Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zare mata kaya wani iskan dad'i ne ya soma shigan jikin ta ta lumshe ido ta bud'e a hankali tare da nemo towel ta d'aura a k'ugun ta ta fito.
          Ga mamakin ta ta ga har matar ta fito mata da sabbin English wears guda biyu duka dogayen riguna, hannu ta mik'a ta d'auki d'aya daga ciki ta saka, sosai tayi mamakin yanda aka yi matar ta kawo mata kaya dai-dai size d'inta Tana gama sakawa taji an bud'e kofan an shigo, matar ce ta ta shigo dan ta duba ko ta gama, muje kici abinci na san zuciyar ki cike da tambayoyi kafin na amsa miki nafi son kici ki k'oshi", babu musu ta bi bayan matar suka fita tana gaba Nana na bin ta a baya har dinning area.
        Makeken gida ne na gani na fad'a ko mai na gidan rassssss tsayawa fad'an kyau da tsaruwan gidan ma b'ata lokacin ne an kashe dukiya iya dukiya komai na gidan was well arranged.
           Tun daga nesa take jin kamshin abincin duk ya cika mata hanci, sai taji wani irin mugun yunwa ya addabe ta kamar taci babu".
           Kujera matar ta jawo mata tace zauna a nan itama ta jawo ta zauna ta hau serving din ta ita dama a koshe take shiyasa wa Nanar kad'ai ta saka, ba shiri Nana ta hau kaftar abinci tana ci sai tausayin ta ya kama matar ai dole ta dinga dagargazar abincin cuz tunda aka kawo ta gidan banda drip babu abunda take sha".
            Sai da ta cinye tass kafin taji cikin ta ya k'oshi ta kora da ruwa tayi gyatsa matar tace" a k'aro miki ne?
          Da tsiririyar muryar ta tace" na koshi".
          Parlour suka koma suka zauna Nana dai Allah-Allah take matar ta fad'a mata yanda akayi ta tsinci kanta a gidan amma ta kasa tambayar ta da matar ta fuskanci hakan tayi murmushi cikin zolaya tace" da kin kwantar da hankalin ki yammata ba gidan yanka mutane kike ba, na ga kin zaku ki san yanda aka yi ki zo gidan nan ko? To bari na baki labari, ta gyara zama Nana ta gyara zama itama kafin nan ta fad'a bayani kamar haka " sunana Sumaiya amma ana k'irana da inna, nayi aure da mijina tunda muke bamu tab'a samun haihuwa ba har mijin nawa ya koma ga Allah". Kafin mijina ya rasu hamshakin mai kud'i ne na gaske bayan rasuwar shi dangin shi suka kwashe komai da ya mallaka suka rik'e na takaita miki na sha fama sosai da wahalar rayuwa kafin nan Allah ya had'a ni wani yaron kirki shi yayi sanadiyan zama na a nan  a matsayin na dinga kula da ke, tunda aka kawo ki gidan nan yake hidimar jinyar ki doctor ne ya neman miki na musamman har gida yake zuwa duba ki, jinyar sati d'aya cikakkiya aka yi miki kafin nan aka shawo kan matsalar, likitan ya tabbatar mana cewa a kowa lokaci zaki iya farfadowa kuma insha  Allah baza ki farfad'o da wata matsala ba Alhamdulillah sai gashi kin farfado lafiya.
         Shiru tayi ta mik'e a hankali ta d'au goran ruwan faro a fridie Nana na bin ta da ido ta b'alla ta sha kafin nan ta rufe murfin ta d'ora a kan table ta koma ta zauna. Haka yayi ta faman jinyar ki sau d'aya yake zuwa a rana yana duba lafiyar ki tun da nake bai tab'a fad'a min sunan shi ba kuma nima ban tambaya ba.........., da dai naga baida niyan fad'a min da kai na na tunkara mishi yace min"ammintacce", da sunan zan dinga k'iran shi kenan. Jira ni ina zuwa ta fad'a ta mik'e ta shige d'akin da yake a matsayin mallakin ta ta fito ta wasu takardu guda hudu d'auke da rubutu a jiki ta mik'a wa Nana"  Ga wanan shi ya bani yace a duk sanda kika farfad'o na baki. Hannu Nana ta mik'a ta karba takardar zuciyan ta cike da tunanin wannan bawan Allah da ya taimake ta,, haka suka yi ta zama inna na bata labari tun tana nokewa har ta d'an saki jiki da ita, ba laifi matar tana da kirki sosai.
          Da daddare d'akin da ta farfad'o ta ganta a ciki shi ta nufa tayi lamo akan gado ta fara yunkurin bud'e takardar d'aya bayan d'aya, har ta warware duka sai ta fasa ta ninke ta ajiye cuz a halin yanzu bata da lokacin da zata karantawa ta koma ta kwanta da tunani kala-kala a kasan zuciyar ta zata so ta san. *WAYE WANNAN MUTUMIN DA YA BOYE SUNAN SHI YA KIRA KANSHI DA AMMINTACCE?* *ME NENE DALILIN DA YA SA YA TAIMAKEcomment
