Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tabbas abin akwai hadin baki in kuwa hakane menene ke tsakaninsa da Salma?
Ban sami amsar tambayata ba sai daga karshen labarin nan danake baku.

Sauran yan sandan suka tusa ƙeyar yan fashin suka fice. Mai dogon gemun nan shine karshen fita daga dakin yan sanda uku abayansa lokacin da ya zo fita sai yayi min murmushi sannan yace.
KAYI HANKALI ACI BULUS BATA DA KIRKI IDAN KAYI WASA ITACE SANADIYYAR KARSHEN RAYUWAR KA.
Sannan ya dubi Salma yace kiyi ahankali yar kyakkyawa ba kullum ake kwana a gado ba.

Yan sandan suka hankada shi cikin duhun daren.
Suka rufo kofar ahankali idan har ba idanuwana suke nuna min karya ba naso naga daya daga cikin yan sandan ya sarawa Salma Sa'adda yazo fita daga dakin.

Kusan mintuna biyu babu wanda yace da wani kala har saida muka ji karar tashin motar yan sandan sannan na juyo ahankali na dubi Salma.
Ga mamakina sai naga ta fashe da kuka na tashi jikina na rawa na matsa kusa da ita.

Salma menene kuma?

Bata daina kukan ba sai ta ci gaba kamar ranta zai fita.

Don Allah Salma kidaina kuka wai me yafaru ne?

Tayi ajiyar zuciya gamida sheshshekar kuka
Fa.. Farisu Wal... Wallahi banida lafiya

Na dube ta sororo duba irin na tababbu.
Me kike nufi?

Nace da kai banida La...Lafiya ku...ma ina ganin bazan taba warkewa ba.

Ta sake fashewa da kuka koda na dube ta sainaga duk fuskarta ta sauya kyawun ta da annurinta sun gushe lokaci guda shekaru sun karu akan shekarunta na gaskiya.

Anya kuwa da haka Salma take tun asali zanji ina kaunar ta kuwa?

Haryanzu bata daina kuka ba jikinta na bari kamar mai hawa bori adaidai lokacin ne to wani abu ya subuce daga kan cinyar ta yafadi akan kafata na dauke shi na duba katin asibiti ne ajikinsa an rubuta Alhaji Sabiu Suhununu ba sunan ne yasa yawun bakina kafewa ba kalmar dake kasan katin ita tafi komai tashin hankali akasan katin tsakanin wasu bakaken layuka guda biyu an rubuta ɓalo ɓalo.
AIDS POSITIVE.....

KASHI NA GOMA SHA DAYAMUTUWAR KASKO-27

KASHI NA GOMA SHA DAYA

Sassanyar iskar safiyar mai dauke da, damshi-damshin ruwa yafara bugun fuskata adaidai lokacin da Salma ta lankwasa kan motar muka bi dogon titin da zai kaimu har zuwa asibitin.

A ina kika sami katin? Na tambaye ta

Acikin wata akwatinsa ce dayake ajiye kayansa na sirri lokacin da aka kashe shi na dauka akwai wani abu mai daraja aciki shine nayi kokarin na boye ta kafin yan sanda su zo sai bayan da aka kammala binciken mutuwarsa ne na tabbata nagama mallake dukiyar sannan na bude ta babu komai acikinta Farisu sai fasfot-fasfot din tafiye tafiyensa na kasashen ketare a kasan akwatin ne naga katin ban...san yadda zanyi ba Farisu domin katin kamar katin mutuwa ta ne tabbas fasfot dina ne na zuwa kiyama domin nasan cutar na nan jikina tunda mijina ne.

Ba dole bane.
Nace da ita ina kokarin kwantar mata da hankali.
Me yiwuwa ke bakida ita.
Ni kaina ban gaskata abunda na fada ba.

Hawaye yafara kwaranya kan fuskata.
Kada ka zolaye ni Farisu kaima kasan wannan cuta na nan ajikina sannan kuma tabbas tana nan jikin Tajuddeen.

