Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na rawa.
Kada ku harbe ni..... Ku
BA harbin ka zamuyi ba soke ka zamuyi da wuka ina tsammanin ahaka zakafi jin dadin mutuwa sannan lukutin mutumin nan yanufi kan gadon.

Na bude baki cikin fargaba abin kamar wasa har kwanan gobe idan na rufe idanuna ina ganin sa'adda ya luma wukar acikin alhaji sabiu maigidana
Alhaji sabiu Ya kwalla kara lukutin mutumin yayi tsalle yafada kan ruwan cikinsa ya daga wukar sannan ya sake aikawa da ita kahon zuciyarsa. Jini ya rine gaban rigar sa. Na kwalla kara cikin kaduwa sannan na yanke jiki na fadi kasa naci gaba da addu'ar Allah yasa kada SALMA ta fito su......
Adaidai lokacin ne kofar dakinta ya bude tana sanye da doguwar riga kanta ba dan kwali a tsammanina ganinsu zaisa ta gudu amma saita tsaya agurin.
GUDU SALMA....!
Nace da ita cikin karaji ta dubeni sai tayi murmushin da yafi komai tashin hankali a gareni.

Ya mutu? Abinda yafara fitowa daga bakinta kenan idan bai mutu ba menene amfanin biyan nu da kikayi lukutin mutumin ya amsa....

Ai yanzu ya zama dan gari a kiyama. Nayi kuka mai tsanani saboda bakin ciki suka bushe da dariya.
Sal... Salma yanzu.... Dan rashin imani kika sa aka kashe shi
Ai bashi kadai bane tace dani.
Kai ma kwanakinka sun zo karshe Daman ance wanda bai ji bari ba yaji hoho sai danace da kai kabar gidan nan ka ki to gareka.
Amatsayina na wacce ta taba sonka iya abunda zanyi ma kenan kai kuma yau kwanan ka sai kiyama toh Farisu a gaida su.....
Wani abu ya daki tsakiyar kaina bakaken taurari suka bayyana a fuskata sannan na daina tunanin komai da komai abu na karshe danaji shine muryar Salma tana cewa
KUYI DUK ABUNDA KUKA SO DASHI BURINA NIDAI SHINE KU HALAKA SHI ASIRINA YA RUFU.
Me kike so muyi masa? Lukutin ya tambaya.
Idan kun so ma kuna iya jefa shi rijiya gaba dubu.....

MU HADU A LITTAFI NA BIYU

Daga Fasihin Marubuci Nazir Adam Salih (nas)

