Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwana bakwai wasim ya fada tarkon su, domin kuwa sanda suka kwakwalo mu suka kashe sa agabana wafiyya..
Wani irin kuka ta kuma fashewa dashi,duk jikinta na rawa har bata san yadda akayi ta sa gwiwarta akasa ba..

"Tace,wafiyya Ranar naji zafi da ciwon da bantabajin irinsa ba..naso Allah ya dau raina,bantaba zaton zan rayu babu wasim ba, nayi baqin ciki mai tsanani,naso inbishi lahirar...daganan binciken karya da shaidu suka tara akaina suka laka min alhakin mutuwar sa,Akace wai nice ma na kashe shi,aka kawoni nan da danyen jego yau watan zairah 20 kenan da haihuwa.

"Da ake hirar zuwanki anan bantaba kawowa ke bace,shekarata biyu rabona da ganinki a idanuna tayaya zan san kedin ce..?

Sai yau din da muka fita na ganki da kyau,believe me saida gabana ya fadi kuma wallh zuciya tayi mummnam bugawa
Amma kwakwalta ce taki amince min da hakan shiyasa nayi shiru,meya kawoki nan wafiyya?nikam nace hala bake bace kamanni ne amma sai gashi na tabbatar ke dince da kikazo kusa dani

Dan Share hawayen ta tayi ta dubi wafiyyar data sulale kasa tana jimami sosai idanunta da suka kumbura sukayi ja suna ta bulbular hawaye..

Cikin dauriya Bahiyya tace
"So Where is my son?..ina nashwan dina yake..where is he?Ko shima yana wajen matrons ne suna kulawa dashi?nikam sabida ciwon zuciyar nan ya matsamin ne na barmusu zaira suna luramin da ita..
nashwan ma yana wajen su ko?

Jin wafiyyar ta bata shiru ya sa ta taho gabanta itama ta rusuna a hankli,hannuwanta duka akan gwiwarta
..muryan ta a sanyaye ta kuma cewa wafiyya
"Nace ina yaronki?ina nashwan.

"Itama dago idanunta tayi a fixge cikin kkrin samun karfin gwuwar iya gaya mata an sace shi, amma sai gaba daya taji ta kasa yin magana, wani abu ne ya tokare mata kirji wanda tsananin zafin sa ga zuciar ta yasata fashewa da kuka sosai can kasar wuyanta tace

"babu nashwan.. Banzo dashi ba"

"Bahi tace meyasa?
Ina kika ajesa?wafiyya kinsan me kike cewa kuwa?tayaya zaki bar nashwan awani waje.

sai tayi shiru bata amsa ba bata kuma yadda sun hade ido ba kukan kawai takeyi..

Ganin haka sai jikin bahiyya atake ya mutu Tuni ta kau da kanta gefe kirjinta ne ya wani bugawa
Da karfi..
Cikin tsananin tsoro da rawan murya
Tace Is he de..ad?
Sun kashe shi ne?

Wafiya ta girgiza kai tana tare hawayenta

Bahiyya Ta runtse idanu cikin kuka tace nikam kifada min,ina nashwan yake for god sake

Wafiyya ta sake fashewa da kuka can cikin sanyin murya tace
"Ai Sun rabani da shi,Thy called me a childtraficker dan su kawo ni nan su rabani da dana.

Nashwan is gone bansan inda yake ba..

,a mugun razane bahiyya ta dafe bango cikin razana ta furta innalillahi wa inna ilaihi rajiun "mene? Kikace sun dauke shi?
Cikin matsanancin kuka Wafiyya ta gyada kai tace bahiyya ki nitsu zan baki labarin abunda ya faru,bahiyya ta fashe da kuka sosai da kyar ma ta zauna ta shiga saurarar labarin duk abunda ya afku da wafiyya a kangon sarkodie, jikinta duk ya mutu murus sakamakon girgizan datayi.

Wafiyya tace a duniya nasan mayor Aseem assidique
Shine kawai maqiyin mu kuma shiya jefa mu cikin wannan ukubar amma bansan meye sa gwamnati zata kwace min dana ba.

