Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aje saman dan table din ta dawo tana fadin taso in nuna maki dakin da zaki zauna kafin in kai gidan da zaki aikin.
Dakine da gado sai mirrow ta nufi wani kofa tana fadin nan bandakine ki shiga kiyi wanka da alwala ki fito.
Tana fadin hakan ta juya ta fita daga dakin kayana na fara cire na nufi bandakin kamar wace za,a cewa na sheka na sheka da gudu.
Ina shiga naja na tsaya wuri daya ina karewa wurin kallo da mamakin ban dakine haka a gyare tsab.
Saida na gama karewa wurin kallo na nufi bakin famfon dake ciki badon na taba amfani dashi ba a fili amma dai nasan yadda ake kunnawa ruwa yazo.
Don an koyamu a makaranta nagani wanka nayi a tsanake zuciyana fam da tunanen inna mu da yan uwana.
Sai kuma tunanen Abban mu dasu Asabe irin maganganun batanci da sukeyi lokacin da zan baro gida don wai kawai ina ya mace suke min hakan.
Sallah na tayar saman kafet din dakin ban tsaya neman sallaya ba don wurin tsab yake ni a ganina ina zaune a gurin bayan na idar da sallah.
Sai ga anty safiya ta shigo dakin tana ganina kasa take fadin subbahanallahi zainab badai a kasa kiyi sallah ba sam na manta da na kawo maki abin sallah a dakin taso muje kici abinci ko ?
Mikewa nayi na biyo ta zuwa falon na samu yaranta da sukaje islamiya sun dawo gida a lokacin.
Ku gaida anty tace wa yaran da suke kallona da mamaki a fuskokin su suka fara gaidani din kamar yadda mahaifiyar nasu ta umurce su.
Wuri ta nuna min na zauna tana fadin ki saki jiki ki nan kamar gidane a gare ki zainab.
Nakai zaune ina murmushi abincin ta debo ta kawo min a gabana tana fadin ci abinci nasan rabon ki da abinci tun safe.
Kallon abincin nayi dan shikafane da miya sai taliya da ganye da nama tsoka uku a sama.
Dan tsakura nayi duk da ya zamo min bakon abincin daya dace inyi dsukin cin shi a lokacin tunda ban saba cin abinci haka ba.
Sai gashi halin da zuciyana yake ciki ya hanani cin abincin sai tunanen yan uwana da innarmu nakeyi a raina.
Gashi yan uwa basu gida aka wuto dani balle ko sallama in samu inyi dasu tunda bansan tsawon lokacin da zan dauka a wurin wanan bautan ba dabazo yi garin kaduna kamar yarda umma tace.
Bansan mijin anty yana gidan ba saida naji yana magana da yaran shi na dago da sauri ina kallon shi.
Gaidashi nayi hakan yasa ya dago yana kallona tare da amsa min gaisuwan da nayi mai yake cewa.
Itace kuka zo din tare eh yar dan uwanane sukai min karamci suka ban ita kaga abin yazo min da sauki ke nan.
To Allah yasa a dace sai ki ja mata kunne sosai don kin san zama a irin gidajen nan ba kowane zai iya rawayu dasu ba.
Daki na mike zan koma anty ke fadin zaki shiga cikin ne kuma kifa sake jiki nan gidane na fada maki.
Nace zan kwantane ina shiga naji mijin na anty na fadin wanan yar yarinyar suka turo ban san me yasa mutanen kauye suke da wanan akidar ba kan yaya mata.
Yadda wanan rayuwa take a yanzu kosu masu dauko yarab dasun gane su dogara da shiga fadawa wani rikici sam duniyan nan cike yake da rudani daban daban.
Sai dai daman ita wanan din da kika dauko ansan gidan su da kuma inda zaki kaita din in don haka ba gaskiya da zan baki shawara ki mayar masu da yarsu inda kika dauko ta.
Nima kaina saida naje naji banji dadin ganin wanan yarince zasu ban ba don uwarta ba karamin rikici akayi da ita ba kafin ta yarda muzo nan din.
Yace ke nan uwar tasan kanta da abinda take yi ga yarinya kallo daya zaikai mata kasan tana cikin wani yanayi.
Zaka iya sani tunda aikin kune hakan ai don nuna fin karfi kawai aikai masu daga ita har mahaifiyar ta aka ban ita.
Shine kuma kika dauko masu ya safiya baki tsoro abinda kaje ya dawo nan gaba kada faki lalata maku zumunci .
Wallahi don dai hjy iyami ce kuma na riga da nayi mata alkawarin hakan kaga idan na saba mata ba zataji dadin hakan ba.
Yace Allah ya sauwa ka saidai kija mata kunne sosai kafin ki kaita na fada maki zama irin gidan nan akwai kalubalin masu yawa ga wanda bai saba hakan ba.


