Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kike yi".
       Pregnancy test ya d'auko ya mik'a mata" karb'a wannan je kiyi fitari a ciki ki kawo min yanzun nan".
         Jiki na b'ari ta k'arba ta tafi tayi fitsarin ta kawo.
        Kirisss ya rage ya fad'i a sakamakon ganin result d'in da yayi ba komai ne ya nuna ba illa positive yaji gaban na bugun cassa'in cassa'in, yayin da uban zufa ya dinga yanko mishi dama da hula a kanshi ya ciro yana firfirta tsabar rud'ewa ya rasa mai zai ce".
          Ido Nana ta bishi da shi cikin tsananin tsoro cuz yanayin shi ne kad'ai ya tabbatar mishi cewa da akwai matsala".
        Ba tare da yace komai ba ya d'auko hijaf ya sako mata ya shiga janta da k'arfi har suka fice cikin sa'a basu had'u da Aina ba har suka shige mota".
       Ita dai ta zauna kamar gunki bata ce mishi komai ba banda raba idon da take yi har suka iso asubiti".
         Office na Usman suka nufa cikin sa'a suka tarar da shi a zaune a kan kujera yana juyawa yana lumshe eye he is enjoying the moment.
         Ko zama baiyi ba ya ja shi waje suka fito cikin tashin hankali" i'm death friend Nana ciki ne da ita?
           "Razanennen ihu ya sake"Whatttt garin yaya ka dura mata ciki?
          "Ban sani ba...ban sani ba wallahi".
         " Kallon shi yayi cike da takaici" i have warn you akan sex babu kalar shawarar da ban baka ba ta yanda zaka dinga having sex da ita ba tare da ta d'auki ciki ba but you refused to listing yanzu wa gari ya waya".
       Fuzar da iska mai zafi yayi daga bakin shi tsabar takaici kamar ya nad'awa Datti duka ko zai huce haushi shi".
          Hawaye Datti yake sharsharrrrr" wallahi friend ban iya controlling kaina ne idan ina sex da ita kaima ka san akan ta na shi yasa da nayi yunkurin cire abun ban iya wa".
           Takaici ne ya ishe Usman jijiyoyin kanshi har tashi yake" tunda baka da control kamata yayi ka sa ma abar padlock, da mai ya saka ka ci?
           Shiru Datti yayi cikin wani irin yanayi marar misaltuwa ya rasa inda zai saka ranshi yaji dad'i babban matsalar shi d'aya yanda idan parents d'insu suka samo labari bai san wani irin fassara zasu mishi ba".
       Ganin yanda hankalin shi yake a matukar tashe Usman yace" i will help you out, yayi saurin d'ago kai yana kallon shi".
       "Dole ne a zubar da cikin nan tun kafin lokaci ya kure mana".
         Ajiyar zuciya Datti ya sake sai yanzu yaji hankalin shi ya fara kwamciya" duk da dai yana jin son cikin a ranshi amma babu yanda ya iya dole ne yayi amfani da shawarar friend d'in shi matukar yana son zaman lafiya". Da wannan shawarar suka koma Office d'in Datti na tsaye Usman ya d'auko Allura ya ja ruwa a wata kwalba gadan-gadan ya tunkare Nana. Kai take karkadawa hawaye na rolling a fuskar ta tana jan baya, ashe basu sani ba tana lab'e a bakin k'ofa tana jin abubuwan da suke fad'a. "Inalillahi wa'inna ilaihiraji'un dan Allah na rok'e ku kar ku cire min cikin nan mutuwa zanyi.....wayyo Allah Uncle karka bari a cire mana babyn mu ka gani ko zai kashe mana baby......tana ja da baya shima yana binta ta saki kuka mai cin rai. Kasa jure kukan nata yayi ya juyo da baya zai fita ta rungumo shi ta baya tana sheshshekar kuka", cakkk ya tsaya a take jikin shi yayi mugun sanyi" juyo da ita yayi ta gaban shi" baby bamu da wani choice da ya wuce mu aborting cikin nan, shine kawai kwanciyar hankalin mu.
         "A'a Uncle idan kai baka so ni ina son abuna zan raine shi na bashi tarbiya ba irin wanda ka bani ba".
         " Ranshi ne ya fara b'aci yace" wallahi ko kin so dole a cire cikin nan ba za ki tona min asiri ki saka mutuncin na ya zube a gaban iyayen mu ba, idan baki san ciwon kanki ba ni na san nawa".
        "Uncle jikin ka ne fa ta ya zaka kyamace jinin ka? Dan Allah ka bari abunda ke cikin yazo duniya".
            " Abun cikin ki k'azanta ne shege ne wanda ba ta hanyar aure aka samu ba dan haka dole a cire cikin nan".
       " Ihu ta kwalla da karfi a lokacin da Usman ya fincike ta da karfi ya raba jikin ta da na Datti.......Sai  Datti yaji kan shi ya mishi nauyi jikin shi yar suma yake yi ya runtse ido yana mai jin kukan ta na ratsa shi har cikin ranshi" Ashe akwai ranar da zata zo zai ga Nanar shi tana kuka tana neman agaji ba tare da ya kawo mata d'auki ba? Ashe akwai ranar da shi kanshi zai bada gudumawa mai tsoka wajen jefa Nanar shi cikin tashin hankali?
            Juyowa yayi da sauri da zumar ya dakatar da Usman wani b'angare na zuciyan shi ya gargad'e shi" da wani suna duniya zata kira shi azzalumi ko adali idan ta samo labari mafi muni na dura mata cikin da yayi? Da wani ido zaka kalli mahaifan ku a duk sanda labari ya iske su, saurin fita yayi jiri na d'eban shi ya dafe bango yana tafiya har cikin ranshi yana jin zafin abunda yayi mata.........
              A Office d'in kuwa Nana kuka take kamar ranta zai fita tsabar kuka har eyes d'in ta sun canja launi zuwa ja.......... Da gwiwowin ta biyu ta tsugunna a gaban Usman ta rik'e k'afafuwan shi tana magiyan ya barta" karka raba ni da baby na uban shi ya k'i shi yace shi shege ne ka barni na raine abuna na nuna mishi soyayyan da ya rasa a wajen mahaifin shi.......... Doctorrrr  *UNCLE DATTI JIKINA YAKE SO!* amma baya son gudan jinina".
            "Gyara ta yayi ta yanda zai ji dad'in zuga mata allurar yana cewa" karki ga laifin Datti dan ya so jikin ki, kece mahad'in rayuwar shi, dan haka i'm sorry Nana banda wani hanyar da zan iya taimaka miki........ yana fad'a ya hau kokarin danna mata allurar ajiki...............


