Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

makiyi.
YA zazzare idanu sannan ya dada da cewa duk wanda ya sake ya taba min amaryata to hakika ya sayawa kansa mutuwa da kudinsa babu wanda ya isa ya taba min ita agabana saidai ko muyi MUTUWAR KASKO.
Dani dashi da ita baki daya amma ba dai ya taba ta ina raye ba.
BANTABA TSAMMANIN SHINE KE FADIN MAGANAR BA.....

******** ********** ******** ******* ************

Karfe Goma sha daya saura......MUTUWAR KASKO-11

BANTABA TSAMMANIN SHINE KE FADIN MAGANAR BA.....

******** ********** ******** ******* ************

Karfe Goma sha daya saura jirgin ya taba kasa ba'a dade ba mutane suka fara fitowa saidai mafiya yawa daga cikin fasinjojin jirgin jar fata ne bakaken fatar kalilan ne wanda akasarin su yan kasuwa ne tun goma da yan mintuna muka isa gurin taren bakin muna nan tsaye alhaji na ta hange hange ni kuma ina dubansa domin bansan amaryar tasa ba kirjina sai bugun uku uku yake saboda nasan nan da yan mintuna zanyi ido biyu da matar data sace zuciyar wannan bawan Allah. Tun jiya nake kwatanta kyawunta da kamannin ta azuciyata amma har zuwa yanzu ban sami wani kwakkwaran hoton irin kamannin amaryar alhaji cikin zuciyata ba.
Ko ba'a wannan jirgin zata zo bane? Alhaji yace dani cikin zakuwa. Na dago kaina ahankali na dubi jerin gwanon fasinjojin dake ta kwararowa daga cikin jirgin na bude bakina zan bashi amsa amma bakin nawa bai bude ba ban gaskata abunda idanuna suke hango min ba abin kamar budar ido bantaba tsammani ba. na rasa farin ciki ne ko bakin ciki ita ce mace ta karshe danake tsammanin zan gani acikin fasinjojin jirgin sanye take da doguwar riga shudiya mai sheki duk Sa'adda ta motsa sai jikinta yayi rawa lokaci guda da rigar dake jikinta fararen kafafunta sanye cikin bakin takalmi a samansa an rubuta da karfe ruwan gwal (MY LOVE) kanta lillibe da farin kyalle saidai bata damu data rufe dukkan gashinta da farin kyallen ba hakan shi ya baiwa iska damar wasa da siraran gashin kanta babu canji kamar yanda nasan ta adacan haka ma yanzu take sai ma kyau data kara yawun bakina ya kafe lokacin dana fahimci Alhaji Sabi'u ma ita yake kallo.

Farisu gata Allah yakawo ta rabin raina.
jiri yafara daukata bana gani sosai sai duhu duhu ba wata yake nufi amaryar tasa ba data wuce SALMA ko shakka babu Salma yake nufi MATARSA..

KASHI NA BIYAR 5
Tun kafin ta karaso tausasan lebban bakinta suka fadada izuwa murmushi fuskar Salma na annuri cike da farin ciki lokacin data nufo inda muke saidai abin bakin cikin bani take yiwa murmushin ba angon ta alhaji Sabi'u Suhununu wato Ubangidana kenan shi takeyi wa bana ko motsi ban kuma yi ko taku daya domin na taryi Salma ba na tsaya kyam kamar an dasa ni jikina a jike sharkaf kamar wanda kunama ta harba saboda gumi.
Farisu...naji muryar ta doki dodon kunnena me ke dam ka n naga duk ka wani firgice?
BA...bu komai nayi sauri nace dashi to amma idan akwai abinda yafi komai ma toh akwai shi agurin.
Har lokacin data karaso inda muke tsaye bata lura dani ba. Kadan ya rage su rungume junan su saboda farin ciki ita tana murmushi shima yana murmushi to amma ba murmushinsa ne ke bani mamaki ba sai murmushin Salma na dube shi na dubi Salma duk dayake dai ance so wai so ne to amma ina shakkar in Salma ta auri wannan mutum ne saboda tana kaunarsa kauna da zuciya daya.

