Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daga cikinsa na bashi labari mai dadi
na ban dariya sai ga sarkin yaki ya shigo cikin tantin nasa
koda ganinsa sai kuyangin suka barsu su biyu
sarkin yaki ya risina ya kwashi gaisuwa sannan ya dauko wata
takarda daga cikin aljihunsa wacce akayi rubutu
akan ta da bakar tawada ya mika masa yace ya shugabana
wannan takarda na dauke da sunayan jarunamu guda arba in
wadanda sarki ya umarceni dana zabosu domin shiga gasar farautar daya ce
nau shirya mana a gobe da safe koda jin
wannan batu sai yarima ya karbi takardar da sauri ya fara dubawa inda ya fara yin arba da sunan sarki sannan nasa da na sarkin yaki
a can karshen sunayen kuma da yaga sunayen wadansu jarumai guda biyu wadanda ake kira RAMJUS DA HATYAN sai ya dago kai ya dubi sarkin yaki
cikin mamaki yace saboda me zaka sanya ramjus da hatyan a cikin wannan gasa alhalin suna jinyar raunikan da suka samu a yakin da sarki ya turasu watanni hudu da suka gabata??
Koda jin wannan tambaya sai sarkin yaki yayi murmushi sannan yace.
Ya shugabana ai duk sun samu lafiyarsu kuma kowannansu ya amsa min da bakinsa
cewar zai iya shiga wannan gasa ba kaga yadda ma suke farin ciki da yin wannan gasar ba
yayina yarima yaji wannan batu sai al amarin ya sake daure masa kai saboda shi dai a saninsa irin raunikan da ramjus da hatyan suka samu ana iya yin shekara guda ana jinyarsa
ya za ayi ace har sun warke a cikin watanni hudu kacal?? Kawai sai yarima ya kada kai ya dubi sarkin yaki yace to menene yanayin wannan gasar ina so naji yadda aka tsarata
sarkin yaki yayi gyaran murya sannan yace abinda na tsara shine gaba dayanmu mu arbain din zamu shiga cikin dajin
darul shamjul a kasa bisa kafafuwanmu mu yi farautar dabbar farko wacce mukayi arba da ita
.
.
Dokar gasar itace ba za a harbi dabbar ba ko kuma a sareta da makami
sai dai a kure mata gudu a kamota da karfin tsiya koda mutum
ya samu nasarar kamata shi kadai sauran jaruman
gasar zasu iya kwaceta daga hannunsa sai dai karfinsa da basirarsa da zafin namansa su kwaceshi
ya dawo da dabbar a hannunsa har izuwa nan sansanin namu shine ya tabbata ya lashe gasar
koda jin sarkin yaki yazo nan a zancensa
sai yarima kamsus yayi doguwar ajiyar zuciya sannan ya dubi sarkin yaki yayi masa dan guntun murmushi yace
tabbas ka iya shirya gasa mai matukar wahala aiko sarki da kansa sa ace zata iya bashi nasara a wannan gasa ba wai karfinsa da dabararsa ba
sai dai ka manta da abu guda a cikin gasar
cikin mamaki da doki sarkin yaki yadubi yarima yace menene abin da na manta dashi?
Yarima yace ka manta kace a cikin dokar gasar babu amfani da karfin sihirin tsafi hakanne kadai zai hana sarki dani lashe wannan gasar a saukake
yayinda sarkin yaki yaji wannan batu sai yayi murmushi yace tabbas kazo min da babbar shimfidarsa ya kishingida yace inka fita ka toromin kuyangina suci gaba da debe min kewa saboda bana zaton zan iya yin barci da wuri
sarkin yaki yace haba ya shugabana kai kuwa menene zai hanaka barcin alhalin baka daya daga cikin
masu tsoron wannan daji na darul shamjul?