*eedatou*



*💫SHINNING STARS WRITERS ASSOCIATION*

'''The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers.'''

https://m.facebook.com/110896360504039/photos/a.110896457170696/110898470503828/?type=3&source=45

🍇🍇🍇 *UNCLE DATTI*🍇🍇🍇.
                 '''JIKINA YAKE SO!'''
         

               *WRITER OF*
*1.MAGANIN MATA(DAMUWA)*
*2.WAYE MACUCI?*
*3.RAYUWAR SUMAYYA*
*4.UNCLE DATTI(JIKINA YAKE SO)!*
             
                            ©
                      *eedatou✍🏻*
'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *eedatou*   

     
        '''Masha Allah nayi matukar farincikin addu'o'in da kuma yi min da kuma tambayar lafiya ta kun nuns min Ku masoyana ne na kwarai, e.'''

                    3️⃣1️⃣—3️⃣2️⃣

Tsorone ya gama kamata ta saki wani firgiccen k'ara yayin da nunfashin ta ke k'orarin d'aukewa luuuuuuu ta tafi zata fad'i Usman yayi saurin janye allurar yana cewa" innalillahi wa'inna ilaihiraji'un duk ya fita a hayyacin shi cuz tsoro yake karta mutu a hannun shi ta b'ata mishi carrier d'in sannan kuma karyayi kisan rai.
             Gani yayi jini ya b'alle mata yana bin k'afar ta abunda kenan ya d'aga mishi yanka kan kace mai ya hada uban gumi, saboda tsabar tashin hankali ya rasa ta inda zai fara" kar dai ace ya committing suicide? Fita yayi cikin tsananin tashin hankali yana bude kofa Datti da ya had'e kai da jikin bango ya d'ago da sauri yana fad'in lafiya? Is it successful....... Maganar ta makale mishi a sanda ya had'a idanu da Usman........ Not really Nana is dying da wani irin murya ya furta maganar tare da kawar da eyes d'in shi gefe tunda yake bai taba jin dana sani ba irin ta ranar have it been bai bada gurguwar shawara ba and kuma yayi hunkurin taimaka ma abokin shi da bai jefa kanshi cikin wannan halin ba".
          Ido ya bishi da shi a tsorace ya fiddo su waje zuciyar shi kuma sai kad'awa yake a take ya jikin shi ya d'auki rawa......, bud'e baki yayi zai yi magana amma ya kasa dunkule hannun shi yayi a haukace ya shako Usman" you killed her? Ka kashe min Nana? Gara na kashe ka kowa ma ya huta idan ya so nima a kashe ni, fada yake amma kana gani ka san hankalin shi baya jikin shi.
          Kuka ne ya kwace ma Datti sosai yayi saurin sakin Usman ya hada kai da jikin bango ya saki malalacin kuka, ganin idan suka ci gaba a hakan anything can happen gashi ko kadan Usman baya son kowa ya fahimci halin da ake ciki and Datti kamar so yake ya tara mishi mutane yayi sauri jawo shi ciki.
          Ba k'aramin tashin hankali yayi ba da ya ga Nanar shi a kwance a kasa a matsayin gawa, sai yaji duk ya tsane kanshi. Rungumo ta yayi jikin shi yana kuka yana girgizata, ranar Datti ya ga tashin hankali marar misaltuwa. Hawaye ne masu uban dumi suka soma gangarowa a saman fuskarshi suke diga akan fuskarta, a hankali ta ja numfashi ta bud'e ido a hankali tana kare ma d'akin kallo......idanuwan ta ne ya sauka akan jinin da ke zubo mata a take tunanin abubuwan da suka faru ne ya dawo mata........... Shikenan sun Rana ta da baby d'inta Datti ya tsane ta tunda har ya nemi ya cutar da d'an shi da ke cikin ta, ba tare da ta d'auke idanuwan ta akan jinin ba cikin zuciyar ta tace" daddy d'inka baya sonka baya k'aunar ganin ka a duniya, ya toshe kofar da zaka shaki iskan duniya........, ta zabura ta hankad'a Datti da bai ma San da farfad'o ba cikin rashin sa'a ya buge kanshi da gefen table na Office d'in, zafin ya shige shi sosai har ya dafe gurin tare da sakin yar k'ara ashh.........ko kad'an bata ji tausayin shi ba ta hau ja da baya a firgice tana cewa i hate you! na tsane ka Datti.......bana kaunar ganin ka again.......
