You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
farin ciki sannan
ya dubeshi cikin nutsuwa yace ina alfahari dakai ya
abbana ba don komai ba sai saboda kai mutunne
mai ki -fadi!
A iya sanina tun tasowata daga kuruciyata kawo i
yanzu baka taba fadin abinda bai faru ba don haka nayi
imani akan cewa sai hakan ta faru idan kuma hakan
bata faru ba to wani babban abin al ajabi zai biyo baya
ni yanzu abinda nake so dakai shine ka taimaka ka
karasa mini wancan labari naka lallai ina so naji yadda
karshen gasarku zai kasance kuma ina son na san matsayin
jaruma luslaiya da na mahaifiyata ta gida lokacin
da yarima kamsus yazo nan a zancensa sai sarki
alkasim ya sunkui da kansa kas jikinsa yayi sanyi
tamkar an zare dukkan lakar jikinsa daga can kuma
sai ya dago kai ya dubi yarima kamsus a lokacin da
idanunsa suka ciko da kwalla ya dafa kafadarsa yace
yakai dana ba komai ne yasa kaga ina ta ja maka rai ba
akan wannan labari ba face na tsani tuno da baya
kuma na tsani duk abinda zai sakani zubar da hawaye
saboda zubar hawayen jarumi babbar illace a cikin
jarumtakarsa da nasararsa koda kuwa yafi kowa karfi da sa'a
yanzu take zan yi kokari in gama baka wannan labari amma
ka nutsu sosai ka fahimci babban darasin dake cikinsa
saboda bana son ka aikata irin kuskuren dana aikata
a rayuwata
ka sani cewa wani lokaci yana da kyau mutum ya hakura
da son zuciyarsa don gudun bacin zuciyar a gaba ''
koda sarki Alkasim yazo nan a jawabinsa sai yayi
doguwar ajiyar zuciya sannan yaci gaba da baiwa yarima
kamsus labari kamar haka...
++ +++ ++++ +++++++++++
'''LOKACIN DA JARUMA LUSLAIYA taji na ce sai dai mu
fita tare daga cikin wannan rami mai mugun zurfi, kuma
akan igiyarta sai hankalinta ya dugunzuma ainun ta
yi shiru tana kallona kawai ta kasa cewa komai ashe tunanin
hanyar da zata cutar dani take yi kawai sai tayi wuf !
Ta kama igiyar tata da nufin ta fara hawa amma sai nima
na kama igiyar na tsaida ita nace nine zan fara hawa
Da jin haka sai nayi murmushi nace Abinda yasa nace
nine zan fara hawa shine idan muka yi nisa a lokacin
da muka jigata zaki iya cutar dani ki dokoni kasa tunda
kina samana
Al amin Ahmed Misau
Guyson ko shagala
sunana kenan
daga zauran Labarai
cikin fishi luslaiya tace to mene ne tabbacin cewa kaima ba
zakayi min haka ba? Nayi murmushi nace ai ni
kin san cewa na kamu da tsananin sonki kuma na ceci
rayuwarki a baya don haka babu yadda za ayi nayi wani
yunkuri na hallakaki duk da cewa ke kin tsaneni fiye
da yadda kika tsani mutuwarki, luslaiya ta dubeni a
fusace tace, wannan imaninka kenan ba nawa ba
A rayuwata ban da iyayena da suka haifeni ban taba
yarda da kowa ba
ba zan taba yarda da cewar ka fara hawa kan wannan
igiya ba saidai mu ci gaba da yaki anan har dayanmu ya
sami nasarar kashe daya kayi sani cewa ban dawo nan
cikin wannan rami domin komaiba sai somin na yanke kanka na tafi da
shi izuwa ga mahaifina domin ya tabbatar da cewar
munyi wannan gasa kuma na sami nasara a kanka
koda jin wannan batu na luslaiya saina bushe da dariya sannan na dubeta
ina mai murtuke fuskata kuma na daka mata tsawa
duk da cewa luslaiya bata san tsoro ba saida naga alamun
razana akan fuskarta
take na gamsu cewa lallai namiji yana gaba da mace
komai karfinta da isarta kuwa....
