Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

MUSLMI BAKI DAYA AMIN YA ALLAH



BISMILLAHIR RAHMANIN RAHIN





Page 76___80




_________________________


Amarya Saudat da Angonta Acikin Mota Sai Fira Suke Suna Dariya Tafiya Sukayi Sosai Wadda Saudat Takasa Boye Mamakin ta




Tace Dear Har Yanzun Bamu Isa ba Murmushi yayi Yace Mun Kusa Zuwa Dai Amarya Saurin Mi Kike Keda Kike da Alhajin ki Daya A Gabanki mun kusa Zuwa Fadata Kinji ko





Saudat Bata Sake Cewa komai ba Sai da Sukayi Tafiya Mai Nisa Sosai Dan Sai da Suka Bar Garin Abuja Sosai Suka Tasamma Garin Kaduna Amman Basu Kai ga Kaduna Suka Yanki Wata Hanya Wadda Babu Mota Gaban su Kuma Babu Ita Abaya





Sunyi Tafiyar Kusan Rabin Awa Amman Babu Gida Gaban Su Kuma Babu shi Bayan su Sunyi Tafiya Sosai





Sannan Suka Iske Wani Irin Katon Gida Kamar ba,a NAGERIA Ba Ada Har Saudat Taji cikinta Na Juyawa Amman Kuma Ganin Wannan Gidan Sai Taji Hankalin ta Ya Kwanta





Wani Remote ne Ya Fidda Ya Latsa Take Get din Gidan Yayi Sama Shikuma Yaja Motar Sai Cikin Gida




Gidan Wani Irin Rikitaccen Gidane Wanda Bazaka Gane Ai Nahin Yanda Yake ba In Banda Kukan Tsun tsaye Babu Abunda Kakeji





Kafin Su Isa Parking Space Ma Aiki ne Dan Inda Kafa Zaka Je Gurin Tofa Sai Ka Hada da Gudu Sannan Zaka Isa Cikin Minti Ishirin






Isar Su Gurin Ke Nan Alhaji Muntari Yace To Amarya Ga Fadata Nan Mukarasa Ajiyar Zuciya Saudat Ta Sauke Dan Yanzun Kam Tafara yin Sanyi Game da Angonta






Sun Danyi Tafiya Suka Isa Bakin Kofar Shiga Harabar Gidan Sunyi Tafiya Nan ma Suka Isa bakin wata Kofar





Yanzun Kam Matsawa Yayi Bakin wani Corridor Ya Dan Taba Wani Abu





Ai kuwa Kofar Tafara Budewa Sannu Sannu Zuwa Can kofar Ta Bude Matsowa Yayi Inda Take




Yace Mujeko Shiga Sukayi Cikin Falon Wani Irin Duhune Sukayi Arba dashi Kamar Wani Mugun Kogo






Wani Irin Tsoro Da Faduwar Gabane Suka Riski Saudat Atake Sai Ta Runtse Ido





Wani Abu Ya Danna Sai ko Dakin Yakawo Wuta Wani Mugun Haske Ya Gauraye Dakin





Yace To Bude Idon ki Mana Cikin Tsoro Tabude Dakin Budewar ta Keda Wuya Taga Ko Ina Haske Ajiyar Zuciya Ta Sauke





Tasamu Kujera Ta Zauna Cemata Yayi Kiji rani Ina Zuwa cewa Tayi To



Wuce ta Yayi Yashiga Cikin wani Daki Kusan Minti Talatin Har Tagaji Dajiran Sa Sai Gashi Yafito Ya Sauya Kayan Jikin Sa Yafito da Jajayen Kaya Fuskar nan Babu Rahma Babu Alamun Annuri Wasu Matane Biye Da Shi Su Kusan Tara Kowace Kagani Tana Cikin Alamun Kamun Yunwa Da Wahala




Ai Da Sauri Saudat Ta Tashi Tsaye Jikinta Na Mazari Karasowa Yayi Ya Zauna Ya Dora Kafa Daya Akan Daya






Cikin Wata Irin Tsawa Yace Kuzauna Kafin Ya Ida Rufe Baku Dukan su Sun Baje Akasa Kamar Masu Neman Afuwa Amman Banda Daya Daga Cikin Su





Yarage Su biyu ne Atasaye Wata Tsawar Yakoma yi Akaro Na biyu Wanda Sai da Saudat Tasaki Fitsare Take Ta Zauna Ita Kuwa Dayar Kin Zama Tayi







Hhhhhhhh Nasani Nabila Dama Bazaki ji Tsorona Ba Amman Kisani Kin Rigada Kin Shigo Babu Fita Ke Ko Mutuwa Kikayi Anan Tofa Gawar ki Bazata Fitaba






Murmushi Wadda Aka Kira da Nabila Tayi Tace Ta Allah Bata Mutum ba Kuma Idan na mutuma Lokaci nane Yayi Kaga Ita Mutuwa Dama Ba,a Guje Mata





Duk Inda Mutum Yaje Tana Tare Dashi Kuma Tana Dauka Kaga Kuwa Miye Abun Tsoro Anan Balle Harma Takaini Da Gudun Mutuwa





Miye ma Acikin Duniyar Ai Sai dai Fatan Cikawa Da Imani




Murmushi Yayi Yace Naji Yarinya Taro Yarone Bai San Wuta ba Sai Yataka





Nabila Aikin Gama Yagama Tunda Aka Bani Kyautar Ki Amman Kash Kin Cika Taurin Rai da Yawa Da Yanzun Baki Duniyar Amman kisani Zan Haka Maki Tarko Kuma Sai Kin fada






Him Aini Zuciyata Tariga da Ta Bushe Na Daina Jin Shakkar Kowa kuma Bana Tsoron Komai Sai Allah na



Ina Fatan Ka Gane Domin Shine Gatana Kuma Mai Bani Kariya Aduk Inda Nake





Kune Mahaukata Kuke Ganina Kamar Banda Gata To Kasani Allah Shine Gatana Kuma Sai Allah Yakawo Karshen Irin Ku






Azafafe Yatashi Yayo Kanta Har Yadaga Hannu Mikuma Yatuno Sai Yafasa Ya Juyo Gurin Saudat yace







Maraba da Zuwa Fadata Kisani Kin Aurowa Kaki Jaraba Na Auro kine Saboda Kwada yinki Kuma Nasan Duk Abunda Uwarki Keyi





Kisani kin Shigo Gidan Yunwa da Azaba Ga Wani Albishir Jinin kine Dodona Yake so





Shiya Turani Kawoki Amman Da Sharadin Aure Daman Yace Da Kinzo Gidan Nan Da Aure To Nasake ki Babu Abunda Mike Bukata Agareki Sai Shanye Jininki Kuma Mu Kwashe Kayan Cikin ki




Daga Nan Anwuce Gurin Hhhhhhhhhh

Wata Iron Kuwa Saudat Ta Watsa




Shikuma Cewa Yayi Wannan Shine Abunda Nake sonji




Yadubi Nabila Yace Kinji Yanda Zakiyi



A,uzu Bi Kalimatillahi Tamatin min Sharri Ma Khalaqa




Wata Iron Zubura Yayi Sai Kan Saudat Yakama Duka Kamar Jaka Saida Yaga Bata Motsi Ya Sallaketa Yatafiyar Sa



Yabasu Atsaye Babu Wanda Yabi Ta Kanta Sai Nabila Tajata Suka koma Inda Suka Fito




*************************




Su mame Sun Isa Gida Inda Ridwan Ke Tallabe da Abba Wanda ke Fama da Ciwon Kai Mai Tsanani






Mame Kuma Tallabe Da Rufaida Wadda bacci Yakama Tun Fitowar su daga Gurin Boka Dan Tukunya Itama Mame Daurewa Kawai Take Dan Itama Bata Jin dadin Jikinta






Suna Isa Falo Suka Yada Zango Inda Turin Zaman Ne Ciwo Yatasowa Ramlat Ganin Halin da Ramlat Take Cikine Yasa Mame Tace Husaina Takai Rufaida Daki






Ita kuma Ta Koma Gurin Ramlat Suka Sa Driver Ya kaisu Asibiti






Basu Dade Da Fitaba Abba Yasamu Bacci Mai Nauyi Koda Ya falka Ridwan ne Zaune Kusa da Shi






Abba ne Yace Ridwan Lafiya dai Naga Kamar Kayi Nisa Atunani





Murmushin Farin Ciki Ridwan Yayi Yace Alhamdulillah Abba Sannu





Yauwa Ridwan Kazan Wani Mummunan Mafalkin Da Nayi





Ridwan ne Yace Abba Bar Zancen Nan Tashi Kayi Wanka Muje Asibiti





Subhanallah Asibiti Gurin waye Abba Gurin Su Mame




Mamen ce Taku Babu Lafiya A,a Abba Ramlat ce Me Labour Ramlat cewar Abba Da Sauri







