Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

can do witou her sabida ko a fuska ma tafisu wayewa,zaira tana da baiwar iya girki sosai danko da taje karatu a makarntan gwamnati tasha neman aikin dafe dafe,serving girl,cleaner,waitress receptionist ta iya computer sosai dan haka har aikin accountant tanayi a manyan hotel da restaurant so is like she have a master degree in cooking and hospitality management tako ta ina ta iya bi da mutane cikin tsari mai kyau gata da tsafta.a kauyen bayan su hudun nan ba a dauki wata yarinya ba manyan mata daga public office ne suka sassaka sunayen su domin suma kudin ya shigo hannun su.

By 7am kowa ta baro gida da kayanta tana public ofice bayan sunyi rehersal wa'azi da gargadi sosai aka musu dan akwai manyan tsarukka da tsauraran dokoki da aka shimfide masu wayanda dole ne subi,6.30pm suka dau hanya sautin surutun da raha babu babba babu yaro wani annurine ke tafe da yanayin matan cikin motar hakan zaisa ka fahimci cewa kowa Allah Allah yake Allah ya sada shi da wannan gida.

Masu tsananin kwadayin abun duniya kamar su bara'atu da kawarta mero ji suke kamar macca zasuje su taba ka'abar Allah

Afiyya ma ba a bar ta abaya ba altho ita gulma da kwakwafi ne nata

ita kuwa zaira
Tunda aka shiga motar ta same seat din dake gefe da window ta kau dakai tayi shiruuu
Cikin tunanin abun da ya faru da ita duka duka a yau'
"Rabon maman ta wafiyya ta tashe ta da asubahi dantaje wani waje tun ranar da ta samu gurbin shiga makaranta
,amma yau sai taga har abun kari ta lallaba cikin magagin ciwon ta mata kuma ta xaunar da ita tana bata abaki tana me ma mata nasiha tana gaya mata yadda zatayi kewarta inta tafi.

Tabbas Hakan na kara mata jin tsananin son wafiya
Dan itace kawai take iya gaya mata kalaman da suke sanyaya mata rai irin wanda tasan bamai iya gaya mata su a duniya
Amma sai yau taga hanklin ta kamar ya
Rabu biyu.

"Farko dai Ta riko hannun zairah ayayin da ta rako ta bakin kofa ta kalle ta har can cikin idanun ta cikin wani irin yanayi me fallasa tarin kalamai masu matukar nauyi da wahalan fassarawa
Tace.."Kiyi aikinki da kyau zairah na"zairah tace namiki alkwari mama,goshin ta ta sumbata..sai kuma tayi shiru ta shafo gefen fusknta kamar zata gaya mata asalin abunda take son cewa wato "ki dubamin lpyar dana but no sai tace "kiyi aikinki da kyau kinji?Acikin rudani zairah ta kuma gyada mata kai tana murmushin daya xo dan kansa badan ta so ba..


Abun sosai ya soma damun ta da kadan kadan hankli ya fara tashi..meke faruwa ne?meyasa mama take nan daban inhar akan batun familyn bmf ne?ta tabbata da aikin nan yaxo ta wani waje ne bazata taba amincewa ba saidai ita ta dau alhakin fita bara ta nemo..

amma wannam farat daya ta amsa but why?bata ma samu amsar hakan ba taga an bude musu wani katon gida sun shiga dayake dare ne basuga komai ba sanda aka dire su wani babban daki Ma'abocin farin haske Mai dauke da lallausan gadaje irin na yan boarding saidai wayannan da wardrob dinsu mata biyu sanye da riga da zani ta atamfa blue su suka kawo masu daukin abinci witout saying much to them sudai Anan suka aje jakunan suka kwana dan dama gobe ne za'a nuna masu inda za fara aikin.

