Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Lokacin na sakewa matar kai nazo don in gaidasu da zuwa a dakin innar mu din .
Saida nakai har kasa na fara gaida su da zuwa anty safiya na fadin wai kada dai ince wanan ce nan wa take da sunama don mantawa da sunana da tayi a ranta.
Inna tace ki dai tuna don kinsan niba fada maki zanyi ba dai ta fada tana mikewa don barin dakin.
A hankali nace Abu sunana gwaggo tace naji dayan da ake kira da anty sa, a tace min haba wani irin Abu kuma keda kanki kike batawa kanki suna haka?
Zainab din ne kike kira da Abu wai kamar sunan wani abu can daban wanan ai suna tsofine nagani.
Nidai na fita ina dan murmushi don jin may suke fada a gatin nan kan wa zai tsaya kirana da wani zainab can.
Nakai kofa naji tana tambayana ina yan uwan ki suke nake fadin suna makaranta na fita daga dakin kai tsaye na koma inda nake kitso .
Yaro inna ta nema ta tura a kira mata Asabe datace zata shiga makwabta tana jin lokacin da take fadawa Lantana hakan.
Ba, a jima ba sai ga Asabe da dan saurin ta ta shigo tana fadin bakin daga birni su waye umma yayan kine su safiya inna tace.
Sai lokacin na tuna dasu da suna yawan zuwa gidan muna kanana amma daga baya suka daina zuwa ban san dalilin hakan ba garesu.
Suna ina Asabe ta tambaya inna ta nuna mata dakinta sai ta dan tabe baki ta nufi dakin inna din .
Muryan lantana ne ya dakatar da ita shiga dakin lokacin lantana na fadin umma kin dawo ashe ?
Na dawo yar nan yanzu yaro ya sameni wai nayi baki daga birni sai lantana tace au baki akayi ashe mu dake gidan ma bakin ciki ya hana a sanar damu.
Dago kai nayi na kalli lantana da take maganan don nasan da innan mu take wanan maganan haka.
Asabe ta shiga basu dade ba suka fito zuwa sashen ta tare da bakin sai lokacin lantana ta tafi gaida su.
Don a nata nufin bazata shiga dakin innan mu ta gaida bakin da zuwa ba don innan mu bata kai mata can ba .
Inna tana gama abinci ta zuba masu a kwano mai kyau ta dauka takai masu ta dawo ta debi ruwa ta sake kai masu a can.
Abba ya shigo gidan yana fadin yanzu ake fadamin anga munyi baki a gidan yasa na garzayo in ga su waye suka zo.
Can ya samesu a aurin Asabe suka zauna sun dan dade a tare kafin su fito suce zasu tafi sai da suka sake shiga dakin innan mu sukai mata alheri kafin su fito su tafi din.
Bayan kwana biyu naji lantana na fadin duk kyau da bokon wasu ga aikatau zasu kare rayuwan su karshe ma su kare ga auren maigadin gida.
Dagani har innan mu kallon juna mukayi lokaci guda don ba wanda ya fahinci may zancen ta ke nufi a lokacin.
Share ta kowa yayi abu kadan yan kwanajkin nan zata ce kyau wasu ya kare ga banza tunda zasu tafiyin bauta a gidan wasu.
Banga wanda ya isa ya tura min dana yawon bauta ba a gidan kamar banda kowa a duniya har dai ranan da dare muna zaune muna hira a dakin inna gaba dayan mu inna ke fadin.
Nikan wanan zancen bautan da amaryan baban ke fadi na rasa gane inda maganan ta ya dosa da fadin haka ko yaushe .
Wanan inna ai ita ko ba dalili kirkiro magana take ta yabawa mutane don kawai ayi fitina tunda bata son a zauna lafiya ita na fada.
To dan wataga za,a tura yin bauta da take fadin haka inna karma magananta ya dameki don Allah saratu ta fada tana jan tsuki.
Shiru mukayi kowa na nazari a cikin ranshi kan zancen don innan mu tafimu fahintan da akwai wani abinda zai faru da diyan ta don haka kawai bai saka lantana tayi ta gorin haka a tsakar gida.
Aiko ranan da safe baba yai kiran mu nida innan mu yana lungun Asabe muka tafi don amsa kiran Abba din.
A zaune muka same su a dakin kowa yai shiru saidai yanayin su ya nuna kowa na cikin bacin rai a lokacin.
