Join Our WhatsApp Group

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

ba. A duniya ko a lahira.

Shehu:
"Laila, Laila, Matar Malam kinga bata motsi fa." Baba mai riga tace.
"Shehu kayi maza kaje ka sanar da iyayen Laila halin da take ciki kamun ta Allah ta kasance, zaiyi wuya yarinyarnan ta tashi. Ka shiga jarawaba, gana rashin mata, gana samun ɗa mata maza.
Shehu ji yayi kamar an kwaɗa mar guduma a maɗigarshi.
"Mata maza Laila ta haifa mun Baba?" Matar malam ce ta katseshi.
"Ta farfaɗo kayi maza Shehu ka sanar da iyayen yarinyarnan halin da ake ciki.
A gigice Shehu ya fita, ya nufi hanyar Bakori. Laila kuwa wani nannauyan baccine yai awon gaba da'ita na baƙar wahala.

Mrs Bukhari ce

Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent, sannan idanuwansa suna kan ƴammata saboda ya samu sarauniyar girki, kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.

Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin👇🏻👇🏻

07068606171
08104335144
08179523215

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

*🤟GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARA TA 2023🤟*
*_Ina kuke masoyan gawurtattu uku ga su ssun dawo muku da wasu sabbin labaransu a wannan sabuwar shekarar, wannan karon salon gawurtacce ne, ku hanzarto kar ku sake ayi babu ku._*
_Sun shirya tsaf a wannan karon don kawo muku labaran da zakuyi fahari da su, tafiyar mai zafi ce sannan ta musamman._

*_Haziƙai kuma gawurtattu ukun sun shirya ne domin kawo muku gwarazan labaran da zaku yi alfahari da su._*

*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_

*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_

*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_

_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_

1 500
2 700
3 1000

_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank

_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._

_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171

*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*

0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171

*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023 SABON SALO SABON TAKU.*

_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_

*Mrs Bukhari ce 👉🏾👉🏻*
MATA IYAYEN GIJI

DAGA ALƘAMIN
BADI'AT IBRAHIM ( MRS BUKHARI)
GAWURTATTU UKU

LAMBA TA UKU

SAMFOTI

*_🔥GAWURTATTU UKU🤟2023_*

*_TALLAH TALLAH TALLA🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️_*

_A HAYYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃💃🏻💃🏻_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894

*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._*
*_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA KUDIN KI IYA SHAGALINKI🤝_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU, INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN ZO 👏👏👏👏👏_*

Ɗambawa garin marasa kyau, duk kaga ɗan ƙwarai baƙone.

Ɗambo
Ƙarƙashin ƙaramar hukumar Bakura, Zamfara Gusau.

Ƙauye ne mai cike da ƙauyanci, da gidadanci sosai, ƙauyene da babu wutar lantarki, babu asibiti, babu makarantar boko, babu ta mahamdayiiya. Duk wannan abun dana lissafo sai ɗambawa sun shigo garin Bakura suke gudanar dashi. Manoma ne, kuma makiyaya.

GIDAN UWAYEN AMARYA:
Uwar biki, taci kwalliya da jojinta sai sheƙi take yi. Mata maƙwabtane naga suna ta shigewa da fantekoki manya, cike da tuwon dawa, tuwon, masara, tuwon gero, tuwon ruwa, ( tuwon ɓula) Ko wacce da nata. Da sun shiga sai su dire wannan fantekar akan gadon kara da aka ajjiye a tsakar gidan. Wannan kawo abinci daga maƙota zuwa gidan uwar biki, wata al'adar auren ƙauyen Ɗanbo ne, daɗaɗɗiyar al'adar da aka ƙi yar da'ita, al'adace da take taimakon marasa ƙarfi sosai. Uwar amarya sai washe baki take yi, tana faman gaggaisawa da jama'a. Mata da yara sai cin tuwo kala kala suke yi.
"Rakiya kuyi da jiki mana, dan Allah a samu aje gidan maza ayi daɓennan mana." Rakiya ƙanwar Uwar amarya ce.
Isowa tayi wajan yar Tata, ga dangin uwar amarya daga gefe, mata biyu suna riƙe da ƙyauren langa_langa sabo fil sai kashe idanu yake yi. Wasu na riƙe da kayan aikin daɓen ɗakin amarya.
"Yaya mu kam mun tafi, gara muje da wuri kam"
"Allah ya tsare hanya."
A jere matannan suka fito kusan rai goma sha biyu. Suna tafe a ƙafa suna waƙar da akeyi in mata zasu je yin daɓen ɗakin amarya. Ga waƙar kamar haka.