Fannin nashwan har yau baisan me ake ciki ba sakamakon shirin yay zafi shikan sa abun ya janye hanklin sa

Sai aka aje maganan neman masa masu aikin a gefe aka tsunduma shirye shiryen hidima dan daga yau baifi saura kwana hudu ayi hidimar ba.

Washe gari da safe aka zo aka musu daukar daddaya inda abun ya mugun basu tsoro dan sun dauka a lokaci guda duk za'a kaisu cikin gidan,anan ma an dauki kowa zairah ita kadaice a dakin bata samu shiga ba,zugum tayi ta kasa yin komai tana zaune..

Jim kadam dan Qarar da metal door din ya saki ayayin da ake budeshi ya firgirta ta daga yanayin tunanin data shiga..daya daga cikin head maids umma saliha ce ta shigo Wato daya daga cikin matan nan da Aka danku su hannun su jiya da daddare da suka iso"

..Tun Bata karasa sake handle din door din ba ta kafe zairah da ido sai dai batace uffan ba zairah tayi saurin mikewa tsaye nan itama Saita dan dago idanunta ta kalle ta da Wani irin taushin murmushi wanda ya kara ma cikakken dattijuwar fuskan ta kyau,gaba daya zairah taji kamr dukan layin dake idanunta sun washe

Gyaran murya matar tayi tare da cewa sallam alaiki

Walaikusalam zairah ta ansa ta a nitse ta karaso cikin ladabi ta karbi kayan dake hannun ta cikin girmamawa ta gaishe ta da "ina kwana" sai ta amsa tare da miko mata package din dake hannun ta

Tace ki bude wannan yan mata babu bata lokaci Sai zairah ta bude.
Wasu korayen kaya ne Riga da zani asalin dinkin buba da plain wraper irin a asalin bayi sai dan kwalin sa very neat duk dama baayi musu adon komai ba warware wa tayi a hankli sai taga kamar size dinsu dai dai da ita akayi HM saliha Tace aikin san meya kawoki nan kuma kinsan dokoki..

zairah tayi saurin gyada mata kai aranta Tana taso ta tambaya ina sauran mutanen suke amma she cudnt sabida hakan yana daya daga cikin gargadin da aka musu na cewa

"U dont ask questions..u just follow oders"

to ina waje Maza ki shirya da kayan hannun ki sai ki taho ki same ni hm
Saliha tana gama fadar hakan zairah tace toh cikin yanayin kazar kazar ta tashi tsaye da kayan a hannu ta
nan ta shiga toilet ta wanke idanuta ta fito ta shirya tsaf cikin kayan Data zo Matan da shi tsaf ta fito ta biyo bayan tasuka fara tafiya tare.

For a while wajen yayi shiru babu motsin komai sai sautin takalmann su, Akan Wata shimfidadiyar titi suke takawa cigaba da Kallon grand circular driveway daya baje a kasar mansoin din ya bada wani irin tsaftaciyar hanya mikakkiya

zaira tayi da kanta a kasa kamar mai jin tsoron wani abu tana bida kanta a hankli tsawon kimanin minti ashirin suna tafiya kafun suka iso bakin wani katon kofa Nan Saliha ta danna kararrawar kofar dakanta ta ta budu,Inda wata katotuwar golden gate ta bayyana wanda baza ta iya misalta fadinshi ko tsawon shi ba,

gaban gate din suka dosa zaira tayi ma wajen kallo daya ta sauke kanta kasa Babu shakka irin gate din nan tagani ajiyan da suka shigo cikin dare sai dai ayanzun tafi ganin girman sa da fadin sa a fili

,..tunda suka shigo
tafiya suke cikin son ta ja aji,cikin dan fargaba take raba idanunta a hankli tana kalle kalle hm saliha tana a gabanta tana tafiyar ta Cikin nitsuwa Wanda Daga ganin ta kasan ita din babban Mace ce mai hankli..,

duk dama a jiyan cikin dare suka shigo amma wani abun Mamakin shine matukar yawan mutanen dake tuttuluwa a haraban gidan a yanzu Kowa yana ta kaikawo kuma kowa cikin samfurin kayar aikin sa..ko driver ne ya gifta to akalla zakaga masu irin unifom dinsa sunkai mutum hamsin.

