Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

naso yi ma.." Abba ya kalli Prince da mmki kafin ya ce "Shi ne daidai da rayuwarta, shi ne Bil-adam shike da ikon kasancewa da ita, ba kai ba da kake Hallitar Ubangiji ta ban ƙasa ina rabaka da son zuciya, koda muke aljanu hakan bai zama lasisin da zamu cutar da wata hallita dake duniya ba, ko me zakai ba zaka taɓa iya cutar da shi ba" A hargitse Prince jiki na rawa yana rikiɗewa zuwa suffar aljanu ya kalli Safwan ya ce "Kai ne ka faɗa masa abin da na aikata ko? Kai ke ko?" Kafin Safwan ya yi magana Prince ya ɗaga sa zuwa sama tare da buga ƙasa da jikin dutse yana ƙoƙarin sake ɗaga Safwan, Abba yai wata kururuwa hakan yasa Prince yin kururuwa shima lokaci guda suka koma aljanu...

08119237616...
*🌈 IDAN BA KE 🌈*

_*Zaku samu cikakken labarin a Arewabooks, kuyi searching sunan littafin ko username Arewabooks@Nimcyluv*_

8....
Ihu da kururuwa Prince ya din ga yi, sbd tsananin azabar da Abba ya ganawa masa. Cikin wata kakkausar murya wacce take nuna cewa ko a cikin Aljanu shi ɗin nada banne, kuma taƙadiri ne. "Akan aurena dake kan Halisa banƙi na kashe kowa na illata shi ba, daga ci hadda kai Abba, ba ruwana da kasancewar ka mahaifina, kada ka rabani da Danejona zakai babban kuskure zanyi ɓarna a duniya" Bakin Abba na fitar da hayaƙi kamar zai kunna wuta a ciki ya ɗaga hannunsa sama gaba ɗaya ya naɗe Prince cikin wata sarƙa da yana bakinsa ɗauke da addu'ar neman samun nasara akan Prince ɗin.
Duk ihun da yake bai hana Abba ya sarƙafesa cikin yanar ba idanunshi ya yi wata kala. Cikin ɗaga murya mai amo! Ya ce "Na raba aurenka da Halisa, babu kai ba ita, kuma a yanzu zan cire cikin dake jikinta mara imani mai muguwar zuciya" yana faɗin haka ya yi girgiza tare da ɓatar da Prince ɗin baki ɗaya daga wajan. A hankali Abba wanda Asalin sunansa ya kasance MURWAS ya sauke numfashi, tare da juyawa ya kalli Halisa dake kwance a ƙasa tana barci, juyawa ya sakeyi ya kalli Safwan dake kwance shi ma. Cikin nutsuwa wacce ba zata addabi dabbobin dajin ba ya yi Girgiza tare da rikiɗewa ya koma suffar mutane sak. Hannuna ya ya ɗauki Halisa Dajeno Rome da sauri ya nufi cikin Rugar Rome zuciyarsa fal farin ciki ganin yau ya raba ɗansa Bilal da Bil-adam.
Babu kowa cikin rugar kamar an share hakan yasa ya fara bin bukkokin Rugar da kallo kamar daga sama Hamma Yabi ya fito daga cikin ruga zufa na yanko masa hannunsa riƙe da ƙwarya maganin gaba ɗaya tunaninsa ya yafi wani wajan bai lura da mutumin dake tsaye yana binsa da kallo ba. "Jamɓanduna" Abba ya faɗa yana kallon Hamma Yabi dake ƙoƙarin yin gaba, tsayawa ya yi yana duba mutumin da ya ce masa Ina kwana, cike da mamaki ya ce "Jamni tawon" ma'ana lafiya. Abba ya jinjina kai ba tare da ya ce komai ba, jikin Hamma Yabi na rawa ya amshi Danejo daga hannun Abba kafin ya ce "Ikon Allah, ina kasa meta? Tsayin mako guda ta ɓace mana ba ita ba labarinta, shai Allahamdulillah" Murmushi mai sanyi Abba ya yi cikin nutsuwa ya ce "Ayyah ni ma yanzu ina iyu a cikin ruwan na ganta kwance gefen ruwan" cikin nuna jin daɗi da manta halin da Dada ke ciki wanda duk rashin Danejo ya haifar da haka ya ce "Shannu, wallahi shannunka kaji" kai kawai Abba ya ɗaga yana ƙarewa yanayin rugar kallo kafin ya juya bayan sun yi Sallama da Hamma Yabi yabar wajan. Yana fita ya ɓace a wajan baki ɗaya.

