Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suna da barkwanci da abun dariya har hirar tasu yakan kaiga hirar hadin auren yayan su,inda hakeem wamako yace zai bada auren dansa ma yar mayor wasim kaita in har ya mace zai haifa
A tunanin sa mayor Aseem bai damu ba amma ashe abun ba haka bane kuwa a zuciyar sa,mayor Aseem secretly wants that marriage alliance ya koma kansa,dn yasan in suka kulla alkwari bada wasa sukeyi ba,amma dayaga hanklin mayor hakeem yafi kwanciya da bada alkwarin auren dansa ma mayor wasim sai ya bar abun a zuciyar sa bai nuna musu rashin jin dadin sa ba sam,har aka kira shaidu da councellor na mayor hakeem wamako babbar attorney ne mai suna mr MAHDI YAZED, sai kuma babban lawyan mayor wasim kaita wato maria mathur da babban shedar su babban amininsu mayor Aseem assisuque.

Agaban kowa aka rubuta aka dinke cewa in mace wasim kaita ya haifa za 'a aurarta ma Nashwan wamako as solidarity marriage kuma hakan aka rubuta aka ajiye harda zoben danyen ruwan white diamond na alkwari da aka rubuta sunan alkwarin auren ajiki

Lami lpya aka cimma hakan kamar da wasa mayor aseem baiso hka aransa ba amma sai bai wani damu ba suka cigaba da rayuwar su normal cikin amana

kwasam sai matar sa jasmine ta samu ciki Nanma aka bude wani sabon shagalin murna Mayor hakeem wamako sanda yafi kowannen su zumudi dan jikin sa ya dade yana basa cewa mayor aseem yana cikin boyayyar damuwa da bakinciki musamman akan familyn sa na mimiko so aganin sa in aseem ya haifu ya sami dansa hala wani abu zai wanye daga bakincikin zuriar sa dake cinsa arai tsawon lokaci

Shikuwa mayor aseem ba haka bane aransa,shidai haka kawai maganan alkwarin auren nan ya damesa amma da jasmine ta samu ciki sai aganinsa ya y tunanin tunda wasim baima samu haihuwar ba Hala shi in ya haifa a juya alkwrin kan nasa

Hakan kuwa ya nuna sosai a behaviours dinsa dayake basa yawan boye boye ma juna wani bin Acikin wasa yakan furta musu amma mayor hakeem haka yaki zancen firr

Kafin cikin jasmine yakai wata 4 sai komaii ya soma sauyawa a bangaren mayor aseem sakamakon mutuwar kakansa inda baban sa ya tattaro bazata ya dawo old nigeria ya kuma soma kokarin controling rayuwar sa yana ta comparing dinsa da abokansa yana nuna masa kasawar sa yana so lallai Mayor Aseem ya biye mashi su koma mimikos empire dan ya tayasa sa cigaba da miyagun harkan safaran drugs da amunition
Tunda kakarsan ya rasu.

Sam sam mayor Aseem yaki amincewa yay tur da batun babansan kuma yace bazai taba yin wannan harkan Ba amma haka uban ya nace mashi kusan kullum sai sun sami sabani duk da haka bai gaya ma abokansa meke faruwa ba,sabida tsakanin uba da da wata bin sai Allah kuma baya jin dadi ace kullum shi yake da kalubale mummana acikin tarayyar su da abokan san

Cikin kankanin lokaci sai Abubuwa suka masa yawa,gashi bai gaya ma kowa damuwar sa ba, sosai ya rude mahaifinsa kuwa bai barsa da maganganu ba komai na rayuwrsa ya tattara yana masa gori akai yana comparing dinsa da abokan sa ta inda abun zai masa zafi sosai For 3 month suna haka har abun yasoma taba zuciyar sa,shaidan sai ya somayin zaman diris a brain dinsa da kadan kadan ya fara biye ma qudirin mahaifinsa.

