Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi.
Can Usman ya nisa yace" tabbb inko haka ne ta yiwu ko haihuwar ka akayi da matsalar ko kuma matsalar jinnu ne?"
"No Usman bana tunanin hakan". Fahad yayi saurin dakatar da shi, a iya tunanina may be process na maturity d'in shi ne ya zo da hakan it might be zuwa d'an wasu lokutan al'amuran zasu dai-daita.
To Allah yasa abokaina amma wannan matsalar babba ne ace kana namiji abu baka jin sha'awa, gayu akwai fa matsala fa".
Haka ne amma da yardar Allah babu komai", ya fad'a.
"Ni wallahi matar ka ce ta bani tausayi wallahi, duniya babu macen da zata amince a aura mata miji mai irin matsalar ka, say tari ma hakan ya kan yi silar kashe aure na sha jin labarin cewa mata da yawa sun halaka da irin wannan matsalar auren domin duk hak'urin mutum jiki da jini, " Yusuf ya fad'a lokaci guda yana kakkab'e jikin shi yace" ku taso muje..............
Mik'ewa suka yi su hud'u suka shiga mota ba su suka wuce ko ina ba sai club suka zazzauna suna chilling, kwalbar bear ne a jjjjugaban su suna sipping a hankali fahad, Usman da Yusuf suka mik'e suna ta rawa da yammata shi kuma Datti yana zaune a wuri d'aya yana kallon kywawawan samari da yammatan da ke wurin, ga mata iya mata wanda suka amsa sunan mata amma duk ba su ishe shi kallo ba, hasali ma bai ga dalilin da ya saka suka tsaya suna b'ata lokacin su akan mata ba shi ko kad'an bai d'auki jinsin mace a bakin komai ba, he is friendly to them amma kwata-kwata baya jin feelings balle ma mu'amala ya shiga tsakanin shi da mace.
Har ga Allah ba yana iya bakin k'ok'arin shi wajen tilas ta ma kanshi ko zai ji sha'awar Aina amma har ila yau baya jin komai game da ita, kuma yana sane da irin kawaicin da take nuna mishi a zaman su na aure, bata tab'a nuna ta kosa da shi, kuma bata tab'a neman shi da nufin kwanciyar aure ba shi yasa yake ganin kimar ta da darajar ta.
So tari yana tsananin tausaya mata da irin tauye mata hakkin da yake yi wanda shi kanshi ya sani halittane yanda bazai iya canja shi ba, da yana da wata dabara da zai biya mata bukata da tuni yayi, sometimes yana trying best d'in shi ya romancing d'inta amma duk da haka tamkar itace yake baya iya tab'uka mata komai, babu kalan romantic novels, blue films, din da bai nemo ba duk dan ya taimaka mishi wajen biyan bukatun shi amma abu yaci turaaa...., daga k'arshe ya rungumi k'addara ya zuba ma Allah idoooo.
What's up guy!!!! cewar Usman kenan dan ya ga tund'asu yake zaune shi kad'ai.