.
Bari na dakata anan nima sbd wannan tsawa da sarki Alkasim yayi na firgita na kasa ci gaba..
Al amin Ahmed Misau
Guyson sunana kenan
Mutum Da Aljan
Littafi Na Shida (6)
Part A.
.
Al amin Ahmed Misau
.
post:Abubakar Ahmad # Adon_masoya
Labari ya isowa guyson cewa...
.
Lokacin da sarki Alkasim yaji tambayar da yarima
kamsus yayi masa sai yayi murmushi yace
ni kuwa dadina dakai gajen hakuri ai a cikin
kankanin lokaci zan gama baka wannan labari
kuma zaka sha mamaki idan kaji yadda karshen
gasarmu yake kasancewa
ni kaina yanzu bana son na tsaya akan
wannan labari da nake baka face na je karshensa
ko muna kan hanyane zan cigaba da bakashi
yanzu dai tunda mun kammala cin abincin zaifi
kyau mu tashi mu kimtsa tunda mu kadai ake jira
ba tare da wata gardama ba sai yarima kamsus
ya mike tsaye
nan da nan shida sarki suka gama kimtsawa suka
hau bisa dawakansu suka jagoranci dubunnan daruruwan jama'ar dake
cikin wannan tawaga tasu suka durfafi
hanyar da zata kaisu birnin sarki masarul
anjana
ana fara wannan tafiya sai yarima kamsus
ya jera da sarkin yaki ya ki yarda wani abu ya
shiga tsakaninsu
burinsa kawai shine sarki ya cigaba da bashi
wannan labari na gasarsa da jaruma luslaiya
bisa mamaki sai yaji sarki yayi shiru har ya zamana
cewa tafiyar tasu ta fara dan nisa don haka
takai tsawon rabin sa'a
Al'amarin da ya jefa yarima cikin tsananin
damuwa kenan yayi kamar ya yiwa sarki
magana amma sai yayi shiru A dai dai wannan
lokaci ne suka iso wani kauye na Aljanu dake
cikin nahiyar kasar sarki Masarul Anjana
nan fa gaba dayan jama'ar dake cikin tawagar
suka cika da tsananin mamaki dukkaninsu suka
zama kamar 'yan kauye domin basu san sa adda
suka wangame bakunansu ba suka kama
kalle kalle saboda gani sukayi kamar mafarki
sukeyi ba a zahiri suke ba
gaba dayan gidajen dake wannan kauye sunkai kimanin
guda dubu uku da doriya kuma dukkaninsu iri
dayane kuma an ginasu ne da tubalin zinare
ko ina a cikin kauyen babu inda mutum zaiga
wata kazanta an shimfide ko ina da dutsen jauhar
Abinda yafi daurewa kowa kai shine babu
kura ko wata iska mai karfi dazata dami mutum a garin
face wani irin yanayi mai dadin gaske wanda babu
zafi kuma babu sanyi
irin wannan yanayine yake sawa fatar jikin
mutum ta rinka sheki laushi da haske tamkar jariri
gaba dayan Al'ummar wannan kauye suna
ta kai kawo suna tafiyar da harkokinsu babu wanda ya kula su sarki Alkasim
sai dai kaga suna ratsawa ta cikin jikkunansu
suna wucewa abinsu
Al amin Ahmed Misau
Guyson sunana kenan
daga zauran Labarai.
