Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jikinsa ya juye zuwa na aljani. "Ukkkkk heee" ya faɗa cikin kumburarriyar wacce ta amsa kuuwa cikin kunan Danejo. Gaba ɗaya rikicewa tai ganin yadda take neman maƙalesa baki ɗaya saboda tsoro da fargaba har take shirin bayyanar da kofatonsa yasa yai saurin riƙo Fuskarta tare da hura mata iska a fuska. Ƙuri tai masa da idanu a rarrabe ta shiga faɗin "Ka kaini wajan Dadata kaji, bana son zama a nan tsoro na keji Da...da...ta.." ta kasa ƙarasa maganar sbd idanunta da suka ruf wani barci mai nauyi ya ɗauketa.

Fuskarta yabi da ido yana hango lokacin da yake tare da mahaifiyarta, duk yadda ya nunawa Dada so da ƙauna amma haka wani mugun babban Malami ya raba shi da ita, ba shi da niyyar cutar da Dada kawai ƙauna ce tasa yake tare da ita, yai ihun tare da magiya amma haka Malamin ya fatatakesa daga cikin Dada bayan ya ƙona shi. Wannan dalilin ya sa yai jinya sosai har bai san inda Dada tai ba sai kwatsam ya ganta lokacin tana ɗauke da cikin Danejo, tun daga wannan lokacin ya ɗauki son duniya ya ɗora akan Danejo, ya manta da batun Dada ɗan tayin dake cikinta kawai yake muradin yaga ya zo duniya.
Sauke numfashi yai yana binta da idanunsa daya gama rikiɗewa har wani hayaƙi yake fiddawa, hannunta ya riƙo ya kama yatsan dake ɗauke da zoben daya saka mata ya jima yana kallonta kafin ya saketa zuwa ƙasa ya kwantar. Tsakiyar dajin ya koma yana Girgiza da surutai cikin ƙaramin lokacin ya koma asalin suffarsa ta aljani yana wani ihu da gurnani kafin kace wani abu ya gama haukata dajin can kuma ya ɓace ɓat.
Yamma Yabi ne da Shatu tare da Sarkin ruga da kuma Giɗaɗo kwance a gaban Dada wacce take cikin halin rayuwa ko mutuwa, bata san inda kanta yake ba, sunan Halisa Dajeno Rome ne kawai a bakinta. Giɗaɗo ya ce "A jiƙa wannan maganin a bata" da sauri Hamma Yabi ya amsa tare da jiƙawa da taimakon Shatu ya ɗaga Dada suka ɗora mata maganin, wani shaƙuwa tai jikinta ya shiga jijjiga can kuma ta kwanta shakaf barci ya ɗauketa. "Na shiga uku na lalashe Hamma Dada ta mutu wayyo yanzu yaya za mu yi Dada ki tashi" idanun Hamma Yabi na taruwa da ruwan hawaye ya kama Shatu tare da riƙeta ya ce "Assha Assha Shatu Dada nada rai, daina kuka yaro barci Dada tai" kuka kawai Shatu take, duk da ƙarancin shekarunta amma ta fahimci cewa Dada ita ce cikon farin cikin su, tare da jin daɗinsu. Sarkin ruga ya sauke ajjiyar zuciya ya ce "Allah shi bata lafiya, Aradu tana gab da mutuwa" jin kalmar Sarkin ruga yasa Shatu ƙara sakin kuka tana jijjiga Dada tare da faɗin ta tashi kada ta mutu ta barsu cikin ƙuncin rayuwa. Cike da takaicin kalamar Sarkin ruga Hamma Yabi ya bisa da kallo yana addu'ar Ubangiji shi ya ɗauki rayuwarsa yabar Dada a duniya ko dan farin cikin Shatu da Halisa. "Ba a samu labarin Danejo ba har yanzu?" Girgiza kai Hamma Yabi yai yace "Aradu ta ɓace babu ita kaf cikin ruga da kuma daji" cikin tausayawa Giɗaɗo ya ce "Wayyo Allah shi baiyyanata" "Kawai iskanci ta tafi, amma ina ne Danejo bata sani ba cikin ruga da dajin ba har kiwo take zuwa ba?" Da sauri Hamma Yabi ya ce "Danejo ba zatai iskanci ba, domin bata san shi ba" fita duk sukai daga cikin bukkar. Hamma Yabi ya dubi Shatu da barci ya ɗauketa a jikinsa a hankali ya kwantar da ita, tare da fita daga cikin bukkar. Yana fita ya shiga irga Nagge wanda ya zama al'adarsa kullum tunaninsa za a iya sace musu Nagge shi ya sa a rana sai ya irgasu sau biyar. Kai tsaye asibiti ya nufa lokacin ana zubawa Dr Iliya magani a cikin mota.

Saukar ruwan ruwan sama ne ya haddasa farkawar ta daga barci, da sauri ta miƙe tsaye jirkinta na rawar ɗari sbd gaba ruwan ya gama yi mata doka, ganin bata da wata mafita ya sa ta fara ƙoƙarin ɗaga ƙafarta Innalillahi sai a lokacin ta lura ashe a kan wani ƙaton dutse mai tsayin gaske take, ita kanta bata iya hango ƙasan dutsen, a hankali ta koma tare da zama saman dutsen "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un wacce kalar rayuwa ce take ciki haka? kenan akan dutsen ta kwana? ina ne nan kuma kwananta nawa? ta haukace ne ko mene? Anya ita ce ba wata Danejon bace daman?" Wani raunataccen kuka ta saka kuka take da dukkan ƙarfinta kenan ita da Rugarsu har abada ina za taga Dadarta? Kuka take sosai na rashin mafita ga rayuwarta ga ruwan sama na dukanta, yunwa take ji sosai, hannunta ta tara ruwa ya shiga sauka a hannun cikin sauri ta shiga shan ruwa sai daya isheta sosai sannan ta koma ta kwanta barci ya ƙara ɗauketa saman dutsen.

"Ke! Ke! Baiwar Allah" aka shiga kiran sunanta wanda yasa ta buɗe idanunta da sauri tare da fatan Allah ya sanya a cikin Rugar Rome take, wasu fatake ta gani su wajan biyar tsaye a kanta ko wanne hannunsa riƙe da abu. Sai a lokacin ta lura ashe a kwance take saman wani ya shi saɓanin ɗazo da take kan dutse. Idanunta take rattabawa tare da binsu da ido ganin ba wanda ta sani yasa ta mayar da kanta ƙasa "Baiwar Allah wace ke daga ina kike? Kin san ina ne nan a Maiduguri kike fa?" Da sauri ta kalli mai maganar sai bata ce komai ba. Wani daga ciki ya ce "Ko bata magana ne? Kamar bafulatana" "Akwai abin da ke damunta Allah kaɗai ya sani" cewar wani, yin duniya sukai tai magana ko ta faɗi garin da take amma tai shiru kamar an kulle mata baki dole suka barta bayan sun yi mata fatan alkairi.
"Danejo" aka kira sunan a taushashe sautin Muryarsa da taji yasa tai saurin Miƙewa yana tsaye kamar kullum sanye da fararen kaya ga tarin nutsuwa da ilhama a tattare da shi. da sauri ta nufesa kamar zata riƙesa sai kuma ya tsaya dab dashi tana sakin kuka tare da faɗin "Ɗan Balarabe ka kaiki gida kaji, tsoro na keji ina son nasan halin da Dadata ke ciki" Prince ya sake mata murmushi yana faɗin "Waya kawoki nan?" Hannu ta watsa alamar bata sani ba da sauri ta ce "Amma ka sanni ko? naji ka iya kiran sunana do Allah ka kaini wajan Dadata" yana kama hannunta ya ce "Ban san inda kike ba, Danejo kuma sunan matata ne ina iya kiran sunan kowa da ita" da fararen idanunta ta kallesa ba tace komai ba, sai hawayen dake suntiri a cikin idanun nata. Hannunta ya riƙe yana janta da Shira tun tana kuka harta daina, tana zaune taga ya kawo mata naman kaji da yawa da kuma kayan marmari ƙin cin komai tai sai da ya fara mata wasa yana bata labarin abin dry sannan ta saki jiki taci kayan marmarin. "Zan kaiki gida" da sauri ta ce "Da gaske kake Balarabe?" Kai ya ɗaga mata yana faɗin "E, Matata" turo baki tai ta ce "Ni ba matarka ce ba" ya ce "Daman ba dake nake ba" kamar ba zatai Magana ba sai ta ce "Yaushe zaka kaini wajan Dada" yana riƙo hannunta ya ce "Ko yaushe, amma kiyi mini Al'ƙawarin na dinga zuwa ina koya miki karatu, kuma kiyi al'ƙawarin zamu zama ƙawaye a duk sanda na buƙace ki, kizo gareni ba zan cutar dake ba na rantse da Ubangiji al'arshi, ba zan bari kuma kowa ya cutar dake ba" tunda ya fara magana take kallonsa cikin rashin sani ya ce "Kuma Dadata zata samu lafiya?" Shiru yai mata an riga anyi masa iyaka da mahaifiyarta, babu abin da zai iya a gareta, sai dai ya sanya Safwan yai wani abu akai. "Uhm ni kayi magana mana" ta faɗa tana jijjiga hannunsa kai ya ɗaga mata ya ce "E, kina zuwa ya kiga ta samu lafiya" Murmushi tai Wanda ya bayyanar da kyanta a hankali ya dinga ɗauke mata tunani harta manta da batun gida sulalewa tai ta kwanta saman ƙafarsa barci ya ɗauketa.

