Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rabi na dare kusan sa'a'o'insu goma sha hudu da barin gidan kenan tun safe kimanin goma saura yan mintuna.
Na sake kara fuskata ajikin labulen dakin naci gaba da ganin barayin a tsatstsaye tun safe da suka barni agidan banyi barci ba zuciyata cike da tunanin abinda zai kasance da Salma bansan abin dayasa ba haka kawai sainaji ina fargabar kada su kashe Salma. Na tuna irin makircin da ta kulla min nakuma tuna umarnin data bayar na ajefa ni cikin rijiya gaba dubu amma duk wannan tunanin bai hanani jin fargabar kada su kashe Salma ba.
Wani mummunan tunani yafado zuciyata yanzu misali idan Salma ta ki bin umarnin su kamar yadda suke tsammani fa idan yanzu tace dasu bazata ba da cek din ba fa? Yaya zasuyi? Cikin fargaba gami da zazzafan gumin daya kwararo tun daga wuyana har izuwa gadon bayana sai amsar abinda zasuyi ta zuwa zuciyata kai tsaye. Tabbas kashe ta zasuyi su kwashi abinda suka samu suyi gaba.

Anya kuwa zai yiwu inaji ina gani akashe Salma? Duk da makircin data kulla min duk da cin amanata datayi bazan manta da yan ranakun farin cikin da suka shude mana abaya ba. na tuna sa'adda Salma ta dafa hannuna tana cewa.
BAZAKA FADA MIN SUNAN NAKA BA?
Na Tuna sa'adda aka yanke min hukuncin daurin rai da rai agidan maza....
Wayyo Allah na shiga uku.
Na tuna irin kukan datayi dakuma irin kaunar data nuna min dakuma kulawar data nuna akaina lokacin da aka sallamo ni daga gidan maza ita kadai ce taje ta tare ni.

Lokacin da tunanina ya zurfafa sainaji zuciyata ta karaya tausayinta ya kamani duk kuwa da cewa ina tattare da masaniyar mummunan abinda ta aikata amma tabbas kam nasan in har akwai abinda zan iya yi zanyi domin na tserar da Salma... Yanzu menene abun yi na tambayi kaina......

MASU KARATU KU BASHI SHAWARAMUTUWAR KASKO-22

Lokacin da tunanina ya zurfafa sainaji zuciyata ta karaya tausayinta ya kamani duk kuwa da cewa ina tattare da masaniyar mummunan abinda ta aikata amma tabbas kam nasan in har akwai abinda zan iya yi zanyi domin na tserar da Salma..
Yanzu menene abun yi na tambayi kaina Zuciyata tafara laluben mafita nasan dai zancen ace zan tsere daga gidan bai yiwuwa to amma da'ace zan sami talfon gumi.
Ya karyo min tabbas da zan sami talfon shine mafita ni yau ina zan samu talfon na tserar da rayuwar Salma?

Motsin danaji a kofar dakin shiyasa na juyo firgigit Nabar leken tagar dakin lallai hankali shike gani ba idanu ba. Dulmiya cikin kogin tunanin Salma shiya mai dani abunda nake leke gashi dai ina leken amma dayake zuciyata ta dulmiya bansan Sa'adda suka bar farfajiyar gidan ba har suka zo kofar dakin sai bayan da suka kwankwasa kofar ne hankalina ya dawo jikina sannan kuma idanuna suka ga wayam babu kowa a farfajiyar gidan sai bakar motar tana sheki cikin hasken fitilu na juyo cikin sauri na nufi kan yar yakunanniyar shimfidar da sukayi min a daben dakin tun kafin nagama zama kofar dakin ta bude.

Menene abun gaggawa ai mun ga duhun idanun ka ta jikin labulen me kake leke munafiki.?
MAI dogon gemun ne ke magana fuskar sa a murtuke kamar fuskar roba.
Me kake leke munafuki yasake daka min tsawa
Da... Dama ina.... Na kasa fadin abunda nake son fada to abin ka da mara gaskiya.
Kayi ahankali wannan shine gargadi na karshe da zanyi maka kayi fatan idan mun tashi kashe ka to mu kashe ka ta hanya mai saukin mutuwa ba wacce zaka sha wuya ba wannan shine kawai saukin da nakejin zan iya yi maka.