Lokacin cikin jasmine na wata takwas major Aseem ya tara su a BMF meeting hall ya musu bayanin cewa yana so ya sa dukiyar drugs da illegal amunition a qaddarorin su abun ya matukar basu mamaki da tsoro dan sanin kansu ne basa hada dukiyar su dama rashin gaskiya ki cin hanci
Sai yau ga mayor aseem yana basu dalilin cewa ai illegal drug da amunitim din nan gadonsa kuma sha yana so ya bunkasa shares dinsa a BMF ya zamto 60% kamar na hakeem wamako,as usual basu amince masa ba kuma hakan bai kawo wani dogin sabani a tsakanin su ba,unknwn to them mahaifinsa yana can yana amfani da hakan nw wajen cusa ma dansa ra'ayi munana akan abokansa.

Yace dashi sabida yanayin baqar tarihin xuriar sa ma kawai ya isa ya sa abokansa su ware sa,yace masa tun farko bason gaskiya
Suke masa ba dan dole suke tare da shi, shiyasa ko auren yaya ma aka ki ahada dashi sukayi komai atsakanin su.

Aseem bai cika daukar zafi akan maganan ba sabida yasan gaskiyar abokansa amma da jasmine tazo ta haihu ta same kyakwauyar ya mace hakeem wamako bai sauya ra'ayi ba sai komai ya soma lalacewa a zuciyarsa, a hankli sai ya shiga bada muhimmanci ma maganan mahaifinsa fiye da abokansa abunda kuma bai taba faruwa dasu ba kenan.

BMF yanada shekara bakwai jasmine ta haifi yarta mace kyakwa mai suna HANADI ASEEM ASSIDIQUE.
A lokacin NASHWAN HAKEEM WAMAKO yana neman cika shekara biyu a duniya.

Aseem yaso a juya alkwarin auren tunda shi mayor wasim bai samu haihuwa ba amma hakan baiyu ba for the first time sai ya nuna fushinsa har hakan ya jawo musu dan jayayya mai karfi a tsakanin su

Yace hakeem kafito fili ka gaya min dan na fito daga zuriar drug lords da gun dealers shiysa bazaka hada zuriar ka dani ba Amma dake wasim zuriar sarauta ne ai tun matarsa bata samu cikin ba kariga kabada danka aure.

Babu kalar bayani da fayyace da basu masa ba kuma yasan gaskiyar su suke fada amma hakan fir yaki ya sassauta maganan aransa.

Wasim ya shiga damuwa sosai yaso yace abar masa alliance din amma mayor hakeem sam yaki,kuma aranar yake sanar dashi cewa ya gane mahaifin mayor Aseem yana so ya gurbata musu abokan takansu

Dan haka basuyi kasa a gwiwa ba suka hada meeting su biyun suka je wajen assidique a boye batare da sanin mayor aseem ba dan su kare abokinsu daga qurbacewa sukuma cece sa daga fadawa halaka.

Sunyi magana mai zurfi kuma mahaifin mayor aseem bai boye musuanufar sa da duk abunda ya gaggaya ma dansa dan ya juya masa kwaklwa ba,su mayor hakeem sunsha mamaki matuka Har kudi mai dumbin yawa sunce zasu bashi dan ya tafi ya fita a rayuwar abokantan
su,da can kamar bazai amince ba amma sai ya karba
Sai dai suna barin wajen aka baza labarin cewa an kashe shi da bindigan sojoji in cold blood ta inda hakan yayi kama da cewa mayor hakeem da mayor wasim su suka sa aka kashe sa

Babu tantama aka dasa ma mayor aseem hakan aransa tunma kafin abokan nasa su masa bayani ya soma jin kamar sun ci amanar sa sun zalunce sa.

Sukuwa basu boye masa komai ba iya gaskiyar abunda ya faru suka gaya masa tare da bayyana masa manufar su amma bai wani qamsu ba.

Hakan sukayi rayuwa a dar dar har na tsawon wata wata biu batare da koda matayen su sunji labarin meke faruwa a tsakaninsu ba.

Kwana biyu sai mayor Aseem yayi shiru da maganan komai,shi bai sake kawo maganan sa kudin gado a bmf ba sannam bai dago maganan auren yayan sun ba,sai yayi kamar komai ya wuce duk dama sukam hankalin su bai wani kwanta ba.

