Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce "Wanne irin hukunci kuma?" Labo ya ce "Kai maza kira mana Giɗaɗo" abu kamar wasa kafin kace wani abu kusan gaba ɗaya ƴan Fulanin Rugar Bello suka zagaye Sheikh. Giɗaɗo ya kalli Sheikh kana ya kalli Labo ya ce "Zaro mana zoben hannunsa daka gani mai tsaida ne" Labo ya kama hannun SHEIKH tare da zare zoben, kusan mutuwar tsaye Sheikh ya yi yama rasa me zai ce, sai gumi dake yanko masa ya shigo ne domin tsinkar wani ganyen magani kalli yadda tsautsayi ya rutsa da shi. Kamar daga sama yaji Giɗaɗo na faɗin "Allhamdulillah mun riƙe wannan zoben matsayin sadaki" Saif-wazir ya ce "What sadakin me?" Giɗaɗo ya ce "Ai yanzu muka aura Wannan Balaraban aure da yarinyar nan, ni ne waliyin yarinyar Labo kuma waliyin Balaraban hakan shi ne hukuncin duk wanda ya yi wa wata fyaɗe a Rugar Bello, yanzu da shi da ita mata da miji ne halak ɗin sa ce....


Free pages yana gab da ƙare wa biya kuɗin ka domin shiga Paid book tuni sun yi nisa da karatu😂🤷🏾‍♀️.... Biya 500 ta Wannan account ɗin 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity bank. Shaidar biya 08119237616. Ƴan nijar sun yi mini magana.
*🌈 IDAN BA KE 🌈*

