Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

namune kodajin haka sai shamila tayi jifa da sailud canbaya yafado kasa yana kakarin amai bisa muguwar shakar da akayi masa

Sarki dawwaz yadubi jama ar gabaki daya yace inafatan kowa yaji sakon najwas ko kuma nasan da amincewar mahafin sa wannan sako yazo to inamai bada umarni gobe dasafe ahada tawaga da aljanu da mutane da dodanni milion shida sunufi birnin sarki shaddad suje subajeshi ko kazar garin bana nukatar ttarayu hatta gidajensu akonesu kurmus yadda ko atarihi baza ataba tinawa dasuba za ayi wannan tafiyane karkashin jagoran cin tagwaye na wato ginbiya shamilu dakuma shamilu annobar duniya nantake sarki yadubi yayansa guda biyu yace yaku tagwayena garanar dakuka dadade kuna jira tazo nasani cewa baku daburi dayafi kuganku astakiyar mutane kuna kisa tamkar masu sassabe agona kusani nabaku umarni baji ba gani kushe kowa acikin birninnan karkubar kowa yarayu

Kodajin wannan batu sai nantake fuskarsu tafadada da murmushi sunamai rugawa ga mahafinsu suna mai rungumeshi suna yimasa godiya nantake akasallami kowa yatafi gida sannan aka zabi zakwakuran damkarun daza atafi dasu birnin shiram bayan waye. War gari dakaru sarki dawwaz suka dauki hanyar birnin sarki shaddad domin isar da umarnin sarkinsu

Wannan tafiya anhada kazaman mayaka wadanda basusan tausayiba domin ko mesuka hadu dashi akan hanya to sunansa gawa haka duk birnin dasuka isa saisun afkamasa dayaki sun kwashe kowa sannan suci gaba datafiya tafiyar kwanaki uku suka shiga nahiyar dake makwabta ka da birnin shiram nantake sukahau mutanen garin dasara da suka ba kakkautawa nabu batun imani ko tausayi kawai kisa suke to acikin wannan kauyen dasuka isa ne suka sha mamaki domin saida sukayi mummunar asarar dakaru sannan suka samu nasarar murkushe birnin akwai wata jaruma mace guda datayimusu wahalar kashewa domin dagak karshema guduwa tayi sunyi iya kokarinsu sucinmata amma ina zakaran da allah yanufak dacara ko ana muzuru ana shaho to sai yayi domin tuni tabace musu bat babu ita babu alamunta

Saida suka kwashe kusan sa a uku suna nemanta acikin daji amma basu gantaba
Dole suka hakura sukaci gaba datafiya domin isa birnin shiram.

Acan birnin shiram kuwa. Tuni sarki shaddad yabayar da. Umarni fita yaki akahada tawagar mazaje wacce keyiwa lakabi da TAWAGAR MUTUWA GAMON AJALI ganinki badadiba saida sarki shaddad yahada mayaka masuji dakansu masu da kakkiyar zuciya da taurin rai kimani milion uku da doriya akar kashun jagoranncin sarkin yaki saif suka dunguma sai filin daga awannan yaki anyishine don ceton rai domin hatta sarki damatarsa da saida suka halarci wannan gasa amma shi yarima hanashi fita akai sabida atinaninsu korike makami bai iyaba shikuwa baiyi musu ba amma kawai jira yake sai sunyi gaba zai biyosu abaya asirrince batare da kowa yasani ba TOM NAJI UWARGIDA TANA KWALAMIN KIRA BARI NA JE NAJI KO ANGAMA TUWON NE NAKWASI RABONA .......................................Ninedai Naku Har Kullin Itz Dan Ustax Ne Nake Muku Barka Dawannan Lokaci Dafatan Kowa Yana cikikin Koshin

Farin cikin maruci comment and like domin hakan nakaramana kwarin guywa✊✊✊✊🏾✊🏾TAWAGAR MUTUWA✊🏾✊🏾gaman ajali Party Na 7

