Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kan abokan gaba

Koda ganin haka Sai shamila da shamilu suka zare makamansu suma suna masu bawa dakarunsu umarni take suma suka ruga izuwa kan abokan gaba suna ihu suma sauran Na ihu ahaka akahadu atsakiya jikake rakwacam take aka ruguntsume da azabebben bakin artabu maitsananin muni da bantsoro tabbas wannan rana kasuwar rayuka tayi bajakolinta domin sabida tsabar masifa saikaga dakare babu hannu ajikinsa Amma ahaka baisareba kara kutsawa yake cikin abokan gaba

Lokacin da aka dauki sa a guda. Anayaki saidakarun birnin shiram suka fara gajiya koda fahimtar hakan Sai akabusa kaho suka yo baya dagudu hakan kuma yasa dakarun Sarki dawwaz sukayi tinanin kosun tsoratane donha ka sukadinda bimsu dagudu

Kash rashin sani yafi dare tabbas dasunsan abudake Shirin faruwa tabbas dabasuyi ganganci binbayansu domin lokacinda sukayi Nisa saikuma yarima najwas yazare farar takobinsa yakurma yana maibada umarni take wasu dakarun suka afka. Musu dagudu yarima yatashi sama baidira ako inaba saigaban dakarun Sarki dawwaz yanadira ya afka musu nasara dasukabm babuji bagani badodo ba aljani ko bil adama. Duk Wanda yasara lahiri kawai yake zarcewa nandanan najwas yahaukata dakarun yatakurasu domin wasunsu sunyi imani yarima bamutun bane domin kolakutar jikimsa sukasa hakanne yasa suka fara jadabaya gareshi suna afkawa dakarunsa kayya aifaruwar hakan kuma yasa shamila da shamilu suka fusata atare suduka suka kurma ihu sukai kan sadauki najwas ahaukce shikuwa. Najwas tinda yahangosu saishima yayi Kansu rike da zabgegiyar takobinsa mai taken GAYAWA JINI INWUCE tana wani sheki yayinda. Idanunsa kefitar da wani haske Wanda yayi sanadiyyar firgitata nazube kasa sumamme
HAKANNE YASA UWARGIDA TAYI WUF TADAUKENI SABIDA KAR DODANNI SITALITSENI

NInedai naku har kullin itz Dan ustax Ne nakewa kowa fatan alkhairi mai dorewa✊🏾✊🏾TAWAGAR MUTUWA GAMON✊🏾✊🏾 AJALI PARTY NA 012................. .

Lokacin da yarima najwas yaruga izuwa kan shamila da shamilu aguje cikin wannan yanayi saisuma suka fara amfani dakarfin tsafin SU take takobinsu yayi wani jan haske mai firgitarwa lokacin dasuka hadu da yarima saisukai masa wani wawan Sara cikin bakin zafi nama najwas yayi kasa saran yawuce kafin yawaigo shamilu ya shammaceshi yagabza masa naushi agadon abayansa saida yatashi sama yaje yabugo wata katuwar bishiya yafado kasa Tim kafin yayi wani yunkuri shamilu yanunashi da Dan yatsansa nahagu tuni wata igiyar tsafi tabayyana jikin yarima tadaure shi tamau hatta nunfashima dakyar najwas yakeyi haryafara kakarin mutuwa

Koda ganin haka Sai hankalin najwas yayi mummunan tashi domin da yayi yunkurin tsinka igiyarnan saiyaji tamkar tana zukar jinin jikinsa dole yarima najwas yasadu da yakaamu hhhhh shamilu yabushe dadariyar mugunta yace tadai yaro bana gayaamaka ba karo nakar she bazaiyi maka kyauba kuma gashi akaron farko kashiga tarkona dama banzo birnin Ku domin nahallaka ba naxone domin kawai inbajeshi kuma indaukeka inkaika ga mahaifina donhaka nagama aikina nafarko bari nakarasa nabiyu

