Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk ya gama yi ma bayani in kana son kwana anan to kaje mai gadi zai nuna maka dakin kwanan ka
Amaryata bata nan tana Turai amma ina tsammanin zata dawo nan da yan kwanaki me yiwuwa uku biyu ko fiye da hakan don haka aikin ka Shine goge goge da sauran su duk abunda ka kake bukata na aiki mai gadi zai nuna maka sauran abubuwa Kuma saina dawo ma tattauna sauri nake. Atakaice albashin ka dubu biyar ne cinka da shanka da sauran duk kananan bukatun ka suna kaina.
Ban gaskata abinda kunnena yaji ba.

******* ************ ************ ***************

Rayuwata tayi matukar sauyawa cikin kwanaki ashirin da suka shude tuni na tare agidan alhaji sabiu babu abunda ke damuna duk tsananin aikina bai wuce karfe goma sha daya idan na gama aikina bana fita ko ina saina zauna a dakina nayi ta karance karancen littattafan addini dana turanci dana hausa wasu lokuta idan nagaji da zama saina fito na taya maigadi hira mutumin kirki ne daga baya na lakanci sunansa ABBATI babu abunda ke damuna ayanzu hankalina ya kwanta.

ARANA WATA LARABA wadda tayi daidai da kwanakina ashirin da biyar agidan sai abubuwa suka fara sauya salo kadan-kadan sai farin cikin nawa yafara rikicewa yana sauya launi kamar yadda kalanzir ke sauya launin ruwa..

Karfe goma sha biyu na dare maigadi Abbati ya shigo dakina nayi firgigit na tashi yayin da yafara barazanar karya min kafada da duka.
Lafiya? Na tambaye shi.
Alhaji ne ke son ganin ka yanzun nan.
Na dube shi cikin mamaki sannan na mike tsaye na bishi abaya na nufi dakin Alhaji sabiu tabbas ina tsammanin ba lafiya ba domin ko da rana bai taba kirana dakinsa ba ballantana karfe goma sha biyu na dare..

Yana zaune akan kujera yana makyarkyata fuskarsa sharkaf da gumi alamun razana karara suke afuskarsa kaikace ido biyu yayi da ALJAN.

Fa....... Farisu. Jikinsa na rawa ya kira sunana na matsa kusa dashi a rude.
Lafiya Alhaji? Na tambaya
Farar takarda ce nannadaddiya ko dayake akwai alamun da suke nuni da cewa an bude ta.
Farr..... Bai iya karasa fadin sunana ba sai takardar ta subuce ta fado kan tattausan koren kilishin dake malale tsakiyar dakin sai bayan da kyawawan siraran kalmomin da aka rubuta suka yiwa idanuna tozali sannan kyawun takardar yafara komawa baki baki mummuna a saman takardar cikin manyan haruffa an rubuta.
MUTUWAR KA TAFI RAYUWAR KA AMFANI.......

******** ********** ********** ******************

KASHI NA UKU 3
Cikin Firgici na dago kaina na dube shi tuni.......MUTUWAR KASKO-07

Sai bayan da kyawawan siraran kalmomin da aka rubuta suka yiwa idanuna tozali sannan kyawun takardar yafara komawa baki baki mummuna a saman takardar cikin manyan haruffa an rubuta.
MUTUWAR KA TAFI RAYUWAR KA AMFANI.......

******** ********** ********** ******************

KASHI NA UKU 3
Cikin Firgici na dago kaina na dube shi tuni jikina ya jike sharkaf da gumi tun kafin ma na karanta abinda ke cikin takardar.

Kar... Karanta Farisu abinda yasa kenan na kirawo ka ya lumshe idanunsa sannan yasake langwabewa akan tattausan kujerar tuni yafara fargabar anya kuwa ba sumewa zaiyi ba.
Nafara karanta abunda ke cikin takardar jikina na rawa kamar ana girgiza ni.

