Fati ce firiri da ita,gyalene a jikinta hannunta ɗauke da key ɗin mota tana jijjigashi,cikeda tsiwa takalli gaji tareda cewa.
"Kar kiyi salati yanzu,ki bari saikinga kina hango wuta kafin sannnan zaki fara salati.
Don ku fito dasu daga ɗakin zuwa filin gidan"
Tana gama faɗin hakan tafita daga ɗakin,wasu murtuƙa murtuƙan mutane guda biyu suka fito da gaji itada atika zuwa filin gidan.
"Dan Allah kayi a hankali karka karya min allon kafaɗa,kaga ƙashin na tsufah ne"
Gaji ta faɗa tana sallalami.
Zubasu akayi a filin wajen da sanyi la'asar.
"Don kuyi musu horo wanda zai jirgita kamanninsu nan da zuwa gobe kada su runtsa idonsu,matsiyata macuta kawai,wato duk abinda anty Abida tayi muku da haka zaku saka mata,kin tura ƴar ki tana cin amanarta,idan kuka kasheta saiku aureshi ku mallakeshi,ku a dole kunga gida. Yau kuwa zaku yi danasanin shigowa garinnan ma ba gidannan ba"
Tana gama maganar kaman jira suke suka hau su gaji da duka ta ko ina babu tsayawa. Tun suna ganin farar wuta har ja tafara haska musu a idonsu.
Ƙarar buga get ne hasasu tsayawa da dukan domin suga wanene,fati ce ta taka fiƙi fiƙi zuwa bakin get ɗin.
Da Mlm Audu suka haɗa ido,hannunsa riƙe dana ɗansa na mijin ƙarami,sauran mata guda uku kuma ƙannen atika suna biye dashi a baya,kayan makaranta ne a jikinsu wacce hajiyan ta sakasu wata biyu dasuka wuce.
Killer smile fati tasake masa tareda cewa.
"Ahh mlm audu ka dawone to sannunka da zuwa shigomana ciki"
Abin yayi masa bambarakwai,danshi dai yasan wannan yarinyar ba kulashi take ba,baidai ce komai ba yayi ta maza yashiga gidan.
Dama wai suna ne yana gadi,tun safe fice sai ya wuni bai dawo ba,yanacan wajen sharholiyarsa,banda gadin ma menene wane aiki zai iya,ko noma ƙaramar gona kasa nomawa yake a shekara.
Da gaji yafara haɗa ido tayi gurfano kaman mai karbar gafara,hancinta da bakinta sunyi dama dama da yawu da jini da majina.
Zaro ido yayi yana shirin fita waje da gudu wani soja ya kamoshi ramm ta rigarsa ta baya.
"Malam ina kuma zakaje,maimakon ka tsaya ka cecemu wato guda kake shirin yi koh,saikazo duk mu haɗu muyi karbi azabar tare,tunda kaima yar kace ba iya ni kaɗai ba"
Bayan gaji ta gama bayanin da dashshshiyar muryarta,fati ce ta ɗora ta bashi labarin abinda atikan tayi.
"Yanzu kaima saika jona su,shima ku haɗashi don"
Aikuwa buɗar bakinsa yace.
"Yallabai wannan labarin da madam ta bayar banida masaniya akan sa,saina wuni bana gidanann bansan mai ake kitswa,dan Allah ku barni na tafi da sauran ƴaƴan"
"Baaba ya zakace haka,wlh kasan abinda yake tsakanina da Alhaji,naga kasha kamamu cikin dare,idan kafara magana sai ya baka dubu goma kayi shuru,daga baya kamma dayace maka aure na zayyi na zama matar gidannan har murna kayi,kake cemin nayi ƙoƙari da dabara na mallakeshi a tafin hannuna,wai har na samu na fitar da anty Abida a gidannan"
Kowa a wajen zaro ido yayi da bayanin atikan,ciki kuwa harda gaji,ita nata baƙincikin ɗaya yanda ake bashi kuɗi duk dare batada masaniyah.
Fati itada sojijinta basu suka bar su gaji ba sai dare,hakan ma suka gamasu da karnukan su suyita binsu da gudu har gari ya waye,kafin asuba duk sun suma babu inda yake aiki a jikinsu.