Mtswwwwe ya ja tsaki lokaci guda yana lallon wrist watch d'in shi, saurin mik'ewa yayi yace" i need to get going guy".
Why!!!!! Cike da damuwa Usman yayi maganar yana kallon Datti".
"Nothing, kawai dai i can't keep waisting my time ne a nan wajen, i see no reason da zan tsaya ina kallon abunda ma ba burgeni yake ba illa ma haushi da yake ban".
Alrght, bye then zan fad'a ma guys d'in cewa ka wuce.
Owkkkkkkk yana fad'a ya bar wajen, gida ya nufa ya tarar da baby angel a kwance a kan cinyar Aina tana tsefe mata k'itso zata wanke mata kai, sallamar shi suka ji Aina tayi saurin sakin kan Nana a tare suka mik'e suka fad'a jikin shi suna dariya ya maida hannun ya had'e su waje d'aya kana Aina tayi saurin raba jikin ta da nashi tayi d'akin shi da sauri tana had'a mishi ruwan wanka.
D'ago da Nana sama yayi yana wasa da ita suna dariya sai ma ya ji moment d'in nan ma yafi mishi ganin matan da yayi a waje wanda yake d'auka marar amfani har Aina ta shigo ta tarar da su a hakan tace" dear d'ina wai baka gajiya da yarinyar nan ne? Shiga goma fita goma baby angel ni dai karta gajiyan min da kai.
Saurin sakin Nana yayi tare da mik'a mata tsarabar ta tayi d'aki tana tsalle kana ya yi wajen Aina ya lakaci hancinta da hannun d'aya yana murmushi wanda ya bayyana dimple d'in shi yace" Mrs complainer an bar miki mijin ki d'in what next"? ya d'aga mata gira.
"Take your bath", cikin muryar shagwab'a sai ya tsaya yana kallon ta.
Me kake kallo bae?
Shagwab'ar ki ce ta burgeni?
How i wish i will have feelings for you da na gwada miki tsantsar soyayya, forgive me wife, ki yafe min na san na gaza ta wajen biya miki bukatan ki, saurin rufe fuskar ta da tafukan hannayen ta tayi, Aina.........., ya k'ira sunan ta da daskararriyar murya tayi saurin cire hannun daga fuskar ta tana kallon shi".
Ba laifi na bane da na zama rago a gare ki".........,
Ba laifina bane da na kasa cika miki mara da ruwa wallahi Aina da da hali da nayi ko zan samu sassauci a zuciya ta domin kuwa zuciyata cike take da tausayin ki da ni kaina".........
Tunda ya fara maganar kwalla ya soma zubo mata ya rungumo ta yana lallashin ta tare da fiddo da hanky yana goge mata a kunne kuma yana binta da tattausan lafazi har sai da ya tabbata ya saka ta dariya kafin nan yace mata ta taya shi wanka, ta waro ido tace" babbar magana!!!!! Ina zata iya cud'a datti sallon taje tayi gane-gene? Duk abunda take fad'a a kasan zuciyar ta ne.

