Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

malam ga Rufaida nan yarka ce kuma Amanar ka karike ta da kyau ka kula da tarbiyar ta nasan bakasan miyake faruwa ba Amman da sannu zaka sani take hankalin malam Adamu yatashi yamike tsaye da Rufaida a hannun Sa kawai Auta ta shige daki da sauri koda malam Adamu ya shiga dakin babu Asma,u Auta babu dalilin ta haka Adamu ya ke ta Neman Auta Amman bai ganta ba har karkashin gado .





Haka Adamu yazo Mani da kuka yana sanar Mani hankali na yatashi duda na dade INA wannan mafalkin dole na dinga ba Adamu hakuri da lallashi nace kawai yabada ke wa kakar ki ta reneki haka kika dawo hannun Mu muka doraki kamar yanda mukayi wa mahaifiyar ki .




Uwani kuwa ta dawo daga gurin bokan ta da mugun nufi duk da ni bansan miye ba Amman Uwani bata ga Auta ba tayi bakin ciki bata neme ki sai bayan kinyi shekara Tara sannan tasa malam Adamu gaba yadawo dake hannun Sa duk da cewa yayi yanason yadin ga tunawa da mahaifiyar ki .





Bayan kin dawo gurin su shine ta maida ke baiwar ta gashi naji makontan Ku na cewa kullum sai ta jika wurin kwanciyar ki komai sanyi komai kuma komai zafi .


Kuma kullum cikin duka da zagi da hantara Amman kici gaba da huri wata rana sai labari .



Andawo labari


Rufaida ta goge hawayen ta tace yauwa malam to ya maganar Kawu kabiru fa malam ya nisa yace ai yayi Aure a inda yake aiki kuma yanada yara kuma naji ance yakara Aure Dan ni Rabo na da shi tun kafin ayi Auren mahaifiyar ki lokacin yanada yara biyu namiji da mace .




Malam yace Muje na rakaki gida kinga dare yayi haka kuwa akayi Rufaida tazo gida bata samu inna Uwani ba duk da tasaba hakan dama ita dai burin ta takawo mata kud'i .




To Rufaida asuba ta gari Dan baki San wane hali Uwani take ciki ba .


Nikam nace Uwani Allah yasa gobe a kara maki.





Masha Allah



*Comments and share*



Daga
alkalamin โœ๐Ÿป

hassy soja

*yar mutan gusau*
4/19/20, 7:43 PM - +234 706 361 7906: ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ

๐Ÿ™†๐Ÿผโ€โ™€BANI CE BA ๐Ÿ™†๐Ÿผโ€โ™€

๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ

(Aljana ce)

BY
Hassy soja





Ina godiya masoyana Allah Ya bar mu tare ameen ina jidadi Addu,o in ku nagode sosai Allah yabar zumuci






Bisimilahi Rahamani Rahim
Da sunan Allah mai Rahama mai ji'kai




Sadaukarwa ga mahaifina Allah Ya jikan sa da Rahama ameen.






Page16----20





********************
Da asuba kuwa Rufaida ta tashi tayi sallah tana addu'a tana cewa Ya Allah ina rokon ka ka bayana mani mahahifiyata idan tana Raye idan kuma ta mutu Allah kayi mata Rahama ameen sai ta fashe da kuka sosai a hakan bacci mai nauyi ya dauketa







Bata falka ba sai do Gari yayi haske misalin10:45 Rufaida ta Tashi da addu'a tace kai yaushi gari yawaye ne bata gama mamaki ba ta tuno inna uwani to ina ta shiga kuma gashi bata tadani ba abunda ban taba gani ba koda kuwa ina ciwo kamar zan mutu tofa aikin nan tunda asuba zanfara nice share share nice girkin karin kumallo gashi koda nayi bazata ganiba sai duka da zagi daga nan sai zuwa tallar goro tunda uwar Safiya dan ma Allah yasa a gidan kakana nake Zuwa do naga takaina gashi har yanzun bata gane ina nake zuwa ba him tanisa tace bari dai naduba gani ko lafiya