Tsigar jikina ta tashi ne kike nufi da tana jikin Tajuddeen?
Ka... Kayafe min Farisu tafara kuka

Direban motar dake bin bayan tamu motar ya danna Hon da karfi adaidai lokacin da kan motar ya dan subuce daga hannun Salma ta raba masa hanya.

Direban ya wuce mu cikin fushi yana zage zage.
Kiyi ahankali Salma nace da ita cikin kaduwa

Nasan kana kaunata Farisu babu wani mutum daya taba nuna min kauna kamar ka ina rokon ka don Allah kada ranka ya baci inason duk abunda zan fada maka ka dauke shi amatsayin kaddara.

Fadi Salma babu komai na samu kaina ina fadin hakan.

Tajuddeen dansandan nan Masoyina ne Farisu ma'ana masoyi amma na shiririta shine dalilin dayasa kaga yana taimaka min cikin dukkan al'amurana nasan cewa yan fashin da suka kama dazu suna iya bada shaidar cewa ni na dauke su haya su kashe mijina saidai kuma Tajuddeen bazai barsu ba koda sun bada shaidar ma abanza Tajuddeen ruguza ta zaiyi domin shima yana jiran na bashi nasa kason daga cikin dukiyar dana mallaka ta Alhaji Sabiu Suhununu.

Kina nufin da hadin bakinsa aciki?
Ai ya ma wuce hadin bakinsa shine ma ya shirya min yadda za'ayi tun farko.

Kwadayi shi ya kaini ga haka saidai kuma duk abunda akayi ma abanza tunda gashi yanzu dani da Tajuddeen din bana jin munada sauran wasu kwanaki masu tsayi a doron kasa.
Ta doki sitiyarin motar da hannunta cikin takaici
Idan har ta tabbata gaskiya inada cutar AIDS ajikina to Tajuddeen bai samun ko allura daga cikin abunda.... Ta sake fashewa da kuka DAKYAR take tukin motar.

Karfe bakwai da rabi saura yan mintuna muka isa asibitin. Likitan data bugawa waya a daren jiya yana farfajiyar asibitin yana jiran mu tun kafin tagama shiga da motar filin ajiye motocin asibitin Likitan yakaraso kusa da motar.

Kafin salma tagama bude motar saida nayi mata gargadin karshe.

Kinga Salma nida zaki dauki shawarata da saiki hakura da gwajin Aids din nan kada kije su gano miki abunda zai tayar miki da hankali me yiwuwa...
Nace dakai ka daina zolaya ta wacce irin kwanciyar hankali kake zance bayan mijina yanada cutar?

Kafin na farga ta fice daga motar ta sami Likitan na sauko jikina a sanyaye Nabi bayanta mintuna biyu dayin hakan sai gamu a ofishin Likitan nuna fuskantarsa.

********* ******** ******* ******** *************

Kiyi Hakuri ranki ya dade wato.....

KU BIYO NI.MUTUWAR KASKO-28

****** ****** ******* ************** ***********

Kiyi hakuri ranki ya dade idan an dauki jinin ki dawowa nan zakiyi ki zauna ki barsu su gama aikin su sai su kawo miki sakamakon doka ce ba'a barin wanda ake yiwa gwajin ya tsaya a dakin gwajin.

Likitan ne ke ta fama da Salma ita ta dage wai akan idanunta za'a yi komai.

Kaga likita jinin nan da za'a gwada na wane bana kowa ba ina ganin gaskiya ni bazan iya zaman jiran sa ba gara ayi komai akan idona.
Bayan jayayya ta kusan mintuna goma Salma ta rinjayi Likitan abinka da mai karfin takardun nasara.