Wuri muka samu muka zauna nikan ina daga kofan dakin don ban shiga ba a lokacin inna tace gamu malam.
Zuwan lantana yasa yayi shiru ya kasa maganan da zaiyi sai Asabe take fadin kayi magana ka tsaya kana wani kimbiya kumbiya kamar kana tsoron matar taka da yarka.
Ke yahanasu bawani abu bane yake son fada maku ke da yarki sai zancen tafiyan yar ki birni da nace a turrata aikatau.
Koba komai zai dan samu abinda zai rage saya mata kayan daki a nan tunda kunki bari ya aje komai gashi sun cika muna gida zagada zagada dasu.
Aikatau kuma umma ina ta fada da mamaki karara a fuskan ta sai naji asabe tacd eh aikatau ko yar taki tafi karfin yin sikatau din ne.
Ina ko tafi umma wanda yake nema ya samu duk wata za,a lalo mashi yaji dumus ai yafi zaman wanan kitson da takeyi kullun tana tara muna munafukai a gida lantana ta fada daga inda take.
Koba zaki bari ta tafi bane Asabe ta fada a hasale tana duban inda inna take zaune.
Abba yayi karfin halin fadin a barta suyi shawara da yarta umma don kinga daga sama sukaji wanan maganan yanzu.
Shawaran me zasuyi wanda yafi wanda na fada yanzu a gaban ta kuma ko kuma sai abinda tace zamubi tunda itace ta ajemu bamu ba.
Ai shike nan tunda kace haka dama ni kai nakejiwa nake tausaya maka tunda hakan ne kawai zatayi ma a matsayinta na ya mace ta taimakawa rayuwan ku na dan lokaci.
Umma ai Allah daya bamu su yasan yadda zai iya mana dasu basai mun kaisu inda bamu san kowa ba don neman abin duniya.
To mara kunya akan yar fadin ki kike kokarin musayan magana dani to kiji ki karaji zuwa birni babu fashi ga Abu.
Idan ta samo kudin bakuso ku bani wani ya hana ki haifota a namiji halan birni daine kamar taje tagama yanzu haka na fada babu fashi ga zancena kuma.
Inyaso idan ta tafi ta shiga duniya karewan rashin sanin kowa inds zata ke nan aikatau daine sai ta tafi.
Wani kuka ne na fashe dashi lokaci guda don jin hukuncin da asabe ta yanke min yau a gidan mu.
Ta hanani karatu don wani manufanta yanzu kuma zata turani birni yin aikatau do kawai a musgunawa innan mu.
Daki inna ta sameni ina rusa kuka itama kukan ta shigo dashi a dakin muka taru muka rasa wanda zai ba wani hakkuri a cikin mu lokaci guda.
Sai nice nayi karfin halin fadin inna kiyi hakkuri in Allah ya yarda ba zan tafi yin aikatau ba a birni.
Yar mairo me nayiwa umma take min haka a raguwana ko yaushe take kokarin sai taga bakin cikina a rayuwan ta.
Ita ya mace ba diya bace da za ai alfahari da ita cikkn zuria da wasu basu gane hakan.
Ban taba bakin ciki da nadaman samun ku a diya matan da kukazo min ba don ban san kyautan da Allah yai min ba don haka bazan butulcewa Allah na ba.
Amma umma kulun magana ya tashi a gidan maganan ta daya ne shine na cika masu gida da diya mata bafa san yadda zatayi da diya matan da nake haifo masu ba.
Innan mu kiyi shiru ki barsu nasan munafuncine aka kula a turani yin bauta a gidan wasu.
Koda Allah ya nufa zan tafi inna nayi maki alkawarin kula da kaina a duk inda na samu kaina din.
Balld ba zaki tafi ba yar mairo muddin nina haifeki ba zaki tafi wanan bautan da umma ke nufin kije ba don kawai ta musgunawa rayuwan mu a gidan nan.
Innan mu don Allah kada kice zakiyi wani abinda auren ki zai tamu gun Abba tunda shima ya nuna baison hakan a gaban mu amma asabe tace sai na tafi.
Kiyi hakkuri ki bini da addua a duk inda zasu kaini ya zama kariya a gareni ko yaushe.
Sai naji ta kara rushewa da wani kukan nima kukan na fara lokaci guds mun dauki lokaci a haka a dakin.
Ranan da wanan bakin cikin gaba dayan mu muka kwana tare da tunanen ina za,a turani shine abinda ke damuna a raina .