ZAINAB IDRIS MAKAWA





🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅


7️⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

RAYUWA KE NAN YAN UWA MU FADI ALHERI KO MUYI SHIRU SHINE KOYI DA SUNNAN ANNABI SAW , , , ,


DON ALLAH YAR UWA KADA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA BA DON ALLAH KI GUJEWA KAYAN ALLAH YA ISA A KANKI

2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 300 NE KACAL ZAKI TURA SABODA ALLAH SHINE HAKKINA GAREKU.


Na dade kwance a dakin badon nayi barci ba tun ina jin karan tv da muryoyin su a falon har nazo na daina jin komai ina jin anty ta shigo tana ja min abin rufa sai naji sonta na yan uwan taka ya kara shiga raina sabanin dazun da nake jin haushinta ina ganin da hadin bakin ta wurin rabani da yan uwana da innan mu.
Tambayan kaina na karayi karo na batkatai mai Asabe da lantana suke nufine a kaina.
Mau ye lafin innar mu da bata ganin laifin Abba shi tunda ba inna kadai ta haifomu a mata ba.
Meye laifin kasancewar yaya mata da asabe ke gani ga innan mu damu wanan halin shi a kowani gida da yaya mata sukafi biyu zuwa ukku kamar mu.
Ba addinine yace a kyamaci diya mace ba wanan hain rayuwane na wasu mutane da hakan ya zama masu al,ada.
A ganina duk da da aka haifa ta sunna walau mace ko namiji albarkan rayuwa ya kamata iyayye su newa yaro.
Ni dai ba zan iya cewa nayi wayau naga inna da Asabe a cikin dadin raiba a gidan mu duk ko da irin biyayyan da ina ke mata sau da kafa.
Ba zan manta a da can baya har talla asabe ta fara dora min idan na dawo boko zan dauki tallan goro ko gyada in fita dashi duk da ina kankanuwa a lokacin.
Da kyat Abba ya samu ya hana wanan tallan ranan kan yasha fitina wurin Asabe ba Abba kawai ba har innan mu ba,a barta ba don cewa Asabe tayi inna ce ta zuga Abban mu don tana bakin ciki ina fita mata talle.
Haka muke abu kamar marayu a gidan mu bawai don mun rasa uwa da uba a raye ba sai don kawai zama da fitinaniyar uwar miji da Allah ya hada inna da ita.
Yanzu kuma tsanar yakai har Asabe ta turoni yin aikatau a birni ba tare da kowa ba gidan mu yasan inda za a kaini ba.
A haka naci gaba da sake saken abinda zan tafi in taras gidan da Anty safiya zata kaini din.
Juyawa nayi ina lumshe idanu tare da fadin Allah yasa hakan shine alherin mu gaba daya kamar yadda anty safiya ta fadawa inna da zamu zo.
Har barci ya daukeni ban sani ba ga dai gadon laushi ga fanka a dakin na samu amma haka bai hanani barci a cikin damuwa ba.
Karfe biyar da wani abu na falka kamar yadda inna ke tayar damu don sallah asuba idona bude nabi daki da kallo .
Sai a lokacin na tuna da inda nake a yanzu da sauri na sauko saman gadon na fada bandakin dake dakin da nake ciki .
Alwala nayi a gurguje na fito na tayar da sallah ina idarwa na dan zauna nayi addua kafin in mike na bude kofan a hankali na fito dakin.
Duk da sauran duhun dare gari bai gama haskawa ba a lokacin amma na gane hanyan kitchen din anty safiya da jiya naga tana shiga tana fitowa da abinci.