Dakin farkon da muka shiga an rubuta (collection room) a saman kofar dakin wanda zai yi gwajin jinin ya karbi form din da Likita ya baiwa Salma ta cike sannan ya sanya safa ja Yakuma umarci Salma data bashi hannunta ya dubeni a tsorace sannan ta mika hannunta yasa roba fara ya daure saman hannun sannan ya dauko wata audugu wacce ke jike da wani ruwan sanadari ya goge gurin dayake son ya soka da allurar sannan ahankali cikin gwaninta saiya soka allurar jikin Salma ya zuko jini tsigar jikina ta tashi Naji kamar jikina ya soka.

Salma ta lumshe idanunta ta damtse fatar bakinta adaidai lokacin da likitan ya danne inda ya soka da allurar da auduga sannan ya zare.
Mintuna biyu da faruwar hakan muka isa dakin gwaje-gwajen jinin (Lab) likitan dauke da sirinjin daya dauki jinin Salma akan faranti fari ya wuce kai tsaye kuryar dakin ya bude cikin wani katon firji ya dauko wata yar doguwar kwalba wacce ya kirata da sunan (Test Tube) sannan ya dauko wata kwalba mai kama da ta maganin ciwon ido gami da wata roba doguwa mai kama da Rula wacce ke dauke da rami a tsakiyar ta.

Likitan ya tsiyaya jinin cikin test tube sannan ya sanya shi cikin wani irin inji na nasara wanda ke dauke da gurbi gurbi kamar gidan dara kusan guraben Test Tube takwas ne a jikinsa saidai kuma dayake safiya ce ba'a dauki jinin jama'a ba kwalbar da aka dauki jinin Salma ita kadai aka saka acikin injin sannan sai injin yafara wanawa kamar fanka da kwalbar acikin daya daga ramuka takwas din dake jikinsa
Bayan kusan minti biyar injin ya daina wanawa a sakamakon kashe shi din da likitan yayi.

DAKYAR muke numfashi fuskar Salma duk ta sauya launi saboda fargaba bata san irin sakamakon da gwajin zai bayar ba.
Lokacin da likitan ya dauko kwalbar Test Tube din daga cikin injin sainaga kamar an tace jinin.
Jajayen dago-dagon jinin sun taru a kasan kwalban yayinda tataccen ruwan jinin ya tsaya a saman kwalbar launin sa rawaya rawaya likitan ya dauko yar robar nan mai kama data maganin ciwon ido ya zuko tataccen ruwan jinin da ita sannan ya dauki doguwar robar nan mai kama da rula ya diga ruwan aramin dake tsakiyar ta sannan ya dauki daya kwalbar mai kama data maganin ciwon ido ya diga sinadarin dake cikinta akan tataccen ruwan jinin sannan yaja da baya muka zubawa sarautar Allah ido ga mamakina sainaga ruwan jinin yana zagayawa ahankali ta cikin farar robar ba'a dade ba kuma sai ruwan jinin ya rikide ya zama tsaki-tsaki fari fat dashi kamar an jika dakakken alli acikin kwalba.

Likitan ya girgiza kansa fuskarsa ta yamutse hakan da yayi kawai ya ishe ni na fahimci gaskiyar al'amarin ko tantama banayi cutar KANJAMAU ta tabbata ajikin Salma tun kafin a bamu katin sakamakon Salma ta fadi sumammiya ahaka na kai ta gida da taimakon MALAMAN ASIBITIN.

******* ******** ****** ********** **************

Washe garin ranar da abin yafaru da safe da misalin karfe goma sha daya Salma ta bude idanunta ahankali tana dubana. Tun jiya dana dauko ta daga asibitin bata farka ba lokacin da zamu taho likitan ya hado mu da nurse nurse Guda biyu wadanda zasu kula da Salma har ta farfado Yakuma ce dani wai akwai maganin cutar sabo da masana kimiyya suka kirkiro kwanan nan acewarsa in har Salma zata sha to akwai yiwuwar takara shekara akalla goma aduniya kafin cutar ta kaita kushewa. Ni ban gaskata shi ba.

Lokacin da salma ta bude idanunta saitayi min murmushi nurse din biyu suna zaune acan kuryar dakin lokacin da sukaga hankalina yakoma kan gadon sai suka matso bakin gadon suna duban Salma.