             Kalaman ta sun kona mishi rai sosai har ranshi yake jin zafin su fiye da zafin da kanshi ke yi mishi, Yunkurin nufar Nanan yayi yana cewa" karya kike baby baki tsane ni..., kina sona baby ......bana son wannan wasan it really hurts.
           Allah ka kuskura ka karaso nan sai na kashe ka, mugu azzalumi kawai ta saki wani irin malalacin kuka mai cin rai, a zuciyanta sai cewa take" they have succeeded in  about my baby", why Uncle......... Wannan shine soyayyar da kake ikirarin kana nuna min duk irin zaman da muka yi a baya?
       Har ranshi yake jin kukan nata ga wani uban ciwon kai da ya addabe shi lokaci guda, ba tare da ya fasa ba ya hau takowa a hankali........Usman shima dai yana jin kanshi cikin wani irin hali taimakon shi d'aya da Nanar bata mutu ba, shine yayi karfin taro Datti" baka da hankali ne? Baka jin abunda da take fad'a ne? Do you want to loose your life". Cikin tsawa yayi maganar cuz komai zai iya faruwa dan ya lura Nanar zata iya aikata fiye da abunda ta fad'a. Baka jin abunda take fad'a ne? Barni nake ta kashe ni zaifi min sauki fiye da zazzafar maganar da take fad'a". Babu yanda baiyi da Usman ba ya ki sakin shi basu san sanda Nana ta fice da sauri ta bar wajen ba.
           Tafiya take tana waigewaige kamar wata  mahaukaciya jini na d'iga daga jikin ta lokaci guda  jiri na neman d'aukan ta har ta fito kan titi kenan wani uban jiri ya d'ebe ta ta fad'i k'asa daga nan bata kuma sanin inda kanta yake ba.
         B'angaren Datti kuwa hankalin su ya tashi sosai sun duba ko ina basu ganta ba, suna cikin tafiya eyes d'in Datti ya sauka akan jinin, hannun shi har rawa yake ya nuna wa Usman.....na tabbata jinin Nana ne wannan.........,baby ina kika shiga kika barni......duk ya rikice.
          Calm down let's follow her footsteps, na tabbata baza ta b'ace mana ba. Cewar Usman kenan cikin tsananin tausayin halin da abokin nashi yake ciki. A tare suka hau bin duk inda suka ga jinin har suka fito bakin titi daga nan kuma suka tsaya cirko-cirko, hankalin su ya k'ara tashi fiye da na baya......sosai kansu ya mugun kullewa cuz basu ga wani alama da ya nuna cewa ga hanyar da ta bi ba, illa gani suka yi jinin ya tsaya a dai-dai gefen titi".
            Hawaye masu uban d'umi suka fara rolling akan fuskar Datti bai san sanda ya juyo da sauri ba Usman na kiran shi amma ina ko tsayawa bai yi ba ya nufin motar shi........ Wani irin wawan reverse yayi saura k'iris ya rage ya buge Usman ya tsaya a gaban shi yana yunkurin tsayar da shi cuz a yanda ya ga Datti ke cin uban motar anything can happen cuz ba a cikin hayyacin shi yake sarrafawa ba. Datti inaaaaa ko tsayawa bai yi ba a d'ari ya fisgo ta ta ya bar wajen da mahaukacin gudu har yana bad'a k'ura................

