Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

raya su san abin da ke zuciyarka ne?" Father ya ce "Abba Hakimi ta ya ya zan ƙi ɗana? Shirman Fatimah ne" da sauri Fattoumah ta ce "Da gaske nake Mijin,ina jin yana faɗawa mother wai a nemo mahaifin Yaa Lee kuma ai ba kyau ƙarya" surutun Fattoumah ya jijjiga Mother bata taɓa haifar yarinyar mai kaifin bakin Fattoumah ba. "shige ki bamu waje Mamana kafin ranki ya ɓaci laɓe kike mana kenan?" Turo baki Fattoumah tayi tace "Mother kawai ki nemowa Yaa Lee Abbansa wanda zai so shi tunda father baya son sa" Abba Hakimi da Mother suka kalli juna da sauri kuma suka janye idanunsu ko wanne tunani fal ransa. Tsawa Mother ta yiwa Fattoumah ta tafi ɗakinu Maimoon tana sakin kuka ta fara bori a ƙasan carpet.

A nutse Abba Hakimi ya kalli Mother ya ce "Aliyu yana state c.i.d Barrister Maryam" a ruɗe Mother ta Kalli Hakimi hankali tashe take faɗin "An kama Babana? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un wallahi sharri ne ba gaskiya ba, kuma zan tabbata da hakan" Hakimi ya ce "Samu nutsuwa Barrister Maryam, mu duka ba zamu ja da ikon Allah ba, kuma da hujjar kare Aliyu, shi ya sa nazo naji ko ya faɗa muku wani abun?" Father ya yi dariyar baƙin ciki ya ce "Wannan ne zai magana? Ko ya yi bata da wani amfani me zamu fahimta banda, A...Aaaa...ƙikkkk... Yeee gaba ɗaya Aliyu bashi da amfani a rayuwarmu, naji baƙin cikin samunsa Matsayin ɗa namiji" wani baƙin ciki ya tukare zuciyar Mother idanunta na cika da hawaye ta ce "Sai yanzu na fahimta larurar Aliyu ta sanya kake ƙinsa? Ubangiji ya ɗora masa shi nake roƙa kuma ya ye masa" Abba Hakimi ya numfasa kalam Father sun bashi mmki a haka ya share ya ce "kayi babban kuskure Aliyu, kuma Sheikh abin Alfaharin duk wani ɗan Kano dama Najeriya ne, muhimmancin bai tsaya iya ƙasar shi ba, har ƙasa mai tsarki.. Allah ya kyauta wata rana zaka gane gaskiya lokacin da za kaji kunya" juyawa kan Mother yai ya ce "Akwai abin da ya faɗa miki ne, ina son shigar da maganar zuwa court ne" Mother ta ce "Yana cikin ƙoƙarin fahimtar dani suka taho wajanka ya faɗa mini bashi ya aikata ba, kuma ni ma na shigar da ƙara ni zan tsaya masa tare da Barrister Zainab" wayar Mother ce ta fara ringing ganin sunan Umar-khan ya sanya ta ɗauka cikin sauri ta miƙe tana faɗin "Ohhh ok on our way" kashe wayar tayi idanunta akan Abba Hakimi ta ce "Umar-khan ya ce muzo yanzu al'amarin ya shige tunani" da sauri ta nufi ɗaki tare da ɗakko mayafi da key car.

Abba Hakimi da Mother suka nufi state c.i.d hankali a tashe Maimoon da Zeefa da Fattoumah sai kuka suke a rayuwa suna ƙaunar yayan nasu duk da babu wata jituwa a tsakaninsu. Ko abinci suka kasa ci sai sallah kawai da suke suna addu'ar Allah ya kuɓutar da Sheikh ɗin. Hankali kwance Father yake zaune yana waya da babban amininsa ko da wasa bai masa magana akan matsalar da suke ciki ba, duk da cewa al'amarin ya gama zaga ko'ina a faɗin Nigeria.
A kiɗime Mother take bin su Saif-Wazir da kallo ganin yadda idanunshi ya yi jajur alamar kuka suka sha. "Ina Babana ina Aliyu mai ya faru da shi?" Shiru Saif-Wazir ya yi mata, ta juya kan Umar-khan ta riƙe wuyansa sosai cikin faɗa ta ce "Where's my son Umar-khan? Ina Aliyuna?" Umar-khan ya yi ƙasa da idanun shi ba tare da ya ce komai ba. Sakin Umar-khan tayi ta nufi wajan Ishaq-hakim ta ce "Ishaq-hakim faɗa mini gsky ina Aliyu me akace yana da gsky ko? Ba aikata abin da ake zarginsa ba?" Hannunsa ya ɗaga tare da nuna mata wani waje da sauri ta juya Idanunta ya sauka akan Sheikh Aliyu Haydar Aliyu wanda aka cire masa Jallabiyar jikinsa aka ɗauresa da Sarƙa tun daga wuyansa hannunsa zuwa ƙafarsa farar fatar jikinsa tayi jajir bakin Ishaq-hakim na rawa ya ce "Mother Sheikh ya amsa laifin da ake zarginsa ya tabbatar shi ne ya lalata ƴan matan hadda ciki.....