__***__

[Sumaimah a mahangar gani]

Yau da wuri na tashi,ba kaman jiyaba da bacci ya ɗaukeni har rana ta fito na makara.
Kai tsaye bayan na gyara ɗakinnamu kamar kullum ƙofar su ammin na nufah.
Koko take zubawa yaran da suka kewaye ta a kofi.
Gaisheta nayi kafin na koma gefe na zauna,saida ta gama dasu tukunna,kafin ta zubamin nawa,jiya girkinta ne da kuma yau,gobe da jibi nasan na inna rammah ne,akwai rowar abinci kenan. Yanzu su biyune a ƙofar Aina'u amaryar baban tayi yaji bata nan,wannan kamma inaga auren tacan tacan,dan ita irin matannane masu shegen son abin hannun miji,idan akwai to da zama,amma idan babu saita ɗebi jaraba tai tayi babu gairah babu dalili. Shikuwa baba samunsa ɗaya idan yayo caca ta gara masa,inkuwa ba haka ba saidai kowa yasan ta kansa,dan kuɗin sana'ar tasa ma ta Aune Aunen kayan abinci dayake a kasuwa kullum su yayah Musbahu ne masu fama da cikaton uwar kuɗin ma ballantana kuma riba.
Hannun nasa na karbi kokon da ammi ta miƙomin,bayan na gama tunanin na yi faɗi ba'a tambayeki ba.
Bayan mun gama gyara wajen nayi kafin na hau kiciniyar ɗora abincin Siyarwa,yau kasuwar garimu ce,dan haka da wuri ake yi kuma yafi na kullum yawa.
Banason wannan ranar ta zagayo,saboda nafi daɗewa a wajen tallen,ga tarin marasa ɗa'a a wajen,saidai kuma ta wani wajen nafi sonta,dan nima inayin wani abun nawa natafi dashi,inna samu riba na saka a asusu.Kuma itama ammi tana sallamata idan na dawo.
Bayan abincin ya kammalu shiryawa nayi nazo ɗauka zuwa kasuwar,shinkafa da miya ce da kuma waje,sai kabeji.
Nida Asiyah muka tafi,dan tunda aurena za'ayi dole itama tafara zuwa dan ta gane kan siyar da abincin.
Kodaɗɗun kayana ne a jikina normal na tsakar gida atampa,sai barin hijabin dana saka,wanda yafara mutuwa ta sama saboda tsufah. Ba wai kayane aka wareni ba'ayimin ba,dama gidaje dayawa masu irin ƙarfinmu daga shekara sai shekara suke ganin ɗinki,hakan ma atampar roba ce. Sauran yara kowa uwarsa na ƙoƙarin ganin tasake masa,wanda kuma ƴan mata ne sun fara hira samarinsu suyi musu. To ni kuwa ciki wannene nakeda shi ɗaya,shiyasa a gidannamu nafi kowa ƙarancin suturar sakawa,hana rantsuwa nema Yah Musbahu yayimin ankon ƴan matan gidan da akayi wata shida dasuka wuce,shine na samu nake ado dashi ranar juma'a.
Kasancewar kasuwar da ɗan tazara tsakaninta da gidanmu,shiyasa saida muka dan taka kafin muka isa.
Wajen rumfata ta kullum na ajiye kayan,itama Asiyah na sauƙe mata nata,yarinyar ba wata babba bace a shekaru,amma nan idan anjima in tafara magana da masu siyan abinci samari,sai ka ɗauka wata hamshaƙiyar budurwa ce,abin yana bani mamaki yanda muhallinnamu gaba ɗaya ya koma haka.
Jejjera komai nayi a muhallinsa na fara zubawa wanda suka zo siyah,wanda dama costomominmmu ne na kullum,sai kuma waɗanda ba'a rasawa.
Hankalina ya tafi wajen zuba abincin,buƙatata na sallami wadanda suka rufemin kai,ohh abin babu daɗi idan aka rufeka kana zuba abincin,wai a hakanma Asiyah na taimakona da zuba miyah,da haka zanyi tayi ni kaɗai,tunda naso ta dunga rakoni amma ammi bata maida hankali da zancen ba,sai yanzu da tasan dole zan bar gidan ai gashinan ta haɗani da ita koh.
