Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mu dace dai.)
Daff da magriba suka kamo hanyar garinnasu,tunda suka tafi wata shida sai yau zasu koma,dama ance in daɗi bai kawoka gida ba wuya ai zata kawo ka.
Shuru sukayi a cikin bodin motar a tsakiyar kayan miyan da bai siyar ba,sai wulla ido suke,ga motar batada gudu ko kaɗan,ko yaushe zasu isa oho.
Kaman a sama sukaji muryar tasi'un yana tashinsu,abin kunya sunyi bacci duk sunyi rugu rugu da tumatir ɗinsa,wani abinma hadda taruhu da tattasai,gasu da ɗanyen ciwo a jikinsu.
Banda mutsu mutsu da nishin azaba babu abinda suke.
Motar ba wani tudu bane da ita,amma saida sukayi dagaske kafin suka iyah fitowa,ko tsayawa yimasa kyakykyawar godiya basuyi ba suka shige gida,dan basa cikin hankalinsu.
Lokacin gari duru duru yake ana shirin ƙiran assalatu.
Inna mairo ta fito da butarta zata shiga banɗaki sai ganin mutane tayi sun shigo gidan,salati tafara jiki yakama karkarwa,dan tayi zaton gamo tayi,saikuma ta kula ashe su gaji ne
"Gaji kuma?"
Tafaɗa cikeda mamaki.



Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan
09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION


*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[07]


Butar hannunta ta ajiye tana kallonsu,sune kuma da gaske,tayiwa kanta wannan tambayar.
"Gaji kune da asubar nan haka,mai ya faru kukayi wujiga wujiga haka?"
Bude baki tayi zatai magana ƴar ta ƙarama ta rigata,tunda su ba ciwo a jikinsu.
"Yaya ce tayi soyayya da Alhaji,shine wasu sojoji sukayiwa su baba duka suka jefarmu a bola"
Kunya ce takama su kaman zasu nutse a wajen.
Saurin wayancewa inna mairo tayi,musamman ganin yanda gaji ke kallon ƴar tata farida kaman zata cinyeta ɗanye.
"Ohh to Allah ya tsare gaba,yanzu kuzo ku zauna,barina fito daga banɗaki na haɗamuku ruwan wanka kuyi mamatsa jikinku."
Cije baki gaji tayi,so take tayi magana amma kuma tana tsoron kar inna mairo ta hana su ruwan kaman yanda tayi niyya.
Kafin gari ya waye duk sun wanke jikimsu sun sanja kaya wanda inna mairo ta ɗauko musu a sashennasu,dan ko ɗakinta basu bariba tun asubar,bare su taka cikin gidan suga mai ya sauyah.
A daren tayi musu abinci mai sauƙi sukaci,hankalinsu ya dawo kansu.
Da safe kuma tasiyo musu burofen da masu shago suka buɗe.

Gaji ce tafito daga ɗakin tana kallon gidan,babu abinda ya sauya a cikinsa,saima fess da yayi kaman bashine sansanin shirgi ba lokacin da suke nan. Ƙofarsu ta nufah domin taga mai ya sauya,tun kafin ta ƙarisa tajiyo kukan saniya,abinne yabata mamaki,saniya kuma a ƙofarsu?.
Turus tayi ganin kewayen ƙofar tata cikeda abincin saniyar da kuma kashinta,wajen sai kace kewayen dabbobi.
Cije baki tayi tareda ƙiran sunan goje da ƙarfi har ƙasan maƙoshinta.
"Gojeeeeeee!!!"
"Na'am"
Taji ya amsa a bayanta.
Wani dum ƙirjinta ya doka saboda firgici,dan batayi tsammani yana gidan ba kuma ya jita,tafaɗa ne kawai yanda zuciyarta tafara tafasa.