Bahiyya Tace nima wasim ya bani labarin abunda ya afku tsakanin mazajen mu wafiyya
Nidai babu abunda zance sai Allah ya sassauta mana
shikuma Aseem Allah yasa ya gane..ya cuci kansa yaci amanan abokansa dn badai mu ya cutar ba.
Wafiyya We must get intouch da lawyar dayace zai bincika miki inda aka aje nashwan dole ne musan dukanin wayanda suke bibiyar rayuwarmu dana yayan mu da sharri

Gyada kai kawai wafiyya tayi batace uffan ba..

Daga nan Sosai sukan zage sukayi kukan bakin ciki mai tafe makokin mazajen su da uwa uba rudanin rashin sanin mafita da makomar rayuwar su Sunfi sati guda cikin jimami da sassaita zuciyan juna har Allah ya sa abubuwan suka zo sukayi musu sauki.

Bayan wata biyu bahiyya ta yaye yarta zairah daga nono inda wafiyya take gwawarmayan samo musu labarin asalin abunda ke afkuwa daga bakin lawyar qwamnati
,akan haka sunsha wuya sosai,dan sai kusan bayan shekara guda suka san asalin meke faruwa ahakan ma da kyar suka samo kan labarin rayuwar mazajen sun wanda tunda sukaji ya haddasa rashin kwanciyar hankali mai tsanani a zuciyoyin su..

MAFARIN LABARI.
_Kerala bhavanam the dark millatary jungle Early:1963 in old columbia!_

Baqin Jejin kerala bhanavam jeji ne wanda ake masa lakani da jejin baqar mutuwa,ba a masan ainihin mazaunin sa a duniya ba amma a canki cankin masanan geography da kimiyya sukan ce ana samun sa a daidai kan 00000.1000°NE of the earth imaginary line on the slighest corner of the world eqota in between kasashen colombia da mexico wani bin wutsiyar jejin yabiya har cikin kasashen india,brazil da korea,shinfide yake a cikin kasa can kasar hanyar magudanar babban ruwan tekun pacific ocean inda in dan adam ya tsinci kansa aciki to tabbas baya kara saka ran dawowa duniya da ransa,acikin wannan jeji babu komai illa halittun Allah wayanda mutum baisaba ganin irin su ba,bishiyoyin su da ciyawai da dabbobin da kwarin da suke rayuwa a wajen basa kama da wanda idanu ya saba gani,thy are xtremely dark green vegetations,very soft,succulent and huge,some r deadly poisonous wani ganyen ma kana tabawa mutuwa zakayi atake
,hakama cixon kwari dabbobin su babu maganin sa sai tsananin azaba da mutuwa,shiyasa jejin ya tara sunaye da inkiyiyo kamar "the devils palor,ghost well,
evilsanctuary,and death forest,. domin duk wanda yaje baya dawo har karshen rayuwar sa.

A Da can ba a ma iya shiga jejin kwata kwata sai dai kallo daga nesa ta naurar leken asiri irinsu locomotive chips da high grade drones.

Amma naci da bincike irin na turawa yasa aka zo Wani zamani da gaggan sojojin duniya wanda suka kai makura wajen sanin sirrrin aikin su, masu tsananin ilimi,fasaha, karfi da jarumta..nd most of them are marine
raiders,army comandos,superior navies da dangerous mayors daga sassa sassa na na kafafen sojoji daga kasashen duniya daban daban.

Acikin jejin suka kafa base base inda
Kowanne kasa take da cibiyarta da makafarta.

Anan ake hade haden world most dangerous war deals,deadly ammunition exercution hatta yaki da aliens wanda bai shafi mutanen duniya ba anan ake hada shi.

Shiyasa duk wani sojan daka gansa a jejin yakai ne kuma ka dauka kawai babu mahadin sa
Kayan yaki nauoriri Bindigogi da bomabamai dake jejin babu iyakarsu wajen inganci hatsari shiyasa awajen kowa yake amfani da ilimi da kwalkwala..

Kansu a matukar hade yake,duk halin da ake ciki bakinsu daya ne Duk da banbancin kasa aiki matsayi da yare da launin fatarsu.
Anan sojoji sukanyi shekara da shekaru basu fito ba sabida ba abu mai sauki bane shiga jejin bare kuma fita.