Yana gama dadin haka Sai yadubi yar uwarsa shamila suka bushe dadariyar mugunta atare sannan suka zare makamansu suka ruga izuwa kan abokan gaba suka fara ragargazasu Kamar Kamar masu barna agonar audiga faruwar hakanne yasa tawagar Sark shaddad suka motsa gabaki dayansu suka afko cikin filin daga aka rungutsume dayaki mai matukar muni hatta nida nakeyimuku tipyn din badon inada dakakkiyar zuciya ba datuni natsure da zawa Amma haka nadaure naci gaba

Lokacin da aka ruguntsume dayaki yazamana cewa bakajin komai Sai ihun mazaje gamida kururuwar su duk inda kawai ga gawarkine birjik tamkar tayi hakan filin yayamutse bakyan Gani Sarki shaddad da manyan jarumansa kutsawa kawai suke cikin abokan gaba domin kaiwa yarima dauki Amma Abu yafaskara

Domin dakarun Sarki dawwaz sunkasa suntsare Tako ina sabida har yanzu sunninka dakarun birnin shiram sau biyar hakanne yasa komai yalalacewa su sarki shaddad

Al amarin shamila da shamilu kuwa abinnasu yakanzanta yamunana domin kawai kisa suke tamkar masu kisan kiyashi Kai daga karshema dasukaga wankin hula zai kaisu dare Sai suka fara amfani dakarfintsafi take gurin gabaki yayi duhu ba a Iya ganin komai ko dan yatsanka kadaga sama bazaka ganshiba tawannan hanyane suka samu nasarar yiwa dakarun birnin shiram kisan sunkuru

Domin lokacinda akadauki lokaci mai dan tsayi ahaka Sai komai yafara lafawa sannan kuma wannan duhun yafara yayaye wa yasalam lokacin da haske yabayyana to alokacin nefa lissafi yacanza domin gabaki daya dakarun birnin shiram babu ko mutun daya atsaye hatta Sarki shaddad sarkin saif dasauran manyan jarumansu duk suna kwqnce cikin jini

Awannan lokacin kuma yarima yadade dasume wa donha ka Bai Masan make faruwa ba Amma al amarin shamila da shamilu kuwa takawa suke cikin izza dakarunsu nayi musu kirari girmankai yana kara shigarsu sunata zagaya filin daga harsukane inda Sarki shaddad yake kwqnce magashiya dakyarma yake Iya nunfashi shamilu yasa hannu yadago Sarki shaddad yakura masa Ido sannan yabushe dadariyar mugunta yatofa masa yau yqce dashi maina gayaamaka dakabi umarnin mahaifina dayanzu bakayi wannan asarar ba gashi yanzu girmankai yajanyo maka karasa jama arka karasa danka kuma gashi zaka rasa rayuwar ka

Cikin karfin Hali Sarki shaddad yamotsa bakinsa yace har yanzu yaki baikkare makaba tinda haryanzu Dana yarima yanaraye tokasani najwas koda zaka kaishi bangon duniya ka kulleshi akasa tabakwai indai kainiyyar cutardani to tabbas saiya zo gurin domin yahukunta ka idan kuma kana shakka to kajarraba cutardani kagani

Shamilu yabushe dadariyar mugunta sannan yace to bari mugani yada takobinsa yasari Sarki shaddad agadon bayansa sarki shaddad yakurma ihu ihun da yakarrade dajin gabaki daya har yazuwa inda yarima kekwance sume ahankali yarima yaji wannan karar firgit yabude aikuwa yana budewa saiyayi to zali da shamilu yana Shirin saren kan mahaifinsa wuf najwas yamike tsaye sannan sannan yakama sarkar da aka daure shi yatsinkata da karfin tsiya yanamai kwallah wata irin kara

Cikin hanzari shamilu da shamila sukawaiga suka ga yarima atsaye yatsika sarkar dasuka daure shi yayi jifa da Ita Sai mamaki yakama su shikuwa najwas kawai mahaifinsa yake kallo yanzu bar dahawaye Sai shamila da shamilu suka dakawa dakrun dodanni da alhaji suna masucewa Ku afka masa kuksheshi nanfa kimanin dodanni dubu gomane sukayi kan najwas