Yaya jikin naki? Daya daga cikin su tace

Da sauki Salma ta amsa sannan tace dasu
Dan Allah idan Baku damu ba ku dan baku guri zamu tattauna ni da Kanina.

To hajiya suka amsa cikin girmamawa bayan sun fice daga dakin sai Salma ta dubeni cikin tsananin damuwa tace dani.
Farisu hakika ko ban fada maka ba kasan ni rayuwata tazo karshe aduniya domin nasan koda lokacin da wannan muguwar cuta zata kashe ni baizo ba nasan tunani da ciwon zuciya ne zasuyi ajali na tafara sharar hawaye.

Kidaina kuka Salma ai ita cuta bata kawo mutuwa.
Kayya Farisu nidai da zaka daina zolayar kanka da ka faranta min.

Yayi shiru sannan tace
Farisu tunda nazo duniya Ban aikata wani abin alkhairi ba arayuwata ba kamar yadda ka sani banida wata al'ada daya wuce bin maza da kokarin mallakar dukiyarsa saigashi daga karshe duk abanza son zuciyata da mugun kwadayin abin duniyata basu kare ni da komai ba sai nadama da takaici Kaicona Farisu dama ace hannun agogo zai koma baya to dana zamo mai kyawun hali na aure ka ka zamo mijina mai sona da marmarina a kowani lokaci.

Ta sake fashewa da kuka sannan ta kama hannuna da hannunta kamar an kara min kwanon tuya saboda dumi koda ta kama hannun nawa sai ta nuna min farkon haduwar mu da ita inda take cewa
BAZAKA FADA MIN SUNAN NAKA BA ?
Saidai wannan lokacin abunda take fadi daban.
Farisu takira sunana tana kuka nasan kana kaunata matuka kaunar da bana tsammanin akwai wani mahaluki aduniya da zai iya kwatanta min koda rabin taka. Sau biyu ina kokarin sanadiyyar karshen rayuwar ka amma duk da hakan kai baka daina kaunata ba saima ni tawa rayuwar daka ceta bazan manta dakai fa Farisu da'ace wani yakan tuna da wani a rayuwar kabari to dana tuna da kai.

Ta yunkura ahankali ta tashi zaune sannan ta sauko daga kan gadon idanunta sun kukkumbure ta lalubi karkashin gadon ta dauko wata yar matsakaiciyar jaka baka ta bude ta sannan tace dani
BANIDA KOWA ADUNIYA FARISU SA KAI.

NASAN DA'ACE.....MUTUWAR KASKO-29

Banida kowa Farisu sai kai nasan da Kanada ikon da zaka cire min cutar nan da ka cire min ita Farisu domin nasan kana kaunata.

Tausayinta ya kamani bansan sa'ar da hawaye yafara zuba akan kirjina ba.

Sal...Salma ni yau yaya zanyi na raba ki da cutar SIDA ?

Nasan babu yadda za'ayi Farisu to amma ka wahala saboda ni ka shiga hadarurruka da dama wadanda ba don Allah yasa kana da nisan kwana ba da yanzu kana kabari ta yi ajiyar zuciya sannan ta turo akwatin gabana tace dani
Kasan ko menene anan Farisu?

Na dubi cikin akwatin babu komai aciki sai wasu yan kananan littattafai masu kama da rasiti.
Ban sani ba nace da Salma muryata na rawa.
Duk dukiyar dana mallaka ce aciki (cek) din da yan fashin nan ne ke kokarin karɓa inason ka sani cewa na mallaki kudi sama da naira miliyan arba'in a banki

(AMMA KU SANI MASU KARATU MILIYAN ARBA'IN IRIN TA DA BA MILIYAN ARBA'IN DIN YANZU BA)

Ta dubeni tana sharar hawaye sannan ta matso kusa dani ta hada hannayeta bibbiyu ta rike ni tace
Banida masoyi kamar ka banida kowa sai kai don haka banga Wanda dukiya ta dace ta tafi gurin sa ba sai kai sannan ta dada da cewa
Zan bada umarni a bankunan dana ke ajiye kudin kan duk a maida su karkashin ikon ka na baka su Farisu mallakin ka ne daga yau Allah ya saka maka da alkhairi daga gobe ma idan kana so kana iya fara daukar abinda kaso mallakin ka ne.