DAGA NI
YARIMA A. GANGARIYA
(jikan sidi mai jaka)MUTUWAR KASKO-17

LITTAFI NA BIYU

Na bude idanuna gamida salati. Can cikin kwakwalwata kamar ana tseran dawaki saboda rugugi da ciwo mai tsananin gaske.
Da farko na dauka a kabari nake saboda tsananin duhun dake lullube dani duk da yake na bude idanuna hakan bai sa ina iya ganin koda tafin hannuna ba ballantana naga abunda ke cikin dakin.
Na juya ahankali sainaji kafafuna da hannayena a daure suke tamau da igiya abun bakin ciki kuma shine igiyar babu damar kokarin kuncewa domin kuwa kowanne Makeri ne ya kera sarkar hakika yasan hada karfe da karfe guri guda ko motsi nayi sainaji kamar sarkar ta kara nannade ni.
Nayi mamakin irin dakin da suka aje ni domin abunda nake kwance babu alamar tabarma balle katifa a tsakar dakin suka jefar dani kamar buhun siminti duk inda na motsa duwatsu ne a tsakar dakin ke kokarin hudani da raina.
Kusan mintuna goma idanuna bude. Abubuwan da suka faru a daren daya gabata suka fara dawowa zuciyata daya bayan daya tamkar ya'yan carbi shin ina Salma.?
KO yanzu anyi jana'izar Alhaji suhununu? Tambayoyin da naci gaba da yiwa kaina kenan aduk sa'ar da tunanin ya fado min sai hoton abubuwan da suka faru su sake bayyana karara azuciyata na tuna sa'ar da katon nan yayi tsalle ya fada ruwan cikin Alhaji suhununu sannan ya soke shi da wuka kamar kabewa shin idan yan sanda suka tsince shi da safe matacce me salma zata ce dasu.
Tun kafin na karasa tambayar kan nawa amsar tambayar ta fado min zuciya idan tace da su yan fashi ne suka shigo gidan cikin dare suka kashe shi... Nasan tagama fita ba dan komai ba kuwa sai don.... Gumi yafara ketowa ta goshina tabbas Salma taci banza tasa an kashe banza abun da kawai yan sandan zasuyi su gane gaskiyar labarin da Salma Ata basu shine su laluba aljihun alhaji sabiu suhununu anan zasu sami wasikar da barayin nan suka aiko masa wannan kawai ya Isah ya fitar da ita.
Idan akwai abu daya dana tsana aduk duniyar nan ayanzu bai wuce Salma ta tsallake wannan siradin abanza ba... Tuni ta sa an kashe mutum gashi kuma.... Tunanina ya katse adaidai lokacin dana tuna kalaman ta na karshe kafin su sumar dani..
IDAN KUN SO MA KUNA IYA JEFA SHI RIJIYA GAƁA DUBU.
Na juya ahankali ciwo mai tsanani ya soki kwakwalwata shin to ko daure ni sukayi suka jefa ni cikin Rijiyar shiyasa nake gani na cikin duhu babu alamar haske ko motsi.
Kamar amsar tambayata adaidai lokacin sainaji motsin wani abu daga bangaren inda kafata take domin alokacin bana iya gane ko da gabas wajen yin sallah ballantana yamma. Motsin yaso yayi kama da motsin takun sawun mutum.
Nayi shiru ina saurare DAKYAR nake numfashi saboda kaduwa tabbas indai har ba acikin rijiyar nake yanzu ba toh nan bada dadewa ba zan tsinci kaina cikin Rijiyar da gaske tabbas nasan ni kwanakina sun zo karshe aduniya domin duk mutumin dazai iya daga wuka ya sokawa mutum aciki toh jefa mutum rijiya kamar jefa dan dayis ne akan fale falen gilashin ludo agurinka.
Abu biyu ne suka faru lokaci guda na farko sautin wani abu dayayi kama da budewar kofa ya bugi dodon kunnena sannan lokaci guda gaske ya mamaye gurbin duhun daya lullubeni kamar bargo
Idanuna sukayi dum sai bayan shudewar wasu yan dakiku da basu wuce lissafin yan yatsun kafa da hannuna ba ne sannan madaukin hoton dake idanuna ya daidaita sabanin dake tsakaninsu da haske a sakamakon dadewa da bakin duhun yayi a gurbin haske. Sannan ne to na ganshi tsaye kofar dakin yana dubana da mitsi mitsin idanunsa kansa sal sal yana sheki hasken danake tsammanin na hantsi ne har yanzu Wandon dake jikinsa na wancan lokacin ne da ya taso ni a daki cikin dare kafar Wandon daya tafi daya tsayi bakar suwaitar ma itace babu canji a kirjinsa an rubuta THE DEVIL.
Nayi sauri na dauke fuskata daga kallonsa lokacin danaga ya murtuke fuskarsa murtuk kamar wanda aka yiwa albishir da bulala dari.
Menene kake kallona?
Ya tambaye ni yana muzurai.
Da wannan idon kasan ina kallon ka daya tafi daya?
Nace dashi ina murmushin karfin hali a tunanina zai matso kusa kusa ya kife ni da mari amma ga mamakina sainaga yayi murmushi sannan yace dani.
Dadina dakai taurin kai kayi ahankali watarana zai kai ka ga halaka.
Na nawa kuma nace dashi
Wai ance da kuturu ka gani yanzun ma ai ya kaini ga halakar ko kun fasa jefani a Rijiyar? Bai amsa ba sai kawai yayi shiru yana dubana kamar wani naman daji sannan ya juya ahankali ya dubi kofar dakin kamar wanda yake tsoron kada yafada wani yaji abunda yake fade.
Tsakanin ni da kai kawai Farisu ina tsammanin da wahala mu aikata hakan.
Meyasa na tambaya ya hade fuska sannan yace
Bana son tambayar banza wacce irin tambaya ce wannan kaidai kawai kaji abunda zan fada maka batareda ka tambaye ni. Sannan ya dada da cewa...
Idan ka sake yi min irin wannan tambayar to tabbas yau a rijiya gaba dubu zaka kwana.
Ahankali yaa matso kusa da inda nake sannan cikin gwaninta ya kwance sarkar dake daure da kafafu da hannayena.
Tashi muje kayi wanka yace dani kadan yaa rage na tambaye shi Meyasa ya kunce ni........