Haka Rufaida nufi dakin Inna Uwani gaban ta nadukan tara tara domin batasan miza ta riskaba tana shiga taga inna Uwani kwance kamar matata fuskar nan kunbure Rufaida tace inna Uwani mai yasa meki taji shiru ta koma cewa Inna lafiya kike kuwa nan ma taji shuru Aiko ta fita waje da gudu tana kiran makociyar su aiko sai ga Asabe da dasauri tashigo hartana tuntube saura kadan da tafadi tace Rufaida lafiya wannan kira haka Rufaida ta rude kawai sai nuna mata dakin inna take aikuwa batayi kasa a gwiwa ba tashiga dakin abun da tagani shiya daga mata hankali take tayi waje sai gata da kofin ruwa batayi wata wata kawai ta kwalaya wa Inna Uwani ai ko nan tasaki wata irin ajiyar zuciya take tafarka tasa ki ihu wayyo Allah na wayyo kakata kizo ki taima keni wayyo uwata wayyo ubana wayyo ni uwani wani irrin Bala'i ne wannan Dan Allah inna Aljana kiyi hakuri wlh bazan Sake be Dan Allah inna Aljana kinji




Ai Asabe da Rufaida kuwa suka baki da hanaci suna kallon ikon Allah sudai ba suga wata aljanaba anyama inna Uwani lafiya take kuwa gata kamar wadda tayi hatsarin mota Asabe ce tayi karfin halin danne dariyar ta tace Ke Uwani hatsari kikayi kasa bata amsa tayi tazo daga hannun hagunta yace baisan wannan ba aiko to kurma uban ihu har sai da Asabe tarufe mata baki tace yauwa Asabe taimaka Mani natashi inajin nata samu targade ne sai alokacin ne idon ta Ya sauka akan Rufaida wadda tazama mutum mutimi Tana tunanin shin ina tajiyo wannan miyagun raunuka Wanda take yimata mummunar fatan gani ajikin to acikin zuciyar Inna Uwani kuwa cewa take tofa ita Kuma wannan Aljanan mitakeyi annan



Haka Kuwa Asabe Taimaka ta gyara gashi itama kafar taji ciwo bata takuwa Asabe kuwa Allah Ya Kara take yiwa Uwani domin daurewa kawai take tana danne zuciyar ta dan Uwani bata ragawa kowa Asabe nagawa tayi mata Allah yabata lafiya tayi gaba abunta






Rufaida tace sannu
Inna Uwani ta juyo tace shigeya mayyar banza mai kika zo yimani adaki iye nace munafuka kinga ban mutuba ko to kurwata dacine da ita


Rufaida tace wlh inna Uwani bakomai najiki shiru shiyasa nace bari na zona gani ko lafiya aiko Inna Uwani tace rufe mani baki


Rufaida tace inna kiyi hakuri wlh bani bace takarasa do radar murya kamar zatayi kuka Inna Uwani tace iyye to munafuka kukan mai kikiyi na dakekine iye Rufaida ta girgiz kai tace Aa


Inna tace mayyar banza tashi kibani waje sai na nemeki Rufaida tace to inna Uwani ga kudin Anshe abunta tayi saida ta kirga taga suncika Rufaida tace Allah Ya baki lafiya itako inna Uwani tace mata nace maki bani da lafiya iyye lallaima sai na ci uban ki shigeya mayyar banza mai faska kamar Aljana

nace hhh inna Uwani taji jiki
















********************
Ridiwan ne zauna bisan kujera tare da su Hassan da Husaina da mami tace my son ya kukayi da Abban ku. Ridiwan yace uhm mami wlh Abba sai a hankali wai yanzu saboda Allah abuda yakeyi ya kyauta kenan mami tace meya faru yace humm waifa Aure zaiyi Mani do duk wadda yaga Dama kuma yace baiyarda nakula yargidan kowa ba haba Dan Allah yayi Mani adalci kenan sai kace wata macen


Nisawa mami tayi tace kuzamo masu biyayya kunji ko domin kuwa wata Rana sai labari suna cikin magana sai ga Ramla tafito Tana taunar cingam kamar wata tsohuwar karuwa babu sallama kawai tafado masu

wai momy tace kuzo sai ta juya ta fita su mami su katashi dama Susan wai kiran tashin hakali ne domin kuwa itace maigidan