Dada na kwance bakinta na fitar da wani ruwa kamar dafara Shatu na gefe tana kuka tamkar ranta zai fita. A cikin wannan halin Hamma Yabi ya shigo cikin bukkar hannunsa ɗauke da Danejo wacce har yanzu take bacci. Jikin Shatu na rawa ta miƙe fuskarta cike da hawayen halin da mahaifiyarsu ke ciki, amma hakan bai hana Fuskarta baiyyanar da farin cikin da zuciyarta ke ciki ba na ganin Yayarta Danejo. Bakinta na rawa ta ce "Hamma ina ka samu Danejo, da gaske ita ce yanzu Dada zata tashi naji daɗi sosai" bai ce komai ba ya kwantar da Danejo gefen Dada idanunsa akanta ya ce "Maza kawo mini ruwa" Shatu ta miƙe da sauri tare da nufar tulo ta tsiyayi ruwan mai ɗan sanyi, tana bashi ya shiga shafawa Danejo yana kiran sunanta. A hankali ta sauke ajjiyar zuciya tana buɗe ido a nutse. "Danejo"... "Halisa" Shatu da Hamma suka kira sunanta lokaci guda,a sanyaye cikin sanyin jikinta kamar kullum ta shiga binsu da idanu. "Kin farka?" Kalmar Hamma ta sanya ta lumshe idanunta kana ta buɗe a hankali tana sake binsa da kallo kafin ta yunƙura zuwa zaune "Naga kuna ta kallona kamar za a cini ɗaya?" Murmushi Hamma ya yi ya ce "Munji daɗin ganinki Danejo, mako guda kenan mun rasaki kin ɓace daga idanunmu" da Mmki take kallonsa ɓata? Mako guda? Taje ina? Ita gani tayi kamar barci take mai ɗauke da mafarkai kala-kala. Shiru tayi tana ƙara sauke numfashi tare da fara tunanin maganar Hamma Yabi. "Hankalinmu ya tashi, Kullum Dada cikin kiran sunanki take, gashi yanzu ko buɗe ido ba tayi jikinta ya tashi ina tsoro kada mu rasa Dada kamar yadda muka rasa Baffa" ambaton sunan Dada ya saka Danejo saurin juyawa zuwa gefenta manyan idanunta ta buɗe "Dadata" ta furta a ruɗe ganin yadda Dada ta ƙanƙame jiki, idanunta na kafewa kamar mai shirin mutuwa cikin muryar kuka ta ce "Na lalashe ni Danejo Dadata kada ki barni kada ki mutu do Allah,Kada kibi Baffana" sai girgizata take amma ina Dada ko motsi ba tayi.
Da sauri Hamma ya fita zuwa bakin hanya tare da samu abin hawa yana zuwa suka ɗauki Dada a mota zuwa asibiti, asibitin babu jama'a sosai. Dr Hamza na zaune a Office gabansa cike da kuɗi ya kalli Dr Iliya ya ce "Kawo maganin nan ya yi mana rawa sosai, na ƙara tura saƙo zuwa ɓangaren lafiya akan magungunan da suka bayar ya ƙare, sbd cututtukan da suke damun jama'ar rugar, ina saka ran cikin satin nan za a kawo maganin" Dr Iliya ya numfasa yana jinjina kai kafin ya ce "That's good. Amma da gaske maganin ya ƙare ne?".. "No ba wani ƙare wa da ya yi, har yanzu ban bawa ko mutum ɗaya ba" cikin fahimta Dr Iliya ya kalli Dr Hamza yana faɗin "huh! za a kawo maganin sauro kyauta ma a raba, sbd yawaitar Maleriya"