MUTUWAR KA TAFI RAYUWAR KA ALBARKA.
Wannan sako ne daga mu zuwa kai alhaji sabiu suhununu abunda sakon ke isarwa shine gargadi da ilmantar dakai ga barin duk abunda ka iya kawo karshen numfashinka a doron kasa muna so daga yau din nan kasa ido domin Zakayi bakin shaidanu meyiwuwa yau zamu zo da daddare ko gobe ko jibi ko sati ko bayan wata daya ko wata biyu wata uku ko shekara ko bayan karni guda duk muna iya zuwa cikin wannan lokutan da muka lissafa abaya kasani Alhaji sabiu kudin ka da mukamin ka dakuma duk abunda kake tunanin garkuwa ne agareka toh tabbas bazasu kare ka daga sharrin shaidanu bakinka ba kada ka sake tunanin sanar da hukumar yan sanda ya darsu a zuciyar ka domin yin hakan kuskure ne babba bance bazasu iya kare ka ba nasan suna iya gadin ka har tsawon rayuwar ka amma bazasu iya gadin amaryarka dake shakatawa a kasashen Turai ba.
Zaman da kake ayanzu babu wani motsi da Zakayi bamu sani ba akwai yaranmu mun bazasu suna kula dakai amma kada ka bata lokacin ka da waige waige ko dube dube domin bazaka taba ganin su ba idan kuwa har ka sanar da hukumar yan sanda to kamar ka ratayawa amaryar ka sarkar mutuwa ne a dogon kyakkyawar wuyan nan nata ina fada ma kamannin nata ne domin ka hankalta kasan kuma na santa sannan kyawunta bai hanamu raba dogon wuyan nata da gangar jikinta in har ka saba umarnin mu kada ka manta mun san maigadin ka daya ne karo wani maigadin na nufin ka saba umarnin ne toh ka sani muna da yawan gaske tuni mun daina zuwa mu yan kadan da yawa muke zuwa da shirin yaki kaga idan ka karo masu gadi to tabbas kamar ka karo yawan gawawaki ne sai ka ganmu ina fatan zaka shirya mana yar ƙwarya ƙwaryar liyafar Girmamawa a matsayin mu na masu
GUZURIN MUTUWA .

************ *********** ************ ***********

Hanjin cikina ya murda guri guda sannan cikina yayi wani irin kugi kamar ana ruguntsumin bikin sallah acikina. Tunda nake bantaba ganin mummunar wasika irin wannan ba.
Nayi shiru ina duban fuskar sa wacce ke kyalli kamar waina idanuwansa a lumshe hannayen sa a nade akan cikinsa idan baka duba cikinsa sosai ba saika rantse da Allah baya numfashi na tashi a hankali a rude na nannade takardar na cusa ta a aljihuna sannan na matsa kusa dashi.

Alhaji na kira sunansa bai ko motsa ba ballantana ma ya amsa min suturar dake jikinsa sun Manne da fatar jikinsa saboda gumin dake tsiyaya kamar ruwa na matsa kusa dashi ahankali sannan na dafa kirjinsa zuciyarsa na bugawa da sauri sauri na juya cikin sauri na nufi kofar dakin amma sai wani tunani ya tsayar daji cak. Shin ya dace na sanar da maigadi kuwa ? Bana tsammanin idan alhaji yadawo hankalinsa zai so hakan nayi niyyar na sanar da maigadin halin da ake ciki
Badon komai ba sai don ya tallafa min mu kai alhaji kan gadon barcin sa amma tunanin danayi shiya sauya min shawara.
Na ciccibe shi ahankali sannan na dora shi akan gadonsa bashida wani nauyi kasancewar sa dan siriri ban ko yi haki ba gurin daukarsa. bayan na kwantar dashi rigingine saina koma kan daya daga cikin kujerun na zauna nafara tunani.
Sun ce suna iya zuwa yau.. Indai har haka ne toh babu inda zan motsa ina nan har saina ga abunda hali yayi domin barin Alhaji shi kadai yana da hatsari Allah yasa kada su zo yau. naci gaba da addu'a cikin zuciyata sannan ne to wani mummunan tunani ya darsu azuciyata.
Yanzu idan suka kashe.........MUTUWAR KASKO-08

Sun ce suna iya zuwa yau.. Indai har haka ne toh babu inda zan motsa ina nan har saina ga abunda hali yayi domin barin Alhaji shi kadai yana da hatsari Allah yasa kada su zo yau. naci gaba da addu'a cikin zuciyata sannan ne to wani mummunan tunani ya darsu azuciyata.
Yanzu idan suka kashe shi ina kuma rayuwata zata dosa? Na tambayi kaina barcin dake idanuna ya zama tarihi kwata kwata ma sainaji na tsani barci tunanin dake zuciyata ya isa ya aje ni a farke daga nan har zuwa kwanaki uku masu zuwa amma duk hakan kafin nafara tunanin SALMA ne.