_*IDAN BA KE...* labari ne da kuka daɗe ba kuci karo da irinsa ba, ƙaddarar labarin akan soyayya ne mai tsayawa a zuciya da saka shauƙi a zuƙatan masu karatu..... Tsammaci abin da baka tsammani salo na musamman🫣💋 08119237616._
*🌈 IDAN BA KE 🌈*

*_Arewabooks@Nimcyluv_*

10....
Kasa magana Mother tayi sai Ishaq-hakim da tabi da kallo tana son gasgata abin da yake faɗa. "Ta ya ya Sheikh zai amsa laifi fyaɗe? Laifin da duk duniya ta san ba zai iya aikatawa ba?" Ta faɗa a fili tana sakin wani raunataccen kuka mai tsayawa a zuciya ba zata iya kallon Sheikh cikin sarƙa a ɗaure ba, kamar wani ɗan fashi ko Kidnapper. Umar-khan ne ya kama Mother wacce take ƙoƙarin zubewa a wajan sbd kukan da take idanunsu ya yi jajur ya ce "Ki daina kuka Mother, wata kila Sheikh ya amsa laifin ne sbd rashin mafita, mu duka abin ya zo mana cikin wani sabon yanayi wanda bamu taɓa riskar kanmu ciki ba, Ubangiji ka ɗai ya san gaskiya kuma shi muke roƙa ya fidda Sheikh Aliyu daga cikin wannan jarrabawar" gaba ɗaya zuciyar Mother ta karaya tunaninta ya tsaya cak duk inda take neman wata hujja ta kare ɗan nata babu.
Da hannu bibbiyu ta riƙe Umar-khan ta ce "Kai ne kake tare da Babana Umar-khan, ka taimaka mini nasan kasan Aliyu ba zai iya aikata hakan ba, yana tsare imaninsa yana amsar rayuwa a duk yadda ta zo masa" Umar-khan ya mayar da hawayen dake cika idanunsa kafin ya zaunar da Mother ya ce "Be patient Mother, muyi addu'a kawai amma da ace zan iya bada shaida, da iya abin da zan faɗa ya isa ya wanke Sheikh daga cikin zargi"

"That's enough, this is not a place to make noise" Wani daga cikin jami'an tsaron ya faɗa yana daka musu tsawa.
Sai a lokacin Abba Hakimi ya yi ajjiyar zuciya domin shi ma Al'amarin ya girgiza shi fiye da tunanin kowa, zuciyarsa shi zafi take masa sosai. A nutse ya juya ya kalli Ishaq-hakim ya ce "Ka mayar da Barrister Maryam gida yanzu, ka ce ina buƙatar ganin Aliyu immediately" da girmamawa Ishaq-hakim ya amsawa mahaifin nasa, idanunshi akan Mother yana jiran ta miƙe.
Cikin kuka ta kalli Abba Hakimi ta ce "Ina son nayi magana da Aliyu Please Hakimi" Kafin Abba Hakimi ya bata amsa wani daga cikin Jami'an tsaron ya ce.
"No way Madam" tana share hawaye ta ce "Don girman ka bani 2 minutes nayi magana da ɗa na, ina son tambayarsa, tare da kwantar da hankalin shi" cutting nata out ya yi da faɗin. "Isn't necessary Maaah..." A ƙagauce Abba Hakimi ya ce "take her out Ishaq-hakim" Mother na kuka sosai tana kiran sunan Sheikh Aliyu aka fitar da ita waje, Aliyu shi ne rauninta ka kaf cikin yaranta tafi ƙaunarsa duk abin da Mother ta mallaka daga cikin dukiyar iyayenta Aliyu ta bawa, She owned all her property for him, Lands, houses, companies, all signed in the name of Aliyu's property.
Su Mother na fita Abba Hakimi ya kalli jami'an tsaron cikin murya mai taushi ya ce "Kun samu hujja mai ƙarfi da kuka kama mini ɗa na?" Ɗaya ya sunkuyar da kai cikin girmamawa ya ce "Har yanzu bamu da hujja, amma a duk bin ciken da mukai Sheikh ƙara shiga ciki yake, yaƙi buɗe baki ya yi magana, gwamnatin Madina da universityn ƙasar sun matsa akan kwana biyu suka bayar idan ƙasa Nigeria bata ɗauki mataki ba, zasu ɗauka da kansu domin su irin wannan cases ɗin kai tsaye suke bincike kuma hukuncin kisa ne" runtse idanu Abba Hakimi hukuncin kisan ya daki zuciyarsa ainun. Umar-khan da bakinsa ke rawa tun ɗazo sbd masifa ya ce "Ita kanta gwamnatin Madinan idan bata da hujja dole ta haƙura, ina masu kawo ƙarar? Daga ina wannan zan can ya fito? Ina ƴan matan da akaiwa fyaɗen suke?"
"Stop raising your voice, we are working on our system, nan ba Court bace" Umar-khan zai sake magana Abba Hakimi ya yi gyara murya kafin ya ce "Ka bari abu komai a nutse, shi ya sa na mai da Barrister Maryam gida" Saif-Wazir dai na tsaye duk yadda suka so a basu Sheikh su yi magana hanawa akai. Kuma a gobe za a kaisa court domin fara gabatar da Shari'a tun da case ɗin ya zo da hargitsi. Haka suka komai gida zuciyoyin kowa babu daɗi.
Sheikh na zaune daga shi sai single da wani farin trousers mai laushi tunda yake a duniya babu wanda ya taɓa ganin tsari da zubin halittarsa sai yanzu, an tuzarta shi tuzarcim daya har zuƙa kuturwar zuciyarsa, shi kaɗai sai tsuma yake shi da ko sauro baya so baya ƙaunar yaga baiwar halittar da tsaraicin jikinsa, yana tsarkake jikinsa domin sirrinsa ne, amma yau da wanda ya dace da wanda bai dace ko wanne tom and jerry gani yake abin ya yi masa zafi ainun. Dalilin daya sanya ya amsa laifin kenan ba tare daya shirya hakan ba.