ZAINAB IDRIS MAKAWA





🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅

6️⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

YAR UWA LITTAFINA NA KUDINE DON DARAJAN ALLAH KADA KI KARANTA KI DAUKI HAKKIN HAKAN A KANKI SAI WACE TA BIYA TAKE DA ALHAKIN KARANTAWA A SAUWAKE NA FITAR DA HAKKIN KI NA FADA MAKI GASKIYA.


Don Allah ki guji daukan alhaki akanki don gujewa fita ko yaushe abinda ka raina shike zama babba gareka wata rana.
Ban gaskanta zancen tafiyana ba sai ranan da anty safiya ta dawo garin wanan karon ita kadai tazo ba tare da yar uwarta ba.
Ina wa wata mata kitso kamar yadda na saba yiwa mata kitso a kullun aka tare ta cikin mutunci ta samu Asabe na gida a lokacin.
Bata wani jima ba a dakin naji asabe ta kwalawa innan mu kira daga lungunta inna ta amsa taje sai Asaben ke fadi Abun ta shirya don anzo tafiya da itane yanzu kamar yadda na fada maku za a kaita birni aikatau.
Cikin karfin hali inna tace basan da wanan zance ba tunda tun ranan na fada karatunta nake so ta karasa ai.
Yahanasu ni kike fadawa hakan ko kinyatani kike son yi a bainar jama, a yanzu ki nuna min kina da iko kan yarki ko ?
Tama nuna in bashi ba umma zaki bada umurni har ta tsaya tana gardama a kanshi don kawai ta nuna ta isa lantana ta fada.
Eh ai naga alaman hakan kedai yar nan don kawai tana ganin an zuba mata ido dasu a gidan ko ?
A,a umma anty safiya ta fada kin san fa irin wanan abin natsuwa yake so tun farko idan har baku sharwace ta bane ta hanyar daya dace gskiya ba,a kyauta wa matar yaya ba Anty safiya ke fadin hakan.
Wani irin a fada mata ko yau kika zo daukan yarinyar nan nace na yarda ga abindana tsara ai in ita mai tunane ba zata tsaya jayaya dani ko ?
Umma ni ba jayyaya nake dake ba gaskiya ta na fada don yatinyar ban diya mace ce kowa ko bs zaiso hakan ga nasa ba a dauki yarinya akai inda ban sani ba kamar bata ds gata.
Eh lalai magana kike son daukowa kanki yahanasu umma tace tana kumfar baki ga innar mu wanda hakan yasa nayi shiru ina sauraren shiru na sauraren su daga inda nake zaune zaman kitso.
Hawaye ne ya fara zubo min sannu a hankali don na fahinci akan me suke magana naga Abba ya shigo gidan da kyat na iya budan baki na fara gaidashi.
Bai tsaya amsa min yadda ya saba ba ya nufi shiyan Asaben inda yake jin muryan Asabe yana tashi a can.
Wai yaya ne meke faruwa kuma ya fada lokacin da yake shiga wurin Asabe din yana mai binsu da kallo gaba dayan su wurin.
Wanan matar takace ke son ta raina min wayau yanzu wai bata sanda wanan zancen ba ita ba mai tafiya da yarta do ita keda abinta.
Anty safiya tace a, a umma bata fadi hakana ba ta dai nuna bata san da zancen ba sai kuma ra,ayinta na son yarta taci gaba da karatun ta tace.
Abba ya juya wurin inna yana fadin idan mugun wuri za a kai yarunyar nan ai ba za,a hada baki da safiya ko muba a kaita.
Tunda umma tace a kaita din ke meye naki a ciki yanzu banda yiwa yarinya fatan alheri kawai.
Amma dai malam kasan ba ai muna adalci ba idan akai muna haka ke nan bamu da inci daga har yaran sai yadda akayi damu ke nan.
Gunma dai kaji da kunnuwan ka yanzu abinda take nufi ke nan tun dazun ita yar nan bata fahinci hakan ba da cewa anty safiya.
Kinga ki kwantar da hankalin ki kada ki tayarwa yarinyar nan da nata hankalin taje can ta kasa tsayar da hankalin ta wuri daya.
Inna batacewa anty safiya komai ba illa mikewa da tayi ta bar dakin muna jin Asabe na fadin in ba wanan ba wani taimakone ya mace zatayi a gidan nan dayafi wanan na dan lokaci.
Dagani har matan da nakewa kitso a gurguje don inyi in gama mata ta tafi kada taji me gidan mu ke ciki batu yabi gari.
Matar ke fadi wai rikicin me ake hakane nace maganar sune ta manyan gida kawai .
