Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

har inna ta kare mata fada bata sake magana ba don fada sosai inna tayi mata tana shiru har inna din ta gama.
Ina jin tayi shiru nace ni inna gaskiya gobe zanyiwa Abba maganan karatuna gashi har zamu fara exam din shiga wani zango ban tafi ba.
Idan kinga zaki iya ai gaki gashi nidai babu ruwa na tunda kikaji umma tace kin daina boko to ki barwan nan zacen a hakan.
Har muka kwanta ba kara magana ba sai faman tunane nake a raina don ba abindake damu kamar rashin karatu da ban fita yanzu na riga da na kwallafa rai ga boko nace ni nurse zan zama idan na girma.
Washe gari baba bai fito dakin lantana da wuri ba har kowa ya gama shiri ya fita don sauran suna zuwa makaranta basu fada kangin Asabe.
Hankalina yana wurin fitowan baba daga daki lantana sai wuran goma ya fito tare da ita tana mai rakiya don kawai kada yace zai biya wurin innar mu su gaisa.
Har yasha dan kwanan fita daga ciki gida na fito da sauri na same shi ina fadi Abba ina kwana.
Ya tsaya tare da juyowa yana fafin yar mairo kun tashi lafiya ina kannen naki sun fita ko ke nan ?
Nace a sanyayaye sun tafi baba sai na fara hawaye daga inda nake tsungune ina dan gogewa da gefen hijabi na.
Me ya sameki kike kuka haka da safe Abba ya tambayeni cikin kullawa kasa bashi amsa nayi sai sharan hawayen da nakeyi a lokacin.
Lantana dake tsaye gefen shi kamar bodyguard din shi ta tabe baki tana fadin ya wuce dai zancen auren ta da umma ke fadi.
Kai haba lantana wani zancen aure kuma yanzu gun yar mairo adaiyi hakkuri ta karasa karatun nan datasa a gaba har kwana nawa yarage ta karasa idan muna raye.
To ai naga kai umma take tausayawa a cikin zancen nan kamar rage maka nauyine umma ke kokarin yi ga hakan.
Ya juyo wurina yana fadin kinga yar mairo kije kiyi hakkuri har in zauna da umma in fahintar da ita ko Allah zai bamu sa,a a kanta.
Lantana dake jin mu ta karyar da kanta gefe tana fadin gamu gani ai indai umma ce a gidan nan.
Na bude baki da kyar ina fadin don Allah Abba ka taimaka min na karasa karatuna ko iya secondary din ne in tsaya.
Taysayinane ya kama Abba lokaci guda sanin yadda gun ina kankanuwa nake son boko har irin dagewan da nakeyi kan karatun a yanzu.
Yayi karfin halin fadin kada ki damu yar mairo insha Allahu zaki karasa karatun ki har ki more a rayuwan ki, duk da lantana na fadin malam kasan fa ka makara kada kwastama su dinga mitan hakan.
Haka yasa Abba ya wuce badon yaso ba don tausayina da yaji a lokaci guda ya rufe mashi zuciya.
Bayan fitan baba lantana ta juyo ta dubeni a lalace tana fadin iska na wahal da mai kayan kara.
Lantana wurin Asabe ta nufa ta fesa mata yadda mukayi da Abba tunda naga ta nufi can zuciyana ya raya min hakan.
KADUNA GARIN GWAUNA

