Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take gwada maku yayi yawa gaskiya.
Karatun ma da zakiyi ki samu madogara a rayuwan ki saida ta hana kiyin shi gaskiya na tsani wanan matar damai irin halin ta.
Muryan Nuriya matar yaya mubarak ke fadin mami ashe kuma an daga tafiyan ?
Mami ta juyo tana ce mata sun daga kedai kin san abin gwaunatin kasan nan baida tabbas ai yanzu kuma sai dai sun kiramu kuma.
Ai wa yan nan sun kwafsa muna wallahi don kila yaya Jafar ya fasa shigowa kasan nan ke nan sai wani jikon .
Yasan an daga ne mami ta tambaya tana kallon jamal dayayi magana sai jamal din ya juya yana kallon jalal yana dariya.
Kudai kuka sani da tsegumi kamar mata haba mami don mun fada mai an daga ranan shine tsegumi shifa ya tambaye mu muka fada mai gaskiya.
Waya aike ku fada mai da ku barshi sai idan yazo yaji ai ba shike nan ba zai kirani ai zamu gamu dashi ta fada a hasale tana mayar da hankali kan sytem din ta data bude a gaban ta.
Nice ta farkon mikewa a falin bayan Nuriya matar yaya mubarak data ja yaran ta suka koma part din su ba don yaran sun so haka ba don ko shigowan nan nasu don assigment din yaran tashigo har dasu.
Dakina na shiga nabi gadona mai laushi na kwanta ga sanyin A C dana sake ya game dakin sai barci.
Bada masaniya ba mami ta sama min makaranta don inci gaba da karatuna a wani college dake gaba da unguwaelr kadan.
Ranan da dare take fadamin zancen ci gaba da karatun nawa lokacin nema kowa a gidan yasan da zancen cigaban karatuna yanzu.
Wanan yasa yan matan nata kara jin haushina sosai banda daman bin motar su kamar yadda mami tace mu rika tafiya tare da safe idan zan tafi.
Ganin haka ban fadawa mami ba nake takawa da kafa ina zuwa makaranta don nisan shi ai bai kai na kauyen mu dana baro.
Zan tashi da asuba inyiwa mami duk wani abinda nasan nice mai mata shi kafin gari ya haska na karasa zan karya in taka da kafa inje school.
Sam mami bata san da zancen tafiyana da kafa zuwa school ba sai wata rana zata unguwa da safe hakan yasa ta fito da wuri daga dakin ta.
Yan matan ta samu zaune suna karyawa take tambayan ina nake nan suka fara kallon kallo a tsakanin sai salmace take fadin mami wayen garin nan banganta ba ai.
Tafa tafi school Nazifa ta bada amsa sai mami tace usman ne ya kaita ya dawo ya dauke ku sai sukayi shiru don sun san da kafa nake tafiya school duk dadewan nan.
Bana son irin haka sai kuyi kwanciyar ku a daki kuna sharan barci sai lokacin da yai maku dadi zaku fito .
Alhalin kunsan da cewa ita nasu school din ana duka idan an makara ko shi malam usman din yayi ta zaman jiran fitowan ku.
Fada sosai mami tayi masu kafin ta fita can ta hadu dani na kusan shiga school din mu ta tsaya tana tambayana yaya akayi na tako da kafa ?
Nace mami bana sin in makara ana duka idan mun makarane maza shige mota in karasa dake ke baki tsoron wanan titin namu gashi shiru babu kowa a wanan lokacin.
Har ta saukeni fada take min ta bude jakka ta zaro five hundred tana miko min tare da fadin karbi wanan kiyi break dashi don nasan baki tsaya karyawa ba kika fito.
Lah mami wallahi na karya kafjn in fito ki bar kudin don mami bata ban kudi sai dai tace na karya kona dauki abinci inje dashi school din.
Ina kallo ta wuce karfe biyu da yan mintoci na shigo gida har lokacin mami bata dawo daga unguwar da ta tafi ba.
Haka yasa na samu daman samun dan barci rana bayan nayi sallah azahar ban sake fitowa ba duk da yunwan da nake ji don kudin da mami ta ban na kasa kashe su don ban saba da kashin kudi ba.