Yarima yace kaga mai daki shi yasan inda yake yi masa yoyo tafi ka bani wuri dajin haka
sai sarkin yaki ya juyo da sauri ya fice
daga cikin tantinsa fitarsa ke da wuya sai ga kuyangin yarima sun dawo
nan dai sukaci gaba da debe masa kewa har saida suka ga barci ya saceshi sannan suka mike
tsaye suka fice suka tafi izuwa nasu tantin
suna tsegumi da gulma inda daya daga cikinsu ta dubi sauran tace
wai shin anya kuwa yarima lafiyayyen namiji ne ko da jin wannan tambaya sai sauran kuyangin biyu suka bushe da dariya sanna
guda tace kece bakuwa a cikinmu shi yasa baki san halayansa ba to ki sani
mu tare dashi muka taso tun kuruciya yarima bai damu da mata ba kuma bai taba yin soyayya ba mun sha yin barci
tare dashi mu kwana daki guda amma bai taba nuna sha awarsa akan
dayarmu ba akwai ranar da muka taba yi masa
irin wannan tambayar da kikayi mana yanzu
amsar da ya bamu itace ya daukarwa kansa
alkawari cewar ba zai taba sanin wata ya mace
ba face matar da ya aura
koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke wannan kuyanga ta jinjina kai tace ai kuwa duk
macen da ta auri yarima ta gama dace da samun babbar sa a domin ya tara baiwa mai yawa irin wacce mazaje da yawa basu da ita da wannan kami kuyangin suka rufe hirarsu
kowacce ta samu wuri ta kwanta suka kama barcinsu...
.
Nima kuma da wannan kalami nawa Guyson naji barci ya fara neman zuwa sbd haka nake cewa sai Allah ya kaimu Gobe zamu ci gaba
Amma kafinnan...
Nidinne dai
Al Amin Ahmed Misau
Guyson sunana kenan
MUTUM DA ALJAN
Littafi Na Uku (3)
Part C.
Author: Abdul aziz M Gini
Rubutawa : Al amin Ahmed Misau
Nickname: Guyson ko shagala
Contack me: 08064594218
Gargadi: Ban yarda wani yayi edit na wannan post ba ba tare da izinina ba..
.
Labari ya isowa Guyson cewa

da wannan kalami kuyangin suka rufe hirar tasu kowacce ta samu guri ta kwanta
suka koma barci abinsu,lokacin da gari yaw aye da sassafe bayan anyi kalaci
jama’a suka sake taruwa a bakin tantin sarki Alkasim inda aka jere jarumai talatin
da takwas wadanda zasuyi gasar farauta a cikin dajin darul samjul , a cikin wadannan
jarumai hard a sarkin yako, sauran jama ar tawaga kuwa sunyi dandazo a gefe
guda suna jiran fitowar sarki Alkasim ana ta kace nace kowa na fadin albarkacin
bakinsa akan wannan gagarumar gasa da za ayi wasu suna mamakine akan
daliin da yasa sarki ya shirya wannan gasa alhalin ana kan hanyar zuwa birni
n sarki masarul anjana , wasu kuwa suna mamakin yadda aka zabo ,mutum
arba’in kacal alhalin ga jarumai nan da yawa wadanda aka taho dasu dubunnan
don su nuna jarumtakarsu acan birnin sarki masarul anjana domin su burge
gimbiya zulfulaifa ko tayi dariya.Jim kadan sai ga sarki Alkasim tare da dansa yarima kamsus sun fito daga cikin tantinsu.
A wannan lokaci duk su biyun sunyi gagarumar shigar yaki mai matukar
kwarjini daban sha awa wadansu bakaken
rigunan fata matsatstsu masu gajeren
hannu suka sanya gami da dogon wando
shima na fata matsatstse gaba dayan
surar jikinsu ta bayyana a fili takalmin
da suka sanyama fata ne dogaye iya
guiwa masu madauri kowannansu ya rataya
zabgegiyar takobi a bayansa kuma ya
saba kwari a bayansa ga baka ruke a hannunsa.