Dark Blue,light blue,maroon da duka familyn brown colour,green and orange wayannan sune uniform din ma'aikata asalin khaki da official police uniforms kuma na jamian tsaro,complet black suites na body gurds sai camouflage na masu dudduba komai da kuma tabbatar da tsaro.

Wajen kamar wani babban makarnta haka yake tsaban yadda zaka ga hadakar thausands of ppl going in and out in various uniforms and check kowa rataye da badge ko Identity card da zai baiyana sunan sa da aikin da yakeyi.

Altho masu share share da lura da tsftar muhalli sunfi yawa dan hardly ka wulga baka gansu rututu ba,nasu kalar kayan dark brown ne na maza, clay brown kuma na mata duka duka masu aikin tsafta zasukai mutane dari biyar manyan sune masu zama anan gidan as permanent sauran kam time nayi za suzo in an tashi sai su tafi.

Bayan su babu yawan masu aikin gida sai
"maids"sukuma kamar bayi suke masu hidima da cikin gida ciki da waje dukan su mata ne dan haka unifom dinsu kamar atamfa take dinkin riga da zani da dankwali suke sawa ta buba in blue or green colour wato koriya da shudi Masu dafe dafen abinci dake gefen su daban yake su suna saka orange colour uniform ne ligh and dark Check da simple finafor.

Sukuma drvers zaka gansu da maroon uniform excpt 10 official drivers din nashwan dake saka cambridge grey khaki da beret.

Tun Daga tsarin kofar wannan katoton golden gate zaka iya tabbatar makanka cewa nan gidan wani babban mashahurin mayakin soja ne
Dan yalwataccen security armed forces dake kare gidan ta kowani fuska.

Tsarin Gidan gaba daya irin Minimalist revamp futuristic monastery mega mansion din nan ne with alot of mini eco house,flats and reatrets.

Ana nufin gidan daya dara ace dashi anguwa tamkar gari guda ne asalin irin futurist din nanne ma suka tsara shi gabadaya

Kuma tsaban girman sa da yelwansa bazaka ce ga farkon sa bare karshen sa ba irin gidan da akan dauki rabin gari a gina su ne shiyasa ginin ke da nesa da cikin gari inda jamaa suke kuma yana kusa jeji inda ba mutane can bakin ruwa kusa da manyam duwatsu masu kyau masu daukar hankli.

Gidan yana da sashe sashe ko ace mini mansions tsalala guda bakwai kowanne da tsarin sa da ma'aikatan dake lura da su

'...babban comtempolary futuristic mega mansion wanda shine jigajigan gidan suke ciki shine a gaba sai Mid century morden mansion na tarban yan uwan su najini
,indusrial mansion na business
,french county da traditional duk na tarihi ne sukuma scandanavian,minimalist, transional
Duk na gayu ne

Zairah tana dauke idanu ta ci karo da wasu irin dirarrun storey buildings guda biyu masu kama da ancient building of rustic architecture

gidajen biyun babu maraban su da gidan wani sarkin its huge 1000 by 1000 times bigger than normal gidan masu kudi kuma kowane storey buiding yana da personal golden door dinsa wanda suka kere tsayin na farko data fara gani yanzu

Da aka bude musu gate na farko wani haddadiyar farfajiya ce ta bayyana cike da mata masu irin kayan jikin ta

Wata tsaftatacciyar iskan datake shaqowa Ta ramin hanci ta yasa tayi noticing reference to nature dake zagaye da dogon Shararren hanya ne daya bada wani rectangular shape, contours da straight line layout ma tsarin gidan,Bishiyon umbrella ne ajere bisa layi kusa da Cool decorative greeny vegatation of palm trees,suma sun jeru sunyi liff kamar da hannu aka zana su,Gefe da wannan waje akwai jerarrun pebles back splashes da water falls wanda suka Dada fallasa kyaun tsafta da nitsuwa Da kuma kwanciyar hankali dake muhallin wajen