********* ******* ******* ******* *******

Lokacin da muka shigo cikin falon duk sai suka dago kai suk dubeni Tangamemen Falo ne mai.........MUTUWAR KASKO-18

Tashi muje kayi wanka yace dani kadan ya rage na tambaye shi Meyasa ya kunce ni........

********* ******* ******* ******* *******

Lokacin da muka shigo cikin falon duk sai suka dago kai suk dubeni Tangamemen Falo ne mai girman banza ba don komai ba kuwa sai don duk girman falon babu koda kujera daya ta alfarma sai dogon benci mai kamar makara a gabansa teburi ne dauke da kofunan shayi da kwanukan abinci.
In ka dauke benci da teburin dakin babu komai sai yar rekekiyar fankar dake barazanar sare kan duk wanda yacika tsayi da yawa kokuma yayi daddage.
Fankar tana lilo a saman dakin gamida rurin toshe kunnuwa dole ne ka daga murya in har kana so dan uwanka yaji abunda kake fade.
Kasan falon babu kafet sai tsohuwar ledar tsakar daki mai dauke da zanen tauraro da fulawa acan kuma bangaren dakin daga yamma kwandon shara ne na roba shudi idan kuma har ka damu da kasan abinda ke ciki to takardun tsire ne da barayin suka ci gamida kwalayen taba da fatocin lemo da burbushin tokar taba da dai sauran ire iren iyalan bola.
Duk wannan na lura da su ne kallo daya.

Barayin biyar ko kuma ince yan ta'addan biyar suka dago kai suka dubeni sannan Nima na dube su daya bayan daya tun daga hannun hagu har izuwa hannun dama.

Mutum na farko daga hannun hagu yayi min murmushi hantar cikina ta yamutse lokacin dana tuna sa'ar da yadoka wukarsa a ƙahon zuciyar Alhaji Suhununu katon mutumin nan ne mai dan karamin kai da fankama fankaman kunnuwa kamar tabarma.

Mutumin dake kusa dashi shima na gane shi yana cikin tawagar da Salma ta tura gidan domin kashe mijinta alhaji Suhununu dan siriri ne mai kirar yan ruwa wasu lokutan idan yana duban ka saika kaga kwayar idanunsa tana kallon bangare daban shi kuma kokon kansa na fuskantar ka.

Na ukun shima siriri ne saidai ya dan fi na biyun abin kirki yana da tarin suma aka shirim kamar dalar gyada fuskar sa doguwa ce saidai bajajjen hancinsa mai kamar begila da ya mamaye duk kusan fuskar shiya bata doguwar fuskar.
Sanye yake da riga ta jeans da Wandonta bakake ahannunsa na hagun akwai wani dan karfe launin azurfa mai kama da awarwaro ajikinsa an rubuta cikin kananan haruffa (A.A ATIKU)

Mutum na hudun ba wai abin azo agani bane dan gajere ne sanye da kwat da Wandon ta bakake. Tsaf dashi kwat din awanke a goge takalmin sa na walkiya saboda goguwa saidai aduk lokacin daya yi dariya sai ranka ya ɓaci saboda katon wawilon dake dasashinsa na sama idan ba dan suman dake kansa ba babu abunda zai iya hanawa ya wuce amatsayin kadangare indai har zai iya jan ciki.

Na biyar din lukuti ne kazami kayansa sunyi dukun dukun a tattare kamar an kwato daga bakin saniya yana da tarin gemu duguzunzum babu gyara kamar shekar ungulu in ba don gemun yayi tsayi da yawa ba to da babu abinda zai hana mata yin maraba dashi wajen yin wanke wanke amatsayin soso saboda kaushin sa.