Nace :lol kika sani ko daga nan ya wulla da ke duniyar dad'i? Abunda kike mafarkin samu ne fa.

Kamar ya gano ta ya d'an ja kunnen ta da k'arfi har sai da ta saki ihu a hankali mai d'auke da kissa da kisissina tace" ouch kunnena zafi!!! Zafi dear ".
" Saurin sakin ta yayi da sauri yayi hanyar d'akin shi kana ya juyo ya kashe mata ido d'aya yace" that's your punishment for disobeying your husband, next time idan kika bijirema umurnina it will be more worsen than this".
Ta marairace fuska kamar zata yi kuka ya kuma mata gwalo ya haura zaman bene da gudu yana waiwayowa yana mata gwalo.
Tana ganin ya tafi tayi d'an murmushi a ranta tace" Matar Datti kenan, zaman gidan Datti gwanin birgewa sannan kuma gwanin kunci, ba dan matsalar shi ba da zata iya cewa tafi kowa sa'an miji".
Cije lab'an ta tayi na kasa ta bi bayan shi itama tana shiga ta tarar yana bathroom, direct wardrobe d'in shi ta nufa ta nemo mishi dogon wando da shirt baka ta d'ora zaman bed d'in shi, bata tsaya b'ata lokaci wajen nemo tuarare ba cuz shi kanshi kayan baya bukatan turare, cuz like b'arin turare akayi a jikin kayan saboda dukan su ma'abota tsafta ne shi yasa a kullum k'amshi kama jikin kayan su yake yi".
Shelve d'inshi ta nufa ta d'auko novel tayi rigingine a kan gadon shi tana karantawa cikin nisad'i cuz story d'in ya d'auke mata hankali matuk'a haka kawai take jin shauki na kamata".
Some parts na labarin dariya yake bata tayi ta tuntsirewa da dariya wasu kuma ya bata haushi, idan aka zo wajen tausayi tayi ta Jan majina da kyar tana kokarin hana hawaye zubo mata jim kad'an sai gashi ya shigo kugun shi d'aure da towel yana rik'o hand towel yana tsane ruwan jikin shi, kallon ta yayi yace" seams like u are carried away?"
Ta juyo tana fad'in" yeah", it's very interested".
Mikewa tayi a hankali taje kan shelve d'in ta ajiye novel d'in a wajen da ta d'auko, ta d'auko kayan da zai saka tayi wajen shi a lokacin har ya gama yana shafa mai.
Sai da ta jira ya gama ta mik'a mishi ya k'arb'a yana mai zuba mata albarka tayi murmushi ta koma main parlour ta bashi wuri ya saka kayan.
Tarar da Nana tayi da Teddy d'in ta tana wasa tace zo nan na k'arasa miki tsifan, ba shiri Nana tayi wajen ta da sauri ta hau tsefe mata kan.
Da yake kad'an ya rage su gama hakan ya saka basu wani b'ata lokaci ba suka gama daga nan ta jata zuwa wajen da suka tanadar domin wanke kai ta wanke mata tsaffff da shamboo ta had'a da anti-dandruff tana gamawa ta hau drying mata kai da hand dryer.
Fitowan Datti kenan ya tarar babu kowa a parlour kamar zai yi d'akin Aina sai kuma ya fasa ko mai ya tuna ya nufi saloon d'in nan ya tarar da har Aina ta gama drying ma Nana suma tana tufke mata da baby pink na ribbon.
Babu abunda kan Nana ke yi idan banda k'anshin tsadaddun mayuka da kuma turare na kai, ga wani irin sexy shinning d'in da suman ke yi.
Waya ya fiddo a ya hau musu video yana tsokanar Aina wai zata kyau da aiki a saloon ji yanda ta dad'a hasko mishi baby angel d'in shi.
Dariya ta hau tace" na ga wacce zata k'ara tab'a kan Nana da sunan wanke kai tunda abun ya zama da tsokana".
A wajen ne yake fad'a musu su shirya ya kaisu family house, sunyi murna sosai da d'oki har rige-rige suke tsakanin Aina da Nana shi kan me zaiyi in banda dariya har suka fito suka nufi hanyar fita a tare suka shige mota sai gida.

Ko da suka iso d'akin tsohuwa suka fara nufa suka tarar da Alhaji Abubakar(baba Karami) da wan shi( baba babba) suna hira da mahaifiyar su cikin shauk'i da jin dad'i.
Sallama suka yi suka shigo ko da tsohuwa ta gansu da sauri ta mik'e ta tare Nana tace" oyoyo jikalleta ta", Aina tace" matsa ni kam tsohuwa na gaida iyayena kin tare min waje, Nana kad'ai kika gani a nan?, ta fad'a da tsigar wasa tab'a botsarewa.
"Iyeeeee ka ji min ja'ira kikayi wasa iyayen naki na naha su amsa gaisuwar taki naga ta fad'in k?"
Dariya Aina tayi" haba aminiyar ai bama haka da ke".
Gara dai......., ta ja kwafaaa su duka suka saka da dariya banda Nana da tayi jikin baba babba ta fad'a tana cewa" oyoyooo babana.
Bayan duk sun shigo suka zazzauna, Datti da Aina suna zaune a kasa yayin da har ila yanzu Nana ke jikin baba Karami yana mata wasa yana cewa wai bata san ta fara girma bane?

eedatou.......

SHINNING STARS WRITER'S ASSOCIATION*

'''The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers.'''

https://m.facebook.com/110896360504039/photos/a.110896457170696/110898470503828/?type=3&source=45

🍇🍇🍇 *UNCLE DATTI*🍇🍇🍇.
JIKINA YAKE SO!