Ina gama mata ta tafi na wanke hannu na na nufi dakin inna kuka na samu inna nayi wiwi zaune a dakin haka yasa nima na samu wuri na fara rera kukan kamar yadda innan mu takeyi.
Muryan Abban mune ya leko falon yake fadin wai ina yar mairon takene ta fito su kama hanya kada a yi yamma a hanya.
Kin tashi nayi sai gashi dakin ya shigo yana fadin bakiji me nace ba tashi ki shirya ku tafi Allah ya tsare hanya.
Wani kuka mai karfi na sake tare da ambatan sunan Abba din ina fadin don Allah Abba kada ku kaini birni bauta.
Har zai fita ya dawo ya tsaya yana fadin kinga kin saka yarinyar nan hankalin ta ya tashi ga tafiyan nan.
Na rasa me kike nufi da hakan gaba daya yanzu kin canza a gidan nan kin dauko rayuwan banza kin sakawa kanki saboda bakin kishi dake cin ki.
Ji Abba fa wai duk haklurin da inna keyi a yanzu Abban mu bai gani har yake fadin haka kai tsaye.
Wani tsawa ya daka min tare da fadin zaki tashi a nan ko sai na makeki wurin nan maza ki tashi ku kama hanya.
Ai gaskiyan umma data kawo sharan turaki birni aiki idan kin zauna nan uban me zaki tsinanawa mutane a nan in bada kullun ku saka uwarku a daki tana koya maku kilibibin baza.
Mikewa nayi ba shiri na shiga daukan kayana a dakin inna ya juya ya fita ganin na fara tsuntar kayana.
A cikin muryan kuka inna ke fadin yar mairo kiyi hakkuri da halin da muka riski kanmu a ciki ki tsare mutuncin ki ibadan ki da kima.
Kije har kullun Allah yana tare da mai gaskiya komai wuya komai dadi ki kula da yin addua kinji sai kuma ta kasa karasa sauran zancen saboda kukan da yazo mata lokaci guda.
Anty safiya ce tashigo dakin inna da kanta tana fadin na fahinci halin da kike ji yahanasu.
Babu dadi ace ba,a fitar maki da hakkin ki ba su sanar dake ku sasanta kanku sai dai nayi maki alkawari insha Allahu wanan tafiyan nata zai zama alheri a gareku baki daya.
Yanzu na kara fahintar rayuwan dake gudana a gidan nan naku na fahinci komai yan mintinan danayi daku a nan .
Murmushin karfin hali inna tayi cikin kukan da takeyi take fadin na yarda dake safiya Allah ya iya muna ya tsare min ita aduk inda take .
Ba komai kitafi da ita din tunda haka suka zabar mata insha Allahu tafiyan nan nata zai zama maku alheri tunda bada zuciya daya suka tura maki itaba.
Ta bude jakka ta ciro kudi masu yawa tana fadin hjyn da zan kaitane ta bada wanan kudin aba iyayyen ta.
Nayi niyar baiwa umma su sai na fahinci akwai kulli cikin harkan nan don haka ki karba kiyi maza ki boye albashin tama idan an bayar nasan yadda zan dinga maku dashi insha Allahu.
Don sam ban dauka ita za a bamu ba nadai zowa umma da zancen muna son yarinya a garin nan idan da akwai yadda za a samu.
Sai yau danazone naga ashe itace zamu tafi da ita ki dauka kamar tana gaban kine insha Allahu.
Jin hakan da anty safiya ke fadi ya kara kwantarwa umma da hankali sosai muryan Asabe ne ke fadin .
Wai ina safiyan take ne in kin soma ki bar bata bakin ki wurin lalashin ta ko ta yarda ko kada ta yarda tafiyan nan ba fashi .
Muna ji muna gani haka muka kama hanya da yan kayana cikin ledan bacco don banda jakkana tafiya da zan saka kayan a ciki.
Inama na taba zuwa hana rantsu daga makaranta mukazo zaria kuma ba a bari an kwana ranan muka koma gida wurin iyayyen mu.
Har kofan gida wurin mota asabe ta biyo mu da lantana tana fadin atafi can a dandadi duniya aji yadda take.
Kina nan zaune gida ba wanda ya taya balle a sallama muna da sunan kiranki zance.
Umma wa zaiso ta a haka tana zama ko yaushe kamar kucaka gari kamar a kansu talauci ya kare a duniya.
Allah yasa dai ta iya abinda taje yi din kar taje ta jawowa mutane abin kunya a can don dai sanin hakin kam.
Kallon Abba nayi don jin abinda lantana ta fada sai naga Abba ya kawar da kanshi gefe daya na mayar da kallona kofan cikin gida namu ko Allah zaisa inga inna ta leko sai dai har motar ta daga banga inna din ba.