Afusace najwas yatsigo gashinsa guda yayi masa wani tofi saiga wani haske yabayyana ahannunsa sannu ahankali haske yarikide yazama wata farar sanda najwas ya juya sanda nan yai kururuwa yai kain dodannin haukace TABDI LALLAI TSUGUNE BATA KAREBA TUNDA AKA CURO WANNAN SANDAR LALLAI DASAURAN TSALLE GASHI KUMA NAJI UWARGIDA NAKIRA INAJIN ANGAMA TUWONNE BARI NA LEKA

Nine dai NAKU HAR KULLIN ITZ DAN USTAX NE NAKECE MUKU BARKA DAWAR HAKA✊🏾✊🏾TÆWÆGÆR MÛTÛWÀ ✊🏾✊🏾GÆMØÑ ÁJÄLÎ party Na 013................ .,.labari ya isomin cewa
Lokacin da sadauki najwas yaruga izuwa kan tawagar dodannin nan suma sausuka kara kaimi domin sucimmasa suyimasa rufdugu sukuma su shamila da shamilu saisuka zama yan kallo kuma suka kasance cikin tsananin razana sabida ganin wannan sandar ahannun sadauki najwas tabbas da mahaifinsu yasan tana hannunsa to sandar zaiturosu sukarba Amma ba yarima Dan haka yanzu gabaki daya lissafinsu yacanza akwai bukatar sukarbe wannan sandar daga hanunsa Amma tayaya hakan zai faru tabbas dasauran aiki agaban su

Shikuwa sadaukin Maza najwas yana ISA inda dodannin suke saitafara juya wannan sanda takowane bangare saidai kaga dodannin da aljanu natarwatsewa tamkar ana nikasu ainji shikuwa yarima kara ragarzar su yakeyi babuji babu Gani kashesu yakeyi Kamar maikashe kwari Amma Kamar yana kara musu yawa dada tittidowa sukeyi Kamar daga sama akeyin ruwansu shikuwa baigaji dakashesu ba Amma babban burinsa yaje inda mahaifinsa ke kwance domin yatabbatar yana matukar bukatar taimakon gaggwa ahaka yarima yacigaba dayaki haryafara gajiya Amma halittun nanna Basa raguwa Kamar ma karuwa suke

Koda sadauki najwas yafuskanci abin dake faruwa kuma yatabbatar yafara gajiya Sai hankalinsa yadugunzuma ainun fiye dako yaushe yafara tinanin mafita abinda yafara ayyanawa aransa shine idanfa haryasake wadannan halittun sukayi nasara akansa shikenan birnin su yazama babu ko mutun daya dazai rayu dimin yatabbatar gabaki daya dakarun su sunkare gabaki dayansu saidai masu rauni ajika wadanda babbancinsu da matattu kadanne

Dan haka saiyarima yakar zagewa Amma Abu Kamar yana kara musu yawa yarima najwas yafisata ainun yakwarara wani wawan ihu Wanda yasa gabaki daya dajin saida ya amsa kuwa hatta wadannan halittun suka razana suka jadabawa suka zuba masa idanu suna muzurai Kamar suci babu

Yarima yawaiga can gefensa tahango mahaifinsa kwance Kamar gawa sannan yahango shamila da shamilu saifamar yimasa dariyar mugunta sukeyi nanfa yakara fusata yafara tinano lokacin da aljanan Nan take bashi Soron yaki da wannan sandar tace dashi wannan sandar duk duniya babu abinda bata tasiri ajikinsa duk abinda kaga taki tasiri ajikinsa to babu ruhi ajikinsa

Koda ayyana hakan Sai najwas yayi murmushin farin ciki yagane cewa wadannan dakarun basu daruhi wani yake sarrafasu dan haka saiyadaga sandar sa sama yayi wani surutu aifaruwar hakan kedawuya Sai sandar tayi wani haske baijiraba yadoki kasa dasandar take wani haske yamamaye fili gabaki daya harba iyaganin komai lokacin da akadauki dan lokaci ahaka sai wannan hasken yafara yayewa sannu ahankali hasken yaye wohoho aikuwa Sai su shamilu suka ahiga rudani dimin gabaki dayan halittunnan sunzama gari Sai yarima najwas atsaye atsakiyar garinsu rike da sandar sa ransa abace