          Kwanan ta hud'u a gidan ba tare da ta had'a ido da Ammintacce ba, da ta gaji da zuba ido ta tambaye Inna" wai wannan mutumin baya bayyana kanshi ne? Dariya inna tayi tace" kece dai kawai bakya ganin shi amma ko d'azu da kike d'aki ya shigo kuma ya tambaya lafiyar ki, nace mishi mishi kin farfad'o ma".
          Hmmmmm Inna wannan mutumin da ban ala'jabi yake ace har yau ban san wa ke taimakona ba?
           "Ke dai bari kawai nima dai da farko lamarin shi tsoro yake bani daga baya kuma na fahimce shi mutum ne mai saukin kai marar son fitina".
          Don Allah Inna idan mutumin nan ya sake zuwa ko me nake yi ki had'a ni da shi".
           " To idan har ya ammince da hakan babu matsala.
           Washe gari da safe bayan sunyi breakfast Nana na kwance a akan kujerar three seater tayi pillow da cinyar Inna, suna hirar su, a cikin kwanakin sun saba sosai har Nana ta kan manta wasu abubuwan da suke damunta duk da dai cewar har yanzu da gurbin mik'in da ke fame a heart d'inta.
          Inno hawaye ne ya gangaro saman tsiririyar fuskarta, Inna taji d'umin hawaye ta mirgina kan Nana tace" Subahanalillah? Y'ar nan me ya faru kike kuka?
         " Wa ya tab'an min ke? duk ta rikice.
        Maimakon da ta amsa mata sai ta hau sheshshek'ar kuka hankalin tsohuwa ya dad'a tashi" Ya salam! don Allah kiyi ma Allah ki fad'a min idan da wani abu da nake yi miki wanda bakya so sai na daina".
          Ganin yanda hankalin Inna ya tashi sosai ta share hawayen ta" babu komai Inna ina so naje gida ne, ina son ganin Ummana".
          Shiru Inno tayi ta sani da gaskiyar Nana duk inda take dole tayi kewan mahaifanta amma  a halin yanzu bata da ikon da zata bata izinin tafiya, da ita da Nanar duk a karkashin wani suke".
           Cikin hikima tace" kwantar da hankalin ki idan ammintacce ya zo zan fad'a mishi, insha Allah zai maida ki gida kamar yanda kika bukata.
         Da wannan tunanin ta samu har Nana ta hakura ta tsaida kukan, zama suka yi shiru-shiru bai shigo ba gashi yanzu wajen k'arfe biyar na yamma.
          B'angaren Ammintacce kuwa yau tun safe ya ke son ya ga ammanar shi amma ba hali abubuwa sun d'an shige mishi gaba hakan ya saka bai samu daman shigowa da wuri ba, sai wajen k'arfe tara da rabi ya samu daman isowa gidan a lokacin har Nana ta gaji da jiran tsammanin fatu tana gyangyad'i Inna ta raka ta d'aki ta kwanta".
         Shigowan shi ciki yayi dai-dai da lokacin da inna ta juyo kenan zata koma d'akin ganin shi da tayi ta hau washe baki tana gaishe shi, cikin girmamawa ya amsa mata.
            "Ya amanata Inna? Da fatan bata yi miki rigima"?
          " Murmushi tayi cikin jin dad'in yanda yake ganin girmanta tace" hmmmm ammanar ka na nan lafiya cikin amminci sai dai yau ta so ta bani matsala yau".
          Fitina ta sakar mini har da kuka wai tana son ganin Umman ta".
         Shiru yayi for some minutes yana tunani sai ya mik'e yace ina zuwa, ya sa kai ya shige d'akin.
          A kwance ya tarar da ita barci ya fara d'aukan ta, ya zauna a gefen bed d'in in a cool voice din shi cikin barcin ta taji muryar shi yana cewa" *BA YANZU ZAKI KOMA GIDA BA IDAN LOKACI YAYI DA KAINA ZAN TAIMAKA MIKI WAJEN HAD'A KI DA MAHAIIFAN KI"*, ya bada baya zai fita kenan ta mik'e a zabure kafin ta kai ga tsaida shi tuni ya fice daga d'akin yayi sallama da tsohuwa ya fita, cikin rashin sa'a ta fito ta tarar babu shi, tsohuwa kad'ai ta gani a parlourn ta koma tana maida numfashi da kyerrrrrrr har sai da tsohuwa tace lafiya kike irin wannan numfashin?
       Innaaaa sai ido muryar da taji ya rikita ta sosai idan ba mafarki take yi ba ta so ta gane mai irin muryar nan. "Ammintacce", ta furta da wani irin dishashshiyar murya, wani buri yake da shi akan ta wanda yake son cimmawa?
          Anya bata kuma fad'awa wani mugun tarkon d'a namiji ba? Me yasa bai  bayyana mata ko shi wanene  ba da dalilin da yasa ya boye ainihin sunan shi, yake amfani da " Ammintacce a matsayin sunan shi"?
 