Wohoho duk wanda yaga wannan da da
uba a wannan lokaci dole ne su burgeshi kuma
dolene su firgitashi saboda yasan cewa su
biyun kacal zasu iya tashin gari guda domin
da gani babu tambaya ansan kura zataci
mutum
Guyson nake magana sunana kenan dan misau
babban abin da zai fi burge mutum shine
yadda kamanninsu tsawonsu da kuma kaurin
jikinsu da surarsu ta zamo iri daya sak
tamkar tagwaye kawai a fuskane za a gane
banbancin shekarunsu
ba tare da bata wani lokaci ba sai sarkin
yaki ya risina ya gaida sarki da yarima kamsus
sannan ya dubi sauran jama ar tawagar
su ma yagaishesu nan take yayi jawabin
yadda za ayi wannan gasa da kuma dokokinta
koda jin hakan sai gaba dayan jama a suka
kama yiwa sarki Alkasim kirari gami da
jinjina ana cewa ai tabbas shine zai lashe
wannan gasa sun manta dani guyson a gefe
nan fa sarki alkasim yaji wani irin farin ciki
gami da girman kai ya shigeshi baisan
sa adda ya kama yin murmushi ba yana dagawa
jama a hannu
a dai dai wannan lokacine yarima kamsus
ya hango jarumi Ramjis da hatyan tsaye a gefe
daya cikin jaruman gasar suna kallon sarki
suna murmushi alamar cewa suna da ja akan
cewa babu tabbacin cewa shine zai lashe
wannan gasa fiye da shekaru ashirin da biyar
baya a birnin misra idan aka yi gasar farauta
ramjis ko hatyan ne daya daga cikinsu ke
lashe gasar saboda dama can sune 'ya'yan sarkin
mafarauta wato gado sukayi ba haye ba
ko sau daya sarki Alkasim ko yarima kamsus
dayansu bai taba shiga wannan gasa ba
don haka yau Al amarin ya zama sabo
ba a san yadda zata wakana ba
kawai sai
yarima kamsus ya baro inda sarki ke tsaye yazo
inda su ramjis ke tsaye ya dubi ramjis yace
tayaya kuka samu lafiyar jikinku da sauri haka
har kuka iya shiga wannan gasa? Koda
jin wannan tambaya sai ramjis da hatyan suka yi yar
dariya sannan ramjis ya dubi yarima cikin
murmushi yace tabbas ya kamata ace mun
samu wata bakwai zuwa takwas muna
jinyar jikinmu kafin mu sake fita yaki ko
farauta amma saboda an shigo fagenmu na
farauta dolene mu fito don kada a yi mana
gori ko kuma a kwace mana matsayinmu
da muka gada tun iyaye da kakanni
koda jin haka sai yarima ya gyada kai yace
gaskiya ne kun burgeni amma kuma kunyi
ganganci domin ko yaya aka fama wannan
rauni naku shi kena9 an dawo daku baya don
sai kun sake maimaita watannin da kuka shude
na warkewa
idan ba zaku damu ba ina son ku kwaye min
raunikan naku na gani
kafin yarima ya gama rufe bakinsa tuni
ramjis da hatyan sun janye kafar wandonsu
sai5a tabon manyan sara akan cinyoyinsu
shi ramjis akan cinyarsa ta hagu aka yi masa
wani lafcecen sara shi kuwa hatyan akan
kaurinsa ne na hagu
gashi dai duka raunukan an dinkesu kuma
saura kiris wajan ya gama kamewa amma
akwai alamun cewa idan aka fama ciwukan zasu
iya dawowa sababbi koda yarima yaga
wadannan raunuka sai ya cika da mamaki kuma
ya fara tunani a cikin ransa cewa abin fa da
yake zargi ba haka bane
ba wani abu yarima ke zargi ba face yana tunanin
cewa ramjis da hatyan basu bane ba a zahirin
suuka shiga wannan gasa jaruma namrita da dan uwanta
jarumi zaihas ne suka juye izuwa kamanninsu
to yanzu dai gashi ya duba da idanunsa yaga
kuma basu bane domin ida sune din da dole
ne ya ganesu saboda wannan rauni da suka
samu tsawon watanni hudu da suka gabata
kafin yarima ya dubi su ramjis ya sake cewa wani abu sai sukaji an busa
kahon tafiya farauta sarki Alkasim ne ya fara
wucewa gaba yana sauri sauri gudu gudu
ai kuwa sai yarima ya ruga gareshi ya take
masa baya koda ganin haka sai ramjis da hatyan
ma suka bisu da sauri....