Na juya ahankali na dubi fuskarsa yana kwance akan gadon yana barci numfashinsa yadawo daidai misali. Haka ma bugun zuciyarsa tunanin ta ya sake fado min abunda yazamo min masifa aduk lokacin da zanyi shiru ni kadai sai tunanin ta ya mamaye zuciyata ta dulmiya cikin tekun tunanin ta da haka har barci ya dauke ni akan kujerar acikin barcina nayi mafarki waiga Salma nan tsaye akaina tana dubana sannan tana tambayata wai ba zan fada mata sunan nawa ba? Sannan kamar daga sama sai wani mutum ya bayyana sannan ya kama hannun Salma yace da ita. A ina kika san shi? Fuskar mutumin a lullube take ban gane ko wanene ba amma loakcin daya kama hannunta sai wata iska mai karfin gaske tazo ta yaye lullubin ko shakka babu
ALHAJI SABI'U SUHUNUNU ne.

********* ******** ******** ******** ************

Motsinsa ne ya tashe ni da asuba yana zaune abakin gadon casbaha a hannunsa na dama.
Sannu Farisu nagode kaji yace dani tausayinsa ya kamani domin da har na fara fargabar zaiyi min fadan kwana masa adaki danayi abin kuma da yafi bani haushi shine farkawar dayayi ya sameni ina ta sharar barci hakika tunanina zai hauni da banbamin fada amma maimakon hakan sai yayi min murmushi yace.
Kaje kayi sallah saika dawo inason magana dakai na dube shi ta gefen idanuna babu wasu kwakkwarar alamun damuwa a tattare dashi saidai idan ka dubi idanunsa da kyau zaka tabbatar da yana cikin tunani mai zurfi.
Na nufi kofar dakin ahankali na janyo ta kenan sai yayi kiran sunana..
KAFADAWA MAI GADI NE ABUNDA AKE CIKI?
Ya tambaye ni
Ban fada masa ba.
Dakyau Farisu yi sauri ka dawo ina jiranka.
Nayi ajiyar zuciya na canki daidai Daman saida nayi tunanin alhaji bazai so na fadawa mai gadin ba.
Na ratsa ta cikin farfajiyar gidan zuciyata cike da tunanin abubuwan da suka faru a daren jiya garin yafara haske farfajiyar gidan bakajin komai sai kukan tsuntsayen dake cikin shuke shuken gidan wasu lokuta idan ka nutsu ka saurara kana iya jiyo carar Zakaru agidajen makwabtan dake can nesa da gidan na nufi rumfar mai gadi kafin na karasa gurinsa ya Mike tsaye sannan ya washe min jerin dogayen hakoransa kai kace alkaluma ne aka jera..

Barka da asuba nace dashi ina duban hakoransa nayi mamakin irin yadda yake amfani da hakoran wajen tauna kashi. Bayan mun gama gaisawa saiya dauko min buta nayi alwala saboda makarar danayi ban samu jam'i ba sai nayi tawa ni kadai shi kuwa yana gefe yana jan carbi bayan na idar saina Mike da sauri da niyyar nakoma gurin alhaji domin nasan yana nan yana jirana.
Inafatan dai lafiya dai ko Farisu?
Lafiya Ƙalau nace dashi muryarta a shashshake na dube shi sannan batareda na sake kara dubansa ba saina nufi cikin gidan da sauri alamun dake fuskar maigadin su suka tabbatar min da cewa karyar danayi bata samu shiga ba tabbas yasan karya nake Nima kuma nasan karya nake saidai kawai babu yadda zaiyi dani ne. Na sake juyawa na hango maigadin har yanzu yana kallona carbinsa ahannunsa na dama saidai wannan karon ba jan carbin yakeyi ba ni yake kallo yana yake hakora a tunaninsa wai murmushi yake kai wannan akwai shashasha nace cikin zuciyata.

