Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Rausum
kenan hankalinsa ya dugunzuma ainun fiye da ko
yaushe.Nan take yarima Kamsus ya kama kafadun
boka Rausum ya tashe shi tsaye sannan ya
dubeshi cikin murmushi yace yakai dirkar Birnina
kayi sani cewa idan giwaye biyu na fada to dukkan
namun daji saidai suyi kallo.Kai dan kallo ne
kawai,bai kamata ka tashi hankalonka ba.Sarki
Masarul Anjana da mahaifina manyan giwaye ne
biyu,sauran sarakunan duniya da sauran jama'ar
mutane da aljanu sune namun daji.Kawai ka zuba
idanu kaga yanda karshen rigimar zata
kasance.Tuni a yanzu labari ya riski Sarki Masarul
Anjana bisa taurin kan Abbana da rashin
tsoronsa,me yasa bai dauki mataki ba a kansa?Kar
ta san kar kuma sai an gwada sannan ake sanin na
kwarai.Muje can turakar ta sarki,yanzun nan zamu
tafi.Koda jin haka sai murna ta kama boka Rausum
ya juya da sauri suka fice daga cikin turakar
yarima suka tunkari ta sarki.Da shigarsu cikin
harabar turakar ta sarki sai suka iske sarki Alkasim
a cikin rafinsa na wanka yana nishadi abinsa,ko
kadan babu alamar cewa yana sauri ko shirin
tafiyar dake gabansa.Koda sarki Alkasim ya hango
Boka Rausum tare da yarima Kamsus saiya
kyalkyale da dariya yace me kukazo yi wajena
yanzu.Ashe tun jiya ba na gaya muku cewa sai
yamma zamu bar garin nan ba?Kafin sarki ya gama
rufe bakinsa tuni Yarima ya tari numfashinsa yana
mai cewa ai na sauya tsarin tafiyar saboda
wadansu dalilai masu mahimmanci.Koda jin haka
sai sarki ya turbune fuska kuma yayi tsaki.Nan
take ya fito daga cikin rafin babu komai a jikinsa
face wani gajeran wando.Wohoho duk wanda ya
kalli sarki Alkasim a wannan lokaci yaga irin kirar
karfin da Allah yayi masa ta manyan sadaukai dole
ne ya sallama kuma ya firgita saboda kirjinsa kai
ya kasance tamkar na zaki cike da gashi,ga tudu
da fadi.Gaba dayan jikinsa a murde yake cike da
kwanji gami da tarin jijiyoyi tamkar ba kashi da
tsoka bane,sai kace dutse aka jajjera.
Zidane Kd
SAI KACE DUTSE AKA JEJJARA.Nan take wata
kuyanga tazo da sauri ta gogewa sarki Alkasim
danshin ruwan dake jikinsa gaba daya.Kafin cikar
yan dakiku an kawo tufafi iri daya dana jikin
Yarima Kamsus an sanyawa sarki Alkasim sai
gashi shima yayi kyau sosai.Kai in ba don sarki
Alkasim yana da saje da kasumba ba da shima
za'a iya cewa matashine kamar dansa Yarima
Kamsus.Ba tare da bata wani lokaci ba aka gama
kimtsa sarki suka tafi izuwa babbar fada su
ukun.Dakaru da kuyangi na take musu baya.Da
isarsu cikin fadar kuwa sai suka iske gaba dayan
fadawa a tsaitsaye a bayan KARAGAR
MULKI.Abokan tafiya kuwa
wato,MAWAKA,MAKADA,JARUMAI da masu
BARKWANCI na tsaitsaye a tsakiyar fadar suna
fuskantar karagar mulkin.Koda shigowarsu sai
yarima ya kurawa abokan tafiyar idanu yana
kallonsu daya bayan daya yana kokarin yaga
wadannan bakin tagwaye amma wayam.Ko
Alamarsu bai gani ba.Ashe shima sarki ya lura da
hakan.Abinda basu sani ba shine a yau tagwayen
basuyi shiga iri daya ba,kuma basa tare a waje
guda kuma ita macen bata rufe fuskarta ba,amma
tayi wata irin shiga ta batar da kamanninta.Su dai
wadanann tagwaye basu kasance yan kasar Misra
ba kuma ba komai ne yasa suka shiga wannan
tafiya ba sai domin su dauki fansa a kan sarki
Alkasim bisa mahaifinsu daya kashe akan wani laifi
daya aika bisa rashin sani a matsayinsa na
bako.Wannan abu ya faru ne kimanin shekaru