ISLAMIC UNIVERSITY OF MADINA.
_Jami'ar Musulunci ta Madinah_ masarautar Saudi Arabiya ta kafa jami'ar bisa umarnin sarauta a shekarar 1961 a tsattsarkan birnin Musulunci na Madina. Koda yake wasu sun danganta akidar Salafiyya da bude jami'ar, ana ganinta a matsayin rashin fahimta sakamakon halayyar da cibiyar ta ke da ita ga kowane akida. Jami'ar ta sami takardar shaidar digiri na jami'a ba tare da banbanta ta ba daga Hukumar Kula da Ilimin Kimiya da Nazari a watan Afrilun 2017.

Jami'a ce mai tsarin gaske musamman Ɓangaren Addini. Ga nagartattun Malamai, da yawan ɗaliban na son karatu a jami'o'in Saudi Arabia sbd dalilai masu yawa. Manyan jami'o'in Saudi Arabia an basu shaidar yabo a bangaren ilimin kimiyya. Wasu daga cikin jami'o'in Saudi Arabia suna cikin manyan jami'o'i a duniya dangane da cibiyoyin bincike. Jami'o'in Saudiyya suna ba da kyakkyawan yanayin binciken ilimin, ta hanyar ingantattun cibiyoyin bincike. Yankunan ilimi da al'adu iri daban daban a jami'oin Saudiyya. Akwai daliban duniya daga sama da kasashe 165 da ke karatu yanzu haka a jami’o’in Saudiyya. Baya ga manyan masana ilimi da ma’aikata da ke aiki a waɗannan jami’o’in. Jami'o'in Saudiyya suna ba da cikakkiyar kulawa mai kyau ga ɗalibanta da kuma malamanta. ire-iren wannan manyan dalilai yasa akeso da burin karatu a jami'o'in Saudi Arabia.

Da sauri ya fito daga ɓangaren hall ɗin da aka ɗauki darasin Islamic Studies and History. Kansa a ƙasa ya tatatare hannayensa cikin milk ɗin Arabian jallabiya daya saka sai wani ƙaramin baƙin hirami da yai rawani dashi, ɗaya hiramin kuma ya ɗora saman kafaɗarsa. Wasu matasa ne manyan suke take masa baya hadda wasu securities. Yanayin yadda yake tafiyar kaɗai zai tabbatar maka babu sassauci a zuciyarsa, idanunsa yai jajur bai taɓa shiga ta shin hankali na yau ba, yana zuwa bakin wata farar mota jikin Umar-khan na rawa ya buɗe masa murfin bayan motar ya shiga, Malamin na shiga mota, Umar-khan ya shiga gaban motar bayan driver ya shiga. Da sauri Driver yai wa motar key ganin haka yasa Saif-Wazir ya shiga wata motar kai tsaye daga cikin University ɗin Prince muhammad bin abdul'aziz international airport suka nufa.