Ban farka ba sai bayan la,asar wanka nayi lokacin ne naga fashin sallah yazo min don haka nayi wanka kawai na fito na dauki always na kimtsa jikina dashi.
Abinci ya fito dani naga ashe yamma yayi sosai a lokacin haka yasa na gane na dade ina barcin rana yau.
Don na samu har yan university sun dawo suna cin abinci mam kande ne ta dauko kuloli take fadin yau kan yar gidan hjy kin sha barcin rana.
Ba dole tayi barci ba tunda taga arzikin banza wanan irun kune idan kun samu wuri kuke mayar da yan gida daga kofa.
A a saidai tasan wanda zata mayar Nazifa tace tana amsawa Rufaida sai naji salma tace wai ku meye matsalan ku da yarinyar nan don Allah ?
Rufaida tace I just hate her wallahi balle yanzu da take clean sai nake ganin gaskiyan maganan dasu Rubby suka fada ranan a kanta.
Ashe bani kadai ke ganin canzawan yarinyar nan ba tundai wanan kayan da mami ta saka aka dinka mata suna fitar mata da suranta na asali waje.
Zakace badaga kauye take ba har wani tafiyan sallo take tana yanga idan tana magana yanzu.
Kai ku din nan kuna da wani magana wallahi koma dai yaya ta koma kunsan ba zata taba kaiku asali ba dai ko ?
Sallama na fadan haka Nazifa tace yanzu waye ya damu da wani asalin mutum can zamanin nan boko ai mutane basu duban haka idan sunga abinda yai masu .
Dariya sosai salma ta kwashe dashi don dama irin du baka ganin dariyan su sai ta baci ni dai ina diban abincin ina jin cinmutuncin da suke min kala ban tankasu ba.
Saidai na kudurta duk ranan da wata daga cikin su ta kara zagan min uba bazan kyaleta ba sai inda karfina ya kare koda hakan na nufin inbar gidan ne na masan hjy ba zata yarda ba da hakan.
Don takan fada min Zainab ina son in ga na taimakeki kin zama wani a rayuwa ki samu ki taimaki yan uwanki tunda dukan ku matane har ku bakwai .
Shiyasa nake son ki dage ga karatun don wata rana ki taimakawa innan ki da yan uwan ki Asabe tasan diya mata ma diyane abin alfahari kuma.
Ire iren wanan tunanen nakanyi inshanye wani abinda ake min a gidan don kawai manufar mami a kaina don kuma burina ya cika.
Karatuna bai hanani yin abinda nazo yi gidan mami ba har na kai wata shida da zuwa gidan .
Iyakata da anty safiya idan tazo in fito in gaida ita tare da tambayan yayan ta da mijin ta ta bani amsa da suna lafiya suna gaida ke.
Sai kuma ta tambaya injin dai baki wani abin asha zainab kada ki manta da kinzo cin arziki ne a nan don haka kiyi biyayya sosai.
Irin maganan da anty safiya takan min ke nan idan tazo gidan ina nan kafin ta tafi
Gashi banji wani zancen kudin aikatauna ba ga bakin kowa nima kuma ba damuwa dana san komai a kan albashi na nayi ba.
Mun samu hutu makaranta naji mami na fadin ya kamata in je in duba gida tunda su basu neme ni ba har yau.
Don tasan yanzu inna na tacan cikin damuwan halin da nake ciki babu dai yadda zatayi ne ta sawa sarautan Allah ido.
Ban san mami har ta saka ranan zuwana gida ba sai dai tace inje aimin kitso a makwabtan mu don akwai wata yar makarantar mu a gidan kusan tare muke dawowa da ita kullun.
Itama takan zo gidan mu in mata nan yan gidan suka san na iya kitso sosai don har mami nakan wa kitso yanzu tunda ta gane na iya kitso sosai da yan matan ta.
Sai dai bankan so yi masu kitso don muna kitson suna zagina har mu gama.
Washe gari na shiga wurin mami in gaida ita da kwana sai na sameta zaune ta fitar da kayan data dawo daren jiya dasu don nice na kwaso zuwa dakin ta.
Sallama nayi ta dago kai tana fadin yawa samu wuri ki zauna dama yanzu nake da niyar kiran ki sai gaki.
Zama nayi kamar yadda ta umurce ni kafin ta fara fadin kinga wa yan nan turamen ta nuna min su da hannu nace eh mami.