bakwai da suka gabata.Akwai wata shekara da
akayi fari na ruwan sha a birnin Misra saboda
gurbatar magudanar ruwan garin sakamakon wani
mugun boka da yazo ya lalata ruwan garin ya
zuba matattun tsuntsaye a cikin ruwan don
gabatar da aikinsa na sihiri.Nan take sarki Alkasim
yasa aka kamo bokan aka tsire shi a bainar
kasuwa kuma ka kafa dokar cewa duk mutumin da
aka sake gani yayi ta'ammali da magudanar ruwa
kisa ne hukuncinsa.Bayan shekara daya da faruwar
wannan abu ne wani matafiyi yazo giftawa ta bakin
magudanar ruwan birnin Misra tare da
iyalinsa,matarsa da 'ya'yansa guda biyu mace da
namiji wadanda shekarunsu sun kai goma sha
daidai.Koda wannan mutum tare da iyalansa
sukazo giftawa ta gefen wannan magudanr ruwa
sai santsi ya kwashi dawakansu suka fada cikin
wani tabo gaba dayansu duk jikinsu da jikin
dawakan ya turbune da tabo.Abinka da rashin sani
sai suka mike tsaye suka shiga cikin wannan
magudanar ruwa tare da dawakan nasu suka kama
wanke tabon jikin nasu.Suna cikin hakane dakaru
sukazo suka kewayesu aka kamasu aka kaisu fada
gaban sarki aka gurfanar dasu aka fadi laifinsu.A
wannan lokaci Yarima Kamsus na zaune daf da
sarki kuma shima baifi shekara goma sha daya ba
a duniya.Ba tare da sarki Alkasim yayi wani
bincike ba sai kawai yace aje a kashe wannan
mutum.Nan take yarima Kamsus ya kama rokon
sarki Alkasim akan ya yiwa mutumin afuwa amma
sai ya ki.Iyalin mutumin na kuka suna ihu gami da
rukunkume shi amma sai aka fincike shi daga
jikinsu da karfin tsiya.Suna ji suna gani aka tafi
dashi ana jansa a kasa har aka isa tsakiyar
kasuwa,anan aka bankare shi akayi masa KISAN
GILLAH.Anan ne matar mutumin da yayan nasa
sukayi ta rusa kuka kamar ba zasu daina ba amma
babu wanda ya tausaya musu.Yarima Kamsus ne
kadai ya tsaya a gabansu yana kallonsu cikin
matukar tausayawa har yana zubar da hawaye.A
lokacin ne uwar yaran ta dauke su suka kama
hanya suka fice daga cikin birnin amma kafin su
kule saida macen ta waigo ta kurawa Kamsus
idanu ita dashi duk suna zubar da hawaye.Idanun
wannan macen sune abinda yarima Kamsus yake
ta kokarin ya tuno amma ya kasa.Lokacin da sarki
Alkasim da Yarima Kamsus suka iso gaban
karagar mulki suka tsaya suka fuskanci jama'a sai
yarima yayu wuf ya yiwa sarki rada a kunne yace
akwai matsala yakai Abbana,banga wadannan
tagwayen ba biyu kuma lallai ya kamata mu san
ko su waye su kafin a fita daga cikin birnin nan
domin zasu iya zama daya daga cikin
makiyanmu.Koda jin haka sai sarki yayi murmushi
sannan yayiwa yarima rada a kunne yace to
waishin wa kake tsoro ne tsakanin MUTUM DA
ALJAN?
SHIN SU YARIMA KAMSUS ZASU GANO
WADANNAN TAGWAYE KAFIN A BAR BIRNIN
MISRA?
ME ZAI FARU A CIKIN WANNAN GAGARUMAR
TAFIYA DA ZA'AYI ZUWA BIRNIN SIN?
TSAKANIN SARKI MASARUL ANJANA DA SARKI
ALKASIM WAYE ZAI FIFITA AKAN WANI?
WACE CE ZATA ZAMO MASOYIYAR YARIMA
KAMSUS?
WADANNE ABUBUWAN AL'AJABI NE ZASU FARU A
BIRNIN SARKI MASARUL ANJANA?
Mu Hadu A MUTUM DA ALJAN Littafi Na Biyu (2)
Don Jin Cigaban Wannan Kasaitaccen Kayataccen
Labari.
Daga Mai Debe Muku Kewa A Koda Yaushe.
Abdul'Aziz Sani Madakin Gini
Suleiman Zidane Kd 09064179602
MUTUM DA ALJAN 1 By Abdul'aziz Sani M/Gini.txt
Displaying MUTUM DA ALJAN 1 By Abdul'aziz Sani M/Gini.txt.
★MUTUM DA ALJAN★!!!
Littafi Na Biyu (2).
Part [A] .
★A-Haleefah Physicist★.