Dauki jakar ka kai mota Naji muryarsa na fadi
Jikina a sanyaye na sunkuya na dauki yar matsaikaciyar jakar da Salma tazo da ita sannan na juya zan tafi sainaji yace..
Farisu Baku gaisa da amaryar tawa ba sannan ya juya gareta yace. Salma wannan shine Farisu sabon Ma'aikacin gida da na dauka bayan tafiyar ki sannan ya juyo gareni yace Farisu wannan itace Salma uwar dakinka ta dube ni na dube ta sannan saita yi min murmushi tabbas murmushin baikai har idanun ta ba iyakarsa bakinta kadan ya rage na mayar mata da murmushin saidai kuma lokaci guda murmushin ya subuce daga fuskarta kai kace an tsikare ta ne da kibiya na tabbata yanzu ta gane ni banyi mamakin rashin ganeni da ta kasa yi da wuri ba domin duk kamannina sun jirkita Naji jiki a yan kwanakin nan ba farisun data sani adacan bane to amma yanzu ta gane ni.

Ai sai mu tafi ko alhaji Sabi'u yace shi bai san abinda ke faruwa ba bai kula da murmushin ba bai kuma kula da subucewar da murmushin nata yayi ba wani abu ya lullube idanuna bana gani sosai sai duhu duhu muka nufi inda motar take ba zato ba tsammani sai naci karo da mutum sai bayan da na dago kaina na lura ashe wani jar fata ne ke kokarin kaiwa ga dakin saukar bakin dake filin jirgin saman.
STUPID yace dani cikin harshen turanci
Ban kula da abunda yake fadi ba saina ci gaba da tafiya
Farisu me ke damunka ne? Naji muryar alhaji Sabi'u na tambaya.
Kai na ke dan yi min ciwo. Nace dashi ban yarda na juyo mun hada ido dashi ba domin gudun kada mu hada ido da Salma wacce ke daf dashi suna tafiya suna hirar su ta ma'abota begen juna.

Na bude but din motar na jefa jakar aciki sannan na rufe ban yarda mun hada ido dasu ba domin gudun kada mu sake hada idanu da Salma al'amurana su rikice nayi sauri na bude musu kofar kujerun baya na motar tun kafin nagama budewa Salma tace
NI ZAN TUKA.
Alhaji Sabiu Bata dan makullin sai kai ka koma gidan baya.
Nayi mamakin irin yadda yake matukar zumudi domin bin ra'ayin ta. zuciyata na kuna na shiga na zauna abaya sannan nafara tunanin ranar da muka fara haduwa da ita inda take cewa...
BAZAKA FADA MIN SUNAN NAKA BA....?

IDAN KA AURENI SAIKA SAKE NI...... MILIYAN UKU ZAN BAKA.

TUNDA NA GANKA NAKE KAUNAR KA...

ADACAN BANA KAUNAR KA...AMMA YANZU BANGA WANDA NAKE KAUNA KAMAR KA BA...
FARISU NASAN YANZU KA TSANE NI MATUKAR TSANA AMMA DON ALLAH FARISU KAYI MIN RAI DOMIN IDAN BAKA AURENI BA BANSAN YANDA ZANYI DA RAYUWATA BA......

Tunanin abubuwan da tace suka ci gaba da zagaya zuciyata saidai abun mamaki yau gashi ta sake aure bayan ada tace idan naki ta batasan yadda Zatayi da rayuwar ta ba nayi mamaki ko shima alhaji Sabi'u Suhununu irin kalmomin datayi amfani dasu kenan a kansa ta yaudare shi
MAYAUDARIYA CE nace cikin zuciyata kadan ya rage tunanin ya fito fili.