********** ******** ******** *********** ********

Tun sa'ar dana karanta wasikar babu wanda ya fado min Arai sai kai. yayi shiru yana dubana a nutse sannan yaci gaba da cewa abinda yasa kuwa na nemi shawarar ka Shine acikin wasikar barayin basu ambace ka ba sun ce dai inada mai gadi guda daya sannan suka gargade ni da kada na karo koda guda guda daya yin hakan sunce karin gawawwaki ne yayi shiru yana dubana ido da ido.
Ina tausayin ka Farisu domin banason wani abu yafaru a kanka kai maraya ne mai karamin karfi Idan har Nabari wani abu ya faru dakai toh naci amanar ka na cuci mahaifiyar ka da kannen ka don haka abunda nake gani tunda sunce mai gadi daya suka sanni dashi toh abinda yafi shine ka tattara kayanka kabar gidan nan tun kafin abinda ba'a so yafaru ni kam na dogara da Allah shi ya sani Awannan kangi kuma shi zai fitar dani......
Babu inda zani Alhaji. Na tari numfashinsa
Duk abinda zai faru yafaru tare dani sannan na dada dacewa.. Shekaru kusan biyu da suka wuce na shiga abinda yafi wannan amma Allah yay fitar dani.

Uhm Farisu kar.....
Nace maka babu komai ina tare dakai daga yau ma bazan sake nisa dakai ba in har bazaka damu ba.
Kusan.........MUTUWAR KASKO-09

Uhm Farisu kar.....
Nace maka babu komai ina tare dakai daga yau ma bazan sake nisa dakai ba in har bazaka damu ba.

Kusan mintuna biyar bai sake cewa uffan ba sannan ne toh ya dago kai yace dani nagode Farisu bansan abunda zan saka maka dashi ba sannan ya dada da cewa toh yanzu ina shawara?

Nayi shiru na dan lokaci sannan nace dashi bakajin yadace muyi dabara yan sandan su shigo gidan nan cikin dare da fararen kaya saika basu gurin buya suyi ta kwana anan har zuwa ranar da Allah zai kawo su kaga sai su cafke su.
Farisu babu abunda nake kauna aduniyar nan fiyeda matata dukiya ta da duk wani abu dana mallaka kai raina ma ina iya bayarwa domin na ceci rayuwar matata.
Tausayinsa ya kamani lokacin danaga yasa gefen rigarsa ya share hawaye
Kaji fa abunda sukace idan na sanar da hukuma kamar na ratayawa matata sarkar mutuwa ne a dogon wuyanta bazan iya daukar hadarin nan ba Farisu abinda kawai yafi shine zanyi ta jiran su idan sun zo duk abunda suke so zan basu indai bazasu taba min matata ba Wallahi farisu ina kaunar ta fiyeda ni kaina.
Nayi shiru ina tunani gameda yiwa kaina tambayoyi shin me yasa ta tafi kasashen Turai yawon shakatawa batareda mijinta ba? Sannan kuma wacece wannan wane irin matsayi da cikar halitta wannan mata take dashi da har zata sace zuciyar wannan bawan Allah ya sadaukar da komai nasa har ransa saboda ita?
Tambayata babu amsa kadan ya rage na tambaye shi sunan matar tasa amma sai nayi shiru
Me zai hana ka tambayi mai gadi wata zuciyar ta tace dani adaidai lokacin ne jiniyar agogon dakin ta dauki kara karfe shida da rabi na safe sannan kamar jira ake jiniyar agogon ta tsagaita sai talfon din dakin ta dauki ruri Alhaji ya kalle ni Nima na kalle shi sannan saiya nufi wajen talfon din ya dauki kan.
Assalamu Alaikum wake magana?
Kamanninsa suka sauya lokaci guda sannan fuskarsa ta yamutse kai kace kunama ya hadiya na tashi da sauri adaidai loakcin da kan talfon din ke kokarin kwacewa daga hannunsa abinda Naji acikin talfon din saida yakusa sani in jefar da kan talfon din na ruga da gudu Wata kakkausar murya ce ke cewa
Sabon Ma'aikacin daka dauka bazai kare ka da komai ba idan muka zo sai mun karairaya shi a gabanka kafin mu binne shi da ransa....