"Na samu Information ɗin hakan, amma idan an kawo gidan sauron, asibitin nan za a Ajjiye mu zamu raba, so za a bawa Kowa akan 1500 each one" waro ido waje Dr Iliya ya yi kafin ya ce "baka ganin zamu iya samun matsala, tunda kyauta gwamnati ta bayar?" Ɗaga hannu Dr Hamza ya yi yana dakatar da Dr Iliya da faɗin "Hakan shi ne ribarmu, ba za mu yi musu bauta ba kamar wasu bayi, they have to pay"
Kafin Iliya ya yi magana Hamma Yabi ya faɗo office ɗin da sauri cikin tsawa Dr Hamza ya ce "Malam ya haka zaka faɗo kamar wani mahaukaci? Me ya sa duk fulanin nan baku da ilimin zaman rayuwa ne, baku san yadda ake mu'amala ba?" Hamma baya gane zancan nasu ya ce "Don Allah ka taimaki Dadarmu, kada ta mutu cikin wannan halin ita kaɗai ta rage mana, sau wajan goma ina zuwa" "Idan munje kanta lafiya zamu bata kenan? Ko zamu hanata mutuwa? Zan maka last warning Kada na sake ganin ƙafarka cikin asibitin nan, na faɗa maka bamu da maganin ko ɗaya me kake so nayi maka? Haba kuna yi mana adalci mu likitoci sai an bimu a hankali mai ya sa zan zuciyarku ya yi yawa ne?" kasa magana Hamma yai sbd Hawayen daya cika masa idanu me ya sa su Fulani ake musu kallon mahaukata wanda basu san me suke ba? Akwai wani bambanci a jikinsu wanda ya bambanta su da sauran jama'a ne? Juyawa ya yi yana zuriyarsa babu daɗi. Danejo na ganinsa ta ce "Hamma ya naga ka daɗe, numfashi Dadata zai gudu ka taimaka, ina masu bada lafiya ɗin?" A hankali ya kama hannunta ya riƙe yana shafa kanta dake ɗauke da suma mai kyau can ƙasa ya ce "Muje gida, ba zamu ƙara zuwa asibitin nan ba, Allah ya a bamu Kuɗi mu kaita asibitin burni" shiru kawai tayi tana kallonsa tare da son fahimtar abin da yake nufi a haka suka koma gida jiki babu daɗi, kwana sukai ba su yi bacci ba, Shatu kawai ta runsta sbd ƙarancin shekarunta. A daren Danejo ta sanyawa ranta zata sai da nono iya iyawarta ta tara kuɗi masu yawa akai Dada asibiti. Hakan yasa ta tashi da asuba ta tatsi kindirmo a ƙwayar gari na fara haske ta nufi cikin burni wajan Abti America.