©
*eedatou✍🏻*
'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *eedatou*

Masoya littafin Uncle Datti jikina take so bana ganin comments and votes d'inku shi yasa jikina yake mutuwa da yin typing Allah had na canja littafin na fara typing wani sabo sako muku ne kawai banyi ba. Ku daure ku dinga karfafa min gwiwa tunanina ya fara karkata na daina typing littafin UNCLE DATTI JIKINA YAKE SO.

5&6

Banga laifin kowa ba duk Datti ne ya gama sangarta ta, cewar tsohuwa kenan.
Turb'une baki tayi kamar zata fatsa kuka Datti na ganin haka ya taso har izuwa gaban mahaifin shi ya tsuguna gaban ta yana lallashin ta ita kamar dad'a k'ara ingiza ta yake yi" shtttttt shtttttt yi shiru mana baby angel kyale tsohuwa fad'a take nema, nan ne ya samu Allah ya taimaka ta maida hawayen da kiris ya rage su zubo mata.
Kwa dai ji da shi, ni kunga tafiya ta ba zan iya da shiriritar ku ba tayi hanyar d'akin maigidan ta.
Ganin haka ya sa su baba Karami da baba Babba suka mik'e suma" tunda kun kuran mana uwar mu muma kunga tafiyan mu.
Bayan fitan su suma suka mik'e suka yi cikin gida, Nana d'akin mahaifiyar ta tayi da gudu tana kwala mata k'ira ita kuma Aina tayi d'akin sirikarta, a parlour ta tarar da ita ta tsugunna har kasa tana gaishe ta. Cike da farin ciki ta amsa mata tana tambayar lafiyan su ta amsa mata da cewa duk suna nan k'alau.
Hamdala tayi kafin ta shiga yi mata nasiha sosai mai ratsa jiki Aina banda godiya babu abunda take mata.
Jimmm kad'an sai ga Datti ya shigo ya samo wuri ya zauna a gefen kujerar mahaifiyar shi tare da sakin k'ara washhhhh umma na gaji".
Ta sakar mishi hararar wasa tace" ban son sakarci banza aikin me kayi?
Hira ne ya b'arke a tsakanin su har har Fu'ad wanda tun shigowan su yake d'akin shi bai sun zo ba ya fito yana latsa waya ya tarar da su, sosai yayi murnar ganin su dan shi mutum ne mai faram- faram da mutane saidai ko kad'an baya son raini ba kamar Murja ba wacce take miskila, idan ba wanda ta sani sosai ba bata fiye sakewa da mutum ba.
Laaa auty ashe kun taho? Ehhh wallahi Fu'ad yanzun nan ma kuwa".
Nemo wuri yayi ya zauna ba tare da ya d'auke idanuwan shi a kan wayan ba".
Wai ina mutuniyar ne ban ji duriyar ta ba? yana nufin Nana kenan, Datti yayi mishi harar k'asan ido yace" me zaka mata?
" Yaya kenan da ka tambayar wajen Nana sai kace me zan mata? Me ma nake dashi da zan bata". umma ki ji min yaya fa? Ya juyo ya shagwab'e fuska yana kallon mahaifiyar shi wacce tun d'azu sai murmushi take yi.
"Hmmmmm ka ma dai da taka kalar fitinar, kai ma ka dai san halin yayan naka sarai, ni dai na ga ranar da Nana zata bar gidan nan ayi mata aure ko binta zaka yi gidan miji ohoo"?
Dariya suka saka su duka banda shi da
Rad'e rai yayi sosai, bai san me yasa ba yaji zuciyar shi ta tsaya cakkkk, ba komai ne ya ya sa hakan ba illa maganar umma, sannin kanshi ne duk son shi da Nana dole watarana sai tayi aure ta koma karkashin wani, to wai ma me ye na suka wannan tunani? Idan tayi aure me matsalar ka aciki? jefo ma kanshi tambaya yayi yana mai tuhumar kanshi.