Jinayi an yafato hijabi nah ta gefe,dama kuma naji hayaniya a kasuwar,dan dai bana ganin mai yake faruwa ne saboda mutanen dasuke kaina.
Juyowa nayi na kalli indo wacce muke zama rumfah ɗaya,saidai ita gwaten doya take kawowa.
Idanunta a zazzare take nunamin wani waje da yatsunta.
"Ke Sumaimah kalli gacan goje agonki zai sokawa wani wuƙa"
Wani dummm gabana ya bugah,cikin firgici na kalli inda hannunnata ya nuna. Daidai kuwa lokacin da ya burma wuƙar a cikin dattijon daya cakwane wuyan rigarsa a tsakiyar kasuwar.
Wani kaɗawa hantar cikina tayi take na fara jijjiga kai kaman wata ƙadangaruwa,ba fah kuma mafarki nake ba koh,dagaskene wani a kashe a gabana akan idona.
Jini ne yafara feshi daga cikin mutumin ya wanke hannun gojen wanda yake riƙeda wuƙar a hannunsa,kowa yaga abinda ya faru,amma kuma tsoro da firgici bazai bar mutum ɗaukar mataki ba.
Bayan ya sakeshi ya faɗi kafin mutane suka riƙoshi aka nufi asibiti dashi.
Hannunsa ya yarfe yanda jini ya wankeshi sharkaf,wani ne daga gefensa ya miƙomasa tsumma,shima da alama ɗan iskanne kuma yaron sane,dan kansa sai kace gonar ayah,anyi wanann abin da suke cewa dadah.
Jikin wata katanga ya samu a gefensa ya zauna tamkar bashine ya ɗauki rayuwar wani ba,ko nace lafiyar wani.
Tabar wiwi aka miƙomasa ,wani kuma ya kunna masa ashana,buuuu hayaƙi ya turnuke fuskar tasa,baka ganin komai sai gashin kansa mai kama da ciyawa a tsatstsaye.
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,ai a zaune take wani satin i yanzu ƙasa ta rufemin ido,gwanda ma tun daga yanzu nafara bankwana da mutane ina neman gafarar su,danna san ana kaini gidan wannan azara'ilun duniyar tofah saidai sunana kawai dazai saura a doron duniyah.
Indo ce ta watsamin ruwa a kan fuskata,sai sannan tayi firgit na kalleta.
"Wayyo Sumaimah lafiyar ki kuwa,tun ɗazu nake tabaki amma ko motsi bakyayi,saida na zuba miki ruwa kafin kika dawo hayyacinki"
"Iyee ...uhm inaga suman zaune nayi,me...uhmmm"
Kasa ma ƙarisa maganar nayi,dama kuma bansan bai zance ɗin ba,dan gabaɗaya notin kaina ya kwance.
"Nasan mai yake yawo a cikin kanki,amma ki kwantar da hankalinki,bazai taba kasheki ba sai kwananki ya ƙare,wancan ba naji ance wai cunensa yayi ga cibiyar tsaro cewar dashi a fashin da akayiwa gidan gwamnati,amma in bahaka ba bai cika kisa akai akai ba,nina sanshi ai anguwar mu ɗayah"
"Hmmmm indo kenan,so kike nace na yarda da maganarki ko mai,kawai dai kina faɗane dan na kwantar da hankalina,saidai wannan batun babu ma shi,dan raina ya daɗe da tashi ya tsaya,inaga kuwa bazai taba sake komawa ya kwanta ba har zai sanda azara'ilu ya zare shi"
"Haba Sumaimah kar kice haka mana,ba kyau mutum yayi ta zatawa kansa mutuwa fah"
In jinta tana ta daɗin bakinta amma ban bata amsa ba,idona nasake mayarwa wajen da goje yake shida mutanensa,dan bana tunanin zansake sakewa nayi abinda ya kawoni,jikina ma yayi sanyi da zuba abincin,Asiyah ce take ta zuba Musu,dan in sunyi magana ma ba jinsu nake ba,saidai nace uhm uhmuhm.
Har zuwa yanzu tabar hayaƙin yake shaƙa bai daina ba,saidai babu hayaƙin kaman na ɗazu,dan kana iya gano dodanniyar fuskarsa ma daga nesa.