Har akazo Wani zamani da ilimin kimiyya da fasaha ya bunkasa, hanya ya bude ajejin sosai aka samu sassaucin shige da fice,sai dai daga nan kuma amana ya soma yin karanci,cin hanci da rashawa ya wanzu, sojoji suka soma saida muguyen bombs,naura da bindigogin su na sirri ma mugaye masu tada tsaye a duniya.

Zamani ne yaxo musu mai wuya amma yawancin sojojin dake nan ta hannan harkan ne sukayi kazaman kudi sunyi arzikin da hankali bazai ma iya daukawa ba.

Sun mance da amana da alkwarin da sukayi ma Allah na kare kasashen su,kowa ya gina kansa da rashin gaskiya,abu daya ne ya rage musu na nagarta wato Hadin kai,dan duk tsiya anan jejin soja da soja basa cin kafar juna saidai in araba abunda aka samu tare ko ayi mutuwar kasko

Tsawon lokaci ana tafiya ahakan har Allah ya kawo sauyi ma wanann yanayi sakamakon shigowar wasu jajirtaccun mayors guda uku.

Na farko shine 8 stared army Mayor Alhakeem sultan wamako.

He is a kabardian.

ya fito ne daga yankin North caucasian daga cikin hadaddiyar kabilar circassian.

Alhakeem wamako dan musulmi ne,practising one, wanda ya samo Tushe daga zuriar sultan wamako from an old nigerin tribe na jarawa,Allah ya albarkaci zuriar wamako da tsananin ilimi, rike amana,nagarta fasaha,basira da dumbin arziki.

da sana'ar Noma na(comercial agriculture) aka fi sanin su dashi tun zamanin da chan kafin suka zo suka surka da electric power generation inda suke da gaggan power industries,energy canals da electricity generation dams

Talaka a zuriar wamako shine wanda ya mallaki a kalla $200 million euros wanda daidai yake da billiyoyin kudi in za'a juya sa a kudin yan africa.

Zuriar Suna da matukar rike amana da gaskiya uwa uba ruko ga addinin Allah shiyasa sukeda dumbin arzikin da sukan su basusan iyakar su ba sai dai Allah bai wani basu tsawon rai ba

Mafi tsawon wanda ya rayu azuriar kaf shine wanda ya mutu yana da shekara 58,hakan yasa hakeem wamako ya taso babu iyayen sa da sauran danginsa altho saida ya girman har yayi aure ya auri budurwan sa na yarinta wato wafiyya ahmet wacce sanadiyar kai ziyaransu gidan marayu ya sameta ita ba taba sanin tushen ta taba amma u can easily tell that she is a swabian musamman daga yanayin Alemannic dialect dinta.
Intana magana seka na ji kamar ita balarabiya ce da yaren ya gama cinye mata baki

Ita da shi har sukayi aurensu babu wani matsala daga baya mahaifiyar sa maysam wamakon itama ta rasu.

Shi hakeem wamako Baije ko jamia ba amma yayi karatun special courses na sojoji kuma tun yana shekara 7 ya iya harbin bindiga.
Aikin sa shine Baiwar sa, dan bayan mutuwar famlyn sa hakem ya kasance cikin jajirtaccun sojijin nan na special troop da tunaninka ma bazai kai wajen ba.

Tun zuwan sa aikin soja hakeem baida abokan da ya wuce mutane biyu wato
Mayor Aaseem Assidique da mayor
Wasim kaita ..
Kamancecceniyar sunan su har yasa ake kiran su"the tripplet military falcons"Komin su atare sukeyi, wani irin strong solidarity bond da amana mai karfi shiya ya daure abokantakn su hakama matsayin aikin su iri daya ne duk dama aikin sun daban daban ne.

Mayor Wasim mesut kaita shiba land army bane,acibiyar navy yake aiki amma dake kusan sa'ar su daya ne da abokansa hakan bai taba raba su.