Aikuwa Take Abba Yatuno Komai Ashe dai Ba Mafalkine ba Da Gaske Ne Wayyo Allah Amman Wannan Matar Ta Cuceni





Tashi Abba Yayi Da Sauri Yace Muje ko Ridwan




A,a Abba Kabari Kayi Wanka Mana A,a Ridwan Muje Kawai Har Abba Nashirin yin Tun tube





Yanda Abba Yafitone Yasa Su Two win Kasa boye Mamakin su Sukace Abba Lafiya Dai Cewa Yayi Kuzo Muje Asibiti Mana





Husaina Tace Ku Tafi Abba In Zan Zauna da Rufaida OK
Muje Kawai Hasan





Ko da Suka Fito Harabar Gidan Duk Wanda Yaga Abba Tare Da Yayansa Mamaki yakeyi Sai Hamdala Ma,aikatan Gidan Keyi





Ridwan Ke Jan Motar Suna Isa Ana Shaidawa Mame Ansauka Lafiya Ansamu Baby Boy Murna Gurin su Ba,acewa Komai Sai Hamdala





Mame ma Ganin Abba Agurin Ba Karamin Jin Dadi Tayiba Har Sai da Bakinta Yakasa Rufewa







Ganin Ramlat Lafiyar Ta Lau yasa Aka Sallame su Suka dawo Cikin Farin Ciki





Isar Su Gida Ke Nan Suka Isko Rufaida da Husaina Suna Tsallen Murna






Har yar Rigaga Akeyi Gurin Daukar Yaron






Abba Kuwa Idon Sa Ya Sauka Akan Rufaida Baki Na Rawa Yace Ke Zo Nan





Ai Ido Kowa Yake Bin Abba da Shi Abba Yakara Cewa Kuna Nufin Baku Gane Ko Wacece Ita ba








Mame Tace Duk Munso Ganeta Amman Mun Mace Inda Muka San Fuskar





Matsawa Abba Yayi Yariko Hannun Rufaida Wadda Ta Zama Status






Zama Abba Yayi Yace Masu Kuma Duk Ku Zauna kowa Guri Yasamu Ya Zauna Abba Yace






Yaya Sunanki Cewa Tayi Rufaida Abba Ya Jinjina Kai Yace Rufaida Ina Asma,u Auta Ina kuma Malam Da Inna





Ai Rufaida Zare Ido Tayi Tace A,INA Kasan Mamata da Kakan nina Cikin Ware Ido Da Alamar Tsoro Tayi Wannan Zancen







Abba Yace Kin Taba Jin Ana Cewa KABIRU Dan Gidan MALAM SHU'IBU Wanda Yake Abirni Bai Dawoba






Ai da gudu Rufaida Takoma Daki Ta Bin Ciko photon Da Tamso Gurin Kakarta Wanda Bata Bude ba Balle Tagani






Koda Ta Dauko Budewa Tayi Tazaro Ido Ganin Tabbas Shine Kawunta Da photo Tafita Da Gudu Ta Kaimasa Ta Fada Jikin Sa Tana Kuka






Dubawa Yayi Yami kawa Mame kowa Mamaki take Ashe Dai Suna Tare da Farin Cikin Su Basu Saniba Sun Godewa Allah Da yasa Basu Gujeta ba






Abba be Yake Tambayar ta Ina Kowa Da Kowa Anan Ne Sukaji Mummunan Labarin Batan Asma,u Auta





Kuka Abba Yake Kamar Karamin Yaro






Ya Akayi Kika zo Nan Anan ma Tabasu Labari





Abbane Yace Tabbas Wadda Takoki Nan Itace Ta Dauki Mahaifiyar ki Kuma Itace Ta Karya Duk Wani Abu Wanda Akayi Mani





Ya Allah Kasa Tadawo Ko Musamu Mugane Inda Taboye Muna Abarson mu





Shurun shi Me dawuya Sukaji Ance........







Comments And Share




Takundai ce



Hassy Soja




Year mutan gusau ce
4/19/20, 7:52 PM - +234 706 361 7906: 🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲

πŸ™†πŸ»β€β™€ BANI CE BA πŸ™†πŸ»β€β™€

🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲


(Aljana ce)



BY
Hassy soja





Ina alfahari da Ku masoyana yanda kuke nuna Mani kauna 🌹🌹




A gaskiya In jidadi comments din Ku sosai Allah ya bar zumunci Amin.πŸ₯°




Ina yinku overπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°



BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM
DA SUNAN ALLAH MAI RaHAMA MAI JIN'KAI





Sadaukarwa Ga Mahaifina Allah ya Jikan Sa yayi masa Rahama Amin.