Najwas yadubesu yace yadai kananun jarumai kuna mamaki ko to wannan ba abin mamaki bane saikunga inda zanyi gutsin da sassan jikinku kuma har cikin birnin Ku saina ahiga nakashe kowa dakomai saina dau fansar jinin jama ata akan mahafinku kuma saina shafe gabaki dayan birnin Ku daga doron kasa Kamar yadda mahafinku yashirya yimana tabbas kunyi nasarar kashe dakarun birnin mu domin hatta mahaifina bana tsammanin yana raye kuma koda yana raye yatabbatar dacewa bazai kara kwanaki masu yawa aduniya ba yanzu zanhuce takaici NA akanku kafin naahiga birnin Ku kuma kusani nayi alkawarin bazan kahseku ba Sai agaban mahafinku domin idan yaji radadin da Ake Ji idan akakshewa mutun dan uwansa kila yarage zalincin da yake yi

Hhhhh shamilu da shamila suka bushe dadariyar mugunta atare sannan suka dubi yarima najwas sukace Kai mahaukaci kasan mwkake cewa kuwa to idanma mafarki kakeyi to takamafa kafarka domin abinda kafada har abada bazai taba yiwuwaba don yanzu nan zamu kama ka muwuce dakai wajen mahaifinmu dimin yayankaka yabawa gunki jinin ka

Wani irin tukukin bakin cikinee yaturnuke najwas baice dasu komai ba kawai saiyaski sandar nan bat tabace tamkar baitataba wanzuwa afurin babu Wanda ya isa agurinnan yace yaga inda sandar taahiga

Yarima najwas tazura hannunsa abayansa tacuro wannan sharbebiyar takobin fara Sol baijira komai ba yazura dugu izuwa kansa ganin haka suma sukayo kansa ahaukace suna ihu yana ihu suka hadu suka ruguntsume da azabebben yaki da yake sadauki najwas amatukar fusace yake Sai uazame masu alakakai kuma kadangaren bakin tulu Kai musu sara dasuka yakeyi tako ina idansa arufe burinsa kawai yagama dasu Amma da yake suma ba kanwar lasa bane saisuka zage dantse wajen Kare Kai gamida maida zazzafan martani ahakanne sukayi nasarar sharbasa Sara har saubiyu sabida tsabar masifa gamida zugi zafin dayaji Bai sadda yadurkushe kasaba bisa guy woyinsa biyu yana haki kuma yana ganin dishi sakamakon jinin dayazuba ajikinsa maiyawan gaske

Koda ganin haka Sai shamila da shamilu sukazo daf dashi sukatsaya suna zagaya shi suna masa dariyar mugunta lokaci guda kuma suka daga makamansu danufin su fille masakai inuwarsu kawai yakalla yaga takobi nashirin sauka awuyansa cikin zafin nama yamirgina can gefe daya suka sari iska kafin sujuyo cikin zafin nama sadauki najwas Kil yasa takobi yasare hannun shamila Na dama takurma Uban ihu hannun yafadi kasa can gefe guda

Cikin tsananin fusata yarima shamilu yakaiwa najwas sara akirji najwas yadurkusa kasa saran yawuce kafin yakai masa wani saran Shima sadauki najwas yayi gaba dakafarsa guda daya Kil yacire tsinniya Shima yazunduma ihu kafin yarufe Baki sadauki najwas yadoki kirjin su suduka biyun suka tashi sama suka fada can

Ashe duk abin dake faruwa Sarki dawwaz mahaifinsu shamilu yana Gani amadubin tsafin sa koda yaga abinda yafaru ga yayansa. Saiyamike zunbur yayi wani surkulle tsafi kawai Sai Gani akayi yabayyana afilin daga tareda dagarunsa kimanin milion bakwai lokacin yarima najwas yana kangawar mahaifinsa Wanda tuni yadade da mutuwa yarima saikuka ya ke