Mayor Wasim mesut kaita ya fito ne daga zuriar wani babban sarki mai suna king mall mesut,ba'asan tushen sa ba but thy speak pure qurayshian arabic daga can wani yanki a yankin saudi arabia.

Dabiu da nagartan Kabilar mayor wasim mesut basu da wani kwakwarn banbanci dana zuriar hakeem wamako duk dama su familyn sarauta ne, sannan babban sana'an su shine tatsa da safaran gwalagwalai da saida man fetur,so arzikin su is mainly base on oil boom and precious stones economy

Wasim yana da shekara 20 a duniya aka masa auren dangin da wata cousin sistersa Mai suna princess bahiyya oumran mall.

bahiyya yar sarkin kudancin yankin sune auren gata aka musu amma bakaramin son juna sukeyi da mijin ta wasim ba har zuriar iyayen su tazo ta shafe,thy kingdom bcom null and lost aka bar wasim da dumbin arziki inda ya dau matar sa suka ya maidata wani kasa,shiyana aikin sojan sa tare da abokan sa.

Na ukun sun shine mayor Aseem assiduque Daga zuriar mimiko ya fito kabilar data fito daga yankin yemen wanda ta hade yare da bakaken labarawar somalia,mimikos empire yayi kaurin suna sabida mugayen mutane ne karfafa wanda basu da saukin kai sosai
Shi mayor aseem assidique ya fito ne a wani shaharren familyn drug lords wato masu safaran miyagun kwayoyi da bindigogi da boma bomai sai dai kusan tsarin rayuwar su iri daya ne da abokan sa amma shi jami'in sojan marine shikam bada wuri yayi aure ba,ya aure matar sa mai suna "Jasmine aboubakr"

ita jasmine cikakkiyar somalian beauty ce wadda ta hada yare da asalin hausawa gaba daya familynta gaggan yan siyasa ne aurene ya tarkato ta itama ya dawo da ita garin mijin ta.

Sai ya kasance Acikin su su ukun nan mayor Aseem shine yake da abun fadi marar kyau sabida wannan safaran miyagyn kwayoyi da saida bindigogin da kakar sa yayi tayi ma mutanen da bai dace ba..

Tun assidiq wato mahaifin aseem din baya son abun har dai yazo ya rinjaye sa shima ya fada,amma dansa mayor aseem yaki ya jona harkan kwata kwata hakan yasa arzikin sa bai kai na sauran aminan sa bunkasa ba, mafi akasari kudin aikin sa ne dukiyar sa,shi sam baya son kudi daya fito daga zuriar sa duk dama suna da shidin sosai.


Mayor hakeem
mayor wasim da mayor Aseem su ukun nan sunyi tarayya acikin tsananin abota,
son juna,yarda kuma amanar dake tsakanin su ya zarce tunanin kowa.

Komai tare sukeyi arayuwar su ban dauke bacci cin abinci ibada da aiki ba, atare suka gina kansu sukayi wani irin tsinananen karfi da suna, cikin tsananin amana da yarda da kara mai girma babu wani babban makafan sojoji da makafan criminals a duniya sa ba san sa zaman abokai ukun nan ba

Wasim hakeem da Aaseem su suka kawo karshen tabarbarewar sojojin dake cikin jejin kerala suka kuma kawo karshen cin amanan kasa cin hanci da saida miyagun bindigogi..


Hakan ya sa suka dawo tamkar icons,heros kuma ake mutuwar jin shakkar su da tsoron su, dan har suka kammala aikin sojan su babu wanda ya tabayin tunanin karawa da su.

Yau Kusan bayan shekaru 20 da barin aikin sojan amma ana kan kimanta su acikin jerin most powerful,famous and undefeatedly rich mayors a duniya baki daya.
LITTAFIN NA KUDI NE game bukata ya biya 300 ta acct "0152983148 mohd sule surayya gtb nd contct me tru 08060712446
[10/19, 12:46 PM] The DUTCHESS🌟: *♡TAKAICIN WASU🌺*
_the destiny untouched.._


_A nigerian historical fiction_ _*WATTPAD SURAYYAHMS*_
_Brilliant writers association_


_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_

_*05,north,west,south*_

Bayan dumbin arzikin da iyayen su suke da shi na tsaban kudi jarumtar su a Ajejin kerala yasa sukayi fice suka same karuwar karfi da sanayya a duniya,thy bcome xtremly famous nd rich and very powerful duk abunda za'ayi a kasashen duniya na yaki da gangamin demokradiya saida su sannan duk abunda suka zantar ya zauna kenan har abada, Kudi power da suna wanda dama shi dan adam ya yake nema ido a rufe gaba daya a rayuwar sa to abokai ukun nan sun same sa.

