Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

 BIRNIN SARAUNIYA...

VISIT www.aihausanovels.com.ng For More Novel.

AIHAUSANOVELS is website consists of hausa novels note, the reason of launching this site is to Entetaint, Motivate and Educate our readers.



We provided hausa novels of many type, Such Adventure, love, romance, fiction, non-fiction, mystry, fantasy, action e.t.c from hausa Authors



We provided a new and old novels both softcopy and hardcopy from our Author with thier permission.



AIHAUSANOVELS shafin yanar gizo ne wanda yake ɗauke da littattafan hausa, dalilin bude wannan shafin shine domin Kayatar masu karatu da kuma ilimantar da su.



Mun samar da littattafan hausa na nau'uka daban-daban, kama daga littafin, soyayya, tatsuniya, almara, Hikayoyi, gyara kayanki (yadda mata zasu kula da kansu a gidan mijinsu) da dai sauransu, daga Marubutan hausa.


TABA KA LASHE

KWANA DAYA MILIYAN DAYA!
Kwana Uku kawai take bukata ya aure ta saiya sake ta takoma gidan tsohon mijinta na da.

Ko wane kwana daya miliyan daya zan baka tace dashi.

Farisu bai yarda da auren kisan wuta ba to amma kuma can cikin zuciyarsa naira miliyan uku na nan tana linkaya.....

BIRNIN SARAUNIYA
NAZIR ADAM SALIH
[3/16, 4:50 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA - 01

Kinsan fa auren da zamuyi auren kisan wuta haramun ne kuma mutumin da kike son ki sake aura bayan kin aure ni amanarsa zakici kina tsammanin da yasan abunda yake zuciyar ki yanzu zai yarda ya baki koda kwandala ce?
Abin duniya fa ba abakin komai yake ba kiji tsoron ubangiji SALMA kada duniya ta......

"Amincewar ka nake bukata ba wa'azin ka ba idan ka yarda kowanne kwana daya zan baka naira miliyan daya.
Miliyan uku kenan kwana uku saika sake ni.... Zo nan ka gani
Ta bude but din motar buhuna biyu cike suke da yan wazobiya sababbi fil.

Zanyi shawara nace da ita duk fa da wa'azin danayi mata abaya yanzu Na manta dashi......

BIRNIN SARAUNIYA
Copyright © Nazir Adam Salih - 1998

Hakkin mallaka (M) Nazir Adam Salih - 1998

KAMNAS PUBLISHERS - 1998

An Buga shi a JET AGE PRINTERS

TARIHIN BUGUNSA.
An fara buga shi a Jet Age - 1998

A KULA
Wannan littafi kagagge ne an rubuta shine badon cin zarafin kowa ba sai don nishadi dakuma gargadi ga al'ummar da ke jin yaren hausa akan irin yadda zamani ya rikice arayuwa.

Tsarin rubutu a na'ura mai kwakwalwa:
URGENT COMPUTERS
NO=497 KASUWAR KURMI
BIA YAN GURASA JAKARA KANO.

Wanda ya shirya.
TIJJANI IBRAHIM KURAWA - BAHAGOH RUWA

BIRNIN SARAUNIYA
NA
NAZIRU ADAMU SALIHU (NAS)

(NAS 98)

BABI NA DAYA
Acikin yammacin wata ranar Asabar ne nafara haduwa da ita yammaci ne mai dauke da ni'imtacciyar iska mai ratsa jiki tareda kamshin damina dake nuni da cewa akowane lokaci daga yanzu ruwa na iya samuwa.
Aduk lokacin da iskar ta busa sai kaji dadi da nishadi maras misaltuwa sun rufe ka hakika muna bukatar sauyi musamman ma idan akayi la'akari da irin zafin da aka zabga a iya kwanakin da suka shude........

YARIMA A. GANGARIYA
(jikan sidi mai jaka)
[3/16, 4:51 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA - 02

Hakika muna bukatar sauyi musamman ma idan akayi la'akari da irin zafin da aka zabga a iya kwanakin da suka shude.
Duk da yake daddadar iskar na busawa ko ina cikin babban titi ne hakan bai hanani gumi ba kodayake ba abin mamaki bane idan akayi la'akari da irin rashin sa'ar data sameni aranar na dubi kayan Marmarin da nake sayarwa wadanda ke gefen titi a gindin bishiya sainaji bakin ciki ya sake rufe ni gumi kuma ya cigaba da keto mini kamar ruwa duk rabin kayan sun lalace musamman ma ayaba duk ta latse ta zama kamar teba sai wani ruwa ruwa ne ke fita ajikinta sannan ne abunda yafaru safiyar ranar yafado mini.