"Miye kike ƙwalamin wannan ƙiran kaman zaki ƙare min suna daga dawowarki iyeee"
Diriricewa tayi tana inda inda,in a lokacin bayane zata iya maida masa magana,amma yanzu gani tayi gabaɗaya ya sauya mata,jikinsa ya sake murɗewa,gashin bakinsa sun sake tsayi,ga wani uban tabon yankan wuƙa a dantsensa na dama. Ji tayi kaman wani zaki yana tunkarota"
"Uhm dama dama bakomai bane,kawai gani nayi ka maida mana ƙofar kamar kewayen dabbobi daga tafiyarmu"
"To wa yace ku tafi ɗin,sanda kuke nan na tasheku na saka ta ne,ina saida kuka tafi yawon maularku tukunna,kunje kun saida musu hali sun koroku rana tsaka,mutane sun zaman zamansu zaku dawo ku damesu. In nan ba inda zanje kuma ban sanja ba,duk wanda ya damu mutane ko ya nemi neman rigima,saina yanke masa wata gaba ta jikinsa,daga ke har mijinnaki da kuma tarin tsiyar ƴaƴan ku"
Muryar inna mairo yaji,hakanne ya tsaya da yiwa gaji tatass wacce take gabansa,tana jinsa amma babu dama ta rama sai yace zai bugeta kokuma yasaka ta a kewayen karnukansa.
"Kai goje kaine fah bakada gaskiya anan wajen,saboda kai kasaka musu dabba a ƙofarsu,sannu kuma tayi magana kace ba madu ba bukar. Kaje ka sunce saniyarka ka maidata inda take da,wato gefen ƙofar ka,ni banga mai zakayi da saniya ba ma"
"Kyauta tace ta farko dana samu sanadin ƙarfina da ƙwazo nah,idan na ganta tana tunamin dani jarumine,dan haka babu inda zan kaita anan zata zauna a gidannan. Tunda kinyi magana zan turo Ragarus ya ɗauketa a wajen"
Cikin tafiya ta izzah ya nufi hanyar waje,wani baƙin kare yana binsa a baya..
Sai bayan ya fice tukunna gaji ta saki wani numfashi data riƙe tun ɗazu.
"Uhhh nina manta ma da wannan basamujen yana gidan,gabaɗaya mutum sai murɗewa yake kaman wani dodo...abinnan yana cimin tuwo a ƙwaryah,kaf cikin yarana babu wanda yake ɗaga cikin plastic na ruwa saboda lalaci,amma shi kalleshi har tanki ma zai iya ɗauka. Narasa mai yakika yimasa yana yaro ya zama haka,kaima da ka sani ai da kayiwa yaranka,waɗannan masu kama da agwagin"
Oh gaji har yanzu kina nan da ɗabi'arki ta zagin ƴaƴan ki,koma dai ya suke ai sune naki,kuma su Allah yabaki"
"Ehh zakice haka man saboda naki jarumine,nawa kuwa ƴaƴan nasan in kinshiga ɗaki dariya kike musu,kin gansu kaman buta"
Kasa riƙe dariyar ta inna mairo tayi,wanda hakan ya ƙara ƙular da gaji tazo har wuyah.
"Kinga ya isa haka ni bazan biyeki ba,kujira yaxo ya daukemuku saniyar ku gyara muhallinku ku koma"
"Mee kashin saniyar tasa na wata da watanni mu zamu gyara masa,zancen banza ma kenan,jakunan ku kuka maidamu keda shi komai,yanda kuke da iko da gidannan fah muma haka mukeda iko dashi"
Jijjiga kai inna Mairo tayi cikeda takaici,ta dawo ai za'a cigaba daga inda aka tsayah.
"Nina fara gajiyah da mitarki gaji,in sun dauke saniyar ku jirashi yazo ya gyara muku wajen,kuce sai ya tattare kashin tunda saniyarsa ce tayi"
Yawu gaji ta haɗiye muƙutt,saboda tasan inna Mairo gatse tayi mata,hakan bazai taba faruwa ba.

          __***__

A zaune take a gaban wuta ta haɗa gumi sharkaff tana suyar awara,gabadaya hankalinta yana wajen,buƙatar ta ta gama soye uban taragon awarar dayake gabanta.
Dama sana'arta ce tun tale-tale kowa yasan ta da ita.