Bayan gwargwmyan su a aikin soja da jejin kerala duka atare sukayi retire suka aje aikin domin suma su gina rayuwar su dana iyalensu da suka bari,dan haka dukan su ukun nan sun dawo ne suna zama a yankin bakaken fata inda ake kira da africa,acikin kasar zuriar su mai suna old nigeria Inda kowa yake tare da matar sa wanda sanadiyar yanayin aikin su yasa babu wacce miji yayi lokacin ta ma bare ta haihu.

Tun farkon dawowar mayors din nan old nigeria suka hada kai suka gina wasu manyan anguwowi da estates guda uku,kowa da location dinsa amma estate din gaba daya iri daya ne zak zak babu banbancin abu guda koda na miskilla zarratin,kama daga design colour kwalliyya yawan maikata da security harta kayan masarufi na rooms nd palo,bayan gida da kitchen lobby hakama motoci da jiragen sama da na kasar su duk iri daya ne zak zak kuma daya bai taba zarce daya a komai ba.

Tare da matayen su suka gina wata sabuwar duniya mai fadi da yelwatan jamaa suna bada tallafin sana'oi suna bunkasa rayuwar bayin Allah da karfin ikon dukiyoyin su da karfin ikon su na masu fada aji, kafin su cika shekara ashirin da barin aikin soja rayuwar su ya sauya sosai,
gaba daya rayuwa ya bunkasa musu
Sai suka kasance kamar shugabannin kasa wa jama an unguwowi da estates dinsu,su suke shimfida dokoki na law and oder,su musu titina asibitai,makarantu banki, kasuwanni
,magudanar ruwa su gina kanfanoni su basu ayyukan yi kala kala da kyakkwar kariya na security duka da su da iyalan su

Ata arewa wato NORTH Mayor hakeem wamako ya gina nashi katoton anguwar mai suna _the Brew paradise_
Shi wannan anguwa tamkar Babban empire ne mai dauke da gidajen estate guda dubu hudu inda kowani gida akwai duplex flat me dakuna dakuna na mutanen da zasu kai akalla ashirin batare da wani muxgunawa ko takura ba.

anan anguwar sa na brew paradise ya aje nashi babban gidan da matarsa wafiyya ahmet wamako,zak irin na abokan sa wanda mutane suka kirar gidan da suna the EAGLE's NEST RESIDENT ko wamakos empire.

Shikuma mayor wasim mesut kaita
Yana zama ne WEST inda ya sa ma anguwar nasa suna _the Brew crew_ babu banbancin komai tsakanin anguwar brew crew da brew paradise na hakeem wamako har yawan mazauna gidajen sun duk iri daya ne,shima anan yake zama da matar sa bahiyya a mansion dinsu mai suna CASTLE HILL RESIDENT ko ace da shi the kaitas village.

Mayor Aseem assidique shikuma a south yake da shi da nashi anguwar da mutanen sa zak zak irin na abokan sa sunan anguwan sa _the Brew crewhouse_
Shima anan yake zama da matar sa jasmine cikin mansion dinsu mai suna SOUTHSONG ESTATE.

Mayors din nan sun kasance tamkar gwamnoni sarakuna da shugaban kasa ma jamaar su,Cikin jin dadi babu hainci kuma kowa ya aje iyalin sa suna rayuwa mai dadi mai cike da zazzafan kauna barkwanci da amana ga yelwatan kudi, ilimi da abinci.

For years ba ataba jin kansu ba bare aga fadawar su ko gazawar su
,al'amuran su na da ayyukan su na alheri kullum bunkasa yakeyi sannan abokan takar su kullum kara karfi yakeyi.