_*Nimcyluv sarauta*_

15....
Saif ya ce "Aure kuma? waya ɗaura, dawa kuma?" Sheikh gyara tsaiwa ya yi zufa na yanko masa ta cikin naman jikinsa,kalmar auren ta gigita masa tunani dama lissafi baki ɗaya. Labo ya kalli Saif-wazir ya ce "Aradu aure aka ɗaura musu, babu wanda ya isa ya warware shi sai ikon Rabbi.. kai Giɗaɗo maza jawo mana su cikin Rugar Bello" cikin gargaɗi Saif-wazir ya nuna Labo da hannu ya ce "Saurara fillo kake kowa, an faɗa maka aure wasan yara ne? Kuma wanda kake cewa zaka aura masa ita already yana da aure wajan matar shi ma zamu, don haka babu wani aure idan ma kunyi sai ku warware auren yanzu nan" Labo ya ɗaga sanda sama gaba ɗaya sauran Fulanin suka ɗaga sanda sama tare da zagaye su Sheikh "ƙarya kake Aradu ina shemeka na sheme banza Alqur'anin Allah, aure kuma dole ne hukuncin duk wanda ya yi fyaɗe ko ya nemi lalata ƴar mutane ke nan, ku shige muje Rugar Bello" Saif-wazir zai magana Sheikh yaja numfashi da ƙyar yana girgiza masa kai domin sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi musamman da yake ɓangaren Fulanin suka shigo tsaf za su yi musu gayya. And he doesn't want that to happen. "But Sheikh....," Sheikh ya ware idanu wanda suke ɗaukan hankali kamar ba zai ce wani abu ba sai kuma ya yi ƙasa da murya kamar wanda aka ɗauke wa In-inar ya ce. "Saif-wazir" kallon Sheikh kawai Saif-wazir yake cikin mamaki.
Suna ƙoƙarin tsallake ta su shige Labo ya yi saurin faɗin "Waye zai ɗaukar maka matar ka? yadda ka kawo ta nan haka zaka ɗauke ta mu ƙara sa Rugar Bello" a fili Saif-wazir ya ce "Tab..." Domin yasan that's the first thing da Sheikh can't do it ba zai taɓa ɗaukan ta ba. A hankali Saif-wazir ya sunkuya zuwa inda take kwance zuciyarsa ta buga da ƙarfi lokacin da idanun shi ya sauka akanta. A ruɗe ya juya ya kalli Sheikh Aliyu haydar Aliyu wanda ya tattare Alkyabbar jikinsa idanun shi rufe lokaci guda jijiyoyin kansa suka fito hakan kuma tabbaci ne na zuciyar shi na kusa, tashin hankalin da Saif-wazir ya shiga lokacin da idanun shi ya sauka akan fuskar Halisa Danejo Rome yafi ƙarfin tashin hankalin da Sheikh Aliyu haydar Aliyu yaji akan batun auren nashi da suke ƙoƙarin ƙaƙaba mishi. Saif-wazir ya daidaita nutsuwarsa wani kuzari na zuwar masa mmkin abin da idanun shi ke nuna masa ya cika masa zuciya. Ɗaukan ta ya yi daidai lokacin da Sheikh ya runtse idanunsa yana juya baya da ɗan sauri bakinsa ɗauke da sunan Allah. Saif-wazir na gaba ɗauke da Danejo Sheikh Aliyu haydar Aliyu na binsa cikin nutsuwa da daddako haɗi da kamala yanayin yadda ya kame kansa yake tafiya zaka ɗauka sarki ko Hakimi ne. Gaba ɗaya ƴan Fulanin suka mara musu baya har zuwa Rugar Bello lokacin tuni saƙo ya isa wajan Arɗo gaba ɗaya sun fito tare da yin shimfiɗa a gaban wata bukka wacce ta cika da yalwar inuwa, tun daga nesa Arɗo ke kallon Sheikh Aliyu har cikin ransa bai na'am cewa zai aikata abin da Giɗaɗo ya faɗa ba, amma ya kasa fahimtar mene ya sanya yaji auren shi ne mafita a gare shi dama su baki ɗaya?. Saif-wazir na zuwa ya kwantar da Danejo wacce har lokacin bata farka daga suman da take ba, jini kuma bai daina zuba daga goshinta ba. Arɗo ya kalli Sheikh cikin mutumtaka ya ce "Ka zauna mana?" Ko inda yake Sheikh bai kalla ba balle ya ama shi, sai ma tsaiwa daya gyara yana ɗan duba time fuskar shi tai jajir. Arɗo ya jinjina kai yana ƙara samun ƙarfin gwiwar abin da zuciyar shi ke ayyana mishi. Cikin nutsuwa ya ce "Sannunku, an kawo ƙarar an kama wancan yana ƙoƙarin aikata abin da Rugar Bello ta hana, wasu sunce ya aikata ga yarinyar nan kwance, bisa doka duk wanda ya yi hakan muna ɗaura masa aure da ɗiyar wannan ya sanya zamu aura masa yarinyar nan a yanzu ba tare da ɓata lokaci ba" Sheikh dai jin abin yake kamar ta tsuniyar yara ko damuwa bai ba, auren Zahrah ba bai taɓa damunsa ba balle na wannan ƴar tayin yarinyar. Saif-wazir ya ce "Amma wannan kuskure ne, idan mutum baya so ba, kuma ai ba haka ake ɗaukan doka ba, shigowarmu garin kenan fa suka fara ihun ya yi me ne kamar wasu marasa ilimi?" Giɗaɗo ya ɗaga sanda zai makawa Saif-wazir Arɗo ya yi saurin cewa "A'a Giɗaɗo, ko ma dai yaya ne kuyi haƙuri aure babu fashi" Modibbo da tun ɗazo bai magana ba ya ce "Sai a karɓi sadaki wajansa ai babu lokaci" Labo ya ce "Ga wannan a wajansa muka amsa" ya miƙawa Modibbo zoben gold ɗin da suka amsa wajan Sheikh. Sai a lokacin Saif-wazir ya ƙara cewa "Ga kuɗi a bada zoben, yana da tsada sosai kuma yana da muhimmanci ga mai shi" Modibbo ya yi murmushin jin daɗi ya ce "Daman abu mai daraja muke buƙata ai" abu kamar wasa akan idanun Saif-wazir da kunan Sheikh aka ɗaurawa Sheikh Aliyu haydar Aliyu aure da Halisa Danejo Rome akan sadakin zoben gold. Modibbo ya zama waliyin Danejo Arɗo ya zama waliyin Sheikh. Mutane kusan ashirin suka shaida daga ciki harda Saif-wazir.