Ta cikin madubin motar Umar-khan yabi Sheikh Aliyu Haydar wanda ke bayan motar da kallo, ya jingina da jikin Kujera sai huci yake fitarwa, ya rirriƙe Jallabiyar jikinsa da hannu bibbiyu, gumi na tsastsafo masa ta tsakiyar goshinsa sbd yadda zuciyarsa ke masa zafi da ta fasa. Girgiza kai Umar-khan yai cike da tausayin yanayin yadda Sheikh Aliyu Haydar ke gabatar da rayuwarsa. Juyawa yai yaci gaba da kallon yadda driver ke sharara gudu, har suka ƙaraso filin tashi da saukar jirgin, The plane is ready to take off. Tun daga bakin wajan securities ɗin suka firfito tare da mamaye motar Sheikh, Umar-khan ya buɗe murfin motar ciki. Sauri Sheikh Aliyu Haydar ya fito a wannan lokacin ma kansa a ƙasa, yana hawa strains ɗin jirgin Saif-Wazir na biye dashi, sai Umar-khan wanda ya ɗan tsaya yana amsa kiran Father. Cikin damuwa Umar-khan ya ce "Kayi haƙuri Father, Sheikh ba zai taɓa aikata hakan ba, zargi ne kawai ake masa, yanzu jirginmu zai tashi be patient Father" tsaki Father yai ta cikin wayar kafin ya kashe. Yana shiga jirgin aka bawa Pilot daman keta hazo, a hankali jirgin ke zagayawa a ƙasan kwalta ya jima a haka kafin ya kete zuwa sararin samaniya.

Jeniyar motocine suka tabbatar da Father Sheikh Aliyu Haydar ya ƙaraso gida Nigeria, da sauri ya miƙe daga zaunan da yake yana zaga haɗaɗɗan parlon gidan, tare da jiran shigowar Sheikh ɗin. Da mamaki Umar-khan ke bin ƴan jaridu da kallo, daga na gidan Redio, T.v, media. Abin har yai tsamari haka yana da tabbaci Sheikh ba zai taɓa aikata abin da ake tuhumarsa ba, zargi ne kawai. A nutse ya sakko da ƙafarsa daga cikin motar kai tsaye ƙofar shiga cikin gidan nasu ya nufa, Umarninka da Saif-Wazir na karesa daga ɗaukan da ƴan Jaridu suke masa. Sako ƙafar da Sheikh Aliyu Haydar yai cikin parlon yai daidai da lokacin da Father yake sauke masa wani lafiyayyan mari wanda yasa Umar-khan saurin juyawa ya fita, domin ba zai iya jure ganin ana cin zarafin babban mutum akan idanunsa ba kamar Sheikh Aliyu Haydar, Saif-Wazir Hawayen da yake maƙalewa ne suka sakko masa, da sauri ya karawaw Umar-khan baya. Cikin faɗa da tsawa Father ya ce "Ka kyauta Aliyu Haydar, ashe wannan dalilin ya hanaka auren tsayin shekaru talatin da huɗu? Ka yaudareni kaci amanar Musulmai kana fakewa da karatun addininka kana lalata yaran mutane a makarantar Jami'ar Madina?" Har wannan lokacin kan Sheikh a sunkuye yake banda cukurkuɗe Jallabiyar jikinsa da yake da hannu babu abin da yake. Father ya girgiza idanunsa cike da hawaye ya ce "Ba shakka biri yai kama da mutum, tunda nake baka taɓa zuwa wajena kace Father na zaɓi yarinya ina son aurenta ba,You betrayed me Aliyu, you deceived me as your father" Ya faɗa yana saukewa Sheikh wani marin cikin tsawa ya ce "Talk Aliyu, kayi magana ka amsa mini Sheikh..!!!" Father ya faɗa yana Girgiza kafaɗar Sheikh. Ɗago kai Sheikh yai bakinsa na rawa laɓɓansa na karkarwa alamar yana son cewa wani abu, amma sam ya gagara sbd rashin iya magana da bai ba. "Ban damu da duk yadda zakai magana ba Aliyu, a yanzu ba zanwa ƙinƙinarka uzuri ba ka bani amsa da gaske wata kaiwa ciki?" Shaaa hawaye ya sauka fuskarsa Sheikh sbd yadda yake son furta wani abu ya kasa. Matsawa ya yi kusa da Father yana buga hannunsa a cinya a hankali hannu na rawa ya miƙa tare da kama kwalar rigar Father, idan ya ɓalle bottle ɗin gaban rigar Father sai ya mayar rufe, da ƙarfi ya buga ƙafarsa yana riƙe wuyan Father hawaye ba zubu masa cikin ƙinƙina ya ce. "Ya....ya.... ya Allah..." Ya ƙare mgnar cikin ƙinƙina yana mai buga ƙafarsa a ƙasa.