Wanka tayi ta shiya a gurguje cikin shigar manyan mata da boko ya gama ratsa su.
Fuskanta babu wani kwaliyan zama a tare da ita sai dan maikon mai data shafa sai man lebe data murza don yanayin garin.
Gurin takalma ta nufa ta saka wanda yai shige da kayan jikinta da sauri ta fito daga dakin duk da sauri takeyi amma idan ka ganta sai ka dauka takon isa da iza takeyi saboda wayewa.
Makullin mota ta dauka don bata bukatan driver a inda zata tafi yau don gidan safiya take son kaiwa ziyara da sa,a.
Tana bude falo sukayi kicibis da bakin ta dake hawo steps din da zai sada mutum da kofan shiga gidan.
Tsayawa sukayi suna kallon kallo a tsakanin su kafin hjy iyami ta fara fadin kune tafe banda labarin hakan.
Sai lokacin Alh isma,il yayi dan murmushi yana kawar da abin kunyan dayaso yi lokaci guda don ganin hjy dayayi a yau bayan tsawon shekarun daya dauka basu hadu ba.
Shima ya wayence da fadin af na manta da gidan bakar baturiya zamu ziyarta dole saida notice.
Kai ta girgiza tare da kallon wanda suke tare tana fadin sannu da zuwa kaidai shi wanan har kullun baya tsufa halin shi na kurciya yana nan a yadda yake da zolaya.
Ke kuma zolayan ne bakya so ba bissimillah ku mana ku shigo kasa na tsaya mun bar bako a waje.
Bako ko baki don nima bokon ne tunda ban taba zuwa gidan ba ai kinga na zama bako.
Hjy iyami tace kaidai ka sani tana ja dan gefe guda tare da nuna masu hanyar shiga don bata yarda su sakata gaba ba kasancewar su maza.
Falon suke bi da kallon yadda ake tsara komai zakace a kasan turai gidan yake don tun a waje suke bin ginan gidan da kallon sha,awa.
Zama sukayi saman kujerun alfarman dake falon kafin aka fara gaisawa tare da tambayan iyali.
Alh isma,il yana tambayan samarin hajiya daya sani take fadin kai ai yanzu sun zama magidanta in ka debe shi na biyun da har yanzu baiyi aure ba yana chaina yana aiki dasu a yanzu.
Kai masha Allahu Alh yace sai kuma yayi mata gausuwan rashin mijin ta don tun lokacin basu hadu ba dashi yace koda suka zo gaisuwa mata sunyi yawa basu shigo ba.
A lokacin yanayin hjy yadan canza take fadin hakane saidai bamu dade ba muka koma don yara dake karatu a can.
Bayan sun dan sha abin shanda aka cika masu gaba dashi yake fadin hjy dama kamar yadda nace dake magana ce tafe damu sai fuska da fuska zamuyi maganan .
Hjy tace kwarai hakan kace yanzu ku nake saurare ai dayan mutumin ne ya karbe zancen da fadin hjy nasan baki sanni ba ni.
To ni sunana Aliyu zaki kubau dan majalissan dake wakiltan nahiyar uku dake makwabtaka damu.
Munzo nan ne da wani bukata ko shawara na duba a gareki wansn ba wani zance bane sai sunan ki da muke son mu bayar don zaman ki macen data cancanci wani mukami da muke son a samu a tamu nahiyar a cikjn gwaunatin nan.
Ni kuma Alh har yaushe na dawo kasan nan da zan iya shiga wanan harkan na siyasan kasan nan yanzu.
Bayan haka kuma ni yanzu duk wani mukami na gwaunati ko wani aiki ban ra, layin shi saboda hutu nake so a yanzu a cikin iyalina.
Me nake nema a yanzu wanda Allah bai ban ba sai hamdala da shukura ga ubangijina ga yara sun kawo karfi suma Allah yana duba mana duk a yanzu.
Mun san da hakan hjy sanin hakan ma yasa mukaga cancantan ki ga wanan matsayin don kece zaki tsaya muna badon kudi ba sai don tausayawa jama,an mu.
Kada kace haka Alhaji don shi mukami da kake gani ba haka yake ba na rike na kuma san meke cikin sa sarau.
Balle mukamin irin gwaunatin kasan nan sai a hankali don mutane ba gaskiya suke so ba a yanzu niko kasan a bisa tubalin mijina nake komai shine gaskiya.