Sun shiga falon suka iske Abban su da Aunty amarya da yaran ta Sun zauna Abba yace Ridwan ashe ban isada da kaiba ko toshi kenan dama nasan za'ayi hakan kuma nagode Amman wlh tallahi humm sai Aunty amarya tace kabar shi basai karan tseba nariga na nemo mashi mata kuma wlh sai Ka Aure ta hankali su ya tashi mami dai batace komai ba Ridwaan dama yasan mami bazata tankaba duk Susan hakan ce zata faru kuma abun nadamun ta batada yanda zatayine

Aunty amarya tace nagama magana to Shannan kuma wata shidda Nasa Za,ayi ambassador take kaji Angama magana
Kada naji kuma kada Nagani haka taron yatashi Anty amarya MA dariyar nasara shi kuma Ridwan najin kamar Ya lakada Nata duka dan dai babu damane








A gurguje bayan wata shidda abubuwa sunfaru yanzun Uwani to daina dukan Rufaida Amman stilling kam da tallah sai abunda yayi gaba




Rufaida ce kwance tana barchi sama Sama taji and magana kamar haka


Rufaidaaaaaa you Zaman wanna bautar yakare yanzun kam zakiyi rayuwa zaki San cewa kema kinda Rana babu Tsoron koma waye kitashi kitafi yanzu.......

Tofa waye wannan ku biyoni muje Dan sanin ina Rufaida zata


Daga

alkhalaminโœ๐Ÿป

Yar mutan gusau
4/19/20, 7:44 PM - +234 706 361 7906: ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ

๐Ÿ™†๐Ÿปโ€โ™€BANI CE BA๐Ÿ™†๐Ÿปโ€โ™€

๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ


(Aljana ce)

BY
Hassy soja


ยฎ๐ŸŒ
*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION..๐Ÿ“š๐Ÿ“š*
_{ฦ˜ungiya Domin, wayar da ฦ™an mata Farin jini writer's domin ci gaban Mata.}_

โ˜…{ F J W A}โ˜…๐Ÿ“

https://www.facebook.com/Farin-jini-writers-association-108359057471117/


Ina alfahari da Ku masoyana Allah ya Saka da alkhairi Allah Ya bar zumunce ameen.






Bisimilahi Rahamani Rahim DA sunan Allah mai Rahama mai ji'kai



Ina godiya da addu,oin Ku a gareni Allah yabar zumunci




Sadaukarwa ga mahaifina Allah Ya jikan Sa da Rahama ameen.








Page 21----25



----------------------------------------taci gaba jin ana cewa Rufaida wannan tafiyar itace mafarin ban kado duk wani Abun da yashige maki aduhu Rufaida tashi kitafi kitashiiiiiii kitafi kitafi nace ce kitafiiiiiiiii.


Firgigit Rufaida ta tashi tana salati take duk wani abu da yasha fi mafalkin ta yake zomata daya bayan daya kamar yanzun Ne ake bata umarnin tafiya to yanzun ta INA zata farane


Haka kawai taji itafa tafiyar nan tayi mata kuma ta kwanta ma arai Amman kuma INA zata dosane



Gashi kuma ita karamar yarinya ce iya karta shekara sha ukku da watanni yanzun Ne take Neman ta sha hudu Dan ma Allah yasa tanada giman jiki idan ka ganta zaka dauka takai shekara sha shidda Ne ko kuma sha bakwai tana cikin wannan tunanin Ne


Inna Uwani ta ahigo dakin kamar wata kububuwa sai huci take kamar wadda ta hadiye kunama tana cewa Dan ubanki uban mi kike yi kina jina inata kwala maki kira kin maidani kamar abokiyar wasan ki ko to Dan ubanki tashi kidauki tallar can tunda ba ubanki bane zai dauka ko kuma kina nufin nice zan dauka munafu ka




Shegiya mayya daina kallona konayi maganin ki yanzun nan


Rufaida tace yi hakuri inna ganin fitowa to kadama kifito mayyar banza

Haka inna Uwani ta juya jin takeyi kamar tamaketa kawai ta huta ita fa baki ace Rufaida ta mutu ba tadaina ganin ta adoron duniyar nan ba musamman da taji malam Adamu hanata talla wai aure zai mata ba karatu take ba gashi tasan duka dukiyar shi zaiyi mata amfani da ita