Lokacin dana sake duban yan ta'addar sainaga Sam Sam basu yi kama da irin mutanen dana sani ba.
Duk sainaga sunyi kama da butu butu a jirkice kamar an tono su daga kabari kowa yagansu yaga annabo muna neman tsari dasu Daga Allah.

Shiga kayi wankan mana mai gemun ya daka min tsawa. mai kafar Wandon daya tafi daya yayi min jagora zuwa bandakin sannan yace.
Duk abunda kake bukata akwai aciki kayi sauri kafito oga yana son ganawa dakai.

Lokacin da sassanyar ruwan yafara kwararowa daga shaya zuwa tsakiyar bayana sainaji dadi
Kwari kwarin jikina suna shiga kasusuwana sannan ne to na jiyo muryar sa yanata babatu.
HAKA SALMA ZATAYI MIN?
Nayi Sauri na kara Kunnuwana Ajikin kofar domin Naji sosai.
ZATA GANI SAI TAYI NADAMA.
NAFIN KARFIN ACUCE NI A KWANA LAFIYA.
Farisu yi sauri mana. Ya kwalla kira hantar cikina ta kada sauran kumfar sabulu akaina nasaka kayana saboda fargaba na rugo da gudu.

****** ****** ******* ****** ************

KASHI NA BAKWAI

ZAUNA ANAN FARISU NABAKA TARIHINA
Sunana Sariku Ma'ana ƁARAWO Idan baka gane ba. Ya shafi duguzunzum din gemunsa yace......MUTUWAR KASKO-19

****** ****** ******* ****** ************

KASHI NA BAKWAI

ZAUNA ANAN FARISU NABAKA TARIHINA
Sunana Sariku Ma'ana ƁARAWO Idan baka gane ba. Ya shafi duguzunzum din gemunsa yace......

Tarihina na da ban mamaki da tsoratarwa sannan kuma yanada ban dariya wasu lokutan kuma Zakayi tsammanin ba kai na daya ba. To duk koma dai me Zakayi tunani ina son ka sani cewa zan baka labarin tarihi na ne Badon komai ba sai don na gargade ka ga barin tunanin tserewa daga hannuna domin kaine garkuwar da zanyi amfani da ita wajen yakar macuciyar nan da kai zanyi amfani wajen yashe duk kudin data mallaka amatsayin gado sannan kuma daga karshe na kashe ta kamar yadda ake kashe kiyashi kai tsaye batareda da motsa idanu ba ballantana kwalla saboda....
To Naji kace zaka rike ni amatsayin garkuwa toh Idan ka gama da Salma ni kuma menene matsayina?
Kashe ni Zakayi kokuwa zaka barni ne nayi tafiyata? Na katse shi.
Me yiwuwa ka tsira da ranka amma banyi maka alkawarin haka ba babu mamaki kaima daga karshe acikin tsohuwar Rijiya zaka karashe kwanakin ka na karshe aduniya.

****** ******* ****** ****** ***** ******

Tun ina ƙarami aka kaini makarantar allo wani kauye.
Yaci gaba da cewa kwana na biyu da zuwa makarantar na fasa wa yara uku kai da Allo.
Na dube shi a ya tsine saidai bai damu da duban nawa ba yaci gaba da cewa
Ka san abinda yasa na fashe kawunan su? Idan kana son sani to ba wani abu bane daya wuce son kai da malamin ke nunawa tsakanin mu yaran uku ya'yansa ne kuma sun dan dara mu a shekaru amma lokacin danaje saina tarar da wata sabuwar al'adar son kai wai kullum da safe za'a tashe mu maimakon muyi karatu sai a tura mu gona muyi ta aikin gonar malamin mu da mu dawo sai yamma likis sannan da mun dawo sai mu zauna karatu to amma haka ma bai yiwuwa in har akwai wani dan sauran aiki agidan malam kamar gyaran katanga ko wanke wanken gida. To amma fa Farisu duk da abin nan ya'yan sa basa aikin komai gasu da rashin kunyar tsiya kamar berayen tanka basu da aikin fari balle na baki sai ka barato abinci su barar idan kuma mai kyau ne sai malamin yace sai sun ci zasu baku sauran.
Kwanana uku da zuwa suka barar min da abincina ban bata lokaci ba na fashe kan yaron na farko biyun suka nufo ni a fusace suma na fashe kawunan su kamar koruka.
Ya dubeni sannan yayi murmushi idanunsa akan fuskata.
Farisu ina baka Tarihina a takaice ba don kuma komai ba sai don kasan abinda yasa na fi sa kudi agabana fiyeda rayukan jama'a watanni na biyu acikin mari kullum sai malam ya zazzane ni abinci ma baya bani tun safe sai dare.
Bayan an kunce ni daga marin sai tafiya ta zamo aiki saidai da kyar nake tafiya kamar mai tata-tata sati daya da faruwar hakan na murmure tun Sa'adda malamin da yasani a mari Nake tunanin yadda zanyi na dauki fansa in yaso daga nan ma ina iya barin makarantar.