Page_______81/85




************************


Assalam Alaikum Ko Zaku Iya Bamu Masauki




Mamaki ne Yakama Duk Wanda Ke Gurin Saboda Basuga Lokacin da Suka zoba Sannan Daganin Wannan Mutanen Ba Yan Najeria Bane Shin Yama Akayi Suka Shigo Batare da Anzo Neman Azini ba




Daga Ganin Shigar Wannan Bayin Allah Tabbas Kasan Cewa duk Inda Suka Fito Gidan Sarauta ne Sannan Kuma Hutu Ya zauna



Abun mamaki ma Taya Akayi Suka Iya Hausa Har Haka Duk da Sunji Hausar Bata Zauna Sosai ba



Da Sauri Rufaida Ta Mike Tsaye Tana bin Matar Da Ido Murmushi Mame Tayi Tace Bismillah Shima Abba Cewa Yayi Ku Shigo Mana Ga Wuri Ku zauna




Ida Shigowa Sukayi Wata Mata ce Tashigo Tare da Wasu Wanda Dagani Ita Matar Ita Keda Mulki Sauran Kuwa Duka Hadiman Tane




A Kujerar Ta Zauna Su Kuwa Sauran Sunkai Su Bakwai A Kasa Suka Zazzauna





Bayan Matar Ta Zauna ne Tace Rufaida Kin Shaida nine ko Zaki Tuna Inda Kika Sanni





Girgiza Kai Rufaida Tayi Tace Naso Nagane Amman Naka Tunawa kuma Nasan Muryar



Zuwa Can Kuwa Rufaida Tace Yauwa Natuna Mama Kece Me Zuwar Mani Amafalki Kina Lallashina Kuma Kece Kika Sanya Nazo Garin Nan Dan Bazan Taba Mance Muryar kiba Insha Allah






Yauwa Yar Kwarai Yarin yar Kirki Kinyi Kai Sosai Tunda Har Kika Shaidani





To Zauna Magana Zamuyi Daku Duka Zama Rufaida Tayi bata Sake Cewa komai ba






Abba Kuwa dasu Mame Sun Kasa Gane Mi Hakan Ke Nufi Dan Sun Shiga Rudani Dan Basu Gane Mi Hakan Yake Nufiba




Cewa Tayi Ku Kwantar da Hankalin Ku Kuma Kada Kuji Tsoro Nazone Dan Warware Maku Duk Abunda Ke A Duhu Yanzun Ku Natsu Kuji Wace ce Ni Da Kuma Dalilin Zuwana




Da farko dai Sunana Sarauniya Farhanatul Nur Al,mansur Ni yar Sarkin Aljannuce Kuma Mijina yariman Wata Masarauta ce




Nazo Ziyara ne A Wannan Kasar Cikin Kakanin Ku Akwai Wanda Yayi Aiki Da Aljannu Acikin sune wani Yayi Aiki da Kanen Kaka na To Saboda Ziyara





Da Mutunta Juna Yasa Ahlinsa Dake Zaune Akasar nan Suna Kai Muna Ziyara Sune Suka Shaida Muna Rashin Lafiyar Sa Shiyasa Mukazo Duba shi Wannan Shine Zuwana Na farko Akasar Nan





Bari Nasanar Daku Abunda Wasu Mutanen Ke Dauka Wasu Basu Dauka Cewa Muma Da Muke Aljannu ba Muna Ciwo To Kusani Ba,abun Mamaki Bane Muma Bayin Allah ne Muna Yin Ciwo




Bari Nadora Maku Inda Natsaya Dan Nan Baku Fahim ci Komai ba Sai In Nakare To Zuwan Da Nayi ne Allah Yasa Mun samu Yaji Sauki Shine Muka Shirya Yawon Shan Iska To Agurin Yawon ne Nabiyo Ta Garin Ku Kai Kabiru





Nazo Wucewa ne Nayi Shigar Yaro matashi Mara jin Magana Inda Nake Jan Duk Wanda Naga Kansa Na Hayaki




Duk da Naji Cewa Mutane Basuda Hakuri Ko Kadan Kuma Zamana Agarin Nan Nashaida Wasu Daga Cikin Halayen Mutane