Atika ce ta shigo ƙofar da sauri daga wajen inna Mairo take,kana ganin yanda take zumuɗi kasan gulma ce take cinta a rai.
Ɗaga kai gaji tayi ta kalleta tareda mikamata wata awarar wacce ta suyah.
"Hungo dan Allah atika zubawa farida Ta ɗari biyu ta kaiwa wani a waje,sannan kema kizo ki kintsa ki tafi wajen tallen ki,kuma maza ki hanzarta kada a gama siyan na kowa a bar naki yayi kwantai mana. Kince nayi miki da ƙwai nayi miki,amma tun ɗazu sai yada kai kike kinƙi tafiyah"
"Ohh gaji zan tafi dai,yaushe ma ranar tayine wai,wani abu fah nazo dashi nake son na faɗamiki. Wai kiji ashe Goje aure zayyi?"
Tsayawa ta juya awarar tayi tareda juyowa tana kallon Atika,alamu duk sun nuna bata yarda da abinda tace ɗin ba"
"Ke bana son ƙarya,kaff garinnan wacece zata auri wannan dodon,in zakiyi ƙarya ma kiyi wacce kunne zai yarda da ita"
"Wlh gaji da gaske nake,kuma gobe nema ɗaurin auren,gashinan inna Mairo ta gyara ƙofar gojen,kuma yanzunan aka kawo mata saƙo,kayane a ciki sabi na mata ta siyah wai na Amaryar ne"
"Ke ƴar nan,ƴar gidan wanne shashan ubanne zai bawa goje ƴar sa,kalan ya danneta sai ƴaƴan hanjinta sun fito nan take?"
"Uhm ai bakiji ma abinda naji bane jiya a wajen talle,har nunamin itama akayi,gata kyakykyawa da itah,ƴar gidan Mijin su inna rammah ce fah ƙawarki,wai a wajen caca dasukayi da goje ya cinyeshi,shine da bashida kuɗi yabashi ita"
Sakin baki gaji tayi tana kallon atika kaman ta samu TV.
"Duk yaushe haka ta faru a garin bansani ba uhm,barina gama suyar awarar nan zanje gidan naji komai ai"
"Ko kuma ki bari sai da daddare ba,kinga babu wanda zaisan kinje,ni labarin naji wai ƙawar indo ce ma nan maƙwantanmu"
"Wai tagamu da ƙaddara,muma da muke gida ɗaya dashi muke ganin takanmu balle ita mai zama dashi? Amma kuwa Mairo bata kyauta ba,duk ana wanann zancen bata faɗawa malam ba,saboda sun rainashi basa ganinsa a uban goje koh? Bari kuwa ya dawo da faɗamasa yanda ake ciki,duk wacce za'ayi ma ayi"
Tafaɗa tana cigaba da suyar ta.

           ___***___

[Sumaimah a mahangar gani]

A zaune nake ina tilawar qur'ani,yau wacce rana banje talle ba,tunda akayi auren masu zuwa tallen ban taba fashi ba sai yau.
Ban san na saba da zuwan tallen ba sai yau,dan jina nake duk wani iri tun safe,na rasa ma mai zanyi a gidan.
Abinci dama banice nakeyi ba su suke kayansu,iya abincin siyarwar ammi kawai nake sai shara da kuma wanke wanke wani lokacin,saboda duk mai abinci burinta ta gama ta kwasa da yawa itada ƴaƴan ta. Wannan mummunar al'adar dasu ce yasa na huta kokuma nace na tsira daga yi musu girki.
Bayan nagama karatun shuru nayi ina tunani,inason yin karatu mai zurfi,amma nasan hakan bazai taba yiyuwa ba,musamman ta muka taso a gidan da babu wanda ya damu da wani abu wai shi ilimi.
Alamar takun sawun mutum naji,hakanne yasa na buɗe idona,Asiyah ce a tsaye akaina tana min kallon marar daraja.
"Wai kizo inji ammi tana nemanki"
Kawar da idona nayi akan ta tareda cewa.