Wasu manyan multi purpose plastic and wood metal furnitures zaka gani a filin inda aka sarrafa su a wani round open space akayi mini palour kamar lambun shakatawa

AHakan ma ba a bar cikin wajen haka kawai ba sai da aka saka royal ottoman walls da relaxing equipment kamar amusement park hala ko dan family Organisational functions.

Idanun zaira tuni ya gaji dan Bazata iya daukar komai da komai ba domin ahakan ma gefe daya suke basu maje asalin cikin mansion dinba, iya dai kallo tayi,amma ita kanta bazata iya Fadan komai tsala tsala ba har suka shiga wata hall way daya mikasu zuwa wata tsaleliyar luxurious cooking deen kai wannan ya wuce nace dashi deen bari akira shi da cooking hall kawai dan Dama Acikin wannan buillding din babu wani tarkace kawai dai lavish lounge area ne masu kayatatun decoration ideas
Katoton morden kitchen shine a tsakiya mai dauke da full range of cooking apliances and machines tsadadu kuma na zamani Gwanin burgewa Its a suprising electic mediterenan inspired mega kitchen filled with artwork and cosy textures,layer of rugs and vintage cushions na hutawa

Irin wajene da talaka ko ya gani baya shawar sa sabida yasan ma bazai taba samu ba sai a aljanna in yana da rabo

****
Wata mata ce ta shigo ta same su nan suka gaisa saliha ta nuna zairah tace wannan itace cikaton baqin hjy turai daga kauye an riga an zabeta a special duties

Wani dumm kirjin zaira ya buga..
Aranta tace speacial duties kuma?

Matar tayi musu murmushi da gefen idonta ta kalle zaira dun sannan Tace
To barkan ku da zuwa ita daya ta rage dama amma kujira ni anan ina zuwa..Tana gama fadan haka sai ta koma cikin wani daki Babu bata lokaci xaira ta cigaba da kallon duniya dan duk kauyancinta yau saida ya fallasa kansa a fili.

design din cikin kitchen ya wuce mahadar Da za'ace dashi wajen girki
Domin kuwa an hado tarin luxurius kitchen cabinets,
smooth kitchen islands,manya manyan fridge sunkai 10 ga xpensive cooking materials in bold colours like turquoise and ornate patterns
Sannan an hada tsadaddun setin gadgets an kuma daidaita marching textures kamar su velvet couches din,metal light fixtures,wood tablets and huge show glasses na aje classic cups dishes da sauran tarkace.

Kitchen rest area harda dinning chairs and sofas kuma anyi sune da wani irin design din silk inda ko nan aka baka akace ka rayu bazaka ce komai ba
Gashi kana taka kasar wajen kanajin wani laushi laushi duka floors da Furnitures Dake Ilahirin wajen an kera su ne da high taste of choice for
marble,hickory da elm,sannan dukan handles din furnitures din su anyi shi ne da Tsadaddun brass knobs wanda ya hada da hannun drawers,cabinets da tuff boards ga kuma airmores.

A gefe da ita kadan akayi ma zaunin wasu shegun copper lanterns dake fidda wasu irin launin farin haske daya dada kara ma wajen touch of simplicity and warm elegance.

Shigowar wannan matar ya dakatar da zaira daga kalle kallen datakeyi,as expected da murmushi kan fuskan ta tace musu a shigo bismillalh sannan tayi gaba suka fara binta abaya.

Tafiya suke Tun Kafin suyi nisa saliha ta dan dube ta,wani Kallon gyara kimtsi tayi matan wanda ya jefa ta cikin nemowa kanta nitsuwa Da kama kai dan haka Ne ma bata kara yin kallon sunnah ma komai ba har suka iske wani amazing royal palour Bazan iya Fadan me ya kumsa ba Tsabar haduwan shi..