******** ******* ******** ******** **************

Lokacin da muka dawo daga filin jirgin saman sai nace dashi kaina ya takura min da ciwo sannan kuma inajin zazzabi.
Babu komai alhaji Sabi'u Suhununu yace dani kana iya zuwa ka huta yadda kaso domin bana tsammanin zan bukace ka Ayau tafi ka kwanta Allah ya sauwake. Daman banyi tsammanin zai saurare ni ba bayan ga Salma akusa dashi ba.
Tun sa'ar dana kwanta ban farka ba sai karfe biyar na yamma bayan na rama sallolin da ake bina saina koma na kwanta ina tunanin irin yadda hannun agogo ke kokarin komawa baya
Hakika sabon zamanin da nashiga mai dauke da farin ciki a yan kwanakin da suka shude ayanzu yafara jirkicewa izuwa wancan tsohon zamanin mai tattare da dimbin tashin hankali abin saiya zamanto kamar a mafarki domin lokaci guda sai naji wani bakin ciki ya lullube zuciyata abinda nakasa fahimta shine zuwan Salma ne ya tuna min da wancan zamanin nake bakin ciki kokuwa ina bakin ciki da zuwan Salma amatsayin matar..... Idan kuwa hakane to abinda nake fargaba yafaru kenan son Salma na nan azuciyata nakuwa hadu da wahala tuni yanke shawarar Barin gidan sannan idan Nabar gidan barin garin ma zanyi zan shiga duniya nayi tafiya.. Tafiya har saina yiwa Salma nisa domin ganinta kawai ba karamin fitina bace a gareni akwai wani abu dake cewa da zuciyata muddin kana tare da Salma to kai da ka iya wani abun arziki da zai amfane ka kuma sai abunda hali yayi.

In Allah yaso nace da kaina gobe warhaka nayi nisa tuni daruruwan kilomitoci sun shiga tsakanina da gidan. To amma ashe bahaka abubuwa suka kasance ba.

******** ******* ******** ******* ***************

GA WAYANDA SUKA FARA BIBIYATA YANZU BAZASU FAHIMCI DAMBARWAR DAKE LITTAFIN NAN BA HAR SAI SUN KARANTA LITTAFIN DANAYI ABAYA MAI SUNA

*BIRNIN SARAUNIYA*MUTUWAR KASKO-12

In Allah yaso nace da kaina gobe warhaka nayi nisa tuni daruruwan kilomitoci sun shiga tsakanina da gidan. To amma ashe bahaka abubuwa suka kasance ba.
******** ******* ******** ******* ***************
Bambancin dake tsakanina da matacce shine ni ina numfashi shikuma ba yayi amma idan har zaka yi la'akari da motsi ko yawan juyine to kana iya kirana matacce Awannan daren. Na dade banyi nannauyan barci ba irin na wannan ranar. Dare ne mai dauke da dadddan iska mai ratsa duk sassan jiki hakan shi ya sa ni bude tagar dakin sannan ban damu dana kulle kofar dakin ba tun sa'ar dana kwanta nake fargaba idan nayi wasa yau sai sallar asuba ta subuce min. To amma nannauyan barcin bai iya hana ni bude idanuna ba sakamakon tsigar jikina danaji ta yi yarrr.

CIKIN talatainin daren kamar ance bude idanun ka sai kawai Naji idanuna sun bude amma zaiyi wuya ka gane hakan idan ba har kana kallon fuskata ba ne a lokacin domin bayan bude idanuna danayi banyi kwakkwaran motsi da dan yatsan kafata ba ballantana wanda ya shigo dakin ya zaci idona biyu.
Tabbas bani kadai bane acikin dakin domin babu abunda zai sa ni bude idanu in har ba'a wanine yashigo dakin ba. Nayi shiru bana ko kwakkwaran numfashi kunnuwana na kokarin jin sautin motsi yayinda idanuna ke kokarin sabawa da duhun dake dakin kadan ya rage na saki fitsari a wando saboda fargaba nayi mamaki idan yan fashin nan da suka aikowa da alhaji wasika ne suka karaso BAKIN SHAIDANU.

Dakiku suka shude babu motsin komai sai sautin ganyayyakin bishiyun dake gogayya da yan uwansu a sakamakon iskar dake busawa sannan ne to na ga dakin ya sake duhu ko shakka babu mutum ne tsaye a kofar dakin hakan shiya karawa dakin duhu mutumin yaci gaba da nufo inda gadona yake tuni na daina tunanin komai saina mutuwa tabbas mutuwa ta tazo mutumin ya zauna ahankali abakin gadon babu cikakken haske ballantana na iya gane ko wanene to amma kamshin turaren daya daki hancina shiyasa Naji jikina ya dada bari gwiwowina sukayi sanyi. Hakika na taba jin kamshin turaren awani wuri nayi ta yan maza nace.
WANENE ANAN? ban iya sheda muryar tawa ba nayi shiru saboda jin ba'a amsa min ba daga inda nake kwance ina iya jin hucin wanda ke zaune bakin gadon yana bugun fuskata na kufula sannan na sake cewa da karfi....
Wanene ne anan ne? Ko kurma ne? Idan ka tsaga jikina alokacin bana tsammanin zaka ga ko jan fenti ballantana JINI.