Sai dai tulin zamn sun nan acikin matayen su babu wacce ta taba tsallaken wata,ada can sun dauka dan basa tare ne da mzajen sun amma da suka dawo nigeria suka dau tsawon shekaru babu haihuwar tun suna damuwa har dai suka hakura suka barma Allah komai suka cigaba da rayuwar su.

Yadda mazajen suke very close hakama matayen suke sai dai wafiyya da bahiyya sunfi shakuwa da juna sosai ita kuma jasmine yar zaga duniya ce bata ma cika lokacin kanta ba,haka nan ake ganin kamar hakeem da wasim sunfi samun fahimtar juna fiye da Aseem dan shi mayor Aseem hr yau yana fama da matsalar zubewar kima da dangin sa suka riga suka jawo masa akan maganan safaran miyagun kwayoyi da bindigogi ta hanyar da bai dace ba abun yakan damesa sosai yakan hanasa samun sakewar zuci da abokansa duk dama abun baiya nunawa.

Wafiyya kafar mijin ta ta biyo,tana sanar bunkasa abinci ma al'umma ta hanyar noma da bunkasa tsaftar muhalli sannan karatun likitanci tayi asalin medicine ta karanta
Itace head doctor na anguwar brew paradise gaba daya inda take kawo tsararruka kala na ci gaba.

Ita kuma bahiyya kasuwanci takeyi,tana saida sayarwa dan haka ta mallaki cargo da manyan jiragen safaran abinci,man fetur gwalagwalai motoci,gidaje harda kayan sawa dan haka business administration ta karanta tayi special course a fannin finance and marketing

Jasmine Aseem itace fashion goddes a cikin su.
Ako ina zaka ji ana kiranta da inkiyar ban girma na yan gayu watoh LADY J.

Kwalliya,da duk abunda ya shafi kyale kyale na mata itace agaba.

Shiyasa a kullum zakaga ganta kamar hurul eyn creme de la creme world class,ga tsaban kyau da iya kwalliya saka kayan zamani, kwalisa da qamshi,she is xtremely werstenized and highly educated,law ta karanta har matakin attorney,saidai batayi aikin kotu ba ta koma ta karance art and fashion design, tsaban iya tattalin jikinta zagaka fatar jikin ta fari sosai yake kamar na vampires ga laushi da tsansti kamar gonan auduga in ana tabawa,yanayin yadda take daukar kanta ontop can sama sama take a kullum tana balain ji da kanta babu karya Kuma tayi balain haduwa.

Jasmine tana da manyan fashion brand and cosmetic producing indusries wanda duniyan fashion da top designer basa juyawa sai da su duba da kayanta r xtremely stylish,fashion top notch,and rare.

Kamfanin kayan kwalliyarta da kayan shafe shafe na jiki duk sunan ta ne ajiki _JASMINE fashion industry_ ,amma sauran brand din suna da yawa kuma tana business shares a mayn brand kamar a turkey ta hada kai da kamfanin nur yertilas hanife certigar atil kutuglo yesmine akat da sauran su dayawa masu manyan fashion brand,
sauran gaggan partnr dinta kuwa sun hada da italians and french designr brand irinsu loris abate,renati balestra sara battagli roberto carvalli antonio D amico domenico dolce giada brioni
BandB italia balmain,arcadia watches, alpha tauri and anna valentine hakama ba abarta abaya wajen damawa da brands din turawa ba etc.

Shiyasa Jasmine bata da lokacin knta a rayuwarta,kullum ita da patners dinta acikin zaga duniya suke tana neman top quality and rare raw materials da zai bunkasa kasuwancin su.

*****
Haka rayuwar ta kasance har shekara ashirun cas babu abunda ya sauya sai alheri da cigaba.

Inda abokai ukun nan suka fara working tukurum akan wani babban project,wanda zai shafi hada dukiyar su waje guda.

Acikin shekaru ashirin din nan babu abunda sukeyi sai tsara hakan dan abune mai wuya da kuma bukatar gaskiya da gaskiya.