Kwasam aka soma shirya babban tea party a matsayin murnan cimma burinsu na rayuwa ukun wanda zaayi sa a BMF cikin dare

A wannan daren wani kazamin qaddara ya gifta cikin rayuwar su yana me ruguza tsananin rikon amana da kakarfan soyayya da abota na gaskiya da gaskiya da suka gina na tsawon shekaru arbain da biyar 45yrs.

Inda BMF gaba dayan ta ta kama da wata unforseen fire outbreak,wutar kuma ta lashe muhimaman ma'adanan takaddun hakeem wamako dana wasim kaita musamman ma na wasim din dan kurmus site dinsa tayi ba a cire komai ba sannan gfe daya na Aseem sai ya tabu amma nashi baiyi illa ba kuma basu yi yunkurin zarginsa ba duk dama bayan kwana biyu hakeem wamako ya bincika sanadin gobarar kuma ya samo gaskiyar zancen.

Aranar Bai iya hakuri ba ya nemi abokan san dan su fuskance juna sai dai rashin gaskiya yasa Aseem baizo meeting din ba amma tabbas yasan sun gane shirin sa dan haka bai bari sun kara kwana daya a duniya ba ya soma shirya hallaka su

Ya tura mugayen mutanen ubansa masu kama da unkn wn terrorist akan suje su kona anguwar brew crew na mayor wasim yace matayen su da yayan su a musu fyade sannan akashe wasim ta yadda zai nuna cewa matarsa ce ta kashe sa,tsaf suka shirya komai dan ma kar azarge sa.

Anguwar mayor hakeem kuwa saka guba akayi a babban makafar magudanr ruwan shansu inda duk wanda ya sha ko yay wanka ko girki bazai rayu ba inma ya rayun to da mumunnan lahanin paralysis ko brain tumor tun acikin daren aka soma rasa rayuka kafin safiya kusan rabin anguwar sun rasa rayukansu

Nan ma dan kar ya shiga zargi yasa aka kai harin harbe harbe ana anguwam brew crew house mutane 200 aka harbe.

Sai abun yayi kama da cewa wani daban ne yake musu hakan su ukun amma sukam tsakanin su su ukun sun fara fahimtar inda gaskiyar zancen ya kwana

Bakaramin tashi hanklin hakeem wamako da wasim kaita sukayi ba.

Ranan gaba daya suna fama ne da lapyar jamar su,wajen kare rayuwar wayanda suka rage da kokarin magance matsalar agaggauce

Zuciyoyin su ya matukar raunana sannan sunyi bakin ciki matuka na gane cewa babban abokin su aseem ya juya musu baya ta hanya mafi rauni sai suka qudira zasu hukunta sa

Kamar da wasa arana ranar can cikin dare yan bindiga suka far ma eagle nest mansion
Wato gidan mayor hakeem wamako inda suka kashe tulin securityn sa kaf shikuma ya gwabza da su amma da kyar ya sha dan ya kare iyalansa ya haura dasu sama can yanata neman yadda zai boye su sabida ba kananan yan ta'ada bane sannan makamai da bindigin da suka zo dasu masu tsauri ne,kafin ma su kashe sa a duk inda zaa same evidence sanda sukayi bombing.

Anan ne mayor hakeem ya kira mayor wasim agaggauce ya gaya masa halin da yake ciki ya kuma umarce sa akan karyaxo ceton sa kawai ya tseratar da iyalansa dan ya dau musu fansa,aciki da kai aka harbesa bayan ya umarce matarsa wafiyya akan ta gudu ta buya ta bar cikin duniya domin ta kare kanta da dansu nashwan

Wafiyya tana barin wajen eagle nest mansion ya kama da wuta bata inda hakeem wamako ya kone kurmus kamar baixo duniyar ba,dare ne da wafiyya bata mantawa kuma tafiya tayi sosai cikin jeji inda bata tsaya ba sai a rugujajjen kangon cespedes sakordie tafiyar kwana talatin da kafafuntaa cikin tsananin yunwa da azaba.