Mother na komawa gida ta samu Fattoumah na zaune ita ɗaya a Parlour da sauri Fattoumah ta ce "Mother ina Yaa Lee? Ba zai dawo ba?" Murmushi mother ta yi tana ɓoye damuwar ranta ta ce "Ya dawo mana Manana, yan gidan Abba Hakimi where's your sisters?" Da hannu ta nuna mata part ɗinsu, Mother ya kama hannunta suka shiga ciki. Yaran duk suna zaune sanye da hijabi sunyi shiru bayan sunci kuka sun ƙoshi, cikin faɗa ta ce "Maimoon, Zeefa what's this? Kuna da hankali zaku shigo ɗaki kuyita kuka kamar anyi mutuwa, Depression kuke son ya kamaku ko mene?" Gaba ɗaya suka miƙe tsaye jikinsu na rawa za su yi magana ta ɗaga musu hannu ta ce "Ku fita a nan wajan, maza aje a kunna kallo ayi" fita gaba ɗaya sukai jiki babu ƙwari mother ta bisu da kallo tausayin su na kamata tasan duk sanadin Aliyu Haydar suka shiga wannan damuwar. Kuma ita idan har ƴar halak ce ba zata sake zuwa wajan Father ba akan maganar Sheikh Aliyu ɗin ba.
Tana fitowa daga cikin bedroom ɗin upstairs ta haura zuwa nata bedroom ɗin wayarta ta ɗauka ta shiga kiran Barrister Zainab akan gobe zasu shiga Court sun daɗe suna waya kafin ta kira Yaya Halima anan ta kwantar mata da hankali ta ce ita ma ta nan zuwa dan sunyi nisa ne. Har Mother ta miƙe da sauri kuma ta koma ta zauna domin gaba ɗaya ta manta da batun Jadda cikin sauri ta danna numberta wayar ta jima tana ringing kafin a ɗaga a fusace akace "Allah dai yai gutsi gutsi da duk wanda yake addabata wannan masifar har ina, ba lallai mutum yaga Annabi ba" A hankali Mother ta ce "Jadda ni ce Maryam" Jadda ta ce "Wata abace Maryam kuma? daga wacce duniya mena haɗa dake?" Shiru Mother can kuma ta ce "Mahaifiyar Sheikh Aliyu" Jadda ta zabga salati da duk ƙarfinta ta ce "Yanzu Maryam cewa nayi ban gane ki ba? Masifar gaisuwa ce bana so, Ina shi Aliyu yana can Madina ɗin ne?" Mother ta ce "Baki san meke faruwa da shi ba?" Jadda dake kishin giɗe tayi saurin Miƙewa zaune tana faɗin "Allah ya isa, dake Maryam da shi Aliyu Allah dai ya isa wani abu ne ya samu Sheikh bani da labari?" Kafin Mother tai mgn father ya ƙwace wayar tare da kashewa baki ɗaya ya kalli Mother ya ce. "Yanzu Barrister akan wannan maganar zaki haɗani da Mahaifiyata? Su kike ta tsine mini tunda kin san bakinta ba shi da tsarki wajan sakin magana da kwasa ta" banza tai masa ba tare da ta ce komai ba, yana ƙoƙarin sake magana ta miƙe tsaye tana faɗin "Idan ka gama ka ajjiye mini wayata, I have something to do with my phone" tana faɗa ta shige toilet domin zuciyarta a kusa dake da shi. da idanu ya bita kana ya ajjiye wayar yana mmkin halin mata a wasu lokutan.

Gari na waye Barrister Zainab ta zo suka fita zuwa State C.i.d ita da Mother abin mamaki gaba ɗaya ƴan jaridu sun cika gidan Redio, da t.v kowa yana jiran a fito da Sheikh Aliyu Haydar Aliyu. Cikin nutsuwa Barrister Zainab dake driving ta kalli mutanan ta ce "Am still wondering ta ya ya zan can nan ya shiga kunnuwan Al'umma" Murmushin taƙaici kawai Mother ta yi wai duk akan Innocent son ɗinta ake wannan tururuwar kamar wanda ya kashe mutum?. "Allah ya kyauta, mutane akwai su da son gulma musamman ƴan jarida wallahi" I.d card ɗinta wanda ke nuna ita cikakkiyar lawyer ce mai zaman kanta ta nuna kana aka basu damar shiga, tun kafin Barrister Zainab ta yi parking idanun Mother ya sauka akan Sheikh wanda aka fito dashi cikin wata ƙatuwar sarƙa tare da wasu manyan ƴan fashi, wani abu ya tsaya mata wanda bata taɓa jin irinsa ba, ko hawaye ta kasa a wannan lokacin. Da sauri ta fita haka ma Barrister Zainab ɗin, ana ƙoƙarin saka Sheikh Aliyu cikin mota wata mota ta shigo da gudu cikin haraba wajan hakan ya sa duk suka daka ta. Wani babban jami'in tsaro ne tare da Abba Hakimi suka fito daga cikin motar sai wata matashiyar budurwa wacce Fuskarta ta kumbura sosai sbd kuka. I.G ya kalli jami'an tsaron cikin tsawa ya ce "Maza a cire sarƙar nan, a bawa Sheikh Aliyu Haydar Aliyu kayansa ya saka, He's Innocent ya fita daga jikin zargi, Wannan matar ita ce wacce ta shirya komai, she's the reason behind, She is the one who harmed Aliyu"
Gaba ɗaya kallon budurwar sukai wacce take kuka kamar ranta zai fita. A karo na farko Sheikh Aliyu Haydar Aliyu ya ɗago idanunshi tare da sauke su akan budurwar wani irin lallausan murmushi ya sauke wanda ya kusan ɗauke hankali jama'a tare da basu mamaki, hatta Mother tai mamakin ganin murmushi a fuskar Aliyun. Cikin ƙaramin lokaci aka sakawa Sheikh wata jallabiya mai kama da Alkyabba tare da wani farin hirami nan da nan kamalarsa ta fito haibarsa ta cika Idanun kowa. I.G ya bada umarnin a kama budurwa Sheikh ya yi gyara murya yana tafiya a nutse cike da kamala tsayawa yai daidai inda budurwar take, for the first time a tsayin rayuwarsa daya tsaya gaban mace kana ya juya ya kalli I.G sanin cewa ba zai iya taɓa jikin I.G ba yasa ya kama hannun Abba Hakimi ya riƙe da kyau yana runtse idanunshi, ƙafarsa ya ɗaga ya buga a ƙasa cikin In-ina ya ce "Aahhhh ahhha abarta, dooo.. do.. domin ba ba ba....ba a faɗa da Aljani.

Not Edited
08119237616
🫰🏽kai tsaye ga mai buƙatar littafin.
*🌈 IDAN BA KE 🌈*

*_Arewabooks@Nimcyluv_*

11.....
Abba Hakima ya kalli Sheikh a nutse yana mai sakin murmushi shi ma, tare da juyawa ya kalli budurwar wacce taƙi yarda ta kalli inda Sheikh ɗin yake, tun daga sama zuwa ƙasa Abba Hakimi ya ƙare mata kallo kafin ya ce "A'uzu bi wajhillahil karim, Wabi kalimaatil lahillati la yujawizuhunna barran wala fajiran, wabi asma'illahil husna kulliha, ma alimtu minha wa malam a'alam min sharri ma yanzilu minas sama'i, wa zara'a fil'ardhi, wa min sharri ma yakhruju minha, wa min fitnatillaili wan nahari, wa min ɗawariƙil laili wan nahari, illa ɗariƙan yadruƙu bikhairin ya Rahamanu. Wa min sharri kulli dàabbatin Rabbi akhizun bi nasiyatuha inna Rabbi ala siraɗin mustaƙim" jikin budurwar ne ya fara rawa sosai, tsoran Abba Hakimi da Sheikh Aliyu Haydar Aliyu suka cika mata zuciya, bata son su cutar da ita tunda ita bata zo da nufin hakan ba, kuma daman Ubangiji ya ɗora mata tsoran Sheikh ɗin tun ba yanzu ba, tana jin girma da nauyinsa tare da shakkar sa kwarjininsa yafi komai dagula mata lissafi. Idan ka ɗauke Abba Hakimi, No one understands the words of Sheikh Aliyu.