LOKACIN DA YARIMA KAMSUS YAJI SARKI
ALKASIM YAYI MASA wannan tambaya yace
waishin me kake tsoro ne tsakanin MUTUM da
ALJAN?Hankalinsa ya dugunzuma ainun saboda
yasan cewa ko kadan sarki bazai damu da batun
wadannan tagwaye guda biyu ba.Shi kuwa ya san
cewa dan hakin daka raina shike tsoka ne maka
idanu.Duk da cewar Yarima Kamsus ya yarda da
jarumtakarsu,karfin damtsensu da iya yakinsu
gami
da karfin sihirinsu na tsafi yasan cewa makiyi
abin
tsoro ne tunda baka san nasa shirin ba da kuma
irin mugun tanadin daya dade yana yi a
kanka.Hakan ne yasa yarima Kamsus ya kudiri
niya
a cikin ransa cewa lallai shi bazai yi sakaci ba
wajen kula da rayuwarsa data mahaifin nasa
kuma
zai ci gaba da zuba ido har ya gano wadannan
tagwaye biyu da kuma dalilin daya sa suka shigo
cikin wannan tawaga wacce zata je birnin Dilhar
don amsa gayyatar sarki Masarul Anjana.Sarki
Alkasim ya fuskanci gaba dayan jama'ar dake
cikin
fadar cikin izza yana murmushi yace,yaku jama'ar
birnin Misra,kuyi sani cewa yanzu ne zamu kama
hanya mu durfafi birnin Dilhar don amsa gayyatar
sarki Masarul Anjana ba don muna tsoronsa ba
kamar yadda sauran sarakunan duniya ke
tsoronsa
kuma ba don muna neman wani abu ba a
wajensa,domin mu mawadata ne sai domin mu
nunawa duniya cewa karfinmu yakai kuma mun
isa
muyi gwagwarmaya da kowa walau MUTUM KO
ALJAN.Koda sarki Alkasim yazo nan a zancensa
sai fadar ta rude da shewa aka kama yiwa sarki
Alkasim jinjina gami da kirari akayi ta kodashi
yana ihu yana daga takobinsa sama.Shi kuwa
yarima Kamsus adaidai wannan lokaci nutsuwa
yayi ya kurawa gaba dayan abokan tafiyarsu
idanu
dake tsaitsaye a gabansu yana nazarin kowa
daya
bayan daya.Kwatsam sai ya hango wani JARUMI
a
cikin tsakiyar jama'ar ya sunkuyar da kansa
kasa.Har tsawon lokaci wannan jarumi bai dago
da
kansa sama ba ya kallo kowa,koda ganin haka
sai
yarima kamsus ya baro inda sarki ke tsaye ya
kutso cikin abokan tafiyar ya nufi inda wannan
jarumi yake amma kafin ya isa daidai inda
jarumin
yake sai ya neme shi kasa da sama ya rasa
tamkar
wanda ya latsa layar zana.Al'amarin da yayi
matukar girgiza yarima Kamsus kenan ya cigaba
da dube dube a cikin dandazon jama'ar.Kwatsam
kuma sai ya hango wannan macen tagwayen a
can
gefe daya,kafin ya isa inda take sai itama ta bace
bat!Nanfa hankalin yarima ya sake dugunzuma
ainun fiye da koyaushe don haka sai ya koma da
sauri izuwa inda sarki ke tsaye ya tsaya a
bayansa
yana muzurai da kalle kallen kowace kusurwa don
tabbatar da tsaro,ma'ana sai ya zamo mai tsaron
sarki na musamman.Nan dai sarki Alkasim ya
gama jawabi akan wannan gagarumar tafiya.Ba
tare
da bata wani lokaci ba aka janyo dawaka,rakuma
da alfadarori dauke da guzuri kowa ya haye bisa
abin hawansa.Sarki Alkasim tare da yarima
Kamsus da dakarunsa na musamman suka tsaya
a
baya,jarumai,makada,mawaka,masu barkwanci da
sauran masu baiwa iri iri sune suka wuce
gaba.Nanfa wannan tawaga ta fice daga cikin
birnin
Misra duu...Kai kace gaba dayan mutanen duniya
ne sukayi hijira saboda yawansu.Mata,yara da
tsofaffi kuwa sai sukayi tsaitsaye a kofar
gidajensu
sunayi musu bankwana gami da fatan dawowa
lafiya.Wasu ma saidai kaga suna kuka da bakin
cikin rabuwa da iyalansu saboda sun san cewa
basu da tabbacin isa birnin Sin a raye su dawo
gida.Kafin cikar wadansu dakikai masu yawa
wannan runduna tayi nisa ga barin cikin birnin
Misra ta nausa izuwa cikin daji.Saida aka shafe
sa'a bakwai ana ta kutsawa cikin daji ba tare da
an
fuskanci wata matsala ba,sannan sarki Alkasim
ya
bayar da umarnin a tsaya a yada zango domin a
huta kuma a ci abinci.Nan take kuwa aka tsaya
aka
kafa tantuna.Ana cikin wannan aiki ne shugaban
dakarun sarki Alkasim wanda ake kira da suna
Uzaila bin Kaidas ya dubi gaba dayan abokan
tafiyar yace yaku yan uwa kuyi sani cewa yarima
ya bayar da umarnin cewa yana son duk sa'adda
muka yada zango mu rabu izuwa kaso biyar,kaso
na farko shine taron jarumai,saina
mawaka,makada,barkwanci da kuma masu
sauran
abubuwan baiwa.Wanda duk yaki sanya kansa a
cikin daya daga cikin wadannan rukunai zai
fuskanci horo da bincike.Koda Uzaila yazo nan a
jawabinsa sai sarki Alkasim ya kamu da farin ciki
kuma yayi mamakin irin wannan hikima ta yarima
saboda indai akayi hakan dole ne a gano makiyan
da suke shigo cikin wannan AYARI.
