Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba dai.
Wani irin kuka ne na rushe dashi ganin ta tafi ta barni daga ni sai halina sai wa yanda a yanzu zan zauna dasu din.
Ganin kuka ba zai min bane yasa ni tashi na shiga bandaki dukda ba a nuna min ba dan zaman da nayi gidan anty na dan fahinci ya ginan birni yake yanzu.
Alwala na dauro nazo na tayar da sallah ban daga ba na dade a wurin ina addua kafin na dan kai kwance sai ga barci ya daukeni a haka ba tade dana sani ba a wurin.
Babu komai a raina sai tunanen halin da mahaifiyata take ciki a yanzu tare ds yan uwana a raina.
Nasan innan mu zata kara shiga wani hali a yanzu don barina kusa da ita dan taimakon su daya ne wanan kudin da ban san ko nawa bane da anty ta bata da zamu zo.
Irin wanan tunanen nakeyi sai hawaye yazo mi lokaci guda don tunanen hakin da inna zata shiga yanzu da ban kusa dasu dama da dan kudin kitson da nake muke tallafawa ake samun abinda akaci.
Gashi yanzu lantana da Asabe sunyi makarkashiyan da aka raba tsakanina da mahaifiyata da yan uwa anya zan iya mantawa da wayan nan mutanen a raina kuwa , ?
.

ZAINAB IDRIS MAKAWA




🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅

8️⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH KA SADA MU DA RAHAMOMIN DAKE CIKIN WANAN RANAN TA JUMMA,AT ALLAHUMA AMIN , , , , , ,

DOMIN SAYA SAI KI TURA KUDI TA WANAN ACCOUNT DON KAMAR HAKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK, , , , , ,