Mother ce ke sakkowa daga upstairs kunnanta maƙale da waya idanunta sanye cikin farin glasses ta fito a Barrister Maryam ɗinta sak. A hankali ta ce "Na riga nayi reporting case ɗin, idan ba a samu good evedance ba akan wanda suka kawo ƙarar Aliyuna, kai tsaye zan maka ko wacce ƴar banza a court dama kawai nake jira" daga cikin wayar aka ja numfashi tace "Barrister Maryam kasa aje court,idan akaje to kin bawa duniya damar zata fahimci halin da ake ciki,abi komai a sannu" ɓayayyiyar ajjiyar zuciya Mother ta sauke idanunta na sauka akan Zeefa da Fattoumah "Ok za mu yi magana bari naje wajansa Allah ya sa ya yi magana, al'amarin Sheikh na bani tsoro yana bani mamaki" ƙara tattaunawa sukai kafin sukai sallama. "sannu da sakkowa mother" idanunta akan Plasma ɗin da suke kallo ta ce "Fattoumah sau nawa zan ce bana son kuna kallon zee world ne? Ashe ban isa daku ba ko?" A sanyaye Fattoumah ta ce "We're sorry Mother ba zamu sake ba" zama tayi ta ce "Change the channel immediately Mamana" Sauya channel Fattoumah ta yi zuwa Aljazeera tana faɗin "Ok Mother" kallonsu ta yi sosai ta ce "Where's Maimoon and Auta?" Zeefa ta bata amsa da "She's inside the kitchen, Auta barci take" Mother ta ce "Bana son barcin yamma taso mini ita" tana faɗin ta miƙe tare da nufar kitchen daga bakin ƙofa ta tsaya tana kallon Maimoon dake haɗa coffee ta ce "Ina Lunch ɗin Sheikh?"... "Gashi a tray mother bari na kai masa" tsareta tayi da idanu ta ce "Bani nan" tray ɗin lunch ta bawa Mother tana ci-gaba da aikin gabanta.
Haɗaɗɗan part ɗinsa ta nufa tun daga nesa ƙirar arar Sheikh Muhammad didat ta ratsa cikin kunnuwanta da Mmkin fal fuskar Mother ganin ƙofar shiga parlournsa a buɗe. Ƙamshin air-cod ya ratsa cikin hancinta. Tana shiga idanunta ya sauka akan Umar-khan dake zaune gabansa ɗauke da system yana duba wani abu, ganin Mother ya sa Umar-khan saurin miƙewa tsaye ya ce "Sannu da zuwa Mother" "Yawwa Umar-khan ina Aliyun?" Hanyar da zata sadaka da bedroom ɗin Sheikh ya kalla yana faɗin "a Parlour na samesa lokacin da nazo, ina fara yi masa magana akan wannan case ɗin ya tashi ya shige bedroom har yanzu bai fito ba" jinjina kai tayi ta nufi bedroom ɗin, babu abin da bedroom ɗin yake sai ƙamshin turarensa ROJA wanda ya a jima da kama ɗakin duk da cewa bai fiye rayuwa a cikin gidan iyayen nasa ba, yafi rayuwa a Madina idan yana ƙasa Nigeria kuma yafi rayuwa a gidan Hakimi. ba kowa nan ma a bedroom ɗin sai tsarin ɗakin da Mother tabi da kallo wanda a kullum yake Sauya mata, komai na ɗakin fari ne tas, ɓangaren clothes, shoes, perfumes. Komai daban yake. Juyawa tayi zuwa parlourn tana faɗin "Umar-khan Aliyu baya nan fa? Ko dai ya tafi gidan Hakimi?" Umar-khan yai shiru ya ce "Bashi da ikon fita, kamar kullum ƴan jaridu na waje ta ko'ina maybe yana Library ɗinsa" sai a lokacin ta tuna da Library tana zuwa ciki ta samesa zaune akan wata ƙyakkyawar kujera wacce take juya kanta da kanta ya rufe idanunsa, sumar kansa ta ɗan bayyana sbd yanayin naɗin rawanin nasa wanda ya yi da farin hirami. Hannunsa harɗe a ƙirji. Zama tayi kujerar dake kusa dashi tana kama hannunsa ta ce "Abbana Babana" ajjiyar zuciya Sheikh Aliyu Haydar ya sauke sbd jin sunan da Mother's ta kirasa da shi amma ya kasa buɗe idanunshi domin baya son ta fahimci halin da idanunsa ke ciki wanda sune kaɗai suke fallasa raunin zuciyarsa. "Buɗe idanunka mu yi magana Babana, ba zan taɓa bari kayi gidan yari ba, zan tabbatar da kai a matsayin mai gsky ba zaka wulaƙanta ba" nan ma shiru ya yi mata bai ce komai ba kamar yadda ta tsammata. Hawayen da take maƙalewa ne ya kwance mata wanda ya zuba a tafin hannun Sheikh. Da sauri ya ƙankame