Sannan sarkin yaki da sauran jaruman
gasar mutum talatin da shida, duk wanda
ya dubi wadannan jarumai arba in a lokacin
da suka durfafi dajin Darul Samjul yaga irin
surarsu kwarjininsu da kuma makaman yakin
dake jikinsu sai yayi zaton cewa zasu iya
hallaka gaba dayan mugayan halittun dake
cikin dajin to amma fa ga wanda yasan dajin
kuma yasan irin mugayen abubuwan hadarin dake
cikinsa yasan cewa ba zasu iya ba da shigarsu
sarki Alkasim farkon dajin Darul samjul sai
kowannansu ya nutsu hatta shi kansa sarki
Alkasim kuwa domin shine ma ya fara rage
karfin gudunsa yana nazarin gefe da gefensa
da kuma gabansa saboda tunanin cewa ko
yaushe wani mugun abun zai iya kawo musu
hari, nan da nan kuwa kowa yayi koyi dashi
domin baiwa kai kariya
dajin yayi tsit a cikin safiyar ba a jin sautin
komai face na kananan kwari da tsuntsaye
komai jarumtakar mutum gami da dakewar
zuciyarsa idan ya shigo cikin wannan daji
na darul samjul dole ne zuciyarsa tayi rawa
saboda yanayin hatta bishiyoyi da irin
duwatsun dake cikin dajin wadansu iri ne
na musamman wadanda idanu basu saba gani ba
sai da su sarki Alkasim suka shafe kusan rabin
sa a suna tafiya a cikin dajin ba tare da sun ga
wata dabba ko guda daya ba face kwari
irin su kunamai, macizai da sauransu dai
Al amarin da ya sa kowa ya fara kosawa kenan
har aka fara tunanin cewa anya kuwa wannan
gasar zata yiwu?
Watakila sai dai a fasa gudanar da gasar a
koma da baya zuwa can sansani tunda
gashi lokaci na tafiya ba a hadu da wata dabba
ko guda daya ba
A cikin wannan hali ne kwatsam aka hango
wata irin dabba ta musamman ta tunkaro
tun da sarki Alkasim yazo duniya bai taba
ganin irin wannan dabba ba bare kuma
sauran jaruman wadanda shekarunsu sun
gaza nasa dabbar tana yanayi da zaki amma
tafi zaki tudu da fadi kuma tana da gajeren
kahonni guda biyu a tsakiyar kanta masu
kauri da tsini, kirjinta a cike yake da gashi
mai tsawo har yana sharar kasa
a kofatun hannayanta da kafafunta akwai
zarazaran farata masu kaifin tsiya saboda
nauyinta idan tana tafiya sai kaji kasa na
rawa tamkar takun toron giwa da farkon
sa adda dabbar tayi arba dasu sarki Alkasim
sai taci gaba da tunkarosu ba tare da shakkar
komai ba amma da taga cewa suma kara
tunkarota suke babu shakkar komai sai ta tsaya
cak ta zuba musu idanu aka fara kallon kallo''
chai kaji manyan jarumai masu dakakkiyar
zuciyar yaki ehm nidai guyson wajan yaki
bana nan sbd haka bari na matsa gefe
Wohoho idan maza da maza suka hadu a
sannan ne ake sanin waye jarumi kuma waye
matsoraci tabbas dasu sarki Alkasim din
da kuma wannan dabbar kowa ya sha jinin
jikinsa yasan cewa ya gamu da gamonsa idan
ka dauke sarki Alkasim da yarima kamsus
,ramjis da hatyan gaba dayan sauran jaruman
a firgice suke tunda akayi arba da wannan dabbar
domin kowannansu da kyar yake iya daga
sawayansa yana ci gaba da takun kafafunsa
haka dai su sarki Alkasim suka ci gaba da
durfafar wannan dabba ita kuwa tana tsaye
kyam a inda take tana kallonsu kawai ko
motsi batayi. Koda dabbar taga cewa saura
baifi taku goma ba kacal a tsakaninsu sai ta
yunkura cikin bakin zafin nama ta juya da
baya ta falfala da azababben gudu na kwatance
nan mafa su sarki Alkasim suka bita aka
kasa mugun tsere hakika masu iya magana sunyi
gaskiya da sukace ba a sanin maci tuwo sai
miya ta kare.