Ni Abu ban taba tunanen zan gani a cikin irin wanan dakin ba ko a mafalki ban taba hango wanan irin gidan a malkina ba.
Yau sai gani nayi barci na falka na ganin cikin wanan gidan ga sanyin AC da kande ta kunna kafin ta fita ya hade dana ties din dakin yana ratsa balgon jikina a hankali.
Duk da sanyin yana damuna ban tashi a yadda nake kwance ba a kasan na dunkule a wuri daya sai faman tunane nakeyi na rayuwa.
Muryan hjyn ce yasani dagawa daga inda nake kwance wanan karon ta sauya kayan dake jikin ta zuwa dogon riga mai laushi da daukan ido jikin shi wani dabbara dabbara ne kamar jikin zabra.
Taci gaba da fadin ke zainab bakya gudun sanyin kasan nan ya ja maki illa kiyi ciwo fa.
Da sauri na dago ina gaida ita dakin take bibda kallo ta sauke idon ta ga jakkan kayana tana fadin ga wardrobe nan ki saka kayan ki a ciki .
Taci gaba da fadin ki dunga kula da kani ki kula da tsafta sai muyi zaman mu lafiya.
Mu gaimaki juns tsakanin mu don kingani nan bana shiri da wanda baida tsafta sam.
Iyakar sikin ki a gidan nan yanzu shine kula da sashina da komai wanda ya shafi rayuwana a cikin gidan nan.
Yarana duka manya ne kuma duk zasu girme maki kinga kenan suna matsayin yayyin ki ne.
Ni a yanzu yar kasuwace kuma mai rike da mukamin gwanatin kasan nan .
Kinga ina da manyan hidimomi a tare dani wanda hakan yasa banda lokacin kaina shine dalilin da yasa nace a samo min yarinya da zata dinga taimakamin.
Sai gashi ke Allah ya nufa a sama min na kuma yaba da irin yanayin dana ganki dashi na natsuwa .
Ina fatan zaki zauna damu gaba daya gidan nan da zuciya daya cikin amana da yarda.
A hankali na dago kai tare da fadin insha Allahu hjy nayi alkawarin hakan.
Ban iddasa rufe bakina ba tace ba hjy nake a gurin ki ba mami nake don ni uwarkice a yanzu ki dauke ni yadda sauran yaran gidan nan suke daukana.
Da fatan kin fahince ni tace ta fara tafiya don fita dakin tare da fadar ki fito kici abinci a falo yanzu idan kin gama saka kayan a ciki.
Na amsa da to hjy da sauri nace mami tayi murmushi ta fita yayin da baki na yake dafe don katobaran dana farayi.
A gurguje na jera kayan kamar yadda tace saidai saida nasha wahala wurin gane yadda zan bude wardrobe din.
Falon na fito na dauka ita kadai ce kamar dazun sai dai naga sabanin hakan don sun kai su gama zaune wurin a ganina.
Ja nayi na tsaya dan nisa kadan dasu ban karasa wurin da suke ba hjy ce ta dago tana fadin.
Zainab zo ki zauna mana kici abincin tana kallon inda naja na tsaya dan nisa dasu kadan.
Firgigit nayi daga sana,ata dana fara watau tunane don yanzu ya zama min abin yi ko yaushe.
Sai lokacin sauran dake zaune suka farga da fitowana falon gaba dayan su juyowa sukayi suna kallona lokaci guda.
Karaso mana kizo nan ga abinci nan ki diba ta kara fada sai naji sun kwashe da wani dariya.
Wai mami sabuwar mai aikice kika dauko kuma take tambayan hjy tare da juyawa taji amsan da zata bayar.
Haba dai mai aiki a haka kuma sai a rasa wace za a dauko aiki sai wanan yar kauyen haka irin yan kauyen nan fa wahalan sha,ani garesu kafin kansu ya waye don basu iya komai ba sai shirme da kauyanci wata yar farafara ta fada.
Dayan ta yamutsa fuska tana fadin but she is dirty mami don Allah kada ta karaso nan inda muke.
Ai kin san halin hajjajo da son mutane yanzu haka wani wurin ta kwasota itama ya fada yana mayar da kai ga abincin da yake ci.
Yar uwan gwaggon Safiya ce kuga kenan kuma ta zama yar uwarku ai .
Yanzu a nan gidan zata zauna damu ke nan ko dai tazo yin wani abune Rufaida ta tambaya a yatsune ?
A haka mami zata zauna damu Nazifa ta fada tana kyabe baki tare da fadin ashe zamu sha kauyanci a gidan nan kuwa.
Hjy tayi murmushi tana fadin in dai wanan da kuke ganine cikin kwana biyu zata goge ta zama yar birni tayi fes kamar kowa.