Shi kuma wasim kaita ya buya ne a gidan kasa a wani gari mai suna jigawa inda aka nemesa sama da kasa ba a same sa ba har tsawon shekara biyu inda Allah ya bada matar sa bahiyya cikin yarsu ZAIRA WASIM KAITA inda sanadiyar matsalan ciwon zuciya da ta samu a yayin haihuwartan yasa da suka fito shima aka kashe sa aka daura ma matarsa alhakin mutuwar nasa.
LITTAFIN NA KUDI NE @300 to subcribe via 0152983148 mohd sule surayya GTB
Or mtn
08060712446
[10/19, 10:08 PM] The DUTCHESS🌟: *♡TAKAICIN WASU🌺*
_the destiny untouched.._


_A nigerian historical fiction_ _*WATTPAD SURAYYAHMS*_
_Brilliant writers Association_


_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_

*6....born spring mates*

A fannin mayor Aseem kuwa tun ranar da akaga afkuwar komai labarin mutuwar mayor hakeem wamako da mayor wasim ya baza duniya sai yayi pretending ya rataya igiya a wuyarsa da alaman ya zauce zai kashe kansa ta hanyar suicide..

Haka yan jarida da media suka yayata labarai cewa zunzurtun bakin cikin rugujewar rayuwan su ne da zafin mutuwar abokin nasa wato mayor hakeem wamako da bacewar mayor wasim kaita ya jefa sa cikin halin dimaucewa.

Kuma Mayor Aseem bai yi yunkurin sa hannun sa akan komai ba,dukiyan su da jama'ar su duk ya bari ya gigice ya daga hankalinsa a karshe ma cewa akayi ankaisa asibitin masu tabun hankali a england ana kulawa da shi har tsawon shekara biyu,alhalin ba asan yana can gidansu a mimikos empire tare da ubansa assidique bane su biyun sunata shirye shiryen shirin zama akan dukiyar mayor Hakeem wamako.

Gaskiyar maganan shine ko shi mayor Aseem baisan cewa baban sa yaudarar sa yayi a farko alokacin daya sa akace masa ya mutu ba,yayi hakan ne dan ya raunana masa zucia akan abokansa ya dasa gaba mai karfi inda aseem zai sa aransa cewa sun zalunce shi sun kashe masa uba Aseem bai gane gaskiyar hakan ba saidaga baya anma alokacin mai faruwa tariga ta faru

Ko wutar gobara da aka sa a bmf ansane bayan ankwashe dukanin sauran copies na dukiya da qaddarorin mayor hakeem dake dama nashi ne yafi yawa da muhimmanci

Dukiyar wasim mesut kaita dana matarsa bahiyya kuwa ya kone ya ruguje sosai abunda ya rage duk yan sa ido ne suka kwashe.

Sanadiyar rugujewan komai na rayuwar su da bacewar mayor hakeem da mayor wasim yasa duk wani abu da suka gina tsawon rayuwar su cikin amana da gaskiya ya lalace

Arxikin su da aiyukan alherinsu da dukan Anguwowin su da jamaar su duk ya shafe ya zamto tarihi,hakama kamfanin su ta BMF ya kasance kamar rugujajjen kango wanda baida amfani

Bayan shekaru biyu da faruwan hakan lokacin nashwan yana da shekara biyar a duniya hanadi tana da shekara biyu mayor Aseem ya dawo garin tare da nuna ma jamaa cewa ya dawo ne dan ya kare dukiyar abokansa

Anan yayi claiming din sauran fici ficin dukiyar abokansa ya saida na siyarwa duka mansions da anguwin ya kulle tarihin su altho baiyi yunkurin kwato sauran dukiyar mayor wasim a hannun mahandama ba dake bai samu ya kashe sa a lokacin ba.