Shiru wajan ya ɗauka Saif-wazir ya rasa ta ya ya zai kalli idanun Sheikh ya ce da gaske Danejo matarsa ce? Zai amince da auren ne ko ya ya? Kamar gilmawar walƙiya haka Sheikh ya juya yana gyara Alkyabbar jikinsa kai tsaye baki n titi kuma ya nufa,ganin haka ya sanya Saif-wazir miƙewa da sauri Arɗo ya ce "Ina zaka baka ɗauki yarinyar ba?" Saif ya juya ya kalleta rauni ya bayyana a fuskar shi har baya son kallon yarinyar gani yake kamar idanunsa ke masa gizau da abin da yake gani ɗin. Da sauri ya ɗauke ta ya marawa Sheikh baya yana zuwa titi ya samu Sheikh zaune acikin mota ya dafe kansa da hannu bibbiyu hayaniyar duk ta sauya masa lissafi baki ɗaya, Saif na shirin saka Danejo cikin motar Sheikh ya ce "N...n.. No!!!!" Ya faɗa cikin tsawa da faɗa idanunsa na fitowa waje sosai da kyau, a tsorace ya ce "Jini na zuba a jikinta kada ta samu ƙarewar jini kuma ba zamu je da ita gida haka ba sai mun fara zuwa asibiti" kallon da Sheikh ya yi masa ya sanya Saif yin shiru yana ƙasa da ƙansa. "Please Yaa Lee Matarka...." Kafin Saif ya ƙarasa Sheikh ya yi wa motar key cikin wani irin azababban gudu ya juya kan motar tare da cillata titi ya nufi hanyar da zata mayar da shi Kano ba tare daya ƙarawa wajan Zahrah ba..
Baki Saif ya saka cike da mmkin zafin zuciya irin ta Sheikh Aliyu da alama za a sha fama kafin Sheikh ɗin ya amince da batun auren Danejo ɗin. Mota ya tsayar ya ce masa asibiti mafi kusa don Allah. Kai tsaye aka kai shi Specialist Yola dake Jimeta. Yana shiga reception yaci karo da wata cikin sauri ya ce "Oh sorry it was a mistake.." Tsaki ta ja ta ce "mistake ko rashin hankali Malam? Kana tafiya kai a sama" kallonta kawai ya yi shi bashi da lokacin ta ma, Saurayina ta ce "Banza kawai" Zahrah da hankalinta ya yi gida sbd zuwan wanda yake shirin zama mijinta ta ce "Wai Surayyerh har lokacin cacar baki gareki ne? Tunda muka zo asibitin nan ki ke neman faɗa" Surayyerh ta ɗaga hannu ta ce "Saurara Zahrah ke tunda kika samu cikin nan kike ji da masifa, daidai nake da ko wanne ɗan iska Wallahi" Saif-wazir ya kalli Zahrah da kyau kaya ne wanda suka kama jikinta sosai hannunta duk farce taci gashin doki, juyawa ya yi ya kalli Surayyerh ba tare ce komai ba ya juya zuwa cikin emergency. Kai tsaye aka bawa Danejo gado Dr ya kalli Saif-wazir ya ce "Suna?" Saif ya shafa kansa sbd sam bai sani ba sai kawai ya wayance da faɗin "Dr ka fara yi mata taimakon gaggawa, sai mu yi magana" Dr ya ce "Dole a buɗe mata file ai" "I knw, amma kulawa da ita ba zai hana buɗe file ba, a duba ta first buɗe file second" Dr ya miƙe tsaye tare da nufar ɗakin da suka kwantar da Danejo abun mamaki ba ita ba alamarta, cikin hanzari ya fito sukaci karo da Saif-wazir ya ce "Yarinyar nan ta gudu bata cikin room ɗin?" Saif ya ce "What?" Da sauri ya juya zuwa waje amma neman duniya babu Halisa Danejo Rome babu ko inuwarta "Innalillahi yau na shiga uku ko dai aljana ce yarinyar nan? Amma babban asibitin irin wannan ina zata?" Ganin bashi da wata mafita ya nemi abin hawa wanda zai dawo da shi Kano domin ba zai iya komawa Rugar Bello ba yace bai ga yarinyar ba, haka kurum su kashe sa a banza.