Hakika masu iya magana sunyi gaskiya da
sukace
maso abinka ya fika dabara.Ashe tun daga
lokacin
da sarki Alkasim ya bayar da umarnin a yada
zango sai wadannan tagwaye guda biyu suka
bace
bat daga cikin ayarin su da dawakansu tamkar
basu taba bayyana ba saboda karfin sihiri da
tsafi.Bayan batan nasu ne suka bayyana a can
baya kadan cikin wata duhuwa.Nan take suka
sauko daga kan dawakansu suka zauna a kasa
dirshan suna masu yin tagumi cikin alamun
takaici
da damuwa.Tsawon yan dakiku dayansu baice
uffan ba sannan namijin yayi gyaran murya ya
dubi
macen yace yake NAMRITA yanzu yaya zamuyi
kenan?Yarima Kamsus yana ta hanamu samun
damar kashe mahaifinsa.In badon yana bashi
kariya ba da tuni mun gama daukar fansar
mahaifinmu.Wannan dabarar daya fito da ita a
yanzu ta ware rukunai biyar a cikin ayarin
wannan
tafiya saita tona mana asiri,saidai mu hakura da
batun cigaba da tafiya a cikinsu in yaso mu fara
tunanin kai masa HARIN BAZATO.Koda jin
wannan
batu sai Namrita tayi kwafa cikin matsanancin
bakin ciki tace ai idan anason asha zuma dole sai
an kawar da uwarta.Kawai mu fara kashe Yarima
tunda shine kadai yake hanamu cika babban
burinmu.Sa'adda Jarumi Zaihas yaji wannan batu
na 'yar'uwarsa Jaruma Namrita sai ya
★Abubakar Haleefah Physicist★
dubeta a fusace yana mai daka mata tsawa yace
yanzu ashe har kin manta kenan da wasiyyar da
mahaifiyarmu ta bar mana cewar kada mu
kuskura
mu ce zamu taba lafiyar 'da saboda kiyayyarmu
akan ubansa.Burinmu shine kamar yadda ya
maishemi marayu shima dan nasa ya zama
maraya.Ki tuna cewa a lokacin da sarki Alkasim
ya
kashe mahaifinmu yarima Kamsus bai so hakan
ba
harma saida ya zubar da hawaye saboda
tausayinmu.Ke da kanki kinga zubar hawayensa
kamar yadda kika sha jaddada mini.Akan wane
dalili yanzu zaki ce mu kashe yarima?Namrita
najin
wannan batu sai tayi tsaki tace aini idan bana
son
uwa dole ne naki yayanta.Bana son sarki Alkasim
don haka babu yadda za'ayi nason jininsa.Na
yarda cewa Kamsus bashi da wani laifi kuma
tabbas ya tausaya mana a lokacin da aka
zaluncemu aka kashe mana mahaifinmu,to amma
ka tuna fa cewa yau shekara bakwai kenan muna
baiwa kanmu horon yaki domin daukar wannan
fansa kawai.a tsawon wadannan shekaru munyi
yawo a duniya izuwa kasashe tara kuma munsha
bakar wahala kafin mu sami sirrikan tsafin da
muka samu tamkar zamu rasa rayukanmu.Shi
kenan yanzu saboda mutum daya sai mu bari
shirinmu na shekara bakwai ya tarwatse a
banza?