Dakin yayi shiru bakajin motsin komai sai hucin numfashin kartin da suke bayansa.
Zamu bar kofar dakin a bude idan kaso kana iya guduwa duk inda kake so daga nan har BIRNIN SIN.
Saidai kuma kada ka zargi kowa in ka tsinci wasashshiyar wuka acikin ruwan cikin ka haka nan kada ka zargi alburushin bindigata in ya sami matsugunni a kokon kanka.

Kayi duk abinda kaso Farisu ka zagaya duk inda kake so a farfajiyar gidan nan akwai abinci kala kala da abubuwan sha na zaki kai har dana maye ma Idan kana so wannan itace alfarma ta karshe da zan iya yi maka domin ina tabbatar maka da cewar babu mamaki sa'o'inka aduniya sun zo karshe babu mamaki gobe kamar yanzu kana KIYAMA.

Ya danyi shiru yana dubana babu kiftawa tamkar idanun mayunwacin kure akan nama.
Don haka ina shawartar ka da ka more rayuwar ka daga nan zuwa karfe uku da rabi na dare zamu fita bakuma zamu dade ba zamu dawo saidai ka tabbata da mun dawo zamu tafi ga Salma Kodai ta amince kokuma idan taki karbar shirin mu itama ta bi hanyar da mijinta yabi.

Yayi murmushin mugunta sannan yace Kanada CIKAKKIYAR sa'a guda daya tak kayi duk abinda kaso kafin mu dawo ka morewa rayuwar ka morewar karshe gobe warhaka saidai ko danka idan kana dashi.
Mu tafi Ya buga musu tsawa suka fice sumu sumu daga dakin kamar yadda suka shigo sannan shikuma ya bisu daga baya koda yakai ga kofar dakin saiya juyo yace.

Ka zargi kanka Farisu neman KACI BULUS da MUTUWAR ZUCIYA duk shi ya jefa ka cikin masifar da kake ciki.

Kafin nagama fahimtar abinda yake nufi Tuni yabace daga kofar dakin yabar kofar a bude
Kamar yadda yafada to amma na tabbata akwai mai gadina a kofar gidan.

Idan har akwai abinda zan iya yi nace da kaina to babu wanda ya isa ya halaka Salma agabana saidai ko ayi MUTUWAR KASKO nida ita dasu gabaki daya ni kaina ban iya gaskata abinda nace ba.

KASHI NA TARA

Ahankali cikin sanda naci gaba da bin dakunan gidan daya bayan daya ina binciken su idan ka tsaga jikina bazaka iya samun jini a loakcin ba saboda tsoro ko takarda na taka sai tsigar jikina tayi Yarrrr.MUTUWAR KASKO-23

KASHI NA TARA

Ahankali cikin sanda naci gaba da bin dakunan gidan daya bayan daya ina binciken su idan ka tsaga jikina bazaka iya samun jini a lokacin ba saboda tsoro ko takarda na taka sai tsigar jikina tayi Yarrrr.

Ba bayan tande tande ko shaye shaye nake nema ba ko ban fada maka ba kasan abunda zan nema KAN Talfon. banyi tsammanin zan samu ba domin dakin farko dana shiga babu komai acikinsa sai manyan kujerun alfarma guda biyar wadanda sukayi wa kansu matsugunni akan tattausan kilishin tsakar dakin akwa katon firji daga kuryar dakin na bude cikinsa domin na gaskata kona karyata abunda suka fada tabbas firjin cike yake da kayan marmari na ciye ciye da shaye shaye to amma basu bane a gabana.
Sauran dakunan duk kusan kamar su daya in ka dauke yan Bambance Bambance na launin kujerun dakin cikin sanda na fice daga dakin na nufi daki na karshe zuciyata tagama karaya domin nasan zaiyi wuya na sami kan talfon wanda itace hanya ta karshe da nake tsammani zan iya tserar da rayuwar Salma.

CIKIN sanyin gwiwa na tura kofar dakin na gaba kamar sauran itama bude take suka barta na lalubi makunnar lantarkin sannan gabana na faduwa saina kunna babu wani sabon abu a dakin sabanin na bayansa duk irin su daya saidai anfi ƙawata shi domin bangon dakin a lullube yake da takarda mai dauke da kyawawan hotunan furanni da fulawowi dakuma tsuntsaye kai har ma da malam buda mana littafi to amma duk kawarsa da daddadan kamshin dake bugun hancina duk abanza tunda dai ban sami biyan bukata ba.

Naci gaba da lalube lalube cikin dakin babu komai cikin dakin sai kayan karau masu ban sha'awar gaske hakan shi ya tabbatar min da cewa wannan shine dakin ogan su. Akwai tebur dan ƙarami a tsakar dakin wanda ke lullube da farin kyalle tun daga kan teburin har kasa sannan akan teburin akwai dan madaidaicin akwatin gilashi mai dauke da ruwa da yan kifaye suna wasa aciki ga mamakina saina ga kwalin taba (Rothmans) akan akwatin gilashin na yi mamakin abunda yasa aka rasa inda za'a ajiye kwalin taba sai kan abin. Na matsa kusa da teburin sannan na dauki kwalin tabar na bude karan sigari uku ne aciki na jefar dashi cikin fushi na duba na sake dubawa babu alamar kan talfon idan kuwa har za'a samu kan talfon to anan ne yakamata asamu na durkusa agaban gilashin cikin bakin ciki.

Babu makawa rayuwar mu tazo karshe ni da Salma hakika bana zolayar kaina na san haryanzu zuciyata na nan da Masifaffen ra'ayinta na kaunar Salma. Na tuna duk makircin datayi min amma gashi ni ina kokarin tserar da rayuwar ta nayi mamakin kaina anya kuwa akwai ranar da zan daina kaunar Salma. Ga mamakina sainaji DANDANON gishiri gishiri abakina na dago kaina sainaji gaban rigata ta jike da hawaye bazan iya ganin kisan Salma kiri kiri agabana ba domin nayi imani cewa babu yadda za'ayi Salma ta basu cek din duk kudin data mallaka wai don gudun kada na bada shaida akanta ni nasan ita tasan ina kaunar ta sannan tana kuma da tabbacin cewa babu yadda za'ayi na bada shaidar da zata dora laifin kisan kai akanta. Idan kuwa hakane to tabbas bazata basu ba idan kuwa taki to su kuwa babu makawa kasheta zasuyi.
Na mike tsaye cikin kunan rai sannan na nufi kofar dakin.

To adaidai lokacin ne naji Naji kafata ta sarke da wani dan siririn abu mai kamar igiya nayi tsalle gefe guda cikin fargaba sannan na dubi kasan kafata yar siririyar wayace fata ta ziraro tun tun daga karkashin teburin nan mai dauke da gilashi har zuwa karkashin kujerar da take fuskantar teburin yawun bakina ya kafe.

Ahankali saina sunkuya na dauki wayar a tafin hannuna sannan naci gaba da bin inda ta ziraro har zuwa karkashin teburin. Gabana yana dakan uku uku na bude dan kyallen.
Yawun dake bakina ya karasa kafewa karaf tamkar kogi lokacin rani. A zaune a karkashin teburin cikin jin dadi da annashuwar ganin na walwala wajen neman kan talfon din ne ja ja wur dashi kamar ruwan soborodo.

Jikina na rawa nafara dandanna lambobin wayar Salma banko damu da na zaro shi daga karkashin teburin ba domin gudun kada su dawo Su gane nayi amfani dashi domin nasan tabbas sunyi tunanin haka don haka suka boye shi saidai kuma tuni sunyi kuskuren da bazasu taba gyarawa ba.

Na kara kan talfon din a kunnena ina sauraro kusan minti daya yana ta ruri acan daya bangaren amma ba'a amsa ba adaidai lokacin da murya ta take neman komawa ciki sainaji ance wanene ne haka?
Duk dayake akwai alamun barci acikin murya amma muryar da bazan taba mantawa ba ce muryar dana ke jin dadinta cikin kunnena tamkar sarewa babu wani mai muryar nan aduniya sai SALMA.

****** ** ****** ******** ******** *******

WAKE MAGANA?
Baki gane ni ba Salma? Naji ta rike numfashinta acan daya bangaren sannan wani dan fatalwan murmushin farin ciki ya subuce min jin cewa daga jin muryata har Salma ta gane ni
Farisu ne?
Tabbas nine in kuwa har bani bane to wani ne mai kama dani.

Daga ina kake magana? Ta tambaya batareda ta kula da surutaina ba.

Daga rijiya GABA DUBUMUTUWAR KASKO-24

Daga ina kake magana? Ta tambaya batareda ta kula da surutaina ba.
Daga rijiya GABA DUBU

Na amsa mata kai tsaye.
Kaga Farisu don Allah menene?

Saurara dakyau Salma abinda yayi miki karanci ne ni nake son nayi miki

Menene yayi min karanci..?

MUTUNCI mana. saurara don Allah kada kada ki katse ni domin Allah ne kawai yasan cikin hadarin da nake yanzu DAKYAR na iya gano tarfon din.

To fadi mana Farisu menene.?

Salma inason ki yi kokari yanzun nan batareda bata wani lokaci ba ki fice daga gidan nan ki boye kanki domin ina tabbatar miki da cewa kowanne lokaci daga yanzu zaki ganmu tare tare da yan fashin nan da kika baiwa umarni kashe ni to basu kashe ni din ba haryanzu. saidai kuma zasu yi kokarin jan ra'ayin ki akan ki basu cek din duk kudin da kika mallaka idan kinki ki basu su kashe ki su kashe ni Hakama idan kin basu ni dai ban tsira ba to amma ta ni mai sauki ne in har zaki tsira ni babu komai.

Ga mamakina sainaji Salma na sheshshekar kuka acan daya bangaren

Kinga ba kuka zakiyi ba bakida wai sauran lokaci kedai kiyi kokari ki gudu kafin mu zo nace da ita cikin ƙaraji.

Farisu... Kana nufin kace duk bayan abunda nayi maka haryanzu kana KAUNATA?
Kuka ya shake muryarta.

Kinga Salma nace dake bakida lokaci kowanne loakci daga yanzu suna iya zuwa mu tafi me yiwuwa kuma su canza shawara su zo miki su kadai duk wannan nafada ne domin na tsorata ta tabar gidan amma maimakon hakan saita ce.

Farisu.. Wal.. Wallahi bantaba zaton Zakayi min haka ba na dauka bayan abunda nayi maka babu wani abu tsakanin mu sai tsana da kiyayya.

Salma zaki gudu ko bazaki gudu ba? Nace cikin ƙaraji.

Bazan gudu ba Farisu tace dani kai tsaye.

Na rike numfashi cikin kaduwa hannuna kankame da ka talfon din.
Me kike nufi?

Abinda nake nufi shine bazan iya gudu Nabar mutumin da yafi kowa kaunata aduniya ba.

Kada ki damu dani kedai ki gudu Salma.

Bazan iya gudun na bari akashe ka ba Farisu gara su kashe mu tare ballantana ma nasan yanda zanyi dasu.

Yadda zakiyi dasu kamar yaya..?

Kada ka damu kaidai kawai idan sunce ku taho kabisu ko taho din kada kaji fargabar komai zansa masu gadina su bar gidan yanzun nan kafin Kuzo.

Salma kanki daya kuwa idan kin kore su to suwa kike tsammanin zasu tseratar dake?

Nace dakai kada ka damu kaidai ka biyo su ku taho.

Ke Salma nidai nayi abunda zan iyayi idan wani abu yafaru to ki zargi kanki amma nidai da zaki bi shawa....

Idan har ba kunnuwa na ke jiye min shirme ba naso Naji sautin injin mota.

Salma ki gudu wannan shine gargadi na karshe..
Na jefar da kan talfon din kan uwar goyonsa sannan na janyo farin kyallen dake kan teburin kamar yadda yake alokacin dana same shi sannan cikin gudu gudu da sassarfa na fice daga dakin na nufi dakina tun kafin na karasa rufe kofar dakin. Dunkuleliyar bakar Jeep din ta silalo farfajiyar gidan kamar yadda kulba ke bin cikin karmami.
Kamar dazu yanzun ma su biyar suka shigo dakin mai dogon gemun agaba su kuma sauran na biye dashi abaya kamar inuwa.