Tace yan uwanki zaki kaiwa su guda shiddane iri daya ne saidai nasa a bambanta kallar su wanan kuma na innan ki ne ta nuna min wasu uku a guri daya.
Sai wanan kiba Sabe daya lantana daya wanan shaddan kuma ki ba mahaifin ki sai sabulai da omo kiba yan uwa da abokan arzikin ku .
Kwana hudy zakiyi ki dawo driver daya kaiki zai dawo ya daukeki ranan ki gaiyar min da innan ki sai wanan ki ba mahaifiyar ki tana miko min wani abu a cikin leda wanan kuma mahaifin ki zaki ba albashin kine na watannin da kikayi a wurin mu na tara maki shine na raba biyu innar ki rabi mahaifin ki rabi.
Kada ki manta ina gaida innar ku kwarai kice na gode sosai sai watarana idan mun hadu.
Hawaye na fara yin a wurin ina tsugune sai mami tace ko kin fasa zuwa gidan ne in aika masu da sakon da sauri nace a, a mami na dai rasa godiyan da zan makine yanzu.
To maza ki tashi ki shiya ga sabbin kayan kinan saman gado sai ki zabi wanda zaki dasu tsufin kuma duk ki hadasu ki kawai kannen ki su karasa su can .
Ko mahaifiyar ki tana sa kwance ki zaba mata wa yan nan dana ware da za a kyautar .
Da gudu nace tana sawa mana mami to jeki ki zabar mata kala biyar daga ciki da sauran tarkacen daya dace ki kai mata .
Na mike don na rasa bakin da zanwa mami godiya don ta hanani yin hakan gareta.
Kayane mai yawa har na rasa wanda zan cirewa inna sai da mami tace ki cire mata zannu da dogon riga zatafi son su ai.
Haka muka dauki hanyar ANCAU da tsaraba taf a bayan mota da zankaiwa iyayyena koma in ce mahaifiyata don itace mai tsaraba da yawa ciki.
Don hjy tafi son inna na fahinta sama da mahaifin mu Abba kodon tana mace yar uwantane ban sani ba.
Malam Usman driver mami bai tsaya ko ina ba dani sai kofar gidan mu tun daga nesa na hango wata na suyar wani abu an baibaiye ta.
Saida muka matso kuss ne na gane saratu ce kanwata ashe ganin mota ya nufo kofan gidan ya kuma ja ya tsaya.
Duk wanda ke wurin ya kurawa motar ido don son ganin kowaye a motar ban fito ba saida na gama dauko kayan dana rike a hannu na fito daga motar.
Saratu zoki kama min kayan nan kin tsaya kina kallona haka muryana kawai ta sheda yasa ta gane ni a lokacin.
Ido ta waro waje tana kallona tare da fadin yayan mu maimakon ta yo wurina sai kawai ta kwasa da gudu tayi cikin gida tana fadin.
Allah mun godema Allah mungodema yau ga yayar mu ta dawo garemu innan mu fito yau Allah ya dawo muna da yar uwarmu gida.
Ashe ba sayar da ita akayi ba a birni ji abinda saratu ke fada yasa sayran kanne fitowa da gudu kafin su ja su tsaya suna ina take ta kwasa tayi hanyan fita suka bita da gudu.
Mun hade dasu a kofan shiga gida sukayo kaina da murnan su da ihu suna jin dadin gani sai ihu sukeyi yayan mu ta dawo yayan mu ta dawo garemu yau.
Jin ihun da yaran gidan suka dauka na murnan zuwana yasa Asabe fitowa daga shiyan ta dan kwali a hannu tana fadin.
Shin Abu Abu kuke fadan tazo ina Abun take ne in ganta tana kokarin wuceni da yan uwana.
Gani nan Asabe na fada ina kokari zuwa wurin ta sai taja baya tana dafe kirji tare da fadin Abuce haka ?
Zonan na ganki na karasa wurin ta sai ta rungumeni tana kuka tana fadin yar nan ina kika shige haka babu duriyan ki har an fara zargina a gari na sayar dake ga yan birni.
Ina gidan hajiyar da kuka kaini tun barina garin nan na da kwana bakwai gun anty kafin ta kaini gidan.
A a ai dada kin dawo garemu ke nab dai yanzu ba komawa wanan birnin kuma dai ta fada tana share hawaye.
Ni dai ban ce mata komai ba sai waige nake ko zanga innar mu ta fito banganta ba yasani sakin Asabe na nufi dakin mu da sauri ina sallama.