BABI NA HUDU
ADACAN NA SHIGA ABUNDA YAFI WANNAN NAFITA. abunda danace da alhaji kenan dazun to amma ayanzu nafara shakkar hakan anya kuwa abunda nake shirin shiga ciki ayanzu ba zaifi wanda na shiga abaya ba?
Duk wannan tunanin nayi shine alokacin dana nufi rumfar maigadi jikina na rawa kamar mazari komai na kalla agidan uku uku nake ganinsa wasu lokutan ma har karo nake ci da fulawowin dake gefen yar siririyar hanyar.
Adaki na bar alhaji kwance akan gado babu yadda yake yace dani zazzabi yake ji kuma kansa na ciwo bayan yayi min nuni da ma'ajiyar magungunansa na bashi yasha na shawarce shi da akirawo likita amma saiya ki yace idan muka kirawo likita masu gargadin acikin wasika na iya tsammanin ko dabara yake shirin yi domin haka saiya ce babu komai Nabar likitan domin a cewar sa kiran likitan wai kamar wasa da ran matarsa ne.

Maigadin na zaune akan kujerar katako yana gyangyadi na same shi har Sa'adda na karasa kusa da shi bai daina gyangyadin ba na jijjiga kafadarsa da karfi yayi firgigit kadan ya rage ya tuntsire daga kan kujera nayi sauri na rike bayan kujerar.
Bi ahankali ba karshen duniya bane yazo ya dubeni yana mutsutstsuke idanu sannan ga mamakinsa sai yayi murmushi dogayen kasusuwan dake bakinsa suka washe.
Barka da zuwa Farisu yace dani yana murmushi zauna mana na nemi guri na zauna bayan yan dakiku sai tsurkun mai gadi ya rinjayi tawa ya dubeni yace Farisu lafiya kuwa alhaji yake naga haryanzu bai fita gurin aiki ba gashi ko kyeyarsa ma ban hango ba kuma kaima duk ganin ka nake wani ajuye baibai duk a birkice kamar ciyawar yara kokuwa......
YA isa haka na katse shi kai tsiyata dakai surutu kamar gada kayi maigadin yayi min murmushi sannan yace.
Lallai Farisu kaci abinci to in kana nufin agurin mahaifina na gada toh shi kurma ne ma bashida baki ma ballantana nagaji surutu agurinsa
Toh in kuwa bahaka bane to da wahala in batareda da cakwaikwaiya aka haife ku ba na fashe da dariyar yake domin banyi niyyar dariyar ba amma don kada maigadin ya harzuka saina fashe da dariya shikuma shashashan saiya miko min hannu muka tafa sannan nayi maganin tsurkun sa nace dashi kansa ke ciwo shiyasa bai fita ba amma ina tsammanin nan da yan sa'o'i zai fita

Sannan kafin maigadin yajefo wata tambayar sai nayi sauri nace dashi kasan sunan amaryar alhaji ne naji yana yawan yi min zancen ta wai tana Turai amma yanzu ni bai taba fada min sunanta ba
Maigadin ya dubeni yana zazzare idanu sannan ya yake hakoransa yace dani inama ace kasani Nima kafada min na dube shi a fusace.
Maigadin ya laluba aljihunsa ya dauko wani...