Duk da Na Hana Hadimmai Na Suyiwa Kowa Wani Abun Cutar wa Saboda Inayin Shigar Mai Hakuri Kuma Inayin Akasin Haka



Mutane Wasu Basu Dauki Hakuri Abakin Komai ba Amman Ni Inason Mai Hakuri Sosai






To Acikin Wannan Yanayin Ne Narashin Jine Naje Gonar Malam Shu'aibu Wato Mahaifin ka






Nayi Masa Barna Sosai Kuma Na zauna Ina Jiran Zuwan Sa Saboda Na Hango shi



Koda Yazo Yaga Aika Aikar Da Nayi Masa Nadauka Zaiyi Masifa ne




Kuma Dai dai Nan ne Mahaifina Yabiyo Bayana Ransa Ya Baci Akan Abun da Na Aikata Bayan Shigar Danayi Ga Kuma Gurin da Na zauna Sannan Kuma Ga Barnar Danayi wa Malam Shu'aibu Har Mahifina Zaiyi Magana




Sai Ga Malam Shu'aibu Yazo Inda Nake Amman Baiga Tawagar Mahaifina ba Kuma Baiga Nawa Hadimman ba Wanda Suke Duke Suna Jiran Hukun cin Mahaifina



Zuwan Sa keda Wuya Yayi Sallama Yace Assalamu Alaikum Bawan Allah Ko Kasan Wanda Yayi Wannan Aikin



Mahaifina ne Ya Hana Kowa Yin Wani Abu Akai Kuma Yana Kallon Malam Shu'aibu



Malam Shu'aibu Ci Gaba Yayi Da Cewa Dan Allah Baka San Wanda Yayi ba Cewa Yayi To Babu Komai Har Yajuya Zai Wuce



Cikin Rashin Ji Irin Na Bil Adama Nace Masa Malam Ai Tunda Bakaga Kowa Anan ba Kasan Nine ko



Juyowa Malam Shu'aibu Yayi Yace Amman Kayi Kokari Tunda Baka Dauki Hakkin Kowa ba Kasani Nayafe Maka






Bani daya Wannan Bawan Allah Yabawa Mamaki ba Dukan mu Wannan ne Yasaka





Mahaifina Yace Lallai Wannan Bawan Allah Zamu Taimaka Masa Da Izinin Allah Sannan Kuma Zamuyi Yaki Da Duk Wanda Yayi Nufin Chatata Masa





Tabbas Malam Shu'aibu A lokacin Bai San waye Niba Bayan Wannan Lokancin Kuma Naci Gaba Da bibiyar Sa







Akwai Wata Rana Yadawo Masallaci Ya Hadu da Wata Karamar Yarinya Tana Kuka Kowa Yazo Gurin Yakan Wuce tane






Dan Mutane Cewa Suke Bazasu Iya Tabata ba Wata Kilama Aljanace






Amman Zuwan Malam Shu'aibu Bai Wuce ba Sai da Yatsaya Gurin Yarinyar Yana Tambayar ta Cewa Ina Tafito Kuma Waye Ya Tabata





Yarinyar Kallon Sa Yayi Tace Masa Inna tace Ta Aikeni Kumu Kudin Yafadi




Haka Kuwa Malam ya tambaya Nawane Tafada Masa Yakawo Wasu Kudin Tabata Duk Wannan Abun Akan Idona Ya faru







Bibiyar da Nake yiwa Malam ce Yasa Nagane Kyawa Wan Dabi,un sa




Kuma Naga Yanda Ya Taimaka wa Marayan Allah Wato Malam Adamu Mahaifin Rufaida





A Cikin Wannan Lokacin ne Nasamu Shiga Gidan Malam Kuma Nasamu Abunda Nakeso






A Lokacin Kaine da kawai Agurin Malam Shu'aibu Amman Naga Kai Kafi Son Boko Fiye da Tunanin ka Sannan Kuma





Nice Nata Yimaka Taimako A Gurin Karatun ka da Kuma Neman Aiki





Sai da Naga Kacika Sakaci da Addu,a Saboda Harkar yanayin Aiki Sannan Kuma Baka Cika Zaga Mahaifin kaba Yasa Nabar ka kagane Miye Duniya







Amman kuma Kasani Anyi Tabibiyar ka Amman Babu Nasara Tunda Ko Bana Kusa Da Kai Akwai Hadimmai Na Dan Haka Ko Wannan Mukamin Naka Da Karasa Shi Tun Tuni