Kwana Uku ina tunane tunane daga karshe ran cikon kwana na hudun na yanke mummunar shawara.
Tun da magariba nafara hada duk wani kayan da zai amfane ni kodayake banyi niyyar daukar kaya dayawa ba abubuwan da zasu amfane ni su na dauka kamar sittiru takalma da kuma katon allon karfen dana sato daga dakin malamin wanda dashi ne nake fatan sassake kan azzalumin malamin.

Karfe daya da mintuna arba'in da biyar na dare garin yayi shiru.
Alokacin babu wani Mahaluki Dake zagayawa acikin gidan daga aljanu saiko BURUNGU aljanar dare kowa yayi dare da rabon ki....ya dubeni yana zazzare idanu sannan yace shin kasan ma'anar Burungu Aljanar dare kuwa Farisu?
Na girgiza kaina cikin kaduwa KURA kenan. Ya amsa min kai tsaye sannan ya dada maimaitawa Kura kenan Farisu su kadai ne ke yawo acikin kauyen garin. Lokacin dana tashi daga dakin da muke duk sauran almajiran sunyi bacci don haka cikin sanda na fito daga dakin na nufi gindin wani katon rumbu wanda nan ne malamin ke ajiye amfanin gonarsa a karkashin sa ne na ajiye jakata.

Na bude jakar ahankali duk abinda nake bukata Na ciki abin kawai daya bakanta raina shine banida ko sisin kobo tabbas gudu kuwa kasan bai yiwuwa sai da kudi. Nan da nan idanuna suka raina fata gwiwowina suka sanyi domin in har abinda nake shirin aiwatarwa ya tabbata dole ne na bukaci kudin da zasu tserar dani daga garin. Abubuwa suka dagula gashi kuma lokaci sai matsowa yake kafin asuba tayi nake son na aikata shi.
Don haka cikin yan mintuna sai dabarar karshe tayi dirar ungulu cikin zuciyata.
Ban bata lokaci ba Farisu ban kuma sake tunanin shawarar ba sai kawai na janyo jakata daga gindin rumbun na zaro allon karfen sannan na nufi can bangaren kudu na gidan..

Bayan nayi yan waige waige na tabbatar da babu kowa cikin farfajiyar gidan cikin sauri na nufi turakar malamin ga mamakina ina tura kofar sainaji ta a bude bayan kuma ga al'adar malamin bai barin kofar dakinsa bude duk tsananin zafi kuwa babu mamaki karar kwana ce.

Ya dan shiru yana dubana yanzu kam na tabbatar da cewa mutumin nan mai kallona tabbas ba kansa daya ba na dubi fuskokin sauran ta'addar dake zazzaune sunyi tsit dasu kamar ruwa ya cinye su aduk iya tsawon lokacin daya dauka yana bani tarihin sa na hauka babu wani Mahaluki da yayi koda kwakkwaran attishawa ballantana har yasa baki cikin maganar...