Karaff kaman abin rashin sa'a muka haɗa ido tashi.
Wayyo bammasan mai nakeji a cikin zuciyata ba a lokacin,gashi kaman abun tsafi kokuma nace ya riƙemin idanuwa na gagara ɗaukewa,wani irin hargitsi nake ganowa a cikin idon da babu ɗigon salama a cikinsu,raina banda kuwwar neman tsira babu abinda yake.
Wata ƴar jarumtace ta gifta mun,wacce tasakani saurin ɗauke idona daga cikin nasa,wayyo nasan shikenan sai ya yanka ni,wayyo wayyo shikenan ya kamani ina kallonsa,nasan irin wadannan mutanen kuwa basaso a kallesu shikenan tawa ta ƙare.
"Sumaimah kingani yaronsa Tunga yana tahowa nan wajen,kuma da alama wajenki zaizo,dan ke yake kallo wlh".
Meee shikenan ta faru ta ƙare,indo ke tauraro mai wutsiya ce,bakya faɗan abin alkhairi.
Zuwa zayyi ya fizgeni yakaini wajensa,nima ya yankamin hanjin ciki kaman wancan mutumin.
Da ƙasan ido nake kallon wanda aka ƙira da Tunga ɗin,kuma dagaske inda nake yake nufowa babu makawa........





Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan
09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION


*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[06]



[Goje a mahangar gani]

Kwanannan ban san mai yake damuna ba,amma baƙinciki nakeji a cikin raina,duk yanda zanyi shaye shaye bana jin zafin zuciyata yana sauƙata,raina jini yake so na dunga ɗauka a koda yaushe. Hakan yake raɗamin a kowanne lokaci.
Yanzuma wannan mayaudariin daba maganinsa nayi ba yau bazanyi bacci ba,mutane gani suke kaman shune na dayayi shine yasaka na yanke masa hanji ,basu san shiɗin muna fikin ƴan fashin makwantanmu ne ba.
Zanyi fashi zan ɗau jini a garinnan,amma bazan bar wani daban yazo ya kafa tasa kujerar ba,saboda wannan garin nikaɗai ne,idan ba goje ba to kuwa ba kowa.
Duba inda nake tara dattin tabar hannun nayi,abin ya ban mamaki danaga na tara har kusan kwarkwaro bakwai,da duk yanayin danakeji daga na shata nakeji ya sauƙa,amma yanzu baya sauƙa sai nasha dayawa tukunna..
Magana naji Ragarus yanayi,banji abinda yace da farko ba,iya ƙarshen kawai na kama.
".......itace fah wacce ogah zai aura wani satin"
Inda idonsu yake kallo nima nakai nawa idon,da wata farar yarinya na haɗa ido. Abin yabani mamaki yanda ta tsaida idonnata cikin nawa,dukkuwa da yanda nau'ikan tsoro suka bayyana akan ruhinta. Ban ɗauke nawa idon ba,dama abune da bana tunanin na tabayi wa wani a rayuwata,wato ɗauke ido,bansan wata abu wai ita kunya ko tsoro ba,wannan abubuwa banida su a halittata..
Ɗauke idonnata tayi tana diriri,kaman an kama munafuki,haka kawai sainaji dabani dariyah,kana ganinta kasan tsoro ya cikata da haɗa idon da mukayi.
"Ogah barina je na siyo maka abinci a wajenta,kaga saikaji ma ko yana da daɗin da inta dafa zaka iya ci,ko ya kace"
"Zancen banza kenan kaidai kawai kace bari kaje kasamu damar yi mata magana kuma ta zubamaka na bati,kafi kowa kuma sanin banason raini. Dan haka idan kaje karma ka ambaci sunana a wajen"
Juyawa nayi na cigaba da tunanin dayake cikin kaina.
Inaji yana mayar masu yanda sukayi da ita,wai daya tambaya daƙyar ta faɗamasa sunanta saboda tsoro.
"Sumaimah"
Na maimaita a raina danaji ya faɗa,hmmm ina tausaya mata inta shiga shirgina,indai zata kama kanta to babu ruwana da itah.

Ƙarar jiniya naji na ƴan sanda,ina jin su Tunga suka tashi  tsaye,so suke nace musu mu tafi kaman koyaushe,saidai yanda na jingina da jikin katangar banason na tashi.
Muryar DSP ce ta ziyarci dodon kunnena,hakanne yasaka ni dagowa na kalleshi.
"Goje abubuwan da kake a garinnan kare bazai ciba,dan haka ka biyomu ofishimmu yanzunnan kaida yaranka,dolene ka fuskanci hukunci,sannann kuma ka biya tarar mutumin daka buɗewa ciki. Babu wanda yafi ƙarfin doka duk shu'umancin sa"
"Hannu ɗayane kawai ya soka masa wuƙa,kuma wannan hannun na gojene,dan haka a dokance iya gojene zai biku kawai koh,don haka muje.
Kai Tunga ko zata mutu ko kuma tayi rai to a ƙaddamar,in kunji lafiya ku sama ta gora kawai"

Murmushi nayi lokacin dana shiga motsar ƴan sandan,idon DSP yayi zuru zuru,da alama ya ankare da saƙon dana aikawa su Tunga.
Kishingiɗa nayi a cikin mota kafin a isa,har bacci ya fara ɗaukata.Duk daren duniyata yanda naga ranar haka nake ganin daren,musamman ma idan na taimaki wani,kokuma wani yayimin abu ban ramaba,narasa mai yasa nake haka,shin kowa haka yake ko kuma ni kaɗaine tawa halittar daban.
Amma yau kam tunda nayi abinda rannawa yakeso to da alamar zan iya samun bacci.
Saida naji motar ta tsaya kafin na tashi zaune,dama bacci nake so nayi inda wadancan yaran bazasu takuramin ba,haka ma inna a gida,tunda zan kwana a wajen sai nayi ta bacci babu wani shedule a kaina.
Suna buɗe bayan motar na nufi ɗakin danake zama idan na biyosu,babu wanda yafi doka injisu da faɗa,to gashi na kawo kaina amin hukunci.
Maganar DSP naji yana yiwa wani ɗan sanda da muke tafiya tareda shi,hmmm su gama abinsu ma,daga ƙungiyar BC(black cobra) sun dawo gobe da yarjenjyata ta shiga ƙungiyarsu,to bazasu sake gani na ba ma,nasan zuwa lokacin nafi ƙarfin wannan kurkunnasu,duk da yanzu ma zancen manyan garine yasaka nake biyosu,amma wannan shine na ƙarshe,shiyasa nazo nayiwa wajen bankwana.
"Kai copur wannan abinda ake yi masa ya ƙare daga yau,ku kaishi cell ɗin da ake saka mai laifi irinnasa,sannann gobe a miƙashi ga kotu,dan ƴan uwan wanda ya sokawa wuƙa sune suka kawo ƙara,kuma sunce kotu zasu kai ƙarar"
Da nayi niyyar na ƙyalleshi na wuce,saidai kuma zuciyata bazata iya ba,in ba gargaɗi nayi masa to bazanyi baccin danake mararin yi ɗin bama
Dawowa nayi da baya har zuwa inda yake tsaye,da wani tulelen cikinsa a cikin rigarsa,an bubbunka haram ciki ya nuna alama.
"DSP sambo in kana cin ƙasa kasani  ka kiyayi ta shuri,babu ruwana da wata ƙara dazasu kai,abune ya haɗani dashi shiyasa nayi masa hukunci,da kunsan abinda yake muku a garinnaku ma da godiya zaku min.
Sannan da kake wani tada ƙayar baya nasan biyanka kuɗi sukayi koh? In mutum yasamu kuɗi kuma iyalansa yake tunkara dashi. To in kanaso suci wannan kuɗin cikin lumana,ƙaramin yaronnan ya dunga zuwa makaranta da ƙafafunsa,sannan wannan ta gidan kar ta haihu lokacin ta bayyi ba.
Shi dana sokeshi ya rayu bari muga in muka mata tiyatar cikinta zata rayu?....."
Cikin sigar jan kunne na ƙarisa maganar ina jaddada masa gargaɗinnawa da idanuna,aikuwa hakan yayi aiki,dan lokaci ɗaya gumin tashin hankali ya lullube jikinsa sharkaff..
Bansake bi takansa ba na nufi ɗakin dana ke sauƙa innazo,har copur ɗin ya buɗemin ƙofah.