Amma duka takardun dukiyar
Mayor hakeem wamako dana matarsa wafiyya ya kwashe ya ajiye amma babban matsalar sa shine baisamu damar sauya suna ko will ba sakamakon security mai tsanani da hakeem wamako yasa ma dukiyar sa tun lokacin da BMF ya kama da wuta ya kuma gane cewa abokinsa Aseem shine munafukin

No one knws amma mayor hakeem wamako ya riga ya sanar da lawyarsa mr mahdi yazeed cewa dukiyar sa bazai tabu ba sai dansa nashwan ya girma ya balaga ya kuma amince
sannan ya basa pasword mai sunan nashwan da zaira ahade "da duk wani original copy na muhimmin takardu aciki harda na alkawain auren sa da yar mayor wasim wato zairah.

Hakan ya zamto babban kalubale a rayuwar mayor Aseem assidique duba da baya son yayi wani abinda zaisa a zarge sa akan mutuwa da bacewar abokan nasa dan tuni mahaifisa ya bada shawarar ya kashe mr mahdi yazed su kafa nasu lawyer amma sam mayor Aseem yaki saidai bakaramin razana shi da takura sa sukeyi ba.

Allah cikin ikonsa yasa attorney mahdin shima wani shegen kansa ne,yasan makaman aikin sa sosai kuma in suka dame sa da matsi akan ya saje musu dukiyar yakan nuna musu cewa ya gane shirinsu ya kuma san sirrinsu duk dama sunyi alwashin cewa in ya bude baki yace wani abu akansu zasu kashe sa.

Wasa wasa lawya mahdi yazeed ya zamto musu kashin kifi a wuya inda hakan ne yasa mayor aseem ya shiga farautar wafiyya da danta lungu da sako har saida suka sameta inda sukayi amfani da gwamnati aka kwace dan aka mata sharrin sato shi tayi dan a jefata gidan yari na har abada ita da kawarta bahiyya.

A tunanin Aseem ai bahiyyar bazata yi nisan kwana ba zata mutu tunda dama tana da ciwon zuciya kuma ababu ababu yarsu saidai ta kare a gidan marayu inma ta rayu.

Ita kuma wafiyya an bata 25yrs in prison amma asalin shirin su shine bazata ma taba fitowa ba harsai ta mutu acan.

Mayor aseem ya karbe nashwan ne dan ya raine sa ya girma sannan ya cika burirkan sa akan dukiyar ubansa sannan ya cika burinsa na aura ma nashwan aure ma yarsa hanadi.

Ya gaya ma matarsa jasmine labarin komai sabida bayason kuskure a lamarinsa

Inda ya umarceta da cewa zata rike nashwan kamar dan cikin ta su rainesa sannan su cimma burukan su akansa in ya girma.

Mr mahdi ya girgiza da wannan lamari amma babu yadda ya iya,sannan har yau basu barsa yasancewa bahiyya da wafiyya suna gidan yari ba infact
Bai san ma bahiyyar ta haihu ba dayake aikinsa yafi shafar rayuwar mayor hakeem ne da dansa nashwan.


Dukan wayannan labarin a sanadiyar binciken su da lwyan gwamnati suka same shi inda shima baiyi wata guda ba aka kashe sa.

Haka wafiyya da bahiyya suka yi zaman damuwa da neman mafita,inda ciwo mai tsanani ya turnuke bahiyyar kullum a kwance take sai ya kasance komai na zaira a hannun wafiyya yake tamkar itace uwarta na asali

Kullum acikin akwarin daukar fansaa mazajen su suke Duk dama sunsan basu da kowa da komai kuma rayuwar su dana yayan su tana cikin mummann hatsari.

****
A fannin nashwan kuwa tunda aka rabasa da mahaifiyar sa bai sake samun lpya ba yayita mafarkai da ciwo mai tsanani kamar zai mutu

Tunda ya warke kuwa ya kasance mai tsinannen taurin kai da fitina da muguwar taurin zuciya ga kafiya da bacin rai mai tsanani dan tun ranar da aka kawosa gidan mayor Aseem har bayan shekara gudan nan daidai da rana guda bai sassauta musu ba ga mr mahdi ya mugun saka idanunsa akan su yana lura da duk wani move yana bibiyar rayuwae nashwan in all angle and space

dan dolen su mayor aseem da matarsa suka biye ma nashwan din suna masa tsananin soyayya da kulawar dole duk dama bakaramin baqinciki da damuwa yake cunkusa musu ba.