Sarki Alkasim bai san sa'adda ya ja linzamin dokinsa
ba ya tsaya a kofar wani katafaren gida mafi
girma da kawatuwa a garin kai da gani kasan cewa
wannan gida mallakar shugaban kauyen ne koda
ganin tsayuwar sarki sai kowa ma ya tsaya faruwar
hakan keda wuya saiga wani narkeken Aljani
ya fito daga cikin wannan gida a cikin shiga
irin ta masu mulki, fadawansa a biye dashi,
da isowarsa daf da sarki Alkasim sai ya risina
kamar zaiyi masa sujjada sannan ya dago
kai ya dubeshi yace '' Lale marhaban da
sadaukin sadaukai , sarki Alkasim na birnin
misra
inayi maka barka da zuwa kauyen LAUSAS
sunana DAMZURUL MASWAD nine shugaban
mazauna wannan kauye na lusas
daga nan
zuwa babban birnin kasarmu wato DILHAR inda maigirma Sarki masarul Anjana
yake tafiyace ta kwana goma sha uku kacal
Kayi sani cewa sarakunanku na bil adama
guda dubu dari takwas da saba in da ukune
suka rigaka isa fadar sarkinmu kuma akwai wasu
da yawa a bayanka
idan kana so zaka iya hutawa a cikin garina
har tsawona Sa'a uku sannan kuci gaba da
yin tafiyarku koda shugaba damzurul maswad yazo nan a jawabinsa sai
fuskarsarki Alkasim ta fadada da murmushi
yace zanyi farin ciki da hakan
nan take wasu hadiman Aljanu suda yawa
suka baiyana tsulum ! Suka kamawa kowa abin hawansa aka sauka
nan dai aka tafi da ababan hawan izuwa wani
wuri daban sannan aka wangame katuwar kofar wannan babban gida take
shugaban damzurul Maswad da fadawansa
suka yiwa su sarki Alkasim jagora izuwa cikin
gidan
saboda zurfin wannan gida da fadinsa da kuma
kayan kawar da aka shirya masa hatta sarki
Alkasim da yarima kamsus dimaucewa sukayi
suka zama cikakkun 'yan kauye cikin kankanin lokaci aka kai kowa masaukinsa
kuma aka basu abinci da abin sha nasu na biladama
kuma na alfarma harda irin wanda shima kansa
sarki Alkasim bai taba dandanarsa ba
Abin da yafi baiwa kowa mamaki shine ganin
yadda a cikin dakiku kadan aka kai dukkan
tawagar izuwa cikin dakunansu kuma mutum
bibbiyu aka rinka hadasu
wadansu kyawawan yan matan Aljanu ne wadanda
kamar su sukayi kansu
don kyau suka rinka yi musu hidima
da yawa daga cikin mutanan wannan tawaga ta sarki Alkasim basu san
sa adda suka kama sambatu ba suna cewa
aisu inda sun san cewa akwai irin wannan
aljannar duniya da tuni sun baro komai da kowa
nasu sun dawo wannan gari da zama koda
kuwa zasu yi aikin bautane a cikinsa wasu
kuwa sai suka kama kuka saboda bakin cikin
sanin cewa babu aure a tsakanin MUTUM DA ALJAN
inda daga cikin
inda da halin hakan da kowa ya auri daya daga cikin
wadannan kyawawan kuyangi masu yi masa hidima
lokacin da yarima kamsus yaga an hadasu tare da shi da
sarki a cikin wannan kasaitaccen babban daki mai dauke
da shimfidu kujeru da gidaje na alfarma sai ya kamu da
tsananin farin ciki da shigarsu cikin dakin sai sarki
Alkasim ya nufi wani luntsumemen gado ya fada kansa ya baje saboda tsananin
taushin gadon take ya fara lumshe idanu alamar cewa
barci na son satarsa koda ganin hakan sai yarima
kamsus ya tasheshi zaune sannan ya dubeshi cikin
alamun matukar damuwa yace haba yakai abbana yanzu
ashe duk barcin da ka keyi jiya a cikin dare bai ishekaba?
Kada ka bamu kunya fa tun yanzu nan kauyene kawai a
cikin garuruwan kasar sarki masarul anjana''
koda jin wannan batu sai sarki Alkasim yayi zumbur
ya mike tsaye yana mai mitsitstsike idanunsa sannan ya nufi kan wata
doguwar kujera yana rike da hannun yarima suka
zauna tare suna masu fuskantar juna sarki Alkasim
yayi gyaran murya sannan yace yakai dana hakika wannan
duniya fadi gareta kuma abin cikinta yawa gareshi
tabbas na daina raina kowa da komai domin komai
na iya faruwa cikin bazato amma duk da haka na yarda
da kaina nayi imani cewa ni zakine abin tsoro zan iya
jada duk wani mai ji da kansa don haka har abada
zuciyata ba zata karaya ba akan mutum da Aljan
domin sai an buga sannan ake sanin na kwarai.
