Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

koma d'aki yana jin pains a k'ahon zuciyan shi.
       Da daddare kusan kwana zaune mutanen gidan suka yi musamman mutane ukun nan.
        Washe gari kuwa iyayen nasu suka sake k'iran meeting bayan an gama hallara baba babba yace ya maganar su ta jiya ta kwana? Shin an samu wanda zai yi sacrifice ya janye ma d'an uwan shi?
        Duka su biyun suka yi shiru ganin haka sai iyayen nasu suka fahimci dai cewa kowa na kan bakan shi na auren ta.
        Kan kace me sai gasu sun had'a zufa tafffff hatta tsohuwa ma bini-bini take sharar hawaye tace" ja'irai kawai kun jefa mu cikin damuwa wallahi ko barci bama iyawa........da ku mayuwa kuna kama mutum tuni zaku cinye shi., tana yi tana sharar kwalla.
      Alhaji ne yayi gyaran murya sai da ya natsa kafin nan ya dubi Nana da ta sadda kanta ta kasa d'agawa tana wasa da yatsun hannun ta, da zaka binciki kasan zuciyar ta damuwa ne yayi mata yawa shi ya sa ta yin hakan.
         B'angaren ki fa akwai wa da kika zab'a ko kuma har yanzu babu mafita?
       Sai ta girgiza mishi kai alamar a'a babu".
        Numfashi ya ja mai nauyin gaske ya sauk'e a hankali sai yayi jimmm kad'an yana nazari can kuma yace" Tunda dukan an rasa wanda zai sadaukar ma d'an uwan shi, kema Nana kin ki zab'ar wanda kike so ina so ki bani zab'i kuma ina fata duk wanda na zabar miki zaki aminta da shi.
          Mugun bugu zuciyoyin su su ukun suka yi a tare ko wanne na tsoron kar d'an uwan shi za'a bawa a hana shi.
     Kai ta gyad'a mishi tare da sharo hawayen alamar ta amince.
       "Shikenan ku tashi ku tafi, Datti da Fu'ad ina so duk wanda ya rasa ya d'auki komai a matsayin k'addara Allah zai yi mishi zab'i da mafi alkhairi......., ba wai dan mun fi son wanda muka zabar mata bane ya sa muka yi hakan dukan ku matsayin ku guda ne baza mu so wani mu k'i wani ba, ko Datti da kwanaki muka yi maka hukunci dan mu natsar da kai muka yi ba wai dan mun ki ka ba dan haka duk sunan da kuka ji an ambata a wajen d'aurin auren d'ayan ku yayi hak'uri".
         Ba dan ransu ya so ba suka fita suna tunanin anya zasu d'auki k'addarar rashin ta kuwa? 
       Daren ranar ya kasance rana mafi muni a gare su gaba ki d'aya family d'in cuz ranar ta zamar musu cike da fargaba, tsananin rud'ani...., rikici mai tsananin gaske..... tsarkakiya......ranar da kowa zuciyar shi ke cike tsoron tunkarar wucewan ta.
        Da ace Datti da Fu'ad na da ikon hana wucewan wannan dare da sun jima da yi saboda tsoron abunda za su bud'e ido su tarar da  shi.
          Washe gari da safe mutanne har sun fara hallara a cikin gidan ana shirye-shiryen d'aurin aure.......Fu'ad tun kafin gari ya gama wayewa ya shiga d'akin Nana ya ta ita a a kwance cikin bargo duk eyes d'in ta sunyi luhu-luhu sun dafe alamar taci kuka sosai d'in nan har zazzab'i ya fara kama ta.
          K'amshin turaren shi taji ta bud'e ido a hankali ta zabura ta mik'e da saurin" Ya Fu'ad na shiga uku za'a aura min miji ban san ko wanene aka zabar min ba........, kaine mafita a lokacin da duhu ya bayyana a gare ni kaine kake yaye min........, kaine Ammintacce na mai tsamo ni a cikin dukka wani bala'in da ya kunno min kaiiiiii,
           Kamar yanda ka zamar min Amintaccen nan na baya wanda ya cece ni, ya taimaka min da iyakacin iyawar shi.......don Allah ya Fu'ad ka zamar min Amintacce a yanzu ka fidda ni daga cikin matsalar da nake ciki.........,ina tsananin fargabar wanda za'a bani a matsayin mijina.
         Runtse idanuwa yayi ya bud'e a hankali har ranshi yake jin kukan nata na ratsa shi.........muryar shi na cracking yace" kiyi hak'iri na zo muyi bankwana ne......., ki sani ba lallai ne na dawwama a matsayin Amintacce ki ba..........wannan k'aron abu ya juya salo yanzu bani da k'arfin da zan baki kariya.......kiyi hakuri da duk zab'in da kika ga an miki har abada ba zan daina son ki ba..........yana gama fad'a ya mik'e ya fita yana sharar kwalla, tana ji tana gani Fu'ad ya tafi, tafiyan da ta san ba lallai ne su had'u a matsayin masoya ba.......