Ai wannan mutumin dan basu san sharrinsa bane da kuma makircin daya haɗamin harma da garin gabaɗaya,dana kasheshi ma da sai hakan yafimin daɗi.wawaye duk a zatonsu harda ni a lalatacciyar satar da aka yi musu,sun raina aikina ma da alama.
Mutum yayi sata a garinnan ko ya kwashi tsiya,inda ma kajine ko akuyah idan za'ayi gashi da sauƙi,amma kuɗi kan basuda wannan arziƙin..
Ina nan kwance akan katifar ɗakin har bacci ya ɗaukeni.

           __***__


Tarin bola ce tsiri guda kaman zata dabo sama,da alama duk faɗin birnin garin anan suke tara tarkashen sharar.
A can cikin bolar saika kula ga hango motsin mutane ledodi sun lullubesu,suna nan kwance har yanzu basu tashi daga suma ko baccin wahala ba.
Malam audu ne yafara buɗe idonsa tareda ture ledar da take kansa,waya sani ma kota kashi ce.
Tashi yayi daƙyar ya zauna yana nishi,saboda tsamin da jikinsa yayi.
Gabas ya kalla kana da yamma,mai kuma suke a tsakiyar bola da ranar Allah.
Zaro ido yayi lokacin daya tuno izayar da suka sha a jiya a gidan dasuke aikin.
Gefensa ya kalla inda gaji ke kwance shame shame akan wasu tsummokara,saikace mahaukaciyah.
Ƙoƙartawa yayi yakai hannunsa ya kwaɗa mata duka a kunkuminta,aikuwa ta saki azababben ihu tana wangale baki.
"Wayyo wayyo kunkumina ku taimakeni jama'a zai cire"
"Ke dallah tashi mubar wajennan idan zamu iya tashi,waɗancan dangin fir'aunan bayan gari suka kawomu cikin bola"
"Bola kuma wacce iri"
Itama ta yunƙura tana kallon tsummokaran da take kai"
Motsin Atika da sukaji a gefensu ne ya sakasu waiwayawa,kuma gaji ta fasa faɗin abinda yazo bakinta.
Kuka take tanan kururuwa kaman a cikin bacci,da alama abinda yafaru jiyanne yake dawo mata.
Jijjigata gaji tayi cikin baƙin ciki,dan koma mai yafaru ai ita ta jawo musu,da yanzu sun gama aikace aikacen gidan suna karyawa da lafiyayyen abinci.
"Shegiyar yarinya mai ɗuwawun bin maza,ai gashinan abinda kika jawo mata,in sonsa kike tun farko da ki faɗamin mana asan surkullen da za'ayi,amma daga ke har ubannaki dayake garorine ku kagu jimanaye kunga kuɗi,sai karba kawai kuke bakwa tunanin mai ya faru. Ban tashi sanin mai yake faruwa ba sai ranar dazan sha duka tukunna.
Sai ku tashi mu tafi ai .......ahhh......."
Shuru tayi tana jujjuya kunkumi,dan dama sojan kunkuminnata yayi ta sambaɗawa kulƙensa.
Hararar malam audu tayi dayayi mata sannu,yunƙurawa tayi ta shi kana ta tashi sauran yaran wanda suke baccinsu hankali kwance.
Bayan sun tashi a wajen tafiya suka farayi zuwa tasha,kowa sai komaɗewa yake yana tafi kaman horon cikin film ɗin mayu.
Duk inda suka wuce kallon su ake,amma ko a jikinsu,tsamin da ƙashushuwansu suke ma ya isa.
Sa'ar da sukayi daga inda suka zubar dasu bashida nisa da tasha,saidai kuma ba a nan gizo yake saƙar ba kuɗin motar komawa garinnasu ne aiki.
Tun safe suke tashar har yamma,ganin bazasu samu mota ba yasa suka samu wani waje a tashar suka zauna.
Hayam hayam kowa sai baza hamma yake kaman zaici babu,idonsu yayi zuru.