Al amarin dakarin Sarki dawwaz kuwa tafiya sukeyi bakakkautawa burinsu kawai su isa birnin shiram su afkamasa dayaki sukashe kowa atinaninsu sarki shaddad baisan datawo warsuba lolacin da shamila dashamilu suka fara hango ganuwar birnin shiram sai zuciyarsu ta cika da murna donhaka suka kara kaimi wajen gudun dawakansu saida sukaje dab dabirnin tafiyar dake tsakanunsu da birnin shiram batawuce tafiyar rabin sa a ba saisuka tsaya domin kowa yashirya kansa dashirin yaki maimatukar kwarjini daban tsoro

Al amarin yarima najwas kuwa lokacin da yabaro gida sai yawuce kaitsaye izuwa cikin daji don yagana dawannan aljana lokacin da isa inda yaboyeta saiya isketa atsaye akofar tantinta cikin tsananin damuwa dasauri yarima yakarasa gareta tana mai tanbayarta meyasa yaganta acikin damuwa alhalin babu wani abu dayake damunta kodajin haka sai aljana rashifa tadubeshi tace yakai yarima kayi sani cewa duk abin dayafaru tsakaninku dadan aiken sarki dawwaz duk nagani naji matukar damuwa da abinda kafada masa lallai katsokano bala in wanda za akirashi da gobara daga kogi wacce bata da magani caraf yarima yatari nunfashinta ya isa haka kisani cewa koda duk hatsabiban duniyane zasu hada kai sazo suce zasu kamani badon komaiba saidon kawai suyankani subawa gunkinsu jinina don kawai sarki dawwaz yanaso ya mulki dunia tokisa cewa ko mahai fina yace zai aikata wannan hukuncin to tabbas kaifin takobine kawai zai rabani dashi

Lokacin da aljana rashifa taji wannan batu saitace bawai nace kabayar dakanka ga sarki dawwaz ba aa inanufin kamata yayi kunemi sulhu hakamnne kawai zaisa ku tsira domin ina mutukar jin tsoron karonku da dakarun sarki dawwaz dimin su balbalin bala ine anno bane karo dasu tamkar karo da dukkan shadanun duniyane kodajin wannan batu sai yarima yace yake rashifa kiyi sanicewa bakin alkalami yariga yabushe yaki yariga yakullu tsakaninmu da sarki dawwaz dinhaka abinda namkeso dake babu wani taimako dazaki iya yimin awannan yaki

Kodajin wannan batu sai aljana rashifa tasaka hannunta abayanta kawai saitaciro wani abu sai sheki yake yana wani haske lokacin datagama ciro wannan abin kawai saiya rikide yazama wata sharbebiyar takobi mai taken gayawa jini nawuce tamika masa yasa hannu biyu yakarba sannan tace dashi inaso kayi yaki dawannan takobi asalinta tamahifina ce awajenshi nagajeta kada kakuskura kayi yaki dawannan sandar domin idan sarki dawwaz yagkano tana hanuun ka to tabbas ko bangon duniya zakaje saiyabika yakasheka yadauketa

Lokacin dayarima yaji wannan batu sai yayi murmushi maitaushi gawannan aljana sannan tasunbaci goshinta yajuya yanausa cikin daji dafarko yafara tafiya ahankali saikuma yafarfa sauri sannan yaruga daf gudu daga karshe kuma saiyatshi sama itadai kawai takura mfasa idanu tanamai mamakin yarima najwas yaro karami amma gashi da dakakkiyar zuciya dataurinkai tamkar aljani talura tuk bayanin datake yimasa akan sarki shaddad kokadan baya jin shakkar komai

Acan bangaren mazan fama kuwa kamar daga sama tawagar shiram sukfajiyo taku adab dasu kawai saisuka mike zunbur suna mai zare makamansu suka zubaama hanya idanu sunajira suga meke shirin afkuwa kwatsam saisukaga kura daga cannesa tamatsosu tareda wani mugun gurnani nantake sarkin yaki saif yabada umarnin lallai kowa yashira ya domin ga tsinannun sun isomu kafin yagama rufe baki tuni kurar nan talafa komai yafito kwatsam saiga saiga zugar mayaka cikin bakaken tufafi sudaya babu adadi sannan gawasu dakaru guda biyu maca da namiji agbansu gaduk alamu sune shuwahaban ninsu bawasu bane ba wadan mutun biyu baface shamila da shamilu cikin gagarumar shigar maimnatukar tabbas duk dakasancewar dakarun birnin shiram nada dakkaiyar zuciya gamida taurin rai amma saida suka razana daganin wannan tawaga domin aiya gwagwar mayar dasuknayi ayaki basu taba ganin tawaga maimnatukar kwarjini daban tsoroba kamar tawagar sarki dawwaz