Farisu.. Yakira sunana yana murmushin yake kamar yadda kaga nayiwa ubangidanka alhaji suhununu haka shima nayiwa malamin nawa na haye bisa ruwan cikinsa na wanke masa fuska da katon allon karfen ya farka a gigice na sake daga allon karfen na tafka masa shi a tsakiyar kansa sannan nasa gindin allon karfen na soki cikinsa ban kuma taba.........MUTUWAR KASKO-20

Ya farka a gigice na sake daga allon karfen na tafka masa shi a tsakiyar kansa sannan nasa gindin allon karfen na soki cikinsa ban kuma bata lokaci ba na lalube dukkan kudin dake dakin ire iren kudin dayake samu na sadaka na hada kudin Nabi dare na sulale. Tun daga ranar ban sake kulla wani abun arziki ba aduniya lokacin da nazo
BIRNIN SARAUNIYA saina hadu da wadanda suka fini busashshiyar zuciya tun daga ranar da nagama da malamina ban sake tausayawa wani dan Adam ba aganina aduniyar nan babu abunda yafi kudi don haka bana saurara wa kowa wajen neman sa koda kuwa hakan na nufin kisan kai ne.

Farisu inason ka sani cewa uwargidan ka Salma kokuma Ince tsohuwar masoyiyar ka ta yaudari kanta datake tsammanin zata iya cutata. ta samu mun kashe maigidan ta don bukatar Son ta gaji makudan kudaden da zai bar mata gado tunda bashi da kowa ita.
Amma abin mamaki sai gashi ta kasa bani yan kalilan din kudin datayi niyyar bani wadanda idan aka kwatanta su da wadanda ta mallaka kamar ta dauke kofin ruwa daya ne daga cikin kogi.
Ganin cewa tunda nake arayuwata bantaba kulla abin arziki ba shiyasa ni tunanin yin murabus na bar sata to amma saina yashe Salma sannan zan salami yarana kowa Yakama Gabansa Nima na kama gabana na sayi gida nayi aure nayi zamana acikin rayuwa irin ta sauran mutane tunda dai idan ka dubeni Farisu zaka san girma ya fara zuwa min ko bahaka ba?
Na gyada kai jikina na rawa. Gobe zamuje unguwa dakai in har abinda muke fata munyi nasara to me yiwuwa ka tsira da ranka nasan da naira dubu hamsin a aljihun ka kana iya barin garin domin gudun kada yan sanda su cafke ka...
Ka... Kana nufin har dani? Na tambaye shi cikin fargaba.
Tabbas kuwa Farisu ai da kai din be zanyi amfani wajen kwashe duk dukiyar ta kaida a tsammanin ka haka zaka zauna KACI BULUS? Cab to ka sake tunani.

Tayaya Zakayi amfani dani? Na tambaye shi
Abinda baka sani ba shine SALMA ta riga ta tabbatarwa da kanta cewa bayan cin amanar ka datayi ayanzu haka bakada abin ki kamar ta kuma tayi imani da cewa duk abinda Zakayi kana iya yi domin ka bata ta. Hakan shiyasa ta bamu umarnin idan mun kashe mijinta kaima mu kashe ka kaga kenan babu sauran wanda zai bada wata mummunar shaidar da zata ruguza dukkan shirin ta sai mu to amma tasan mu muka aikata laifin hakan bazai yiyu ba mu tona asirin ta ga kowa.

Tuni dama nayi tunanin zata gwada cutata don haka na hana yarana su kashe ka har sai ta biya ni to abin kuwa da nake gudun yafaru domin yau kwananta hudu da mallakar dukiyarsa baki daya don haka yanzu tanada yakinin tagama damu tunda ta tara kumburarrun banza wai amatsayin masu gadi kuma a tunanin ta mun kashe ka.

Ni haryanzu baka bani amsa ta ba shin tayaya zakuyi amfani dani kuma kana tsammanin duk kudin data mallaka agidan suke cikin akwatuna a kulle ballantana kayi tunanin kwacewa?
Yayi Min dariya sannan ya shafi gemunsa hakan dayayi shi ya tuna min da IJAKALA babban yaron HINDU EL-BASHEER nayi mamakin halin datake ciki ayanzu.

Abunda baka sani ba Farisu shine idan akwai abu daya da Salma ta tsana shine mutuwa kaga dai babu kunya babu tsoron Allah tabamu KWANGILAR kashe mijinta amma ita akan kanta bata ko san jin zancen makabarta idan kuwa hakane toh ya zama dole ta bamu cek na kudin data mallaka gaba dayansu tasa hannu idan kuma bahaka ba to zamu rabu dakai kayi tafiyar ka.
Yayi shiru yana murmushi ban fahimci abinda kake nufi ba ku sake ni na tafi kamar yaya.?
Kai tsiyata dakai baka fahimtar al'amura Farisu nafada maka idan akwai mutum daya da Salma ta tsana aduniya kaine to itama kuma a tunanin ta kagama tsanarta don haka da zarar mun ce da ita ga ka nan da ranka baka mutu ba zata kidime domin tasan dole ne ka kai dukkan labaran kisan kan da mukayi gun yan sanda. Ya rage namu mu dai munsan Daman dole ne laifin kisan kaine a kanmu kuma ko banza Daman mu bamu da wani sauran buri aduniya duk rayuwar mu abanza tafara haka zata kare to amma Farisu kana tsammanin Salma zata yarda ka kai labarin ga yan sanda? Kana tsammanin zata zabi ranta akan dukiyar data mallaka tuni nafa fada maka duk zalamanta akan kudi bata kai koda rabin yadda take tsoron mutuwa ba.

Ya shafi saman gashin sa sannan ya kanne idon sa daya yace. Gane min hanya Farisu wai makaho yayi dare in dai har inda Salma zata hana mu cek din kudin?
Na girgiza kaina cikin kaduwa sannan nace kana nufin idan ta baku cek din nikuma tawa ta kare kenan?
Ashe dai kana fahimta. Ya amsa min sannan ya dada da cewa dole ne in har tana so mu kashe ka don gudun tonuwar asirinta to tabamu cek din.

Idan ta baku cek.... Din.... Kashe ni din zakuyi da gaske? Na tambaya muryata na rawa ya dubeni ya dubi sauran yan ta'addar sannan yace dube ni sannan ka dube su shin duk acikin mu akwai wanda yayi kama da yan gidan ku?

Na Dube su cikin kaduwa na girgiza kaina tabbas basu yi kama da yan gidan mu ba saidai Ince maka sunfi kama da wadanda aka tono daga kabari
Toh in dai kuwa hakane babu abunda zai hana mu kashe ka in har bukatar mu ta biya ko ba haka ba Yan samari...
Hakane BOSS suka amsa baki daya. Ban gaskata Kunnuwana ba..

KASHI NA TAKWAS

Na Leko ahankali ta cikin shara-sharan labulen dakin mai kamar tarun kamun kifi adaidai lokacin da katuwar (Jeep)din tayi wa kanta matsugunni a gindin bishiyar dorawar turawan dake farfajiyar gidan....
Mutane biyar Suka dinga tsirgowa daga bayan motar daya bayan daya kamar ya'yan carbi....MUTUWAR KASKO-21

KASHI NA TAKWAS

Na Leko ahankali ta cikin shara-sharan labulen dakin mai kamar tarun kamun kifi adaidai lokacin da katuwar (Jeep)din tayi wa kanta matsugunni a gindin bishiyar dorawar turawan dake farfajiyar gidan.

Mutane biyar Suka dinga tsirgowa daga bayan motar daya bayan daya kamar ya'yan carbi.
Zaiyi wuya ka iya ganin koda tafin hannun ka acikin duhun daren gami da karin da duhun bishiyoyin farfajiyar gidan da suka kara baiwa duhun daren goyon baya to amma albarkacin fitilu biyar masu satar hasken rana da suka haske gidan shiya baiwa idanuna damar yiwa motar kallon tsaf.
Mutanen biyar din da suka tsirgo daga cikin Jeep din ba wasu bane da suka wuce yan ta'addar nan da suke rike dani amatsayin fursuna saidai Sam Sam ko kusa ko alama basu yi kama da mutane sosai ba sunfi kama da Aljanu fiyeda mutane ko wannen su sanye da bakaken kaya kawunan su nannade da bakin rawani shirim kamar karamin dalar gyada wani abin kari ga rawanin nasu shine zumbutun rawanin ya gangaro tun daga kyeyarsu har zuwa gadon bayan su kamar jelar tunkiya tafin sawun su sanye cikin takalman roba wadanda zaiyi wuya aji motsin takun sawun mutum.

Naduba ahankali daga jikin labulen na dubi agogon dake jikin bangon dakin da suka kulle ni aciki karfe biyu da

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

1 Comments On MUTUWAR KASKO
avatar
mahamane-noura

1 year ago

Reply

Oui

Please Login or Register in order to submit comment