hannunsu dake riƙe da nata yana buɗe idanunsa a hankali wanda suka sauya daka rinewar da sukai. Fararen idanun nasa ya ɗora akanta ganin hawaye a Fuskarta ya ƙara sashi cikin damuwa amma sam hakan bai bayyana a garesa ba. "Kayi magana Babana rashin maganarka shike sawa a dinga tunanin baka da gasky, zuciyata ba zata jure ganinka haka ba" Kallonta yake har lokacin bai ce komai ba. Ganin bashi da niyyar magana yasa Mother fashewa da kuka sosai tana miƙe tsaye da sauri ya riƙe hannunta gam! Yana miƙewa tsaye jallabiya ce jikinsa mai kyau da tsada ga laushi da tsantsi. Kai ya fara Girgiza mata yana matse hannunta sosai babu abin da Sheikh yake ƙauna sama da mahaifiyarsa sai Father daga su Hakimi sune duniyarsa. Hannunsa mother ta riƙe ta ce "Try to speak Sheikh ban damu ba nasan zan fahimce ka, zamu Court bani da wani proof da zan kareka, mene gasky?" Riƙe hannun Mother Sheikh ya yi tare da fara buga ƙafa yana ƙoƙarin buɗe bakinsa. Ganin haka yasa Mother taimaka masa wajan riƙe hannunsa tana faɗin "Ahha say something, speak Babana, say it" hannunta duk biyun ya kama ya riƙe yana runtse idanunsa sai buga ƙafa yake tuni hawaye ya fara cika idanunsa. "Yee... Ƙaƙƙƙaaa... M...mmm" kai ta ɗaga masa tana shafa kansa a fisge bayan ya buga ƙafarsa da ƙasa yana saka hannun Mother a bakinsa ya ce "Babbbban akaita ba, bbbb ba zan taɓa yin yin yin haka ba mother" yana faɗin hakan yana ƙara saka hannun Mother a bakinsa duk ya jiƙa mata hannu da yawunsa mai ƙamshi a ƙoƙarinsa na ganin ya yi magana daidai waya baiwa ta Sheikh idan koyarwa zai yana samu maganarsa ta fita yake fara karatu cikin sauri baya tsayawa sai ya gama yana gamawa baya ƙara cewa komai yake fita daga hall. Wani irin rauni ya kama zuciyar Mother tausayi da ƙaunar Sheikh ya ƙara wanzuwa a zuciyarta wacce irin larura ce haka wacce bata barin har babban mutum? Zare hannunta ya yi domin har ransa bai san lokacin daya saka hannunta a baki ba a hankali ya juya zai bar wajan da sauri mother tana goge hawaye ta ce "Aliyu" cak ya tsaya tana ƙoƙarin magana Umar-khan ya shigo wajan da sauri gaba ɗaya suka bisa da kallo Umar-khan ya ce "Sheikh na shirya mota a ƙofar baya, yanzu zamu bar gidan nan jami'ai na hanyar zuwa nan zasu kamaka" ko motsawa Sheikh bai ba shi dai ya san ba zai taɓa hana abin da Ubangiji ya tsara afkuwa ba. "Jeka Aliyu ka bisu su fitar dakai Sheikh" Mother ta faɗa tana jan hannunsu ganin haka yasa ya bita har zuwa bakin wata sabuwar mota shiga ya yi. Drivern yaja, Umar-khan shima ya shiga mota, Saif-Wazir ya shiga wata motar. Motar ƙarshe kuma Ishaq-hakim ya shiga kai tsaye suka nufi wata hanya ta daban. Sbd gujewa haɗuwa da jami'an da kuma ƴan jaridu, kasancewar duk sunyi connecting wayoyinsu dana juna yasa Umar-khan gyara bluetooth na kunansa ya ce "Saif-Wazir" Saif ya amsa da "Ina kan layi" haka Ishaq-hakim da kuma Drivern Sheikh. Cikin jin daɗi Umar-khan ya ce "Saif-Wazir idan mun isa Shatalelen gidan gwamna kabi hanyar Amado bello way" Saif-Wazir ya ce "Noted bro" Umar-khan ya ce "Ishaq-hakim kabi hanyar Asibitin nasarawa, Drivern Sheikh Kabi hanyar ƙofar nasarawa,ni kuma zanbi hanyar kasuwar tarauni, gaba ɗaya hanyoyin zasu haɗamu a titin Dawaki roud zamu sauka gidan Hakimi.." haka duk suka amince suna zuwa Shatalelen gidan gwamna ko wacce mota ta ɗauki hanyarta suka ɗauke tunanin jami'an tsaron daka hanyar da zasu bi, Sheikh na bayan mota ya zubawa ikon Allah idanu a haka suka ƙarasa Dawaki roud motocin suka haɗu waje guda kai tsaye suka ƙarasa gidan Hakimi. Sheikh na fito da ƙafarsa waje aka riƙe hannuna tare da saka masa sarƙa kamar daga sama yaji ance "You are under arrest.....