Ina shiga da hango ina zaune saman dan gadon dake dakin tayi tagumi ns karasa gareta ta da sauri ina fadin inna gani nazo gare ku yau.
Murmushi inna tayi kawai sai dayan kanwar mu data sawa kira daga dakin a daidai lokacin da yara suka fara shigo da kayana dakin.
Irin surutun da yaran dake shigo da kayana gidane ya sa hankalin lantana dake daki bakin cikin dawowa ya hanata shakat tunda saratu tazo tana ihun na dawo wani tukukin bakin ciki ya sokar mata zuciya.
Don Lantana sam bata so in dawo gidan ba a lokacin don so tayi ace ba bata da gaskiya kamar yadda ta kulla sherin haka har zance yabi gari gaba daya kowa ya dauka hakan ne.
Inna eta bada kudi wai a sayo min ruwan leda nace basai an sayo min ba inna a dai sayawa driver hjy daya kawoni.
Wai wanan mutumin driver ne yanzu saratu ta fada nace drivern gidan hjy ce shi ke kai yaran ta makaranta ya dauko su idan da aike kuma sai a aike shi.
Bawada ya ankara da zuwan lantana daki namu tazo ta tsaya a kofan dakin ta tokare hannayen ta da katon kofan dukka gefe biyu.
Saida ta gama saurarebn mu ta kalleni tsaba ta fara fadin eyya Abuce ta koma haka ?
Gaba daya dakin muka juyo muna kallon ta lokaci guda taci gaba da fadin halan a cikin injin suka sakaki aka wankeki haka.
An maidoki kamar wata karuwan birni koda yake wasan abinda kike a burnin wanan bude idon haka lokaci daya.
Amarya ke nan ai inkiga mutum yayi abu yana da gadon shi ne ban gada ba babu dana da zai taba zina da yardan Allah inna ta bata amsa.
Kinsan aikin mutum sai ya dauka shi kowa keyi ko ina ya samu kansa ni Allah ya tsare mi yata a birni don bata gaji watsar da kai ba.
Kaina yana duke kasa ina tunanen wai yaushe inna ta fara magana haka sai naji lantana na fadin wa kike nufin ya gada to ?
Wanda yasan ana haka har furtawa yata dashi nakeyi abu yaso zama rigima don har saratu taso shiga maganar inna ta kwabe ta.
Andaiyi abin kunya ta fada tana batin kofan dakin don bata zaci innan mu zata bata amsar maganan taba.
A kofa ta hadu da asabe da takawo min zogale data gyara tana shirin ci cewa lantana tayi muna ganin kilibibi a gidan nan.
Ya tadawo yawo tazubar har ake wani riritata don kwadayin duniya muna jin ta a daki nace har yanzu wanan matar tana wanan haukan duk data haihu girma yazo mata yanzu.
Ina girma a nan banda iya shegen data karo cin mutunci dai ne mutum ya guji karshen shi.
Asabe ta shigo da sallaman ta tana aje min kwanon ganye a gaba tana fadin kici yar nan dan ganye na gyara sai gaki.
Saratu takai hannu zata diba takaiwa saratu dundu a baya tana fadin mara kunya ba a ke nakawo ba bakuwa na kawowa.
Sai dana huta nayi sallah kafin malam usman ya aiko wai zai tafi na samu inna ta dan dama fura ta aika mai kafin yayi sallah yasha ga awara da saratu ta cika mai leda dashi har kwan zabbi inna ta aika a nema cikin gari ba a samu dayawa ba hakan ma naji dadi yadda akai mai.
Bayan mun dawo daga rakashi ne na bude kayan don saratu ta ta demeni da tambaya mena kawo masu ?
Tundana fara bude kayan jikin kowa yayi sanyi kafin ma in farawa inna bayani kamar yadda mami tayi min.
Nan dai na labartawa inna rayuwana a gidan hjy saidai na boye mata irin cin fuskan da yan matan hjy kemun a gidan.
Don tsakanin mahaifa da diyan su sai Allah sararu ce ta dauki na Asabe da lantana takai masu nasan don fitina tace itace zata kai.
Lantana ta fara kai ta karbi kayan a tsune tana fadin duk da ance kayan zina kamar kayi zinane kaima.
Amma wanan zani ya shereni ba zan barshi ya tafi ga banza ba tunda a haka aka sameshi.
Saratu tace dadai yafi tunda ba yau aka fara cin kayan zina ba don har na tsohuwa an saba ci cewa da uwar lantana din.