KADUNA

Hjy iyami zaune a dining din gidan bata da hutu a yanzu tun soma wanan zancen aikin data samu din koda yaushe tana makale da waya a kunnen ta.
Yanzu ma wayan ta kare da wani lauyanta kan kammala mata duk wani takarda da take bukatan samu wanda za a tura abuja a tura zauren majalissa.
Abincin dake gaban ta ta kalla tana dan jan tsuki kafin ta kai hannu ta sama warmer din abincin dake gaban ta.
Budewa tayi sai ga tururin abincin dake cikin kulan yana tashi kamshi ya daki hancin ta tabe baki tadab yi don tasan ba lalai ne yayi dan danonon da take so ba.
Plate ta jawo zuwa gaban ta ta fara diban abincin kadan ta tsakura don ba gwana bace wurin loda abinci a cikin taba.
Lemo ta tsiya ta fara kaiwa a bakinta tana lumshe ido do sanyi da dandanon shi dake shiga cikin ta lokaci guda.
Sallama akeyi a kofa ta amsa tana ba maishi umurnin ya shigo tafiya yake a cikin isa da izza har ya karaso inda take zaune.
Daga tsayen da yake suka fara gaisawa dashi idon shi ya sauke kan abincin dake gaban ta kafin ya amsa mata gaisuwan nata.
Bissimillah ka zauna take nuna mashi kujeran zama dake wurin yace ba zama nazo yi ba nazone in kara jin abinda kika yanke ga maganan mu.
Alh Adamu ina dai yanzu kasan ba,a karskshin ku nake ba don mai rabawa ya raba tsakani da yayan ku ko.
So banga wani abinda zaisa ka jefa kanka a cikin lamarin rayuwana ba kuma.
Yara daine babu taulali a cikim su gaba dayan su sun kawo girma don haka ka barmu muyi rayuwan mu a cikin sallama don Allah.
Jin abinda ta fada yasa ya dan sakd murmushi a fuskan shi yana jawo kujeran yakai zaune tare da fadin zaki iya fadin haka tunda baki so gaskiya.
Kin sani sarai wanan abinda nake neman ki dashi ba haramttacen abu bane sunnan ma aiki zamu raya ta hakan.
Wani kallo ta watso mai tare da fadin Alh Adamu na fada ma ka fita hanya da maganan banzan ne shin wai yin aure dolene ?
Ya dan kara sake murmushi yana fadin amma kinsan aikin ladane ko na rasa meke damun ki kan hakan idan don ta matatace kinsan dai a yanzu kinfi karfin ta ta ko ina.
Mikewa tayi a fusace tana nuna mai kofa tare da fadin fita min daga gida tunda kai bakasan abin arziki ba.
Kai ko kunya bakaji kazo ka kalli idona kace wai aurena kake son yi don kawai kunga kasa ya fufewa mijjna ido.