"No!!!"
Sheikh Aliyu Haydar ya furta a nutse yana riƙe hannun Abba Hakimi wanda bakinsa ya kasa yin shiru da addu'ar da yake, dalilin hakan yasa budurwar ta nemi birkicewa wanda kuma daga Abba Hakimi sai Sheikh ɗin ne kawai suke ganin hakan. Shiru ya yi da addu'ar yana kallonta kafin ya juya ya kalli Sheikh fuskarsa ɗauke da annuri irin na cikakkun dadtawan nan ya ce. "Yaushe Aliyu ya samu abokai haka bani da labari" a wannan karan Sheikh bai murmushi ba sai rirriƙe hannun Abba Hakimi da ya yi yana lumshe idanunsa tare da buɗewa alamar "Bai san yadda akai hakan ya faru ba" riƙe hannu Sheikh ɗin kai tsaye Abba Hakimi ya yi domin kai tsaye ya fahimci karatun idanun na Sheikh.
I.G dake tsaye shi da Barrister Maryam yana bata haƙuri ya ce.
"I'm sorry, action was taken without investigation, we were wrong" kasa riƙe kanta mother ta yi cikin losing control ta ce. "You have defamed Sheikh's name, all those who respect him have now stopped, Sbd Kuskuren ku my son is innocent na riga dana faɗa muku, but you refused to understand me" Bar Zainab ta numfasa cikin rashin jin daɗi ta ce "Everything that has happened has already happened, kawai a kira ƴan Jaridu a shaida masa Sheikh bashi da laifi, sharri ake masa bai san komai ba a wanke sunan shi daga ɓacin da ya yi" cikin martabawa da nuna rashin daɗin abin da duk ya faru I.G ya ce.
"Aikinmu ne hakan, za muyi abin da ya dace muma ba zamu so sunan Sheikh ya lalace ba yana da girma da daraja a idanun ba" Mother gaba ɗaya haushin duk wasu jami'an tsaron take ji hakan yasa cikin sauri ta juya zuwa inda Abba Hakimi da Sheikh suke tsaye, idan ka gansu zaka ɗauka da gaske Hakimi shi ne ya haifi Sheikh sbd tsananin haibar dake maƙale a jikin ko wanne kusan duk halin Hakimi Sheikh ya kwashe shi tas.
Kallonsu ta yi cike da son ko wanne wanda ke rinjayar zuciyarta ta ce "Thank you Abba Hakimi" murmushi kawai ya yi bai ce mata komai ba, tana ƙoƙarin sake magana ya yi saurin barin wajan zuwa cikin motar da Umar-khan ya buɗe masa baya.
Tsaye Sheikh yana bin mahaifiyar tasa da kallo ganin tai shiru ya waro mata manyan Idanun shi yana son cewa wani abu amma ya ja bakinsa ya yi shiru a hankali ta ce "zaka bini ko Abban naka za kabi?" Bakinsa ya motsa yana rufe idanu tare da fara buga ƙafa yana riƙe jikinsa da kyau cikin In-ina ya ce "Zazzzza... zan zan zanje gida wajan fa... fa.. father ina soooo son ganinsa"
haushi ne ya kama Mother ganin duk abin da ake Sheikh yana maƙale da son mahaifinsa. "Father baya gari, kaje wajan Hakimi ka huta da kyau gobe sai kazo mu tattauna, ina tunanin za a haƙura da zuwa Madina haka" girgiza mata kai ya yi bai ce komai ba ya juya ganin har lokacin Abba Hakimi na zaune bayan motar, yanzu zuwa shima ya shiga baya Ishaq-hakim ya jasu. daga nan Bar Zainab gidanta ta shige hakan yasa Umar-khan ɗaukan Mother a ɗaya daga cikin motocin Sheikh suka nufi gida, Saif-Wazir kuma ya tsaya domin magana da ƴan jarida.

Suna tafe a hanya Sheikh na yiwa Abba Hakimi hira cikin nutsuwa duk da In-ina yake amma Hakimi na fahimtar komai da Sheikh ke faɗa, a duk maganganun Sheikh ba za kaji kalmar MACE ta fito daga bakinsa ba, balle har ya ware wata musamman yana magana a ganta, Murmushi kawai Hakimi yake Ubangiji ne shaidar son da ya kewa Sheikh a jinin jikinsa yake.
A haka suka ƙarasa haɗaɗɗan gidan Abba Hakimi dake Dawaki roud, gida ne irin na sarauta mai kyan tsari da fasali ko'ina ma'aikata ne , motar na tsayawa Sheikh ya fito ƙwayar idanunsa na nuna gajiyar da yake ciki.
Bai tsaya jiran Abba ba, kai tsaye ya nufi part ɗinsa wanda yake cikin gidan Abba Hakimin wanka ya yi da ruwa mai zafi yana gamawa ya fito ɗaure da babban towel idanunshi na janye wa barci na cin ƙarfinsa ya ɗauki wani tsadaddan lotion, Shea body butter ya shiga shafawa saman fatarsa a kasalance, Engage Cologne Spray ya fesa a fatarsa sbd ɗauke zafin da ya keji yana gamawa ya miƙe zuwa clothes ɗinsa ya ɗauki wani trousers mara nauyi ya saka ko riga bai saka ba, ya cilla mint bakinsa ya kwanta saman bed yana lulluɓe jikinsa da bargo, ganin rana ce ya sa ya kunna A.c tare da rufe idanunshi cike da fatan barci ya ɗauke shi.

Washegari gari tun da Sheikh ya farka bai koma barci ba, har ya fita sallar Subhi sai da gari ya yi haske wajan 6:30 ya dawo gida jikinsa duk ciwo yake masa sbd rashin gym da bai ba, wanka ya ƙara yi ya shirya cikin Scabal wool suit white colour sai red ɗin necktie. Sai Diamond Rolex daya maƙala a hannunsa, yau a Yaa Lee ya fito ba a Sheikh ba, domin kusan siffa biyu gare shi, idan zashi bank shigar suit yake duk abin da ya danganci addini ajjiye shi yake a gefe amma yana zuciyar shi, idan kuma ya sanya Alkyabba da rawani yana matsayin Sheikh a wannan lokacin ne ba Yaa Lee ba. Wayarsa ya ɗauka jacket ɗin sa a hannu cikin nutsuwa ya fita zuwa main parlour.
Ƙamshin ROJA shi ne ya fara kaiwa su Abba Hakimi ziraya yana zaune da jallabiya gefensa kuma Ishaq-hakim ne da Saif-Wazir shirya zasu shi wajan aiki, sai Momi A'isha tana zubawa Abba Hakimi Shayi mai zafi. "Mrng Yaa Lee" jinjina kai ya yi idanunshi akan Abba Hakimi ya furta. "B...bar bar barka da safi fifi fiya".