Inaji a jikina cewa a tsakaninmu ni dakai dayanmu zai
cika burin sarki masarul anjana na sauya rayuwar 'yarsa
lokacin da sarki Alkasim yazo nan a jawabinsa sai
yarima kamsus ya bushe da dariyar farin ciki sannan
ya dubeshi cikin nutsuwa yace ina alfahari dakai ya
abbana ba don komai ba sai saboda kai mutunne
mai ki -fadi!
A iya sanina tun tasowata daga kuruciyata kawo i
yanzu baka taba fadin abinda bai faru ba don haka nayi
imani akan cewa sai hakan ta faru idan kuma hakan
bata faru ba to wani babban abin al ajabi zai biyo baya
ni yanzu abinda nake so dakai shine ka taimaka ka
karasa mini wancan labari naka lallai ina so naji yadda
karshen gasarku zai kasance kuma ina son na san matsayin
jaruma luslaiya da na mahaifiyata ta gida lokacin
da yarima kamsus yazo nan a zancensa sai sarki
alkasim ya sunkui da kansa kas jikinsa yayi sanyi
tamkar an zare dukkan lakar jikinsa daga can kuma
sai ya dago kai ya dubi yarima kamsus a lokacin da
idanunsa suka ciko da kwalla ya dafa kafadarsa yace
yakai dana ba komai ne yasa kaga ina ta ja maka rai ba
akan wannan labari ba face na tsani tuno da baya
kuma na tsani duk abinda zai sakani zubar da hawaye
saboda zubar hawayen jarumi babbar illace a cikin
jarumtakarsa da nasararsa koda kuwa yafi kowa karfi da sa'a
yanzu take zan yi kokari in gama baka wannan labari amma
ka nutsu sosai ka fahimci babban darasin dake cikinsa
saboda bana son ka aikata irin kuskuren dana aikata
a rayuwata
ka sani cewa wani lokaci yana da kyau mutum ya hakura
da son zuciyarsa don gudun bacin zuciyar a gaba ''
koda sarki Alkasim yazo nan a jawabinsa sai yayi
doguwar ajiyar zuciya sannan yaci gaba da baiwa yarima
kamsus labari kamar haka...
++ +++ ++++ +++++++++++
'''LOKACIN DA JARUMA LUSLAIYA taji na ce sai dai mu
fita tare daga cikin wannan rami mai mugun zurfi, kuma
akan igiyarta sai hankalinta ya dugunzuma ainun ta
yi shiru tana kallona kawai ta kasa cewa komai ashe tunanin
hanyar da zata cutar dani take yi kawai sai tayi wuf !
Ta kama igiyar tata da nufin ta fara hawa amma sai nima
na kama igiyar na tsaida ita nace nine zan fara hawa
Da jin haka sai nayi murmushi nace Abinda yasa nace
nine zan fara hawa shine idan muka yi nisa a lokacin
da muka jigata zaki iya cutar dani ki dokoni kasa tunda
kina samana
Compilied By Abubakar Saleh AlQuyraemey
Whatsapp Number 08138873799
Visit www.rumbunlabarai.com For More Complete Documents
cikin fishi luslaiya tace to mene ne tabbacin cewa kaima ba
zakayi min haka ba? Nayi murmushi nace ai ni
kin san cewa na kamu da tsananin sonki kuma na ceci
rayuwarki a baya don haka babu yadda za ayi nayi wani
yunkuri na hallakaki duk da cewa ke kin tsaneni fiye
da yadda kika tsani mutuwarki, luslaiya ta dubeni a
fusace tace, wannan imaninka kenan ba nawa ba
A rayuwata ban da iyayena da suka haifeni ban taba
yarda da kowa ba
ba zan taba yarda da cewar ka fara hawa kan wannan
igiya ba saidai mu ci gaba da yaki anan har dayanmu ya
sami nasarar kashe daya kayi sani cewa ban dawo nan
cikin wannan rami domin komaiba sai somin na yanke kanka na tafi da
shi izuwa ga mahaifina domin ya tabbatar da cewar
munyi wannan gasa kuma na sami nasara a kanka
koda jin wannan batu na luslaiya saina bushe da dariya sannan na dubeta
ina mai murtuke fuskata kuma na daka mata tsawa
duk da cewa luslaiya bata san tsoro ba saida naga alamun
razana akan fuskarta
take na gamsu cewa lallai namiji yana gaba da mace
komai karfinta da isarta kuwa....
.
Bari na dakata anan nima sbd wannan tsawa da sarki Alkasim yayi na firgita na kasa ci gaba..
Al amin Ahmed Misau
Guyson sunana kenan
Mutum Da Aljan
Littafi Na Shida (6)
Part C.
,
typing by..
Al amin Ahmed Misau
Guyson ko Shagala Boy
call 08064594218 For more info.
Doka ' ban yarda a juya wannan post dinba in ba
tare da izinina ba...
.
Labari ya isowa guyson cewa..
.
Kafin wannan macijiyar ta kawo mini wani harin tuni na
zare addana na mike tsaye zumbur nan fa muka
kacame da masifaffen yaki ya zamana cewa macijiyar
na kawo mini sara da cizo ina gocewa cikin zafin nama ina kai mata sara da suka
duk da cewa na yiwa wannan macijiya rauni akanta jini
na zuba saida muka shafe sama da sa a guda muna
gumurzu da kyar da sidin goshina shammaci macijiyar na
dakatsalle sama na sare mata kai ta sulale kasa matacciya
A wannan lokaci a jikina akwai raunika sama da guda
ashirin wadanda macijiyar tayi mini nan take jiri ya
rinka dibata sakamakon jinin dake zuba a jikina na rinka layi
tamkar wanda yasha barasa ya bugu daga can kuma saina
yanke jiki na fadi kasa sumamme++
wow Sarki Alkasim kaga Rayuwa namijin fama
Nima Guyson kunsan fa nasha wahalar nan fa ehem
Al amarin jaruma luslaiya kuwa lokacin da ta nausa
cikin daji cikin tsananin farin ciki sai data shafe kusan rabin sa a
tana tafiya sannan ta tsaya cak nan take ta gane cewa
tayi babban kuskure da ta baro wancan wuri inda ta baroni
macijiya zata hallakani kamata yayi ta tsaya taga yadda
macijiyar zata hallakani domin ta sami damar cire kaina
kafin macijiyar ta hadiyeni
koda gama ayyana hakan saita juyo da sauri ta falfalo
da azababben gudu zuwa inda ta baroni lokacin da jaruma
luslaiya ta iso inda ta baroni saita tsaya cak tayi turus ta kasa
motsin komai saboda tsananin mamaki gangar jikin
macijiyar ta gani kawai babu kai ga jini male male a wajan
kuma babu ni babu alamata saboda ganin wannan
abin mamaki jaruma luslaiya bata san sa adda zancen
zucinta ya fito fili ba tana cewa ''ta yaya Alkasim ya iya kashe
wannan macijiyar ''??
Kwatsam ! Saijin dariyata tayi a bayanta a firgice jaruma
luslaiya ta juyo da sauri take tayi arba dani a tsaye ina
rike da kan wannan katuwar macijiya duk jikina tabone
na raunikan da macijiyar tayi mini na shafesu da magani
jaruma luslaiya ta kura mini idanu kawai tana mamaki ta
kasa cewa komai
A sannan ne nayi mata wani dan guntun murmushi nace
shin kin mantane cewa manyan mazaje basa faduwa kasa
da sauri?
Kinyi babban kuskure har da kike tunanin cewa wannan
macijiyar zata sami nasarar hallakani shin kin aro idanun mujiyane shi yasa kika
cigaba da tafiyarki kika barni A nan?
Zaifi kyau muci gaba da yin wannan gasa tamu yanzu domin hutun jaki da
kaya zamuyi idan mun zauna a nan cikin alamun karayar
zuci da sanyin murya jaruma luslaiya ta dubeni tace
tayaya zamu cigaba da tafiya a wannan duhun dare haka
alhalin inda zamuje yana da nisan gaske? Hanzarin me kake
yine hakahar da kake son mu cigaba da yin gasar yanzu?
Koda jin wannan tambaya saina murrtuke fuskata nace
ke menene dalilin da yasa kike yin hanzari a baya?
Na sani cewa kin kagu ne kiga na hallaka sai kuma gashi na
cika taurin rai batum duhun dare ba uzuri bane cikin
wannan tafiya tamu tunda yanzu nan kika dawo daga tafiyar
kimanin rabin sa'a, kada ki manta cewa akwai gagarumin aiki
a gabanmu na sato gunkin da arnan daji suke bautawa, sannan kuma akwai
gasarmu ta karshe wato ta farauto dabba mafi karfi da hadari idan kuma kin
sare ne ba zaki iya ci gaba da gasar ba to ki fada naji
shikenan ya zama nine na lashe wannan gasar
ina gama fadin haka sai nayi wurgi da kan macijiyar na
soke addana cikin kufenta naje na karyo icen bishiya na
hada fitila sannan na dubi jaruma luslaiya nace muje zuwa
ba tare da wata gardama ba sai jaruma luslaiya ta bini
a baya muka nausa cikin daji babu abinda ya baiwa jaruma
luslaiya mamaki face ganin yadda na rinka yi mata jagora
a cikin wannan tafiyar tamkar nasan hanya alhalin itace
ta san ko ina a cikin dajin kuma itace ta san inda zamubi
harmu isa inda birnin arnan dajin yake haka dai muka cigaba
da tafiya muna ratsawa ta
cikin duhuwoyi kwazazzabai da duwatsu da koramai da
fadamomi
wani lokacin ma wadansu fadamomin akwai mugayen halittu a cikinsu irin su kadoji amma ko kallonsu
bama yi saidai mu wce ta gabansu ba tare da sun kawo mana
hari ba
sai da muka yi dan nisa a cikin tafiyar lokacin da dare ya raba sosai sannan na rage sauri
a cikin tafiyar tawa ita kuwa jaruma luslaiya saita rinka kara saurin nata har tazo
ta giftani ya zamana cewa tazarar da ita takai taku shida
koda ganin haka sai nayi zargin cewa akwai wani mugun
abu a kusa wanda jaruma luslaiya take son na fada cikin
sharrinsa don haka nima saina kara saurin tafiyata har na risketa muka jera
kafada da kafada
kwatsam ba zato ba tsammani sai mukayi kicibis da wani
katon tsauni a gabanmu tunda nazo duniya ban taba
ganin tsauni mai tsawo da fadinsa ba saboda tsananin tsawon
tsaunin bama iya hango abin dake kansa shidai wannan
tsauni ya tare hanyar da zamu wuce gaba daya don haka indai zamu wuce
sai daimubi ta kansa
kawai sainaga jaruma luslaiya ta dubeni tAce Akan wannan
tsauni birnin Arnan dajin yake idan ka kasa
kunnanka da
Kyau zaka jiyo sautin kida na tashi a can saman wannan tsauni
kwana suke suna bautar gunkin nasu don haka yanzu
komai jarumtakarmu da karfin sihirinmu ba zamu iya sato uban gijin nasu ba saidai
mu bari gari ya waye a lokacin da suka baro dakin bautar
suka shiga gidajensu suka kwanta suna barci
A WANNAN LOKACINE zamu iyaamfani da dukkan
karfinmu zafin namanmu da karfin gudunmu