A safiyar ranar an tashi da iska mai karfi wanda a sakamakon haka ne wani katon reshen bishiya ya karye abin tsautsayi saiya fado akan teburin kayan gaba daya ya tintsire wasu daga cikin lemukan suka watsu kan titi motocin suka tattake ayabar kuma ta lallatse daga karshe na tattaro kayan na sake wankewa na shanya ragowar masu kyaun a gefe su kuma lamutsatstsun gefe guda.
Abinda yafi damuna a yanzu shine tun tun safiya har zuwa yanzu banyi cinikin koda naira arba'in ba abin kamar hau innalillahi Wa'inna Ilaihi raji'un abinda na cigaba da cewa kenan acikin zuciyata lokacin dana duba agogona naga karfe hudu na yamma.
Tsoro da fargaba su ka kamani domin bansan abunda zan cewa mai kayan ba idan nakoma wajen sari gobe daman kayan bashi muke dauka idan mun sayar mu biya mu dauki wani to ga shi kuma abinda yafaru ni kuwa nasan ko yanka ni zaiyi saidai ya yanka ni din domin bani da abin biya saidai ko.......
Tunanina ya katse adaidai lokacin dana hango shi ya nufo inda nake ba zato ba tsammani kamar an jefo shi shine mutum na karshe danake tsammanin zan gani agurin. Ya nufo ni yana murmushi mai kayan ne dake bamu bashi.
Assalamu Alaikum
Amin Wa'alaikumussalam..... Bakina ya kasa amsa sallamar abunda ya hanani amsa sallamar shine irin kallon danaga Yayiwa teburin kayan ta yamutse sannan ya dubeni yace ya samu kayan na gansu haka a ratattake kamar garken shanu ya bita kai? Wal..wallahi reshen bishiya ne ya yafado musu nace dashi ina in ina wannan wani abune da bai shafe ni ba yace dani.
Inafatan ka hada min kudin kayana sannan yaci gaba da cewa daman karbar kudina ne yakawo ni saboda an kawo mini wasu kayan masu araha inason sayen su don haka ka ganni anan yanzu ma daga wurin su SALLAU Nake duk sun bani nasu.
Yayi shiru yana duba na nasan abunda yake nufi don haka saina zato cinikin naira arba'in din danayi na tura masa gabansa na juya kaina gefe guda na bata rai.
Menene wannan? Ya tambaye ni. Cinikin danayi ne nace dashi saika jira zuwa gobe idan na sayar na cika maka kudin ka ni na dogara da Allah ya mayar mini da asarar danayi domin nasan babu mamaki sainayi maka ciko.
YA dubeni a fusace sannan yace cikin irin muryar da zaka iya kira bambaro
Ai bamuyi haka dakai ba babu kuma abinda ya shafe ni da asarar dakayi ko kusa bata dameni ba daman ai sai dana gindiya maka sharudda kafin nabaka kayan kasan kuwa acikin sharuddan harda asara ko da faduwa kayi saika biyani kudina.
Yayi shiru na dan lokaci yana mai da numfashinsa fuskarsa ta hada gumi sharkaf kamar ruwa.......
[3/16, 4:52 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA-03

Fuskarsa ta hada gumi sharkaf kamar ruwa.

Dana san haka zata faru da ban baka kayana ba daman saida nace bazan bada kayana ba amma sallau ya takura min nabaka na amince dana baka amma ni daman da ganinka nasan zakayi sakarci in banda shashanci ina kai ina.....
Kada ka zageni na katse masa hanzari domin nafara ggajiya da surutan banza dayake mini idan kudkinsa ne kakeyiwa wannan ihun to ka ceci numfashinka kar ciwon zuciya ya kama ka abanza zan biyaka amma idan na sayar...
Baka isa ba yace dani ko sallau da muka dade dashi muna yin harkar bai isa yayi mini haka ba ban damu asararka ba ni kawai abinda na damu dashi shine kudina.
Yayi shiru na dan wani lokaci muna duban juna yan mitsi mitsin idanunsa sunyi jawur katuwar faddadar fuskarsa mai kama da faifan garmaho ta hadu da gumi har naso takeyi kamar waina dan gajerene kakkaura baki bashida gashin baki bashi kuma da gemu sai dan tsurut din hana karya dayayiwa kansa hanya tsakanin habarsa dakuma fatar bakinsa kamar jela tsatstsewala hancinsa ya hade da fuskarsa amma ya dan bude daga karshe hancin yafi kama da usur fiyeda hancin mutum bakinsa wangameme kamar an datsa masa da gatari idan ba ganin kusa kayi masa ba saika rantse da Allah bashida kunne domin duka girmansa bai wuce fadin kwankwalati ba rigar dake jikinsa ruwan tsanwa-tsanwa ce wandonsa kuma launin fatar jakine takalminsa kamar kwale kwale tsohuwar hular dake kansa ita ta tuna mini da wani tsohon kakana daya rasu shekaru kadan kafin al'amarin yafaru zaren dake dinkin hular ya ratattake ya kode yakuma jeme har wahalar duniya tasa shi yafara zazzarewa da kansa. Ahaka mutumin ya tsaya agabana yana dubana da mummunanr fuskarsa.
FARISA ya kira sunana akaro na farko nikuwa ko sunansa ban iya tunawa saboda yau kwana goma kenan da fara karbar kaya agurinsa. Kasan duk yanda za'ayi ka hada mini kudina daga nan zuwa gobe yaci gaba da cewa idan kuma kaki to Wallahi hukuma ta karbar mini abu guda ne baka gane ba farisu shine banida mutunci akan harkar kudi zan jiraka gobe karfe bakwai na safe idan bakazo mini da kudina ba to karfe takwas a folis siteshon zatayi maka yace dani ta hanyar amfani da wangamemen bakinsa kafin na sami abin cewa tuni yayi gaba yabar ni sororo agurin zuciyata cike da tunanin hanyar da zanbi na samo masa kudinsa.
.
Zuwansa gurin shiyasa sani manta da duk abinda yafaru abakin titin. Domin dodon kunnena baya sauraron komai sai maganarsa.
Na daga kaina ahankali lokacin da rugugin motocin dake ta famar safa da marwa akan titin yaci gaba d adukan dodon kunnena. Lokacin dana dago kaina saina fahimci ashe har yara sun taru agindin teburin nawa suna sauraron bambanin fadan mutumin. Dago kaina keda wuya sai duk yaran suka watse wadanda mafi yawansu almajiraine.
Motoci suka ci gaba da safa da marwarsu launi daban daban nikuma ina kallonsu ina mafarkin mallakarsu idan nace wannan azuciyata idan wata tazo saina fasa. Karfe hudu da minti arba'in da biyu tayi lokacin tashina ya kusa kenan don haka sai gabana yacigaba da faduwa domin nasan tabbas gobe a ofishin yansanda zan kwana domin banida hanyar da zan sami kudin da zan biyashi. Ahaka na tsaya gindin teburin inata karanta duk addu'ar da tazo bakina sannan zuciyata ta koma baya tun sa'ar dana gama karatuna na makarantar gaba da firamare wato sakandire aduk shekararmu babu wanda ya samu sakamako fiyeda nawa sakamakona yayi matukar kyau a jiharmu nine na daya wato dalibin dayafi kowa samun sakamako mai kyau amma abin bakin ciki saigashi rashin kudi ya hana ni cigaba da karatuna saboda karatun ya zama na kudi duk kyawun sakamakaonka idan bakada kudi to ya zama shirme domin baiyi ma amfani saidai ka saka sakamakon agaba kayita kallo.