Don haka tun zancen baiyi nisa ba ina rokon ku da ku janye wanan magana a duba wata da ake ganin ta cancanci hakan a bata don Allah.
May na fadama Alh isma,il ya fada yana kallon abokin nasa cikin dan murmushi nasan wanan matar ba zata canza ba ai a yadda na santa tun farko.
Kaji ke nan ina nan a yadda nake har yanzu hjy iyami ta fada sai dayan mutumin yace hjy zamu baki lokaci kiyi shawara yadda ya dace don bamu son wanan daman ya kubbuce muna a yanzu.
Don dama ne da hujja da muke dashi akan ki na mace mai ilimi da matsayi irin wanda ake nema a wanan nahiyar tamu a yanzu.
Shiya sanni yasan ko wacece ni banda ra,ayin irin wanan mukamin ko a majalissan dunkin duniya danayi aiki dasu acan da ka fadi sunana sun san dani a wurin.
Hjy ki dai kara shawara a duba abin kamar yadda nake fada maki a yanzu don wani abin ansan badon kudi mutum ke rike sa ba sai don al,umman nahiyan ka.
Zatayi shara yanzu dai mun fada maki bukatan mu don Allah muna son kiyi duba ga wanan abin kafin mu sake dawowa muji shawarab da kika yanke akai.
Hakana dai sukai sallama ba tare da sunga alaman yarda daga gurin hjy iyami ba shi dayan mutumin daya kira kanshi da Ali zaki kubau yana cike da mamakin hjy iyami din don bai dauka akwai irin matan nan a jaharsu ba haka.
Unguwar da hjy bata fita ba ke nan a ranan don bayan tafiyan bakin ta sai taji kasalan fita ya kamata lokaci guda don tunanen maganan bakin nata da sukazo mata dashi.
Tsuki taja tana gyara kafan ta saman kujera data dagwara don taji dadin zama da kyau tana fadin ina zaman zamana kuja min sabon zagi da tonon asiri da tsufana.
Nikan dariya nayiwa hjy ina fadin hjy ina tsufan yake a nan saidai inda babu tsofin ko za a kiraki da tsohuwa ko dadtijuwa din.
Don babu mai ganin ta a yanzu yace itace mahaifiyar wa yan nan yaran nata a yanzu.
Sai data dan dade zaune ta tuna da zancen unguwar da zata tafi do yau taso ta ba su safiya mamaki ta ziyarci gidajen su su sanda suma yan uwane kamar kowa.
Don kawai sun fito ba ciki daya da yan uwan su ba bai kamata ana ware su haka ba a cikin dangi don tasha alwashin ida nufin marigayin mijin ta duk akan yan uwanta idan tana raye a duniyan nan .
Saidai muce Allah ubangiji ya ida nufi na alheri hjy da haka mata suke duka wurin raya zumucin da zumunci a yanzu bai tabarbare ba a duniyan nan.
Shigowan yaran ta dake gida suna hutu ne ya dawo da hankalinta garesu gurinta suka nufo kamar yara kanana muhsin ya zauna a gefen ta tare da rankwafo kanshi saman wuyan ta yana fadin wallahi mami na gaji sosai.
Kafin dayan ya zauna a makari kujera dayan gefeb yana fadin hajjaju zaman garin nan fa ya fara isata wallahi.
Gashi ko a nan zaku zauna don ba zan yarda wani cikin ku ya kara niss dani ba kamar yadda kewan dan uwanku ke wahal dani a yanzu.
Wai mami idan an tashi magana sai ki kawo zancen yaya jackson shifa ina jima yanzu ya manta da Nageria a ranshi.
Dan duka takai mai ga kai tana fadin daga min ya daga da sauri yana fafin wassh Allah na yana shafan wurinda ta dukeshi din.
Tana fadin har daku cikin batawa dan uwanku sunan shi na musulunci da kiranshi wai wani jackson cen ba dadin ji.
Allah hajjaju idan ba kince haka ba a turai babu mai gane shi ake afadi don jackson din ko jack ya rufe sunan nasa a yanzu.
Bai rufe ba ta fada a hayayyake shima idan yazo zan mashi magana kan hakan idan baso yake yaje lahira ana tayar dashi da wanan sunan kafiran ba.