Wanke wanke na sama tare a kitchen din ban tsaya jiran komai ba na shiga wanke su a hankali don kada in tayar da mutanen gidan don har lokacin banji motsin kowa a gidan ba.
Na gama na share kitchen din na fito zuwa falo na fara shara da kakabe kujeru da suka kewaye falon can naji motsi alaman wani na fitowa daga dayan dakunan su na kwana.
A, a naji muryan anty safiya na fadi zainab kece a nan kuma har kin tashi ashe ban sani ba yau na gajine sosai dan tafiyan nan da mukayi jiya duk jikina ciwo yake min wallahi.
Ban bata amsa ba sai kaiwa da nayi kasa ina gaida ita da kwana ta amsa min a gurguje tana shiga kitchen din ta.
Sai kuma gata ta fito tana fadin ke yaushe kika tashi halan da kikayi wanan uban aikin haka zainab kin koyi barci da dare ko kin kasa barcine kina tunanen gida.
Nace nayi barci dana tashi nayi sallahne na fito na wanke su tace ikon Allah toh sannu da kokari ashe tafiya zatayi kyau tunda baki da son jiki haka ?
Abinci ta hadawa yaranta yayin da ni kuma na share ko ina na gidan sai gaidani da aiki takeyi tana fadin kinga idan har zakici gaba da hakan ina mai tabbatar maki zaki ji dadi sosai a wurin hjy.
A raina nace watau ma wurin hjyce za a kaine kenan matar mai kudine tunda naji harda hjy anty ta kirata matar yanzu.
Ni tace in shiga in shirya yaranta a wani daki nayi ta bin dakin da kallon mamaki a raina tana min bayanin abinda zan masu.
Ta fita ta barni da yaran a dakin ina shirya su bayan nayi masu wanka da broshe tsab suka fito a tare muka fito daga dakin tace dani kinga koma ki gyaro min dakin nasu in karasa shirya su a nan.
Dakin na koma na fara tattara kayan da suka watsar kafin in hau gadon dakin da gyara kafin wani lokaci sai ga dakin tsab dashi kamar bashi bane suka bata dazun da tarkace ko ina.
Nan anty safiya ta yaba min sosai tana kara min bayanin kinga tun da safe idan kin tashi kinyi sallah.
Kada ki tsaya sanyin jiki ki yi duk wani aikin da kika san naki ne a gidan tunda kina da kwazom tashi haka da safe.
Don Allah zainab kada ki yarda ki bani kunya don inda zan kaiki nima gidan kunyanane can tayi bugun gaba ne dani tasa in samo mata yarinya natsatsiya mai kwazo da tsabta da amana.
Idan kinga abu ba a baki ba kada ki yarda ki taba shi komai son da kikewa wanan abin a ranki.
Na amsa da to anty tace zaki ga kudi kamar a banza mai yuyuwa zata gwada ki na dan lokaci taga idan kina da amanan hakan kafin ta yarda dake bandai sani ba.
Zan fada mata gaskiya ke din yar uwatace ta jini don ba zan lamunci suyi maki wullakanci irin wanda akewa yan aiki ba ke kuma sai ki rike min amana sosai don Allah wanan abin taimakon kai da kai zamuyi tsakani nidake zainab.
Insha Allahu anty na fada don idan ta kirani da zainab din nan yanzu sai inji kamar badani take magana ba.
Wasa wasa na share sati daya gidan anty safiya banji zancen tafiya gidan da za a kaini din ba, nima kuma ban tambaya ba.
Ashe hikimar ta na barina a gidan ta don dai in koyi wani abinda ta fahinci ban sani ba kada ta kaini a sha wuya a can .
Gashi kullun cikin yi min bayani take da fahintar dani komai na rayuwa a birni wanda mu can kauye bama yin su.