            Gida ya nufa ya ko gama daidaita parking bai yi ba ya nufi parlor ya banko kofan da karfi Aina na zaune akan carpet tana yankan farce ta mik'e a da sauri a kuma razane ta tsorata sosai. Ganin Datti tayi a cikin yanayin da tunda take bata tab'a ganin shi a ciki ba........sai surutai yake like he wasn't in his senses" Nana ki fito na san gida kika taho  baza ki gudu ki barni ba........dan Allah idan hiding kanki kike karna ganki dan kin tsane ni ki fito na ganki ko da sau d'aya ne nayi miki alkawarin ba zan sake tak'ura miki ba".........Zuba mishi ido Aina tayi da mugun mamaki" dear ba tare kuka fita ba ai bata dawo ba".
          What? Ya fad'a da wani irin murya yana zaro ido waje, " kina nufin kice min bata taho nan ba...... Ohhhh Aina stop please joke apart, this is not the right time to joke........  sai ya hau dube-dube ko zai  ga hanyar da Nana zata  fito".
        Ji tayi zuciyar ta ya mugun kad'awa ta had'iye miyau mai d'aci, duk da dai cewar bata fahimci abunda ke faruwa ba amma jikin ta na bata ba lafiya ba, to idan ma lafiya ne ina me yasa yake tambayar inda Nana take bayan a tare suka fito? Me yasa ya shigo gida cikin wannan halin? Cakkkk maganar ta ta mak'ale a sakamakon ganin stained na jini a gaban rigar shi ta hau bin shi da birkitaccen kallo shima bin inda take kallo yayi da sauri.......tsam bai lura da hakan ba......., Magana take yi kamar ta mai stammering tace" Ina.....ka samo wann....an? Idan kashe ta kayi kayi gaggauwan fad'a tun kafin na aikata mummunar abu akan ka".
            Kuka mai tsananin k'arfi ya kwace mata cikin sheshsheka yace" nima ban sani ba........bansan inda take ba........... Aina ki yarda da ni ban kashe ta ba".
            Idan ba kashe ta kayi ba ina ka kai min ita? Baka da wani hanya da zaka kare kanka Datti you better tell the truth.
        Inalillahi wa'inna ilaihiraji'un Aina kanki d'aya kuwa? Da bakin ki kike cewa na kashe Nana? Me ta tsare min da har zan kashe ta bacin kin san irin son da nake mata?"
       Toshe kunnuwan ta tayi cikin sauri ta fashe da wani irin malalacin kuka mai cin rai" me yasa ba zan yi zargin ka ba bayan na san cewa a tare kuka fita, and kuma ka dawo kai kad'ai ba tare da ita ba?
              "Yana jinta tana sambatu ya fice ya bar gidan ya nufi gidan su Ummi, da Aina ta san irin halin da yake ciki yayi imani ba zata tab'a jifan shi mugayen kalamai ba, cuz duk yafi kowa jin zafin rashin Nana a gare shi, ta ko ina idan ya rasa ta kamar ills ne ga rayuwar shi".
           Da taimakon Allah ya samu ya iso gidan.
          D'akin tsohuwa ya nufa ya tarar da parents din su gaba ki d'aya a d'akin suna tattaunawa.....yayin da Fu'ad ke kwance a kan carpet ya d'ora k'afa d'aya bisa d'aya yana latsa waya, fuskar shi kuma na kallon bakin kofan d'akin".
         Kallo daya Fu'ad yayi mishi ya d'auke kai kamar bai ganshi ba yaci gaba da abunda yake yi a waya". Shi kan tsamm hankalin shi baya jikin shi bai ma san da Fu'ad d'in bama balle ya damu da hakan.
            Gad'an gadan ya nufi gaban iyayen nasu da gwiwa biyu ya zube a gaban tsohuwa yana cewa" tsohuwa ina Nana take? Kinga ta boye ko ta tsane ni bata son ganina".
          Ba tsohuwa kad'ai ba hatta iyayen nasu sai da suka cika da mamaki". Baba babba yace" kaci gidan ku, kai ba'a tambaya inda take ba dan ka raina mutane kake tambayar ta?
          Ince Nanar a gidan ka take?
         Shikenan na kad'ai wallahi baba babba guduwa tayi.......Nana ta gudu ta barni babu inda ban duba ba amma ban ganta ba".
       Salati suka doka su duka tsohuwa ta rik'e hab'a tana tafawa," garin yaya hakan ta faru me kayi mata ta gudu? Cewar Umma kenan ta mik'e a fusace tayi maganar.
        " Ummaa ku yafe min a halin yanzu ba zan iya fad'an mugun abubuwan da na aikata muku ba.......na cuce ku na cuce ka ina..........ba zan yafe ma ka ina a bisa abunda na aikata ba".
             Umma da zuciya ya gama d'iban ta ta kai hannu zata kwala mishi mari Alhaji yayi saurin dakatar da ita. Koma ki zauna Umman Datti ba za aiyi abu cikin fushi ba. Baza ta iya jayyaya da shi ba tana ganin girman shi ko ba komai mahaifine a gare ta tunda uban mijin ta ne, ba dan ta so ba ta koma ta zauna tana jan kwafa" ai raini ni ne ban da haka me yasa zai dubi saban  idon su yace ba zai iya fad'an musu abunda ke faruwa ba?
         Baba babba ma ji yake kamar ya kai mishi bugu wata kila idan yaci uban shi da kyau zaiyi bayani". Fu'ad kam bai san sanda ya mik'e ya shak'o kwalan rigar Datti ba duk irin tsawar da Alhaji yayi hakan bai hana ya sake shi ba, aka hau bam-bare Datti daga jikin shi" wallahi k'arya kake.... Kayi kad'an ka salwantar da rayuwar Nana ......dole you must pay for it".
           "Enough baba k'arami ya daka mishi tsawa yayi saurin sakin Dattin jikin shi na kad'awa....... Baba karami ba dan na san cewa kaine mahaifin Nana ba da cewa zanyi tsintota kuka yi? Kai da Ummi kun cuce Nana da kuka bada yardar ku ma Datti........ I warn you several times without number amma ga irin ta nan yanzu wa gari ya shafa? Ku sani baku ji komai ba tukunna sai zuwa gaba zaku yi dana sani wanda zai zamo marar amfani". Yana gama fad'a yayi hanyar d'akin shi ya had'a kai da jikin bango yana rusar kuka".
            Ba komai ne ya tsaka shi hakan ba illa tsananin tausayin Nana da ya gama mamaye ilahirin bargon jikin shi.......Allah yayi gaskiya da yace idan zaka so mutum kaso shi d'an dai-dai, idan zaka k'i mutum ka k'i shi dan dai-dai masoyi na iya zama makiyi haka zalika makiyi na iya zama masoyi, gashi duk irin soyayyar da Datti yake ikirarin yana nuna wa Nana he end of hurting  and ruined her life.
            Magana yake a k'asan zuciyar shi" Duk inda kike ina tare da ke Nana idan bana tare da ke zuciya ta na tare da ke na kudurta a raina sai na kwace miki hakkin ki, ko ta wani hanya sai na ka amsa laifin ka Datti,, da ka ki da ka so sai na fallasa asirinka".........