Kada ka daga murya Farisu nice anan kuma inada kunnuwana ba kurma bace.
Wata tattausar murya tace dani. Muryar da bazan taba mantawa da ita bace itace muryar data sha yabona tasha begena itace da tafi kowacce murya zaki acikin duk muryoyin dana sani muryar wacce nake so sannan nake tsoro ce muryar MAYAUDARIYA ce ko ka santa?
SALMA ce...

******* ******* ******** ******* ****************

Salma nakira sunanta muryata a tausashe ban iya tashi daga kan gadon ba ballantana har na zauna daga inda nake kwance ina iya hangen shacin kyakkyawar fuskarta mai haske...

KASHI JAMA'A AYI MIN AFUWA DATA DINA YA KARE MU HADU A WANI LOTON IDAN NAYI SUBSCRIBE....

YARIMA A GANGARIYA
jikan sidi mai jakaMUTUWAR KASKO-13

******* ******* ******** ******* ****************
Salma nakira sunanta muryata a tausashe ban iya tashi daga kan gadon ba ballantana har na zauna daga inda nake kwance ina iya hangen shacin kyakkyawar fuskarta mai haske...
Farisu ta kirani cikin kakkausar murya da har izuwa lokacin ban taba imani d cewa Salma zata iya yin amfani da muryar akaina ba.
Me ya kawo ki nan? Abinda yakawo ni shine ina shawartar ka da gobe idan Allah ya kaimu ka tattara naka ya naka kabar gidan nan tun da sauran rabonka aduniya. Ta danyi shiru tana dubana ba karamar kaduwa nayi danaji abinda take fadi ba.
Menene dalili Salma?
Dalili shine banga amfanin zama da wanda ke kokarin kawo cikas ga rayuwata ba na lura da cewa tun ranar dana fara haduwa dakai ban sake haduwa da farin ciki ba sai bacin zuciya na zubar da kimata amatsayina na 'ya mace na kaunar ka da zuciya daya a tsammanina zaka aure ni domin ba'a san da ace ka aureni toh danayi sallama kenan da duk wani bakin cikin rayuwa domin tunda na tashi arayuwata ban taba shafe shekaru uku a jere cikin farin ciki ba. Auren ka shi nake tsammanin zai kawo karshen wahalata amma sai kayi kememe ka kini ka wulakanta ni sannan ka watsa min kasa a ido shine sanadiyyar barina garin nan haar tsaron watanni uku daga baya na fahimci muddin inason kaina da kwanciyar hankali toh na fitar dakai daga cikin zuciyata amma abin bakin ciki sai gashi bayan dana gama wahalar sake shiryawa kaina sabuwar rayuwa sai......
Cewa zakiyi bayan kin sake yaudarar wanda kike tunanin zai iya maye gurbin EL'MAHDI sai Kika aure shi da nufin idan ya mutu sai kiyi gadon dukiyar sa kamar yanda kika so kiyiwa mijin ki na baya ko? Na katse ta.
Kana iya fadin duk abunda ka so ni dai abunda nake so dakai shine ka tattara komatsanka kabar gidan nan. Domin bana bukatar ganin ka yadda na tsani mutuwa ta haka na tsani ganin ka domin na lura da cewa zama dakai kamar zama da masifa ne ko nace ANNOBA.
Ban gaskata abunda kunnuwa na ke jiye min ba da'ace wani lokaci daya wuce abaya wani zaice dani Salma zata fada min maganganun nan toh da kuwa bazan sassauta gurin nadashi sarkin makaryatan duniya ba amma sai gashi Salma na fadin abinda ta so.
Zaka bar gidan ko ko bazaka bari ba? Ta tambaya.
Umarni kike bani ko kuwa shawara ce?
Na rama tambayar.
Idan har kana son kanka da arziki
Idan kana son kayi aure ka sami zuri'a
Idan kana son kana son kaci gaba da numfashi abayan kasa.
Toh kana iya kiran kalamaina da umarni.
Idan Kuwa ka gaji da rayuwa toy BISMILLAH. kana iya daukar kalamaina shawara kayi duk abinda ka so saidai ina son ka sani idan har kana da wasu yan kadarori masu amfani toh ina shawaratar ka dakayi rabon gado tun da sauran numfashinka. Ta tashi tsaye sannan ta kunna lantarkin dake dakin.
Dakin ya gauraye da haske Arike a hannunta na hagu bindiga ce yar karama irin wadda matan turawa ke amfani dasu. Nayi mamaki ko Daman abunda ya kaita Turai kenan.
Na dube ta bakina na rawa nace. Ashe tsakanina dake Salma har abin yakai zafin haka?
Ashe dai kana fahimta Farisu toh Gaskiya ina fargabar abin ma yafi haka zafi in har ka wuce gobe agidan nan. Ta kashe wutar duhu mai tsanani ya mamaye dakin ina mamakin in duhun kabari haka yake.......