Dariya suka sa gaba dayan su a lokaci guda nidai ina tsaye a inda nake ina kallon su kasa kasa ina jin cin mutuncin da suke min.
Zainab kinja kinyi tsaye karaso mana ki dibi abinci kici hjy ta fada tana yafutoni da hannu.
A, a mami don Allah dai karta matso nan ta bari idan mun gama sai ta zo ta diba amma ai haka raina mu zatayi ta dauka daya muke da ita.
Tsawa hjy ta dakawa mai maganan tana fadin karna sake jin haka daga gareki ita din ba mutum bace kamar kowa nima a haka mahaifin ku ya daukoni ai.
Shiru sukayi suna cigaba da cin abincin su yayin dana karaso inda hjy take na dan labe ina kaiwa kasa na fara gaida su.
Ku duba yadda ta baku girma yanzu a cikin mutunci amma ku kuna kokarin zubar da darajan ku a idanunta, baku san cin fuska baida dadi ba.
Shiru sukayi kowa na kai abinci ga bakin shi tashi ki dibi abinci hjy ta sake fada karo na barkatai.
Plate wace batai magana ba ta jawo ta fara zuba min salma ke nan ta juyo tana fadin may za, a zuba maki ?
Na nuna wanda ke cikin plate din dayan namijin dashima baiyi magana ba sai kallon banza da yake min.
Dariya suka kwashe dashi ya dago kai yana tambayan menen suke cewa choice din ku daya da yarinyar nan abincin ka ta nunafa.
Ware idanuwa yayi waje tare da fadin ke ni sa,arkice bakiga kowa ba a wurin nan saini halan.
Yana fadin haka yai kwafa ya ture abincin ya tashi daga wurin sai suka kara fashe mai da dariya.
Miko min abincin tayi na karba tare da dan rusunawa ina fadin nagode na juya zan bar wurin naji hjy na fadin ina kuma zaki tafi kici abincin ?
Dan marairaicewa nayi ina fadin dakina hj, , mami ba zaki sake jikin ki ba har yanzu kina kewan gidane ko nidai na danyi murmushi na juya na tafi.
Ina kallon abincin wai duka wanan naman da aka zuba a ciki nawane ni kadai kai yan birni kan suji dadin su.
Wanan ai shine zamuci duka gidan mu da sallah idan yazo don sallah kadai muke cin nama sai ko idan rabo ya ratsa Abba ya sayo muna a ci.
Gaba daya na cinye abincin tas na dauko plate din zuwa kitchen don na fahinci a nan kitchen din yake dazun da mama kande ta fito da abinci.
Na canka daidai na samu baba larai tare da wata mata tana juya miyan da zasuci da dare miyan kaine saidai ban san ko kan me bane na daiga ya ciko tukunya sosai tana motsawa.
Gaida su da aiki nayi kande ke fadi kin kamala ci yar nan ina jin marasa ta idon gidan nan dazun sunayi maki shakiyanci da suka iya.
Ki fita batun su dan haka halin su yake da rainin wayau tsiya tundai in sun raina da kuran mutum sai suso su raina shi.
Don ma hjy tana taka masu burki aida abin nasu yafi nan wallahi dayan matar ta fada.
Inda wanke wanke suke na nufa na shiga hadawa da sauri kande tace yar nan me zakiyi nace wankewa zanyi mama.
Rufa min asiri kada hjy tazo tagane ki tace na baki aikin da yafi karfin ki ko dazun saida ta kara jaddamin zance a kanki.
Zan iya ai basu da yawa na fada ina kokarin hada kayan wa yanda sukaci abinci dasu da yamma.
A gurguje na wanke kayan tas dayan matar da ake kira larai tana saka min albarka na kare tare da fadin aikwai wani aikin da zanyi kuma mama na tambaya ?
Babu yar nan sai dai kizo muje dakin hjy na fara gwada maki aiyukan datace a nuna maki na bangaren ta.
Hannu ta dauraye tana gaba ina binta baya muka nufi inda sashen hjy yake don gyarawa a kofa muka tsaya.
Tana kwankwasawa kafin a bamu izinin shiga daga ciki hjy tana kwance kishingide saman wani kujera mai kaman gado a dakin.
Ga wani abu babba kamar waya a gaban ta tana latsawa ta dago tana fadin kande baki bar yar nan ta huta ba yau yau da kawota.
Ai sai taga aibun kan hakan to hjy nayi laifi wai gani nayi dai ta fara sani tun yanzu ai ba aikin zatayi ba a yanzu gani kawai zatayi ta koya.
To shi ke nan hjy ta fada tana mayar da hankalin ta wurin abinda takeyi a lokacin.