ZAINAB IDRIS MAKAWA






🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅

1️⃣1️⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA


YA ALLAH KA KAWO MUNA TSARO A KASAR MUNA NIGERIA, KASAWA WANDA IF,TILLA,I YA FARU DASU HAKKURI DA SANIN KADDARA A RAYUWAN SU, , , , , , ,

DARI UKU NE NOVEL DINA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALLAMA YAR UWA DON TURA KUDI GA NOMBA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN MTN KO EIRTEL NA DARI UKKU.



Abba bai shigo gida ba sai gap da magariba ya dawo lokacin ina alwala a tsakar gidan mu dani ya fara arba.
Ja yayi ya tsaya tare da fadin wa nake gani nan kamar Abu ya fada cikkn mamaki don bai san da zuwana ba ashe sai wanan shigowan da yayi ya ganni.
Amsa na bashi ina mikewa a daidai lokacin ina kai dan ruwa a baki kamar yadda yin hakan ya zama min al,ada tun ina gida ba tafi kaduna har yanzu kuma ban daina yin hakan ba idan na idar da alwala don sallah.
Abba nice na fada cikin dan murmushi Abu ina kika shiga haka babu labarin ki ga kowa ita din da tazo ta dauke ki bamu kara jin wani zance a gareta ba har wanan lokaci.
Safiya bata kyauta muna ba ta barmu cikin zargi da fargaba don ba haka mukai alkwari da ita ba.
Ayi hakkuri Abba kasa anty ma,aikaciya ba ko yaushe take da lokacin tafiya ba irin hakan.
Yar mairo koma menene ai ya dace ta dan waiwayo musan halin da ake ciki dake a can .
Yanzu kai ganin ta yasa ka tsaya nan kana zuba har ka mata irin bakin cikin data jefa ku a tafiyan ta .
Lantana ce ke fadawa Abba hakan tare da mika hannu tana fadin ban ledan kafin ka shiga can a wawashe.
Tana mika hannu ta fisgi ledan daga hannun Abba ta juya tana fada abin kunya yarinya taje gantali tsawon wani lokaci saida tagaji don kanta ta dawo har kuna wani jin dadin hakan.
Abba yai tsaye kamar ba Abban dana sani ba yana bin inda tabi da kallo kafin ya juyo har na bar wurun ina kokarin shiga dakin innan mu ko.
Da mamaki a raina yadda naga komai na gidan namu ya kara hargitsewa ga baki daya na tayar da sallah.
Bayan na idar da sallah muka zauna da inna sai lokacin nayi mata bayanin komai a tsanake har sakon mami na dauko na bata na nuna mata na Abban mu da tace a bashi.
Inna tace aidai bata don wanan yarinyar tana kyala ido a kansu sai taga bayan su a lokaci guda.
Nace koma meye ai dai na isar da sako saidai inna nifa wasu abubuwa da nake gani a gidan suna daure min kai tun zuwana.
Me kika gani daya daure maki kai ai dama shi ramin mugunta kurarene idan wanda akewa yayi hakuri.