Ana fara yin wannan azababben gudu ne aka
fara barin jaruman gasar a baya domin gudu
ne na kare iyawarka ko nace kare kukanka, Al amin Ahmed Misau Guyson
Sunana kenan shugaban zauran labarai page
sai da aka shafe sa a uku ana falfala gudu ga
dabbar a gabansu suna hangota itama tana
waigensu tana ganinsu amma sun kasa
cimmata ita kuma ta kasa bace musu da gani
A wannan lokaci gaba dayan jaruman gasar sun
sare sun zube kasa suna haki kamar ransu
zai fita saura mutum hudu kacal biye da
dabbar basu sare ba saboda bakin nacinsu da
juriyarsu
ba wadansu bane ba wadannan mutane hudu
face sarki Alkasim , yarima kamsus,
ramjus da hatyan saikuma guyson me rubuta labarin
duk sa adda sarki Alkasim ya waigo bayansa
yaga yarima dasu ramjis da hatyan na biye
dashi basu sare ba sai ya cika da mamaki
domin shi a zatonsa ba zasu iya kawowa
haka ba suna wannan tseren gudu alhaliin
dukkaninsu babu wanda ya ke amfani da karfin
sihirin tsafinsa, kawai suna amfani ne da
tsagwaron horon da suka samu na gado
dakuma juriya da jarumtaka Abu dai kamar wasa
har saida yarima dasu ramjis suka hada
kafada da sarki amma an rasa mutum daya
da a cikinsu wanda zai iya cafke wannan dabba
a wannan lokaci tazarar dake tsakaninsu da dabbar
bai wuce taku biyar ba babban abinda ya
dugunzuma hankalinsu shine ko kadan babu
alamar gajiyawa a wajan dabbar su kuwa
dukkaninsu sun fara gajiya da yin haki
alamar cewa nan da wani lokaci zasu iya
sarewa ko da suka fahimci hakan sai dukkaninsu
a lokaci guda suka daka tsalle sama suka
diro akan dabbar kowa ya kai mata cafka
kaico bala'i ba a sa masa rana kuma ita masifa
ba a san farkonta ba bare karshenta koda
wannan dabba taji an cafketa ta gaba da bayanta
sai ta fara kokarin kubuta nan fa aka
ruguntsuma da azababben fada atsakaninta
dasu sarki Alkasim ta rinka kai musu suka
da kahonninta cizo da hakoranta gami da
yakushi da faratanta da kafafunta su kuma
suka rinka gocewa suna gabza mata wannan
naushi iya karfinsu amma sai gashi tana
shanye dukan nasu tana makesu suna faduwa
kasa amma sai dai kaga sun mike zumbur
cikin bakin zafin nama gami da jarumtaka
a iya gwagwarmayar da wadannan jarumai
hudu sukayi a duniya basu taba haduwa da
dabba mai karfin wannan ba domin duk sa adda
.ta dako tsalle ta kawowa dayansu bangaza
da kirjinta idan ya goce duk abinda ta
doka da kirjin take yake ratattakewa ya
rugurguje ko da kuwa abin ya kasance
dutsene ko bishiya.
Ganin wannan al amarin yasa sarki da yarima
suka fusata ainun suka kara zage damtse
suna amfani da dukkan karfinsu akan
dabbar ramjis da hatyan kuwa sai suka
dan ja da baya suka zuba musu idanu suka
samu damar hutawa amma sai haki suke
ta faman yi kamar ba zasu iya ci gaba
dagumurzun ba
Lokacin da dabbar taga sarki da yarima naso
suyi mata illah saboda kai mata mugun naushi
da bugu suke ta ko ina har tana faduwa kasa
in ba don ma tana da mugun zafin nama ba da
tuni sun yi mata lugudan da zata kasa tashi
sai ta shammaci yarima kamsus ta doki gadon
bayansa da kanta
take yarima ya kurma uban ihu sakamakon
tsananin zafi da zugin da yaji kashin bayansa
ya karye sai gani aka yi ya kife kasa da ruf
da ciki
Koda ganin abinda ya sameshi sai sarki Alkasim
ya fusata ainun ya cafi makoshin dabbar da
hannayansa biyu ya kauta kasa ya danne kuma ya
shaketa iya karfinsa nan fa dabbar ta fara
kakarin mutuwa koda taji tabbas zata rasa
rayuwarta sai ta fara saran jikin sarki da
faratan hannayanta da kafafunta nan fa
jikin nasa ya rinka darewa jini na tsartuwa
sarki ya rinka kurma uban ihu saboda mugun
zafin da yake ji ga jiri na dibarsa amma saboda
bakin naci yaki yarda ya saki dabbar saboda
fusatar da yayi, abinda ya ayyana a ransa
kawai shine sai dai suyi ragas shi da wannan
dabbar tunda babu mamaki mugun dukan
da tayiwa dansa zai iya zama sanadin ajalinsa.
Lokacin da ramjis da hatyan suka ga halin da sarki
da yarima suka shiga sai suka kalli junansu
nan take suka daka tsalle a lokaci guda
suka kama wuyan dabbar da hannayansu a
sama suka murdeshi nan take dabbar ta
sulale kasa matacciya, shi ma sarki alkasim
ya fadi kasa a matukar galabaice jiri na dibansa
da jan jiki ya isa inda yarima yake kwance
ya mirgino fuskarsa sai yaga ashe da ransa amma ya kasa mikewa
ne saboda
mugun dukan da dabbar tayi masa a gadon baya
sarki yasa hannunsa ya shafi kasusuwan bayan
yarima sai yaji babu wanda ya karye tsabar
buguwace kawai tasa ya galabaita nan take
ya saki murmushin farin ciki...............