Ayye lalle, ayye lalle waya kawoki, Baba daya kawoki mi aka baki? Tuwo aka bani da fura, inda naji kiran nan da gudu nika sheƙawa, inbanso neran nan wazobiya ta ɗori, Allah bani mijina koda ƙadangarene, mu shige ɗan ɗakunmu, sunɗunɗun, maɗunɗun.
Aka suke ta waƙarnan suna tafe.
Ɗabe itama wata al'adar aure ce a Ɗanbo. Dangin amarya suke yin daɓen ɗakin amarya, su shafa makuba a bango, da Ƙyaure. Amma in aure ya mutu, ana cire ƙyauren, in rabuwar rashin daɗi sosai akayi, har daɓen ake farfasawa. Washe gari kuma sai a kawo jere, da yamma masu kai amarya su kawota. Gagarumin biki akeyi sosai a ranar daɓennan.
Da sallama su Rakiya suka shiga gidan maza.
"Ahuwanku dai masu gida, ga baƙin arziki, baƙin daɗi, munzo yin daɓen ɗakin Amarya ne." Ƙanwar mahaifiyar Audu Ango tace.
"Maraba lale da zuwan baƙin arzki. Ku muje a nuna muku shiyyar surukan gidan." A baya suka bita, suna tafe suna waƙa, tsofaffin cikinsu nayi musu amshi da tafi. Gidan a batse yake da jama'a fam. Kuma yau da Yamma abokan ango sun shirya wasan Dambe, a gidan wasan Ɗan kande, kasancewar Damben gargajiya shine aikin Audu, duk da ma dai suna taɓa sana'ar fawa. Yawanci mahauta sune masu yin damben gargajiya kamar yanda yazo a tarihi. Mahauta sukan yima saurari dariya, in baya shiga fili, harma su kirashi da matsoraci, wani sa'ilin har mata yake rasawa. Dan ko wacce mace tafi son jarumin maza, ba rakkon maza ba. Hakanne ya sa mahauta suke damben gargajiya sosai.
"Ga ɗakinnan" Tana nuna musu ta wuce tana guɗa.
Ɗakin falle ɗaya ne babba. Nan dangin uwar amarya suka zage, sukaita aikin kwaɓar bigaggiyar ƙasa. Suka shiga daɓen ƙasan ɗakin amarya, suna yi suna waƙar al'ada mata sai tafi suke yi. Ga waƙar da akeyi in anga daɓen kamar haka.
Ke kika ce kina so, da baki ce kina soba da ba'a baki shiba. Ta zama _ta zama ɗakko hula. Ta zama _ta zama ɗakko buta. Ta zama _ ta zama ɗakko riga. Haka har zuwa ƙarshe. Mata kuma suna shewa, ana tafi da amshi.
Suna gama daɓe, suka saka ƙyaure, sannan suka shafa makuba a bangon ɗakin, ya fito shar dashi, sai ƙamshin ƙasa yake yi.
Dangin ango ne, suka dire musu fanteku. Ɗaya cike da dawo, ɗaya cike da nakiya, ɗaya cike da diɓila. Bisa ga al'ada. Haka suka ɗauki wannan fanteku aka suna tafe suna waƙa da tafi, har zuwa gidan Uwar amarya.
Da yamma su Audu suka gabatar da wasan dambe.
Washe gari, bayan sakkowa a masallaci, aka ɗaura Auren Audu da Shamsiyya. Da rana ƙwal aka soma fito da kayan jeren ɗakin amaya, gado da kwaba tuni mata suka soma gaba da'ita, kwabar nan aka mata suka azata. A ƙarƙashin kwabarnan mata sunfi rai ashirin. Haka masu ɗauke da gado ma.
Suna gaba, mata masu ɗauke da jere aka suma suna biye. Kwalla, kumbo, fanteku, samiru, ɗan china, kwanon sulba, gidauniyar cin tuwon mai gida, languna. Da adakar kayan lefe. Ga kuma fanteku manya da aka cikosu da wara. Dan tuyan wara shine sana'ar Shamsiyya, kuma al'adace ranar auren yarinya, a samu fanteku a tsaƙe da abinda take siyarwa, naci a kai gidan surukanta, suci su ture, tare da kayan gara, irinsu. nakiya, ga diɓila, ga ajaye, ga nakiya. Ga su buhun shinkafa, buhun gero, buhun dawa, buhun masara, ƙwarya bokatan ƙarfe. Da kayan noma dangin su, haiwa, garma, guraye. komai aka kuma da ƙafa ake kaiwa."
Sun samu tarbar kirki, tare da dangin Audu, da maƙota aka haɗu aka jere ɗakin Shamsiyya. Tas.
Da yamma kuma, ƙanwar mahaifin Shamsiyya ita ta goyo Shamsiyya a baya. Ana tafe a ƙafa da mata da ƙawayen amarya ƴan rakiya, suna tafe ana waƙa. Amarya ƴar gata tana baya tana shurɓune majina. A haka aka kaita ɗakin mijinta. Kwanan ƙawayen amarya biyu a ɗakin Amarya.
Ana Ukunne abokan Audu suka rakoshi ɗaki shima.