Ka sani cewa komai zanyi sai nayi shi muddin
zan
sami nasarar kashe sarki Alkasim koda kuwa zata
kama cewa sai na kashe gaba dayan mutanen
birnin Misra bawai yarima shi kadai ba.Lokacin
da
jaruma Namrita tazo nan a jawabinta sai hankalin
dan uwanta Jarumi Zaihas ya dugunzuma yayi
shiru yana nazari da tunani saboda yasan cewa
tafi
zafi kuma batayin magana biyu.Daga can sai ya
dafa kafadunta da hannayensa biyu ya dubi cikin
idanunta a lokacin da nasa idanun suka ciko da
kwalla,yace yake yar uwata kin sani cewa a
shirye
nake na rasa rayuwata muddin wannan buri
namu
zai cika,amma ki sani cewa wannan sarki da
muke
son kashewa ba kanwar lasa bane,ba'a taba
samun
makiyin da ya sami nasara a kansa ba.Ansha kai
masa hari sau ba adadi babu sa'a kuma komai
yawan rundunar dakarun sumame basa iyawa
dashi kadai,bare mu da muka kasance mu biyu
rak.Ki tuna cewa duk shirinmu muna son mu
kashe shine ta hanyar KISSA da SHAMMATA
domin
babu yadda za'ayi mu sami damar yin GABA DA
GABA dashi.Ni a tawa shawarar shine mu jarraba
kai masa harin bazato koda zai kai sau biyu ne
ko
sau uku.Idan ba muyi nasara ba sai mu fito muyi
gaba da gaba dashi idan yaso ayi ta takare ko
mu
ko shi,tunda dai bamu san iyakar karfinsa da
shirinsa ba shima kuma bai san namu ba.Sa'adda
Zaihas yazo nan a jawabinsa sai jikin Namrita
yayi
dan sanyi ta sunkuyar da kanta kasa daga can
kuma sai ta dago kan ta dubeshi a cikin
murmushi
tace yau dai a karon farko kayi galaba a kaina na
amince da wannan shawara taka amma lallai ka
hanzarta tunanin irin harin da zamu fara kaiwa
Sarki Alkasim da kuma lokacin da zamu kai harin
sannan ka tabbatar da cewar ba zamuyi kuskure
ba kuma babu ta yadda zai iya tsallake
sharrinmu.Dajin haka sai murna ta kamu Zaihas
ya
rungume Namrita yana mai cewa lallai a cikin
wannan dare na yau zamu kai masa wannan hari
kuma ina mai tabbatar miki da cewa babu yadda
zaiyi ya iya tsira da rayuwarsa.Koda jin haka sai
itama Namrita ta kamu da tsananin farin
ciki.Wannan shine abinda ya faru tsakanin
Jaruma
Namrita da dan'uwanta jarumi Zaihas tagwayen
da
suke shafe shekara bakwai suna tarkon Sarki
Alkasim domin daukar fansar ran mahaifinsu.
*A Can Sansanin Su Sarki Alkasim Kuwa Kamar
Yadda Yarima Kamsus ya bayar da umarni haka
al'amarin ya kasance wato saida aka raba gaba
dayan abokan tafiyar izuwa rukuni biyar,dakarun
sarki da hadimansa ne kadai ba'a tarwatsa su ba
ya zamana cewa duk suna cikin harabar da tantin
sarki yake.Nan take aka sa dakaru suka kewaye
sansanin gaba dayansa don tabbatar da tsaro.Kai
bama sansanin ba har gaba da bayan dajin
kimanin tafiyar zango ashirin-ashirn saida aka
baza dakarun leken asiri kwararo domin su lura
da
dukkan mostin wani abu mai rai wanda ka iya
kawo harin bazato.Bayan an gama dukkan
wannan
shiri ne sai Yarima Kamsus ya fara shigowa cikin
rukunan biyar daya bayan daya yana karewa
abokan tafiyar kallo.Bayan ya gama duba kowa
ne
rukuni sai kansa ya daure ya kamu da tsananin
mamaki domin baiga tagwayen nan ba kuma duk
binciken da yayi babu wanda ma ya taba ganinsa
a
cikin wannan tawaga bare yaga sa'adda suka
sulale suka gudu.Babu takun sawayensu kona
dawakansu.Wannan ce tasa yarima Kamsus yaji
a
jikinsa cewa lallai wadannan bakin tagwaye ba
karamin shiri ne dasu ba don haka sun tabbata
abin tsoro duk da cewa kuwa shi sarki baya
shakkar kowa.Shi dai Yarima Kamsus a koda
yaushe a cikin zuciyarsa baya raina
makiyi,sannan
kuma duk irin baiwar da yake da ita ta
jarumtaka,sa'a da kuma karfin damtse dana sihiri
yana sawa a cikin ransa cewa za'a iya samun
mahalukin da yafishi duk wadannan abubuwa
sabanin sarki Alkasim wanda shi gani yake kamar
ma in duk duniya zasu taru a kansa shi kadai
baza'a iya samun nasara a kansa ba.Sarki
Alkasim
na zaune cikin tantinsa bisa shimfidarsa ta
alfarma,kuyangi na shayar dashi giya kuma suna
ciyar dashi abinci sai nishadinsa yake tayi kawai
tamkar babu wani abu dake damunsa a
duniya.Kwatsam sai ga Yarima Kamsus ya shigo
cikin tantin.Koda ganinsa sai kuyangin suka
watse
suka fice daga cikin tantin suka barsu su biyu
rak.Nan take Yarima Kamsus ya zauna daf da
sarki
Alkasim suka fuskanci juna sannan ya dubeshi a
cikin nutsuwa gami da gyaran murya yace yakai
Abbana yanzu a iya tunaninka akwai ABOKAN
GABArka wadanda zasu iya bin bayanka a cikin
wannan tafiya namu?Koda jin wannan tambaya
sai
Sarki Alkasim yayi shiru kuma ya daga kansa
sama yana tunani har izuwa.