!
Nima kuma Guyson na saki murmushin
ajiye typing
ANAN NE KUMA LITTAFI NA UKU YAZO KARSGE
SAI MUN HADU A CIKIN LITTAFI NA HUDU DOMIN
JIN CIGABAN WANNAN KASAITACCEN LABARI
Mutum Da Aljan
Littafi Na Hudu (4)
Part A.

yan suka taho izuwa kan sarki Alkasim suka tsaya suka yi cirko cirko suna kallonsa kawai
.
Al amarin da yayi matukar bashi mamaki kenan ya dubesu a fusace ya daka musu tsawa yace menene zaku tsaya a kanmu haka kuna kallonmu kawai ba zaku taimaka mana ba mu mike tsaye mu koma can sansani ba !
.
Koda jin wannan batu sai ramjis da hatyan sukayi girgiza suka juye izuwa kamannin jarumi zaihas da jaruma namrita, cikin kaduwa sarki Alkasim ya mike tsaye zumbur jiri na dibarsa sakamakon jinin dake zuba a sassan jikinsa yayi wuf ya zare takobinsa ya fuskancesu yana mai gyara tsayuwarsa kawai sai yaga namrita ta kyalkyale da dariya
.
Lokaci guda kuma saita turbune fuskarta ta dubeshi a fusace tace ya za ayi mu yakeka kana cikin wannan mugun hali
ba zamu dauki fansa ba a kanka sai kana cikin koshin lafiyarka gami da jin izzarka
.
Ka sani cewa bamu shiga wannan gasa ba domin mu samu damar da zamu hallaka ka ba sai domin mu nuna maka cewa dan hakin da ka raina shike tsone maka idanu ka sani komai karfinka komai mulkinka zaka iya faduwa kasa a ko yaushe saboda ita wannan duniyar fadi gareta kuma abin cikinta yawa gareshi
.
Babuwanda yasan iyakarsa ka tsaya kayi tunani wannan fa dabbace kawai ta galabaitar da kai haka in ba don mun kawo maka dauki ba da sai dai kuyi ragas kai da ita
ka tuna fa cewa ko birnin sarki masarul anjana bamu isa ba inda za a tara gaba dayan jarumai da matsafan duniya
.
Kanka ka sani kawai amma baka san sauran mutanen duniya ba babu mamaki akwai wadanda suka fika da yawa amma kace idan muka sake kawo maka hari zaka kashemu to mu ma mun dauki alkawarin cewa ba zamu sake kawo maka hari ba har sai mun isa can birnin sarki masarul anjana ina mai tabbatar maka da cewa har abada ba zamu taba durkushewa ba a gabanka mu nemi gafararka ba face mun cika burinmu na kashe ka ka kashe mana mahaifinmu kuma mahaifiyarmu ta mutu a sanadiyyar ciwon zuciyar da ka dasa mata na ganin gawar mijinta
.