Share as so much as you can💋... Not Edited👏🏻

#Sarautar marubuta
#True life story
*🌈 IDAN BA KE 🌈*

_*Arewabooks@Nimcyluv*_
Follow my account👇🏾
https://arewabooks.com/u/nimcyluv

7...
"Heeeyyy..faaa..Father,babb babu uhmuuu macen dana taɓa laaahhh latawa" a wahale ya Ƙarasa maganar sbd zafin ƙinƙinar dake cinsa take basa wahala, yana buga ƙafa a ƙasa tare runste idanunsa zuciyarsa na maza zafi da raɗaɗi sosai na cin zarafi da sharrin da ake son yi masa, amma ko kaɗan fuskarsa bata nuna damuwar da yake ciki ba, ƙinƙinar ita ke azabtar da zuciyarsa wacce take kassara dukkan wani mafarki nasa. Hannun Sheikh dake wuyan Father ya ture cikin ɗaga murya ya ce "Ok ƙarya za ayi maka kenan Sheikh? Mutane dubu nawa ne a makarantar ba ace sune suka aikata haka sai kai? Kasan halin da ake ciki yanzu gidan Jaridu na gab da sakin labaran? Mata nawa ka lalata, mata nawa kai wa ciki?" Cikin zafin maganganun Father Sheikh ya ƙara runste idanunsa kansa ma sara masa, shiru kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba. Father ya yi tsaki yana juyawa zuwa upstairs har lokacin bai dai na faɗa ba. "Kaje ka kare kanka daga zargi Aliyu, at anytime jami'an tsaro na iya zuwa, You are accused of a serious crime, we have no evidence to defend you in court"

"Wanne Irin Court Father? Laifin Aliyu har ya yi girman da za a kaisa court? Wallahi babu mai kai mini ɗana Court" Hajiya Maryam wacce suke kira da Mother ta ƙare maganar tana sakkowa daga upstairs, domin lokacin da motocin su Sheikh suka shigo Sallah take. Father ya Kalli Hajiya Maryam tare da nuna Sheikh wanne yake ta damƙi Jallabiyar jikinsa. sam bai damu da duk zargin da za a yi masa ba, idan ƙaddararsa ce ta zo da haka babu yadda za ayi ya goje mata. "Sai ki tilasta masa ya yi magana, na faɗa masa ya nutsu ya ajjiye ƙinƙinarsa a gefe ya bani bayani, amma yaƙi, kina tunanin iyayen yaran zasu ɗaga masa ƙafa ne akan laifin fyaɗe da ya yiwa yaransu? Sbd kasancewarsa Malami kuma mamallakin S.A.H BANK..? ki Ajjiye son da ki ke masa a matsayin ɗanki, ki kwatantanta adalci tsakaninsa da sauran yaran daya lalata Maryam" Cikin faɗa Mother ta ce "Look Aliyu, idan kai ba zaka iya ƙwatarwa ɗan ka ƴanci ba, zan shiga ko'ina domin ganin an wanke Sheikh daga zargin da ake masa, ba abin kunya bane ace wai kai ne mai bada goyon baya akan Aliyu Haydar ya aikata hakan?" Father wanda Hajiya Maryam ta kira da Aliyu dake sunansa aka sakawa Sheikh ya yi Murmushin ta kaici. "Idan taƙamar maki Lawyer ce, kada ki manta su ma yaran Gwamnati na iya ɗaukar musu lauyoyi, dake da gwamnati sai ku zuba muga, kada ki manta daga can Madina aka zo da zan can, an kai maganar state C.i.d idan jami'an Nigeria bata ɗauki mataki ba, na Madina zasu ɗauka suna gab da bashi takardar kora daga aiki" yana faɗin hakan ya haura sama cike da baƙin cikin abin da Sheikh Aliyu Haydar ya ja musu a cikin Alhhali.