         Bangaren Nana kuwa satin ta biyu tayi ba tare da ta san inda kanta yake ba a lokacin babu irin cigiyar da su baba Babba nasu bayar ba a kafafen yad'a labarai, har hotunan ta an buga a jarida sannan kuma ana haskawa a akwatin talabijin amma ba wani takamammen amsa da zai bada tabbacin an gano inda take".
          Datti ya birkice ya koma wani iri magana d'aya biyu zai yi sai ya had'a da sunan ta suma mutanen gida hankalin su ya tashi sosai, Ummi wani sa'in ta fake idon su Umma ta lab'e a wajen da babu mai ganin ta tayi ta rusar kuka, addu'a iya addu'a suke yi kuma suka bada taimako almajirai na taya su yi, Aina ma ansha fama da ita sosai dan sai da ta tattara ta koma gidan har zuwa yanzu  cewa take Datti ne ya kashe Nana ta d'auki k'aran tsana ta d'ora mishi, ta wajen Aina baya samun sauki haka ta bangaren zuciyar shi ma dafi ne na rashin babyn shi, ga wani mugun sha'awar ta da yake mugun bijire mishi har yana jin cikin shi nayi mishi ciwo time-time. Ko kad'an bai bari iyayen shi sun fahimci halin da yake ciki ba cuz idan suka gano cewa sha'awa na damun shi zasu suspecting d'in shi k'arshe ma dole su yarda da abubuwan da Nana take fad'a a kanshi idan kuma hakan ya faru dole kowa ya tsane shi.
          Dana sani iya dana sani yayi kan muguwar kaddarar shi ji yayi ma da ace sha'awar ne ma kwatata baya ji da yafi mishi sauki kan ace sai mace d'aya take iya biyan mishi bukatun shi". 
          
         Sai da Nana ta shafe wajen sati biyu da kwana hud'u kafin nan ta farfad'o ta bud'e ido a hakali tana kallon wuri......yunkurin mik'ewa tayi taji kanta nayi mata wani irin zogi tayi saurin dafewa da sauri sai ga hawaye na bin kuncinta. Tunowa tayi da abunda ya faru da ita ta matso hawaye mai uban d'umi Shikenan Datti yayi nasarar zubar mata da cikin ta, she lost her baby,  wani irin rashin imani ne ace at this early edges of hers abubuwa na faruwa da ita beyond her expectations, she didn't deserved this at all, rayuwar da zo mata b'aragurbi wanda ake k'ira bahaguwar rayuwa". He puts her through much pains da kwakwalwar ta sunyi kad'an su d'auka.
        Tana cikin tunanin ne taji muryar wata mata tsohuwa wacce tayi sa'an k'akarta tsohuwa tana cewa sannnu baiwar Allah, masha Allah kai mun gode ma Allah da ya saka kika farfad'o lafiya..............., hawaye ne ya mak'ale a fuskan ta na tare da ta furta komai ba ta d'ago mata.
            Abinci matar tasa aka kawo mata mai ji da lafiya ta taimaka mata ta kaita band'aki tayi brush tare da sheka wanka ta fito sai taji kamar yan

Please Login or Register in order to submit comment