Amma lokacin dayaga wannan mahaukaci yar tawagar tabayyana saiyashare hayensa yajuya yakura musu Ido koda sukayi Ido biyu da Sarki dawwaz idanunsa jajawur Kamar angas danbuda awuta gashi gabaki daya jikinsa cike yake daguraye natsafi hawaye nazubowa daga idanunsa Amma hawayen nasa najinine baruwaba tabbas yaruma tunda yake baitaba jin tsoron kofar gaba ba Amma yau akaron farko dayaga Sarki dawwaz awannan yanayi saida yarazana. Amma azahiri bainunaba. Sai yakara rike takobinsa dakyau danufin idan sunshirya sutawo KAIJA MA A WANNAN WACE IRIN ZUCIYA YARIMA NAJWAS YAKE DA ITANE HABA WAINI KAM YAZA AI NAZAMA JARUMI KAMAR YARIMA NAJWAS NE YADDA ZANRINKA FATAKAR MAZA AFILIN DAGA kubani shawara
Wanda yasani yagaya min innadawo anjima yanzu kam UWARGIDA
Tamiko tuwo kuma dan haka Sai an jimanku

Nine dai naku har kullin Itz dan ustax Ne nake cemuku mukwana lafiya✊🏾✊🏾TÆWÆGÆR MÛTÛWÀ✊🏾✊🏾 GÆMØÑ ÁJÄLÎ party 014

Lokacin da akayi kallon kallo Na yan dakiku tsakanin sadauki najwas da Sarki dawwaz da tawagarsa ga kuma yarima shamilu da ginbiya shamila acan gefe dakaru sumdau kesu sunnufo dasu izuwa guhaifinsu lokacin da aka iso dasu ga mahaifinsu sai yarungume su yana mai kukan takaici yadubesu yace yaku Yaya Na kuyi sani cewa bantaba tinanin cewa. Aikin danaturoku yakai haka ba tabbas natafka kuskure Amma kada kudamu yanzunnan zandatse kansa agaban Ku domin tahakanne kadai nudaku zamu huce takaicin abinda yayimana

Koda gama fadin haka Sai Sarki dawwaz yadubi yarima cikin nutsuwa gamida tsananin tsana yanunashi dawata sandar tsafi take wani haske yasure yarima yadinga hajijiya dashi a iska saida yagalabaita shi sannan yamakashi dakasa yarima yaksa daga koda hannunsa sabida galabaita Sarki dawwaz yakara nunashi da sandar nan danufin yasake wujijigashi Amma kafin hasken sandar nan yasauka akansa saikawai akaga wani katon tsuntsu yasure yarima da gawar mahaifinsa yayi sama da Ita ya luluka acikin gajimare yanata famar tsala azabebben gudu tamkar zaije bangon duniya

Amma. Al amarin Sarki dawwaz kuwa. Yayi Iya kokarinsa domin yatsaida tsuntsun nan tahayyar tsafi Amma yakasa ahaka. Har tsuntsunnan yabace musu dagani don ha ka Sai Sarki dawwaz yabada umarni wadakarunsa yace bayan tsuntsunnan duk inda yashiga Ku yatabbatar kun kashe shi kun dakkomin najwas takowane Hali aikuwa Sai suka tashi sama suna masu bin inda tsuntsunnan yabi

Faruwar haka Sai Sarki dawwaz da bukarabansa suka bace bat tamkar basu taba wanzuwa awannan wuriba amma. Al amarin wannan tsuntsun kuwa tunda yadauki yarima najwas da mahaifinsa sai yadinga tsala azabebben gudu dasu harnatsawon kwanaki bakwai sannan ya iso wani kasurgumin daji maitsananin kwarjini sannan yasaki fuka fukansa yasauka awannan daji saukarsa kedawuya Sai ya ajiye yarima da mahaifinsa sannan yarikide yazama wata kyakkyawar aljana duk jikinta raunikane sakamakon harinda sarki dawwaz yayi mata wannan aljana bawata bace baface aljanar da yarima yatemakawa acikin daji

Cikin wannan yanayi datake cikine tayiwa yarima magani araunikansa sannan taduba Sarki shaddad Amma shi babu rauni maigirma ajikinsa dan haka saita kwantar dasu agefe guda takoma tamike zata tafi itama Sai nantake Jiri yadebeta tafadi kasa sumammiya