KAUYEN ANCAU

Iska na wahal da mai kayan kara a gidan nan yarinyace dai ta tafi ba dawowa zatayi ba balle mutum ya shige daki yaki fitowa.
Lantanace ke magana ita kadai a tsakar gida inna na daki tun bayan tafiyan mu har yara suka dawo boko suka tafi islamiya taki fitowa waje.
Gashi sai tambayana suke inna ina yayar mu bamu ganta ba tun dazun tace dasu ta fita kawai daga haka kowa ya shiga harkan gaban shi.
Sun tafi islamiya sun dawo sun samu inna a yarda suka barta haka yasa saratu mai dan wayau a cikin su sake tambayan inna.
Inna wai lafiya kike yau kuwa ina yayan mu tajene tun dazun bata dawo ba kuma ban santa da zuwa unguwa haka ba ai.
Hawayene ya fara zubawa inna da sauri saratu ta juya wurin jakkan kayana tana dubawa tare da fadin inna sun dauke yayan mu sun turata aikatau ke nan ?
Wani irin kuka inna ta kara fashewa dashi lokaci guda saratu ma kukan ne yazo mata sai hakan ya jawo hankalin sauran yan uwan mu dake wasa kofan inna.
Saratu ke fadin wayo yayan mu ki dawo kada kije aikatau don Allah an ce ana lalacewa wurin aikatau din nan.
Haba dakin inna ya koma dandalin kuka da tashin hankali don kuka sosai yaran keyiwa inna.
Da gudu lantana taje ta kira Asabe tana mayar mata da karya wai ga inna can ta tasa yara a gaba sai kuka sukeyi don tafiyana.
Asabe ta fito babu ko dan kwali a kanta sai a hannu ta rike tana fadin bamu cikin abin kuka da yamman nan .
Kuyi muna shiru masu mugun manufa da sheri don tafiyar yar uwarku zaki zauna ki dasa muna kuka ke da yara haka kamar anyi mutuwa a gidan.
Asabe wallahi sai kin dawo muna da yayan mu ko zaman gidan nan ya gagareki keda munafukanki da cewa lantana.
Mara kunyar banza da wofi koke can kika nufa idan naji dadin yar uwanki ana turo min kudi irin haka marasa hankali kawai.
Da kuna zaune a gida kara zube ina zamu samu irin kudin da muka samu yau a gidan ba gashi har kun dawo kun samu anyi abinci ba yau.
Kowan nan sai ya dandani wanan hanyar aini yanzu gaba haihuwan ku ya kaini tunda na samu mafita daku.
Ana cikin hakane Abba ya shigo yana fadin yaya yayane tun a kofa nake jin muryan ki umma.
Asabe tace barni da mutanen kawai din nan wai tafiyar yarinyar nan yahanasu ta saka yaran nan a gaba suka mayar muna da gida gidan makoki.
Yahanasu kina da hankali kuwa ke yanzu idan kina da tunane ai wani nauyi aka rage maki Abba ya fada.
Fada mata dai ko zata gane hakan ina nan gashi dan kudin da hajiya ta fara bayarwa kowa ya fara amfana dashi gidan nan ba gashi kunci shinkafa da wake ba yau a gidan.
Umma kyale ta barin ganta ni yahanasu har mamaki take bani yanzu kan yarunyar nan babu nuna kawaici a kanta ko kadan.
Idan ma bata nuna ba ita ta sani nidai na nuna mata nike da iko da abina daga diyan ko har kai a gidan nan ko wa yan nan na samu mai daukan su bayar dasu zanyi zuwa birni.
Ba saki bada muba tunda ke kika haife mu cewan Saratu sai inna takai mata duga daidai Abba na shigowa dakin inna din.
Bar dukan ta rabuwa da dan uwa nada zafi tundai irin wanan na yarsu nima dai ba haka naso tafiyan nataba kai tsaye so nayi muje tare inga wurin.
Koma dai menene yanzu aikun nuna min kukeda yarku saidai ina son ku sani naji umma na fadin har wa yan nan za a tura min can birni aikatau.
To wallahi hakan ba zai yuyuba wanan ya isa haka idan da hali dawo da yata zanyi gabana yafi mun kwanciyar hankali idan kasa mukeci mu kwaba muci tare.
Toto to ya isa haka yana sa hannu ga aljihun shi ya ciro yan dubu guda biyu yana fadin ga wanan kya samu ko sabulun wanki ku saya.
Da da nake saya kai kake ban kudi katafi da kudin Allah ya isan ka can kuci ku kadai ku gani.
Kwadan ku ya fada kun raba ni da yata kun rabata da gatan ta da Allah yai mata don kawai tana diya mace.
Shiru Abba yayi don inna bata taba tsayawa ta fada mai magana ba haka kai tsaye irun ranan.
Kwafa yayi ya fita bayan ya mikawa saratu kudin yana fafin karbi ki aje mata idan ta sauko zata karba a wurinki.
Yana fadin haka ya fita daga dakin don kada yayi laifi a gurin lantana dake tsaye ta rike kugunta tun shigan Abba dakin inna.
Yana fitowa fuskanta ya fara kallo ta watsa mai wani harara ta juya zuwa dakin ta shima abba yasan sauran zancen ranan a guri lantana don haka wani dabara ya fado mai.
Yana shiga dakin ta juyo zata fara fada yace me zakiwa fitina kin san dai ba zama nayi a can ba rufe mata baki nayi da dubu biyu ke kuma ga naki dubu biyar ki rike.
Sai lokacin lantana ta dan saki murmushi tana fadin wallahi yau Allah yaso ka da kakoma can ka kwana surin tsohuwar matar ka
Nina fara hakan gani da dalleliya kamar ki inje dakin da warin fitsari da kwamatse ya ciki.

NEW G R A KADUNA

A hankali mama kande take koyar dani komai duk wani abinda ya shafi mami da zirga zirgan ta na cikin gida nice mai mata hidinar shi..
Da na zauna zaki ta kirani da zeey zan amsa da na,am mami in zo da sauri don biya mata bukatun ta wanda ba wani aiki bane.
Sai dauko min kaza jiki mayar da wanan a cikin wardrobe ko dauko min ruwa shine aikin nawa kawai dawai mami bata iyawa sai an dauko mai mata wanan hidimar da ban daukeshi a aikin komai ni.
Sai gashi cikin sati daya kacal na gane komai na mami nasan lokacin tashin ta daga barci .
Zan shiga dakin in gyara gado in wanko mata ban daki zan koma in hada mata ruwan wanka tana zaune tana lazumi don mami akwaita da yawan ibada sosai.
Zan dawo dakina in jirata tana tashi zata kirani in dawo in share dakin duk da ba wani datti ke ga dakin ba amma kullun sai nayi gyaran shi sau biyu a wuni.
Kafin ta fito wanka nagama hada komai sai in koma dakina can kuma idan ta fito zata kirani da zeey zan zo in je dining in hada mata tea wanda wani ruwa ne baki kawai sai dan sugar kadan bata shan madara da suga ita.
Idan na gama zan koma dakina inyi wanka in shirya in dan huta kafin ai mi wani kiran kuma inzo.
Kai masu kudi suna shagalin su banda abin aikin kudi wai wanan dinne aikin da aka raboni da gida do shi aikin da mutum zaiwa kansa ba sai ya nemi mataimaki ba.
Amma hjy gashi tana ganin ina aiki sosai sai fadi take yarinyar akwai kwazo da sanin ya kamata.
Do ita gani take yanzu komai na zuwa mata da sauki a nata bangare har zata samu tayi barci ta huta na dan lokaci.
A bangaren yaran gidan hjy kuwa ba ruwab su da shiga tsabgata nima hakan ne dasu.
Saidai su wani lokacin zasu sakani wani aiki a gidan wanda ya shafi rayuwan su suma ga tsana karara da ko wace ke nuna min.
Dan gara salma da har yanzu ba zance tsanane ko tausayina ba a ranta don na kasa fahintar inda ta dosa dani a ranta.
Wani lokaci inji sanyi a wurin ta wani lokaci kuma idan ta daka min tsawa sai na gigice don tsoro.
Ita irin mutanen nan ne shiru shiru da mugun ta don surutu bai dameta ba ko kadan za a zauna wuri ba zakaji bakin ta ba sai wani lokaci ta furta idan ta furta daya kuma shike nan.
Duk wanan abinda suke min bai damuna naka ma raya a raina idan naga sun dau wanka zasu tafi school nakan ce inama a ce nice a matsayin su haka.
Nasan da ko Asabe ba zatayi gigin takani ba balle lantana dana tsana fiye da kowa a gidan mu yanzu.
Ni dai na rasa dalilin da yasa yaran gidan hjy suka tsaneni a baki dayan su in ka debe hjy da mama kande da suke nuna min kulawa a gareni.
Tun dai ace yan matan don a fili suke nuna min kin jini da kyama duk da yanzu nasan nima ina tsabta fiye dacan da nake Ancau din mu.
Na kanyi tunane indon dun kauyancine da kazanta yazu duk na daina wanan a ganina do na canza nayi fes na kara zama shar kamar bani ba.
Ga mai da turare na yan gagu da hjy taban tace in dinga shafawa idan nayi wanka gun kashe gari dana zo.
Komai ina yi shi a taka tsamtsam a gidan ban yarda in ketare iya inda aka ajeni ga aikina dan dama wani lokaci idan zama ya isheni nakan shiga kitchen in taya su mama kande aiki do su basu da hutu kamarni.
Ko yaushe a cikk girki suke dan hutun su kadan ne tundai idan yaran gidan suna gida wancan yace kaza yake so wana yace baya cin kaza yau.