★MUTUM DA ALJAN★!!!
Littafi Na Biyu (2)
Part B .
★A-Haleefah Physicist★.
KUMA YA DAGA KANSA YANA TUNANI har izuwa
tsawon yan dakiku daga can sai ya dubi Yarima
yayi murmushi yace yakai dana kayi sani cewa
sama da shekaru goma baya na firgita gaba
dayan
makiyana ya zamana cewa sun razana dani
ainun.Da yawansu na turmushe su na kau dasu
daga doron kasa,wasunsu kuwa hijira sukayi suka
bar kasashen su,suka bazama izuwa sassan
duniya nesa da inda nake.Ina mai tabbatar maka
da cewa na kashe sama da sarakai arba'in a
wannan lokaci,don haka ina da tabbacin cewa
babu
sauran irin makiyana a wannan nahiya tamu gaba
daya.Lokacin da sarki Alkasim yazo nan a
zancensa sai ya bushe da dariyar mugunta yace
haba yakai dana wai shin me kake shakka ne har
yanzu?Yanzu kai a tunaninka har akwai wani
mahaluki walau mutum ko aljan wanda zaiyi
gangancin farautar rayuwata alhalin yasan cewa
nine GUGUWAR ANNOBA mai baje birane kuma
nine KOGIN JINI mai shanye ALKARYA.Sa'adda
yarima Kamsus yaji wannan batu na mahaifinsa
sai
yayi ajiyar zuciya yace yakai Abbana ka yi sani
cewa wannan duniya tana da fadi,haka kuma
abubuwan cikinta yawa garesu kuma komai nisan
gari akwai wani a gabansa.Tabbas na yarda
cewa
kai ZARTO ne abin tsoro kuma kai tauraro ne
wanda ya haska duniya amma ka sani cewa
ZAMANI RIGA CE.Dole ne mai laya ya kiyayi MAI
ZAMANI.Kullum shekarunka tafiya sukeyi kuma
kullum ana samun sauyin al'amara na cigaba.A
halin yanzu a iya binciken da nayi na gano cewa
akwai makiyanka a cikin wannan tawaga
tamu,amma gashi ni da kai da dukkan dakarunmu
mun kasa gano ko su waye wadannan
makiya.Asalima mun kasa ganinsu a zahiri.Shin
ba
zaka iya tuno da makiyanka na karshe ba
wadanda
baka sami nasarar kawar dasu ba ko kuma akwai
wadanda kake zargin cewa nan gaba zasu iya
zama makiyanka?Koda sarki Alkasim yaji wannan
tambaya sai yayi shiru kuma ya nutsu sosai,nan
take ya fada cikin kogin tunani bisa abinda ya
faru
a baya.Bayan ya gama tunanin ne ya dubi yarima
Kamsus yace shin zaka iya tunowa da al'amarin
daya faru a birninmu kimanin shekaru bakwai
baya
sa'adda baka fi shekara goma sha daya ba a
duniya?Koda jin wannan tambaya sai zuciyar
yarima Kamsus ta buga da karfi.Sarki Alkasim ya
cigaba da cewa akwai watarana da wani bakon
boka ya sauka a birnin ya gurbata ruwan
shanmu,na kafa doka mai tsauri akan duk
mutumin
daya sake bata mana ruwan sha Hukuncin kisa
ne
a kansa.Bayan shekara guda da faruwar
al'amarin
ne wani bakon bafatake tare da matarsa da
'ya'yansa guda biyu tagwaye suka zo suka sake
gurbata mana wannan ruwan sha namu.Koda aka
gurfanar dasu a gabana sai nan take na yankewa
mutumin hukuncin kisa ba tare da nayi bincike
naji
dalilin laifinsa ba.Wannan shine kuskure na guda
daya jal a rayuwata wanda har kwanan gobe
nake
yin nadamar aikatashi saboda nayi amfani da