********* ******** ********** ******* ***********

KASHI NA SHIDAMUTUWAR KASKO-14

Ashe dai kana fahimta Farisu toh Gaskiya ina fargabar abin ma yafi haka zafi in har ka wuce gobe agidan nan. Ta kashe wutar duhu mai tsanani ya mamaye dakin ina mamakin in duhun kabari haka yake.

********* ******** ********** ******* ***********

KASHI NA SHIDA
An tashi da gagarumin hadari aranar tun safe hadarin ke haduwa shi bai baje ba shi kuma bai saki ruwa ba haka hadarin yayi ta yawo tsakanin aradu da walkiya bai tashi sakin ruwa ba sai bayan da aka kammala sallar isha'i sannan ruwa ya barke gami da mummunar iskar dake kokarin yaye rufin dakunan al'umma. Yawan ruwan shi yasa baka ko ganin gabanka idan kana tafiya hakan shi yasa kowa ya sami mafaka ya boye.
Babu kowa aduk fadin titin in ka dauke ni.
Sannan kuma ina iya cewa bayan Nima akwai wasu daban.

Tun sassafe na bar gidan ban tashi dawowa ba sai yanzu ba karamin farin ciki nayi ba da haduwar hadarin domin wannan shi zai bani damar shigewa dakina batareda Salma ta ganni ba. Me yiwuwa tayi zaton Naji tsoro Nabar gidan tun da kuwa tun safe bata ganni ba abinda nake so Daman tayi tunani kenan.
Ada can kafin ta shigo dakina nayi niyyar barin gidan baki daya amma shigowar ta shi ya ruguza min shirin tafiyata kamar yadda bata son ganina haka Nima banason ganinta.
Datayi hakuri nan da washegarin ranar Nabar mata gidan to amma zuwan ta ya karantar dani abubuwa guda biyu.
Menene dalilin dayasa take kokarin gaggawar gami da zumudin korata daga gidan sannan menene dalilin barazana ga rayuwata in har naki barin gidan? Na tabbata wai don kawai bata son ganina bai isa ta takura min haka ba har tayi barazana ga rayuwata ba. Akwai abinda ke shirin faruwa agidan tabbas akwai wani abu acan kasan zuciyata dake gargadina da cewa wani Mummunan al'amari na shirin faruwa agidan toh amma bansan ko menene ba saidai ayanzu kam ina bukatar sanin ko menene wannan shine dalilin dawowa ta saikuma abu na biyu banajin zan iya barin Alhaji batareda nasan karshen yadda zata kata tsakaninsa da shaidanun bakinsa ba.
Yayi min mutunci ya daukeni kamar dansa don haka bai dace na tafi na barshi cikin barazanar wasu mutanen banza ba.

Maigadi ya dubeni cikin mamaki lokacin daya dago kai ya dubeni sharkaf dani duk na jike da ruwa
Daga ina haka Farisu? Kardai kace tun fitar ka ta safe sai yanzu?
Wallahi sai yanzu nace dashi ina murmushin yake.
Ya yangare hakoransa kamar gonar kashi yace
Ai sai ka karasa ka cire jikakkun kayan ko? kada sanyi ya kama ka.
Kaima da gaskiyar ka nace dashi.
Saida safe
Allah ya kaimu ya amsa haryanzu bai daina yangare hakoran ba wai shi a tunaninsa da murmushi yake.