Menene kuma abin gudu munafiki bani nace ka zagaya kaci duk abunda kake so ba ko wani Munafurcin kake kullawa?

Numfashina ya dauke na dakika guda Allah yasa dai bai gane talfon nayi ba. Nayi shiru bance dashi komai ba kaina a sunkuye ina duban daben dakin ina sauraron wacce zata fito daga bakinsa ga mamakina sainaji yace.

Ina fatan ka cika tumbin ka cikawar danake tabbatar maka da cewa itace cika tumbin ka na karshe aduniya domin gobe warhaka kayi sallama da duniya babu mamaki ma kafin asubahin yau.
Yayi shiru na dan lokaci sannan ya dubi agogon dake hannunsa yace saimu tafi ko Farisu lokaci ai ya karaso.

Tun kafin nagama fahimtar kalmomin dayake fada mutun biyu daga cikinsu suka yi yo taku uku uku suka dakumi rigata sukayi waje dani zuwa gindin mota.
Dakyar kafata ke taba kasa nayi mamakin halin da Salma ke ciki a halin yanzu..

KASHI NA GOMA

Banyi tsammanin zamu sami koda kaji a titin birnin sarauniya ba ballantana mutane wadanda Awannan sa'a kusan kowa na can kwance akan gadonsa yana hutar da gangar jikinsa kafin kuma Allah Mahaliccin komai ya sake soko safiya acikin duhun daren.

Karfe uku da yan mintuna muka isa birnin sarauniya. Abin kawai daya bani mamaki shine duk maganganun da jama'a ke ta kururutawa na wai kusan ko waccce sa'a tun daga safiya har zuwa wata safiyar wai akwai yan sanda wadanda ke sintiri akan titunan birnin suna kula da duk wani mai mugun guzuri to amma sabanin hakan lokacin da kuka shiga birnin babu mahaluki daya mai kayan sarki da muka hadu dashi saidai na san babu mamaki me yiwuwa da karfe sha biyu ne muka zo zamu iya samunsu me yiwuwa wannan shine lagon da yan fashin suka samu na sakacin yan sanda dan haka suke amfani da sa'o'in asuba wajen yin Ta'addancinsu.

TUNDA muka baro titin BARON har zuwa kan titin gidan Salma bamu hadu da dansanda daya ba saidai daidaikun karnuka Dakan bimu da dan makararren haushi aduk Sa'adda muka gifta su. Nayi mamakin irin halin da yan fashi zasu shiga da Allah yasa ace karnuka na da ikon rike bindiga kamar mutane....MUTUWAR KASKO-25

TUNDA muka baro titin BARON har zuwa kan titin gidan Salma bamu hadu da dansanda daya ba saidai daidaikun karnuka Dakan bimu da dan makararren haushi aduk Sa'adda muka gifta su. Nayi mamakin irin halin da yan fashi zasu shiga da Allah yasa ace karnuka na da ikon rike bindiga kamar mutane. domin su suna da juriyar zama tsawon dare suna gadin iyayen gidansu.

Wasu daga cikin masu gadin dake kula da gidajen jama'a su kan dago kai ta cikin kofar da suke boye a bayanta su hange mu ayayinda muke wurwuce daruruwan gidajen da suke unguwar Sannan ahankali motar mu ta gama tsayawa.

Kowa daga cikinsu yayiwa bindigarsa gurin zama a cikin tafin hannunsa sannan mutum uku suka fito daga motar suka nufi Tangamemiyar kofar mai kama da kofar gari.
Suka tura kofar ta bude to cikin mamakin ganinta a bude amma a agurina abin ba abun mamaki bane domin Salma ta sanar dani cewa zata ce da masu gadin su bar gidan.
Kirjina sai bugawa yake fat.... fat..... fat....
bansan abunda Salma ke shirin yi ba.

A hanyar mu ta tahowa gidan na ayyana abubuwan danake tsammanin zata iya yi cikin zuciyata amma duk abanza duk abunda na ayyana saina ga bai da wata ma'ana.
Yan ta'addar uku suka shiga cikin gidan suna sanda kamar hawainiya. Sun burge ni ba don komai ba kuwa sai don rashin tsoron da suka nuna yanzu da'ace masu gadi suna nan fa me zai faru da sunada hankali yakamata su yi tunanin me yasa za'a bar kofar katon gida irin wannan babu masu gadi kuma abin a sake dubawa ma shine kofar a bude saidai kuma babu mamaki sun dauka maigadin daya ne me yiwuwa ma tsoho wanda bai dogara da komai ba sai adda da takobi da yan asire asiren da bazasu kare shi daga sharrin bindiga ba ko kuma duka da bulon siminti a tsakiyar ka.

Tabbas ina tsammanin abunda yasa kenan suka shiga gidan babu fargaba domin sun san a mafiya yawan gidajen masu gadin su buzaye ne Tsofaffi wadanda basu iya cutar dasu da komai in har sunada bindiga.

Ba'a dade ba sai kofar gidan ta bude daya daga cikin yan fashin ya leko sannan ya yafito mu da hannu.
Mutane biyun da suka rage suka cakumo ni sannan suka iza ƙeyata muka shiga gidan har yanzu gidan na nan ayadda nasan shi saidai sabanin wancan lokacin wannan sa'ar mafiya yawa daga cikin bangarorin gidan cikin duhu yake mutane ukun na tsaye a tsakar gidan suna muzurai mai dogon gemun ya dubi direban daya tuko mu. Kafin ma yace wani abu direban ya gane ya binda yake nufi.

Dan haka saiya juya cikin gaggawa yanufi kofar gidan ba'a dade ba ya tada motar yashigo da ita farfajiyar gidan sannan yakoma da gudu ya rufe kofar gidan saika rantse da Allah babu kowa aciki babu wanda zai taba tsammanin akwai yan fashi aciki.

MAI dogon gemun ya iza ƙeyata muka nufi babban dakin shakatawar marigayi alhaji sabiu suhununu zuciyata tayi min kunci lokacin dana tuna irin mummunan karshen da matarsa Salma ta aikata masa.

Ya kwankwasa kofar kamar wanda ke tsammanin za'a amsa sannan cikin kwanciyar hankali da kuma tabbacin babu abunda zai iya faruwa koda ya shiga dakin kai tsaye saiya tura kofar falon ya shiga mutanen hudu dakuma ni mai bin shi abaya kamar masu fareti ko wannen su da bindigarsa ahannu muka shiga dakin saidai kuma baka iya ganin koda tafin hannun ka saboda duhu in ka dauke dan siririn hasken farin watan daya yayiwa kansa hanya ta cikin yar siririyar kofar ta daya daga cikin labulayen tagar dakin da yayi kuskuren bari.

Dakin kamar kabari yake saboda duhu daya daga cikin yan fashin ya dasa hancin bindigarsa a kuguna yayinda sauran suka fara laluben makunnar lantarkin dake dakin babu zato babu tsammani sai haske ya gauraye dakin sannan gaba dayan mukayi turus.
Bani ba hatta yan fashin saida ta sa su kaduwa tana zaune cikin luntsumemiyar kushin din datake fuskantar kofar dakin. Sanye take da doguwar riga fari irin ta bacci kanta babu dan kwali kunnuwanta babu dan kunne Hakama hannayen ta babu awarwarro ballantana kayi tsammanin ko zaka sami takalmi a kyakkyawan sawun ta SALMA CE.

Tayi murmushi yayinda ta daga hannunta sama tace dasu.
Kuyi ahankali yan mazan jiya shin har yakin duniyar na uku yazo ne na ganku haka da bindigogi kamar mafarauta.?

Mai dogon gemun yayi musu alama da hannunsa kafin kiftawa da bismillah sun saye bindigogin su acikin aljifan bakaken kayansu shi kadai ne ke rike da tasa bindigar sannan yace cikin muryarsa mai razanarwa.

Inafatan zaki gafarce mu yar kyakkyawa domin ziyarta ki kai tsaye cikin talatainin dare babu sallama saidai kuma kamar Daman kinsan da zuwan mu Salma tayi murmushi sannan tace.

Ina cikin bacci sai nayi mafarki akace dani wai gaku nan zuwa shine na zauna anan ina jiran zuwan ku tayi murmushi.

Amma kuma cikin duhu? Ya tambaye ta cikin gatse yana dariyar mugunta.