Pls share votes and comment

*eedatou*
   


*💫SHINNING STARS WRITERS ASSOCIATION*

'''The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers.'''

https://m.facebook.com/110896360504039/photos/a.110896457170696/110898470503828/?type=3&source=45

🍇🍇🍇 *UNCLE DATTI*🍇🍇🍇.
                 '''JIKINA YAKE SO!'''
         

               *WRITER OF*
*1.MAGANIN MATA(DAMUWA)*
*2.WAYE MACUCI?*
*3.RAYUWAR SUMAYYA*
*4.UNCLE DATTI(JIKINA YAKE SO)!*
             
                            ©
                      *eedatou✍🏻*
'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *eedatou*   

~Comments d'inku na jiya sun rikirkitana ni, wannan page kyauta ne na ware ma dukkan masoyana💘💘~

                     3️⃣3️⃣—3️⃣4️⃣

Tana cikin wannan tunanin taji an dafata kafad'an ta ta baya, ko ba'a a fad'a mata ba ta san cewa Inna ce, fuskarta tafffffff da hawaye ta juyo tana kallon ta, hanken da ke gauraye da illahirin parlourn ne ya Inna ta fahimci halin da take ciki".
          Girgiza mata kai Inna tayi alamar kar tayi kuka amma ina kuka ya kwace mata ta shige jikin Inna tana sheshek'ar kuka". Ummana Inna, ina so na ganta na san a duk inda take hankalin ta a matuk'ar tashe yake, idan zanyi fushi da kowa bazan iya yi da ita ba".
            Bayan ta Inna ta hau bugawa cikin hikima tana zancen zuci, ita kanta zata so ace an sada yarinyar nan da mahaifan ta amma ganin yanda Ammjntacce ya fice da kuma yanayin Nana ya tabbatar mata da cewa bai ammince da bukatar Nanar ba".
         "Kiyi hakuri kici gaba da zama damu Nana Allah shi yasan nufin hakan, idan da rabo wata rana zaki koma ga iyayen ki".
            Sai da ta ci kuka son ranta kafin ta share hawaye ta dubi inna cikin kuncin zuciya tace" Don Allah a wani gari nake yanzu? "Hmmm Nana ba hurumi na bane na fad'a miki garin da kike, ni dai aikina a nan na baki dukkan kulawan da kike bukata".
         Zata kuma yin wata tambayar Inna ta ja hannun ta da sauri muje ki kwanta dare ya fara nisa", ba dan ranta ya so ba tabi bayan ta suka shige d'akin ta.
         Makeken gadon ta ta hau ta kwanta Inna ta d'auko bargo ta rufa ta dashi kasancewar hunturu ne ana sanyi sosai  yasa tayi hakan cuz bata son sanyi ya cutar da lafiyan ta", ta koma ta zaune a gefen gadon tana mata hira can kuma  barci ya fara d'aukan ta tana gyangyad'i
          Sai tausayin ta ya kama Nana ta san cewa duk dan tsaron lafiyar ta take yi, cikin hikima ta lumshe idanuwan kamar mai barci komai ne yasa ta hakan ba sai dai dan ta ba ma Inna damar da zata je ta kwanta tayi barci, bayan haka itama kanta Nanar tana bukatar kad'aici".