ZAINAB IDRIS MAKAWA






🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅

5️⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

YAN UWA MASOYA ANNABI ALLAH YA KARAWA ANNABI DARAJA YABA MU IMANIN A MAI ANFANI A ZUKATAN MU AMIN, , , , ,

DON SAMUN LITTAFI BA TARE DA DAUKAN HAKKI DA NAUYI A KANKI BA SAI KI TURA DARI UKU A BANK DINA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA TA WANAN LAYIN 08036959257 KO 09036


Tun bayan fitan Abban mu ban koma daki ba wankin dana tara na farayi muna kafin yan kitso su fara shigo min su hanani aikin komai.
Ina shanya kayan ne nake jiyo zagin da Asabe ke durawa wanda ba sosai nake jiyo su ba daga inda nake har na samu na gama ruwa na diba naje nayi wanka.
Ban kai ga karasawa aikai sallama ko ban leka ba nasan masi kitsonane suka fara shigowa lokacin .
Makwabciyar mu hassana ce da yaranta yan mata biyu da zan wa kitso suka shigo fitowa nayi na dauko tabarman da innan mu ta bani don yan kitso din na shifinda tare da gaida ita.
Dakin inna na shiga tana zaune tana gyaran sarkan kanwarmu daya katse nake fadin inna ko zan dora abinci ne kafin in zauna.
Jekiyi tsabgan gaban ki gunda ga mata sun fara shigowa barni in gama in dafa muna fate da guntun tsakin daya saura muna shekaran jiya.
Ko zai kaimu har dare tunda ba abinda zamu dafa da daren inna Allah zai bamu da yardan ubangiji tunda ga yan kitso nan sun fara shigo min yanzu sai a sayo ko taliyan hausa a dafa da daren.
To kije ku zauna kada matar mutane ta dade a zaune inna ta fada na juya na fita raina babu dadi a lokacin don a yanzu kan ina iya fahintar halin da mahaifiyar namu ke ciki na mijinta da sauran mutanen gidan mu din.
Daga kofan innan mu kadan nake zama muyi kitso don Asabe tace bata yarda ana sake masu gashin mata barkatai a gida ba kada azo a barbada masu tsiya a gida.
Ina kitson ina tunanen halin da innar namu take ciki na bakin cikin rayuwa duk saboda kasancewan mu mata a gareta don kila badon mun fito a yaya mata ba da bata fuskanci duk wanan nakin cikin haka ba.
Muryan lantanane ya dawo dani ga dogon tunanen dana lula ina rike da kan yar karamar yarinyar dana farawa kitson lokacin.
Wai har an zauna wanan bakar sana,an da babu karuwa a kullun a cika muna gida da yan gulma da sunan kitso nikan malam ya dawo ya tare min wurina don wanan abin ya isheni hakana.
Kai ke nan duk abinda kakeyi idon mace na kanka a zubama ido a fita dakai waje ana baradawa a cikin gari.
Dagani har matan da nakewa kitso ba wanda ya tanka a cikin mu don idan da sabo sun saba da wanan halin na habaici idan sun zo kitson don kiri kiri ake nuna min hassada ga yin kitson kuma.
Maimakon ta shiga dakin datayi niyar shiga da farko sai kuma ta juya ta koma lungun Asabe ta dade kafin ta fito.
Lokacin har na gamawa yaran duka biyu na farayiwa uwar saura kadan mu karasa kitson namu tana yan wake waken ta na hausa mai kama da habaici.
Naji matar da nakewa kitson tace uhumm wanan matar baban naki da jan magana take naga dai kullun nazo kitso gidan nan sai ta samu abindata fada a kanmu.
Ina jin dadin yadda baki kulata kike aikin gaban ki ba tare dakin damu da ita ba don irin su saboda bakin ciki suke haka don tayi sanadin da zata saka a hanaki kitson ga baki daya tunda sun san kina samu a nan.
Ba komai ai wata ran sai labari na fada mun gama ta dauko dari biyar sabuwa ta mika min na girgiza kai tare da fadin a, a wallahi ki ban dari ko dari da hamsin .
Haba Abu kullun na turo yara a kyauta kike min kitson nan ki karba baban sune ya bamu mu kawo maki da nake fada mai alherin da kikewa yaran shi kullun.
Dole na karbi kudin badon naso ba damun wanan kudin ya zama kamar buduwar hanyar alherina ranan don duk wa yanda sukazo kitso mun samu alheri sosai a wurin su.
Bansan yaya Asabe sukayi da mahaifin mu ba ya dai bani hakkuri kan in hakkura da karatun nan kawai a yanxu.
Ranan nayi kuka sosai kamar ba gobe tun innan mu na ban hakkuri har ta gaji ta kyaleni ta saka min ido.
Saratu ne abinka da dan uwa data dawo innan muke fada mata wuni nayi ina kuka a daki yau don Abba yace ba zancen komawa makaranta a wurina.
Tashi tayi ta sameni a dakin tana ban hakkuri tare da ban shawaran da muke ganin zai fitar dani daga kuncin da Asabe ds lantana ke shirin jefani s ciki.
Fitowa nayi don taya innan aiki gitkin dare haka ma su sararu da sauran yan uwan mu suna debo ruwa daga rijiyan uguwar mu suna cika duk kayan dake gidan na ruwa.
Har sun kusa cika na kofan lantana don sheri kawai lantana tace wai habiba ta saka hannu a ruwan don haka bata so sai dai su zubar su debo mata wani.
Wanan ya kawo rikici a gidan mu sosai ranan don har inna takai ga tanka masu Abba kuma ya dawo ya hau innan mu da fada ta inda yake shiga ba nan yake fita ba.
Wai inna ke goya muna baya muna iya shegen da mukaga dama a gidan ai lantana ma kamar uwa take a gurin su tunda tana auren shi.
Saratu dai taki komawa diban ruwa kuma ta hana yan uwa zuwa su debo suka kada guga a riya karshe dai ruwan da ba,a deboba ke nan har Abba ya dawo hake wanan fadan .
Kwala min kira yayi wai na kwashe ruwan randan innan mu guda in zubawa lantana a nata randan in yaso mu mu zauna ba ruwan tunda saratu ta zama abinda ta zama a yanzu duk gaba daya zai hadamu yai muna aure lokaci guda tunda ba finta nayi da wani girma ba.
Inna kan bata da aiki sai kuka don hakane kowa ke kokarin takata yadda yaso a gidan don rashin maganan da bata yi idan suna mata abinda sukaga dama, mu a namu ganin ke nan.

Hjy iyami abin duniya y isheta ga matsin da gwaunati da yan siyasa ke mata dole ta zauna da yaranta da yan uwanta kan maganan.
Inda suka bata shawaran karban mukamin don taimakawa rayuwan tallakawa da sauran al,umman nahiyar su din.
Haka yasa ta shedawa Alh Aliyu zaki kubau amincewan ta wanda ba karamin farin ciki yayi da jin hakan ba daga bakinta ,.
Duk da yana hangen da wuya su iya tafiya a yadda suke so da ita don ra,ayin daya hango a tare da matar duk da ba laifi ko yaya ne ai wayau maza yafi na mata ya fada.
Tawaga guda sukayo zuwa gidan sun dade suna tataunawa da ita kafin suyi mata godiya su tafi.
Hakan yasa taji duk ta gaji ga ranan don yan aikin ta kawai bazasu iya mata abinda take so ba daidai a hakane safiya suka zo gidan suka same ta cikin gajiya.
Bayan sun gaisane tare da mata murnan abin arzikin dake shirin faruwa da ita take fadin anya safiya zan iya wanan abin yanzu.
Yau kawai duk nabi na gaji dan dawainiyar dana wuni inayi da jama,a agidan nan .
Shiyasa nake son a samo min yarinya yar maidaidaciya da take da rikon Amana in zauna da ita don wa yan nan kinga su ba zama sukeyi ba ko ba school sai sun kirkuro fita sam basu zama a tare dani.
Na rasa inda zan samu irin yarinyar da nake bukata na kusa wace zata dinga min hidima ko yaushe.
Dan shiru safiya tayi kafin tace za a duba a gani indaya dace sai a samo maki yarinyar kamar yadda kika bukata.
Zanje kauye in duba maki mai dama mu gani idan zata iya idan kuma ta gaza sai a mayar da ita a sake duba wata.
Dakin mun hakan dana gode kuwa safiya shiyasa nake kara jin dadin ki wallahi na dade ina tunanen ta ina zan fara duba yarinyar data dace yadda nake so nan gari.
Da wanan maganan suka rabu ranan inda safiyan ta koma gida da tunanen inda zata duba yarinyar data dace takawowa hjy a yanzu gashi tayi alkawarin hakan gare.
Kafin gari ya waye ta yanke shawara a ranta zata duba ta gefen mahaifiyarsu ta gani idan hakan zai samu garesu.
Don koma meye zata iyayiwa hjy iyami indai zata iya baifi karfinta ba don ko meye hjy ta cancin hakan garesu .
Don ta nuna a duniya su yan uwan mijintane a yanzu don ko wani wuri zata tafi na alfarma suna daga cikin masu mata rakiya.
Wanan abin yana ba mutane da dama haushi har suka fara fadin asiri sukai mata suka shiga zuciyan hjyn a lokaci guda.
Daga hjy harsu suna jin ire iren wanan magana saidai ba abin mamaki bane hakan da mutane suke fadi don yanzu mutane basu dogara ga Allah sun manta da ba duga aka zama daya ba.