Tuni matar da ta kawo su ciki tayi gefe ta tsaya

Zaira kuwa alokacin tayo tsumewar tsaye dan Wata kyakkwiyar mata ce ta dauke mata ido, she bet she is in her early fifties amma ina asalin shekarun ta sun haura 60 azaune agaban full size screen tv irin wall to wall din nan take xaune tana amsa waya tana dariyar ta mai cike da nuna kasaita da aji.

Kallo daya zaka mata kace queen ce
domin kuwa jikin ta sanye yake da wani tsadadden red alkyabba mai velvet gown ta ciki red in colour mai dauke da ratsin black diamond stones kanta tamke da Nadin turban Shi kuma baki.

Haka suka jira ta gama amsa wayar ta,data juyo ta kalle su wani Murmushi ne ya shimfide a angelic face dinta wanda hakan yasa zaira taji cikinta yayi kugi har gabamta yana dif dif shi kadai Ido kawai matar tayi ma dayan matan ta fice ta bar su da su su ukU da headmaid saliha

Zaira tana gani sahila ta rusuna da sauri cikin girmamawa tana cewa

Allah ya ja zamanin ki hajiya turai mace mai Tarin albarka ga nan yarinyar da aka baki labari na kawo ta wajen ki.

A Nan ma murmushi kawai matar tayi batace uffan ba mikewa tsaye tayi cikin Salon kwarjini da kasaita ta iso gareta tabita da Wani nitsatsen Kallo

Karamin ajiyan zuciya tayi A sanda take faman daidaita Kasaitacciyar tsayuwar ta agaban zairah data kasa daga kai tsaban tsoro

Karkwawa hannunta ya fara yi dakanshi duk Tsoro da fargaban inuwan matar ya cika mata mara tam da fitsari sai Zaro ido waje take ta rasa abun yi mai gaba daya

Da shike matar batace uffan ba sai Wajen yayi wani shiru kamar an kashe dan banxa,
zaira dai ko da ba'a gaya mta ba ranta ya bata cewa irin wannan kallo na karance ta ne tsaf daga sama har kasan ta Babu ragi
Matar ta duba.

..sai da taja dogon sight relieve kafin tace "Ure most welcome"..

ta na fadan hakan Da sauri zairah dago dan kuwa sautin muryan ta mai mugun tsada ce sai dai barin baki ya hanata ta amsata akan lokaci

MAtar Tace saliha ki kira min jasmine sai kuzo tare

Atake jasmine Tace toh angama ranki shi dade sai tayi waje ta barsu Atake.

Matar Bata sake kallon zaira ba ta Juya ta koma kusa da tsakiyar hall din Sai da ta dan bata Rata tukun ta juyo tace yarinya Meye sunan ki?

Babu bata lokaci zairah ta dago Cike da dauriya Nace"sunana
...Zairah...
Sai Tayi Shiru.

"Zairah"...Matar ta maimaita sunan a hankli daga nan Bata sake cewa uffan ba But She was looking at her closely like tana so ta fahimci wani abu

Ita kuwa zairah with each minute fargabn ta yake ninkuwa suna haka saiga budewar kofar su saliha da wata godess cos she is more than a queen
Mace wacce taji gaba taji baya ta kuma ci kyafafun sutura da kwalliyar zamani..

Hannu ta daga ma saliha ta fice sannan ta karaso gaban wancan matar sukayi magana cikin sirri wanda zaira bataji ko digon aya a ciki ba suna gamawa duka suka juyo suka kafeta da ido

Ayadda dayar matar ta nade hannayen ta da su kaji jan qunshi da kwalagwalai yasa xairah jin tamkar ina gaban wata sarauniyar matan duniya ne Gaba daya.