Ita kuma gashi bata jin cewa akwai ranar da Rufaida zata zama wani Abu balle har ta kaita ga aure tariga ta kudurci cewa sai taga bayan Rufaida tunda duk kanin boka yen nata tsoron taba Rufaida suke itafa abun na damunta Abu kamar uwarta da takasa ganin bayanta duk da yake babu Wanda yasan inda take kilama ta mutu tunda boka Dan tsito yace mata shi yabatar da ita kuma ya haukata ta



Itafa yanzun burinta shine kawai ta kawadda Rufaida gashi ko INA ta tafi sai ace ta kiyaye domin ita Rufaidar ko sunnan ta ta fada sai sunyi mummunar asara ga duk wani aikin da suke so gashi ba boka daya ba duk inda taje maganar dayace



Shiyasa take cemata mayya gashi har yanzun ta kasa fadawa kowa cewa ana tsorata ta kuma ana dukanta akan wata banza can



Haka dai inna Uwani taci gaba da saka da warwara ta samu bakin gado ta zauna taci gaba da zancen zuci itafa yanzun Dole Ne ta dauki matakin da ya dace akan Rufaida tun kafin malam Adamu ya dawo tana cikin wannan tunanin Ne


Taga kayan jeren ta na zubewa kamar amafalki kafin ta Ankara har anfara jefo kayan a saman kanta gashi tayi yun kurin tashi ta arta a guje Amman kamar andaure ta kuma ta kasa yin ihu balle tayi









Ita kuwa Rufaida tafito domin daukar tallar sai taga bataga kayan ba gashi ko alamar fura wuta bataga anyiba abun yayi matukar bata mamaki har takama hanyar dakin inna Uwani komai ta tuna kawai sai ta koma hanyar kofar gida bata tsaya ko ina ba sai gidan malam wato kakanta tana zuwa tashiga gurin kakarta inna bayan sun gaisa take cewa Rufaida ina tallar ne naga shiru tace wallahi inna yau banga anyi ba Amman tace nazo natafi koda nafita banga komai ba kuma ba,a fura wuta ba


Ni nasan ni keyin girki yau batace ayi komai ba Dan naga kamar yau halin ya motsa ne arasa gane kanta komai fada da zagi



Inna ta nisa tace yi hakuri Rufaida wata rana sai labari yanzun mikika zo nema ne


Yauwa inna Dan Allah ki bani photo mamata da yayan ta Inna tace miza kiyi da shine tace kinga Inna Uwani ta kone Mani nawa da duk wani Abun amfani haka innar ta tausaya mata ta shiga daki ta bin ciko mata ta kawo mata ta ce gashi harda Wanda muke tare haka kawai na ganshi naji sha,awar dauko maki





Ai kuwa Rufaida tayi murna da ta amsa ta boye a cikin hijab dinta bata ko duba ba tace mata tayi gida sukayi sallama tana kawowa kofar gida ta hadu da malam ya dawo gurin daurin aure malam yace matar harzaki tafi da ban dawoba da mun samu sabani ko Rufaida tayi murmushi tace to yanzun mun hadu ai zan wuce yace Allah ya kiyaye kuma Allah ya kawo maki mafita a cikin al,amuran ki Allah yakara maki hakuri Allah ya bayyana maki mahaifiyar ki


A gaskiya Rufaida taji dadin addu,ar malam kamar bazata kara ganin saba hakan take ji har idon ta ya cika da hawaye tace amin nagode malam gashi tana son fada masa abunda ke damun ta Amman ta kasa kamar anrufe mata baki sukayi sallama da har ta juya malam yakirata yace zo matar ga kudin cefanen ki shima dai yau tsakana take ji sai dariya suke yabata kudin tace yawwa malam INA sauran kudin da kake ajiye mani

Makuwa yaji dadin yanda yaji zata anshi kudin ta yau Dan yana son farin cikin yar jikar Sa yace jirani yanzun nan zan baki kuwa haka malam yashiga gida ya dauko mata ya bata tayi murna sosai suka rabu