Nana kam tana can b'angaren mahaifiyar ta tunda ta shigo gidan ta lik'e mata sai surutai take mata, Sallama aka yi aka shigo" Fu'ad ne ya shigo Nana ta wani had'e rai kamar wanda bata tab'a sanin shi ba, yana sane da hakan amma ya fuske cuz shi dai haka kawai yarinyar bata wani burge shi, ya rasa dalilin da yasa brother d'in shi ke nan da nan da ita tamk'ar duk familyn itace kad'ai gare su".
Kallo d'aya yayi mata ya d'auke kai ya koma gefen ummi dama a parlour suke ya bi lafiyar three seaters ya kwanta tare da fad'in" Ummi yunwa nake ji ko zan samu ragowar abinci a wajen ki?
Murmushi tayi mishi tace" Fu'ad kenan me zai hana? Idan ma babu ai sai na saka Nana ta dafa maka".
Saurin mik'ewa yayi ya zauna da mugun mamaki yace" what? Wata Nanar ba dai wanan ba?
" Ita d'in dai da ka gani a gaban ka?"
"Me wannan zata iya dafawa banda jagwalgwale?"
Dariyar sosai ta saka dama da wasa tayi maganar banda abunshi du-du-du nawa Nanar take da har zata saka ta dafa mishi abinci ita da ko tafasa ruwa ba'a koya mata ba?, mai da wukar wasa fa nake maka." Ga mamakin su, ji suka yi Nana ta saki tsaki mai k'arfi duk suka bita da kallon mamaki, magana ce ta hau yi a zuciya bata sani ba ashe ya fito fili tana cewa", Allah ya sawwake ma na dafa ma abinci, wallahi ko yunwar kashe ka zata yi ba zan dafa ma ba gara ka mutu............ummi saurin buge bakin ta tayi da k'arfi tana cewa" ja'ira sai dai ke ki mutu amma ba shi, banda bakar zuciya ma d'an uwan ki kike ma fatan mutuwa?,
Sosai yayi mamakin rashin kunyar Nana yarinya k'arama kamar ita ace ta gasa mishi magana dan rashin kunya har da ja mishi tsaki? nan da nan yaji ranshi ya mugun b'aci idanuwan shi ne suka sauya launi saboda b'acin raiya, kyale ta kawai ummi zanyi maganin rashin kunyar ta, yaja kwafa ya koma ya kwanta".
Ba tare da ta bi ta kanshi ba ta hau wa Nana fad'a ta inda take shiga ba ta nan take fita, Nana kam ta sa kuka da gudu tayi b'angaren umma, hira suke yi amma tun daga nesa yake jiyo sautin kukan ta yaji gaban shi ya mugun fad'uwa, iso wajen su tayi na ganin Datti ta dad'a k'ara saurin kukan ta ta fad'i k'asa tana birgima tana cewa" an tsane ta, dama ba son ganin ta make a gidan ba", a rikiceyayi wajen ta da Sauri" ya Salam !!!!!! da wata irin dashashiyar murya yayi maganar me ya same ki kike kuka? Wa ya tab'o min ke? Yi shiru Nana ta ki fad'a min".
Jawo ta yayi a jikin shi yana lallashin ta ita kam tamkar ingizata yake haka take ji, ta dad'a lafewa a jikin shi cike da shagwab'a ta cigaba da rera kukan ta". Shiru yayi na y'an wasu dakika yana sauraran ta, yayin kukan nata ke dad'a rasa shi, k'irjin shi yayi mishi nauyi da yawa kamar an aza mishi dotse a ka. Ba komai ne yafi d'aga mishi hankali ba illa kukan Nana da ko kad'an baya k'aunar ji. Ganin ba zai iya jure hawaye a fuskar Nana ba yayi saurin raba ta da jikin shi ya dunk'ule hannun shi ya kaiwa iska naushi yana huci kamar mayunwacin , su ummi kam banda ido babu abunda suke binshi da shi, ita kam ba ma kukan Nana bane, yanda duk ya rikice akan ta ne ya mugun bata mamaki har ta fara zargin cewa gaba akwai kallo tsakananin su, ba dan Aina shakikiyar Nana bace wallahi babu abunda zai hanatayi zargin cewa Datti na tsananin son Nana, ba so irin na wa da k'anwa ba, so na auratayya".