ANCAU
Tunda safe na samu masu kitso don haka na zauna muna kitson ga innan mu tana aikin girkin gida don yau Abba yayo cefane ana dafawa aci duka gida.
Ditin mota mukaji a kofan gidan mu sai dai bamu dauki hakan wani abu ba don ba wanda zaizo gidan mu da mota ai.
Haka yasa muke zaton ko makwabtan mu motar tazo yin wani abu sai can mukaji sallaman mata na shigowa gidan namu lokaci guda.
Amsa masu sallama mukayi dani da matan da nakewa kitso sai inna ta dago dan ganin masu shigowa gidan lokacin.
Tarbon su tayi tana fadin wa nake gani yau kamarsu hjy safiya garin namu ?
Ba kama bane mune dai din kike gani don kasancewar su kamar tobasai tunda tana auren yaya a garsu.
Dakinta ta kaisu don Asabe bata gidan lokacin ba laifi don dakin inna duk da yawan mu koda yaushe tsab yake don tsabtan ina yara basu hanata gyaran daki da tsakar gida har din muka koyi hakan.
Don ko a kauye akwai masu hali irin na yan birni da zaka samu a talauci amma komai nasu yana tsab.
Tabarma ta shimfida masu saman sumintin dakin dake sheki sai dan kamshin turaren wutan dake tashi ba wani mai kamshi ba amma duk da hakan ba laifi dai dakin don ba zakace dakin mai yara bane.
Ruwa ta kawo masu a kofin silver tana fadin ga dai ruwan namu babu sanyi don har yanzu yayan naku baija wuta ba gidan nan.
Ikon Allah duk wutan nan daya kewaye garin nan ba a ja maku wuta ba har yanzu inna dai bata ce komai ba kada zancen yayi nisa a hakan.
Safiya ta dauka ta dan kurba kadan ta mikawa anty Sa, a kaita girgiza alaman ba zata sha ba ta aje kofin a gefen ta.


4 Comments On ABU CIKIN DUHU
avatar
khadija-8-3

1 year ago

Reply

I want to download this book

avatar
daiy

1 year ago

Reply

Replying to khadija-8-3

You have to subcribe to our package in order to download our novels

avatar
zainab-3-3-5

1 year ago

Reply

I also want to download this book

avatar
daiy

1 year ago

Reply

Replying to zainab-3-3-5

You have to subcribe to our package in order to download our novels

Please Login or Register in order to submit comment