"Kice ganinan zuwa"
Bata sake cewa komai ba tabar wajen,tafiyar ta bani da kallo,bansan lokacin da dariyah da kubcemin ba. Tafiya take tana turo kunkumi baya,ƙirji kuma gaba,wanda yake kaman allo babu komai a jikinsa,dan ko ƙirgen danginma bata fara tukunna.
Hmm nace a raina tareda cewa....'in kikayi haƙuri ma nono kam zai fito miki har ki rasa yanda zakiyi dashi indai kinyi gado. Dan ammi Allah yayi mata arziƙin nono har cinyarta suke tabawa,inda tanada ƙiba da za'ayi mutanennan ne masu nonon su yafi girman ɗansu idan suka haihu,amma kasancewar rayuwar tada tsinci kanta sai yazaman basuda girman sai tsayi,in bata saka riga ba sai suyita rito kaman igiya....
Kunkumine dai da ƙyar ki samu,dan kaff ƴan ɗakinnasu a shafe suke ta baya.
Kawar da wannan marar amfanin tunanin nayi na tashi zuwa wajen ƙiran da akayi min.
Yanzu nagama kuwa tunanin yanda take,ina shiga ɗakin da ɗaurin zani a kunkumi na sameta,tana goge tsakar daƙin dan ba laifi tanada ƴar tsafta,shiyasa nake sallah a ɗakinnata da rana hankalina kwance.
"Ammi gani,Asiyah tace kina ƙirana"
Ɗagowa tayi ta kalleni saikuma tace.
"Ohhh ehh haka,zauna barina gama wannan goge gogen tukunna,ai takaicinnan ya isheni,ace bakada ƙaramin yaro,amma ko yaushe kana cikin goge fitsarin yaran wasu can"
Ban tofah komai ba a cikin sababin da takeyi,sai zama kawai danayi ina jiran ta kaman yanda tace.
Bayan ta gama wata leda ta miƙomin baƙa da kaya ciki.
Mamaki ne ya cikani,ban yi ƙasa a gwiwa ba na tambayeta.
"Ammi wannan kuma na menene"
"Mairo ce ta kawo ɗazu wai kayanki ne"
"Mairo kuma...."
"Innar goje"
Tayi saurin katseni,dan tasan konayi nazari akan sunan bazan ganota ba. Saurin a jiye kayan nayi kaman wanda suka ƙona ni,kuma hakane ƙona ni sukayi a zuciyata.
Hannu na ɗora akan ƙirjina ina ƙoƙarin hana zuciyata fitowa daga cikin ƙirjinnawa,dan naga kaman hakan take ƙoƙarin yi.
"Sumaimah yakamata zuwa yanzu kin fara kwantar da hankalinki,domin razanar da kike ko shiga ƙunci bashi zai hana a fasa ba,koda an fasa kaiki gidan goje to babanku bazai iya biyan kuɗin dayake binsa ba,karki manta in akwai kuɗin goje a wajenka to duk bayan wani lokaci ƙaruwa yake har sai sanda ka biyashi,in kuwa kaki biyansa to ranka yake ɗauka a matsayin kuɗinsa. Kinga kuwa in kinga an fasa aurennan to saidai ya ɗauki ran sa kenan a matsayin kuɗinsa,shin zaki iya zuba ido ya kashe mahaifinki ne kina ganin kuma zaki iya cetonsa?"
Shuru nayi ina saurarenta,zancenta gaskiya ne duk da kuwa ina jiyo son kai a cikinsa,da ƴar ta ce za'a kai gidan goje bazata bari ba,saidai uban kowa ma ya mutu a gidan. Amma ni ji yanda take zaromin bayani dallah dallah saboda na amince,tafi kowa sanin kuma inna shiga gidan nima bazan fito da rai ba a hannunsa,saidai kuma ya zanyi dama kullum amfani ake da sanyin rai na da kuma karayar zuciya ta,ga kuma bugu da ƙari banida gatan dazai tsayamin a wannan cutarwar da ake shirin yimin.