Har na dan fara sabawa da yaranta yanzu sosai ranan da dare muna zaune falo muna kallon wani shiri na yara naji anty ta ambaci sunana .
Hakan yasa na juyo ina kallon ta cikin ladabi take fadin ina ganin gobe zan kaiki wajen hjy dazun muyi waya da ita take tambayana ke .
Wani irin ba dadi naji a raina lokaci guda damuwa da fargaba ya dira min a zuciyana lokaci daya.
Ganin canjin yanayina take fadin ki kwantar ds hankalin ki can ma nafada maki gidane a garemu ai tunda gidan babban yayan mu ne saidai shi a yanzu bai raye matarce kawai da yaran su a gidan kuma yaran ba yara kana bane sun girma kananan ma zaku zo yan sa,a daya dasu.
Sai dai daga mazan har mata kada ki shiga tsabangan kowa duk abinda suka saki indai baya kaucewa idini bane wanda kuma ya shafi gaban kowa a cikjn gida kiyi.
Na fahinci may anty ke nufi a nan ma, ana na kama mutuncina da kimata ga kowa a gidan dai.
Haka na kwanta da tunane mai yawa sai kewan gida ya dawo min sabo sosai a raina don haka ban samu barci sosai a ranan saboda tunane.
Karfe goma na safe muka bar unguwan su anty safiya wanda nake jin ana kira da barnawa muka doshi inda zasu kaini a motar mijin anty safiya din.
Anty ta ban wani jakka nata na saka yan kayana wanda ta sai min kala hudu dana zo don tace nawa ba zasu tafi ko ina ba a haka.
Sai bin garin nake da kallo yayin da anty suke gaba da mijinta zaune suna dan hiran su da ban san ko a kan wa suke zancen su ba.
Kafin mu bar gidan anty safiya sai da sukai min nasiha sosai mjin anty safiya yace in kiyaye ibadana inyi hakkuri da duk yanayin da zangani a gidaba, ainyi biyayya ga wa yanda na sama a gidan.
Shiga nan bullo nan har muka kawo unguwar mai kama da kasan waje muka fita ba jahata na kaduna ba.
Uguwar kanshi abin kallo ne ba mutane sai motoci jefi jefi da suke wulgawa saman shimfudeden kwaltan da aka zuba a titin.
Idan kaga wanan ginan sai kace shiyafi kyau sai kuma idan kaga wani kallo ya koma sabo.
Wani katon gida daya tafi da imanina tundaga nisa mijin anty ya tsayar da motan shi yana danna horn.
Kafin wani mutum daba tsoho ba ya fito yana dan lekowa naji anty na fadin bude get mune da mijina.
Ya amsa yana washe baki tare da saurin komawa sai naga kofan na budewa kamar injin.
Ya danna kan motar zuwa cikin gidan naji mutumin gidan yanayi masu sannu da zuwa da alama dai yasan anty din sosai .
Saida mijinta ya tsayar da motar shi ne take fadin amma dai kasa yau zaka shiga ku gaisa da hjy ko ?
Yace zan shiga kodon ta san yarinyar nan tana da muhinmaci sosai a garemu ai don ni dai da kinbi tanawa da ba, , ,
Please dear ina mun gama wanan zancen tun a gida sai kuma ta juya da harshen turanci tana magana.
Ko ta dauka bokona baikai indanji abinda take fada bane oho do maganan da sukeyi da alama mijin nata yace a mayar danine kota rikeni tunda yar uwarta nake.
Allah sarki nace a raina wanda ma suka haifeni suka san zafina sun kasa barina a gaban su balle anty da daga sama ta ganni haka.
Don ina jin tana fada mai taso hakan amma kawo ni nan din shine mafita a gareta naji yace to shike nan Allah ya tsaya mata da hausa.