Bai wuce dai abinda kikaji ba tsakanin umma da lantana ko wanda kika gani yanzu tsakanin ta da mahaifin ki.
Duk waya ja hakan sai umma gashi kuma tun ba,aje ko ina ba abin ya koma tsakanin su yanzu.
Tana ji tana gani ganin danta yana batun gagaran ta a gidan nan tayi fada har ta gaji ta saka ido idan da can tayi mai aure ne don ni a gidan nan, yanzu bani kaida ke ganin bakin cikin ba harda ita.
Shiru jayi ina tunane a raina tare da fadin mai yai zafi tsakanin Asabe da lantana kuma yanzu.
Abba bai shigo dakin inna ba sai bayan sallah isha,i zama yayi muka gaisa na mike na dauko mai sakon shi kamar yadda mami tace in bashi.
Duban kaya yayi yana juyawa tare da fadin ikon Allah duk wanan matar ta bayar a kawo min nace Abba ai mami mutumiyar arzikice.
Zamanta mai kudi baisa ta raina tallaka ba nan dai na gutsura mai dan labarin mami din da aiyukan da nakeyi a gidan.
Abba ya kalli takardan dake hannun shi yana juyawa a hankali kafin ya fara kokarin budewa kudi suka soma zubowa daga cikin takardan yan dubu daya sabbi fil dasu.
Da mamaki yake fadin yahanasu kudine fa matar nan tayo muna sako a cikin takardan nan.
Na amsa da fadin cewa tayi kudin aikina ne in kawo maka da zanzo duban kudin Abba yayi kafin ya juyo ya dubi inna da ko kallon inda yake batayi a lokacin.
Wanan matar wani irin kudine gareta haka yar mairo ko harda wani sana,a kike mata bayan wanan ?
Gaskiya matar kwarai Allah ya hadaki da ita a birni don ba kowa bane zai iya maka hakan .
Mamaki kalaman Abba ya bani don na dauka zai tambaye fiye da hakan sai ga Abba ya buge da fadin in kara kwazo don gaba ta aiko da wanda yafi wanan din yana mikewa.
Malam iya abinda zaka fada mata ke nan dan ka rike kudin da baka tabbatar daga ina suka fito ba kamar yadda matarka ke fadi kullun.
Bana zargin tarbiyan diya na ko kadan don nasan tarbiyan da muka basu tun farko.
Allah yasa a kanshi take don nina tsuke da sakon wanan matar gaba daya hankalina bai kwanta da hakan ba ko kadan.


4 Comments On ABU CIKIN DUHU
avatar
khadija-8-3

1 year ago

Reply

I want to download this book

avatar
daiy

1 year ago

Reply

Replying to khadija-8-3

You have to subcribe to our package in order to download our novels

avatar
zainab-3-3-5

1 year ago

Reply

I also want to download this book

avatar
daiy

1 year ago

Reply

Replying to zainab-3-3-5

You have to subcribe to our package in order to download our novels

Please Login or Register in order to submit comment