Kaman yanda ta faɗa kuma bazan iyah guduwa ba ya kashe mahaifina,duk da baya yimin abinda uba ke yiwa ƴaƴan sa,amma shiɗin mahaifina ne bazai kuma tashi daga wannan matsayin ba har abada. Gashi kuma shikaɗai ya ragemin a duniyah,bansan ƴan uwan mahaifiyata ba ko ɗaya,tun ba ƴar nan bace a yawon ci rani ya aurota,bayan yayi mata ƙarya kala kala ta yarda ta biyoshi garinsu,duk da taga ba haka bane amma ta zauna dashi,saidai mai hakan bai isaba saida matansa suka kasheta. Wannan zaluncin har ina?
Kukane ya kubcemin wanda ammi take ganin na auren goje ne,amma va haka bane,abubuwan da suka haɗu sukayimin yawa na shekara da shakeru nake son na rage zafinsu da kukan.
Bata rarrasheni ba bata kuma hanani ba,saima tashi datayi tabani waje tana min kallon tausayi,bazanga laifinta ba don tayimin iya ƙoƙarinta a matsayinta na mariƙiyata,kuma ina yabama ta bazan taba mantawa da halaccinta ba har abada,koma mai zanji tayimin a baya,matsayinta danake gani na mahaifiya bazai taba bacewa daga kan idona ba.
Kayan na ɗauka cikin sanyin jiki na nufi ɗakinmu wanda zuwa gobe zan barshi na tafi wata rayuwar,ban taba kawowa barin gidan a wannan lokacin ba,dudu zancen auren bayyi sati ba da farawa,gashi gobene ɗaurashi uhmm rayuwa mutum yana nasa Allah ma yana nasa..

Wayyo nikam har banaso gobe tayi na rubuta auren Sumaimah da goje,ku kanku kunsan bata dace dashi ba kohhh........duk mai wata idea to muhaɗu a commen secition toh🤣🤣🤣




Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan
09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan
09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION


*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[08]


Washagari da safe da sanyin jiki na tashi da kuma bacci,saboda jiya da daddare vansan lokacin da baccin wahala ya ɗaukeni ba.
Hamma tayi tareda yin mika,uhm yanzu shikenan nagama kwanan gidanmu sai kuma na kabari dazan tafi kwanannan koh.
Nafaɗa a raina..
Yunƙura nayi zan tashi sai naji ƙarar keda,kayan da ammi tavani jiya ne wai inji innar goje,ni ma manta dasu sai yanzu,saboda lokacin data bani ko buɗewa banyi ba.
Ledar na kunce domin naga menene a ciki. Kaya ne kala uku,biyu riga da skirt ɗaya kuma doguwar riga,dukkansu atampar roba ce amma sabi ne,saikuma hijabi ɗaya da kuma takalmi na roba.
Duk da cewar nasan matsayin auren da kuma wa zan aura ɗin,amma banyi tsammanin haka rayuwar aurena zata kasance ba,nayi zaton kodah bansamu kaman yanda nake tunani ba amma dai zai fi haka,saidai kashsh tsugunne bata ƙare min ba,don da alama akwai sauran rina a kaba.
Jikina na kalla bayan na ajiye kayan akan katifah ta,babu lalle babu kurkur irinna amare dasuke,haka nake a koɗe kaman amaryar mutuwa.
Katifah ta nasake duba,ita ɗin ma ƴan matan gidanne suka gama da itah na karba,to ko kuma a wacce zan cigaba da kwanciyah oho,koma tabarma ce duk Allah ne kaɗan yasani. Dan banji kodah wasa wani yace an siyamin wani abun ba. Nice ma na bawa indo ƙawata kuɗi ta siyamin kayan aikin gida,tunda daga nan gidansu babu nisa saita kaimin idan suka kaini.
Guntun hawayen da bansan dalilin zubarsa ba na share kana na fita waje.
Da ubaidu nayi turuss a hanya zai shiga ƙofar mu. Wani tsayayyen kallo yayi min kafin yace.