Basu suka farfadoba Saida suka kwana suka yini sannan suka farka yarimane yafara farkawa firgit yamike atinanin sa zai ganshi agaban su Sarki dawwaz Amma Sai ya ganshi a wani daji daban bawan can ba Wanda yabaroba sannan yaga gawar mahaifinsa aakusa dashi saiyakurma ihu ihun da yasa aljanan farfadowa tatawo dasauri ga yarima cikin hanzari yadubeta yace meke faruwa da mahaifina yimaza kidubashi kada tataba shi saitaji harya sandare

Cikin Kuka tadubi yarima tace mahainka yamutu afusace yarima yadaka mata tsawa yace ke wawuya kinsan mekike cewa kuwa tasake tabbatar masa dacewa mahainka yamutu tabbas wannan rana yarima najwas yayi bakin cikin dabaitaba yiba yayi kukan da tinda yazo duniya baitaba yinsa sabida saida yakwana yayini akan gawar mahaifinsa yana Kuka dakyar aljanar nan tabashi hakuri gamida bashi Baki sannan yahakura suka binneshi awannan dajin sukuyiwa kabarinsa Gini sannan yarima yayi rantsuwa da kolouwar rantsuwa cewa saiyaga bayan Sarki dawwaz da dukkanin wani masoyinsa kuma saiya mayar da birnin su komai dadewa

Asannane sukayi bankwana da wannan aljanar yatafi tabashi wani kalaman tsatsuba Wanda duk lokacin da yake son ganinta yakaranta wannan sunsa kotana bangon duniya Ne zatazo nantake sukayi bankwana tabace bat sannan yarima yajuya yakama hanyar tafiya yanayi yana waigen kabarin mahaifinsa yana Kuka har yabace masa dagani

Ahaka yarima yaita tafiya baji babu Gani babu hutawa sabida tsananin fusata gamida yanda zucuyarsa ke tafarfasa koruwa baya tsayawa yasha balle yatsaya yaci abunci tafiya yake babuji babu Gani yana tafiya yana sanbatu gamida surutu akan Sarki dawwaz

Yana cikin tafiyane Kamar daga sama yaji motsi abayansa baiwaigaba kawai saiyaci gaba datafiya abinsa tamkar baiji komaiba aikuwa saiyaji wata iska abayansa dasauri yawaiga aikuwa Sai yayi arba dama shi adaidai wuyansa cikin hanzari yasunkuya kasa mashin yawuce yarima yataso afusace yadubi Wanda ya harbo mashin nan aikuwa Sai yayi arba dadakarun Sarki dawwaz Na lajanu masu fuka fukai hmm yarima yafisata ainun wato bama zasu barshi hakaba bibiyarshi zasuyi tayiko aiko yana gama wannan tinanin baijira komai cikin tsananin fusata yazare takobinsa maitaken GAYAWA JINI NAWUCE kawai afka musu dasaradasuka gamida sauke musu ruwan Bala I cikin abinda baiwuce dakika talatin ba yatarwatsasu Amma saiyaga sunmike Kamar basu yakasheba dayake yarima bayasan bata lokaci sannan wannan aljanar tayimasa nasiha dacewa har abada bazai taba samun nasara akan Sarki dawwaz ba Sai yahada wata babbar tawaga wacce akeyiwa lakabi da TÆWÆGÆR MÛTÛWÀ kuma acikin tafiyarsa zaisamu wannan tawa koda ayyana hakan aransa saiya ruga da gudu izuwa cikin daji aikuwa saisuka rufa masa baya

Nanfa aka kasa tsere tsakanin su da sadauki najwas Amma dayake nagaba yayi gaba nabaya Sai labari tuni najwas yamace musu bat Amma dai sunsami nasarar harbinsa da kibiyoyi sau babu adadi ahakane har tafadi kasa sumamme shine kekuma kikataimaki rayuwata kikaymin magani