Mother ta bi bayan Father da kallo, tana mamakin rashin ko'in kula da Father yake nunawa Sheikh kamar ba ɗan cikin sa ba. Juyawa tayi tare da kallon Sheikh da har yanzu kansa yake ƙasa tasan he never talk domin damar maganar bata damesa ba, sbd ƙinƙinar da Ubangiji ya jarabce shi da ita. Tana ƙoƙarin yi masa magana ya juya da sauri zai bar parlourn sbd raunin daya hango cikin ƙwayar idanun mahaifiyar ta shi. Yana saka kansa zai bar parlourn Umar-khan ya shigo da sauri jikinsa na rawa ya ce. "Innalillahi wacce irin masifa ke shirin tunkaro Mother?" Mother na ɓoye damuwar ranta ganin yadda Umar-khan ya firgita ta ce "Me ne ya faru Umar-khan?" Idanunsa akan Sheikh wanda ya ɗan jinkirta da fitar Umar-khan ya ce "Na rasa tayaya ƴan Jaridu suka samu wannan labarin, gaba ɗaya sun cika gidan nan da waje baki ɗaya, duk yadda securities sukai ƙoƙarin hana faruwar hakan amma abu ya gagara" Sheikh na jin haka ya juya alakar tafiyarsa zuwa haɗaɗɗan sashinsa dake cikin gidan nasu. Mother ta bi bayansa da kallo kafin ta juya ta kalli Umar-khan tace "Na jima banga mutum mai taurin kai da tsayayyiyar zuciyar irin Sheikh ba, duk abin da za ayi masa ba zai taɓa cewa komai ba" Umar-khan yaja numfashi yana mai ƙara gasgata zan can Mother, domin babu wanda bai san Sheikh da kafiya ba. "Yanzu ya za mu yi Mother? Al'amarin nan ya shige tunaninmu, ba tsammaci haka ba" Mother ta zauna kujera tana tunani ta ce "Zan shigar da ƙara Court, da kai da Saif-Wazir kuji da ƴan jaridu subar ƙofar gidan nan Immediately"

"Court Mother? Waye zai tsaya masa? bakya tunanin shiga Court ɗin kamar latata rayuwar Sheikh ne?" A taƙaice Mother tana danna waya ta ce "Hakan ne mafita Umar-khan, batun lawyer ni ce zan tsayawa ɗa na da kai na" "but Mother" hannu ta ɗaga masa cikin sakin murya ta ce "Umar-khan...!!! Stop asking to much" jinjina kai yai ya fita yana jinjina girman yadda abin ya lalace cikin ƙanƙanin lokaci haka.

Sheikh na shiga bedroom ɗinsa yaja numfashi sbd wani sassayan ƙamshin turarensa na ROJA daya daki hancinsa wanda ya jima da zama abokin hirar ɗakin. Ƙamshin daya haifar masa sauƙi a zuciyarsa, kasa zama ya yi ya shiga kaiwa da komowa a tsakiyar bedroom ɗin, tunani fal ransa wacce yarinya ya lalata? ba mace ɗaya ba har mata da yawa, kuma harda ciki? Bayan tunda yake maganar minti 20 bata taɓa haɗa shi da mace ba, idan ka ɗauke mother. Bai taɓa jin sha'awar mace ba, duk daɗin muryar mace bai taɓa ji ba, kamar an saka masa tsanar mata haka yake ji a ransa balle a wayi gari yau wata ta birgesa ba. Yinin ranar a sashinsa yake, Mother ba tai tunanin zuwa wajansa ba, ta san ba zai taɓa saurararta ba, koda Maimoon ta nufi part ɗinsa ɗauke da try na dinner yadda taje haka ta dawo, bugun duniya yaƙi buɗewa haka ta juya tana mai jin tausayin yayan nata.

Mother dake zaune a Parlourn Father dake cikin sashinsa ta gyara zama ta ce "I couldn't believe what was happening,Aliyu is your son, you gave birth to him. Me ya sa ka yarda a ranka zai aikata hakan?" A nutse Father ya ɗaga kansa ya kalli Mother kafin ya ce "na fiki sanin ɗana ne, tunda akan idanuna ki kai Labour ɗinsa, amma hakan baya nufin zan saka masa Idanu, sai yanzu na fara tunanin tsayin shekarun da Aliyu ya kwashe a wannan duniyar ba tare da tunanin yin aure ba, kamar ko wanne namiji, nasan Aliyu nada lafiya balle nace, ke shaida ce how many times da zan kira Aliyu nace ya fitar da matar aure ya ce na bashi shekara ɗaya ko wata kaza? He is thirty-three years old now, but to this day there is no thought of marriage in his mind. Ni da kai na, na fara shakku da tantama idan ba lalata yaran mutane yake" wani irin ɗaci Mother taji a ƙasan zuciyarta, wanda ya sa ta fara ladamar yarda da Mijin nata da tayi. Magana ɗaya zai yi a janye Case ɗin amma yaƙi infact bai damu da matsalar ɗan nasa ba. Miƙewa tsaye ta yi tana kallonsa idanunta na sauyawa amma ta hana kanta zubar da hawaye ta ce.
"Court zata tantance mai gaskiya, kuma zata wanke Sheikh daga sharrin da ake masa" tana faɗin hakan tai waje cikin ƙonar zuciya. Bayanta yabi da kallo yana faɗin "If you give evidence that Aliyu is innocent, zan tsaya wajan karɓar masa haƙƙinsa Maryam" sosai kalamansa suka daki kunnanta amma ta share.
Tana zuwa parlour ta samu yaranta zaune sun zabga tagumi "Maimoon zugi driving nawa, Zeefa ke da Fattoumah ku zauna, I'll be back 10:00 ki tabbatar kunyi alwala tare da sallah kun kwanta barci, kada na dawo naga kuna kallo ok" Fattoumah ta ce "Mother ina zaki? Yaa Lee har yanzu bai fito ba fa?" Mother ta ce "Kada ki takura Sheikh, idan kika takurasa sai ya shaƙeƙi tas kafin ya baki amsa, You better be careful, bye my babies"... "Bye Mother" fita sukai har lokacin wasu ƴan jaridun na ɓoye suna jiran ganin motar Sheikh ta fito. Maimoon na fita taja motar da gudu ta ɗauki hanyar da zata kaita Maiduguri road.

Tafiya kawai Danejo take babu takalmi kalbar kanta duk ta hargitse duk wanda ya ganta a wannan lokacin babu tantama zai kirata da mahaukaciya wacce ta jima cikin ciwon haukan. Tafi futu futu baya hayyacinta baki ɗaya,ita kanta ba zata taɓa tuna kwanakin data shafe tana tafiya ba, kuma abin mamaki ko gajiya ba tayi duk wanda ya ganta tambayar duniya idan zai mata ba zata taɓa kallon inda yake ba, balle kuma ta bashi amsa. Cikin ikon Allah ta samu kanta a gefen Rugar Rome inda take zuwa kiwo, tana zuwa nan ta yanke jiki ta faɗi babu numfashi. A hankali jikinta ya shiga Girgiza wani hayaƙi nafitowa ta jikinta a hankali hayaƙin ya cure waje guda, a haka ya rikiɗe zuwa suffar Prince.. idanunsa na kanta yana ƙoƙarin zuwa inda take yaji an daka masa tsawa wacce ya sanya ya tsaya da zuwa inda take, ko ba a faɗawa Prince ba ya san wane yake masa wannan tsawar domin shi kaɗai ya isa ya yi masa tsawa ya saurara.
"Ka Saurara Prince, kada ka kuskure ka taɓa Bil'adama ɗin nan" Prince ya juya idanuna ya sauka akan mahaifina wanda yake cikin suffar mutane cike da kamala. "Matata ce Abba, ina da ikon taɓa ta a lokacin da nasu kada ka hanani aikata hakan" Wanda aka kira da Abba ya kalli Prince ya ce "Ban san yaushe ka zama mai son zuciya ba, zuciyoyi nawa zaka baƙantawa? yanzu bayan wannan ƴar tayin kaje ka saka bawan Allah cikin masifa me ya yi maka?" Prince yana huci ya ce "Abba wannan bawan Allan shi ke shirin rabani da farin cikina, na jima da sanin haka shi ya sa na fara yin abin da ya dace, kashe sa

2 Comments On IDAN BA KE
avatar
al-kausar

5 months ago

Reply

Dan Allah ci gaba daga page 11 naga a page 10 ya tsaya Kuma kince akwai complete anan arewa books

avatar
taskar

5 months ago

Reply

Replying to al-kausar

sai dai ki saya littafin a wurin marubuciyar ga nambarta 08119237616

Please Login or Register in order to submit comment