"Farar mace(yanda yaka ƙirana) ke kuma yanzu wannan gazagin zaki aura?.......wai ai ta ƙaremiki farar mace danni ma lokacin daya sauƙemin allon kafaɗa na daɗe banyi motsiba,wannan inaga ba mutum vane inaga"
"Kai menene haka ka tsayar ta kana ƙara rikirkitata bayan wanda take ciki,kaima ai shirginsa ka shiga shiyasa yayi maka haka,idan tayi duk abinda yace indai ba shine magajin fir'auna ba ai bazai yi mata komai ba. "
"Hmmm ammi zakice haka,to har aka gama abin ɗaura auren fah baya nan,ance ma wai tun jiya yana jeji"
"Oh an ɗaura aurenne"
"Eh an ɗaura yanzu,wani ƙanin babansa ne yayi masa wali,mai anguwa ne yabada dubu goma sadakin gojen"
"In kuɗin toh yake"
"Vaba ya karba,tacan ma ya wuce wai zaije ya siyo dawa dashi,dama jarinsa ya karye"
"Kutt wai nikam Baban yara ina zaije da wannan halinne,yarinyar nan ya bayarta saboda abinda ya aikata,bai siya mata komai ba irin wanda uba ke yiwa ƴar sa,sannan kuma bayan haka wani maga Allah yabada sadaki wanda haƙƙinta ne shima kuma ya karbeshi?"
Cikeda takaici take magana,kanaji kasan ranta ya baci,itama kenan daba ita akayiwa ba,inaga kuma ni,yazanji kenan.
Kallon su kawai nake a nutse,amma cikin raina a dagule yake.
Kallona ammi tayi da sigar rarrashi zatayi magana. Inaa banason wannna rarrashin da babu abinda yake ƙaramin sai raunin zuciya,a barni kawai da daɗin bakinnan,lokaci ne kuma daya kamata nayi jarumta,tareda tarar duk abinda yake shirin tunkarata. Aurene burin kowa yacika an riga an ɗaura shikenan,Allah yabani ikon ɗaukar duk abinda zai biyo baya. Dan haka saurin katseta nayi tun kafin tace wani abun.
"Bakomai ammi tunda an ɗaura auren zance ya ƙare,Allah yabani ikon cinye jarrabawata"
Daga Min kai kawai tayi,da alama tausayina ne ya kamata,ni yanzu banason mutane suna nunamin wannan tausayin ma,don ba komai zai kawomin ba bace karyar zuciya.
Shigesu nayi nakoma ɗakinmu don bansan mai zanyi a cikin gidna ba,babu wani taro sosai har yanzu,da alama kosai yamma ƴaƴan gidan zasu zo.
Ban daɗe da shiga dakin ba najiyo sallamar indo itada shareefah,ita Shareefah ƙawata ce ta hadda,ita kuma indo a wajen abinci muka haɗu da ita,dukkansu sunada mutunci sosai,don sune ma masuyimin siyayyar dazan bukata,duk da nasan a yanwancin abin sun Cikaminne da kuɗinsu,godiya nayi musu har bansan adadin ta ba.
Kaman yanda na faɗa kuwa sai wajen la'asar kafin mutane suka fara shigowa gidan,inda tani za'a biye to bazan so kowa yazo ba,dan ba komai yake kawosu ba face gulma da ganin ƙwaƙwaff.
Fitowa ta daga banɗaki kenan na iyo wanka,da cewa nayi ma bazanyi ba,Shareefah ce ta tursasa min,ita kam indo inna ce shikenan,tunda aka fara zancennan koyaushe mita take wai an cuceni,nice ma nake tarar numfashinta wani lokacin.
Murya Aisha naji tashigo gidan ƴar inna rammah suna gaisawa da matan gidan dasuke tsakar gida.
Wani mai chemist take aure a can tsallekenmu Abdullahi,saurayine yayi karatunsa,dani muka fara soyayya dashi muna haɗuwa dashi a hanyar makaranta,harna fara sonsa kuwa saboda barkwancinsa,zuwansa gidannan na farko Aisha taɗora ido a akansa. Nan duniya kuwa tace shi take so kaman zata mutu,ta shirya ƙarya da gaskiya wai ai saurayinta ne nice na ƙwaceshi.