karfin mulkina ne don tsorata masu kawo wargi
na
tafka zalunci saboda wannan bakon bafatake
ba'a
kan laifi na hukunta shi ba.Yayi laifin ne bisa
tsautsayi da rashin sani.A iya tunani yayan
wannan
bafatake zasu iya girma su zama abokan gabata
tunda a gaban idanunsu nasa aka kashe mahaifin
nasu suna kuka da ihu suna rokona gafara.Bazan
taba mantawa ba a sannan saida kai ma ka roke
ni
akan nayiwa mahaifin nasu afuwa.Koda sarki
Alkasim yazo daidai nan a labarinsa sai nan take
yarima Kamsus ya tuno da lokacin da Jaruma
Namrita ta waigo tana kallonsa,sa'adda
mahaifiyarsu ta janyesu ita da dan uwanta
lokacin
da suke ficewa daga cikin birnin misra.Nan take
Kamsus ya gane cewa wadannan idanu daya gani
a shekaru bakwai baya sune ya sake gani a
yanzu
akan fuskar wannan macen tagwayen.Kawai sai
hawaye ya zubowa yarima Kamsus ya dubi sarki
Alkasim cikin alamun karayar zuciya yace tabbas
wadanann yayan bafatake sune ke biye damu a
cikin wannan tafiya tamu domin su dauki fansa a
kanka kuma ina ji a jikina cewa suna nan a kusa
kuma a koyaushe zasu iya kawo harin
bazato.Koda
jin wannan batu sai sarki Alkasim ya takarkare ya
bushe da mahaukaciyar dariya ta
mugunta.Al'amarin daya firgita gaba dayan
jama'ar
dake sansanin kenan har shugaban dakaru da
sauran yaransa suka rugo da gudu izuwa gaban
tantin sarki.Koda ganin haka sai sarki ya mike
tsaye ya fito daga cikin tantin ya dubi shugaban
dakaru Uzaila bin Kaidas yace dashi maza ka
janye
gaba dayan yaranka daga cikin sansanin nan da
wajensa bana bukatar daya daga cikinku ya sake
bani tsaro har sai na sake bukatarku da
kaina.Koda jin wannan batu sai hankalin kowa ya
dugunzuma musamman na yarima Kamsus don
haka sai ya dubi sarki cikin alamun matukar
kaduwa gami da firgici yace haba ya Abbana ai
wannan ba karamin ganganci bane kayi tamkar
ka
siyar da rayuwarka ne ga makiyanka.Sarki
Alkasim
ya dafa kafadar yarima yana maiyin murmushi a
gareshi yace yau ne zan nuna maka cewa bakin
rijiya ba wajen wasan yaro bane,kuma ni
MURUCIN
KAN DUTSE ne ban fito ba saida na shirya.Karo
dani sai DUBU TA TARU.Wadannan tagwaye guda
biyu na dade da saninsu kuma nasan da zuwansu
kasata a wannan lokaci.Macen Sunanta Namrita
shi
kuma namijin sunansa Zaihas.Saida suka shekara
bakwai suna yawo a duniya suna ziyartar manyan
bokaye da manyan jarumai suna koyon fada,yaki
da tsafi ba don komai ba sai domin su sami
nasarar daukar fansa a kaina.A yanzu haka suna
can gaba kadan cikin wani daji mai DUHUWA
wanda ake kira SURFAL wanda tazararmu dashi
bata wuce zira'i arba'in ba.A yau din nan idan
dare
ya raba zasu kawo mini harin bazato domin su
hallaka ni don haka nake son kowa ya kauce
daga
kan hanyarsu banda yarima domin mu biyu ne
kacal zamu iya tsira daga sharrinsu.Sa'adda sarki
Alkasim yazo nan a...