Karamin yaro ne amma Yaki sam ya kimanta su bare ya kira su mumy dady kamar yadda yaga yarsu hanadi tana cewa.

Asalin tsana da taurin kai yake nuna musu,duk abunda sukace suna sonsa da shi to insha Allah nashwan saiya nuna a duniya babu abunda ya tsana kamar abun

Kama daga School abinci muamalar sa da jama'an gidan duk wani abu in dai dominsa ne to ya tsana,ga tsawa ga hantara baya kuma daraja kowa bare ya bada respect kuma adan dole ake nuna masa so ake fifitasa ana sangarta sa yana baudewa

Tun abun bai wani damesu ba har halayen nashwan ya soma qure musu tunani dan kuwa abun ya hade masa ne da ciwon kwakwala wato mental instability
type ODD wato opossitional defiant disoder, ciwon kwawalwa ne wanda yke iya kama yara sakamakon damuwa and is charcterized by defiant behaviour irin kaga yaro ya bushe idanun sa ya zamto kangararren marar kunyar nan,boldy yana raini yana sa'insa da kowa,dayan alamar kuwa shine
Negativism wato in ana left shi yana right in akace good yace bad,sauran illar cutar ya hada da chronic disobedence wato tsinannen rashinji da strong hostility towards nagaba da shi ko da ma hukuma ne ko sa'ion iyayen sa.

Nashwan tunda ya rabu da mahaifiyar sa yayi gamo da wannan ciwon amma ba wanda ya sani kawai an dau ka tsaban taurin kaine da zuciya kuma ahaka ake zama da shi ana masa soyayya da gatar dole dan tun zuwan sa southsong mansion ake sangarta sa aka kuma daukaka sa fiye da kowa amma hakan baisa ya rusuna ya zamto musu da ba sabida halayen a brain dinsa yake kuma ahakan yake ta girma da shi.

Zaman Nashwan a familyn mayor Aseem yasa burinsu ya dan soma cikawa duniyarsu ta bunkasa sosai sabida media da jounarlist kadai ma sunsa duk duniya sun dauka cewa mayor Aseem ya sadaukar da rayuwrsa ne dan ya kare abunda abokansa suka bari.

Bayan bazuwar labarin mutuwar mayor wasim kaita aranar Dashi da matarsa jasmine suka fito suna kuka suka kuma shaida ma duniya zasu cigaba da gwagwarmyan kare amanan abokan su sannan zasu nemo su wafiyya da bahiyya wanda da sa hannun su suke zaman gidan yari.

Sun sayi imanin jama a ne da irin gata da soyayyar da suke nunawa nashwan gaba daya suka sangartasa

Bama makaranta daya aka sashi da hanadi ba,highest level of education da duk wani favour na rayuwa duk mashi aka bayar sannan ko acikin wasa ba a tsawatar masa bare a hanasa abunda yake so.

Shikuwa nashwan acikin damuwa da ciwon rashin uwarsa yake rayuwarsa Duk dama yana munanan dabiu baya daraja kowa amma sabida kasancewar sa a cikin su yasa dan dole mr mahdi ya sakar dawani bari daga cikin dukiyar ubansa ma mayor Aseem da zimman ayi amfabi dashi a bunkasa rayuwar sa

yana gama primary kuwa aka kaisa kasashen europe inda aka sa shi a world class team komin sa irin na top forbes list kids da yaran shugabanin kasa irin ma world super powers din nan,makarantar sa da inda yake zama da masu kulawa da shi duk a tsare yake.

Ita kuma hanadi a kasahen larabawa tayi nata rayuwar duk dama lokacin hutu dan dole ake dawowa dasu gida suyi hutu tare
Dan har yau mayor Aseem bai rusuna akan burinsa na son hada auren hanadi da nashwan ba.