Haka takama hanyar gida tana tunanin Inna Uwani domin kuwa idan taga kudin nan kashin ta ya bushe cewa zatayi nata Ne kuma gashi duk sanda tane mi kudin ta ta rasa sai ta chage tas wannan ne dalilin da yasa take barin kudin gurin kakanta

Haka ta isa gida bata ga Inna Uwani ba kawai ta fada dakin ta ta dauki kayan ta da basu kala bakwai ba domin Inna Uwani ke amshe mata kaya tana gama dauka tafito sai gurin mashin tace a kaita tasha suna zuwa tasha ta hau mota



To Rufaida sai kuma wane garin ke nan



Inna Uwani kuwa na hango andaga ta sama ita ba samaba kuma ba,akasa ba sai halin ta take wato ihu wayyo waye zai CeCe ni wayyo makota wayyo malam kadawo muna gidan guguwa wayyo zamu bar maku gidan ku wayyo jama,a kuzo kuyi jahadi wayyo ni kaina inna Rufaida kizo ceto wallahi yanzun Inna Rufaida zan rika ce mata kuma zan dinga goyata inbata abinchi abaki wayyo inna aljannu kuyi Mani rai duk wannan kuwar da keyi idon ta arufe suke domin tana budewa zata ga kamar zata mutune






A Abuja kuwa Anty amarya ana nan ana mulki kuma tana nan kan bakanta na yiwa Ridwan auren dole..................







Comments and share

Takun nan daice

Hassy soja

Yar mutan gusau
4/19/20, 7:44 PM - +234 706 361 7906: ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ

๐Ÿ™†๐Ÿปโ€โ™€BANI CE BA๐Ÿ™†๐Ÿปโ€โ™€

๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ



(Aljana ce)


BY
Hassy soja







Ina Godiya DA Addu, oin Ku Allah Ya Saka DA Alkhairi Allah Ya Bar Mu Tare Amen







Alhamdulillah Nagode Da Addu,oin Da Kukayi Wa New born Baby Da Allah Ya Azurta Antyna Da Ita Allah yabar Zumunci Amin




Bismillahir Rahamanin Rahim DA Sunan Allah mai Rahama Mai Jin'kai






Sadaukarwa Ga Mahaifina Allah Ya jikan Sa Yayi Masa Rahama Amin.





Page 26----30





Anty Amarya kuwa tana Nan Ita DA yayan Ta Sai Shige DA Fice Suke Akan Auren DA Suke kidan Su Da Rawar Su Domin kuwa Jin Suke Babu Wanda ya Kaisu farin ciki Domin Kuwa Abba ya Sakar masu Bakin Ajihu kudi suke Tatsar Sa Babu tausayi ko nan da in duk wannan Abun da suke yi babu wani Abun Azo Agani da Sukeyi Suna Dai Fatat Takar Kudin ne kawai Gashi duk yarin yar da suke Son hada shida Ita Batayi Masuba








Akwai wata Yar Kawar Anty Amarya Wadda Take Mugun Son Ridwan Gashi Maman ta Kawar Anty Amarya ce Irin Sosai din nan Safina Yarinya ce Mai Son Namiji Hadadde Gashi Tana Ganin Bakin Cikin Su Anty Amarya yayi Mata Cikas Ita da Maman ta Sun kyafce Wannan Auren Shi Yasa duk Wannan Bata Lokacin Duk Aikin Sune Domin Hajiya Khalisa Mace ce Maison Kanta Sosai Kuma Tana Kawan Cene da Anty Amarya Dan Tasamu Burin Ta Yacika Akan Abba da Dansa Da Dukiyar Su Yanzun Burinta Wannan Auren ne Take Son Ta Canza Shi Ayi DA Yarta Da Anyi Yanda Ta Tsara Shike Nan