Koda sarkin yaki saif yagan abinda ke shirin faruwa gamayakansa saiyadaka musu tsawa yana maicewa yaku tawagar shiramawa kada kumanta cewa wannan yaki dazukiyi zakuyishine donceton rayuwarku iyalanku dakuma dukiyarku dakomai naku idan bakuyi wannan yakiba zaku zama bayi marasa yanci za adimga azabtardaku kamar dabbobi sannan kuma kunaji kuna gani za akama yarimanku kamar kare aje ayi masa yankan rago abawa wani katon banza jininsa yasha to kusani narantse da girmar kaeagar sarki shaddad wannan yaki tazama wajibi akanmu lokacin da sarkin yaki yazonan azancensa sai nantake dakarunsa sukazare makamansu sannan suka fuskanci abokan gaba to asanna nne shamila dashamilu suka futo gaban tawagarsu suka tsaya ga wasu mahaukatan dodanni da aljani natake musu baya sai dalalar dayawu suke sunga ba atsaya wani bata lokaciba. Shamila tabada umurnin a afkawa abokan gaba take dakaru kimani milion uku dadoriya sukai gunji sannan suka ruga kan abokan gaba. Domin su shafesu adoron kasa koda ganin ha ka saishima sarkin ya ki saif yazare takobinsa sama yana kwarara uban ihu yace ku muje mazaje lallai kada yawan abokan gaba yatsoraku muyi yaki iyakar karfin dadabarun mu lallai mununa musu mu shiramawa jarumta ajininmu take

Wohoho nanfa dakaru suka zare makamai suka ruga izuwa kan abokan gaba dabakar zuciya akayu wani irin mugu gwamo jikake kwaran kwatsam anhadu atsakiya nanfa aka bude kasuwar rayuka mutuwa takama shawagi saman mutane lokaci guda idan shamila da shamilu sukakai saran damakaman su saidai kaga suna girbe kan mazaje tamkar masu sassabe agonar aduka kisa suke baji bagani tabbas wadannan dakaru na. Sarki dawwaz ba karamar annoba bace domin kisa sukeyi kamar mahaukatan zakuna gabaki daya sun rikita dakarun shiramawa sunhanasu sakat suntakurasu kai sabida tsabar bala in da ake saukewa shiramawa saida wasun suka fara zub damakan.su suna rugawa cikin daji domin ceton rayuwarsu amma ina damar haka bata samuba domin duk wanda yayin kurin guduwa caraf shamila zata bayyan agabnsa tatsinke masa wuya

Tabbas gaba dagabanta wai aljani yataka wuta tabbas wannan rana shiramawa sunga bala in dabasu taba ganinsaba shikuwam sarjin yaki kutsawa kawai yakeyi cikin dandazon mayaka burinsa kawai yahadu da shamila da shamilu domin yasani cewa sukadai dirakar xakarun sarki dawwaz dazarar yagama dasu to shikenan yaki yazo karshe tabbas rashin sani yafi dare duhu da sarkin yasan masifar wadannan jaruma guda biyu da bayyi gangancin tun kararasu dayakiba yana cikin gudune wani dodo yamangareshi yafada can gefe amatukar galabaice yayunkura zaimike amma yamakara tuni shamilu ya bayyana agabainsa yadaga takobi danufin yadatse masa kai saura baifi kamu ukuba takobin shamilu tahadu dawuyan sarkin yaki kwatsam saiyaji anmabza masa wani wawan naushi saida yatashi yasama yaje yabugo wata bishiya abinka da shaidani kawai sai yadawo yatsacak da kafafunsa sannan yayi duba izuwa gawanda yayimasa wannan duka ransa amatukar bace idanunsa sunyu wani jajir tamkar angasa danbuda awuta tabbas kowaye wannan yatabo fishin maza NIKAM GANIN YADDA SHAMILU YAFUSATA NE YASA NAFIRGITA BANSAN LOKACIN DANA WULLAR DA ALKALAMINA🖋️BA MABOYE BAYAN WANI DUTSE. Toby CONTINUE Naku Harkullin itz dan Ustax ne nake cemuku mukwana lafiya✊🏾✊🏾TAWAGAR MUTUWA ✊🏾✊🏾gamon ajali.......party 8 ............................................. yarima shamilu yadago fuskarsa afusace domin ganin. Wanda yayimasa wannan duka bawani bane bafce sarki shaddad ransa abace yakama hannun sarkin yaki yatashe shi sannan yadubi shamilu yace kai yaro kafusatako tolasani yau kimanin.shekara dari dadoriya minazaune daku lfy babu abin dayataba shiga tsakaninmu daku shine yanzu zaku karya wannan tarihi to kasani kunyi babban kuskure kuma tabbas mahafinku saiyayi nadamar turoku yaki birnin shuram dayayi koda jin haka sai shamilu yabushe dadariyar mugunta saida yayi mai isarsa sannan yaturbne fuska yadubi sarki shaddad yace kai tsohon.sadauki kuma kaskan taccen sarki kayi san cewa kune zakuyi nadamar bijrewa umarnin mahaifinmu yau zaku sance wa karo da sarki iko sarki dawwaz babu dadi

Sarki shaddad yayi murmushi yace yaro yaro ne ayadda babu kasa anan ake garadar kowa yau zakasan cewa. Shaddad murucin kan dutsene baifitobaa saida tashirya kafin yarima shamilu yace wani abu tuni sarki shaddad yazare takobi gamida jijjiga garkuwa yayi kansa dagudu koda ganin haka saishima shamilu yayo kansa ahaukace sauara kadan su hadu sai dukkannin su suka dakatsalle sama suna masu kaiwa juna mummunan saran maitaken kwaf daya jikake kall haduwar takubban su tartsatsin wata gamida hayaki suka rufe gurin suka rikito kasa sukaa ruguntsume da azababben yaki maimatukar bantsoro shidai yarima shamilu tunda yafara gwagwar maya baitabaa haduwa da mayaki maimatukaar zafinnan dajuriya irin sarki shaddad ba domin dik lokacin da sarki shaddad yakai masa sara datakobinsa idan yakare jiyake kamar katon duste aka dakko aka dora masa domin wani lokacin har durkushe wa kasa yake amma sai kaga yayi zunbur yamike sunci gaaba da yaki baji bagani

acan bangaren dakarun yaki kuwa abin yayi muni da yawa domin.awannan lokacin tun shigowar sarki shaddad filin.daga saidakarunsa suka sami kwarin guywa suka zage yaki suke tamkar jikinsu bana jini datsoka bane awannan lokacin dakarun birnin manohar sunji ajikinsu domin dakaru sarki shaddad sun fusata fusatar da basu taba yintaba domin saikaga dakare guda daya yadebi dakaru sama dabiyar yawatsar sannan yasa takobi yasare kawunan tsinannu jikin.kaankanin.lokacin lissafi yacanza domin ragar gazar dakaru sarki dawwaz akeyi kamar ana sassabe agona kai da bala I yakai bala I masifa takai masifa dakarun birni manohar saida suka fara shirin guduwa amma ina damar hakan bata samuba domin duk wanda yayi yinkurin guduwa take masu baka dakwari zasu sakarmasa harbi

Cukin kankanin lokaci gurin yahargitse yayamutse bakajin komai sai ihun dakaru da kururuwarsu hardakarun birnin manahar sukafara jadabaya koda shamila taga abin dake shirin.faruwa sai nantake tatarwatsa dakarun dake kewaye da ita tarufe idanununta tayi wani surutu take saiga wasu jibga jibgan halittu daga jinsin aljanu da dodanni sunshigo filin shigowarsu keadawuya saisuka afka wa shiramawa dayaki tofa awannan lokacin dakarun birnin shiram suka hadu da bala I domin wadannan halittun basajin.sara kosuka jikin su tamaka dutse haka yake nanfa akabude kasuwar rayukan bil adama saidai kaga aljani ko dodo yadaga kafa yatalitse bil adama sama dahamsin lokaci guda hakanne fa yarikita dakarun sarki shaddad suka fara jada baya

Kwatsam saisuka hango wani haske daga sama yatawo luuu yadire agaban wadannan halittun ahankali hasken yafara rikidewa yanazama mutun ahankali har yazama wani sadauki murdadde maikirar mazajen fama fuskarsa arufe kawata sharbebiyar takobi ahannunsa sai sheki ta keyi kilam wannan jarumi yatsaya baiko motsaba hakanne yafusata wadannan halitun sukayi kansa wani dodo yakaimasa wafta caraf tarike hannun dodonnan sannan yasa takobi yazabtarawa dodonnan sara akirji kit taraba dodon gidabiyu yaraf tafadi kasa baiko shuraba

Koda ganin abindaa yafaru sai sauran sukaa fusata sukaa afkawa bakon jaruminnan dasara dasuka tako ina tofa ananne sukari ajalinsu domin tsalle daya yayiyadira atsakiyarsu yafara rabamusu mutuwa kyauta saidai kaga lolaci guda yazaf tare kan dodo ko aljani gudu goma ko yasare kafafuwansu duk lokicin daya daga takobin sa sama yasoketa akasa saidai kaga samada ashirin sunzube kasa maatattu nandan ya haukatasu harsuka fara kashe kansu koda yaga yaka sai tasulale yafice daga cikinsu yabarsu suna takahse junan su ya afka cikin abokan gaba yabude wata sabuwar kasuwar lokacin dadakarin birnin.shiram suka rufa masa baya ashe lokacin dayafice daga cikin aljanunnan shamila taganshi donhaka saitabi bayansa dagudun tsiya domin tacimmasa taimasa kwaf kiris tariske shi takaimasa wawansara kamar ance waiga bayanka yana waiga saiko yaga hasken takobi daidai maqo gwaronsa jikin zafin nama yadurkusa kasa takobin yawuce amma duk dahaaka saida tayanki gashin kansa sannan tasake kaimasa wani saran danufin tatsarge masa kafada cikin fushi yakawuce saran kafin takawo wani harin yadun kule hannu yagaza amata wawan naushi akirji fu tatashi sama kamar an janyeta da majaujawa tafado kasa tim

Ahasa shenku wanene wannan bakon jarumin
Mai matukar jarutar ban al ajabi NIKAM NABI TANAN NAJI UWARGIDA NAKORAFI INJIN MASAR TASOYU
NIne dai Naku Har kullin Itz dan Ustax Ne nakewa kowa fatan alkhairi Mai dorewa✊🏾✊🏾TAWAGAR MUTUWA✊🏾✊🏾 GAMON AJALI party na 09 .................................................................lolacin da bakon jarumin nan yadaki kirjin ginbiya shamila da hannunsa taje tabugo bishiya tafado kasa tim sairai zunbur tayi wata irin alkafura tamanyan jaruman fama tamike tsaye tokurawa bakon jarumin nan idanu ranta abace sabida tsabar fusata harfuskarta tanayin yatsinewa shikuwa baibi takantaba hankalinsa nawajen sarki shaddad wanda dodanni kimanin dubu biyu suka kewayeshi

Nantake yajuya yaci gaba da gudu domin tariski sarki shaddad aikuwa saishamila ta fusata tayunkura zatabi bayansa amma sai dakarun sarki shaddad masu yawa suka suka zagayeta suka afkamata tayi iya kokarinta domin ta tarwatsasu amma abu yagagara sabida dakarine masu tsananin naci dakarfin zuciya

Acan bangaren sarki shaddad kuwa dodannin nan sun kuntatashi sun hanashi sakat burinsu kawai sukasheshi amma ina abu yagagara domin shima yazage wajen kare rayuwarsa gamida maida zazzafan martani saidai babban abintashin hankalinsa shine dakarun dodanninnan basaji sara dasuka inko yasamu nasarar naushinsu ko bugun su daka jiyake tamkar dutse yake duka yadoki ko ina ajikinsu amma yakasa samo lagonsu anacin haka ne wani dodo yagab za masa wani wawan duka sabida tsabar karfin dukan saida yaisama yadawo takife akas ko mitsi baiyiba lokacin da dodannin sukayi ca a akansa domin sucaka masa wawa

Wannan bakon jarumin duk yaga abin dake shirin faruwa don haka sai yakara kaimi wajen gudun nasa adaidai lokacin dawani dodo yadaga wani kato gatari domin yasare sarki shaddad wuhuhu tundaga nesa yarima yakwalla ihu sannan yacillo takobinsa yana maiyin wani surutu aikuwa takobin nan tayi wani haske tatafi aune daidai lokacin datsakanin takobin dodon da sarki shaddad batawuce kamu dayaba kil takobin bakon jarumin tafille hannhn tsinanne kuma adai lokacin da iso gurin caraf takobin takoma hannunsa kil tacirewa dodonnan kai yafadi kasa sharaf yana birgima

Lokacin ne sauran dodannin suka kewaye bakon jarumin yayinda shikuma yadauki sarki shaddad yagoyasa abaya sannan yarike takobinsa da hanun dama yana maijijjuyata atsakiyarsu lokaci guda suka afkamasa domin yimsa rubdugu kamar ancillashi yatashi sama kafin sudaga kawunansu shikuma tuni yadiro kansu yasare kawunan goma asama sannan yakaraso kasa yasare kadafun wasu dayawa

Nanfa yafara sauke musu bal balin bala I baji babu gani tamkar maisassabe agonar shinkafa haka yake kashesu sukuwa sunkasa koda lakutar jikinsa kafin cikar sa a daya yatarwatsa su yakashe nakashewa yaraunata narautawa lokacin dayake tasaye kikam ga takobinsa na digar dawani bakin jini ga alama bajin bil adama ba ne

Kwatsam yarima shamilu yahango abinda dayafaru ga dodanninsa nantake ransa yabaci yadaga wani dogon mashi yacillowa bakonnan shikuwa yakabeshi yafadi gefe tofa saishamilu yakara harzuqa yayo kansa aguje asannan sarki shaddad yafar fado daga suman dayayi fit yadiro daga bayan bakonan kamar wanda yayi mafarki alokacin kuma.ya hango shamilu yayokansu saiya yinkura danufin ya afka masa amma amma sai wannan bakon yayi caraf yariko hanunsa kuma adaidai lokacinne akabusa kahon tsaida yaki ako wane bangare

Nantake kowane bangare yajanye dakarunsa amma akaja tunga akatsaya suna huci gamida hararar juna lokacin da tawagar sarki shaddad takoma gefe kowa yana haki alokacin hankalon.kowa nakan bakon jaruminnan kowa yakagu yaga kowaye kawai saiyaye rawaninsa yacillar dashi aikuwa sai mamaki yakama kowa bawani baneba face yarima najwas nanfa mamaki yakama mutane sabida aiya saninsu da majwas ko makami baitaba rikewaba amma saihashi shine gwarzon fama wanda badon shiba datuni sarki shaddad yadade dahalaka

Sukuwa shamila da shamilu ransune yai matukar baci ganin yaron dasukazo kamawa yazama gagara badau lallai akwai sauran aiki agabansu makarmiba domin wannan yaron koda sunyi nasara awannan yaki ba abune mai saukiba

Shikiwa najwas yadubesu yace yaku taron tsinannu kuma tan badaddun azzalumai kusani cewa yariman da akaturoku kukama ba kanwar lasa bane nazama zaki kuma kadan garen bakin tulu akarshi akar tulu akyaleshi yayi barna yanzu kuna dama guda zaku iya juyawa kukoma birninku kusanar da sarkinku aikin da yaturoku yafi karfinku saidai shiyazo dakansa idan kuma kuna ganin zakuci gaba dayakar mu to ga fili gamai doki sai akasa tseren mugani nikuma barantse da girman karagar mahaifina dayanku bazai bar wurinnan araye ba
NIKAM NABITANAN NAJI UWARGIDA NAKIRA INAJI ANGAMA NE Ninedai naku har kullin Itz Dan Usatax Ne Nake cemuku muzama lafiya
✊🏾✊🏾TAWAGAR MUTUWA✊🏾✊🏾 GAMON AJALI party na 010......................................

Caraf ginbiya shamila tatari nunfashin yarima tana mai daka masa tsawa tace kai yaro kabar cika baki ba aja da ikon mahaifinmu kuma yaudinnan zakasan cewa bijirewa umarnin mahaifin mu daidai yake dataro aradu dayaki kun shamacemu akaro nafarko tabbas bamusancewa kai jarumi bane haka kuma bamusan kunada zakwakuran mayaka ba sai yanzu amma babu komai akaro nabiyu zakusha mamaki domin shirinmu yawuce yanda kuke tunani tana gama fadin haka taja zugarsu suka koma sansaninsu inda suka yada zango ganin haka saishima sarki shaddad yabada umarnin akaoma gida take kuwa aka koma cikin gari

Bayan kowa yaci yakoshi anyiwa masu rauni magani sai sarki shaddad tareda manyan jarumansa suka kadakita domin ayi shawara tahanyar dayakamata abiyowa wannan yaki akaro nabiyu domin sunsani karo nabiyu bazai yimusu kyauba indai basu canza shiriba shikuwa yarima yana gefe baice komai ba can wani sadauki yamike yadu jama a yace yaku jakma ar birini shiram kuyi sani cewa tabbas akaron farko yaki yaso yacimu amma hakan baiyiwu ba kuma hakan.yafarune sakamakon zuwan sadauki mu mai abin al ajabi wato yarima najwas tabbas yarima yabamu mamaki matuka agida muka barshi aboye amma yaushe haryasulale yaje filin daga yayi wannan abin al ajabi alhalin ko takobi bai iya sarrafawa tabbas akwai alagmun mutanbayi shi amma yanzu bamuda wannan dama sabida lokacinmu akure yake saidai mujira zuwa karshen wannan yaki sannan zamuji komai

Yace abunda zamuyi yanzu akaro nabiyu atawa shawarar shine zamu kasu kaso uku daya kar kashin jagorancin sarkin yaki saif tawaga tabiyu kuma karkashi jagoran cin yarima najwas wanda yanzu zamu koma dakira jarumi najwas sannan tawaga takarshe karkashin jagorancin sarki shaddad tawaga dayace zata fara shiga daga mun fuskanci sunfara jigata za abusa kaho suyo baya nabiyu su shiga ina tinanin idanmukayi haka tabbas zamu nasara cikin sauki batare da munsha wahala ba

Tabbas jama a sunji dadin wannan tsari nasadauki yasir donhaka kowa yadauki shawara sa ahaka taro yawatse kowa yakakma gabansa acan bangaren su ginbiya shamila da shamila kuwa sunkoma sansanindasuka yada zango cikin matukar bakinciki dadamuwa domin Basu tabatinanin cewa birnin shiram nada zakwakuran mayaka gamida taurinkai danaciba saiyau bugu dakari GA sadauki najwas da aka Basu umarnin sukamashi yafi kowa sadaukantaka abirnin gashida baiwa kala kala

Hakanne yasa shamilu yadubi yar uwarsa shamila yace yake yar uwata tabbas yaki yabiyo mana ta inda bamuyi tunaniba Amma yanzu shawarar danayanke shine akaro nabiyu zamuyi amfani da karfin sihirin tsafinmu Ina tinanin idanmukayi haka zamuyi nasara sabida nafiskanci bazasu kaimu karfin sihiriba Na tabbatar dacewa indai mukaci gaba dayaki dasu dakarfin dantse koda makami bazamu taba yin nasara akansuba sabida mayakansu nada karfin zuciya gamida juriya da naci da kishin kasarsu zasu Iyayin duk inda zasuyi domin Kare kasarsu

Koda jin haka Sai shamila tanumfasa sannan tadubi shamilu tace duk abinda kafada gaskiyane Amma gaskiya nayi matukar mamakin karumtar najwas. Du ka yau she akahaifi yaronnan Amma haryazama gagarabadau haka gashida dakakkiyar zuciya baisan wani Abu waishi tsoroba Amma babu damuwa zamu hadu akaro nabiyu tabbas saiya rainakansa tazare takobinta tasari iska sannan tayi rantsuwa dagurman mahaifunta akaro nabiyu saitayi gutsin gutsin da sassan jikin najwas koda jin haka Sai shamilu yarungume yar uwarsa shamila yanamai sunbatar goshinta nantake sukayi sallama kowa yaje yakwanta MEGIDA MI KAKEYINE HAR YANZU NA AM UWARGIDA GANINAN ZUWA TO 👉👂KO
DON HAKA SAIDA ANJIMANKU NINEDAI NAKU HAR KULLIN ITZ DAN USTAX NE NAKECE MUKU BARKA DAWAR HAKA GASKIYA FRIENDS INA ALFAHARI DAKU DA GUDUN DAWAR DAKUKE BANI HAKAN KESAWA INTA SUBUR BUDO MUKU POST KULLIN 📝✍️
✊🏾✊🏾TAWAGAR MUTUWA ✊🏾✊🏾GAMON AJALI party Na 011

Gari yawaye duhu yayaye kowa acikin burnin shiram yayi shigar yaki maitsananin kwarjini dabantsoro kowa yashirya tsaf domin afuta filin daga Sarki shaddad kawai Ake Jira yafi to yabada umarni arafi wajen abokan gaba

Kwatsam akabusa wani kaho gamida kida dabushin algaita alamuncewa ga Sarki nan tataho lokacinda Sarki shaddad yafi to ga yarima ahannunsa nadama cikin shigar yaki wannan lokacin najwas nasanyene dawasu kaya nakarfe gamida hular karfe gwata sharbebiyar takobi yarataya abayansa

Ahikuwa Sarki shaddad yayi shigane tabakin sulke gawani zabgegen mashi ahannunsa Kai wannan ahiga dasarki yayi bakaramin kwarjini takara masa ba take Sarki yaje yatsayu agaban dagarunsa yakare musu kallo yatabbatar dacewa yau kowa yafitone dashirin amutu komuma ayi rai

Batare da wani bata lokaciba. Sarki shaddad yabada umarni take akadauki hanya saifilin daga tafiya suke cikin kasaita batare da wata fargaba ko shakkaba. Wasunsu ma harsun kagu SU ISA filin daga. Kawai afidda rainin

Acan filin daga kuwa dakarun shila da shamilu tuni sundade dabayyana domin tunsafe suka iso filin daga dasukaga shuru babu alamuncewa SU Sarki shaddad zasu fito harsun shirya ahiga cikin birnin domin sukashe kowa kwatsam saisuka hango kura gamida buahin algaita donhaka saisuka dakata ahankali kura nailafawa kwatsam saiga tawagar Sarki shaddad tabayyana afilin daga

Nanfa akafara kallo kallo awannan lokacin Ne shamilu yadubi yar uwarsa shamila yace yau aikin namu kadanne da alama dakarunsu dayawa suntsorata shiyasa Basu fito filin dagaba shamila tai murmushi tace da Dan uwanta kada kacika Sakin jiki domin shi yaki Dan zanbune zata Iyayiwuwa wani Shirinne namusamman sukayi mana

Abangaren dakarun birnin shiram kuwa nantake Sarki shaddad yarima najwas sarkin yaki saif suka ahiga gaban dakarun SU sukatsatu tamkar gumaka sunamasu yimusu kallin kaskanci take Sarki yadaga takobinsa yanamai bada umarnin a afkawa abokan gaba take dakaru suka zare makamansu suka sari iska sannan suka ruga aguje izuwa

Please Login or Register in order to submit comment