Hannun shi d'aya ya aza a saman kafadar ta, dayan kuma ya d'ora a saman lab'an shi yayi da tsigar lalashi yace" sheeeee......., kana ya tausasa murya a hankali yace" kukan ki nasa nima naji kamar nayi kuka angel, kina so nayi kuka ne Nana?
Ta girgiza kai tana sheshshek'ar kuka, to idan bakya so nima nayi dan Allah ki fad'a min, wa ya saka ki kuka?"
Sai yanzu ta samu damar tsagaita kukan nata, ta hau kora mishi bayani har ta gama, ji yayi ranshi ya kuma baci sosai fiye da na farko a zuciye yayi hanyar b'angaren Ummi duk suka bi bayan shi cuz a tsorace Duke da lamarin shi".
Tarar da su yayi hankalin su kwance suna hirar su har ga Allah sun ma manta da mai ya faru dan Fu'ad had ya tashi ya sako abincin yana ci yana zuba santi wai ya rasa tsakanin ta da Umma wa tafi iya girki, banda tsiya da dariya babu abunda take mishi, ga zaton su sai ji suka yi Datti ya damko Fu'ad da k'arfi ya sharara mishi mari ji kake tasssssss, ya nuno shi da hannu yana wuci idanuwan shi had rufewa suke cuz of tsabar b'acin.
How dear you!!! Wa ya baka dama ka saka baby angel kuka?
Ba su umma kad'ai ba hatta ummi duk sun rikice sun rasa abun yi yayin Fu'ad ya dafa da kuncin shi yana murzawa ba kad'an marin ya shige shi ba, a take yaji ranshi nayi mishi suya, ji yayi ya tsana yarinyar tsana mai matukar gaske, a yanda zuciya ta d'ebe shi kamar ya kama ta ya nad'a mata duka dan ya wuce haushin tunda akan ta ne d'an uwan shi ya mare shi.
Ya had'iye miyau mai d'aci zuciyar shi cike da dafi yace" yaya akan Nana zaka mare ni? Me kuma tace nayi mata?
Yi min shiru munafiki ni zaka tambaya?
Shiru yayi tare da jefa wa Nana harar tsana ya ja kwafa ya fice daga parlourn abincin da bai gama ci kenan ba ya nufi main parlour ya zauna. A take yaji wani irin tukukin bak'in cikin ya ya kama shi, ba shiri ya ciro waya a aljihun wandon shi ya shiga failing numban friend d'in shi Kamal.
Bayan ya d'aga wayan ne ya shiga kora mishi labarin abunda ya faruwa yana gamawa yace" wallahi tallahi na sha alwashin sai na illata rayuwar rayuwar ta..........! sai na  maida  Datti abun tsana da kyama a waken al'umma..............., domin kuwa sai na d'auki fansar abunda yayi min............bashi ne kuma sai ta biya, aka ce ramakon gayya sai tafi ta gayya zafi!!!!!!! kit ya kashe wayaan ba tare da ya jira komai ba".
Abunda bai sani ba ashe a kunnen baba babba yayi maganar da ma ya part d'in tsohuwa ya so ya zauna a nan.
Kunnuwan shi na jiye mishi mugayen zantuka daga bakin fu'ad ya daka uwar tsawa yace" Baka isa ka cutar da Nana ko ka tozartata ba...........kuma ina mai tabbatar maka da cewa duk abunda ya same ta kaine sila!!!!
Shan jinin jikin shi yayi ,sumi-sumi ya mik'e ya bar parlourn.