"Ya ka kwana? da ciwon kan?" Rufe ido ya yi tare da buɗewa alamar "Allahamdulillah" Momi A'isha ta amsa gaisuwar Sheikh ɗin wacce ya yi mata ita cikin In-ina, tea ta haɗa masa mai zafi ta zuba 2spoon na honey ta juya kaɗan tare da bashi. Amsa ya yi a kame yake shan tea ɗin yana sauraran maganar Abba Hakimi da yake ce masa "komawa Madina ba yanzu ba, kada ya fara tunanin hakan" sanin ba zai iya ja da maganar Abba Hakimin ba yasa ya miƙe yana ajjiye cup ɗin hannunsa, Ishaq-hakim da Saif-Wazir suka miƙe tare da bin bayansa, wata farar mota ya shiga mai Sheikh no 5 yana shiga driver ya ja. Ishaq-hakim da Saif-Wazir kowa ya shiga motarsa suka nufi S.A.H BANK.
tun kafin ya Ƙarasa cikin bank ɗin wanda ya kasance mallakinsa ma'aikatan bakin Sheikh Aliyu Haydar bank suka shiga mutuwarsu ƙwarai. miƙewa ake ana gaida shi hannu kawai yake ɗaga musu har ya shige wani baban office. Wunin ranar Sheik cikin duba files and Ducoments yake.
3:30 yana ƙoƙarin barin Office ɗin saƙon father ya sauka Wayarsa. Da fararen idanunsa yake bin message ɗin da kallo yana mamakin yanzu kuma kiran gaggawar mene?. Da wannan tunanin ya shiga mota Driver ya ja suka nufi unguwar su Sheikh.
Tun a harabar gidan ya san akwai matsala domin kai tsaye idanunshi ya sauka akan motar Abba Hakimi data Yaya Halima sai ta Uncle Haroon.

Ƙamshin turarensa ya bayyana zuwansa, Mother dake zaune saman Kujera yana kaɗa ƙafa ta kalle shi kafin ta ɗauke kai, Uncle Haroon ma kallon Sheikh ɗin ya yi, a kame ya ƙarasa kusa da Abba Hakimi ya zauna yana ɗauke idanunshi daga kan jama'ar daya rasa meeting ɗin me ake.

"Tun da Allah ya kawo shi sai aji ta bakinsa, amma Sheikh ya shige lokacin da za a yi masa auren dole, a baya ba ai masa ba balle yanzu?" Yaya Halima ta furta cike da jin haushin father. Shi ma father da zuciyarsa ke kusa ya ce.
"Bashi da amfani, domin ba zai faɗi abin da kowa ke buƙata ba, na daɗe da sanin cewa Aliyu shi ne ƙaddarata, shi da yake namiji wanda ya kamata ya tsaya kan dukiyata amma ya kasa hakan, duk mutanan da suke buƙatar contract daka gareni idan har suka ji yadda Aliyu ke banzar maganar shi suke contract In-inar Aliyu ta ja mini asara mai yawan gaske, don haka ni bashi da amfani a gareni" sai a yanzu suka fahimci rashin jituwar da babu tsakanin father da Aliyu cikin ladabi Abba Hakimi ya ce "Baka yarda Ubangiji ya ɗorawa Aliyu wannan larurar ba? kenan baka

2 Comments On IDAN BA KE
avatar
al-kausar

5 months ago

Reply

Dan Allah ci gaba daga page 11 naga a page 10 ya tsaya Kuma kince akwai complete anan arewa books

avatar
taskar

5 months ago

Reply

Replying to al-kausar

sai dai ki saya littafin a wurin marubuciyar ga nambarta 08119237616

Please Login or Register in order to submit comment