       Fu'ad na barin ta d'akin shi nufa ya d'auko car key d'in shi ya fito ya ya kashe wayan shi saboda kar ma a kira shi balle yaji abunda zai d'aga mishi hankali haka ya bar gidan cuz ba zai jure ganin an d'aura auren Nana da wani ba balle ace akaita gidan wani ba, gudu yake ta zafgawa a titin kamar zai tashi sama duk inda ya gifta a motan sai ya bad'a wa mutane k'ura........, da haka har ya kawo wajen da yake so ya je ya nemi guri a gefen  titi ya parking ya fito ya zauna a saman motar shi, yayin da sanyin huturun da ke kad'awa a hankali ya ratsa jikin shi.
         "Yanzu Nana ba lallai ne ta zamu nashi ba? " Idan ya rasa ta ya zai yi da rayuwan shi bayan ya d'auki son duniya ya d'ora mata?
       "Shi dai ya cire rai da samun Nana domin ya tabbata ba lallai ne a bashi ba.
        B'angaren Datti ma tun safe ya d'auki Sadeeq suka bar gidan ya kashe wayan shi, Usman yayi mishi fad'a sosai da hakan ya tursasa shi lallai lallai sai sun tafi amma sai ya k'afe yace babu inda zai je, haka Usman ya halacci gurin d'aurin aure yana ma abokin nashi fatan samun nasara.
Gudun kar Usman d'in yaje ya jiyo mishi mugun abu yayi zumburrr mik'e ya d'au d'an shi suka bar gidan ba tare da kowa ya san inda suke ba......ya saka Sadeeq a gaba yana kuka wi-wi da hawayen shi yana surutai kala-kala" mamanar ka zata yi mana nisan da har abada baza mu cimma ta ba......., shi kenan mun yi loosing d'in ta".
          "Nana ta zame min magani amma kaddara ta k'i had'a mu ban san ko sai na koma ga mahaliccina ba kafin nan mu had'u a matsayin ma'aurata da ita. Haka yaci gaba da kukan shi yaron na kallon shi kamar zai taya uban kuka.
        Mutanen gida sai faman k'iran layin su ake yi dukkkk a kashe, tun ana saka ran ganin su abu yaci tura har mutane suka gaji da zaman jira wani aminin Alhaji ya lek'a  me ake jira ba'a fito ba an shanya mutane a waje, a sannan ne suka fiffiito aka fara gudanar da daurin aure.
Kamal da Usman sun yi cirko cirko ko wannen shi na so abokin shi ne jarumin da zai mallake Nana sai aikin harara suke sakar ma junan kamar idanuwan su zai tsiyayo, kowannen su sai shan k'amshi yake a matsayin shi na abokin ango suna cika suna batsewa kamar y'ay'an sarakuna.
Ana cikin haka Alhaji ya tarar da su yake tambayar su ko sun san inda abokan nasu suke, Usman yace Datti na gidan shi yayi yayi da shi ya fito su tafi amma ya k'i yayin da shi kuma Kamal yace tun d'azu yake k'iran layin Fu'ad baya shiga.
Alhajin yace yace suje da baba babba su tusa k'eyan shi ya zo gurin d'aurin auren nan, baza su iya da sakarcin su ace ana sure a gidan su dukan su sunk'i hakarta?
Babu b'ata lokaci suka tafi ga mamakin su basu tarar da shi a gidan ba haka suka dawo suka fad'a ma Alhaji.
         Cikin narasa aka d'aura har aka gama mutane suka fara neman ango domin su taya shi murna ba ango, sai su Alhaji ne suke ta bada hannu ana musabaha har jama'a suka watsewa.
        Gida suka shige su Umma suka hau tambayar da wa aka d'aura baba Karami ya fad'a musu........,fatan Allah ya sanya alkhairi suka musu, Alhaji yace kar ayi saurin fad'a musu maganar auren tunda har yanzu babu ango, bayan hakan ba su san wani hali zata k'arb'a zab'in na su ba."
         Hakan kuwa aka yi har aka gama budurin buki dare nayi aka d'auki amarya aka kaita gidan ta da ke unguwar Federal lowcost, tamfatsetsen gida ne wanda Alhaji ya gida a sirrance shine aka kai amarya ciki aka yi mata jera rasssss gidan yayi kayatu sosai, daga nan aka barta daga ita sai Mardiya.
        Tun Mardiya na ra ran ganin ango har ta gaji ta mata sallama zata tafi Nana take tambayar ta da wa aka d'aura auren tace itama bata sani ba su baba basu fad'a mata ba.
       Shiru tayi har Mardiya ta tafi ta barta kana ta koma tayi lamo a ranta tana fargabar had'a ido da wanda zata gani a matsayin mijin ta wanda zata yi rayuwar aure da shi, to ko ma waye ta d'auki zaman ta da shi a matsayin k'addara cuz iyayen ta baza su tab'a zabar mata abunda zai cutar da ita, kuka taji ya zo mata ba ta hau sheshshek'awa..........
     


*eedatou*


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment