Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba domin da yasan haka da Bai yanke wannan hukunci ba

Tafiya sukeyi cikin daji dasauri natsawon yini guda batare da sunyada zangoba kuma basije karshen wannan daji ba saida dare yaraba asannan suka fara Zuwa karshen dajin domin sunfara hango hasken fitilu agaban su hakanne yatabbatar musu da cewa sun iso wani babban birnine don haka Sai suka tsaya suka yada zanggo anan gurin da nufin cewa gobe da safe zasu karasa cikin birnin domin guzurinsu yakusa karewa nan take suka kafa tantina suka kwanta suka kama bacci abinsu abinka da gajiyayyu cikin kankanin lokaci bacci yayi awon gaba dasu harda munshari saikace sunkasance acikin birnin su ba acikin daji ba

Basu suka farka ba saida gari yawaye suna farkawa suka Mike sukayi kalaci sannan suka shirya suka nufi wannan birnin gabansu

Acan birnin Sarki dawwaz kuwa tunranar da Sarki dawwaz yakoma birnin sa saiyakasa zaune yakasa zaune domin abinda yake yimasa yawo azuciya shine. Tabbas sunkashe maciji basu sare kansa ba domin shida kansa yatsirata da shaidanci irin nayarima najwas tinda yagari zugar dakarusa har yaraunata yayansa guda biyu wadanda yake da yakinin cewa subiyu zasu iya yakar duniya Amma Sai gashi wannan dan tatsitsin yaro yakarya lagonsu har yayi musu illa tabbas likaci yayi dazai tashi tsaye dakasa domin ganin karshen wannan yaro idan kuwa ba haka to ko shakka babu shine zaizamo sanadin ajalinsa

Lokacin da Sarki dawwaz ya rasa mafita saiyashiga halwar tsafi yadukufa da binciken mafita awannan al amarin Amma saida yakwana arba in sannan yasamu mafita kuma bawata hanyar baceba baface zaidinga aikawa duk wani birnin dayasan yarima najwas zaije can zaibada hotonsa dazarar anhanshi to alama shi zaibada kyauta maitsoka gaduk Wanda yakamo shi yakawo shi gareshi

Al amarin sadauki najwas da ginbiya Hansika kuwa lokacin da suka shiga birnin nan saisuka tarar da birnin acike makil saikace mutanen duniyane suka taru abirnin koda ganin taron jama a Sai najwas yasamu wani matashi yatanbayesa me akeyi acikin birnin nan Sai matshin yace masa ai sarkin garinne yake ahiraya wata gagarumar gasa maitsananin hatsari sunan gasa shine gasar mutuwa
Amarin wannan gasar ne duk karshen shekara. Kuma ita wanna gasa anayinta ne zallar zalincin da zubar dajini kai inta kaicemaka labari anazuba wadansu dakarune masu cin Naman mutane gamida Shan jini su goma wanna dakarun basu da wani abinci Sai Naman mutane don haka awannan gasa duk mutumin da yashiga wannan gasa to sunansa matacce sannan kuma anazuba kudi masu yawan gaske idan jaruminka yalashe wannan gasa to zaka samu dukiyar har jikokinka bazasiyi talauciba

Koda jin haka sai yarima yadubi ginbiya Hansika Amma saitayi masa nunida karyaahiga wanna gasa Bai mata gardama ba Amma yace mata suje suyi kallo kawai suga yada Ake gabatar da gasar batayimasa gardama ba haka suka tafi sukaje suka zauna acen sama wani Gini suna kallo yadda wannan gasar ke tafiya tabbas tinda yarima najwas yazo duniya baitaba ganin rashin imani da rashin tausayiba irin Na wannan rana domin lokacin da suka hau kan wannan Gini lokacin da idon yarima tokasa asannan wadansu dakaru sunkai ashirin suka afkawa wani mutun maikamada dodo suna ihu shikuma Sai dalalar dayawu yakeyi yasamu nama suna isa gareshi suka rufeahi da sara da suka abin mamaki saisukaji Kamar suna saran dutae domin ko kwarzane jikimsa Bai yayi caraf yacafki mutun daya yadagashi sama yayagi wuyansa yacillar dashi sannan yakama wani yayagashi Gida biyu yajifa da gangar jikinsa nanfa yashiga kama jaruman nan yana yimusu mugun kisan gillah sukuwa manyan sarakuna dake wajen kawai kyakyata dariyar mugunta kawai sukayi

Saida wannan aljanin yagama kashe dakarunnan saura guda daya wani saurayine kuma yarone mai karancin shekaru bazai haura ahekara Sha bakwaiba yayar da makaminsa yana Shirin guduwa Amma ina filin agarkame yake dakeji kuma ansa kwado ankulle babu ta inda mutun zaifita saidai tasama kejin santsine dashi mutun Bai isa yakama yahau ba

Nantake saurayin nan yadurkushe kasa ya fashe dakuka yana maineman taimako Amma anrasa Wanda zaikulashi saima dariyar mugunta da suke tayi masa Amma kuwa yankallo tuni wasu sunfara kwallah sabida tsananin tausayin da wannan saurayin yabasu adai dai lokacin wannan aljanin ya isogabansa yana dalalar yawu yakama wuyansa da hannun daya sannan yarike kafarsa dadaya hannu yayunkura zai yagashi nanfa narashin nan yakurma ihu irin Wanda yasaddakar da mutuwa yarufe idanunsa yana kuka

Yayinda aljanin nan yayunkura zai yagashi to anannefa lissafi yacanza domin kawai saigani akayi wani mutun yafado daga sama Kamar anjefoshi take take yazare takobinsa fara sal tana sheki Kil yazabagawa aljaninnin sara agadon baya Kil yaraba tsinanne Gida biyu yafadi kasa ko shurawa baiyiba yabaje kasa matacce gabaki dayan mutanen dake wannan fili saida suka Mike tsaye ba wai iya yan kalloba hatta manyan sarakunan saida suka Mike sabida tsananin mamaki WAYE ZAIGAYAMANA WANENE WANNA JARUMIN TO UWARGIDA TAYI KIRA INAJIN ANGAMA TUWONNE BARI NA LEKA KUNSAN YANZU TUWO YAFI NAMA 🤪🤪🤪NINE DAI NAKU har kullin Itz Dan ustax Ne nake cemuku mukwana lafiya✊✊TÆWÆGÆR MÛTÛWÀ✊✊ GÆMØÑ ÁJÄLÎ party na 017
.
Bawani bane bafa wannan jarumin face sadauki najwas yayinda yakashe wannan aljani saiyayi carf yacafe wannan saurayin yafado hannunsa Sai najwas ya ajiyeshi bisa kasa sannan yadubi tawagar manyan sarakunan saiyaga duk sunmike fuskarsu amurtuke babu annuri
Amma dayayi duba izuwa kan yan kallo da kuma talakawan gari yaga sunata daga masa hannu gamida yimasa jinjina nandanan yarima yaji sanyi acikin ransa sannan yakama hannun saurayin nan yajashi dimin sufuta daga cikin kejin nan

Yayinda dayaje daf daf dakofar kejin tofa anannefa yaji wani irin mugun gurnani abayansa Wanda Bai taba jiba dasauri ya waiga aikuwa saiyayi arba da irin wadannan halittun daya kashe guda Tara atsaye abayansa kawai saiyayi Kamar Bai gansuba dama da wutsiyar Ido yakallensu saiyacigaba da tunkarar kofar kejin yakama zaibude Amma saiyajita agarkame
Yakalli manyan sarakunan saiyaga saiyumasa dariyar mugunta sukeyi nanfa sadauki najwas yafusata ainun baisan lokacin da yasa kafa yadaki kofar ba take kofar tafada dakarfi kura tatashi sama yarima yayunkura zaifita Amma saiyaji wani Abu Kamar igiya yadaure masa wuya tadagashi sama yanareto akasa yarima yayi kokarin kwacewa Amma yakasa al amarin daya dugunzuma hankalinsa kenan yayi duk inda zaiiyi Amma yakasa kwacewa

Yayinda yawaiga yaga menene yayimasa wannan shaka aikuwa saiyaga bawani Abu bane bafa Sai wadannan halittun kuma wannan igiyar harshene nadaya daga cikin su kuma alokacinne wannan halittar tazuko yarima tana mai wangame baki Kai kace kofar garice danufin ta hadiye najwas aikuwa tuni sadauki najwas yagama ayyana yanda zaiyiwa halittar nan mummunan kisa

Domin lokacin data zukoshi yayinda yazo daf dabakinta kawai sai yazare farar takobinsa mai suna GAYAWA JINI NA WUCE yazabgawa harshen nan sara dadukkanin karfinsa tuni yasare harshen yarima yafado kasa sharaf yayinda ahukuma wannan aljanin yafadi kasa yana matagun namutuwa kafin cikar dakika biyar yace gagarinku nan tuni yasandare

Al amarin da fusata sauran kenan suka ihu suka ruga izuwa kan sadauki najwas domin sudaka masa wawa koda ganin haka Sai yarima yayi sauri yakama hannun saurayin nan yacillashi waje sannan yajawo kofar yarufe ta bam yajuya ya fuskanci wadannan halittun yayinda suke dada tunkaroshi aisai Shima yazare takobi yasari kasa sannan yaruga da gudu izuwa kan su yayin da yarage baifi saura taku gomaba atsananin su saiyadaka tsalle daga inda yake yadira atsakiyar su aikuwa Sai suka kacame da azabebben bakin artabu maitsananin muni domin suna kaimasa sara dasuka dafaratansu gamida harsunasu shikuwa yadage domin Kare kansa gamida maida zazzafan martanin aikuwa cikin kankanin. Lokaci suka tashi hankalin kowa dake fadar nan

Tabbas mutane aunsha mamaki matuka bisa gagarumar jarumtaka tasadauki najwas domin a Iya tarihi wadannan halittun basu taba yin yaki natsawon dakika sittinba komai yawan mayaka acikin kankanin lokaci suke gamawa dasu Amma Sai gashi yau dan tatsin bil adama yana nema yagaresu atsawon dakika sittin don haka saisuka fusata suka feso masa wata farar wuta Amma yarima yana gocewa yakauce nan yazille nan Amma fa duk da haka wutar tana tabashi kuma duk inda tataba saita konashi aikuwa nandanan suka haukata yarima suka rikatashi tahakanne daya daga cikin su yasamu damar zabgamasa duka da har Shen sa aikuwa saida yaje yabugo yabugo bangon kejin sannan yafado kasa sharaf ruf daciki komotsawa baiyiba

Koda ganin nasarar da wadannan halittun suka samu sai manyan sarakunannan suka kama yin dariyar mugunta har sunasuna tafawa sukuwa yan kallo tuni hankalinsa yatashi sunfara tausayin yarima najwas kuma gashi wadannan halittun suna kara kusantarsa suna dalalar dayawu

Harsuka iso ga sadauki najwas Amma. Ko alamar motsi babu atattare dashi yayinda suka iso daf dashi saidaya daga cikin su yasa yadurkusa danufin yayagi jikin yarima

Hamm hakika rashin sani yafi dare duhu domin duk wannan Abu da halittunnan sukeyi yarima yana kallon su kawai lokacin da aljaninnin yakai bakisa ga daidai wuyan yarima aikuwa Sai sadauki najwas yayi zunbur yamike kafin kace me tuni ya lafkawa aljaninnin takobi awuya aikuwa Kil yacirewa tsinanne Kai kansa yasama yafada tsakiyar yan uwansa yayinda gangar jikinsa tafadi can gefe guda

Aikuwa Sai gabaki dayan yan kallo suka kaure dashewa gamida ihu suna yiwa sadauki najwas jinjina gamida yimasa tafi nandanan yaji wani sabon karfi yashigeshi yadaga kansa yakalli sama inda yabar ginbiya Hansika kawai saiyaga tadago masa hannu tana maiyimasa murmushi Wanda yasa yaji anyi masa bushara dacikar burinsa naduniya don haka kawai saiyajuya cikin kwarin guywa ya fuskanci ragowar halittunnan yayinda suka kura masa idonsu jajawur Kamar angasa danbuda awuta TO NAGAFA SUNA KALLONA BARI NABOYE KADA SUZACI NINE YARIMA SUYI KALACI DANI SUBAR UWARGIDA DA HAWAYE KOBA HAKABA UWARGIDA 🤪🤪KARKU MANTA NINEDAI NAKU HAR KULLIN ITZ DAN USTAX NE NAKECE MUKU ASUBA TAGARI✊✊TÆWÆGÆR MÛTÛWÀ✊✊ GÆMØÑ ÁJÄLÎ party 018

Lokacin da akayi kallon kallo Na yan dakiku tsakanin sadauki najwas da halittunnan Sai sukayi kukan kura gamida. Bugan kirjin su suka kalli gawar yan uwansa guda biyu sannan suka dubi sadauki najwas saisuka sari kasa da mahaukatan faratansu Kanan suka ruga da gudu izuwa kan sadauki najwas koda. Ganin haka Sai Shima sadauki najwas yasari yajuya takobinsa sanna yaruga aguje domin ayi gamon karshe maitaken mutuwa dole

Amma acan bayan filin gasa kuwa al amarin manyan sarakunantun nan tunda sukaga yarima najwas yayi nasarar hallaka azzaluman dakarunsu guda biyu saisuka shiga tattanawa akan yadda zasu biyo suga bayan wannan yaro domin sun fahimci cewa indai akaci gaba da wannan yaki to babu shakka Sai yakarar da wadannan halittun kuma indai hakan yafaru to tabbas zai karya musu tattalin arzikin dasukayi ahekara da shekaru suna samun makudan kudade ta dalilinsa

Suna cikin wannan tattanawa ne tsakanin su su goma Sai sarkin wannan birni Wanda akeyiwa lakabi da Sarki husal yadubesu yace akan wanna dan tatsitsin yaro kuke wani damun kanku hhhhh yayi dariya yace lallai kunba ni kinya ace duk jarumtarku gamida hatsabiban cinku gimida izzarku ta sarauta amma. Kuke tsoron wannan dan tatsitsin yaro lallai bantaba tinanin cewa Ku shashaa shai bane saiyau

Koda jin haka sai sauran sarakunan suka kama kalle kalle gamida jin kunya don haka Sai suka zuba idanu domin ganin abinda zai wakana acikin wannan gasa

Acan cikin keji kuwa kuwa yayinda akai mugun gamo tsakanin sadauki najwas da wadannan halittu Sai sadauki najwas saiyanuna musu cewa shi mutunne ba dabba lokacin da suka iso daf dashi saiyadaka tsalle sama gamida zare takobinsa kafin su daga kawunansu yadiro asamansu aikuwa baijira komai yakai sara gabas da yamma sai akaga kawunan guda uku yana yawo Asama yayinda yadira akasa saiyasa takobi yasare kafafuwan guda sanna yasa takobi yasoke musu makogwaro babu shiri suka zarce lahira

Tofah sai sauran guda ukun suka fusata nantake suka hadu waje guda sannan suka fesowa sadauki najwas wata farar wuta aikuwa Sai tatawo gareshi aune sadauki najwas ko gezau baiyiba yayin da wutar ta iso gareshi saikawai yamike takobinsa aikuwa wutar natabar takobinsa saita dinga shigewa ciki harta shige ciki gabaki dayan ta sai yarima ya kurma ihu sannan yanuna wadannan halittun da takobinsa aikuwa saiga wutar nan tafuto baka kirin tayi kan halittun nan aguje sunyi iya kokarinsu domin kawuce wutar nan Amma ina aibasu isa suja da ikon gwaniba domin tuni wutar takamasu takoneau kurmus ko tokarsu babu aqajen

Koda ganin wannan nsara sai mutane yan kallo masu son sadauki najwas suka kaure da shewa gamida tafi yayin da wannan saurayin da sadauki najwas ya ceci rayuwarsa yarugo da gudu izuwa cikin kejin yayinda ya iso daf dashi sai sadauki najwas yadaukeshi cak yana maijuyashi Asama yasunbaci goshinsa saurayin nan yamikawa sadauki najwas Hanu suka tafa sannan suka dunkule hannu suka hada hannuwa alamun sunzama daya

Nantake yan kallo suka kara kaurewa da shewa wasu suka shigo ciki suka daga sadauki najwas sama suna maiyi masa jinjina suna juyashi itama gimbiya Hansika ba tasan lokacin da turo daga inda takeba tazo daf da sadauki najwas tana daga masa hannu shikuwa yakura mata idanu ko kiftawa bayayi

Wannan al amari yayiwa manyan sarakunan nan ciwo don haka saigani akayi guguwa tatashi tarufe ko ina acikin filin harba iya ganin komai koda ganin haka Sai hankalin kowa yatashi yayinda sadauki najwas yarike wannan matashin da hannunsa nahagu yarike ginbiya Hansika da hannun dama sannu ahankali sai guguwarna nan tayaye komai yafito fili aikuwa Sai hankalin mutane ya sunzuma ainun domin arba da abin dake zake dasu manyan sarakunan nan ne augoma kowanensu cikin gagarumar shigarsu yaki Sai muzurai sukeyi fuskarsu hartanayin wani yatsimewa sabida da fusata yayinda sadauki najwas yaga haka kawai saiya yabude kofa kowa yafuta sannan yafuskanci manyan sarakunan nan TABDIJAN NAGA YARIMA NAJWAS YANA KALLONA BARI NA FECE KAR YAMAKENI DASANDA YABAR UWARGIDA DA KUKA TONI KAGA TAFITAMA UWARGIDA TANA KIRANA

KAR kumanta nine dai naku har kullin Itz dan ustax Ne nake cemuku barka da safiya✊✊ TÆWÆGÆR MÛTÛWÀ✊✊ GÆMØÑ ÁJÄLÎ party na 019

Lokacin da wannan bakar guguwar ta kewaye ko ina acikin filin sai hankalin jama a ya dugunzuma ainun suka kama koke koke da iface iface saida aka dauki lokaci mai dan tsawo ahaka sai wannan guguwar ta fara yayewa sannu ahankali hasken yafara futowa harkomai yafito fili nanfa hankalin jama a ya kara tashi sabida ganin manyan azzaluman sarakunan guda goma sun kewaye kejin cikin damarar yaki mai matukar kwarjini daban tsoro

Koda Ganin wannan yanayi sai sadauki najwas ya tabbatar babu lafiya don haka Sai yabude kofar kejin nan kowa yafita waje Amma banda ginbiya Hansika da kuma wannan matashin shidai wannan matashin yana bayan sadauki najwas alakube itakuwa ginbiya Hansika tana bisa kusa da sadauki najwas. Abangaren daman sa tazare takobinta tariketa da hannu biyu tana Jira taga ta inda za a fara

Shikuwa wannan wannan matashin saiyarike hannun sadauki najwas yace yakai dan kada kabari wadannan azzaluman sarakunan susake daukeni domin azzalumaine shekarata goma suna azabtar Dani koda jin haka sai sadauki najwas yakara kakkame hannun matashin nan sosai

Nantake manyan sarakunan sukadubi sadauki najwas suka daka masa tsawa Kai yaro wanene Kai da har zaka shigo har cikin birnin mu kace zaka kashe mana dakarunmu masu tsananin tarihi kasani tabbas munason sanin kokai waye kafin mukasheka

Koda jin haka sai sadauki najwas yayi dan guntun murmushi maikama dayake yadubi sarakunan nan yace sunana yarima najwas bin shaddad daga birninin shiram birnin da Sarki dawwaz yaje yaci dayaki yarugujeshi nikadaine mutumin dayatsira awannan birni kusani cewa banshigo burnin Ku domin yaki dakuna hanyace tahadani da birninku guzirinmu yakusa karewa shine muka shigo domin musayi guziri muwuce saimuka ana wannan gasa mukatsaya kallo

Kuyi sani cewa banshigo wanna gasa domin komai ba face sabida wannan kazamar gasar taku tayi muni dayawa zalincin yayi yawa nikuma ba a zalinci agabana nagani nakyale shiyasa nakashe wadannan halittun domin banga anfanininsu ba

Koda manyan sarakunan nan sukaji cewa wannan shine yarima najwas Wanda maigirma Sarki dawwaz yabada kwangilar akamoshi sai farinciki yakamasu suka dubi yarima najwas sukace ka tafka babban kuskure domin dama farautar ka mukeyi zamu dankaka ga maigirma Sarki dawwaz

Suna gama rufe bakin su Sai kowane Sarki yadakawa dakarunsa tsawa yace kukama manashi araye ko amace domin cika umarnin shugaba

Wohoho nanfa kowane Sarki dakarunsa suka zare makamai sukayi kan sadauki najwas akallah kowane Sarki yanada dakaru kimanin dubu goma Amma gabaki dayan su suka rufawa yarima sabida mugun nufi

Shikuwa sadaukin Maza najwas yayinda yaga zugar mazaje sunnufoshi da farko yayi nufin yagudu badon yanajin tsoron yawansuba aa kawai shi bayasone yazubar dajinin al umma domin ba al adarsa bace

Amma Sai yafasa sabida tuna cewa Sarki dawwaz yaturosu sukamashi kawai sai yatsaya kikam kamar gunki nantake yakama hannun saurayin nan sannan yakama hannun ginbiya Hansika yadanka matashi yace wannan yaki banaki bane nawane don haka kama kirike shi kukoma inda muke azaune kizama yar kallo tabbas yau zannunawa mutanen duniya cewa nisaduki kuma namijin dayagaji jarumtaka domin bahaye nayi ba gadone

batayi masa wani masuba takama hannun matashin nan tacilla igiya sama nandanan tahaye sama tasamu wuri tazauna Amma hankalinta Bai kwantaba sabida yawan dakarun tana ganin Kamar zasu iya hallaka shi dukdadai tasan Shima ba kanwar lasa bane Amma ai sarkin yawa yafi Sarki karfi saidai sarkin karfin yafishi dabara

Yayinda dakaru kimanin miliyan daya suka ruga izuwa kan sadauki najwas domin cika umarnin iyayen gudansu sai sadauki najwas yazare takobi guda da takobinsa ta asali wacce akeyiwa lakabi da GAYAWA JINI NA WUCE sannan Kuma yazare takobin da hayagada ahannun mahaifinsa
Yahada biyu hagu da dama sanna yaja dabaya taku goma hakika Jada baya ga rago ba tsoro bane Shirin fadane

Saida yarage saura baifi taku goma ba dakarun nan suriskeahi kawai saiya kurma ihu maitsananin firgitarwa irin Wanda ke tarwatsa Maza afilin daga yadaka tsalle tamkar tsun tsun yadira atsakiyar su

Wohoho nanfa yafara sauke musu wutar Bala I kasuwar tafara baje kolinta mutuwa tafara shawagi afilin nan

Sadaukin najwas yahaukace kawai kisa yake tamkar mai sassabe agona duk lokacin da ya kurma ihu yahada takubbansa giri daya saikaga wani haske fal saikaga dakaru sama Dari suntashi sama sun fado mace cikin abinda baiwuce sa a daya da rabiba sadauki najwas yatarwatsa dakarun nan yahanasu sakat akallah yakashe kaso hudu acikin gomansu kuma jiyake tamkar yanzu yafara yakin

Dabala i yakai bala I gabaki daya wannan kejin ankakkar yashi ko ina koface yayinda hankalin yan kallo yatashi domin. Gani suke Kamar akoda yaushe dakarun nan zasu iya yin galaba akansa

Amma al amarin manyan sarakunan nan kuwa da farko sunata kyakyata dariyar mugunta Amma dasukaga sadauki najwas nayi dakarunsu kisan kiyaahi tamkar basu kasance mutaneba sai hankalin su ya dugunzuma suka kasa tsaye kozaune domin sun tabbatar dacewa idanfa akaci gaba da wannan yaki ahaka babu makawa sadaukin najwas zai Iya karar dadakarunsu gabaki daya kuma idan haka tafaru to suma basu da tabbacin zasu iya kamaahi

Tabbas yanda sukayi zafin yarima najwas yawuce nan acan cikin kejin kuwa abin yakazanta yamunana yarima yasamar dakogin jini gamida bolar gawar waki duk inda yawaiga babu abin dakake Gani face gawarwakin bil adama rutu babu kyangani wasu babu hannu wasu babu kafa wasu kuma gangar jikinsu akaraba Gida biyu

Kai inda ace mutun baya gurin akayi wannan yaki idan akace dashi mutun dayane yayi wannan barna bazai taba yardaba sabida abin yafi karfin tinani

Yayinda dayarima yaci gaba da ragargazar dakarun sukuma basu dena afka masaba tamkar ba kashesu akeyiba kyauta akebasu shikuwa sadaukin najwas badaina aikasu kiyama

Saida akasa ke daukar sa a guda cir sannan dakarun nan suka fara tsorata da lamarim sadauki najwas don haka Sai wasunsu suka fara ja dabaya suna guduwa domin ceton rayuwarsu shikuwa sadauki najwas duk Wanda yaga yaja dabaya to kyaleshi yakeyi

Koda manyan sarakunan sukag haka saisuka dakarun su tsawa suna masu basu umarni sujadaya aikuwa babu gardama duk sun jigata gashi ankashe kaso bakwai acikin gomansu

Nantake suka koma hefe suna haki Kamar ransu sannan ne manyan sarakunan nan sukayi layi agaban sadauki najwas suna masu yimasa wani irin kallo maikalmada Anya wannan bil adama ne kuwa

Shikuwa sadauki najwas saiya daka musu tsawa yace La anannu tsinannu tanbadadu kuyi sani cewa nafi karfin kura bata farautar zaki saidai zaki yayi farautar kura kusani nafi karfin aturo kananan jarumai sukamani saidai shi Uban gidannaku yazo dakasa

Tom anan zantsaya NAJI UWARGIDA NAKIRA bari naleka ko angama dumamen safe

Naku har kullin Itz dan ustax Ne nake cemuku barka da safiya✊✊TÆWÆGÆR✊✊
MÛTÛWÀ
GÆMØÑ
ÁJÄLÎ
Party Na 020

Koda manyan sarakunan nan sukaji furucin sadauki najwas gamida cika bakinsa sai suka hassala suka kumbura suka cika suka batse shugaban su maisuna rauzuf yadakawa yarima najwas tsawa Kai yaro kake kaje da ikon manya kayi sani cewa yaudinnan ko mahafinka ne Sarki shaddad yadawo diniya yàshigo wannan da ira ban isa yatsira ba ballatana Kai karamin alhaki kayi sani cewa yaune ranar muruwar ka acikin wannan birni zokayi mutuwar wulakanci domin gawarka ma bazata samu gatan binnewaba dodanni zamu zubawa sucinye ka

Koda jin haka sai yarima ya yakarkare yakurma Uban ihu Wanda yarazana ilahirin yan kallo bama iya suba hatta manyan sarakunan nan saida suka razana azuci Amma basu numaba azahiri