Lokacin da yarima najwas yazo nan alabarin da yake bawa wannan budurwar Sai nantake idanunta suka ciko da kwallah sabida tsananin tausayin yarima najwas datayi sannan tadubi yarima tace gaskiya natausaya maka matuka dayanayin da katsinci kanka Amma babu komai kaddarace takawo hakan kuma kasani aiki dayane agabanmu kuma nima Sarki dawwaz shine silar rasa iyayena dadukkanin yan uwana Amma babu da lokacin da zanyi maka wannan bayani Amma kabini bashi indai Muna tare watarana zangaya maka komai

Koda jin jaka Sai yarima yashare kwallar dake idanunsa sannan yadubeta yace babu komai Amma idan babu damuwa inason jin koda sunanki ne koda jin haka saitayi murmushi mai taushi ga yarima najwas murmushin dayasa zuciyarsa tabuga da karfi akaron nafarko dawata bace ta birgeshi koda taga yarima yakura mata Ido saita dafashi firgit yayi saikace Wanda yafarka daga barci tace dashi yadai lafiya aikuwa Sai kunya takama shi yayi kasa da kansa tace ni suna gimbiya Hansika ni asalin yar sarkin wani kauye ce dake kudancin kasarku wato birnin shiram TO NAGA UWARGIDA TANA HARARATA KARKUJAMIN TAHANANI TUWO ANJIMA

AFUWA AFUWA MASU KARATU KUNJINU SHURU KO JIKIN NE SAI AHANKALI BANI DA CIKAKKIYAR LAFIYA AMMA MASHA ALLAHU SAUKI YANA SAMUWA INSHA ALLAHU ZAKU KESAMUN POS AKAI AKAI KAMAR DA

NINE DAI NAKU HAR KULLIN ITZ DAN USTAX NE NAKECE MUKU BARKA DAWAR HAKA✊🏾✊🏾TÆWÆGÆR MÛTÛWÀ✊🏾✊🏾 GÆMØÑ ÁJÄLÎ PARTY 015

Ginbiya Hansika tadubi yarima najwas tace lokacin da tawagar Sarki dawwaz suka nufo burnin shiram ainaji kace sunrufawa wani kauye sun kashe kowa sunbaje shi Amma wata jaruma guda daya tagudu kuma sunyi nemanta har sukagaji basu ganta ba najwas yace tabbas ginbiya Hansika tace to bawata bace wannan jaruma ba face nidinnan

Tadubi yarima najwas tace lokacin dana ruga izuwa cikin daji Sai dakarun Sarki dawwaz suka rufamin abaya munyi gudu dasu natsawon sa o I dayawa daga busani kuma Na bace musu sakamakon fada yanayi cikin wani katon rami mai tsananin zurfi Wanda kafin naje karshensa tuni nasume sabida tsananin razana danayi bisa zurfin wannan rami nidai daga wannan lokaci bansan inda nakeba kawai dai nafarka naganni ne akan wata shinfida ta fatar damisa acikin wani Kasai taccen kigo gakuma wani tsoho acan gefe daya daganinsa kasan shahararren matsafine domin gabaki daya jikinsa acike yake da guraye yana zaune bisa wata shunfida tafatar zaki yanata Sur kullensa

Lokacin da yaji motsi Na alamun nafarfado Sai yataso yazo gareni nantake gabana yayi muguwar faduwa domin tunda nake aduniya bantaba ganin mutun mai tsufan wannan mutumiba saida nafara tinanin wannan ba mutun bane aljanine koda ganin haka Sai mutumin yadafa kafada ta yace kwantar da hankaliki nibamai cutarwa bane sunana boka. Muzaffar Na ga duk abinda yafaru tsakanin Ku da tawagar Sarki dawwaz Naga irin zalincin dayayimuku dandai banida ikon taimaka mujune shi yasa banjeba domin yanzu Sarki dawwaz yanakan sharafinsa ne don haka kowa yayace zaitareshi dayaki bazaitaba yin nasara akansaba nayi Iya bincikena ingano mafita Amma abin ya faskara Iya abin danagani shine zakuyi nasara akansa bayan kun hada babbar tawaga wacce akeyiwa lakabi da TÆWÆGÆR MÛTÛWÀ

Koda jin haka Sai nadubeshi nace yakai wannan boka yanzu tayaya zan Iya hada wannan tawagar alhalin bansan inda sukeba koda jin haka Sai boka muzaffar yayi murmushi maitaushi agareni sannan yadubeni yace kisani cewa ba azama wane abanza dole Sai ansha wuya kuma Sai anzubar dajini