Domin Akan Shirya Kashe ka Yafi A Girga Sannan Kuma Ko Kwance Maka Burkin Moto Anyi Kusan Sau Goma






Allah yasa Matar ka Tana Kokarin Tuna Maka Zuwa Duba Mahaifin ka Ganin Kana Yawan Kawo Mata Uzuri Yasaka Ta Daina Tuna Maka Wannan Abun da Kuka Aikata






Shiyasa Nabar Maku Kaltume Tashigo Gidan Ku Domin Koyar da Ku Hankali Da Kun Tunada Su Malam Da Abun Bai Kai Haka ba Damma Allah yasa Kana tunawa da Kanwar ka Kafin




Har ko kinka Suka Dauke Maka Hankali Kama Daina Tuna Zuwa Inda Suke




Kuma Mance Hakkin Iyaye Akan "Yayan Su Kamance Duk Wata Wahala Da Sukayi Dakai Tun Kafin Zuwan ka Duniya Har Zuwa Lokacin da Kamallaki Duk Wata Dukiya Dakake Da Ita






Kasani Duk wata Musiba Allah Yana Kare Bayinsa Bisaga Addu,ar Iyaye To Kai Kuma Ka Mance da Hakan Duk da Tarin Ilimin Ka Gashi Saboda Wannan Allah Ya Jarab ce ka Da Mata Mushrika




Bawai Dan Ban Iya Komai Akaiba Kawai Nabar ka kane Ko Allah nasa Katuna Iyayen ka





Yaranka ma Sau biyu Kana Zuwa Dasu Sannan kuma Ridwan ne Sai Ramlat Kawai Amman Banda Sauran




Kanji Wannan Game da kabiru Sauran Asma,u mahaifiyar Rufaida







Nice Na Karbi Haihuwar Asma,u A lokacin Ina Zaune ne Agidan Malam Shu'aibu Ina Kula Da Asma,u Sosai Allah yasa Mani Sonta A sanadin Son danake Yiwa Asma,u ne Yasaka Yarima na Barina Akasar Inda Nasanya Wasu Daga Cikin Haddimai na Kula Mani da Kabiru




Nikuma Ina Kula Da Asma,u Tun Tasowar Asma,u Naga Al, Amura Masu Riki Tarwa





Tabbas Nasan Tsaka Ninta da Adamu Akwai Aure Harda Iyali






Malam Shu'aibu ya sanya Auren Asma,u da Adamu Ganin Yarasa Mai Bashi Mata Saboda Halin Matar Sa Uwani Wadda Da Bin Bokaye Tasamu Tashigo Gidan Sa Kuma Itake Kora Masa Mata Harda Hauka tarwa





Saboda Ina Son Malam Shu'aibu Yasan da Nine Yasa Nafara Yun kurin Hana Haure A Wannan Ranar Ne Kowa Yasan Dani Harda Adamu




Anyi Aure Lafiya Alhamdulillah Duk Abun da Uwani Keyi Akan Asma,u Takasa yin Nasara Tunda Taga Haka bata Hakura ba Sai da Takoma Bayan An Haifi Rufaida Inda Suka Chanza Shawara Saboda Nakan Batawa Bokaye Aikin Su Indai Zasuyi Aiki Akan Asma, u





Shawarar Da Suka Chanza Kuwa Itace Danne Asma, u Da Filo Ko kuma Su Zuba Mata Miyar Kuka Abayi Idan Taje Wanka Tafadi Kuma Kafin Tafito Sun Makure Rufaida Ta Mutu





Sunyi Shiri Sosai Kuma Zasu zo da Maganin da Dazarar Taji Muryar Uwani Tofa Dole ne Ta Mutu ko kuma Ta Haukace






Nikuma Sai Nasa wa Asma, u Jin Wani Abu Zai Faru Da Ita Shiyasa Tabar wa Malam Adamu Wasiya Tabar Masa Rufaida A Hannun sa




Shigar Ta Akin Dakin ne Na Dauketa Nayi Wannan ne Dan Kada Afadawa Adamu wata Magana Akan Batan Asma, u





Najewa Malam Shu'aibu A cikin Barcin Sa Kamar yanda Nake Zuwar wa Rufaida Nasanar Masa Abun da Nayi Dakuma Dalili