Mahaifana basuda karfin da zasu nauyina dama sakandiren ma wani makwabcinmune aminin mahaifina ya dauki nauyin karatun ina shekarar karshe a makarantar Allah yayi masa rasuwa ina da kanne biyu mace da namiji amma duk acikinsu ni kadaine nayi karatu saboda karamin karfin da mahaifinmu sukeda shi mahaifina lebura ne a wani kamfanin kwarori dan albashin da ake bashi bai isar mu saye abinci balle ayi zancen cigaba da karatuna ganin haka shiyasa na yanke shawarar samun sana'ar yi domin tara kudin da zan cigaba da karatu to ga irin sana'ar nan nafara kwana goma kacal da farawa saigashi har ana hsirin kaini ofishin yan sanda da farko aikin kamfani nafara to abin ka da dan boko ko kuma ince malalacin mutum irina saboda inada lalaci danaga bazan iya ba saina hakura shine to daga karshe na sami sallau wani mutum ne na kirki a nan unguwar mu nayi masa bayanin halin da nake ciki shine yaji tausayina ya hadani da......
Tuunanina ya katse hankalina yakoma bakin titin.
Malam ko bakajine inata faman kira wata zazzakar muryace mai kamar sarewa take cewa dani haka.
Nayi firgigit na fuskanci bakin titin kamar a mafarki sainaga zungureriyar mota a dab da inda teburina yake banji lokacin da ta tsaya ba don haka sai abin yabani mamaki motar ruwan tokace tana sheki kirar marsandi ce sannan ajikin fale falen lambar motar an rubuta kamar haka
SALMA ONE....
[3/16, 4:53 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA-04

Ajikin fale falen lambar motar an rubuta kamar haka SALMA ONE.

Santala santalan kyawawan kafafuwanta ne suka fara taba kasa sanye suke cikin bakin takalmi wanda ke lullube da tattausan gashi mai sheki in dai kuma har ba idona ne yake nuna min karya ba arubuce ajikin dan wani karfe dake lilo ajikin takalmin kalma ce kamar haka GOLDEN HEART.

Tun kafin jikinta yagama fitowa daga cikin motar kamshin turare ya hade gurin tunda nake ban taba shakar wani abu mai dadin turaren jikinta ba.
Tunani kakeyi ne? Tace dani tana dan murmushi lokacinda ta matso kusa dani sai kamshin turaren dake jikinta ya dada rudani jikina ya dauki rawa na kasa yi mata magana abinka da farin shiga ni ko acikin abokaina matsoracin matane murmushin daya ci gaba da bayyana fuskarta shi ya tabbatar mini data gane halin danake ciki
Yaya naga duk lemon naka ya lalace tace dani haryanzu murmushin bai bar fuskarta ba.
Nayi karfin hali na daga kaina muka hada ido da ita akaro na farko tun zuwanta nayi matukar mamaki domin fahimtar ashe kallona take bata dauke ido.

Reshen bishiya ne ya fado musu hajiya..... Nace da ita ina in-ina na dubi kayan dake jikinta masu sheki alokacin data karkatar da kanta zuwa kan teburin kayan marmarin da nake sayarwa tana sanye da doguwar riga siliki launin sararin samaniya kanta lullube da jan gyale mai shara shara
Ta juya da fararen manyan idanunta kan fuskata muka sake ido hudu a karo na biyu kwarjininta shiyasa na fara kawar da fuskata atunanina zatayi min kimanin shekaru ashirin da biyar zuwa da takwas sannan indai ta shekara za'a bi to yayata ce.

Dan samari ban ko san sunanka ba? Tace dani tana murmushi mamaki ya rufe ni bangane abinda take nufi ba yaya daga sayen lemo za'a tambayi sunana.
Na dubeta sannan nace da ita menene dalilin sanin sunana? Laifi ne don an tambayi sunanka? Tace dani tana murmushi sannan taci gaba da cewa daman lemon da ayaba nake son saya saidai kuma gashi nayi rashin sa'a duk lemon kanana ne gashi kuma mafi yawansu sun lalace.
Nayi shiru inajinta da kunnen sauraron tazo-mu-ji-ta domin nasan duk maganar da take fadi karya take a iya tsawon kwanakin danayi gurin na fahimci abu guda ba irin sune suke sayen lemona ba. Mafi yawancin masu sayen lemona leburori ne da kananan ma'aikata to amma wannan da duk jikinta ke cewa NAIRA yaushe....
Ta katse tunanina don Allah idan bazaka damu ba kuma kaga babu takurawa ga kudina zan baka gobe idan kaje gurin sayo kayan ka sayi mini manya manyan lemo da ayaba din zan aiko direba gobe da rana ya daukar mini ga mamakina sainaga ta bude jaka ta dauko damin kudi na wazobiya ta miko min na bude baki zanyi magana saita daga hannu har yanzu murmushin nan bai bar fuskarta ba kada ka damu idan ka saya ka rike guntun kudin ka rage asarar dakayi.

Zan tafi tunda kaki fada min sunan naka. Tace dani tana murmushi sannan ta nufi motar nikuma nabita abaya ta shiga ta zauna sannan ta leko kanta ta tagar motar azatona wani abu take son fada don haka saina matsa kusa na dafa tagar motar da hannuna muka sake hada ido da ita sannan ta kanne idonta daya.

Murmushinta yafadada ta dafa hannuna da tattausan hannunta mai sanyi sannan ta zaro wani dan karamin kati daga cikin jakarta ta miko mini adireshin gidana ne me yiwuwa direban nawa bazai sami damar zuwa ba kaga saika kawo mini kayan da kanka kenan. Ban ko duba katin ba saina tura shi a aljihun dana zuba kudin data bani haryanzu hannunta adafe yake da hannuna.

Tattausan hannunta ya sake matse hannuna sannan tayi kasa kasa da murya tace dani. Bazaka fada min sunan naka ba?

Nayi murmushi akaro na farko sannan nace ita sunana FARISU

Alokaci guda kuma na janye hannuna dake karkashin nata hannun.
Tayi sauri ta sake rike hannuna sannan tace dani Haba Farisu yaya zaka tafi muna yar hira na dubeta sainaji kunya ma ta rufe ni.

Sunkuyo nan kaji tace dani na tura kaina ahankali cikin tagar motar cikin mamaki sannan kamar da wasa sai siraran kyawawan yan yatsunta suka shafi fuskata sannan tace dani Sunana......

Bata karasa ba sainaji dirin mota abayana ban juya ba saboda ganin yanayin dake fuskarta ta bude baki kamar zatayi ihu idonta na kallon motar dake bayana ta tsaya..
Wani abu mai kama da kofaton doki ya mari fuskata ta baya naji anyi sama dani an buga da kasa sannan akasa kafa aka take wuyana wani kuma ya rufe bakina sannan aka jefani bayan kujerar motar ta baya aka rufe karti uku suka danne ni sannan duka abin yafaru ne cikin abinda baifi dakika talatin ba aka fizgi motar da gudu nikuma suka cigaba da luguiguita ni kamar lemon yara suka dora wata zungureriyar wuka a makogwarona sannan dayansu yace dani.

Zaka iya yin ihun idan kaso amma kada ka zargi wukar idan ta zarce kai tsaye ta rabaka kanka da gangar jikinka sannan yaci gaba da cewa.
Abinda yafi maka sauki shine kayi shiru kawai mai yiwuwa idan kayi hakan ka tsira da ranka amma fa dole ne mu dan sassama ka mu dan karya kafarka da hannuwanka.
Suka fashe da dariya sannan ne to motar taja ta tsaya suka jefoni waje tun kafin na gama fadowa wani daga cikinsu yasa kafarsa ya daki bayana sannan.......
[3/16, 4:54 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA-05

Tun kafin nagama fadowa wani daga cikinsu ya daki bayana na fado da fuska agefen titi.

Na yunkura na tashi zaune fuskata duk ta kukkuje samarin hudu suka zagayeni duk kusan shekarunmu daya dasu guda uku daga cikinsu kansu daya sunada matsakaicin tsaho na ukunsu shine dogo fari mai dogon gemu kamar burushi kansa a aske yake tas dukkansu suna sanye da yankakken wando jeans dakuma bakar suwaita agaban kuma rigar babban nasu an rubuta cikin manyan haruffa kamar haka IJAKALA.

Menene hadinka da ita? Babban nasu ya tambayeni na buda baki zan amsa saiya cigaba da cewa ba kai ba ita daga yau abinda tace mu ce dakai kenan idan kuma ka sake muka sake ganinta da ita toh sunanka Gawa. Banga lokacin daya daga hannunsa ba amma naji lokacin da naushin ya sauka a fuskata babu abinda zan iyayi akai. Na fadi anan sumamme
lokacinda na farka sainaji ni lullube cikin wani abu kamar buhun algarara abin haushi koda na tashi sainaga ashe gurin sayar da lemona suka dawo dani suka kuma sakani a karkashin teburin lemon sannan suka rufeni da buhun algarara.

Na tashi tsaye kaina nata buguwa kamar ana wasa da guduma aciki har yanzu kayana suna nan kamar yadda nabarsu ban ko damu da in dauke su ba sai na nufi gida. Misalin karfe goma na dare na bude dakina na shiga. Mutanen gida sunyi barci in ka dake muryar babana dake karatun alkur'ani mai girma fitilar kwan da na manta da safe ban kashe ba haryanzu tana ci na lalubi aljihuna na zaro katin data bani sannan na duba abinda ke rubuce a jiki

BIRNIN SARAUNIYA
NO-007
TITIN LUMFA..

Nayi ajiyar zuciya gamida godiya ga Allah daya sa katin bai fadi ba akalla dai nasan inda zan sameta. Birnin sarauniya.... Na nanata sunan cikin zuciyata ban taba zuwa unguwar ba saboda ba ajina bace. Amma duk da haka gobe zan gwada.....

TOH MASU KARATU SAIKU BIYO NI ZUWA GOBEN DON GANIN YADDA ZATA KAYA
[3/16, 4:54 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA-06

Na lalubi aljihuna na zaro katin data bani sannan na duba abinda ke rubuce a jiki
BIRNIN SARAUNIYA
NO-007
TITIN LUMFA..
Nayi ajiyar zuciya gamida godiya ga Allah daya sa katin bai fadi ba akalla dai nasan inda zan sameta. Birnin sarauniya.... Na nanata sunan cikin zuciyata ban taba zuwa unguwar ba saboda ba ajina bace. Amma duk da haka gobe zan gwada.....

BABI NA BIYU

Yau bazakaje sarin lemon bane? Mahaifina ya tambayeni lokacin danaje gaidashe awashegarin ranar da abin yafaru.
BIRNIN SARAUNIYA nake son zuwa nace dashi ya dubeni na dan lokaci sannan yace dani me zakaje yi acan? Kaifa baka rabuwa shiririta daga farawa har zaka fara kawo matsala ko?
Nayi shiru na dan lokaci sannan nace dashi wani aiki ne za'a samar mini acan ina tsammanin kuma yafi sayar da kayan marmarin riba. Har zaiyi magana sainaga yayi shiru yana duban fuskata me ya sameka haka a fuska? Tuni daman na shiryawa wannan tambayar Babur ne ya bugeni jiya zan tsallaka titi yayi shiru na dan lokaci yana jan tasbaha sannan daga karshe yace dani.
Tashi ka tafi Allah ya taimaka idan ka sami aiki shikenan idan ma baka samu ba to gobe kaje sarin lemonka domin ni dai abinda nake so da kai shine kayi kokarin ganin kacigaba da karatun ka ni kuma sainaji da Wahalhalun gida.
To baba. Nace dashi lokaci guda na tashi tsaye sannan na nufi dakina tun da asuba daman nayi wanka. Tun daren jiya na lissafa kudin data bani Naira dubi biyar ne acikin kudin ne na ware dubu daya sauran kuma na boye su ina fitowa daga cikin gida saina nufi kasuwa wajen da muke saro lemo.

Karfe bakwai da rabi na isa kasuwar rabin awa kenan ya rage ya turo mini da yansanda tun daga nesa na hango wangamemen bakinsa mummunar fuskarsa ta yamutse lokacin da ya hange ni jama'a sun fara cika rumfar kowa na harkar gabansa masu sara da kudinsu nayi masu karbar bashi ma irin namu nayi sannan agefe guda almajirai na ta tsintar rubabbun lemo.
Assalamu Alaikum na yi sallama sauran suka amsa amma shi bai amsa ba.
INA KUDINA?
Yace dani cikin rawar murya mutane sukayi shiru suna sauraren mu na zaro naira dari biyar da ashirin daga cikin naira dubun data bani sannan na tura masa kudin cikin aljihun babban rigarsa na juya ban ko ce masa sai anjima ba ina barin gurin sainaji hayaniya ta sake barkewa adaidai lokacin ne na hango Sallau ya nufo gurin nayi sauri na sauya hanya saboda banason bata lokaci tuni daman na gama shirin tafiyata tun jiya da daddare don haka saina wuce kai tsaye zuwa bakin titi ban dade ba wani dan tasi ya bullo na daga

Please Login or Register in order to submit comment