Ɓangaren Halisa ana kwantar da ita a saman gado A.c ta fara ratsa ta, ta farka da sauri tana dabe kanta, tsoro ya kamata tana mamakin yaushe tazo. Ita dai ta fito tallan Kindirmo ta ce bari ta biya ta Rugar Bello a hanya yunwa da jiri suka yarda ita, kanta ya daki wani dutse bata ƙara sanin inda take ba. Miƙewa tsaye tayi jikinta na rawa ta ce "Hande en boni gidan cire kai aka kawo ni wayyo Allah Dadata na lalashe, lalashewa ta sameni" kuka take sosai har da majina fuskarta tai jaa. Leƙewa tayi ta window taga ashe bayan asibitin ne, da sauri ta kama tagar ta dira baya duk da zafin da kanta ke mata amma haka ta dinga gudu kamar barewa a haka ta isa Rugar Rome. Shiri sosai Zahrah tayi ta tarbar Sheikh amma har dare babu labarinsa baƙin cikin duniya duk ya kamata ga ƙawayenta duk ta tara zata nuna musu haɗaɗɗan mijin da zata aura amma ya kwafsa mata.

Misalin 10:23 Abba Hakimi na zaune a Main parlour dashi da Momi kamar daga sama su kaga Sheikh ya shigo hannunsa guda ɗaya dafe da kansa, Momi zatai magana Abba Hakimi ya Girgiza mata kai alamar tai shiru,babu wanda ya kula ya shige part ɗinsa dake gidan, kai tsaye bathroom ya nufa bayan ya zame kayan jikinsa abin da bai taɓa yi ba shi ne, amfani da ruwan sanyi ya tsaya a shower na sauka akansa sanyi na ratsa masa tsakiyar kansa, sai numfashi yake fitarwa dan kansa ya kashe shower ɗin ya naɗe jikinsa a cikin wata bathroom mai ɗan kauri, idanunsa na rufewa sbd azababban ciwon kai a haka ya kwanta saman gado ya daɗe kafin barci ya ɗauke sa.

"Lafiyar Sheikh ɗaya kuwa?" Abba Hakimi ya ce "Kinga alamar bai da lafiya ne?" Momi ta ce "A'a, kawai yadda na shigo gidan ne" Apple ɗin hannunta da take miƙa masa ya amsa ya ce "Kada ki damu, duk sanda ya yi haka alheri ne ke bibiyarsa" tattaunawa sukai akan gobe za a kai kayan lefen na Sheikh ita ma zata a hankali ya ce "Allah ya kaimu" sai kusan 12 na dare Sannan Saif-wazir ya shigo ganin dare ya yi kai tsaye ya nufi part ɗinsa, motar Sheikh da ya gani ya bashi tabbacin ya dawo gida. Da batun Auren Sheikh ya kwana yana tunanin ya faɗawa Abba Hakimi ko ya yi shiru? Har barci ya ɗauke shi ba samu mafita ba.

Washegari da yamma wajan 5. Dr A'isha ta zabga tagumi Yaya Halima ta ce "Dr wai lafiya tun da muka dawo kike wata kala?" Dr A'isha ta ce "Wallahi Yaya tausayin Sheikh nake, ina zai kai wannan uwar matar? Na girgiza ban san rashin tarbiyyar ta ya kai haka ba, kalli da ita aka amshi kayan lefen fa?" Yaya Halima ta kalli Dr A'isha tana mmkin rashin control na bakinta da bata iya riƙe zance. "Kowa da tsarinsa fa Dr Allah dai ya sanya albarka" daga bakin ƙofa akace "Ba Amin ba, mugun ji da mugun gani ruɓaɓɓan baki ya kau daga kan Gadanga, yau ko ni ko uban Gadanga ya zaɓa" gaba ɗaya suka kalli bakin ƙofa, tana tsaye taci lace ɗauri har gaban goshi ta lafta uban Glasses a fuska wanda ya cinye rabin fuska. Cikin farin ciki Mother ta miƙe tsaye tana faɗin "Jadda" haɗe fuska tayi ta nemi waje ta zauna, Uncle Haroon ya shigo hannunsa riƙe da torelly ɗin Jadda ya zauna kusa da ita. Cikin farin ciki Mother ta ƙara cewa "Sannu da hanya Jadda ashe kina tafe" Jadda ta ɗauke kai sai da Mother tabar wajan, ta juya ta kalli Uncle Haroon murya can ƙasa ta ce. "Munafuka Algunguma duk masifa da yaƙin da ake a gidan fa bata sanar dani ba, shi ya sa na haɗe mata fuska na kame kai na, ba kaga jikinta ya yi sanyi ba, ai wlh yau sai sun bala'i ya sauka" murmushi kawai Uncle Haroon ya yi ta haɗe rai tana ƙanƙantar da idanu ta ce "Kaji masifa ko? Ba murmushi za kai ba cewa zakai nayi daidai" ya ƙara murmushi ya ce "Jadda duk abin da ki kai ai daidai ne" cikin ƙaramin lokaci Mother ta cika gaban Jadda da kaya kala-kala, Yaya Halima da Dr A'isha suka gaidata ta amsa a ciki. "Kinga ba kwaɗayi ya kawo ni ba, maza kira mini mijin naki" Mother ta haura sama yana zaune yana duba Invitation ɗin bikin Sheikh dana Zahrah Mother ta shiga a hankali ya ce "Barrister ya dai?" Kai tsaye ta ce "Jadda na kira" tana faɗin hakan ta juya, yabi bayanta da kallo da sauri kuma ya miƙe shima. A hankali yake sakkowa daga benen yana sakin fuska bayan ya zauna ya ce "Sannu da zuwa Jadda" banza Jadda tayi masa, ta zare Glasses ɗin idanunta ta miƙawa Uncle Haroon, ta cire mayafi shima ta miƙawa Uncle Haroon, fuskar Father cike da tsoro ya ce "Jadda lafiya me kike shirin yi haka?" Bata kula shi ba, ta buɗe rigarta tana nunawa father ta ce "mene wannan?" Kansa a ƙasa ya kasa cewa komai ta ce "Idan ba zaka iya ba, ai Ubangiji ya tsaga mini bakin magana nonon dana shayar da kai ne, kasan Allah tun nonon yana kwance ka lalata batun auren Gadanga da wannan gantalalliyar yarinyar, idan ba haka ba zan ɗaga maka nonon sama ka lalace kaje duk inda zaka...


*Not edited*
Masu tambayar yadda zasu biya kuɗin IDAN BA KE. Book 1, 2 ne. Mutum zai biya ₦500 har a gama littafin baki ɗaya. 6850917335 Na'ima Shu'aibu sulaiman fidelity bank. A tura shaidar biya ta nan 08119237616.
*🌈IDAN BA KE 🌈*

*_Nimcyluv Sarauta_*

16....

*I am proud of my fans wherever they are, nayi mamakin yadda kuka amshi littafin IDAN BA KE fiye da ZAIN-ABEED. Masoya TSINTACCIYA, MOON, UNCLE NE duk ba a barku a baya ba🥰💋for the first time zanyi rubutu akan labarin zanan ƙaddarar soyayya zallah🫰🏿a shirya a gyara zama sosai yanzu aka fara...*
#TEAM SHEIKH ALIYU HAYDAR ALIYU
#TEAM HALISA DANEJO ROME
#TEAM EL-BASHIR AHMAD SARKI
#TEAM ZAHRAH FAROUK