              Inna dai na nan a haka idan ta gyangyad'a sai ta bud'e ido, da dai taga alamar barci ya d'auke Nanar tayi mata addu'ar barci ta fita tare da rufa mata k'ofa, ta nufi d'akin ta ta kwanta ta hau sharara barci abin ta.
       B'angaren Nana tana ganin Inna ta bar d'akin ta mik'e a hankali ta zira k'afarta ta a k'asa ta taso a hankali tana takawa taje jikin tagar d'akin tana lek'awa, dan k'arfin hali duk da tana jin sanyi na ratsa ta, jikin ta na  rawar sanyi  kattt katttt katttt bata yi yunk'urin kare kanta ba ko tsoron dare bata ji ba balle taji darrrrr a ziciyan ta ta fara tunanin kar tayi gamo......ance tsananin bakin ciki na cire tsoro idan mutum yaji tsoro to bai had'u da bakin ciki bane tabass hakan ya faru ga Nana a wannan lokacin."
           Hawaye ne masu uban dumi suka hau zubowa ta kasa tsaida su  zuciyan ta falllll cike take da tunanin........tayi dana sani mai tarin yawa na ba ma Datti kanta da tayi, duk da dai ta san cewa a lokacin bata da wata cikakkiyar wayo amma duk da hakan sai da taji haushi da zafin  kanta na sakin jiki da tayi da tayi da shi sosai, ta bashi damar da zai sarrafa ta ya driving d'inta to his test".
           Tsiraren hawaye suka sake yankoma mata da ta tuna da Auntyn ta Aina, wata k'ila alhakin ta cin amanar da tayi mata ne yake binta gashi nan an killace ta a gida da bata san ko na wanene ba bata da damar fita". Kaiiiiii ba zai yihu ba ko ta halin yaya sai ta nemo hanyar guduwa baza ta ci gaba da zama a gidan shi ba cuz bata san wani irin buri yake so ya cimma akanta ba".
          Wannan dare ko runtsawa Nana bata yi ba banda aikin kuka babu abunda take yi har sai da taji kanta ya fara yi mata ciwo kafin nan ta hak'ura ta koma ta kwanta.
          Da safe bayan ta idar da sallah ta nufi d'akin Inna har kasa ta tsuguna ta gaishe ta ta amsa mata".
          Tana lura da yanda fuskar Nanar yayi luhu-luhu alamar taci kuka sosai daren jira, Inna ta d'an had'e rai tace wato baza ki hakura ki saka wa kan ki salama ba? Yanzu haka kike so ki ta zama kina kuka? Gaskiya idan kina haka baza mu shirya ba tsammm banji dad'in haka ba sai ki saka na fara zargin cewa da wani abu da nake miki wanda bakya so amma kin kasa fad'a".
           "Ganin yanda ranta ya fara baci ta hau fad'a sai ta hau bata hak'uri tare da yi mata alkawarin baza ta sake yin kukan ba".