Su suka fara fita daga motar kafin anty din ta zagayo ta bude min gefen da nake tana fadin in fito.
Na fito sai bin gidan nake ko ina da kallon mamaki ina rayawa a raina wai yanzu mutane ne sukai wanan ginan haka da hannun su ?.
Nidai ina bisu a baya ina karewa gidan kallo ta danna wani abu a bango ba, a dauki lokaci ba sai ga wata yar dattijuwa farace tafito tana fadin waye sai sukayi arba da anty dake tsaye a kofa.
Hjy kece take cewa anty safiya nice kande ko hjyn tana ciki ta tambaye ta ?
Tana nan yanzu ko tashiga daga cika ta fadi tana matsawa daga kofan da take tsaye.
Shiga mukayi kai tsaye saida naja baya don abindana fara takawa ko ina na falon sai kyali yake da daukan ido.
Zama sukayi a kujerun dake katon falon yayin da nakai kasa daga gefen anty din mijinta ya kalleni tare da fadin ki zauna saman kujera mana.
Naji anty tace kasan ta ai da halin su na yan kauye barta kawai zata zo ta saba wata rana ai.
Matar da naji anty ta kira da kande ne ta dawo falon dauke da tire da abin sha a ciki.
Ga kan shin girki yana tashi a wani bangare na gidan duk da kamshi da falin keyi bai hana na girkin ziyaran hancina ba.
Ga abin sha hjy kafin hjy ta fito, ta fada tana ajewa a gaban su bin abinda ta aje din nayi da kallo.
Saida suka dan taba hira da mijin ta muna zaune ni dai sai bin hotunan dake tsaye a falon manya manya dasu kamar mutun ne tsaye a wurin nakeyi da kallo.
Sai ga matar gidan ta fito da fara,a a fuskanta tana fadin ashe kuna tafe yanzun nan na shiga ciki.
Tun safe yaran nan suka tayar dani da rigimar su na fito tarba na mutunci naga tana masu tana saki fuska da jiki dasu.
Ta kalli mijin anty tana fadin yau baka fita aiki ba ke nan ta fada tana kallon shi.
Ban fita daga nan zan wuce ya bata amsa da kara fadin yarinyar nan muka kawo dama.
Ta juyo tana kallona tare da dan kuramin ido na dan lokaci tace masha Allah.
Yarinya kamar kin shiga zuciyana kinga irin age din da nake so ta kasance min gashi ko kin samu ai anty safiya ta bata amsa.
Menene sunan ki ta juyo tana tambayana kafin ince Abu naji anty safiya tace zainab ce sunanta.
Kai zainab kice uwata ce ashe yarinya kin samu suna mai kyau kuwa tana kallona da kulawa.
Aikuwa na manta sunan mama na unguwar rimi ke nan fa dacewa kanwar mahaifiyar hjyn .
Mijin anty ne yake fadin ni zan tafi hjy don Allah sai a hada da hakkuri don kin san yarinyar akwai kurciya da kauyanci a tare da ita yanzu.
No no no kada kuji komai wallahi muma ai kauyene asilin mu a da ko kowa ka gani daga kauye yake ai.
Shigowa wasu yara kanana su biyu mace dana miji falon yasa zancena ya tsaya a nan suka juya magana kan yaran.
Anty ke fadi a a ashe mutanena suna nan sai hjy tace wai yau hutu sukeyi basu je school ba sun shiga meet time break ne.
Hannu anty safiya ta mika masu suki tare da make kafadun su suka nufi sirin kakan su kai tsaye.
Tafiya ya fara yi tare da fadin to zainab a kulla kinji banda rashin ji anty safiya tace in tayi rashin ji ai zata gamu da nine sosai.
Karfe nawa zaka dawo yace na fada maki sai yamma don haka idan kin gama ki koma gida don yara kada su dawo school bakya nan.