B'angaren Datti kuwa bayan barin Fu'ad wajen ya ja hannun Nana keeee suka fita daga gidan Aina na ganin haka tabi bayan su da sauri gyale a hannu sanin kanta ne muddin ta bari suka tafi to sai dai ta taho a motar kasuwa, ko acab'a gashi a al'adar ta bata kaunar sa.
A mota kuwa masifa yake tayi har suka iso gida, yayin da take jero dankaren dana sani a zuciyan shi," ji fa daga zuwan su ko minti talatin ya tabbata basu kai ba amma dan rainin yaron nan sai da ya sanya mishi angel kuka, Aina kam shiru tayi abunta gudun karya sauke haushin a kanta cuz kad'an daga aikin shi kenan, Nana kam ko a jikin ta sai ma dad'in da take ji a ranta musamman da ta ga ya mare Fu'ad dama haka take so cuz Fu'ad nayi mata shishshigi da yawa,

A raina nace; Nana at this aged kike cewa gardeden kato namiji kamar Fu'ad yayi miki shishigi?
Sati guda suka d'auka ba tare da sun waiwaye gidan ba cuz fushi sosai Datti yake da su ummi, a cikin satin ne ma ya neman ma Nana wani tsadadden makaranta cuz a wajen yake so ta zana jarabawar ta ta JSCE. ABUBAKAR TAFAWA BALEWA INTERNATONAL SECONDARY SCHOOL shine makarantar da ya samar wa Nana shi ke kaita ya d'auko ta, kuma ya nemar mata mai yi mata extra moral lesson zuwa wani watan za'a yifara mata lesson.
A ranar da ya kawo mata form d'in makarantar ba karamin murna tayi ba, kasancewar ba wani tazara sosai tsakanin gidan su da kuma makarantar. Ranar farko da Nana ta fara halartar makarantar ta ga sauyi sosai, tsarin makarantar kuya ya kayatar da ita matuk'a.
Principal office ya fara kaita yayi mata registrations both PTA da school fees d'inta, daga nan ya damkata a hannun principal na makarantar ya nuna mata ajin ta tare da introducing d'inta gaban sauran y'an uwanta students.
Bayan fitan shi ne wata fara tsiririyar yarinya mai tsawo kad'an, wanda shekarunta ba za su wuce na Nana ba ta taho ta zauna a kujerar ta, time d'in Nana na bud'e litattafan ta tana rubuta sunanta a jiki da kuma ajinta, JS2B shine ajin da naga Nana ta rubuta a kan littafin ta, tana jin zuwan yarinyar amma bata d'ago ta kalle ta ba balle ta sa ran zata kulata, ganin haka ya saka yarinyar ta bugi bencin a hankali lokaci guda tace" hi", a sannan ne ta d'ago ta kalle ta d'auke kai tare da amsa mata ciki-ciki.
Ta so ta ja Nana da hira amma bata samu fuska ba, ba shiri ta koma seat d'inta da zauna dan ko kala Nana bata kuma furta mata ba, tana nan zaune ita kad'an ta har teacher ya shigo ya gabatar da darasin shi, a ranar sun sha darasi sosai almost duka periods d'in sai da aka shigo musu, Nana har gajiya tayi Allah cikin ikon shi closing hours na cika Lamar had'in baki sai ga datti ya parking mota a d'an nesa da ajin su kad'an yana jiran ya ga fitowan Nana.
Daga bakin ajin su ta tsaya tana kallon yanda mata da maza ke ta giftawa, duk ta kosa taje gida cuz yunwa ta kama ta sosai, kamar ance ta d'ago ta hangi motar Datti da sauri ta nufe shi, daga nesa ya hango ta ya tsare ta da ido, fuskar ta ya fara kalla ya ga tayi wani irin fresh zai oya rantsewa da Allah a kaffff makarantar babu wacce rayi na biyu balantana ta kama kafar Nana

Please Login or Register in order to submit comment