Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a cikin wani ayari take na fatake? Amsar da alkasim ya kasa baiwa kansa kenan
haka dai alkasim yayi ta wannan hasashe da zulumi a cikin zuciyarsa har ya dawo cikin birnin misra da shigarsa cikin gidan sarautar sai ya wuce kai tsaye izuwa fadar sarki inda ya zube gabansa ya kwashi gaisuwa
guyson sunana ko kuce Al amin Ahmed Dan misau
Daga zauran labarai
shikuwa sarki sai ya dubeshi cikin alamun matukar mamaki yace yakai dana abin alfaharina ya kai dodon maza zaki uban dawa kuma guguwa mai baje birane yau kuma me ya faru
naga ka dawo daga farauta babu komai a tare dakai shin babu sauran dabbobine a cikin dajin namu ko kuwa ka fasa yin farautar ne ka juyo da baya?
Lokacin da yarima Alkasim yaji wadannan tambayoyi guda biyu sai yayi ajiyar numfashi cikin alamun karayar zuciya nan take ya kwashe labarin duk da ya faru tsakaninsa da wannan bakuwar jaruma ya zayyane masa
koda jin wannan labari sai sarki ya takarkare ya bushe da mahaukaciyar dariya yana mai tsananin farin ciki tamkar wanda aka yiwa albishir babba
Al amarin da yayi matukar baiwa kowa mamaki kenan daga can sai sarki ya tsuke bakinsa yayi shiru ga barin yin dariyar sannan ya dubi yarima alkasim cikin murmushi yace wannan bakuwar jaruma itace matar da zaka aura har ka samu haihuwa da ita
toh Guyson nake magana
gobe ka sake yin shiri ka tafi daji ba don kayi farautar dabba ba sai domin farautar wannan mata taka duk wahalar da zaka sha da duk irin wulakancin da zaka fuskanta ka juresa
yayin da alkasim yaji wannan batu sai shima fuskarsa ta fadada da murmushi ya mike tsaye ya dafa kirjinsa da hannu guda ya dubi sarki cikin dakakkiyar zuciya yace yakai abbana idan har na cika jininka nayi maka alkawari cewar duk irin gabar da zamu yi da wannan jaruma sai na siye zuciyarta ta kaunaceni''
typing by me Al amin Ahmed Guyson
daga zauran labarai
koda jin haka sai sarki ya sake kamuwa da matukar farin ciki ya mike tsaye daga kan karagarsa ya rungume alkasim yana mai cewa ina alfahari dakai yakai dana nasan zaka iya
har dare ya raba alkasim bai rintsa ba domin da zarar ya rufe idanunsa baya ganin komai face fuskar wannan bakuwar jaruma a yinin gaba daya ka kasa ci da shan komai
ko a zaune ko a tsaye sai yayi ta tuno da abubuwan da suka faru a tsakaninsa da bakuwar jarumar a daji
dakyar dai alkasim ya samu yayi dan barcin amma alfijir na ketowa ya farka nan take yasa kuyangi suka shirya masa ruwan wanka da abincinsa na kalaci ya kimtsa kafin gari ya soma haske tuni ya gama shirin tafiya farauta ba tare da bata wani lokaci ba yarima ya hau dokinsa ya fice daga cikin gidan sarautar ya nausa izuwa cikin wannan daji wanda ya hadu da bakuwar jaruma a cikinsa jiya
alkasim yaci gaba da nausawa cikin dajin yana ta dube dube da waige waige kai wani lokacin har saukowa yake daga kan dokinsa yana duba kasa ko zaiga sahul bil adama amma ko alamarsa bai gani ba
sai da ya shafe sa a biyu da rabi yana ta kai kawo a cikin dajin banda dabbobi da tsuntsayebabu abinda yake gani
da yake wannan karon ba tasu yake ba sai dai su wuce ya wuce abinsa babu mai tankawa wani hakanne yasa alkasim yaji ya kosa kuma zuciyarsa ta fara karaya da saran cewa zai sake haduwa da wannan bakuwar jaruma duk da mahaifinsa ya gaya masa cewa itace matar da zata zamo abokiyar rayuwarsa
lokacin da rana ta kwale sai alkasim ya nufi wata katuwar bishiya mai yawan ganyaye domin yaje ya zauna a karkashinta ya huta da isarsa bakin bishiyar sai ya sauka daga kan dokin ya daure dokin a jikin bishiyar sannan ya zauna a lokacin da wata irin iska mai dadin sanyi ta fara kadawa hakan ne yasa ya kishingida yana mai jingina gadon bayansa a jikin bishiyar
saboda gajiyar dake jikinsa sai kawai ya fara yin gyangyadi faruwar hakan keda wuya sai yaji wani abu na yawo a jikinsa tun daga kan kafafunsa
a firgice alkasim ya yunkura domin zare takobinsa amma sai yaji an kanannade jikinsa gaba daya kafin yayi wani yunkuri tuni wannan bishiya ta dare saiga wata kofa ta bayyana nan take wata iska mai karfi ta fito daga cikin kofar ta zuke alkasim a lokacin da yaji wata irin kasala ta shigeshi yadda ko hannunsa ba zai iya motsawa ba ashe wata murtukekiyar macijiyace ta kanannade shi gaba dayan jikinsa
kawai sai gani yayi an fyadashi da kasa a tsakiyar wata kasaitacciyar fada.
Fadar ta kawatu ainun da kayan kyale kyale kai kace fadar birnin misra, Al amin Ahmed Guyson sunana' koda alkasim ya dago kansa cikin matukar karfin hali sai yaga ashe babu kowa a cikin fadar face mutum daya jal kuma ba kowa bane face wannan bakuwar jaruma ita kadai zaune aakan wata katuwar karagar mulki taci ado irin na 'ya 'yan sarakai.
Koda yarima Alkasim yaga jarumar a cikin wannan hali sai ya kidime yaji ya kara kamuwa da tsananin sonta fiye da ko yaushe..
Don haka sai ya kura mata idanu yana murmushi ita kuwa saita murtuke fuskarta ta dubeshi a fusace tace mazaka bani amsar tambayar da zanyi maka yanzu in ba haka ba kuwa zan gana maka azabar da ba a taba yi maka irin taba
koda jin wannan batu sai alkasim yayi murmushi yace '' ina sauraronki me kike so kiji''
,

kuma a nanne MUTUM DA ALJAN littafi na HUDU (4) Yazo karshe
marubucin yace:-
SHIN ME ZAI FARU A CIKIN TAFIYAR YARIMA ALKASIM DA JARUMA LUSLAIYA?
.
KAFIN SU KAMMALA GASARSU HAR TA KAMU DA SONSA SUYI AURE KUMA MENENE SANADIN AJALINTA?
.
IDAN AKA ISA GARIN SARKI MASARUL ANJANA ME ZAI FARU TSAKANIN GIMBIYA ZULFULAIFA DA YARIMA KAMSUS KUMA MAI ZAI FARU A TSAKANIN SARKI ALKASIM DA SARKI MASARUL ANJANA?
.
INA LABARIN JARUMI ZAIHAS DA YAR'UWARSA?
.
SHIN ZASU SAMU NASARAR DAUKAR FANSA A KAN SARKI ALKASIM?
.
mu hadu a littafi na Biyar domin jin cigaban wannan labari.

Mutum Da Aljan
Littafi Na Biyar (5)
Part A.

Ku ziyarci Shafin www.rumbunlabarai.com domin samun littattafai masu daɗi da debe kewa


JARUMAR TA MIKE TSAYE DAGA KAN
KARAGAR MULKIN, ta tako kafafunta
tazo har daf da alkasim ta tsugunna
fuskarrta na kallon tasa yadda har
suna iya jin numfashin juna sannan
ta dubeshi fuskarta a daure ta dubeshi fuskarta a daure tace
wnene kai kuma me kake takama
dashi har da zakayi kokarin zaluntata
ka rabani da abinda na farauto a daji
alhalin hannuna ya riga naka kaiwa
kan dabbar?
Sa adda yarima alkasim yaji wannan
tambaya sai yayi murmushi yace
bazan baki amsar wannan tambaya
ba sai kin fara gabatar da kanki
tukunna nasan ko ke wacece.
Koda jin haka sai jarumar ta fusata ta
mike tsaye zumbur ta koma da sauri
zuwa kan karagarta ta zauna
zamanta keda wuya sai ta yi nuni da
hannunta zuwa kan alkasim take
wannan murtukekiyar macijiya data
kanannadeshi ta sauka daga jikinsa
amma sai wadansu sarkokin karfe
suka fito daka cikin bango kimanin
guda dubu suka kanannadeshi har
kansa suka janyeshi zuwa jikin
bangon suka shiga matseshi
yarima alkasim bai san sa adda ya
fara kurma ihu da kururuwa ba
sakamakon tsananin zafi da zugin da
yake ji
koda ganin haka sai jarumar ta fara
kyalkyala dariyar mugunta tana cikin
yin dariyar ne kwatsam taji alkasim
ya daina yin ihu da kururuwan kuma
nan take sarkokin suka karkatse suka
zube kasa gutsungutsun sai gani tayi
Alkasim ya baro jikin bangon ya
durfafota yana tafiya da karfinsa
tamkar wani abu bai taba samunsa
ba
Manya gatan wasa kenan sarki
Alkasim.
Cikin tsananin kaduwa da mamaki
jarumar ta mike tsaye tana kallonsa
kawai alkasim ya iso har daf da ita
yadda suna iya jin numfashin juna
kamar yadda tayi masa dazu ya
dubeta cikin murmushi yace
duk abinda kike takama dashi nima
ina da irinsa ko ma wanda ya fishi
akan wane dalili zaki dauki girman
kai a gareni alhalin nine yakamata
na zamo mai girman kai a gareki tun
da na kasance da ga sarkin dake
mulkin wannan kasa da kike cikinta.
Koda jin wannan batu sai jarumar
tayi murmushi sannan tace dama
saboda kai nazo wannan kasa
abinda yasa banje fada kai tsaye ba
shine ina son na gabatar da abinda
nazo yi a sirrance ya kasance a
tsakaninmu ne kawai mu biyu
sunana LUSLAIYA YA GA SARKIN
MAFARAUTA NA BIRNIN TEHERAN
tun ban fi shekara takwas ba a
duniya mahaifina ya bani horon yaki
wanda ina iya fuskantar zaratan
mayaka guda dubu sannan ya bani
horon gumurzu da manyan dabbobin
daji
baya ga hakan ya bani horon rayuwa
a cikin daji gami da yin gudu na
tsawon kwanaki tara ba tare da
tsayawa ba sama da dakika arba in
ba
bugu da kari mahaifina ya tsumani a
cikin tsumin tsafi irin wanda samun
mai irinsa sai an tona
lokacinda na samu shekaru goma
sha takwas ina samun wannan horo
ya zamana cewa na zama budurwa
cikakkiya sai na kawai da dukkan
yan fashin dake cikin dazuzzukan
kasarmu ni kadai
hakanne yasa yan fashin suka fusata
suka nemo taimakon yan uwansu
dake cikin kasashen ketare amma
duk da hakan sai na zame musu
alakakai na zamo tamkar shaidaniya
a cikin bil adama
akwai wata ranar da wadannnan yan
fashi suka ritsani a daji adadinsu
yakai miliyan shida amma ni kadai
na kashe mutum miliyan uku da rabi
daga cikinsu sauran suka tsere daga
wannan rana ne na dinga jin kamar
babu wani mayaki ko sadaukin da
yafi ni jarumtaka amma sai
mahaifina ya dubeni yace yake yata
kada ki kuskura ki dorawa kanki
girman kai bisa wannan jarumtaka
da kika ga kin samu
a halin yanzu ina mai tabbatar miki
da cewa akwai wani dan sarki wanda
karfinsa da jarumtakarsa har da
karfin sihirinsa zasu iya zuwa dai dai
da naki koma yafiki
koda jin wannan batu saina kamu da
tsananin mamaki na tuna irin karfiin
da nake dashi amma ace wai har
akwai wanda ya kaini koma ya fini
bisa wannan daliline na yanke
hukuncin nazo na hadu dakai domin
muyi gasa guda mu banbance
tsakanin aya da tsakuwa gasa ta
farko itace gudun tseren da zamuyi
tsawon kwana tara ba tare da
tsayawa ba ta sama da dakika arba
in ba
gasa ta biyu itace akwai wani babban
gari na arnan daji dake can
kudancinmu na taheran ina son mu je
mu sato gunkin da suke bautawa
domin mu tsokano yaki dasu
wadannan arnan daji suna da mugun
yawanda ba asan iyakar adadinsuba
ni dakai dai zamu yakesu domin mu
tantance iyakar jarumtakarmu
gasa ta uku wacce itace ta karshe
zamu shiga daji kowannanmu yayi
farautar dabbar da babu kamarta ya
kasheta yazo da gawarta idan har
dabbar da na kashe tafi taka hadari
ka tabbata cewa nafika karfi da
jarumtaka kenan
Al amin Ahmed Misau
Guyson sunana kenan
daga zauran labarai page nake typing
nan take zamu rabu na koma kasata
cikin farin cikin cewa nafi ka komai
yayinda jaruma luslaiiya tazo nan a
zancenta sai hankalin alkasizancenta sai hankalin alkasim ya
dugunzuma ainun saboda zuciyarsa
ta karaya akan wannan abu guda uku
amma daya tuna cewa shifa mutum
ne mai sa a da nasara bisa duk
abinda yasa a gabansa sai yaji
dukkan tsoro ya kau
daga cikin ransa don haka bai san sa
adda ya dubi jaruma luslaiya ba yace
na yarda da duk wannan sharadi na
gasar da kika shirya mana kuma
saina tabbatar miki da cewa nafiki
karfi da jarum taka
wow nima Guyson saina tabbatar
muku da cewa jarumi ne ni.
Yanzu idan na lashe wannan gasa
menene sakammenene sakamakona?
Koda jin wannan tambaya sai
mamaki ya kama luslaiya tace inda
dai ace kai ba dan sarki bane toda
saina baka dukiyar da har ka mutu
kai da danginka ba zaka yi talauci ba
amma ai mahaifinka yafi mahaifina
dukiya yanzu ban san dame zan iya
biyanka ba
koda jin wannan batu sai alkasim
yayi murmushi yace ai kuwa kece
kike da abin da zaki iya biyana yake
jarumar jarumai kuma tauraruwar
taurari ba komai nake so a wajanki
ba face soyayyarki da aurenki idan
har na lashe wannan gasa akanki to
na siyi soyayyata kenan kuma babu
abinda zai hana aurenmu
koda jin wannan batu sai jaruma
luslaiya taji zuciyarta tayi baki kirin
kuma nan take taji ta tsani yarima
alkasim fiye da komai a duniya
saboda tunanin cewa ya na so yayi
mata dole ta soshi kuma ta aureshi
cikin tsananin fushi ta dubeshi tace
nayi maka alkawari zaka sha bakar
wahala da baka taba sha ba a
rayuwarka a cikin wannan gasa
wacce zata kaika ga rasa lafiyarka ko
rayuwarka gaba daya
kuma ina tabbatar maka da cewa
baka da jarumtakar da zata iya
burgeni har zuciyata ta kamu da
sonka don haka duk yadda zanyi
naga ka fadi wannan gasa sai nayi ya
kasance ne ne na lashe gasar
ka sani cewa babu hada kai a cikin
wannan gasa ni dakai sai dai kowa
tasa ta fishsheshi kuma
kowannanmu zai iya shiryawa dan
uwansa tarkon mugunta domin ya
hallaka
iana son mu zamo tamkar abokan
gaba masu farautar rayukagaba masu farautar rayukan juna
lokacin da sarki alkasim yazo dai dai
nan a labarin da yake baiwa yarima
kamsus sai yaga idanun yarima sun
ciko da kwalla kuma hankalinsa ya
dugunzuma ainun ya tari
numfashinsa yaana mai cewa daka
ta yakai abbana yanzu kana bani
labarin wata jaruma a matsayin itace
mahaifiyata to ita kuma junaina
wadda na taso nake ganinta a
matsayin uwata wacece ita??
Koda jin wannan tambaya sai
hawaye ya zubowa sarki Alkasim
yayi shiru kamar ba zaice komai ba
daga can ya dago kai ya dubeshi
cikin rawar murya yace yakai dana
kayi hakuri zakaji amsawar wannan
tambaya da kayi min a karshen
wannan labari da nake baka kafin mu
isa birnin masarul anjana
Tabbas zaka tantance a tsakanin
mahaifiyarka junaina da kuma
mahaifiyarka jaruma luslaiya zaka
san matsayin kowacce a wajenka
koda sarki alkasim yazo nan a
zancensa sai zuciyarsa ta karaya ya
fashe da matsanancin kuka al amarin
da ya dugunzuma hankalin yarima
kamsus kenan ya shiga rarrashin
sarki a lokacin da yaji ya kamu da
tsananin tausayin mahaifin nasa
sarki Alkasim
da kyar ya shawo kansa ya daina
kukan sannan yarima kamsus ya
dubeshi cikin zakuwa yace na rokeka
dakaci gaba da bani wannan labari
domin naji yadda karshen gasarkdomin naji yadda karshen gasarku da
jaruma luslaiya zata kasance sannan
kuna na gane banbancin dake
tsakanin luslaiya da mahaifiyata
junaina
Al amin Ahmed Dan misau
Guyson sunana kenan
daga zauran labarai nake magana
tayaya zan karbi luslaiya a matsayin
uwa ta alhalin ban san wata uwa ba
face junaina
gama fadin haka keda wuya sai
hawaye ya kwararo bisa kumatun
yarima kamsus take shima sarki
alkasim yaji ya kamu da matukar
tausayinsa don haka sai ya
rungumeshi akan kirjinsa sannan
yaci gaba da bashi labari yana mai
cewa.....
.
LOKACIN DA NAJI ABINDA LUSLAIYA
ta fadi cewar a cikin wannan gasa
zamu zamo tamkar abokan gaba
kuma zamu rinka shiryawa juna
tarkon muguntar da zan iya hallaka
sai hankalina ya tashi saboda dalilai
guda biyu.
Dalili na farko shine na kamu da
tsananin sonta dalilina biyu kuwa
bazan iya shirya mata mugunta da
zata hallaka ba nan take zuciyata ta
gamsu cewar lallai zan sha bakar
wahala a cikin wannan gasa
musamman da na tuna cewa inda
zamu je mu gabatar da wannan gasa
acanne nahiyar su jaruma luslaiya
don haka ban san sirrikan
dazuzzukan dake can ba.
Yayin da luslaiya taga na sunkuyar
da kaina kasa ina tunani da nazari
saita kyalkyale da dariyar mugunta
sannan ta hade fuska tace yaro bai
san wuta ba saiya taka ta yanzu
saika tashi ka koma gida ka sanar da
iyayenka duk abinda ya faru a
tsakaninmu domin kayi musu
sallama ka dawo mu tafi ka sani
cewa tun daga nan gasar mu zata
fara don haka kayi amfani da
damarka ta kowa a gidansa sarkine
duk yadda zakayi ka tabbatar kaga
bayana kafin mu bar nahiyarku
dajin wannan batu sai yarima
Alkasim yayi murmushi ya mike
tsaye ya juya mata baya har yayi taku
uku gaba zai yi tafiyarsa sai ta kira
sunansa ya waigo ya dubeta cikin
mamaki
ita kuma sai tace da sassafe zaka
fito gobe ka sameni anan wurin idan
ka baata min lokacin zanyi tafiyata
sai kayi da gaske zaka riskeni
alkasim yayi murmushi yace babu
matsala zanzo akan lokaci
yana gama fadin hakan sai ya juya
yayi tafiyarsa har yarima alkasim ya
isa gida jikinsa a sanyaye yake kuma
hankalinsa a tashe yake domin
guiwarsa tayi sanyi ainun bisa
wannan gagarumar gasa dake
gabansa
da isar yarima Alkasim a lokacin da
magariba ta gabato sai ya nufi kai
Tsaye bisa mamaki sai ya hango
kofar dakinsa a bude al amarin da
yayi matukar bashi mamaki kenan
domin babu wanda yake da ikon
shiga dakinsa ba tare da izininsa ba
face mutum biyu daga sarki sai
mahaifiyarsa
a fusace yarima Alkasim ya kunna
kai da sauri cikin turakar tasa da
nufin yaci mutuncin wanda ya bude
ya shiga koda yayi arba da wanda ke
zaune a cikin dakin sai zuciyarsa ta
buga da karfi ba wani bane ba face
mahaifiyarsa tana zaune bisa
shimfidarsa kanta a sunkuye hawaye
na diga daga idanunta cikin firgici ya
karasa gareta da sauri ya durkusa a
gabanta
ya rike hannayanta biyu yana
dubanta cikin tsananin damuwa yace
yake ummina ina dalilin zubar
wannan hawaye daga cikin idanunki
sa adda taji wannan tambaya sai
tasa hannunta na dama ta share
hawayan nata sannan ta janyo
yarima izuwa jikinta ta rungumeshi
akan kirjinta tace
ya kai dana yau shekara talatin da
kadan kenan ina tare dakai bamu
taba rabuwa ba amma yau sarki ya
tabbatar min da cewa a wannan
karon zaka nisanta dani kuma zaka
yi wata tafiya mai hadari wacce
zama ka iya rasa rayuwarka
koda jin haka sai yarima alkasim yayi
murmushi cikin nutsuwa yace haba
yake ummina akan wane dalili zaki
damu kanki alhalin kin san duk
ahalin gidan nan yana da sa a da
nasara bisa duk abinda yasa a
gabansa ke da bakinki kin sha bani
labarin irin
gwagwarmayar da sarki yayi a
rayuwarsa tamkar ba zai tsira da
rayuwarsa ba
wai shin ma me yasa kika shigo cikin
turakata kika zauna kina ta kuka?
Shin yanzu kina nufin ki ce dake za
ayi wannan muguwar tafiya ne?
Nayi murna da ganinki a yanzu
domin dama akwai wani abu daya
shige min duhu ina son kiyi min
cikakken bayani kada ki boye min
komai
taji zuciyarta ta buga da karfi tsoro
ya shigeta ta fara zargin anya kuwa
sarki bai sanar dani sirrin da suka
boye ba tsawon shekaru cikin karfin
hali na budi baki nace
yake umma ina sonki sanar dani
matsayina
kafin yarima alkasim ya karasa fadin
abin dake bakinsa sai yaji motsi a
bayansa don haka sai ya waigo da
sauri
sarkine tsaye a bayansa fuskarsa a
murtuke yana mai kada kansa wato
yana yi masa nuni da kada ya fada
mata abindake bakinsa...
Zidane kd
Mutum Da Aljan
Littafi Na Biyar (5)
Part B.
.
Marubucin littafin
Abdul aziz sani madakin gini
typing by
Al amin Ahmed Misau
Guyson
Call;- 08064594218
Doka;- Ban laminta ba ayi edit na
post dina ba tare da sanina ba.
.
Labari ya isowa guyson cewa......
KAWAI SAI SARKI YA DUBI
MAHAIFIYATA yace ina son nayi
magana da dana shin zaki iya bamu
dama?
Ba tare da tace uffan ba sai ta mike
tsaye ta fice daga cikin tantin a
sannan ne sarki ya dubi alkasim a
fusace yace
shin baka da hankaline har da kake
shirin tambayarta matsayinka a
wajenta kana yin garaje a cikin al
amarinka kuma ita gaggawa bata
haifar da komai sai nadama
kayi hakuri kaji karshen labarin da
nake baka tukunna a sannan ne zaka
san matsayinka a wajenta ba wai sai
kaji daga bakin taba ni yanzu abinda
ya kawoni wajenka ba komai bane
face na sanar dakai cewa kada ka
kuskura ka bar zuciyarka ta karaya
bisa gasar da zakuyi kai da luslaiya
yar sarkin mafarauta na birnin
taheren
duk irin masifar da zaka gani a cikin
tafiyar taku duk irin tsananin wahalar
da zaka sha kada ka karaya domin
ba a samun komai a banza a cikin
wannan duniya dolene sai an sha
wuya sannan akansha dadi
duk abinda ya faru a daji tsakaninka
da luslaiya na gani a cikin madubin
tsafina don haka kayi sammakon
riskarta a dajin gobe da safe kamar
yadda ta umarceka
taimakon da zan baka a matsayin
babban guzuri a cikin wannan gasa
da zakayi shine ka rike abu uku
wannan abubuwa uku ba komai bane
ba face gaskiya hakuri da amana
sune kadai abubuwan da zasu
kubutar dakai daga sharrin luslaiya
amma ba karfin damtsenka ba ko
karfin sihirin tsafinka ba saboda duk
a bin da kake takama dashi itama
tana dashi
ka sani cewa nima na taka irin
wannan matsayin da kake kai yanzu
kafin na mallaki mahaifiyarka
wannan al adar gidannance babu
wani sarki da ya taba auren matar da
bata kasance basadaukiya ba
Al amin Ahmed Misau
Guyson sunana kenan
kuma jaruma abar kwatance a duniya
an tsara hakanne domin dukkan zuri
armu su rinka shan jarumtaka a nono
da wannan furuci nake yi maka
sallama kuma nasa maka albarka ka
tafi abinka nasara na tare dakai
koda gama fadin hakan sai sarki ya
dora hannunsa na hagu akan tsakiyar
kaina faruwar hakan keda wuya sai
naji wani irin gagarumin karfi ya
shiga jikina kuma naji dukkan tsoro
da fargaba sun kau daga cikin raina
har ina jin kamar cewa ni kadai zan
iya yakar duniya.
Saboda farin ciki bansan sa adda na
duka har kasa ba zan yiwa mahaifina
sujjada amma saiya kamo kafaduna
ya tasheni tsaye yace kwanta ka huta
dana gobe akwai gagarumin aiki
gabanka yana gama fadin haka sai
ya juya ya fice daga cikin dakin ya
barni ni kadai
nan dai naje na kwanta a shimfidata
na lumshe idanuna domin nayi barci
amma saina kasa domin fuskar
luslaiya naci gaba da gani ba
sassauci
har gari ya waye barcina rabi da
rabine wato rabi tunani rabi barci
kashe gari kuwa tun kafin alfijir ya
keto na gama shiri kuma nayi
sallama ga mahaifiyata duk mu
biyun muna kwalla muka rabu cikin
gaggawa nayi gagarumar shigar yaki
mai matukar kwarjini da ban tsoro na
hau dokina na sukwaneshi da guda
na fice daga cikin gari na naushi daji
hakika masu iya magana sun yi
gaskiya da sukace komai
sammakonka wani a tafe ya kwana a
iya tunanina sai dai naje wannan
wuri inda mukayi alkawarin haduwa
da luslaiya na jirata amma ina isa
wajan na isketa a tsaye gaban
wannan katuwar bishiya wacce ta
zukeni waccen karon
luslaiya ta ruke kugunta tana kai
kawo alamar cewa har ta gaji da jiran
isowarta
koda ta hangoni na durfafota sai tayi
dan guntun murmushi da isowata daf
da ita sai ta dubeni tace in dai baso
kake ka zalunci wannan doki naka ba
zai fi kyau ka sake shi ya kama
gabansa domin zaka ja shine izuwa
hallaka
kuma kada ka manta cewar daga nan
ne zamu fara yin gasar gudu ta
kwana tara
kuma tabbas wannan doki ba zai jure
hakan ba
ba tare da wata gardama ba saina
sauka daga
kan dokin na bugeshi ai kuwa sai
dokin ya juya
da baya da gudu yana mai bin hanyar
da muka fito
nan da nan kuwa ya kule muka daina
ganinshi
a sannan ne na juyo na dubi jaruma
luslaiya da kyau ai kuwa sai na rude
kuma na kidime naji na kara kamuwa
da tsananin
sonta fiye da koyaushe
a wannan lokaci luslaiya na sanye da
riga
da wando ne na fatar damisa
wadanda suka
kasance matsatstsu don haka gaba
dayan
surorin jikinta sun fito karara ni kam
in dai
tambayata za ayi to zance duk
duniya babu
wata ya mace mai kyan sura da kyan
fuskar mahaifiyarka luslaiya
luslaiya ta daure wadansu gajerun
adduna
guda biyu akan cinyoyinta dama da
hagu
a gadon bayanta kuwa tana rataye da
wata sharbebiyar takobi dogon
gashin
kanta kuwa ta tattareshi a bayanta ta
daureshi ya zuba har kan kasan
kwankwasonta sai sheki da walwali
yake
duk da cewa nayi gagarumar shigar
yaki sai
da na raina kaina domin tata shigar
tafi tawa
kyau da kwarjini
luslaiya ta sake dubana cikin wani
irin murmushi mai kama da mugunta
ko yaudara
tace idan ka shirya yanzu zamu fara
gasarmu
ta farko ta gudun kwana tara babu
tsayawa
ta tsawon sama da dakika goma
Al amin Ahmed Misau
Guyson,
Dajin haka sainayi murmushi nace ai
tunda har
na dawo gareki na gama shiri kafin
na gama
rufe bakina sai kawai naga luslaiya
ta zabura
ta falfala da azababben gudu izuwa
cikin
daji koda ganin haka sai nima na
falfala
nan da nan kuwa na risketa muka
jera muna
gudun tare da zarar naga ta rage
karfin
gudun nata sai nima na rage nawa ya
dawo
dai dai da nata
koda ganin haka sai tayi murmushi
na mugunta nima sai na maida
mata da martanin murmushin
muguntar saboda
nasan cewa na fita sanin sirrin
wannan daji
da muke ciki kuma na tabbatar da
cewa bata san
irin hadarin dake gabanmu ba akan
wannan hanya da muka biyo Abinda
luslaiya bata sani ba
shine anan gabanmu kadan akwai
wani kogi
na tabo wanda indai mutum ya fada
cikinsa
babu yadda zai iya kubuta sai dai ya
nutse a cikinsa face wani ya
taimakeshi
koda ya rage saura baifi dakika dari
ba mu iso
inda wannan kogin tabo yake saina
fara
rage guduna ta hanyar nuna alamun
cewa na fara gajiya
koda ganin haka sai luslaiya ta fara
murna
kuma ta karawa kanta karfin gudu
hakika rashin
sani yafi dare duhu tabbas inda
luslaiya tasan masifar
dake gabanta da batayi wannan
ganganci ba na
kara karfin gudun nata shi dai
wannan kogin tabo
gaba da bayansa a lullube yake da
tsirrai
babu yadda mutum zai iya ganewa
cewa kasan
tsiran tabone sannan kuma tabon
yana da zurfin gaske
Al amin Ahmed Misau
Guyson nake magana
daga zauran labarai page.
Da isowarmu daf da wannan kogin
tabo luslaiya na kan gaba ina
bayanta
koda ta waigo taga na karo guduna
ina son
na risketa saita daka tsalle sama
domin ta bani
tazara mai yawa kawai saiji tayi ta
fado cikin
tabo ta makale da kasa gaba da baya
nan fa ta fara amfani da karfin
sihirinta na tsafi
domin ta fito daga cikin tabon amma
saita kasa kuma
sai taji tana kara nutsewa kasa a
hankali
Al amarin da yayi matukar
dugunzuma hankalinta kenan
ta juyo bayanta
da sauri ta dubeni kawai sai gani na
tayi a
tsaye nayi turjiya na zuba mata idanu
ina
mata murmushin mugunta luslaiya ta
daka min tsawa tace meka
tsaya kana jira ka ci gaba da
gudunka ka barni a anan tawa ta
fishsheni
idan ma na mutu anan shi kenan ka
lashe gasar
koda jin wannan batu saina sake yin
murmushi
a karo na biyu nace tayaya zan iya
tafiya
na bar masoyiyata a inda zata
hallaka ai dole ne
na ceto rayuwarki
luslaiya tace ai kuwa inka ceci
rayuwata kayi
babban kuskuren da saikayi
nadamarsa
da jin haka saina gyada kai nace har
abada masoyi
baya nadama akan taimakon
masoyinsa
koda na gama fadin haka saina
kwance jakar
guzurina dake rataye a kafadata na
fiddo
wata doguwar igiya na cillawa
luslaiya
ta cafe sannan na rinka janyota daga
cikin tabon
a wannan lokaci tabon ya shanye
dukkan
wuyanta don haka gaba daya jikinta
ya baci
da tabon
da kyar na samu na fito da ita tana
gama fitowa
sai ta nufi cikin wata korama ta
kama yin wanka
ni dai ina tsaye a gefe daya ina
kallonta kawai
saita daka min tsawa tace shin
tarbiyarka daka samu kenan ta kallon
mata?
Koda jin haka sai nayi sauri na juya
mata
baya ina mai cewa ki gafarceni nayi
kuskure
bayan luslaiya ta gama wanka gaba
dayan tabon
jikinta saita fito daga cikin kogin tazo
kusa
dani ta dubeni tace
yanzu ta yaya zamu iya haye
wannan kogin
tabo muci gaba da yin tafiyarmu duk
inda
kika ga nasa kafata kema ki saka
naki
ina gama fadin hakan saina nufi kan
karshen
gefen kogin tabon naci

Please Login or Register in order to submit comment