Wai har yanzu motar bai tashi bane hjy ke tambayan anty motar ta kafin anty tace wanan motar ai sai wata yanzu gashi yaki ya saya min wata ina ta faman bin shi yana ja mi rai.
Ki bar kanina ya huta safiya indon motace zan sa a duba maki idan ba zaki raina ba dai kai kai kai kice wanan zuwan takice ashe mijjn ta ya fada .
Kasan ai safiya ta hannun damana ce sosai tafi danan a gurina in dai tana so.
Ya tafi tare da ma hjy sallama nabishi da dan kallo kamar ince don Allah kada ya tafi ya barni.
Anty ta mike tabi bayan shi bayan tafiyan tane falon ya danyi shiru tana ta danne danne a wayan ta sai ga anty safiya din ta dawo falon.
Zama tayi sukaci gaba da hira a cikin hiran nasu ne take fada mata yadda muke da ita .
A hiran na kara fahintar irin zumuntar dake tsakanin mu da ita din wai ashe mahaifiyar su da Asabe ce ya da kanwa.
Asabece ya mahaifiyar su kanwarta tace kai kice min ita din ta gidace ashe eh ta gidace gaskiya sai dai gaskiya kin san yadda zumuncin zamanin nan yake ai.
Koma dai yaya ne ai takice ita zan duba inga yadda zamu zauna sai ta kira wanan matar ta dazun data kawo ruwa tana fadin.
Kande ga bakuwa ki bata daki wanan na kusa dani zaki bata don ni tazo gidan nan don kula da harkokina.
Don haka zaku zauna tare sai dai kowa da aikin shi daban ke naki kula da kitchen ne da sauran ayukan da kika sa kinayi.
Ita din dai ki barta dani sai zuwa gaba idan ta saba zan fara nuna mata aiyukan ta yadda ya dace.
Sannu da zuwa kande tace min tana kokarin daukan jakkar kayana da anty ta shigo dashi ta aje a kuss dani.
Kagin anty tace na karbs ni har na mike ina karba matar na fadin ai da ki barta bakuwace fa nace a a mama kawo in dauka.
Jeki ta kaiki daki da zaki zauna kafin in shigo hjy ta fada tana dora kafanta saman dan table din dake kusa da ita.
Muka nufi cikin gidan wanda bai isata da kallo matar na gaba ina binta har zuwa cikin dakin da akace ta kaini din.
Dakin ta bude tana fadin bissimila shigo daga ciki nabi bayanta muka shiga.
Wanan shine dakin ki sai ki zauna ki huta kafin girki ya sauka a wuta muci ni nawa dakin yana can daga waje kadan ta hanyar kitchen idan kina nemana.
Daga haka ta juya ta barmin dakin ina tsaye sai bin dakin nakeyi d kallo nida ke santin gidan anty safiya sai gani a wanan dakin da fadin tsaruwan shi bata lokaci ne.
Anty safiya bata bar gidan ba sai karfe dayan rana bata tafi ba saida ta shigo dakin ta kara min nasiha kan nayi biyayya ga kowa a gidan .
Ta tafi ta barni cikkn kadaici da damuwa a gidan da ban san kowa a cikinsa ba ban ma san a inda nake

4 Comments On ABU CIKIN DUHU
avatar
khadija-8-3

1 year ago

Reply

I want to download this book

avatar
daiy

1 year ago

Reply

Replying to khadija-8-3

You have to subcribe to our package in order to download our novels

avatar
zainab-3-3-5

1 year ago

Reply

I also want to download this book

avatar
daiy

1 year ago

Reply

Replying to zainab-3-3-5

You have to subcribe to our package in order to download our novels

Please Login or Register in order to submit comment