Zan taimaika miki da mutun daya wato yarima najwas dan Sarki shaddad mai mulkin burnin shiram dashi zaku hadu kuyi wannan tafiya da sannu zaku hadu dasauran abokan tafiyarku kuma ko wanensu Shima zaikasance maitsananin ga ga Sarki dawwaz da kuma zazzafar fansa kisani wadansu jaruman dazaku hadu dasu saikun gwanza kazamin yaki sannan daga bisani sulhu yashiga tsakanin Ku don haka aikin dake gabanku ba karami bane yakanmata tunda kinsami kwarin jikinki kitashi kiciga ba datafiya kiyi yamma da wannan daji domin acikinsane zaki hadu da sadauki najwas namiji Uban mazaje

Ginbiya Hansika tace nandai mukayi sallama da boka muzaffar yakama hanyar da ya umarceni ahakane nahadu dakai cikin wannan yanayi shine yataimaka maka Amma bansan cewa Kaine yarima najwas ba saida kabani labirinka

Koda jin haka Sai yarima najwas yayi ajiyar zuciya sannan yadubi ginbiya Hansika yace to narantse da kabarin mahaifina duk ranar danasake yin gaba da gaba da Sarki dawwaz saidai ayi daya cikin biyu kodai yaksheni kokuma ni in kashe shi Amma bazan sake gudunsa tunda yakasance azzalumi gakowa awannan nahiya nasan cewa yanzu Bani da cikakken horo ko karfin damtsen ko karfin sihirin da zantareshi dayaki gaba da gaba Amma babu damuwa yajira Zuwa lokaci nine zanzamo sanadin ajalinsa EHMM KUNJIFA UWARGIDA NAYIN GYARAN MURYA BARI NA LEKA KARTAYI ZUCIYA TA HANANI TOWO KUBARNI DAZARE IDO

NINE DAI NAKU HAR KULLIN ITZ DAN USTAX NE NAKECE MUKU BARKA DAWAR HAKA DAFATAN KOWA YANA CIKIN KOSHIN LFY NAGODE SOSAI DA ADDU ARKU GARENI ALLAH YABAR ZUMUNCI
TÆWÆGÆR MÛTÛWÀ GÆMØÑ ÁJÄLÎ party n 016

Lokacin da ginbiya Hansika taji kalaman yarima najwas sai tadafa kafadunsa tace tabbas abinda kafada zai Iya faruwa Amma ba yanzu ba dimin yanzu bamu da karfin da zamu tafi Sarki dawwaz dayaki domin yayi mana tazara nesa bakusaba kasani Sarki dawwaz yawuce tinanin ka domin ahalin yanzu tsayuwar nan damukeyi yana kallon mu kuma akoda yaushe zai Iya farmakarmu don haka yana da kyau mugaggauta barin wajen nan

Sadauki najwas baiyiwa Hansika gardama ba haka yabi bayanta suka kama tafiya suka mausa cikin daji sushiga wannan surkuki sufita tanan sudai kawai suna tafiyane Amma basusan inda suka dosa ba kawai kutsawa suke suna tafiya babu Wanda yake cewa da wani uffan sabida kowanensu kunyar dan uwansa yakeji itakanta ginbiya Hansika tayi mamakin yadda ta aminta da yarima najwas hartasaki jiki dashi alhalin yayan manyan sarakuna sunnemi soyayyayarta Amma taki amince dako da dayan su Amma gashi yanzu lokaci guda taji takakmu da son najwas tabbas dolene tadakatar da wannan soyayyaya domin zata iya ruguje mata burinta dadaukar fansa akan Sarki dawwaz

Shikuwa sadaukin Maza najwas lokaci guda yaji soyayyayarta ta ahiga zuciyarsa akaron farko da wata mace tabirgeshi Amma yayi alkawarin bazaitaba bayyana mata soyayyayarsa agareta harsai ita tabayyana cewa tana sansha tabbas yarima Bai San wacece Hansika

Please Login or Register in order to submit comment