Shamsiyya

Na ɗauka rayuwar soyayya haka za taci gaba da ɗorewa. Harma a kwanakin amarcina nayi magana da gogan nawa kan cewa.
Ni naji sai cewa akeyi aure haƙuri ne. Kuma tausayi da haƙuri ke riƙe ma'aurata ba soyayya ba. Ni kuma sai naga saɓanin hakan Audu. Shi kanshi a lokacin giyar soyayya ashe ta buga shi, baya gane komai, cemun yayi
"Romun soyayyarmu dai ba mai ƙarewa bane, haka za muita sharɓarshi in sha Allah.
Haka rayuwa taita garawa damu, kwanaki, watanni, shekaru sai Shuɗewa suke yi. A haihuwa ta biyu, anan na soma ɗanɗana baƙin ciki da takaicin ɗa namiji. Audu madokine sosai, ko yaya nayi mishi kuskure sai duka, dukan da zaima sa'anshi a filin daga, irinshi yake yi mun, du ya farfashemun baki. Dana zari mayafi na tafi gida. Mahaifina ya rakoni da duka har ɗakin mijina. Na rasa wanda zai tausaya mun ya dubeni. Ƴa mace rayuwa take mara ƴanci, ko a gidan iyayenta. Iyaye su suka soma banbance mu. Dan da zaran sun haifi ɗa namiji, zasu saka rayuwarmu a kwandon shara. Da wannan tunanin mazan suke buɗe idanu. Suna buɗe idanune suga iyayensu mata ai basu da wata daraja a idanun iyayensu maza. Amfaninmu shine, girki, haihuwa, kashe musu ƙishi. Iyakar darajarmu kenan. Ɗiyata ta farko macece mai sunan Mahaifiyar Audu wato Aishatu, muna kiranta Shatu, ban cireta a nono ba na kuma haihuwar Zaliha, ina tsige Shatu, Zaliha ta cabka. Lokaci ɗaya nabi na susuce, haihuwar konika nake yi, a cikin shekara bakwai da aure, yarana uku, ga wani cikin a maƙale a jikina. Tsohon cikine a jikina, amma haka jiya da daddare Audu yai mun duka, dan kawai nace ya bani kuɗi in ɗan tsitstsinto kayan jarirai, dan na Shatu duk ya mutu, Zaliha ce take sawa, Shatun ko suturar arziki bata da'ita. Nan ya shiga farfaɗamun magana, ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba. Shine harta kaimu ga duka, haka na wayi gari cikin nauyin jiki da tsami. A zaune nake a dokin ƙofata ina kaɗa ma Baba Shatu lagwani, na jiyo Sallamar Goggo Rakiya, ƙanwar mahaifiyata.
MRS BUKHARI