"Yanzu kana gani zamu mutu bazaka nemo mana abinda zamuci ba,huhulahu kawai"
"Wai nikam gaji meyasa tunda kika shi a cikin bolar nan ni kike sauƙewa tujara,ya isheki fah haka,wlh zan sake mangareki ba ruwana da ciwukan da suke jikinka"
"Hehehe to ko sun duka ƙwalƙwalwarka ne take faɗa maka zaka iya dukana iyeee,kalleka fah kaima a doddoken kake ba iya ni kaɗai ba,ƴan ƙafafunka ma daƙyar kake ɗagasu sai kace lagwani. Kaff danginku haka kuke sai kace ƴaƴan kunika,zama dakai yasa duk ƴaƴana haka suke ƙafafu kaman liƙo cikin kuwa kaman randa,ni ba abinna zagesu ba kaima haka kake. Shiyasa nake mamakin ya akayi goje yakeda ƙira da ƙarfi,ubansa da uwarsa ba haka suke ba,har Addu'a nake ko ƴaƴana zasu iyoshi,na huta da aikin kashinsu da yawa,yaro in ka haifeshi bazayyi tafiya ba sai ya shekara uku tukunna wani abin ma..........."
"Dan Allah gaji kiyi shuru haka,dan Allah ku bar faɗannan sai munje gida,kowa sai kallon ku yake"
Kaman tayiwa dutsi magana ko kallonta basuyi ba,wata harara malam audu ke yiwa gaji kaman idonsa ya fito,dan yaji zafin wannan wankin babban bargon da tayi masa a tasha.
"Hmmm ke yanzu har zakice ma danasanin aure na kikeyi,daɗinta ma mu gidanmu ba mayu bane bama tanɗe kuruwar mutane,kowa yayiwa wannan ubannaki shaidar ko tsuntsune ya gifta da kan gidanku sai ya tanɗe kuruwarsa. Bandama ƙaddara data haɗani take,kaff abokaina da ƴan uwana babu wanda yayi na'am da aure na dake,nima kaina bansaniba ko tanɗeni kikayi"
"Hhhhhh narasa mai zan tanɗa inma maitarce sai kuruwarka,ko ban tanɗe ta bama a tanɗen take,dan daga ganinka yanda kake haka ma kuruwar taka take"
Tashi atika tayi tabar wajen,kowa sai kallonsu yake amma su babu ruwansu,ina zatakai wannan abin kunyar,wai dama haka auren yakene,kowa na ganin hanjin kowa,shiyasa fah ta tsani aurenma ita a rayuwarta,tafiso kawai a hole in holewar tazo a wuce wajen.
Tana cikin tunaninne taji muryar wani ɗan garinsu. Juyowa tayi suka haɗa ido da tasi'u,shima da yace yana sonta,kayan gwari yake kawowa daga garinnasu zuwa nan,dama sana'arsa kenan.
"Lahhh tasi'u kaine"
"Ehh nine atika mai kike anan wajen ga jikinki duk ciwo?"
Inda inda tafara na ƙaryar dazata yimasa,can kuwa wani abu ya faɗo mata a rai.
"Uhmm dama gida zamu tafi to shine jiya barayi suka shiga mana gida,bayan sun ƙwace komai kuma suka yimana duka"
"Innalillahi garin ya haka,in su malam ɗin suke,dama tafiya gida zanyi ko zakuzo mu tafi kawai,saidai zamuyi dare a hanya saboda motar tawa batada gudu"
"Babu komai hakanma mun gode,barina ƙirasu toh"
Wajen iyayennata ta koma,zuwa yanzu sun daina faɗan kowa ya karyar da kai yana nishi na wahala da yunwa.
Lokacin data faɗamusu yanda sukayi da tasi'un ba ƙaramin murna sukayi ba.
Biredi ya siya musu da zobo irinna ɗurawar nan ganin sun fita hayyacinsu.
Kaman almajirai kuwa haka suke turawa a cikinsu,kowa so yake yayi maganin yunwarsa. Banda ruwan albarka babu abinda suke masa,kaman basune sukayi masa cin mutunci ba dayace neman auren atika,a ganinsu shi ba sa'anta bane,yanzu gashinan babu kunya suke masa godiya daya taimakesu.
(Shiyasa a duniya ba'a son kaci mutuncin mutum ko ya yake kuwa,saboda Allah ne kaɗai yasan ranar da zai maka rana,a lokacin da bakayi tsammani ba. Allah yasa

Please Login or Register in order to submit comment