Shin Wai Wane Miye Wannan Tsarin Na Su Hajiya Khalisa Da Yarta






Duk Wannan Abun Da Hajiya Khalisa Keyi Anty Amarya Bata Gane Nufin Taba Duk Da Boka Dan Tukunya Yana Jamata Kunne Akan Wasu Daga Kawayen Ta Kuma Yafada Mata Cewa Aikin Su Baison Yarda Da Kowa Amman Takasa Kin Bin Shawarar Kawar Ta Dukda Tasan Yarta Nason Ridwan Tasan Sharadin Dan Tukunya Gashi Tafi Yarda Da Auren Yar kauye Wadda Take Jihila Batada Ilimin Isalama Bare Ilimin Boko Dan Haka Bataga Wanda Zai Lalata Mata Aikin Shekara Da Shekaru Shiyasa Take Ta shirin Yiwa Ridwan Auren Zabin Kanta Yanzun Hakan Saura Sati Biyu Ya Rage






Ridwan Bawan Allah ko Ajikin Shi Wannan Auren Domin Yasan Badan Mahaifin Sa Ya Rantse ba Da Babu Wanda Ya Isa Yamasa Dole Amman Babu Komai Idan Aka Daura Ranar Zai Sakar Masu yarin Yarsu Him Indai Nine Ridwan To Sai Nayi Maganin Yar Tashar Nan







************** Allah Sarki Rufaida Ko Acikin Mota Bata San Inda Zataba Amman Taji Ana Cewa
Kano Kaduna Zamfara Sokwato Abuja Da Dai Sauran Su Ita Dai Kawai Tarasa Wace motar Zata Hau Kawai Tayi sha Hada Ta Rutse Ido Tayi Halin Yarin Ta Kawai Tafara Nuna Motocin Da Yatsa Tafa Inci Nan Ko Inci Nan Ta Allah Tacce Inci Nan Aikuwa Haka Ta Rikayi Babu Tsayawa Mutane Har Tsayawa Suke Suna Kallon Ikon Allah Wasuma Abun kallo Yasamu Sai Dariya Suke Sun San Akwai Kuruciya Atare Da Ita
Wani Bawan Allah Ne Dattijo Yazo Gurin Ta Yace Yarinya Ina Zuwa







Itakam Rufaida Sai Kawai Taji Tace Masa Abuja Zani Aikuwa yarinya Kinga Gurin Da Ake Biyan Kudin Kibiya Ku Wuce Dan Mutum Daya Ya Rage





Haka Rufaida Tabiya Kudi Suka Kama Hanyan Abuja Yanzun Kuma in Muje Abuja Gurin Waye Zani Kuma A Inane Zan Sauka Allah Ka Kawo Mani Mafita Allah kado Rani hannun Kwarai Rufaida Ce Ke Wannan Tunanin Har Bacci Ya Dauke Ta Bata San MA Sunzo Ba Har Sai Da Taji Ance Yarinya Mun Iso


Bayan Rufaida Ta Sauka Ne Takama Hanya Tafita Tasha Taje Gurin Masu Bread Da Lemo Ta Saya Tasamu Wani Masalacin Mata Tayi Sallah Ta fara Jero Addu,oi Iri Iri Da futa Takama Hanya Tana Tafiya Gashi Batasan Ina Zata Dosa ba Gashi Dare Yasoma A haka Allah yakawota Gurin Wata Mai Abincin Sayarwa Taje Ta Sayi Shinkafa Da Miya Harda Su Nama Gashi Abinchin Da Tsada Kunsan Abuja Da Tsadar Rayuwa Haka Takoma Gefe Tacinye Ita Ko Mai Abinchin Da Kallo Take Ta Binta Cikin Zuciyar Taji Lallai Yarinyar Nan Tana Bukatar Taimako Koda Na Gurin kwanane Tunda Taga Tagama Cin Abinci Amman Kuma Tana Zaune A Inda Take Bata Tashi Ba Take Ta Matsa Kusa Da Rufaida Tace Baiwar Allah kin Manta Gurin Da Zakine Ko Unguwar Ce Kika Manta Ai Kuwa Rufaida Tace Eh Hajiya Na Mance Sunan Unguwar Ne Gashi Yanzun Ban San Gurin Da Zan Dosaba

Matar Tace Allah Sarki To Zan Taimaka Maki Idan Nasayar Da Abinci Na Daman Yakusa Karewa Taso Kizauna Cikin Shagona Kafin Ya Kare