         B'angaren Datti iya wuya hankali ya gama tashi sai baza ido suke yi a kafafen yad'a labarai amma shiru, Fu'ad ma yayi iya nashi kokarin na bada guduma dan nemo inda sahibar shi take abu amma abu yaci tura, tsakanin shi da d'an uwan shi babu wani kyakkyar alaka da ace baiyi halin b'eran ci ba da babu abunda zai saka su cikin wannan halin". Kuka iya kuka yake yi a duk sanda tunanin ta ya fad'o mishi a rai sai yaji duk duniya babu wanda ya tsana kamar Datti.
         Su Umma da Abba duk sun juya mishi baya, Alhaji ma ya fita harkan shi anyi anyi ya fad'a laifin da ya aikata amma ya ki hakan ya dad'a hasala su". A b'angaren k'anwar shi ce kadai da Ummi da kuma baba karami yake samun sauki amma duk da halin da yake ciki kowa yayi banza dashi, ai ba yaro bane da har za'a ta tambayar shi yana raina wa mutane wayo".
         Idan ya shigo d'akin tsohuwa cewa yake su neman mishi Nana idan ba haka ba shima guduwa zaiyi ya shiga duniya, ko tausayi baya bata tayi mishi tatasss da zagi"shi yayi sanadiyar gudun shi zai nemo ta ai shi ya san sirrin da ke b'oye wanda ya kasa bayyana wa".
          Itama Aina bata ragar mishi ko kad'an babu kalar habaice-habaicen da bata yi mishi ta mata da cewa a baya dear d'inta ne wanda ta d'auki dukkan yardar ta ta d'ora mishi".
          Duk da irin mugun haushin shi da take ji ko da wasa bata fad'a wa su baba Babba cewa kashe Nana yayi ba........, ta zuba mishi ido ne har zuwa tsawon lokacin da zai d'auka da kanshi ya fallasa komai.
         Wata ranar Alhamis da rana da misalin karfe d'aya Fu'ad ne ya shigo d'akin tsohuwa za shi wajen Aina kasancewar tunda ta koma gidan a b'angaren tsohuwa take zama. Tarar da ita yayi akan kujera ta d'aga ido tana kallon ceiling hankalin ta baya jikin ta bata san ma ya shigo ba har ya nemi wuri ya zauna. Jin motsin mutum a kusa da ita ya sa ta saurin d'agowa ta dube shi tana had'a ido da shi hawayen da take kokarin mak'alewa suka samu daman gangarowa saman cute face d'inta".
           "Yanzu shikenan Fu'ad Nana ta barmu kenan har abada? Ba mu ba sake had'a ido da ita? Shikenan ya kashe mana Nanar mu? Maganar ta dake shi sosai a zuciya sai ji yayi shima hawaye ya hau zubo mishi, a yanda take maganar duk ta karye mishi zuciya".
        Cikin dishashiyar murya yace" Kin ga gawar ta ne? Ko kinji labarin wanda ya samo gawar ta? Tayi saurin girgiza mishi kai".
          "Me yasa kike zargin cewa ta mutu bayan ba ki da wata cikakkiyar shaida akan haka".
         " Share hawayen ta tayi ta ta d'au hanky a gefen kujerar ta fece majina murya na breaking tace" Baka.....ga.... ab......n da na.....ga..ni ba Fu'a....d, da ido......na naga jiki a Jikin Datti, ya shigo shi kad'ai bacin tare suka fita, wan......nan hujjar kad'ai ya tab.......batar min cewa mutu.......wa tayi ku.....ma shi ya kashe ta........
           Shiru yayi shi kad'ai tare da hard'e hannayen shi yana nazartar kalaman ta har ta gama.........Tabbass akwai k'amshin gaskiya a maganar Aunty Aina dole d'an uwan shi na da hannu akan b'atan Nana........., dole ne ya zurfafa bincike ya gano gaskiya idan har Datti yana da hannu akan b'atan Nana sai yayi sanadiyar yankewar jin dad'in rayuwar shi".
          " Mik'ewa yayi yace" babu komai Aunty insha Allah sai na bi dukkan wata hanyar da zan bi na kwato mata y'ancin ta wannan alkawari ne".
          "Kana ganin zaka iya?"
      Indai akan Nana ne zan iya yin komai ki kwantar da hankalin ki ba zai ci bulus ba he must pay for it", yana gama fad'a ya sa kai ya fita".