KUDINGA MIN UZURI
IDAN KUNJI SHIRU BANYI POSTING BA

AKWAI TARIN UZURURRUKA DA SUKA SHA KAINA AMMA DUK DA HAKAN NAKE YAKICEWA NAYI DON DAI SAUKE AIKIN DANA DORAWA KAINA.MUTUWAR KASKO-10

Sannan kafin maigadin yajefo wata tambayar sai nayi sauri nace dashi kasan sunan amaryar alhaji ne naji yana yawan yi min zancen ta wai tana Turai amma yanzu ni bai taba fada min sunanta ba
Maigadin ya dubeni yana zazzare idanu sannan ya yake hakoransa yace dani inama ace kasani Nima kafada min na dube shi a fusace.
Maigadin ya laluba aljihunsa ya dauko wani gutsuren goro ya balla sannan ya jefa a baki sannan yayi yan waige waige kamar wanda ke tsammanin wani ya labe yana sauraron sa bayan ya tabbatar da abunda yake son tabbatarwa sai yace min cikin Rada.
Zakayi mamaki Farisu idan nace dakai ko ganinta bantaba yi ba domin Nima ban dade da fara aiki agidan ba tsakanina dakai duka baifi sati zuwa kwana goma ba
Kana nufin kace kaima baka same ta agidan ba?
Kwanan ta daya da tafiya nafara gadi agidan nan ko inuwar ta ban taba hange ba ballantana na ganta.
Nayi shiru ina jujjuya maganganun maigadin cikin zuciyata ina mamakin abinda ya hana su tafi tare da alhaji abin ko kusa bai dace ba mutun kamar alhaji yayi sabon aure sannan yabar matar ita kadai ta tafi Kasar Turai anya kuwa haka zata yiwu a dafa kaza a jefar? Hakika akwai wani abu a boye wanda ban yarda ba bansan abunda yasa ba amma tun sa'adda alhaji yafara yi min bayanin matarsa sainaji zuciyata ta bukatu da son ganinta bansan menene dalili ba amma hakan kawai nake son ganinta na dago kaina ahankali saina lura ashe maigadin ni yake kallo tunanin danake shi ya hanani na lura da hakan tun farko.
Lafiya Farisu? Kake irin wannan zuzzurfan tunani yaronka dakai?
Lafiya Ƙalau nace dashi
To ne yasa kake son kasan sunan matar alhaji?
Nadube shi sannan na mike tsaye nace dashi abunda yasa kake son kasan sunanta ko ka ganta Nima shi ya sani.
Maigadin ya fashe da dariyar da tayi sanadiyar tashin wasu tattabaru dake hutawa a kan rumfar kwanon sa.
Angaida Farisu. To menene yasani nake son sanin sunanta? Ai saika fada min. Yace yana dariya
Ai kafini sani nace dashi
Wani abune daya wuce TSURKU.?
Sannan nayi masa tambayar danake tsammanin in har ban dace ba toh saidai na hadiye tsurkuna har sai matar alhaji ta dawo na ganta da idanuna.
Amma nasan dai ai ka taba ganinta a hoto ko?
Maigadin yayi shiru sannan yace lallai kafini tsurku to in abinda kake son kaji kenan to na taba ganinta sau daya shima ranar da nazo muka je dakinta dani da alhaji yace na share shi kafin asami mai aiki wato kai kenan hoton kato ne suka dauka ita da alhaji yana nan makale ajikin bango saidai bana tsammanin zaka samu damar shiga dakin in kuwa har ka sami damar shiga dakin to ka bani labarin kammmanin uwargidan tamu idan ka dawo domin ni ganin tsoro nayi mata ya fashe da dariya hakoransa na barazanar raba harshen sa biyu.