Haka Kuwa Akayi Abincin Na Karewa Suka Nufi Gidan Matar koda Suka Isa Matar Tabude Gidan Suka shiga Ta Nunawa Rufaida ko Ina Kuma Tace Tayi Wanka Tayi Sallah Sai Ta Kwanta Ta Futa






Rufaida Kuwa Tayi Murna Sosai Kuma Ta Gode Allah Domin Shine Yakawo Mata 'Doki
Bayan Rufaida Tayi Sallah Ta Kwanta Domin Futawa Da Kuma Tunanin Yanzun Kuma Daga Nan Ko Sai Ina Oh Allah Ka Kawo Mani Mafita A Haka Har Bacci Yayi Awon Gaba Da Rufaida


To Rufaida Asuba Ta Gari








******************** Keeee Rufe Mani Baki Wato Ke Tubar Mazuro Ko To Yau Taki Tazo Karsheeeeeeee Ai Inna Uwani Bata San Sanda Tafara Fesa Zawo Ba Gashi Da Mugun Wari Sai Kiran Take Wayyo Inna Ta Kiyi Mani Rai Ai Duk Halina Ya Sauyu Da kansa Idai Dan Nice Uwani Bazan Koma Shiga Fadar Kuba Gidan Nan MA Yafita Raina Amm Amm In In Kuma Daga Yau Kowace Sallah Bata Wuceni Nazama Malama Uwani Ba Muguwa Uwani Ba Kuma Zan Nemi Malam Da Duk Wanda Nacuuutaaaaaa Yafuya BalanTana Ma Inna Rufaida Haihuwar Albarka Yar Malam Adamu Jikar Malam Shu'aibu Aikuwa Aka Bushe Da Wata Irin Dariya Mai Firgitar wa Aikuwa Uwani Ta koma Somewa





Kuyi Hakuri Naso Nafi Haka Amman Saboda Hidima Ga Wannan kuyi Hakuri Da Shi






Comments And Share




Daga Alkhalamin โœ๐Ÿป

Yar mutan gusau



Hassy Sojaaaaaaa
4/19/20, 7:45 PM - +234 706 361 7906: ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ

๐Ÿ™†๐Ÿปโ€โ™€BANI CE BA๐Ÿ™†๐Ÿปโ€โ™€

๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ๐ŸŒฒ


(Aljana ce)


BY

Hassy soja



ยฎ๐ŸŒ
*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION..๐Ÿ“š๐Ÿ“š*
_{ฦ˜ungiya Domin, wayar da ฦ™an mata Farin jini writer's domin ci gaban Mata.}_

โ˜…{ F J W A}โ˜…๐Ÿ“

https://www.facebook.com/Farin-jini-writers-association-108359057471117/

Wow Ina Alfahari Da Ku masoyana Allah Ya Bar zumunci Amin.





Bismillahir Rahamanin Rahim Da sunan Allah mai Rahama mai Jin'kai












Sadaukarwa Ga Mahaifina Allah Ya Jikan Sa Yayi masa Rahama Amin.




Page 31-----36


*************************




Koda Su Rufaida Sukayi Sallar Asuba Basu Kwanta Ba Sunata Faman Aikin Abinci Sune Basu Gama Ba Sai Gurin karfe Takwas Bayan Sun Gama Ne Sukaci Abincin Sannan Matar Tace Rufaida Jeki kiyi wanka Kinsan Yanzun Zanfita kigama Kizo Muyi Magana Rufaida Tace To Hajiya
















Bayan Rufaida Tafito Ne Tana Shafa Man Shafin Da Akabata Sai Matar Tafara Yimata Bayani Kamar Haka













Duk Da Ban San A,ina Kika Futo Ba Kuma Naga Kinada Hankali Shiyasa Na Sauke Ki A Gidana Duk Da Ban San Inda kike Nemaba Nabaki Sati Daya Har ki Futa Kuma Kigane Gurin Mutanen Da Kikazo Gurin Su Duk Da Girman Garin Abuja Amman Insha Allah Zaki Gane Gurin Da Kikazo Domin Kalar Ki Da Yanayin Da Na Ganki Bai Nunamin Cewa Kin Gudo Bane Ko Kuma Kinzo Yawon Duniya

Please Login or Register in order to submit comment