Wanda Uwani Tayi Mugun Kafi Akan Asma, u Kuma Duk Wanda Yaje Gurin Wani Boka Akan Rufaida nike zuwa Dakaina Gurin yin gargadi







Wannan ne Ya Hana Uwani Cin Nasara Akan Rufaida kuma Nike Dauke Kudin Uwani Dan Insa Rufaida Tagane Ba Ita Tahaife ba






Saboda Wani Makirci Da Suka Hada Na Uwani Ta Rike Rufaida Kamar Yar Cikin ta Yanda Zasu Bakan Tamara In Ta girma Sannan Ta Sangar Tata Tanda Zata Tashi Lalatatta Rufaida Shiyasa Nikuma Na Tsiri Daukar Kudin ta Nazuwa Gurin Boka Da Take Tarawa







Saboda Kudin ne Ta nuna Tsanar Rufaida Afili Sai Ta Chanza Shawara


Shiyasa Take Dukan ki Rufaida Kinji Tarihin Da Malam Bai Sanar dakeba nabari Uwani Na Dukan ki Bawai Dan Ban Iya Komai Akanki ba





Sannan Wani Albishir Mai dadi Shine Yanzun Haka Nasa Akawo Maki Mahaifiyar ki Kai kuma Kanwar ka Abar Sonka Ku kuma Gwoggon Ku





Wani Abun Farin Cikin Tare da Adamu Mahaifin ki Rufaida Shima Adamu Na Dauke shine Na Hada shi da Matar Sa Asma, u Tun Lokacin da Kukaga Yayi Tafiya Bai Dawo ba Ni Nahana su Dawowa




Saboda Ina Son Fara Aikina Akan Duk Wani Azzalumi Malam Shu'aibu Agaskiya Mutumen Kirki ne Yayi Hakuri Sosai Ga Rashin Kabiru Babban dansa Ga kuma Rashin Autar Sa Kuma Harda jikar Sa





Amman kuma Malam Shu'aibu Yariga da Yasan Duk Wannan Abun Tun da Jimawa





To kunji Abun da yashige maku Aduhu Kun kuma ji Tarihin Abun da Baku Saniba






Ga baki Daya Gurin Kukane Me Tashi Sannan Tace Yanzun Lokacin Murna ne Ba Kuka ba





Yanzun Ridwan Tashi Kashigo da Baki Gasu nan Abakin Get





Ai Da Gudu Ridwan Yatashi Yana Zuwa Yaga Mace da Namiji Abakin Get Kallo Daya Yayi Masu Yagane Lallai Wannan sune Gwaggon Shi kuma Iyayen Rufaida Da Gudu Ya Karasa Gurin Su Ya Rungume ta Yace Kushi go Gwaggo na





Hannun Sa Suka Rika Sukayi Cikin Gidan Isar Su Babban Falon ke nan Abba Yayi Ido Biyu da Kanwar Sa da Aminin Sa Aifa Da gudu Suka Run gumi Juna Suna Kukan Farin Cikin





Mame ce Ta Task Tariko Hannun Asma, u Ta Hadata da Rufaida Tace Ku Rungumi Juna Dan Kusamu Sassauci Acikin Ranku





Da Sauri Suka Rungumi Juna Suna Kukan Farin ciki




Rufaida ce Tace mamana Ashe Zan Ganki Azahiri Ashe Nima Inada Mama Kar Kowa




Mamar ce Tace Rufaida ni Na sanki Kuma Ana Kawo Mani ke Ki Kwana Atare Dani Sai Gab da Asbane Ake Maida ke Kin dauka Amafalki Ne Kike Ganina Ko




Daga Kai Rufaida Tayi Maman Tace To ba Mafalki Bane Faskiya ne





Kara Rugumeta Tayi Tana Hawayen Farin ciki




Malam Adamu ne Yace Rufaida Ni kuma Anmace Dani ko Ai Dagudu Tayi Gurinsa Ta Rungume Sa Tana Hawaye





Tace Abbey na Nayi kewar ka Shima Rungume Yarsa yayi Gaskiya Fadar Irin Farin cikin Wannan Ahlin Suke ciki Baya Faduwa




Wannan Matar ce Tace To Zan Wuce Gurin Su boka Yakamata kuje Gurin Malam Shu'aibu Gobe In Allah Yakaimu Kuje Harda su




Mai jego Dan Kara Ganin Tushen Su





Sallama Tayi Masu Tace Sai Wani Lokacin koda Tatashi Sunyi Mata godiya Sosai Murmushi Tayi Tace Masu Sai mun sake Dawowa Shan Bikin Suna ko Asma, u