Ko ya akayi rana tsaka mun fara soyayya yace nan duniya aisha yake so,abinnan ya ƙonamin rai har kwana nayi ina kuka. Haka ina gani akayi aurenta dashi waccar shekarar,suna nan zaune itada shi,tana ma da yaron ciki.
Har yanzu wannan abin yana ƙonamin zuciya,musamman yanzu idan ya ganni yayi ta bani haƙuri yana cewa ba laifinsa bane,duk da nasan ba laifinsa bane amma kuma yanda yake tunanin muyi mutunci hakan bai kasance ba. Kowa a gidan yasan babu wanda yayi wannan aikin sai inna rammah,amma haka aka zama makafi akan lamarin.
Ido muka hada da itah na kawar da kaina zan wuce.
"Amarya ykk,tun ɗazu naga kina ta kallona,kinga yanda na sanja nayi kyau koh,to ina samun cima da kuma kulawa yanda ya kamata,tunda na auri mai hankali da nutsuwa,ba ɗan daba mai suffar mahaukata ba"
Ɗan murmushi nayi mata,dan wlh har raina ta bani dariyah,wai fah ita a hakan dani take.
"Mashaallah kam aisha kinyi kyau abinki ina miki murna,amma kuma nai hasken ciki kika yi koh,jiki kuma dama haka na sanki baki ƙaru ba,inmiki fatan Allah ya raba,ni barina tafi ko"
Na zaga ta gefenta na wuce,ita kanta tasani inaga mantawa tayi,inada sanyin rai amma kuma bana ɗauka irin wannan maganar sam.
Duk inda na baza kunnena maganganu kawai nake ji suna shigomin,wasu na jijjiga kai wasu kuma kawai na basar.
Su Shareefah sai baki suke bani,a tunanin su hakan yana damuna,basu san an shani na warke ba.
Zuwa yanzu dare yafarayi,mutanen da suka zo kowa ya fara tafiyah gidansa.
Riga da skirt ɗin daya fi ɗan kyau a cikin kayan na saka,dan har an fara shirye shiyen kaini gidana.
Ba laifi kayan yayi min kyau anyo masa ɗinkin zamani,kuma ya ɗan kama jikina kaɗan.
Bayan nasaka kayan hijabin na ɗauka na saka,ta gefen idona naga Shareefah sai kallona take.
Kallonta nayi dauke da murmushin ƙarfin hali akan fuskata.
"Menene yafaru Shareefah kike kallona haka kaman wadda zan tafi inda bazamu sake haɗuwa ba"
"Uhmm ba wai tafiyarki ne yasakani kallonki ba,abubuwane da yawa acikin kaina na gameda yanda rayuwarki da sauyah Sumaimah,a islamiyyah kinfi kowa ilimi,haka ma a makarantar safe da mukayi JSS,ke kikemana na daya,amma haka kika daina zuwa makaranta lokaci ɗaya. Wlh banaso naga mace mai ilimi wacce take son cimma burinta na ilimi kuma hakan bai faru ba. Inama munada ƙungiya masu irin wannan aikin,da sun hana wannan aurennanku saboda cutarwa ne.
Amma kuma tunda ya riga ya faru yanzu abinda zakiyi shine yin abinda Allah yace a gidan aurenki Sumaimah,wannan mutumin da muten ke ƙira da dodo kokuma ɗan daba,kefah yanzu ya tashi daga wannan matsayin ya koma mijinki aljannarki kuma duniyarki. Yanzu duk wata ragama na linazamin aurenki yana hannunki. Nasan kina tsoro Sumaimah kuma bazan ce ki daina tsoronsa saboda nasan hakan abune mai wuya,amma ki tuna abu ɗaya ke macece,kinada baiwa a matsayinki na ƴa mace. Duk kwarjinin na miji da wuyar sha'ani kisa a ranki zaki iya dashi,in kikayi hakan sai kiga komai ya tafi a tsari mai ma'ana"
Ƙirjina ne ya buga kana wasu hawaye masu ɗumi suka zubomin,tabbas idan da yana matsayin ɗan daba a wajena to fah yanzu a matsayin mijina yake. Wannan wasu tarin gaskiya ne masu zafi da kuma matuƙar ɗaci Shareefah ta tunamin,wanda kuma komai zanyi hakan suke bazasu canja ba.