★Abubakar Haleefah Physicist★
Jawabinsa sai Uzaila ya risina yace an gama ya
shugabana.Nan take shugaban dakaru Uzaila ya
tattaro gaba dayan dakarun sarki ya tafi dasu
izuwa can gaban sansanin suka kafa nasu
sansanin.Suma ragowar gaba dayan abokan
tafiyar
sai suka bi su Uzaila ya zamana cewa saura
sarki
da yarima Kamsus kadai a cikin sansanin suna
kallon juna.Shidai Yarima Kamsus tsananin
mamaki ne yasashi yayi shiru kawai yana mai
kurawa sarki Idanu domin ya firgita da
al'amarinsa,bai taba zaton cewa yasan komai ba
haka akan wadannan makiya nasu.Kawai sai sarki
ya dubi Yarima yace kai kuma me ka tsaya kake
jira!Ai sai kabi sauran jama'ar kaima so nake a
barni ni kadai.Koda jin haka sai Yarima Kamsus
yayi wuf ya durkusa bisa guiwoyinsa ya kama
kafar
sarki yace ina mai rokonka daka barni naga
yadda
zata wakana tsakaninka da wadannan abokan
gaba.Koda jin haka sai sarki yayi shiru yana
tunani
sannan yace shi kenan na amince zan barka ka
tsaya tare dani amma bisa sharadi biyu.Kada ka
tayani yakar wadannan makiya nawa kuma kada
ka
karesu.Sa'adda Yarima Kamsus yaji wannan batu
sai hankalinsa ya dugunzuma ainun amma saiya
kudurce a cikin ransa cewa saiya zartar da
abinda
ke cikin ransa koda ransa zai baci daga baya don
haka sai ya dubi sarki cikin murmushi yace na
amince da wannan sharadi naka.Lokacin da dare
ya raba sai dajin gaba daya yayi tsit,ba'a jin
sautin
komai face na kadawar iska gami da kukan
kananan kwari da tsuntsaye.A wannan lokaci tuni
sarki Alkasim ya dade da fara yin bacci harda
munshari abinsa,shi kuwa Yarima Kamsus yana
zaune a gefe daya cikin tantin ya kurawa sarki
Idanu kawai yana mamakinsa yana mai cewa a
cikin ransa waishin sarki wane irin hatsabibin
mutum ne shi haka?Yaya shi da yasan cewa za'a
zo kashe a cikin wannan dare amma kuma saiya
kwanta ya kama bacci abinsa ba tare da fargabar
komai ba?Gama fadin hakan keda wuya sai kawai
yaji saman tantin nasu ya dare gida biyu.Kafin ya
daga kansa sama yaga abinda ke shirin faruwa
tuni
Jaruma Namrita da Jarumi Zaihas sun duro cikin
tantin sun kaiwa sarki Alkasim suka a ciki da
takubbansu.Cikin bakin zafin nama sarki Alkasim
ya doki kasa da tafin hannayensa yayi sama
tamkar da majajjawa aka janyeshi,sai takubban
nasu suka soke a cikin kasa suka lume.Kafin su
zaro takubban tuni sarki ya tale kafafunsa a
sama
ya doki kirazansu.Duk da karfin dukan kirjin nasu
da yayi basu fadi kasa ba amma saida sukayi
baya,nanfa aka kacame da azababben yaki mai
tsananin ban tsoro da al'ajabi.Duk wannan abu
dake faruwa Yarima Kamsus na zaune a inda
yake
ko motsawa baiyi ba kawai ya zubawa JARUMAN
UKU idanu yana kallon masifaffen yakin da sukeyi
na ban al'ajabi da ban tsoro.Saida aka shafe
kusan
rabin sa'a anayin wannan BAKIN ARTABU ba tare
da tagwayen biyu sun sami nasarar koda
kwarzanar jikin sarki Alkasim ba kuma tunda ka
fara gumurzun sarki Alkasim bai mayar da
martani
ba kawai kare kansa yakeyi fuskarsa cike da
murmushi tamkar wasa yakeyi ba yaki ba.Ashe so
yake kawai ya fahimci iyakar jarumtakar
wadannan
tagwaye.Koda yaga tagwayen biyu sun kasa yi
masa komai saiya daka tsalle sama ya luluka
sama yana katantanwa tamkar an murza dan
mazari,shi kansa yarima Kamsus bai taba ganin
irin wannan jarumtaka ba don haka bai san
sa'adda ya daga kansa sama ba yana kallon
IKON
ALLAH.Suma tagwayen biyu haka suka daga
kawunansu sama suna mamaki.Koda sukaga
sarki
Alkasim ya cigaba da lulukawa sama yana neman
kulewa a cikin gajimare sai suka dubi junansu
nan
take sukayi amfani da karfin sihirinsu na tsafi
suma
suka tashi sama kamar tsuntsaye suka bi bayan
sarki Alkasim da nufin su cimmasa.Kwatsam ba
zato ba tsammani sai ganin sarki Alkasim sukayi
daf dasu tamkar zukoshi akayi.Kafin dayansu yayi
wani yunkuri tuni sarki Alkasim ya gabza musu
wawan naushi akan kirazansu saboda karfin
naushin sai suka rikito kasa suna aman jini duk
su
biyun suka fado kasa tim suka baje a cikin wani
irin mugun hali mai kama da suma sun jirkitar
hankali.Kawai sai sarki Alkasim ya nufosu daga
saman yana mai saito cikin kowannensu da
tsanin
makami zai soke su.Koda Yarima Kamsus ya
kyallara idanu yayi arba da fuskar macen
tagwayen
a wannan lokaci yaga irin tsananin kyawun da
Allah ya bata wanda bai taba ganin irinsa ba
kuma
yaga cewa tabbas sarki kasheta zaiyi kuma ya
kashe dan uwanta sai ya zabura cikin bakin zafin
nama ya janyesu daga inda suke kwance tamkar
shaho

Please Login or Register in order to submit comment