Aganin su tunda sun same komai na rayuwa cikin sauki why not su kafa babban tambarin su zallan su ukun wanda bazai shafe yin hulda da wani kamfani ko gwamnatin kasa ba.

Suna nufin gina wani babban jigo na matattaran arxikin su suyasu,da zimman cewa koda daya ya mutu za a san yadda za'a kare masa dukiyar sa a saukake

For 20yrs sun tsara hakan har suka kammala duk wani plan sannan suka nemi wani makaken kauye suka saye shi baki daya aka gina musu,kamfanin 250 snail shape skycrapper building mai bari uku gini iri daya xak xak
,maikatan a hade ne amma kowa da nasa shashin....

Ba karamin dukiya suka narka awajen ba babu yadda manyan mutane da gwamnti bata so ta fada ciki ba amma haka suka ki firr sakamakon sunyi wannan project din ne ma kansu su ukun iya suyasu.

Hakan yasa aketa jin haushin kamfanin nasu sosai akayi envym wannam tsarin nasu

Sukuwa basu damu ba sam wani shahararren gawurtaccen grand opening akayi ma wajen wanda ba ataba irinsa ba,inda Suka sa ma wajen suna THE BRAVE MEN FALCON aka masa logo da gold an rubuta _"BMF"_
Tsaban haduwar wajen bazai iya fassaruwa ba sanadiyar haka day by day suka soma tara abokan gaba.

Cikin kwarewa da strong bond dinsu na abokantaka suka soma tafiyar da harkokin su na BMF at same time suna kulawa da jama'ar su

Duk wani abu daya shafi BMF zakagan sa da babban Tambarin gold an rubuta bmf din kama daga Donations,projects,
Da duk wani abu nasu na taimako cigaba ko tallafi.

Within just five years BMF ya zaga ko ina ya shahara yayi karfi,mayors din nan kowa yayi investing dukan kudin sa da gadon sa,inda mayor hakeem ya fisu percntage sakamakon dumbin arzikin da zuriar uwarsa da ubansa suka mallaka masa danashi shi kansa so yana da 60% shares a BMF

Hakama mayor wasim mesut kaita hade da kudinsa dana gadon sa yana da 30% shares shikuma mayor aseem dake baban sa da kakar sa suna raye sai baida gadon sa tukun so 20% kawai ne nashi a BMF.

Saidai Duk da haka ko kadan wani abu bai sauya daga amanar gaskiya da gaskiya da son tsakani da Allah da sukeyi ma juna ba.

Shekara biyar bmf tana tafiya smoothly saidai zuwa yanzu har ikullum mayors din nan in suka zauna babu abunda suke tunani da tsarawa sai inda zasu samu magadan arxikin su wanda in sun mutu zasu rike musu abunda suka bari a duniya duba da shekaransu ya soma nitsawa ga matayen su still young and healhy.

Anan ne mayor aseem yakan nun maitar sa na son samun da namiji hakama mayor wasim yace amma mayor hakeem wamako cewa yayi duk wanda ya samu daga Allah zai karba hannu bibbiyu.

Kusan kowani rana in sun gamu a bmf sai sunyi wannan hirar kwasam saiga matar mayor hakeem da ciki har na tsawon wata biyu,tamkar bashi yay cikin ba haka abokan sa suka fisa murnan samuwar cikin,a ranar kusan kowa sanda ya gane suna cikin tsananin farinciki,as usual atare aka hada hannu ana kulawa da wafiyya aganin su ko nasu matayen basu samu haihuwa ba dan hakeem zai zama magajin su uku bayan ransu shi zai kula da arzikin su.har cikin wafiyya ya girma cikin ikom Allah ta haifi da namiji wanda aka sanya masa suna NASHWAN HAKEEM WAMAKO.

Ba karamin murna da shagali akayi ba sakamakon kowannen su tsakanin wasim da aseem burinsa kenan ya samu da na mijin saiga hakeem ya riga ya samu sai kowannen su ya saduda suma suka dawo cewa koma wani gender Allah ya basu suna so

dake

1 Comments On TAKAICIN WASU
avatar
gaji-gaji

9 months ago

Reply

Great read

Please Login or Register in order to submit comment