Yace shi kansh miijin maki ai da zai tasone a yanzu zaiyi alfari da abinda nake shirin aikatawa a yanzu.
Eh na yarda lalai namiji baida kunya yau Adamu kaine da kanka wai kazo neman yardana akan in aureka don kasa ya gama rufe minin idon miji ko ?
Har kamanta da irin tsana da kiyayyan da matarka ta saka min a gida lokacin da kuke ganin kowa a banza a idon ku shine yanzu don baka da kunya zaka dawo da wani zance a kaina.
Matsalan ku ku mata ke nan dawo da abinda ya wuce baya kada ki hada wancan lokacin kurciya da yanzu garemu.
Ni niyana na alheri ne gareki nasan ko yaran ki zasu farinciki da zaben dan uwan mahaifin su a matsayin mijin ki a yanzu.
Ka fice min gida kafin in saka a fitar min dakai ta tsiya ya ce bazan gaji da tunkaran ki da wanan zancen ba har lokacin da zaki sauko don kanki.
Yana fadab haka ya juya ya bar gidan bishi tayi da kallon takaici da kunan rai wanan yana daya daga cikin abinda ya hanata dawowa kasan tun rasuwan mijinta.
Yana fita gidan wuri motar shi ya nufa kai tsaye yashiga ya dade a zaune yana karewa gidan kallo yata da motar ya tafi.

Mun kawo lokacin yamma baiyi ba sosai don la, asar ya wuce a lokacin kai tsaye gidan anty safiya muka nufa.
Gidane tsarare mai ban sha,awa gaskiya ba laifi gidan ya hadu ni dai a ganina ciki muka shiga yayin da muka zauna a falo.
Tau zainab kinga gida yau dai don har umma bata san inda muke zaune ba duk zumuntan mu da ita yau sai gashi ke Allah ya kawo ki gidana.
Mikewa tayi zuwa wurin fridge ta dauko min ruwa mai sanyi a fridge ta aje min tare da fadin sha ruwa kafin ki shiga ki watsa ruwa kiyi sallah sai ki fito muci abinci.
Daukan ruwan nayi da zuman sha sai naji sanyin shi yayi min yawa a bakina ta yadda bazan iya sha ba.
Mayar da kofin nayi na

4 Comments On ABU CIKIN DUHU
avatar
khadija-8-3

1 year ago

Reply

I want to download this book

avatar
daiy

1 year ago

Reply

Replying to khadija-8-3

You have to subcribe to our package in order to download our novels

avatar
zainab-3-3-5

1 year ago

Reply

I also want to download this book

avatar
daiy

1 year ago

Reply

Replying to zainab-3-3-5

You have to subcribe to our package in order to download our novels

Please Login or Register in order to submit comment