Ta yaya kake tsammanin zamu iya yafe maka har abada babu yafiya a tsakaninmu dakai
ga wannan dabbar sai ka dauka ka koma da ita can sansanin a matsayin kai
ne ka lashe wannan gasa sai ranar da zamu cika burinmu akanka sannan zamu
sake haduwa koda gama fadin hakan sai jaruma namrita da dan uwanta jarumi zaihas
suka bace bat daga wajen tamkar basu taba wanzuwa ba
a wannan lokaci zuciyar sarki alkasim ta kama tafarfasa kamar zata kone saboda tsananin bakin ciki don haka
bai san sa adda ya takarkare ba ya kurma uban ihu mai tsananin firgitarwa wanda
yasa gaba dayan halittun dake cikin dajin darul samjul suka firgice suka dimauce
babu shiri tsuntsaye suka kama tashi suna sauya sheka dabbobi kuwa da sauran
kananan kwari suka rinka shigewa cikin ramukansu suna buya
kai hatta halittun dake karkashin ruwa lambo sukayi suka ki tasowa izuwa saman ruwa
ashe duk wannan abu dake faruwa tun a farkon fara gumurzun da wannan katuwar dabba sai dabbar ta make sarkin yaki ya fadi kasa
kansa ya gwaru da wani dutse
take kan nasa ya dare jini yayi ta tsartuwa ya baje a kasa sumamme a wannan lokacine da sarki ya kurma uban ihu
sarkin yaki ya farfado daga dogon suman da yayi a firgice ya mike zaune ya dubi gabas da yamma kudu da arewa sannan
ya lura da sarki wanda ke tsaye a gabansa ruke da takobi jikinsa na kyarma ga jini na
yoyo a sassan jikinsa kuma ga gawar wannan dabba a gefe guda, shi kuma
yarima yana kwance a kas a gabansa ya kasa tashi , kawai sai yaji sarki ya daka masa tsawa yace maza ka dauki
yarima ka goyashi a bayanka ka ruga dashi izuwa can sansaninmu domin likitoci su dubaku
cikin hanzari sarkin yaki ya suri yarima ya goyashi a bayansa har ya juya zai tafi sai ya dubi
sarki yace ya shugabana tunda dao ka samu
nasarar kashe wannan dabba ai saika daukota mu tafi tare domin jama a su tabbatar da cewa kaine ka lashe wannan gasa
Al amin Ahmed Misau
guyson sunana kenan
daga page na 'zauran labarai'
sarki Alkasim ya gyada kai yace bani ne na kashe wannan dabba ba makiyanane suka kasheta zaihas da yar uwarsa namrita kuma sun juye
kamannin ramjis da hatyanne suka shigo wannan gasa maza kayi sauri ka kai yarima tantinsa zan jira isowarku a can
koda jin haka sai mamaki ya kama sarkin yaki amma sai yayi shiru bai kara cewa uffan ba ya runtuma da gudu izuwa hanyar da zata kaishi sansanin goye da yarima kamsus a bayansa
nan dai yayi ta gudu ba tsayawa kuma babu waiwaye yana isowa sansanin ya hango sarki zaune a kofar tantinsa bisa kujera likitansa na dinke raunukan jikinsa'
hm kunji aikin tsafi fa wai Guyson nake magana
a guje wadansu dakaru hudu suka taryi sarkin yaki suka karbi yarima suka shigar dashi cikin tantinsa suka kwantar dashi
nan da nan shima nasa likitan ya dukufa a kansa aka shafa masa wani irin magani
na musamman a gadon bayan nasa sauran jaruman gasa dai
Tuntuni daya bayan daya suka rinka dawowa sansanin tun sa adda suka sare
sakamakon azababben gudun tseren da akayi na kece raini ramjis da hatyan ne kadai ba a ga dawowarsu ba abinda ya kara daurewa
jama a kai shine sarki ya dawo dauke da raunuka a jikinsa kuma babu wata dabba a hannunsa shi kuma
yarima an kawoshi a matukar galabaice to wai shin menene yake faruwa ne haka amsar da aka rasa wanda
zai iya bayar da ita kenan
shi dai sarki alkasim tunda ya dawo daga dajin darul samjul baice uffan ba kuma baiyi magana da kowa ba har aka gama dinke raunukan jikinsa aka shafa masa magani
kawai sai akaga ya shige cikin tantinsa yaje ya kwanta gaba dayan
hadiman ma korarsu yayi daga cikin tantinsa kuma yaki ci da shan komai saboda bakin ciki abu na farko
da ya fara tunowa shine maganganun da jaruma namrita ta gaya masa na batun ya kashe mahaifinsu kuma
mahaifiyarsu ta mutu a sanadiyyar bakin cikin mutuwar mijinta abu na biyu kuma shine batun cewa ya daina tunanin cewa yafi kowa karfi
isa da iko domin za a iya samun wadanda suka fishi a cikin wannan duniya mai fadi
idan kuwa hakane ashe ya dade a cikin jahilci irin na iyayensa da kakanninsa wadanda suka tabbatar masa da cewa zai iya ja da kowa a wannan duniya walau mutum ko Aljan
idan maganarsu gaskiyace to ya ya akayi dabbba ma ta gagareshi har ya zamana cewa ta yi kusan hallakashi yanzu a haka ne zai iya zuwa ya tari sarki masarul anjana sarkin da dukkan aljanu da mutanen duniya ke tsoronsa da shakkarsa
koda sarki alkasim yazo nan

Please Login or Register in order to submit comment