Gani nayi a mafarkin an nuna min ku cikin bakaken kaya shine Nima kuma naga bai kamata ba na tarbi masu bakaken kaya cikin haske kokuwa me ka gani DAN MUMMUNA.?

Hirar tasu kamar wasan kwaikwayo saidai jin abunda ta fada shi ya sauya launin fuskarsa daga baki zuwa launin toka toka ya juya a fusace ya dubeni sannan ya sa hannu ya mangare ni saida nayi juyi a sararin samaniya kafin nayi zaman yan bori a tsakiyar teburin cin abincin dake tsakar dakin.

Jini ya fallatsa daga bakina na kwanta rub da ciki ina murkususu kamar mai nakuda.

DAGA YAU KA SAKE MUNAFURTA TA.
Yace dani sannan ya juya ga Salma cikin fushi yace
Acikin mafarkin da kikayi ba'a nuna miki ina harbin kokon kanki da bindigata ba?

KO kusa ba'a nuna min hakan ba Salma ta amsa kai tsaye
Saidai an nuna min kai da kuma yaranka daure ajikin durarruka cike da yashi wai sojoji suna koyon harbi akan ku.

Ke Salma banason sakarcin banza ba surutu ne yakawo ni ba.

To me ya kawo ka?

Zancen kudina

To bani da loakcin ka

Tun kafin tagama fadi kofar ta bude yan fashin suka juya loakci guda suka sami kansu suna masu fuskantar hancin bindigogin masu bakaken kaya Sama da ashirin.

Kada ku motsa wata murya mai kama data aradu tace dasu.

Bindigar dake hannun mai dogon gemun ta subuce ta fado kasa kyangaran kamar an saki KWANDALA AKAN DABEN SIMINTI.

****** ****** ******* ******* ***********

WASH NA GAJI DA RUBUTU WAYE ZAI TAYANI ?MUTUWAR KASKO-26

Kada ku motsa wata murya mai kama data aradu tace dasu.

Bindigar dake hannun mai dogon gemun ta subuce ta fado kasa kyangaran kamar an saki KWANDALA AKAN DABEN SIMINTI.

****** ****** ******* ******* ***********

Hancina da bakina sun daina tsiyayar da jini. Na dago kaina ahankali adaidai lokacin da daya daga cikin yan sandan ya tallafo ni ahankali sannan yayi min jagora zuwa kan daya daga cikin kujerun dakin ya zaunar dani.

Yan ta'addar biyar sun jeru ajikin bango kamar kadangaru hannuwansu a sama sannan kirjin kowanne daya daga cikinsu yana fuskantar sama da hancin bindiga biyu.
Dansandan ya bisu daya bayan daya ya bubbuga musu ankwa sannan ya juyo ahankali ya dubeni yayi murmushi sai yanzu na gane shi dan sandan nan ne da suka ceci Salma daga hannun su IJAKALA lokacin da suka same mu tare a dakinta. Yayi Min murmushi kyakkyawan gashin bakinsa ya baje akan fatar bakinsa yana sheki

Wannan shine kanin naki da kike fade? Ya nuna ni da yatsa Salma ta gyada kai. Ka cika saka kanka a rigima kanin Salma haka ma fa wancan lokacin DAKYAR muka ceci rayuwar ka daga hannun ire iren wadannan kayi ahankali watarana bazaka tsira ba kaji ko?
Kafin nagama nazarin abinda yace tuni ya fice daga dakin kafin ya fice daga dakin sai da ya dagawa salma hannu.
Nagode TAJUDDEEN

TAJUDDEEN wannan shine karo na farko da nafara sanin sunansa abinda ke damuna ga dukkan al'amarin nan shine ga alamu tajuddeen yasan gaskiyar duk abunda ke faruwa domin duk sakarcinsa zaiyi wuya ace dansanda kamar sa ya yarda da tatsuniyar Salma har sau biyu wai ni kanin ta ne kuma aduk lokacin baiyi wata kwakkwaran tambaya ba da zata nuna kwazonsa akan aikin

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

1 Comments On MUTUWAR KASKO
avatar
mahamane-noura

1 year ago

Reply

Oui

Please Login or Register in order to submit comment