Jadda ta ƙara cewa "Kalle ni da kyau uwarka ce Jadda, Wallahi nono zan ɗaga maka kawai kabi duniya kaje duk inda zaka Aliyu tunda ka gagara, idan ya so ana nunaka da baki ana cewa gashi can uwar shi tai masa baki ta ɗaga masa nono shi ya sa yake ta galantuyi a duniya, duk wanda bai yarda ba, ni nai maka baki ba zaka iya kawo shi wajena na tabbatar masa" zufa ta dinga yankowa Father a hankali ya zame daga kan kujera zuwa inda take ya ce "Jadda don girman Allah kada kice haka, ki tsaya ki fahimci al'amarin nan I have a reason why I want Sheikh to get married with Zahrah." Uncle Haroon ya ce "Mene dalilin naka? Uwar yaron nan bata so, I don't agree either" Jadda dai kaɗa ƙafa take har lokacin tana riƙe da ƙirjinta cikin rarrashi Father ya ce "Jadda don ki fahimce ni Sheikh ba zai iya kula da dukkan al'amarin daya shafi kasuwancina da dukiyata ba, kullum ƙarfina ƙasa yake abubuwa na neman yi mini yawa, na bashi dama yafi sau goma akan ya kawo matar da zai aura amma yaƙi, Umar-khan yace tunda Sheikh yake magana bata taɓa haɗa shi da wata mace ba, kalli sharrin da akai masa tun daga jami'ar Madina, da ace yana da aure babu mai binsa da wannan sharrin shi ya sa na yanke hukuncin aura masa ƴar aminina tasan kan business sosai zata janye hankali Sheikh ɗin zuwa kasuwancin, Jadda ina son Sheikh Aliyu ban taɓa son wani abu kamar shi ba, kiyi mini uzuri ayi auren nan idan yarinyar ba tai miki ba sai ki ɗauki mataki" Mother ta girgiza kai cike da takaicin yadda Father yake tsara zan ce. "Aini duk bani da labarin haka, jiya jiya labari ya saman ana ta yaƙi a gidan naka, kuma yarinyar ƴar iska ce" Father ya kalli Jadda da kyau ya juya ya kalli Mother yana faɗin "ke kika faɗa mata Zahrah ƴar iska ce sbd ba ƴarki bace shi ya sa zaki ai bata musu ƴa?" Rai ɓace Mother ta ce "Ni na faɗa Engineer tunda haka zuciyarka ta shaida maka, kaga yaushe rabon da naje wajanka akan maganar Aliyu ko auren? Aje ayi aure lafiya nima zan zaɓawa Sheikh yarinyar da nayi niyya na aura masa ita" tana faɗin haka ta miƙe tare da nufar upstairs zuciyarta cike da tarin baƙin ciki. Baki buɗe Jadda ke kallon kowa kafin ta ce "Na amince ayi auren kuma na amince Maryam ta zaɓawa Gadanga yarinyar da duk tai niyya" Father ya ce "Amma Jadda daka aura masa Zahrah sai ya yi mata kishiya? Ba ai mata adalci ba" Jadda ta miƙe tsaye tana ƙanƙance idanu ta ce "Wai wacce ƙaniyar ce Zarra ko me? Ba ita ba ko uwarta ka aurawa Gadanga kwaranƙwasa sai anyi mata kishiya, Allah dai ya nuna mini ƴar banzar yarinyar da idanu naga abin da bai mini ba, maza ɓace mini da gani ko mene haɗina da kai dana tsaya shiga sabgar ka" Father ya miƙe tare da barin wajan yana faɗin "A huta lafiya Jadda" sai da yabar wajan Jadda ta sauke numfashi tana raɗawa Uncle Haroon ta ce "Ba gashi ba anyi sulhu komai ya lafa daman duk iskancin mutum ina zuwa shikenan, ai Alsulhu khair" murmushi kawai Uncle Haroon ya yi yana cewa sai Anjima zai dawo.
Sai a lokacin Jadda ta lura da Yaya Halima da kuma Dr A'isha kowa yana danna waya abinsa kasancewarsu masu ilimi da dukiya ya sanya suka kame kansu basu saka baki cikin abin da babu ruwansu ba.