Nantake sadauki najwas ya amurtuke fuska sannan yayi wani dan guntun murmushi yadubi sarakunan nan yanunsu da takobi yace a inda babu kasa anan Ake gardamar kokawa gafili ga mai Doki Sai muzuba mugani idan kuma narantse nikuma narantse da Sarki dayake busamun nunfashi ayau sanamayar Daku tarihi

Koda jin haka sai manyan sarakunan nan suka fusata suka kurma ihu atare suka zare takobi danufin su afka ma sadauki najwas sai Sarki zairuf yadakatar dasu yace abin kunyane mutaru gabaki dayanmu mu yaki wannan dan tatsitsin yaron don haka mutun dayane zaije yagama mana dashi

Nantake mace maikirar mutanen farko gata amurde kaidaanin ta kasan karo da Ita ba abin mai saukiba anakiranta da sarauniya yazrina takasance matsafiya hatsa bibiya kuma shaidaniya wacce sabida hsaidancinta Mafi yawan mutane sunfi kiranta sarauniyar mutuwa ta kasance azzaluma mara imani domin sabida rashin imaninta hatta mutanen birnin sungaji da wannan zalincin nata kawai don babu inda zasuyi da itane domin idan sunce zasuyi yaki da Ita to bazasuyi nasara ba sabida ita kadai tana iya Zuwa tafarwa birni guda cikin abinda baiwuce yini gudaba take gamawa da shi tadebe. Dukiyar su sannan takame mazajensu da matansu masu kwari ajika amatsayin nayi tabbas karoda sarauniya yazrina bakaramin bal balin bala I bane

Lokacin da sarauniya yazrina tashigo gaban manyan sarakunan nan sai sauran suka koma sukazauna bisa wasu kujeru Na alfarma. Suka zuba Ido yayinda da sarauniya yazrina tozo daf da sadauki najwas sai yakasance babban cinsu abayyane yake domin yanda kasan an ajiyae bera agaban katuwar kyanwa haka. Babban cin jikinsu yake

Tabbas yakadu daganin wannan halitta tinda yazo duniya baitaba ganin mutun mai irin wannan kirarba Amma ko kadan baiji tsoron ta yadarsu aransa ba hasalima kallon raini yakeyimata

Koda akayi kallon kallo Na yan dakiku tsakanin sadauki najwas da sarauniya yazrina sai dukkanin sukaja da baya taku goma sannan. Suka rugo aguje izuwa kan juna suna hadu ruguntsume da azabebben yaki tabbas gaba da gabanta wai aljani yataka wuta tabbas sarauniya yazrina tayiwa sadauki najwas tazara maiyawa tabangare daban daban tafishi karfin damtsen gamida zafin nama tafi juriya da naci tafishi karfin sihirin tsafi takowane fanni sarauniya yazrina tayiwa sadauki najwas Nisa do haka cikin kan kanin lokaci tayi kacaca dasai dakarfin dantsen ta da kuma wata Shar bebiyar adda nandanan sadauki najwas yafita hayyacinsa domin yahada masa jini da majina tayimasa manyan raunuka har guda bakwai

Sabida tsabar bala I ylsadauki najwas bansa sadda yasaki talobinsa tafadi kasaba sarauniya yazrina tabankeahi da kafa yaje yagauro bango yafado kasa yana. Aman jini tabaki ta tahanci nantake sarauniya yazrina tadako tsalle tadira gaban da tadubi gabas tadubi yamma tadubi kudu tadubi arewa tace ina masiyan yarima suke to kuzo gashi nan zaiyi masa kisan wulakanci idan akwai Wanda ya isa yazo yadakatar Dani nikuma narantse da karfin tsafina sainayi gunduwa gunduwa dasassan jikimsa

Awannan lokacin ginbiya Hansika nacan sama tana kallon abin dake Shirin faruwa Amma takasa motsawa sabida sadauki najwas yayi gargadeta akan ko Gani

Please Login or Register in order to submit comment