******* ******** ******** ******** **************

Sha biyu saura na nufi dakin alhaji tun kafin na karasa dakin na hango mai girke girken abincin gidan ta fito daga cikin dakin. tsohuwa ce yar Kusan shekaru sittin saidai tsufanta bai hana ta yin teba kamar giwa ba tana sanye da zanin riga da atamfa launin kasa masu zanen ganye na dubeta sannan nayi mamakin irin kibar data shirga a zamanin kuruciyarta sunan matar TABAWA na juya da baya da niyyar nakoma dakin na jira har sai alhaji yagama cin abincin sannan na koma.
Farisu... Tabawa ce ke kirana alhaji yana son ganin ka tace dani adaidai lokacin data nufo inda nake na ratse gefe guda domin ta samu hanyar wucewa batareda munyi karo da ita ta karairayani ba.
Toh nace da ita... Ina kwana.?
Lafiya lau Farisu tace dani tana kukkumbura kumatu kamar mai busar algaita.
Shigo alhaji yace dani lokacin danayi sallama yana kwance akan gado ya taso kai da matashi mujallar taurarin wasan kwaikwayo wato TAURARUWA ahannunsa tun kafin nagama shiga dakin yace dani ka iya mota Farisu? Na dube shi cikin mamaki sannan alokaci guda na dubi abincin da tabawa ta jera masa akan teburi bai ko bude lillibin dake kan farantin ba ballantana yaci.
Na iya nace dashi amma banida lasisin tuki ya gyada kansa cikin gamsuwa yace bakomai in dai ka iya motar Shikenan gobe in Allah ya kaimu misalin karfe goma sha daya zaka rakani filin saukar jirgin sama zan taro amarya ta yanzun nan ta bugo min waya tace tana nan tafe gobe.
Yayi murmushi hakika yanzu nasan yana masifar sonta dubi duk irin barazanar dayake ciki amma jin cewar amaryar sa zata dawo gobe duk saiya washe in banda yar fadawa dayayi saika rantse da Allah babu abunda ke faruwa.
Mukayi shiru na dan lokaci babu wanda ya sake cewa kala sai bayan yan mintuna nace dashi alhaji bakajin dawowarta na tattare da hadari? Ina ganin abinda ya dace ka buga mata waya tayi zamanta acan har sai mun ga abunda hali yayi kokuwa me kake gani?
Farisu wadannan mutane miyagu ne sunce duk ab...bin da nake suna lura kaga yanzu idan nace ma kada tazo yanzu toh zata yi ta zama ne acan bazan iya jure zamanta acan ba Farisu tuni na zaku ta dawo in banda ma ta nace akan cewa ita kadai zata tafi ba da wallahi tare zamu tafi to amma danaga ranta ya baci saina kyaleta domin babu abinda naki jini irin naga ranta ya baci.
Gara ta dawo gida Farisu in yaso suzo su same mu tare ko rayuwata ce saina bayar in dai har zasu rabu da ita Daman abunda nake tsoro shine kada su kashe min ita batareda na sani ba amma indai tana kusa dani nasan babu abunda zai faru da ita dukiya wani abu ko menene koda raina ne saina bayar domin na fanshi ran masoyiyata matata.
Yayi shiru yana duban bangon dakin kamar wanda ke kallon bakin allon boko yayin darasi a makaranta kaidai Allah yakawota goben Daman abunda nake niyyar yi na buga mata waya ta dawo gida kusa dani to sai Allah ma ya taimake ni tun kafin na buga mata mata wayar saita bugo.
Farisu abunda nake son ka gane shine duk rudewar danayi jiya bata tsoran rabani da dukiya ta bane ko raina abinda ya rikita ni shine matata da suka sako acikin al'amarin amma tunda yanzu ta dawo kusa dani to banga wanda ya isa ya taba min ita ba yayi shiru yana huci kamar kumurcin maciji idonsa ya kada yayi ja.
Yanzu yafi kama da maciji ba kamar jiya da da ya zama mai zuciyar mata ba canjin dana gani a halayyar sa saiya bani mamaki fiyeda abunda yake fadi ya Mike ahankali ya nufi wata loka dake kusa da gadonsa ya budeta a tsammanina kwayoyin magani zai dauko kamar budar ido sainaga ya daukota ya juya ta a hannunsa sannan ya dube ni yace
Farisu nasan kasan wannan abar ko? Zaka iya kiranta KIBIYAR AJALI kokuma kace da ita BINDIGA.
Yawun bakina ya kafe Gumi yafara tsatstsafo min.
Ka taba rike bindiga Farisu? Na girgiza kai...
UNGO rike kaji irinta yace dani yana murmushi don ganin nagama tsorata Uhm Uhm cikin sauri muryata na rawa tuni har nafara ja da baya.
Abinda yasa na dauko ta Farisu...
Yaci gaba da cewa
Saboda ka sani Kuma ka zama shaida in har Allah yakawo min matata gobe na ganta zaune kusa dani to na daina fargabar ko wanene

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

1 Comments On MUTUWAR KASKO
avatar
mahamane-noura

1 year ago

Reply

Oui

Please Login or Register in order to submit comment