Ita kuwa jasmine kallon kurel takeyi mata har Sai da ta lura na natsu kafin ta sake sauke ajiyan nunfashi

Cikin iko da nuna isanta na matan gida ta mata tambayoyi game da aiyukan girki data iya ciki harda shekarun ta da matsayin karatun ta

Cikin nitsuwa da sanyin kalami zairah ta amsa nd she dint freak out as much as she felt.

Bayan jasmine ta gamsu ta juya ta gyada kai ma dayan matar sai kawai ta fice abunta,saliha ce ta shigo ta tsaya a gefe

Dayan babban matan ta matso kusa Tace sunana hajiya TURAI MIMIKO nice kakar gidan nan gabadaya
,nice danaje kauyen ku nasa aka debo ku.Kina da wata kawa ko?Zairah ta daga ido cikin sanyin jiki tace Afiyya.

Hjy turai tayi kwafa tace uhmmm yes..
bazan iya rike sunan ta ba amma i think yes itace sai tayi descrbing affiyar kadan

Tace..."tana aiki ne a fanni na and She told me evrything abt u.
"i mean ur cooking skills.."kuma antabbatr min da cewa baki da rawan kai kuma kinada kiyaye sirri hakan yasa zan baki wani aiki mai wuya.

And i will personally double ur payment.
Littafin na kudi ne the ACCESS FEE IS
300#
VIA 0152983148
MOH'D SULE SURAYYA GTB.
OR MTN vtu tran via 08060712446

Screenshot ur evidence to.
08036651119
08060712446
[10/24, 7:15 PM] The DUTCHESS🌟: *♡TAKAICIN WASU🌺*
_the destiny untouched.._


_A nigerian historical fiction_ _*WATTPAD SURAYYAHMS*_
_Brilliant writers association_


_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_



*11...road to southsong*

Zairah ta dago idanun ta cikin sauri duk dama
rudewar datayi najin offer bai sa ta firgice ta nuna gazawarta a fili ba
"Wani aiki ne wannan hajiya?A hankli ta furta tambayr inda motsawar labbanta ne kawai zai shaida maka fitar su"U will cook privately for my grandson"..
Hjy turai ta bata amsarta amma a hankali cikin sautin muryan da babu wasa aciki.

Shiru zairah tayi tana zzzare idanu kamar wacce take jiran karin bayani

Can Hjy turai ta koma ta zauna akan kujera remote ta dauka ta kara sautin tv ta kuma maida idanun ta kan screen din tana kallo batare da ta dubi zairah ba
can dataga zairah ta nitsu sosai sai tace".Wannan maganan sirri ne tsakanin mu,And If u fail me..bata dai karasa ba ta lumshe idanun ta sosai sannan ta kuma budesu akan zairah wacce already tsoro yasa ta sunkuyar da kanta itama can kasa sosai.

Hakan yadada sawa ta fara harsashen cewa yarinyar is innocent hala zata iya yarda da itan,gyara zama tayi sannan ta umarce zairah data zauna akan kujera but she cudnt sabida fargaba,dan rakubewa tayi a kasa agefe tana me bada dukan hanklin ta,wani shiru ne ya gifta can hjy turai tace zairah ke kadai zakiyi aikin girkin nan ma jikana KON
Kuma ki tbbatar min da baxaki gaya ma kowa ba wani Rass gaban ta ya fadi sai taji gululun da hanjin cikin ta yakeyi ya tsanan ta
Tace hajiya
KON kuma?innalillhi na shiga uku.. ta ayyana hkn aranta..wani zufan bazata suka fara sauko mata idanunta sunyi tsuru tsuru kamar taci kudin aika....
Cikin dauriya tace
"Ex..cu...sse me maaa.

'hajiya turai ta juyo
"U know him?..
ta tsareta da tambayar zairah ta rasa me zatace dan bata da mafita
Can dai ta gyada kai tce yes mana inajin sunan sa
Hjy turai tace good
Toh Kinga shi KON baya cin abincin taro.