ZAINAB IDRIS MAKAWA





🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅

9️⃣

YAR UWA NOVEL DINA NA KUDINE KIJI TSORON ALLAH KI BAN HAKKINA KAFIN KI KARANTA DON GUJEWA SHIGA HAKKIN WANI, , , ,

2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KI TURO KATIN WAYA DARI UKU NE KACAL BA YAWA, , , ,

Ina daki naji muryan hjy tana kwalla min kira daga dakin ta nima na amsa da karfi da Na,am mami.
Fitowana daga wanka ke nan lokacin don haka na dauki riga a gurguje na saka a jikina don zuwa amsa kira hjy din.
Na sameta zaune tana waya saman gadon da yasha gyara a wurina tunda safe nake gyaran dakin mami din don duk wani aiki da zata kai ga bude baki tace inyi kafin ma tace nayi din tunda yanzu nasan aikina a gidan.
Bana jin kiuya ko kasala tunda na saba aikin daya fi wanan a kauye don hakane hjy bata samun matsala dani koda an samu din ma saidai gyaran dan abinda ba,a rasa ba kawai.
Ganin tana waya yasa naja na tsaya daga nesa kadan ina jiran ta gama waya ta bani umurnin abinda zan mata lokacin.
Wasu kaya data fitar ta nuna min da hannu alaman in dauko mata su ban tsaya ba na juya zuwa wurin kayan na fara dauko su ina ajewa a gaban ta.
Sai waya take ta faman yi mai kama da fada da alama dai da danta ne ko wani kanin ta take waya yadda nake jin tana fitar da kalamai gareshi.
Bayan na gama kwaso kayan ne naje gefe na tsaya don bata ban umurnin in tafi ba.
Hango tawul din data fito wanka ta goge jiki nayi gefen gadon ta na juya zuwa wurin na dauke tare da nufar kofan ban daki na shiga na baza shi a dan karfen da ake bazawa.
Unders din da suka taru a duk da na ranan dana daren jiya datai amfani dasu ne kamar rigan nono da buje da handkacin amfanin ta.
Sai na tsaya na wanke tun ina jin muryan mami tana waya har nazo na daina ji da alaman ta dai gama wayan ne a lokacin.
Nafito ta bini da kallo tana fadin wai dama kina cikin dakin nan zeey ?


4 Comments On ABU CIKIN DUHU
avatar
khadija-8-3

1 year ago

Reply

I want to download this book

avatar
daiy

1 year ago

Reply

Replying to khadija-8-3

You have to subcribe to our package in order to download our novels

avatar
zainab-3-3-5

1 year ago

Reply

I also want to download this book

avatar
daiy

1 year ago

Reply

Replying to zainab-3-3-5

You have to subcribe to our package in order to download our novels

Please Login or Register in order to submit comment