08119237616.
*🌈 IDAN BA KE 🌈*

*_Nimcyluv sarauta_*
_*E.O.W*_

9...
"You're under arrest?" Umar-khan daya fito daga cikin mota ya ƙara maimaita kalmar ɗan sandan wanda ya yi ɓadda kama cikin kayan gida. Ɗan sandan ya kalli Umar-khan fuska ba walwala ya ce "As you heard" Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Shi ne kalaman da Saif-Wazir ya faɗa domin Umar-khan kasa motsawa ya yi idanunsa a ƙasa baya taɓa jin zai iya haɗa idanu da babban mutum kamar Sheikh Aliyu Haydar cikin wannan halin. "Yallaɓai kayi mana afuwa mu shiga ciki mu tattauna, ba sai an tafi da Yaa Lee police station ba please" Wanda aka kira da Yallaɓai ɗin ya ce "Stop interfering with our work, because we know our work well, kuma wane ya faɗa maka police station zamu kai Aliyu Haydar Aliyu? State C.i.d zamu" da tsoro sosai akan fuskar Saif-Wazir ya ce "C.i.d? Wajan da ake ajjiye manyan masu aikata criminals, ƴan fashi,ƴan daba, Kidnappers Sheikh bai dace da wannan wajan ba, don Allah kada ko taɓa mana martabarsa.....," Ishaq-hakim ya katse Saif-Wazir da faɗin "har yanzu ba a tabbatar da abin da ake tunanin ya yi ba, zargi ne kawai" Wani daga cikin ma'aikatan ya ce "Say whatever you want to say,We must arrest Sheikh Aliyu Haydar Aliyu" cikin zafin zuwa Ishaq-hakim ya kalli ɗan sandan yana nu nasa da hannu ya ce "Idan ta ƙamar kai uniform ne a jikinka mu kuma mune da garin, wallahi idan ya tabbata Sheikh bashi da laifi sai munyi Shari'a da kai" yana faɗin hakan ya juya da sauri ya nufi babban gate ɗin shiga gidan Hakimi, kasancewar daman a ƙofar gidan suke. Sheikh dai na tsaye tamkar ba akan sa ake wannan muƙabalar ba, ya tsorawa hannunsa dake maƙale da ankwa ido shi kaɗai zai iya fasalta halin da zuciyarsa ke ciki sai kuma Abba Hakimi dake iya fahimtar raunin zuciyar Sheikh ɗin lokaci guda. Suna ƙoƙarin saka Sheikh cikin wata baƙar mota mai kyau wacce babu wanda zai iya ganin Sheikh ɗin a ciki gyarar muryar Abba Hakimi ta karaɗe wajan. Cikin mutuntawa da tarin ladabi duk jama'ar wajan suka sunkuyar da kansu ƙasa. A hankali Sheikh ya ɗago kansa tare da sauke ganinsa akan Abban nasa Hakimi, raunin idanun Sheikh ya bayyana sakamakon zuwan Hakimi wanda shi kaɗai ya fahimci hakan, shi kansa ya kasa yiwa Sheikh ɗin gwaggwaran kallo, idan akwai abin da Hakimi ya keso a rayuwa bai shige Sheikh Aliyu Haydar Aliyu ba, son da yake masa ko ƴar ƴan cininsa su Ishaq-hakim ba ya yi wa soyayya ce ta musamman tun Sheikh na zanin goyo.

Zame ido Abba hikima ya yi daga kan Sheikh yana mayar wa kan jami'an tsaron da suke jiran suji mai zai ce, domin su basu da wani laifi akan aikinsu suke komai, ko da basu aikata hakan ba, gwamnatin ƙasar Madina zata ɗauki mataki, matakin da zaiwa kowa ciwo da zafi a zuciya. "Zaku iya tafiya da shi" Abba Hakimi ya furta a nutse yana shafa sumar Sheikh tare da ɗaukan hiraminsa ya fara naɗa masa sabon rawani. Da sauri Ishaq-hakim ya ce "Abba ta ya ya zaka bari a tafi da Yaa Lee? Kai ne wanda nake tunanin zaka dakar dasu daha tafiya da shi?" Murmushi mai laushi Abba Hakimi ya yi yana ɓoye damuwar ransa kafin ya ce "Mulki daban, hukuma daban Ishaq-hakim a barsu suyi aikinsu muma muyi namu" Umar-khan juyawa ya yi tare da shiga mota ya kifa kansa jikin Kujera ba zai iya zuba idanu a gabansa a tafi da Sheikh ba. Saif-Wazir idanunsa ya yi jajur gaba ɗaya yanayin baya yi masa daɗi. "Aliyuna" Abba Hakimi ya kira sunan a taushashe yana kallon Abban nasa, cikin kulawa ya ce "Kayi haƙuri, ƙarya fure take bata ƴaƴa, lashakka gaskiya zatai halinta ka ɗauka kai ni kana daga cikin bayin da Ubangiji zai gwada imaninsu" ƙanƙame hannun Abba Hakimi Sheikh Aliyu Haydar Aliyu ya yi, hakan ya tabbatar wa da Abba Hakimi Sheikh ya amince da zan can nasa. Sakin hannunsa ya yi gaba ɗaya jikin jami'an tsaron ya yi sanyi bisa dole suka saka Sheikh cikin mota tare da tafiya da shi.

"Ishaq-hakim kawo mota, zuwa wajan Aliyu da Barrister Maryam" jinjina kai kawai Ishaq-hakim ɗin ya yi, tare da buɗewa Abba Hakimi bayan mota ya shiga, Saif-Wazir da Umar-khan suka bi bayan motar su Sheikh domin suji inda zan can zai tsaya.
Mother na tsaye ta kasa zama sai number ɗaya daga cikin samarin take gwadawa amma basa ɗagawa, hankalinta ya ƙara tashi fiye da ko yaushe tunanin abin da ya samu Sheikh ya wanzu a zuciyarta. Upstairs tayi da sauri kai tsaye part ɗin Father ta nufa yana zaune a ƙawataccen parlournsa mai kyau, hannunsa riƙe da jarida cikin baƙin ciki yake karanta inda aka saki zan can Sheikh tare da photonsa,gaba Al'amarin ya wanzu a duniya dama media baki ɗaya. Shigowar mother ya sanya Father Kallonta yana jiran jin abin da zata faɗa wannan karan. "Barrister Maryam lafiya ki kai mini tsaye?" Da mmki ta dubesa sosai kafin ta ce "lafiya kake tambaya? Wai me Aliyu ya yi maka da baka kula da al'amarinsa ne?" Hannu ya ɗaga mata ya ce "Saurara Barrister Maryam ni na aiki Aliyu ya aikata hakan? ko da izinina ya ke lalata yaran jama'a yana musu fyaɗe?At Aliyu's age, I will not be surprised at all that he did, ba a shaidar ɗan yau Maryam da ace yana da mata babu mai zarginsa da aikata haka" tarin mamaki da ya gama cika Mother ya sanya ta kasa cewa komai sai kallon Father kawai da take "Aliyu ɗan ka na cikinka kake wa wannan shaidar, shaidar iyaye ita ce shaidar Allah fa, banda na san kai ne mijina kai ka samar da Aliyu da babu abin da zai sanya nace ba kai ka haife shi ba, amma kaje lokaci ne zaka fahimta idan baka son sa muna son shi" kai kawai ya girgiza mata yana faɗin "Zaki iya zuwa ki nemi Mahaifinsa a waje, tunda kina tantama" kafin Mother tayi magana Fattoumah ta shigo Parlourn kallon iyayen nata tayi ganin kamar hayaniya suke, fahimtar hakan yasa Mother yin murmushi ta ce "Mamana ya akai? Ban hanaku zuwa waje ba without permission zan fara bulala fa" marairaice fuska tayi ta ce "Am sorry mother ina ta sallama tun ɗazo" kallon yadda Fattoumah ta tsare Father da ido mother tai cikin sauri ta ce "Ya akai to?" Da sauri ta ce "Abba Hakimi yana Parlour kizo ke da Father" tana faɗin hakan ta juya da sauri tana jin Father na faɗin "Fatimah.. Zarahh..!!" Amma tai banza da shi, Fattoumah irin yaran nan ne masu riƙo da kuma kishin iyayensu mata gaba ɗaya taji abin da Father yake faɗa akan Sheikh.

Fita Mother tai tana sakkowa fuskarta ɗauke da fara'a tasan tun da taga Abba Hakimi to Sheikh yana can gida cikin kwanciyar hankali. A ƙasa ta zauna tana gaida shi ya amsa a nutse kafin ya yi magana Father ya fito shi ma ya zauna saman Kujera ya ce "Sannu da hanya Abba Hakimi" kai kawai ya jinjina idanunsa akan Fattoumah yana faɗin "Matar zo nan mana ke dawa haka?" Turo baki tayi idanunta na sauyawa ta ce "Mijin me ya sa Father baya son Yaa Lee?" Sa mamaki Hakimi ya kalli Father yana faɗin "Aliyu ya akai haka? Me ya sa kake barin

2 Comments On IDAN BA KE
avatar
al-kausar

5 months ago

Reply

Dan Allah ci gaba daga page 11 naga a page 10 ya tsaya Kuma kince akwai complete anan arewa books

avatar
taskar

5 months ago

Reply

Replying to al-kausar

sai dai ki saya littafin a wurin marubuciyar ga nambarta 08119237616

Please Login or Register in order to submit comment