Rufe Fuska Tayi Suka Suka Sanya Dariya Da murna Rufaida Za,ayi Kanne Ko Kanwa







Juya Sukayi Kafin Su Ida Fita Kofa Suka bata bat



Sukuwa Babin Fira suka bude Inda Rufaida Take Makale Da Iyayenta Shima Ridwan yana Tare da Su Ga kuma Jaririn Ramlat










To Bari Muleka Gurin Su Uwani mugani









Wai Wai wai Him Wayyo Allah Mun tuba Munyi Nadama



Yelwa Wallah Kishin Ruwa Yadame ni Ga Uwar Yunwa Ga Fitsari




Wayyo Allah Yakawo Inna Aljana Allah ya Huci Zuciyar Inna Aljana





Uwani Har Kinada Bakin Magana Ki Duba Ki Gani Haduwa Ta Dake Babu Wani Abunda Ya Tabuka Mani Sai Tarin Nadama





Uwani A Gaskiya Ina Mai Bakin Cikin Sanin ki A Rayuwa Anya Uwani Kina Tuna Kalar Mugun Abun da Kikayi A Rayuwa Kisani Uwani Wallahi Nayi Tuban Gaskiya






Yanzun Kiduba Wa Incan Bokayen Ashe Suma Bazasu Iya Attaka Komai ba Inda Zasu Iya Da Sunyi wa Kansu Magani






Boka Dan Tsito kiduba Yanda Duk Suka Koma Kalar Tausayi Duk da Ba,abun Tausayi A gare Su Kiduba Yanda Sukayi Katon Ciki Lamar Masu Shirin Haihuwa ko Ruwan da Muke Dan Samu Muyi Kurbi Ukku Su Basu Samu






Yanzun Uwani Wannan Abun fa Azabar Duniya ke nan Inga Azabar Lahira Tabbas Munyi Mummunan Kuskure Kuma Kuma Jahilci ne Yajawo Muna Duk Wannan Abun





Shiru Yelwa Tayi da Tagama Wannan Maganar Hawaye Nazuba A Idon ta





Uwani ma Kukan Take Harda Shashshe ka Hawaye Zuba Kawai Yake Idonta Duk Sunyi Kumburi Saboda Kuka





Cewa Take Cikin Rawar Muryar Wallahi Yelwa Nayi Nadama Ta Gaskiya Tabbas Mahaifiya ta Ta Cutar dani Da Ace Inaga Dangin Mahaifina Da Nazama Yarinyar Kiki Kuma Abar so Ga Kowa Amman Yanzu Miye Amfanina Shin Wai Mahaifiyata Ta Taba Tunanin A,INA Nake




Koda Taji Zafi Nasan Wa,inda Na Cuta Sun fita Shiga Wannan Halin




Tabbas Bani son In Mutu da Hakkin Jama,a Yanzun Taya Zanfara Neman Wanda Nacuta Shin Yanzun A,ina Zan Gansu Na Rokesu Suyafeni ShinKo Hakkin Malam Adamu ma Kawai Ya Ishe ni Wayyo Ni Kaina Uwani Innata Kin Cuceni Kin dorani Mummunar Hanya Ya Allah Natuba





Su boka Kuwa Nishi Daya days Take Fita daga Bakin Su Ga Wasu Ruwan Kumfa Na Fita Aba kunan Su






Duk Wannan Abun da Suke A Tsaye Take Tana Kallon Su Kuma Duk Abun da Suke Fada Tana Jinsu





Matsowa Tayi Tace Tabbas Uwani Kunyi Kuskure Amman Ku Tubar wa Allah Sannan Kuma Ku Koma Duk Wanda Kuka Cuta Kunemi Yafiyar Sa






Yanzun Zan Maidaku Gida Jen ku In Kun Gyara Kanku juyawa Tayi Gurin Bokayen Tace Kuma Zan Maida Ku Dajin Ku Kuci gaba Da Inda Kuka Tsaya




Hannu Tasa Nuna Su Take Suka bace Bat





Sannan Ta dubi Gefen ta Tace Kun Ganar wa Idon Ku Wannan Mutanen Masu Iron Halinku






To Kusani Duk Abun da Kuka Shuka Shi Zaku Girba Dan Tukunya Zan Maida kai Dajin Da Kafito Nasan Baka Mance da

Please Login or Register in order to submit comment