Dama na dauko kune sabida ku bama baqin mu wani salo na girke girken gargajiya wanda basu taba ci ko gani ba,wanda zai kayatar da su ko? Aladabce Zairah ta gyada tace hakane tuni hjy turai ta tasa fuskn damuwa tace" aynxu ba subane damuwata ni Jika na ne,shiba haka yake ba, kuma ina so yaci abincin gargajiyar shima ya san mun iya girki fiye dana turawa
amma in ya san cewa ana hada masa abincin sa da na baqinmu bazaici ba..So pls u have to help me Its also a matter of security bazaiyu abarshi yaci abinci anyhow ba, Inhar kin san waye KON yakamata kisan cewa shi mutum ne mai matukar muhimmanci ga rayuwar al'umma ko?toh Karki sake kiyi mini wani shirme,they r cameras evrywhre agidan nan and ure smart huhn?
Zaira tayi shiru tanata kallon kasa

Umma Saliha ce ta matso kusa..da sauri ummu salihar ta xo ta rusuna agaban hajiya turai

"gata nan ki tafi da ita ku karasa ta can.
sai ta dube zaira din a nitse tace"So, Ke kadai zaki rika masa abinci da abun sha daga nan har na tsawon kwana hudu da xakuyi nikuma zan biyaki na musamman mudin ma inyaci sosai.

Murya ararrabe kamar wacce aka saka dole ta amsa
zairah ta bada amincewarta tare da yin godiya.

Nan umma saliha ta wuce da ita wani sashe inda zallan manyan shuwagabanin maid din gidan suke atare su goma ne kuma ko kowacce tana jagorarntar dumbin ma'aikata overall head dinsu itace ake kira da umma baraka wacce tunda satim nan ya shigo aiki ya mata yawa ba a maga idanun ta ba,Dukan su basu da wani tsauri ko walakanta dan adam amma zairah bakaramiin dokoki da iyaka aka shimfida mata ba Do's and don't's har babu iyaka,da wanda akace tayi da wanda aka haramta mata daga ciki harda kebewa da gujewa daga inda mutane suke dan haka tun zuwan su bata sake ganin idon su afiyya ba

Wani shashe na daban aka kaita mai private dakin bacci self contain Ta Inda Kana bude back yard dinsa zakaci karo da wani beautiful master suite me dauke da katon dressing room da 2 bedroom na shakatwa shima nan bana kowa bane just a top residential design

Acikin sa ne akwai Large kitchen mai dauke da sink with super huge fretum dan wannan yaci uban ace da shi channel da alama yayi conecting ne tun daga matattarar waste water da septic tanks na gidan mai gaba daya, Tare da special maid tazo nan ma kwanan ta uku anan ana mata gwaji kowani rana tana dafa kala kalan country food made of rice,beans
alkalama masara gero, ridi ganyayyaki,flour doya dankali kala kalan kunun da ababen sha dana gasawa ko soyawa abincin zamanin ma tana surkawa but as in desert kawai dan dakan ta take serving take kuma kaiwa inda ake aje masa amma bata taba yin mafarkin ganin sa.

Arana na farko baima kalli abincin ba haka aka dawo mata da shi rana na biyu ya tattaba kadan ahakan ma stain din spoon din zai baka shaidar hakan badan anci da yawa ba amma a daren ranan datayi heavy meals kamar tuwon sakwara da kayataccen miyan egusi,garlic offal pepper soup, gingered kunun gyada da wata kafurar desert ta cinnamon pancake
Kusan rabin abincin is gone.

Aranar bakin hajy turai har kunne yake tsaban murna da yamma ma taxo har kitchen din tace ma zairah tayi kokari Ta kuma gaya mata duka family sunji

1 Comments On TAKAICIN WASU
avatar
gaji-gaji

9 months ago

Reply

Great read

Please Login or Register in order to submit comment