******** ****** ******** ********* ****** ********

Bayan na sauya jikakkun tufafin dake jikina da busassun sai na bi lafiyar gado har na kwanta saina tuna da abinda yafaru a daren jiya don haka saina tashi na nufi kofar dakin na janyo ta nasa makulli na rufe sannan na koma na kwanta. Bakajin motsin komai sai rurin iskar dake fatali da ruwan saman dake zuba daga sararin samaniyar Subhanahu Wata'ala haryanzu keta ruwan ake kamar baza'a daina ba kai kace bakin teku aka jirkito ake shekowa ba'a dade ba nafara tunanin abinda ya dace nayi idan gari ya waye shin guduwa zan sake yi cikin gari sai dare yayi na dawo kokuwa zuwa zanyi na sanar da Alhaji Sabi'u halin da ake ciki nayi sauri na kawar da shawarar daga cikin zuciyata aduk lokacin da tunanin hakan yafado sai kuma tunanin karamar bindigarta gamida abinda tace ya darsu azuciyata.
INA FARGABAR ABIN YAFI HAKA ZAFI FARISU.
Na tuna da abinda tace ahaka barci ya sace ni batareda na kai koda rabin tunanin dana shirya yi ba.

*** *** *** *** *** *** *** **** *** *** *** *** ****

Ana kwankwasa kofar idanuna suka bude lokaci guda na tashi zaune na kasa kunne ina sauraro. Shiru ban sake jin komai ba. haryanzu ana sheka ruwan kamar ma alokacin aka fara nafara tunanin ko kuwa kunnena ne keyi min gizo babu mamaki ma rugugin iskar ruwan Naji na ke tsamma..... Aka sake kwankwasa kofar.........MUTUWAR KASKO-15

*** *** *** *** *** *** *** **** *** *** *** *** ****

Ana kwankwasa kofar idanuna suka bude lokaci guda na tashi zaune na kasa kunne ina sauraro. Shiru ban sake jin komai ba haryanzu ana sheka ruwan kamar ma alokacin aka fara nafara tunanin ki kuwa kunnena ne keyi min gizo babu mamaki ma rugugin iskar ruwan Naji na ke tsamma..... Aka sake kwankwasa kofar dakina a tausashe kai kace wanda ke kwankwasa kofar baya cin abinci. Wanene ke kwankwasa kofar?
Na tambayi kaina nasan nasan dai ba Salma bace domin tabbas nasan yanzu tayi imani da cewa tuni na bar gidan to idan ba ita bace wanene ne?
Maigadi? Kwarai kuwa babu makawa Shine to in kuwa shine me zai sa shi baro gidansa yazo dakina cikin talatainin dare? Karfe biyu da minti daya da yan dakiku agogon bangon ya nuna. Nayi shiru ina tunani. Aka sake kwankwasawa akaro na uku nayi kwafa kai wannan akwai sakaran Maigadi wallahi haka kawai ka bari gidanka kazo ka gallabe ni da kwankwashe kwankwashen banza.
Na nufi kofar dakin a fusace na bude da nufin zan ganshi yana yangare hakora. Ina budewa saina ce
Kai don Allah ka rabu dani haka kawai kazo ka dami mutane wacce uwa kake..... Maganar ta makale a fatar bakina ban iya karasata ba domin wanda ke kofar dakin ba mai gadin bane wani dan siriri ne mai siffar aljanu kansa yasha sal sal yana kyalli kamar madubi kafar dogon Wandon dake jikinsa daya tafi daya tsayi sanye yake da bakar riga suwaita a kirjin sa an rubuta cikin harshen turanci. THE DEVIL. babu KO tantama shedanun bakin alhaji ne suka bayyana nayi mamakin ki su nawa ne awaje.
Muna da yawa. Yace dani cikin shakakkiyar murya murya. Hannun bindigar na kokarin sakin harsashi kai tsaye izuwa tumbina bantaba kaduwa irin ta ranar ba.