Mother na zaune tana waya da wata friend ɗinta kamar daga sama Father ya faɗo ɗakin cikin faɗa ya ce "Burinki ya cika kin haɗani da mahaifiyata,she insulted me in front of people data hana auren Zahrah da naki auren ma sai ya mutu" tunda ya fara magana bata kula shi ba sai ƙafa da take girgizawa tana ci-gaba da yin wayarta hakan ya ƙona ran Father yaso ta tanka masa ya wanke ta tsaf.
Saif-wazir na zaune gaban Abba Hakimi ya kasa cewa komai. Abba Hakimi ya ce "Ya kai ne Saifuddeen?" Ya sauke numfashi ya ce "Abba ban san ya zaka fahimci maganata ba" Abba Hakimi ya ɗaga kansa tare da kallon Saif-wazir ya ce "Tunda ba zan fahimta ba ta shi kaje" da sauri ya ce "No Abba I'm sorry" shiru yai can dai ya ce "Daman akan zuwa Yola da mukai da Sheikh ne, tsautsayi ya faɗa masa na auren wata ƴar Rugar Bello" Abba Hakimi ya ƙara kallon Saif-wazir da idanun na fahimta a hankali ya ce "Uhm Aure dai?" In short, Saif told Abba Hakimi about everything that happened daga zuwansu Yola har fitar Sheikh mota da zuwan Fulanin har auren da aka ɗaura da zoben Sheikh ɗin matsayin sadaki, har maganar zuwa asibiti da ɓacewar yarinyar.
"Aiki jaa" Abba Hakimi ya faɗa a ransa wannan shi ne dalilin daya sanya Sheikh ya dawo a rikice kenan? "Kace yarinyar ta gudu? Zaka gane ita Rugar?" Saif ya ce "E, ta gudu Abba Rugar ma zan gane domin akan hanya take, amma bana ganin Sheikh zai amince da auren mata biyu lokaci guda" murmushi Abba Hakimi ya yi wanda shi kaɗai yasan ma'anar shi a nutse ya ce "Auren da ai masa na haɗi ne, wannan kuma Ubangiji ya ƙulla, Allah ya nuna mana zuwa Yola ɗaurin aure zamu je can Rugar" Saif-wazir ya jinjina kai alamar gamsuwa ta gefe guda kuma ya kasa faɗawa Abba Hakimi abin da ya gani a tattare da ƴar fillon wanda ya ruɗa masa lissafi ya hana shi bacci daren jiya. "Jirginsu Mai martaba ya tasu, zuwa ƙarfe huɗu zasu sauka yace Sheikh buƙatar ya je ɗakko shi, yanzu kuma lokacin barcin Sheikh ne" Saif ya duba lokaci ya ce "Yana barci tsakanin Zhur zuwa Asr jirgin kuma 4 zai yi landing akwai time Abba" Abba Hakimi ya ce "Mafi mushkila"
Bayan fitar Saif-wazir Momi ta ce "Amma bana ganin wannan auren ya ɗauro fa?" "Me ya sa A'isha?" Momi ta ce "Naga babu wani na Sheikh a wajan sai Saif" jinjina kai kawai Abba Hakimi ya yi yana ci-gaba da rubutun shi ta ce "kayi shiru?" Bai kalleta ba ya ce "Idan kika sake cewa I'll do the same thing, aure ba shaidu da sadaki yake buƙata ba? Saifuddeen ya ce shaidu wajan 20 a wajan, Zoben da suka amsa kin san darajar shi kam?, Aure ya ɗauro kamar na ko wanne ma'aurata" Momi tai murmushin jin daɗi ta ce "To Allah ya sa albarka,ya sanya matar shi ce har aljanna sai a faɗawa Barrister" nan ma Abba Hakimi ya ce "A'a Maganar ta tsaya iya mu, bana son ko su Umar-khan da Ishaq-hakim suji, hatta Barrister Maryam da mijin nata bana son suji" hira sukaci gaba dayi.

Ƙarfe 4:5 daidai Sheikh Aliyu Haydar Aliyu ya fito sanye cikin dark blue ɗin shadda jamper da babbar riga, sai ƙamshin Roja yake wanda ya a cika parlourn. Ƙafarsa cikin Leather shoe sumar kansa wacce ya rufe da hirami ta sha Ginger Geminal Oil-hair daga sajansa zuwa gemu sai kyallin Luxury Beard oil yake. Bakinsa sai ƙamshin LB Breathe herbal sugar breath freshener spray. Fitowar shi cikin parlourn ya yi daidai da shigowar Abba Hakimi, Umar-khan da Ishaq-Hakim na binsa a baya. "Daman yanzu nake shirin zuwa sashin naka sai gaka" zama ya yi Sheikh yana gyara Babbar rigarsa yau ba saika Alkyabba ba, a nutse cikin kamala murya mai ɗauke da kwarjini ya buɗe baki ya ce "Barka da yamma Abba" kallon kallo akai tsakanin Umar-khan da Ishaq-Hakim jin yau Sheikh bai In-ina ba, Abba Hakimi kam murmushi kawai ya yi hakan bai wani dame shi ba ya ce "Yawwa Sheikh Dadynka Mai martaba ya sauka yanzu kai suke jira" Sheikh ya duba agogo ya riga yasan sai biyar jirgin zai sauka yana komai bisa tsari. Bai ce komai ba ya miƙe tsaye Abba

2 Comments On IDAN BA KE
avatar
al-kausar

5 months ago

Reply

Dan Allah ci gaba daga page 11 naga a page 10 ya tsaya Kuma kince akwai complete anan arewa books

avatar
taskar

5 months ago

Reply

Replying to al-kausar

sai dai ki saya littafin a wurin marubuciyar ga nambarta 08119237616

Please Login or Register in order to submit comment