A sanyaye na gama shiryawar Ƙanwar babammu Baaba Ladi ta kamo hannuna muka fito..
Dan dama ita ke kai duk wata yarinya da akayi aurenta ɗakinta..
Bayan mun fita su indo ne suka biyo bayanmu muka fito daga ɗakin
Da ammi naci a karo a bakin ɗakin tana kallona.
Wani kukane naji ya ƙwacemin da bansan ta ina ya faro ba,idan nace babu shaƙuwa tsakanina da ammin to nayi babbar karya,dan tun vanni da wayo na tashi na ganta,da daɗi da babu daɗi dai haka ta riƙeni.
Cikin raunanniyar murya nace.
"Ammi .........."
Ban iya cewa komai ba dan babu kalmar dazata sake fitowa bayan wannan ɗin.
"Babu komai Sumaimah,ki daure aure dama shi yaƙin matane,kowacce mace da haka ta girma,balle ke naki da kuma tsoro,dan haka saikin haɗa da haƙuri kinji...bazan samu damar rakaki ɗakin ba dan haka kuje Allah ya ƙare yabada zaman lafiyah....saikuma a yayyafi juna na abinda ya faru"
Ɗaga mata kai nayi kawai,dan narasa ma mai zance.
Hanyar waje muka nufah,baba kam tunda ya karbi sadaki na babu wanda ya sakashi a idonsa,dan haka ba zancen yin sallama dashi,in yana nan ma mai zaice min,shiba wa'azi sai min ba ko nasiha,dan in kura zatayi maganin zawo tafara daga kanta tukunna.
A ƙafa muke tafiya shuru babu wanda yake cewa komai har muka isa anguwar su gojen.
Ohh ni Sumaimatu ina ganin rayuwa,aure a yanzu ko maƙwantanku ne sai anje da mota an zagayo dakai. Amma ni ganida ƴan rakiyar da sayyadarmu mukazo. Kodayake ana ta kai waya ke ta kaya na samu ma na tsira da raina da lafiyata.
Baaba ladi ce a gaba,itakuma tayi sallama da muka shiga gidan.
Muryar wata matace daga wata ƙofa ta amsa,kanajin hayaniyarta tun daga bakin ƙofar gidan da yara. Da alama itace matar ƙanin babannasa,wai dagajin muryar ya kuwa jarababbiyace,danni tsabar zama da masifaffu tun daga muryaru nake ganesu.
Iya amsa sallamar bai isheta ba saida tafito daga ƙofar tana riƙeda kunkumi a gabanmu.ohh dama ba ramammiya bace yanda nake hasashenta,tanada ƴar ƙiba. Magana tafara cikeda isa da gadara.
"Ohh amarya ce ta iso sannu zuwa,gashi ango kuwa tun jiya babu shi babu labarinsa. Sunana gaji matar kawunsa nima nan uwarsa ce da........"
"Dan Allah gaji ya isa haka,yanzu suka shigo maimakon ki tarbesu kibasu wajen zama kuma kin tsaya kina surutun da bashida amfani"
Yanzu wata dattijuwa ce tayi magana,wacce na tabbatar itace kenan innar goje kuma surukata. Ita kam tanada kirki da kamala a ido sabanin matar data ƙira da kanta Gaji. Indai haka innarsa take to albasa batayi halin ruwa ba. Koba komai naji daɗi da innarsa ba masifaffiya bace..
Bin innar gojen mukayi zuwa ƙofarta bayan mun wuce gaji a tsaye tana mita.
Ruwa ta kawomana tareda yimana sannu dazuwa.
Gaisuwar mutunci sukayi da Baaba ladi,alamu ya nuna dama sunsan juna kenan..
Bamu daɗe da zama ba baaba ladi tace zasu tafi,yanda kuka san na jawo ta na zaunar da ita haka naji.

Please Login or Register in order to submit comment