wajan samun nasara
Lokacin da jaruma luslaiya tazo nan a zancenta sai na gyada
kai alamar cewa na yarda da duk bayanin nata
amma sai nace yanzu tayaya zamu iya hawa wannan
tsauni har mu sauko daga kansa lafiyakoda jin wannan
tambaya sai jaruma luslaiya ta dubeni cikin murmushi ta
nuna kanta da dan yatsa tace kayi amfani da kwakwalwarka
ka sani cewa koyaushe ana son jarumi ya zamo mai tunani
basira da kiyasta al amura tun kafin lokacinsa yazo
akwai hanyar da ake bi a hau wannan tsauni amma ba
zata hawu ba a wajanmu zomuje kaga zahiri
tana gama fadin haka saita jani muka nufi kudancin tsaunin
saida mukayi tafiya ta kusan rabin sa a sannan naga luslaiya ta fara yin sanda
nima saina yi koyi da ita koda muka iso wani wuri saita tsaya cak ta leka
da kanta kadan bayan tsaunin sannan ta juyo da sauri
ta yafitoni da hannu tana mai yi mini inkiyar nazo na leka
cikin hanzari na isa bayan luslaiya na leka inda ta leka kwai
sai na hango dakarun Arnan daji kimanin su miliyan daya
zazzaune akan wata matattakalar bene da suka gina bisa
tsaunin kowannansu na rike da muggan makaman yaki
ita dai wannan mtattakalar bene tayi sama ne har izuwa
karshen wannan tsauni su kuwa dakarun dake tsaron
wannan matattakala ban taba ganin girda girdan karti masu
tsawo da kaurin jiki irinsu ba kai da gani ba
tambaya ka san cewa kura zata ci mutum ma ana dolene su
kasance sadaukai masu karfin gaske don haka karo dasu
ba wasa bane kawai sai nayi doguwar ajiyar
zuciya na dubi luslaiya nayi mata inkiyar mu koma can baya
ba tare da wata gardama ba kuwa sai jaruma luslaiya ta bini muka koma can bayan
muka tsaya muna nazarin tsaunin muna tunanin yadda zamu hayeshi Abinda
ya fara fado min a rai shine hawa wannan tsauni yana da matukar hadari
domin idan muka yi nisa akansa duk sa adda mutum ya
gaji ya subuto kasa sunansa gawa
'shin tayaya zamu hau wannan tauni cikin nasara da sirri ba tare
da mun
fuskanci wata matsala ba?
Koda gama aiyana hakan sainasa hannuna na kwakuli
jikin tsaunin bisa mamaki sai naji da dan taushi alamar cewa
zai iya huduwa saboda
dankararriyar kasace koda ganin haka sai na dubi jaruma
luslaiya nace zamuyi amfani da wukake biyu wajan hawa
wannan tsaunin duk abinda nayi ki yi koyi dani
ina gama fadin hakan saina zaro wukake guda biyu a jikina masu tsini da kaifi
nan take na fara caka wukaken a jikin tsaunin ina zarewa
ina zakawa a sama
nan da nan sai gashi na fara hawa can sama koda ganin
haka sai itama jaruma luslaiya tayi koyi dani kafin cikar sa a
guda mun kai tsawon rabin tsaunin
A dai dai wannan lokacine matsananciyar gajiya ta riskemu bisa dole muka tsaya
muna hutawa muna haki kamar ranmu zai fita in ba don
sautin kidan da arnan dajin keyi ba da tuni asirinmu
ya tonu anji sautin caka wukakenmu da kuma numfarfashinmu
Luslaiya ta dubeni fuskarta a murtuke tace duk da cewa
na tsaneka kamar yadda na tsani mutuwata dolene na
jinjina maka bisa wannan basira taka nayi mamakin yadda
akayi ka tuno da wannan hikima ta hawa kan wannan tsaunin
sa adda naji wannan batu sainayi murmushi nace
ai sainan gaba ma zan burgeki tabbas zaki gamsu cewa ni jarumi ne na kwarai