Kai ni dakin alhaji yace dani
Idan Kuma ka sake kayi wani kwakkwaran motsi toh shine zai zamo motsin ka na biyun karshe aduniya domin faduwar ka kasa itace zata zamo motsin ka na karshe.
Na shige gaba babu musu muka nufi dakin alhaji sabiu ruwan saman da ake tafkawa ya rufe min idanu da kyar nake ganin gabana kuma banida ikon da zansa hannu na goge fuskata domin yin hakan kamar wasa ne da rayuwata tun kafin mu karasa dakin suka rinka fitowa daya bayan daya ta cikin duhun daren kamar aljanu ko wannen su sanye da bakaken kaya kamar ifritai tun suna su biyu hat suka zama su shida sannan ba'a dade ba wasu mutum uku suka bullo daga cikin duhun daren muka zama mu goma in ka hada da lissafinka harda ni.

Kafin na tura kofar dakin sai tunanin Salma ya fado min nayi tunanin ko tana ina yanzu sainaji ko kusa ko alama bana son wani abu ya sami Salma haushin kaina da kaina ya kamani shin haryanzu ina son Salma ne duk da abinda tayi min?
Na bude kofar dakin ahankali muka shiga tun kafin mu shiga Naji tsinin hancin bindigogi uku sun dunguri kuguna lokaci guda sannan wata shakakkiyar murya tace dani.
Kunna mana wutar dakin muryar sau daya take bada umarni bata kuma maimaita abinda ta fadi da farko jikina na rawa na lalubi makunnar lantarkin na kunna dakin ya gauraye da haske.
Yana kwance akan gadon cikin kwanciyar hankali yana barci a tsammanina zanga Salma a kusa dashi kwance amma maimakon hakan sai gashi shi kadai.
Na dubi kofar dakin Salma wacce ke fuskantar dakin alhaji kai tsaye sannan nayi mamakin in Salma barci take kokuwa idanunta biyu atake agurin na sami kaina ina mai addu'ar Allah yasa tayi zamanta aciki idan idon ta biyu.

Mutanen tara suka dubi mutumin daya dake kan gado kwance baya ko motsi sai rigar sa dake sama da kasa a sakamakon numfashin dayake. Sannan ne to dan siririn daya fara ritsa ni ya mai da bindigarsa aljihu nayi ajiyar zuciya ganin ya maida bindigar aljihu lokaci guda kuma sai sauran suka zazzaro tasu bindigogin suka yi saitina da ita.
Idan ya motsa kuyi ta harbinsa saiya zama kasa ya umarce su cikin shakakkiyar murya........MUTUWAR KASKO-16

Sai sauran suka zazzaro tasu bindigogin suka yi saitina da ita.
Idan ya motsa kuyi ta harbinsa saiya zama kasa ya umarce su cikin shakakkiyar murya........
Sannan dan siririn mutumin ya fice daga dakin bayan wasu yan mintuna yadawo Ya koma gefe ya kame ga mamakina haryanzu alhaji bai farka ba
Kofar dakin ta sake budewa ahankali kamar wadda dan karamin yaro ke turo ta wani jibgegen mutun ya shigo dakin. Da farko sai kayi zaton giwo ce ta mike tsaye rigar dake jikinsa na barazanar darewa saboda ƙiba haka ma Wandonsa abun mamaki kansa dan kankani kamar gayan fura idanunsa kanana saidai kuma kunnuwansa ne faka faka kamar murfin randa.
Yana dauke da lema ta ruwa wacce bana tsammanin zata kare rabin jikinsa da ruwan da ake ketawa nayi mamakin abinda ya hanashi sayen babbar Lema maimakon karama abin dayasa yawun bakina kafewa shine a rike a hannunsa na dama zungureriyar wuka ce tana sheki na dade banga wuka mai tsawon ta ba.

Adaidai lokacin ne to alhaji sabiu ya farka agigice mutanen goma suka dube shi suna murmushi.
Nasan kana tsammanin zuwan mu ko? Katon yace.
To gamu mun zo kashe ka muke so muyi bama bukatar komai.
Don Allah ku min rai alhaji sabiu ya roke su muryarsa

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

1 Comments On MUTUWAR KASKO
avatar
mahamane-noura

1 year ago

Reply

Oui

Please Login or Register in order to submit comment