          A main parlour suka had'u da Umma Datti ya tusa ta a gaba yana mata sambatu har taji zuciyar ta ya fara cika da tausayin shi shine ta sa kai ta fita ta bar mishi d'akin".
            "Yauwa Fu'ad dama kai nake nema", yayi saurin karasowa ya zauna a kan kujera ya sadda kanshi kasa yana wasa da farcen yatsan kafar shi.
          Zama tayi a gefen shi ta kafe shi da ido cikin tuhuma" maganganun da ka fad'a ranar sun rikita min tunani musamman da naji kana cewa bamu yi dana sani yanzu ba, sai zuwa gaba zamuyi, d'an uwan ka ma yak'i fad'a mana laifin da ya aikata har yayi sanadiyar guduwan Nana ta barmu, don Allah idan akwai wani abu da kuke b'oye mana ku fito fili ku fad'a mana".
          Idanuwan shi ne suka kad'a zuwa launin ja ya d'ago kai yana kallon mahaifiyar shi da rinannun idanuwan shi wanda babu alaman fari a ciki".
               "Ummaaaa", kiyi hakuri nima ba zan iya fad'a miki komai ba a halin yanzu, a baya babu irin shawarwarin da ban baku ba kuka yi banza dani, idan mai laifi bai amsa laifin da yayi ba ba zaku gamsu da abubuwan da zan fad'a muku ba cuz a baya ma ba d'aukawa kuka yi ba, and kuma banda shaidar da zan tabbatar muku da ita".
          Dogon numfashi ta ja ta sauk'e a hankali" shikenan tashi ku tafi amma ka sani kai da d'an uwanka kun jefa zukatan mu cikin zullumi".
         Mik'ewa yayi za shi d'aki dai-dai lokacin Datti ya fito daga d'akin Umma cuz ya gaji da zaman jiran ta hakan yasa ya fito ko zai ganta".
           Fu'ad ya ga yanda ya zafge ya rame har ya fara kashin wuya idanuwan shi sun fito waje sosai, tsaki mai k'arfi ya ja yayi shigewan shi ko ufan bai ce mishi ba sai ma cewa yayi d'an ba k'ara ba yace abun nashi ba saiti ba ya samu yarinya yana ta danna mata ga irin ta nan, akwai  ranar kin dillacin".
         Ko ta kanshi Datti bai bi ba domin bai da lokacin da zai tsaya yana kula Fu'ad bayan da nashi matsalar da tafi komai d'aga mishi hankali.
       Zai yi wajen Umma ta d'aga mishi hannu" ka kuskura ka k'araso nan sai ka had'u da fushi na, haka ya mak'ure a guri d'aya hawaye na rolling a saman fuskar shi d'aya bayan d'aya".
          Da ta gaji da ganin shi a cikin wannan halin ta tashi ta bar shi a wajen,  haka yayi ta tsayuwa da ya gaji ya fita ya bar gidan tunda basa tausayin shi bayan ya fisu jin zafin rashin babyn shi mai d'auke mishi lalurar shi, ta tafi ta bar shi da tsananin kewan ta da na dumin jikin ta sannan kuma ga garuwar da yayi kullum cikin radadin rashin ganin ta.
        Cikin dare Aina ta fito main parlour she was taste a lokacin and babu ruwan sha a fridge d'in tsohuwa gashi baza ta iya hakuri har zuwa safiya kafin ta sha ba kawai ta fito ta hamma ta nufi fridge d'in, har ta d'auka zata koma taji motsin mutum a bayan ta. Datti ne da tun shigowa ta yake kwance ciwon ciki ya addabe shi ya rik'e ciki yana murd'e murd'e shi kad'ai".
          Tana had'a ido da shi ta tamke fuska kamar yana ganin ta tayi sauri zata bar wajen dai-dai lokacin cikin shi yayi wani irin murd'awa zufa ya fara sassako mishi cuz of tsabar azabar da cikin ke yi mishi, cikin sarkewar murya yace" help Aina i'm dying ".
            Juyowa tayi da baya zata tafi ta ga ya rarrafo ya rik'e k'asan rigar ta da wani irin dishashshiyar murya nana jan numfashi da kyar yace" please ki taimaka min mutuwa zanyi", ciki na ciwo wife, karki tafi ki barni cikin wannan halin".
       Jikin ta ne yayi mugun sanyi a sanyaye ta d'ago ta dube shi sai taji zuciyar ta ta karaya sosai, he

Please Login or Register in order to submit comment