Shiyasa hanadi tun tana yar kankanuwa ta sa aranta nashwan wamako shine mijinta insun girma,sannan hakan iyayen nata suka dasa mata aranta duk dama nashwan din bai barta ba,lokacin da suke kanana sosai ma bakaramin duka yake mata ba sau dayawa yasha fasa mata kai wani bin har saita sume amma ba a iya masa komai.

Lady Jasmine tashayin bori ma mijinta akan halayyan nashwan, harta zo ta gaji babu abunda ya sauya saidai mayor Aseem ya rarrashe ta yace tayi hkri ta daure daga haka har nashwan din ya soma girma, da kyar da fitina ya soma jinkan hanadi har sukan yi magana kamar yan uwa amma bashi zai hana ya baza mata muguwar halayen sa ba.

Fannin su wafiyya kuwa day by day jikin bahiyya yana ragwabewa ga wahalan zaman gidan yari,tsaban ciwo har yasa zairah ta soma daukar wafiyya kamar ita ta haifeta ba bahiyyar ba,itakam bahiyyr dama hakan tafiso dan tana ji ajikin ta bazatayi nisan kwana ba kuma ahalin yanzu bata da kowa a duniyar sai wafiyya da yarta zairah ,Ita kuwa wafiyya sam bata taba rusuna ba dan sosai tasha alwashin yin yaqi da dukkan rayuwarta danta daukar musu fansa.

A ranan da zaira ta cika shekaru bakwai cas a duniya Allah yayi ma mahaifiyar ta bahiyya rasuwa

Wafiyyar tayi baqinciki sosai ka tayita kuka amma sanadiyar mutuwar bahiyyan Allah ya bude mata hanya ta samu ta kufce ita da zaira suka bi hannun wani lawyar alfarma aka sa sunan ta a wayanda aka musu afuwa batare da sannin manyan munafukan prison din ba..

wafiyya tunda ta bar gidan yari ta kama hanyar gabas ita da zairah inda tayi tafiya me nisa danta kare rayuwar su biyun.

_*******15 years Later._

Jan Kura irin na kan titin kauye wanda baiga darajar samun gyara ko kwalta ba shiya bule bus din gwamnati daya sauke dalibai a Abakin titin dan karamin kauyen mabarata.

wata yar budurwa ce mai madaidaicin jiki ta sanya doguwar hijabi,Tafe take cikin nitsuwa da kimanta kanta dauke da jakarta agadon bayanta amma dukanin fuskanta a killace yake da mayafi ba'a iya tantance kamannin ta karara

Murmushi takeyi amma idanun ta kaf sun fada sabida tsaban yawan hawayen da suke bulbulowa a ciki
Cikin zuciyarta kuwa babu abunda takeyi sai maimaita zance...

cikin tunanin nata take ayyana cewa Macen da take mutuwar kauna a duniya bayan mahaifiyar ta itace wacce tayi yawon barace barace
da ita rungume a kafadunta duk danta ciyar da ita ta kuma inganta rayuwarta tun tana yar kankanuwar ta

Wannan matar awajen ta itace mace na farko data gani me tsananin rikon amana Wacce Ta kasance acikin baqar talauci fadi tashi wahala da sadaukarwa mai tsanani wajen bada muhimmaci a dukkan fannin rayuwar ta.

bazata manta ranar ba, a lkcin tanada Shekaru bakwai a duniya suka samu yancin kansu suka fito daga gidan yari
one of the worstest era of thy life.

sannan a kauyen mabarata acan gabas sukayi sauran shekaru sha biyar din nan ita da wacce take bata darajan mahafiyarta

daga ganin zairah zakasan cewa ba wafiya bace ta haifeta amma yanxu ji take koda ace Allah xai halarta wa bautawa wa wani dan adam sabanin sa da tuni tayi sujudu gaban ta dan ko kadan batajin iyayenta na asali ma xaso sota su kimanta

1 Comments On TAKAICIN WASU
avatar
gaji-gaji

9 months ago

Reply

Great read

Please Login or Register in order to submit comment