Ayi haƙuri babu yawa. Yau asabar mai gidan ya kafa ya tsare 😀

Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent, sannan idanuwansa suna kan ƴammata saboda ya samu sarauniyar girki, kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.

Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin👇🏻👇🏻

07068606171
08104335144
08179523215

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

*🤟GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARA TA 2023🤟*
*_Ina kuke masoyan gawurtattu uku ga su ssun dawo muku da wasu sabbin labaransu a wannan sabuwar shekarar, wannan karon salon gawurtacce ne, ku hanzarto kar ku sake ayi babu ku._*
_Sun shirya tsaf a wannan karon don kawo muku labaran da zakuyi fahari da su, tafiyar mai zafi ce sannan ta musamman._

*_Haziƙai kuma gawurtattu ukun sun shirya ne domin kawo muku gwarazan labaran da zaku yi alfahari da su._*

*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_

*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_

*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_

_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_

1 500
2 700
3 1000

_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank

_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._

_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171

*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*

0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171

*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023 SABON SALO SABON TAKU.*

_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_
MATA IYAYEN GIJI

BADI'AT IBRAHIM ( MRS BUKHARI)
( GAWURTATTU UKU)

*_🔥GAWURTATTU UKU🤟2023_*

*_TALLAH TALLAH TALLA🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️_*

_A HAYYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃💃🏻💃🏻_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894

*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._*
*_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA KUDIN KI IYA SHAGALINKI🤝_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU, INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN ZO 👏👏👏👏👏_*

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN KACOKAM GA JAM'IYYAR MATAN AREWA, KUMA INA MIƘA GODIYATA A GAREKU SHUGABANNIN JAM'IYYAR MATAN AREWA.

KUMA INA ƘARA MIƘA SAƘON TA'AZIYYAR HAJIYA LAILA DOGON YARO UWA MA DA DA MAMA GA JAM'IYYAR MATAN AREWA. MUTUWACE WACCE BAZA'A MANCE DA'ITA BA, DUK DA TSOWON LOKACIN DA RASUWAR TA ƊAUKA, AMMA DA ZARAN ZA'A TAƁO JAM'IYYAR MATAN AREWA, DOLE MUTUWAR HAJIYA LAILA DOGON YARO TA DAWO ƊANYA SHARAB DA DUBBAN JAMA'A"

JAM'IYYAR MATAN AREWA BA ZATA SHAFE SUNAYENKU BA, HAR ABADA, DOMUN KUN TAKA MIHIMMIYAR RAWA WAJAN GANIN JAM'IYYAR TACI GABA.

HAJIYA MURJA WAMBAI ( FARA MAI FARAR ANIYA)
HAJIYA RABI SAULAWA
(SHUGABAR ƘASAR JAM'IYYAR MATAN AREWA MAI CI A YANZU, BAYA GOYA MARAYU)
HAJIYA GAJE ( YA GA SUNUSU LAMIƊO)
ANTY RABI MUHAMMAD ( BAN MANCE DAKE BA)
ANTY AISHA MUHAMMAD ( NA JINJINA MIKI)
HAJIYA HALIMA ADAMU
BARISTER AISHA USMAN ( DOLE IN SANYA DAKE)
HAJIYA ZULAIHAT MUHAMMAD ( KIN TAKA MUHIMMIYAR RAWA)

ANTY NURATU ADAMU FASKARI ( KIN BANI GUDUNMAWA TA MUSAMMAN, NA KUMA YABA DA KULAWARKI GARENI)