abin kwatance kuma da kanki zaki sallama mini cewa na fiki jarumtaka
jaruma luslaiya ta kau da kai ga barin kallona ta ci gaba
da hawa saman tsaunin ba tare da ta sake tanka mini ba nima
saina cigaba da hawa tsaunin sannu sannu bata hana zuwa
saidai a dade ba aje ba lokacin da muka iso saman
tsaunin saina leko da kaina kadan koda idanuna sukayi arba
da miliyoyin gidajen arnan dajin sai zuciyata ta buga
da karfin gaske irin bugawar da bata taba yi ba ba
komai ne ya haddasa mini hakan ba face ganin tsananin
yawansu a wannan lokaci mazansu da matansu
suna can cikin dakin bautar tasu daga can nesa muke
jiyo sautin kade kaden nasu da muryoyin surutunsu
sai da muka tsaya muka sake hutawa sosai har izuwa
tsawon dakiku masu yawa sannan na dubi jaruma luslaiya cikin
alamun rashin yarda na ce yanzu mecece hikimarki ta cewa
muje mu sato gunkin Arnan dajin nan a yanzu lokacin
da suke cikin dakin bautar gaba dayansu tayaya zamu iya
ratsawa ta cikinsu har mu isa inda gunki yake kuma mu
iya daukoshi sna ji suna gani mu tsira?
Sa adda jaruma luslaiya taji wannan batu sai tayi
murmushi tace ai idan ba a wannan lokaci ba babu
lokacin da zamu iya kusantar inda dakin bautar yake sannan
kuma ai ba ta cikin kofar zamu shigaba
mutum takwas ne ke gadi a bakin kofar wannan daki na bautar
muna isa garesu zamu yakesu ne mu kashesu farat daya
maimakon mu bude kofar dakin mu shiga zamu haye
saman dakin ne muyi ta gudu har mu iso tsakiyarsu
tsakiyar dakin zamu fasa da takubbanmu mu rufa ciki
a dai dai lokacin inda gunkin yake
Zamu fada a sannan ne fa zamuyi amfani da dukkan zafin
namanmu da karfin damtsenmu mu cire gunkin nasu mu
tarwatsa su mu dako tsalle sama mu fito inda muka shiga
kada ka kuskura kafafunka su duro kasa ta kan
rufin dakin gidajensu zamu cigaba da gudu har mu iso
karshen tsaunin....
Mutum Da Aljan
Littafi Na Shida (6)
Part D.
.
Al amin Ahmed Misau
Guyson Ko shagala boy
ke magana
Call 08064594218 For more imfo
Doka ban yarda da duk wanda yake edit na
post dina ba indai bada izinina ba..
.
Labari ya isowa Guyson cewa..
.
Kada ka kuskura kafafunka su duro kasa ta kan
rufin gidajensu zamu cigaba da gudu har mu iso
karshen tsaunin..
Koda luslaiya tazo nan a zancenta sai tayi shiru ta kura mini idanu kawai
ni kuwa saina dubeta a fusace nace to yaya kika yi shiru?
Kin fadi yadda zamu iya sato gunkin amma baki fadi yadda zamu iya sauka ba lafiya daga kan wannan tsauni
kuma baki fadi yadda zamu iya tsallake irin mugayen haren
da zasu kawo mana ba a lokacin da muke kokarin guduwa
da abin bautar tasu koda jin wannan batu sai luslaiya ta dubeni cikin
murmushin mugunta tace a ina ka baro basirar taka da jarumtakar taka?
Ai sune amsar wannan tambaya taka kaine ya kamata kayi
tunanin hanyoyin da zamu bi mu kai ga nasara dajin haka saina gyada kai nayi murmushi nace
zan samo mana mafita muje zuwa kawai
kafin luslaiya ta kara cewa wani abu tuni daka tsalle
sama na dira akan tsaunin na zare takobina na falfala
da azababben gudu izuwa tsakiyar birnin ina cikin
falfala wannan azababben gudu nawa kawai sai motsin luslaiya
naji a baya na