Na gama rudewa na rasa bakin ciki nake ko farin ciki na dube ta nace.
Salma me like nufi ne?

Haba Farisu yau aka haifaka ne? abinda kayi min da kuma irin kaunar da ka nuna min tafi karfin abinda na baka da'ace inada abinda yafi wannan ma dana baka ina son kayi min alkawarin karshe Farisu.

Fadi mana Salma me kike so?
Inason don Allah bayan na mutu ka daure lokaci lokaci in Kanada iko kana ziyartar kabarina ka rokar min Allah ya saukaka min kwanciyar kabari.

Ta fashe da kuka sannan ta daga karkashin matashin kanta ta dauko katin dake dauke da sakamakon gwajin da akayi mata jiya tace dani.
Ga wannan ka bari sai gobe bayan na mutu ka kaiwa Tajuddeen domin shima ya dandana azabar fargabar da zatayi sanadiyyar mutuwa ta idan kayi haka farisu kagama biyana nagode wa Allah farisu da ba MUTUWAR KASKO zamuyi gaba dayan mu ba akalla dai ina da sauran me yi min addu'ar alkhairi aduniya.

Tashi ka tafi Farisu Allah ya zaba maka masoyiya ta gari mai halin kwarai da nutsuwa ba Irina ba marar amfani

Kidaina fadar haka Salma nace da ita ina kuka sharaf sharaf.

Kada ka bata lokacin ka Farisu tashi ka tafi bana son kaga mutuwa ta don Allah ka tashi ka tafi kada ka batan rai.

Jin cewa zan bata mata rai saina tashi sannan nace zan dawo go...

Wayace maka zan kai gobe?

Na nufi kofar dakin hawaye sharaf sharaf.
Farisu Salma ta kira sunana nadawo da sauri dauki akwatin ka tafi da ita ko ka manta yanzu taka ce.

Ta dafa kafada ta sannan tace cikin sassanyar murya
Bani da abun so kamar ka Masoyina ina kaunar ka Farisu don Allah kace min kaima kana kaunata.

Na dube ta cikin takaici nace da ita cikin kuka.
INA SONKI SALMA HAR ABADA INA KAUNAR KI... INA KAUNAR KI.

Ahaka Nabar dakin ina kuka lokacin dana isa babban falon saina samu nurse din nan guda biyu suma suna kuka babu mamaki sun ji duk abunda ke faruwa.

******** ********* ********** ******** **********

Washegari Salma tace ga garin ku nan ta akwatin rediyo na sami labarin mutuwar ta sun bada takaitaccen tarihin mutuwar ta a cewar su ciwon zuciya ne ya kasheta sun kuma danganta hakan da kisan gillar da yan fashi sukayi wa mijinta a kwanakin baya.

Saidai abunda ya firgita ni shine.......

KASHHHHHHH NEPA SUNYI TSIYA
KU KASANCE KUSA DA WAYOYIN KU DAI

DA ZARAR NEPA SUN DAWO DA WUTA CIGABAN NA NAN TAFEMUTUWAR KASKO-30

ƘARSHE......

******** ********* ********** ******** **********

Washegari Salma tace ga garin ku nan ta akwatin rediyo na sami labarin mutuwarta sun bada takaitaccen tarihin mutuwar ta a cewar su ciwon zuciya ne ya kasheta sun kuma danganta hakan da kisan gillar da yan fashi sukayi wa mijinta a kwanakin baya.

Bayan mutuwar ta da kwana biyu nayiwa ofishin Tajuddeen tsinke bayan wasu yan kananan tambayoyi na sami ganinsa yana zaune akan kujera teburin dake gabansa fal da tarin takardu karan sigari a bakinsa.

Fuskarsa ta yamutse lokacin daya ganni.
Me kuma yakawo ka SARKIN BARAYI? Tunda ta mallaka maka komai menene kuma na zuwa gurina kura da shan bugu gardi da kwace kudi?

Na dube shi cikin mamaki nace A ina ka sami labarin cewa ni ta yiwa kyautar dukiyar ta?

Wanene baisan da labarin ba

Kai baka karanta jaridu? Ta hanyar bankunanta yan jaridu suka sami labarin. Tashi ka fice daga nan bana son sake ganin mummunar fuskar ka anan.

Na zaro katin data bani sannan nace dashi
Hutar da bakin ka kar hauhawar jini ta kama ka kaima ai ba ta barka haka ba. na mika masa katin na zura masa ido.

Da farko katin bai bashi wata ma'ana ba sai daga baya sannan fuskarsa ta yamutse nan da nan shekaru suka karu akan nasa na da gumi ya lullube shi.

I...ita ta baka wannan?

Ita ta bani wannan tace nakawo maka shine sakamakon abunda kuka aikata itama abinda ta tsira dashi kenan.

Na dubi katon dansandan dake fuskanta ta duk kwarjinin dake fuskar sa tarikide ta zama nadama da takaici dakuma fargabar irin mummunan karshen dake fuskantarsa.

Farisu bata bar min komai ba sai wannan?

DATA bani dana baka ai ba ga wannan na kawo maka ba.?

Ga mamakina sainaga hawaye sun fara kwaranya akan manyan kumatun dansandan.

Haba YALLABAI.... nace dashi
Kuka bai kamaci babban mutum kamar ka ba

Don Allah kayi min wata alfarma mana guda daya Farisu

Alfarmar me? Na tambaye shi
Na dade ina aikin nan Amman ban tara wani abin kirki ba don Allah kazo ka taimaka min da rabin abinda ta baka.

Na dube shi cikin mamaki domin ganin duk da barazanar cutar dake jikinsa bai daina hadama ba.

Abinda nake nufi Farisu shine ina da iyali da yawa idan na mutu bansan irin halin da zasu shiga ba kaga kuwa ni rayuwata tazo karshe.

Hakane saidai kuma ina ganin rabin abunda ta bani yayi maka yawa indai ba har kana ganin kyautar datayi min ce bata dace dani ba kokuma tayi min yawa

Ya shafi gashin bakinsa jikinsa na rawa sannan yace I... to kusan abinda nake nufi kenan domin kaima fa idan aka bi gaskiyar al'amari bai kamata ka karbi kyautar dukiyar ta ba tunda kasan ba hakkin ta bane.

Hakane nace dashi
Saidai kuma akalla ni ba'a hada baki dani an kashe mutum ba. Na mike tsaye

TO YALLABAI Ni zan tafi
Kana nufin bazaka bani komai ba?

Na dube shi sannan na tuna da maganar Salma inda take cewa DA TAIMAKON SA NE AKA KASHE UBAN GIDAN KA ALHAJI SABI'U SUHUNUNU
Gaskiya ina mai tabbatar maka da cewa bazaka sami komai ba alkawari daya zanyi maka.

Ya dubeni sannan yace.
Alkawarin me?

Atunaninsa alkawarin kudi ne na dube shi sannan nace dashi
Nayi alkawarin zan aiko maka da LIKKAFANI aduk lokacin da cutar ta aika ka kiyama.

Na fice daga ofishin da gudu-gudu na barshi tsaye agurin sundum-dum kamar mutum mutumi.

ƘARSHE......

NAZIR ADAM SALIH (Nas)
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

1 Comments On MUTUWAR KASKO
avatar
mahamane-noura

1 year ago

Reply

Oui

Please Login or Register in order to submit comment