LAMBA TA HUƊU
"Shamsiyya kece kika fige kika dawo haka, uwa wacce ake gutsuran namanki?" Baba Shatu tace.
"Haba Rakiya, mai makon ki tausheta kuma, sai kike ƙoƙarin ingizata inda bai dace ba." A zafafe tace.
"Amman Shatu kina gani Audu ya ɗakko shirin nakasa mana yarinya? Dubi yanda jini ya taru a idanunta fa, ga tsohon ciki a jikinta, ina ganin rashin tausayin ai kamar yayi yawa ko?. Ya kamata a tsawata mishi, kawar da kai da muke yi, baya nufin bamu damu da Shamsiyya ba, muna yin hakanne dan siya mata mutunci da kima a idanun surukanta, da facalolinta." Buɗar bakin Baba Sahura kishiyar Baba Shatu tace.
"To kema kinsan ba zamu kasa tsawatar mishi ba, albasace ba tai halin ruwa ba, kinsan yaranmu na yau, ganinmu suke yi mu iyayensu mata kamar ba abakin komai ba, to yaro tun yana cinyarka za'aita zaginka, ana wulaƙantaka a gabanshi, sai kiga sun taso basa bamu daraja. Amma ai kamar yadda mahaifiyarta tayi haƙuri da dukan mahaifinta, itama ya kamata tayi koyi da mahaifiyarta ko?" Naji ciwon maganar Baba Sahura sosai, haka hawaye yaita sintiri a kuncina. Hannun Goggo Rakiya naja muka wuce ɗaki, dan ta kasa haƙuri sai zazzagama Baba Sahura jaraba take yi, ni kuma ina gudun abunda zai jawo mun abun faɗe a wannan ƙauye namu. Muna shiga na fashe da kuka, nan Goggo Rakiya ta shiga lallashina.
"Goggo Rakiya dama ashe haka auren yake, ashe haka maza suke, shine ake tururuwar yin aure, ashe babu komai a cikin aure, sai ƙunci da tashin hankali? Tun muna yara muke ganin mahaifiyarmu na kuka, wata rana muna jiyo yanda mahaifinmu ke zaneta tamkar jakar daya ɗauro ma kaya, taƙi tafiya. Yau gashi nima na faɗa irin taskun da mahaifiyata take ciki. Kuma nasan a haka zanta zaman haƙuri, har ranar da Allah zai kawo mun ɗauki." Goggo Rakiya tace.
"Da zan fasa miki irin haƙurin da Ta Annabi tayi a zaman aurenta ko da zaki kwashi abubbuwa da dama Shamsiyya. Mahaifiyarki bata taɓa gudowa gida da sunan yaji ba, kuma bata taɓa kawo ƙarar Babanku ba. Sai ranar da muka gani da idanuwanmu, a lokacin ta haifeki da ɗanyen jego a jikinta, ranar sunanki da safe. A jikin ƙarfen gado mahaifinki ya ɗaure Ta Annabi, ya riƙa tabka mata dorina tana ihu. Suna cikin wannan halin muka shigo muka same su, maƙwanta sun shigo kawo mata ɗauki. A ranar maƙwabtanta suka labarta mana irin ayar da mahaifinki yake gasa mata a hannu. Karki manta a lokacin akwai yayyenki maza biyu a gabansu. Yau gashi ankai wani matsayi da matakin da Ta Annabi itace hasken cikin gidan mahaifinki, tayi haƙurine ba dan komai ba, sai dan ku data haifa dan bata ko sha'awar tsallakewa ta barku." Tsabar tashin hankali da kaɗuwa take naƙuda ta kamani. Kafin Magriba ta rufa, na santalo yarinyata mace. Babu irin zagi da ɗiban albarkan da Audu baiyi mun ba, akan haifar mace dana kuma yi.
Ranar suna yarinya taci suna Tahira. Ashe a ranar aka ɗaura auren Audu, ni ina ɗaki bansan wainar da ake toyawa ba.
Zaman doya da manja muke yi tsakanina da Amaryar Audu Hindu. Audu ya tare a ɗakin amarya, anata ɗonan romon Amarci, ni kuma ina daga gefe ina kula da yarana.
Gorantama Audu aka soma yi a gidan dambe, har anayi mishi kirari da ragon namiji. Ranar kuwa nasha zagi a wajan Audu. Hindu tace.
"Ka sha kuruminka goga na Hindu, ga cikin magaji nan a jikina. Nice zan haifa maka magaji da yardar Allah. Tun daga wannan rana, Audu ya ƙara ƙaimi wajan kulawa da Hindu, har zuwa lokacin data sintilo ɗanta kyakkyawa namiji. Ranar suna yaro yaci sunan mahaifin Audu. Muttaƙa, ana kiranshi da Baban gida. Sai da Hindu ta Haifi yaronta na biyu, Audu ya dawo ɗakina kafin Hindu ta gama biki, dan rabon kwanan da yake yi mana na rashin tsoron Allah ne. Zai iya kwana bakwai a ɗakin Hindu kafin ya dawo ɗakina, wani lokaci daya kwana ɗaya zai koma ɗakin Hindu, a hakan na kuma haifan Basira, harda ƙaramin ciki a jikina yanzu haka.. Ashe dawowa ɗakina da Audu yayi hakan ya ƙona ran Hindu ainun. Har ɗakina ta shigo ta dinga tsiwa akan Audu, tana yi mishi ɗiban albarka. Daya fusata ya shiga jibgarta kamar anyi mishi wahayi. Baki na taɓe, ai miji madoki baya dena duka, har sai ranar da tsufa ya rufan mishi.
"Allah ya isana, shege mara mutunci, tsinanne azzalumi. Inji Hindu wacce bakinta yaƙi rufuwa. Duka har tsakar gida. Baba Shatu, da Baba Sahura suka tawo a guje, suka riƙe Hindu wacce take ta kutuntumawa Audu zagi, bakinta duk ya fashe yana zubar jini.
"Shege ɗan gidan taƙi zama."
Wani irin naushi Audu ya kai mata, Baba Shatu ta tare Hindu, ai kuwa Audu ya sauke mata naushi a bakinta. Ji kake gib. Take bakin Baba Shatu ya fashe, yawu da jini, da haƙora biyu suka zubo. A take ta hangure ( suma).

Mrs Bukhari ce.

Ai mun dai afuwa, yau lahadi oga na gida. Masu ƙorafin sun rikice kuma. Ya kamata ku gane wani ɓangaren labarin na taɓa. Dan labarin mata iyayen giji, bai ta'anlaƙa a kan tauraruwa ɗaya ba. Muna da taurari da yawa, kuma zamu shiga gidajensu da garinsu, mu taɓo rayuwarsu. Allah yasa kun fahimta?

Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent, sannan idanuwansa suna kan ƴammata saboda ya samu sarauniyar girki, kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.

Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin👇🏻👇🏻

07068606171
08104335144
08179523215

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

*🤟GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARA TA 2023🤟*
*_Ina kuke masoyan gawurtattu uku ga su ssun dawo muku da wasu sabbin labaransu a wannan sabuwar shekarar, wannan karon salon gawurtacce ne, ku hanzarto kar ku sake ayi babu ku._*
_Sun shirya tsaf a wannan karon don kawo muku labaran da zakuyi fahari da su, tafiyar mai zafi ce sannan ta musamman._

*_Haziƙai kuma gawurtattu ukun sun shirya ne domin kawo muku gwarazan labaran da zaku yi alfahari da su._*

*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_

*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_

*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_

_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_

1 500
2 700
3 1000

_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank

_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._

_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171

*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*

0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171

*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023 SABON SALO SABON TAKU.*

_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_
BADI'AT IBRAHIM ( MRS BUKHARI)
(GAWURTATTU UKU)

*_🔥GAWURTATTU UKU🤟2023_*

*_TALLAH TALLAH TALLA🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️_*

_A HAYYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃💃🏻💃🏻_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894

*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._*
*_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA KUDIN KI IYA SHAGALINKI🤝_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU, INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment