Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

KUN ZO 👏👏👏👏👏_*

SAMFOTI





LAMBA TA BIYAR

Saleri:
Ƙarƙashin ƙaramar hukumar Azare, jihar Bauchin Najeriya.

Saleri ƙauyene ƙayayau, daga Azare sai an wuce rugage biyar kafin a iso Saleri. Kab garin Saleri, basu da katangar ƙasa, sai dangar kara. Gidajen ƙauyen a jere suke babu fasali, dan in ka shiga gida ɗaya, a cikinshi zaka iya ɓullawa gidaje sama da goma. Suna da makarantar boko, da malamai biyu, malamin lissafi, da malamin turanci. Wannan makarantar ada ana karatu a ciki, shima daga lokacin rani kawai, da zaran damina tayi, yara suna gona. Amma yanzu ba'a karatu a wannan makarantar, wani mahaukaci ne yake kwana a ciki. Babu asibiti, har sai sun hau Bodi ya fita dasu zuwa Azare tukunna. Babu wutar lantarki, rijiya ɗaya ce a garin jol, duk jama,ar Saleri a wannan rijiya suke ɗiban ruwa, sai rafi da suke zuwa wanki, dabbobinsu ma a rafin suke shan ruwa. basu da injina, Mata ke surfe hatsi su dake ya zama gari, sai su sarrafashi, in buski zasu yi kuma, a dutsin niƙa na hannu suke zuba hatsin su ɓarje shi. Suna noma ka'in da na in. Mata da yara in damina tayi, tare duk ake zuwa ayi noma. Mace zata iya hayan gona, ita da yaranta maza da mata su nome gonar. Mai garin Saleri wanda ya rasu yana da kambun baka. Da yaga saurayi ya taso da gaye, da jarumta, zaiyi tofin Allah ya tsine akan yaron. Da sannu sannu yaron zai kwanta jinyar da saita zama silar ajalinsa. Amma yanzu Allah yayi ma Mai garinnan rasuwa, har an naɗa wani.


Musina:
Alwala nake ɗaurawa, ina zaune akan wani dutsi. Kukan Yarona Ƙasimu na jiyo, a zabure na miƙe, dan inje in ɗaukoshi, shekaran jiya_jiyannan ya faɗo akan maulidi (gado mai rumfa) ya dauje hanci. Salati na jiyo Baba Hauwa na rabtaɓawa harda tafa hannaye.
"Kai amma Musina baki da kunya wallahi. A gabana ina uwar mijinki kike zabura dan ɗanki kin jiyo yana kuka? Lallai Yawale ya auro mana fitsararriya, ko dama ance kinyi makarantar firamare. Amman in banda rashin neman albarka yaushe zaki yi haka a gaban Yar miji ma, ballantana har kiyi a gabana ni uwar mijinki. Kishiyarta Baba Huwaila ta amshe da cewa.
"Ke kin mance sanda Yawale ya karɓi Idi ya baki ne, wanne irin kuka da rama ne bata yi ba. Har yanzu ƙulafacin Idin take yi. Mu da sai mun haifi yara uku ana kwacewa, saika haifi na huɗune za'a barma. Haka zamu kawar da kanmu akan yarannan, har sai sun girma zasu san iyayensu na ainihi, raɓarmu ba bama bari yarannan suyu sabida kawaici irin namu na hausawa." Jin faɗowar Ƙasimu da shiɗewarshi, yasa na bar wajan a jijice, ni nama mance da su Baba Huwaila sam. A ƙasa na taddashi, hancinshi ya kuma daujewa, bakinshi sai jini yake zubarwa. Hannuna yana rawa na ɗagoshi, kujerar tsugunna na jawo na zauna a gaban kwabata, kusa da kumbunan dake ƙasa a jere hawan hawa. Nono na zura mishi, na soma shafa kanshi, sai ajjiyar zuchiya yake saukewa. Ni kuma sai hawaye nake fitarwa. Wannan wacce irin rayuwace mara ƴanci, rana zafi inuwa ƙuna. Zafi a wajan surukai, zafi a wajan miji, zafi a wajan facaloli, a hannun uban mijina kawai nake samun dama dama, sai Yayan Yawale, da ƙannen sa maza.
"Yayi tabbatacciyar maras kunya. Ni ina magana shine kika tawo kika barni a wajan ko?. Mu ada, in uwar miji na magana ma, wallahi tari wannan baki isa kiyi ba, balle ki ki tafi ki barta a tsaye tana magana, da shike iyayenki sun damƙa ragamar tarbiyyarki a hannun yahudawa marasa addini shi yasa. Amma a al'adance ke fitsararriyace ta ƙarshen zance" Da sauri na ɗago, Baba Huwaila ce riƙe da labulen ɗakina. Kasa cewa komai nayi, dana bata haƙuri zata ce na kuma yin wani babban laifin, koma tace zaginta nayi. Hawaye kawai nake zubarwa.
"Yayi kyau, sabida anyi miki faɗa, shine kika tusa yaro a gaba, kina zubar hawaye ko? To bari kiji shi kanshi Ƙasimun kina yayeshi zan karɓeshi, kiyi maza ki tashi ki koma bakin aikin girki, su A'i ai ba bayinki bane da zasu gwafe suna daka, ke kina ɗaki, kuma a gama tuwon kifi kowa bakin ci.. ." Labulen ɗakin ta saki. Wani irin kuka ne ya turniƙeni, da ƙyar na rarrashi zuchiyata nayi shiru. Ƙasimu na shinfiɗe a gadon bono. Sai naji danshin ruwa a jikina. Dana duba jikin Ƙasimu sai naga baiyi fitsari ba. Zanin na sake, na fita tsakar gida na sako alwala, amma ina cikin Sallah na kuma jin danshin ruwannan, sallamewa nayi jikina ya shiga rawa
To meye wannan, daga ina wannan ruwa? Kai bari dai in sake alwala."
Fita na kuma yi na sako alwala, a taƙaice a daddafe nayi sallah a ranar, daga jikina ruwannan yake fitowa gashi harna kuma jiƙe zanina. Kuka na rushe dani dana gane na kamu da lalurar yoyyon fitsarine, hankalina ba ƙaramin mugun tashi yayi ba.
Kuka nake rerawa mai sauti, a haka Baba Hauwa ta buɗe labule ta sameni."
"Au har yanzu kukan kike yi tabbatacciya? Zaki tashi kije ki kama musu aiki ne ko yaya, maras kunya fitararriya."
Kiyi haƙuri Baba, ganinan.
"Moin rufa mini baki, wacce bata iya shiru in babba nayi mata magana ba."
Labulen ta saki, ina jiyota tana zage_zage a tsakar gidan.
Tashi nayi na fita wajan girkin.
Amma kamun mu gama girkin, na shiga sakaki, ( bayan gida) yafi sau ashirin, fitsari nake yi sosai. Bayan mun gama girkin muka shiga rabo. Surukan gidan muka soma cirema, sai ko wacce ta ɗakko langar tuwo da miya na mijinta. Bayan mun zuzzuba musu, sai aka zuba ma yara. Muma muka zuba namu a ƙawuwar ƙwarya wacce ake kira da mazubi. Lauma biyar nayi ma tuwonnan, na tsame hannuna. A jiƙe na koma ɗakina, ina hawaye. Ƙunzugu nayi da fallen zani guda. Ina zaune ina ba Ƙasimu daya farka nono, zuchiyata sai harbawa take yi da sauri, tunanina baya jikina sam. Yawale ne ya shigo sai wani cicciza yake yi, yana ta batsewa. Langar tuwonshi na jawo mai gabanshi, da kwanon sha dana zuba mishi farau_farau a ciki.
Sannu da dawowa Yawale" A daƙile yace.
"Musina karki kuma bari su Baba suyi ƙararki akan rashin kunya da kike yi musu akan yara. Dan har yanzu ban mance fitsara da ɗiban albarkar da kika yi ba, lokacin da na tsige Idi a nono, na ba Baba ba. Kuma shima wannan kina Yayewa zan kyautar dashi, kina kuma haifa zan kuma kyautarwa. Sannan wallahi in kika sake tado mun da maganar inje Birni in dubo Idi kuma, zan iya salwantar miki da iyoyin aurenki, danni ɗiban albarkar da kike yi mun a gidannan takai intaha." Yawu na haɗiye muƙut, take jikina ya shiga kakkarwa. Dan mu matan hausawa muna tsoron saki, mace duk ƙuncin da take ciki, tana kiyaye abunda zai zamana an kai ga sakinta. Alhalin a mafi yawan lokuta sakin shine a'ala a garemu, duk da inka fita daga gidan auren naka, baka san gida wa zaka kuma faɗawa ba, tunda mazan ba tukwane bane balle ka ƙwanƙwasa ka samu gidi, amma kuma a rashin tayi ake barin arha . Ina mamakin irin wannan milkin mallakan da iyaye suke yi mana akan yaranmu, yanzu laifine dan na damu da nawa, a matsayina na Uwa? Nisawa nayi nace.
Yawale kayi haƙuri, in sha Allah ba zaka sake jin bakina akan ko wanne yarona ba. Wannan yaron kuma tuni na jima da sama zuchiyata dangana. Rayuwar shekara biyu yayi, a ƙirjina da cinyata, aka rabani dashi, daga baya ma aka kaishi almajirci na dena ganinshi baki ɗaya ma."
"Kuma in maza ɗari zaki haifa haka zasu tafi almajirci, ko kina mutuwa kina tashi ne, nj yarana bazan miƙa su hannun turawa ba, kamar yanda iyayenki su ka yi kiskuren miƙa ki, gashi a sakamakon karatun boko zaman aure, da bin miji yana shirin gagararki." kwanon tuwon ya ja ya soma kantara loma. Ni kuma sai kallonshi nake yi. Ina ina ɗigar hawaye.
Yawale." Ɗagowa yayi yace.
"Wooo haba Musina kar inci abincinne koko me kike nufi ne?. Ɗauriya na ara na yafa ma kaina, nace.
Daman gani nake kamar yoyyon fitsarine ya kamani, shine nake neman izininka, gobe zan shiga Azare inje asibiti a duba ni." Jim yayi yana kallona.
" In sha Allahu ma ba yoyyon fitsarin daya kamaki, yama akayi kika san yoyyon fitsari?"
"Yayata marigayiya Hanne, ciwon daya kasheta kenan, ita asibin binni ma Babanmu yasa aka kaita. Kuma tun la'asar nake sunturin shiga sakaki, yanzu haka maganar nan da nake yi maka, ƙunzugune a jikina" ina kaiwa nan na soma kuka.
"Ke dalla tsayar da kukannan haka, banson shirme irin naku na mata. Maganar asibiti kuma babu inda zaki wallahi. Ki shirya dai in kaiki waccan ruggar ta fulani wajan malam Sakaraɗa, ya baki magani kizo ki dafa kiyi ta sha. Ince dai babu wanda yasan halin dai da kike ciki a cikin gidannan ko?
Kai na girgiza mishi halamar eh. Sannan nace.
"Yawale kayi ma Allah ka yarda inje gida Baba ya kaini asibiti, wallahi yaya Hanne ma da maganin gargajiyar aka soma, saida ciwon ya cinyeta aka kaita asibiti dana gidan yaƙi." Tsawa ya daka mun, saida na zabura, tsabar ƙarfin tsawar.
"Tunda gidanku ne ke auranki ai dole kije gida a kai ki asibiti, wata kan kinma raina duk ƙoƙarin da nake yi a kanki ko? Maganin gargajiyar da zan karɓo miki shi ba magani bane?asibiti ko shirmen banza. Ke duk maganin gargajiyar mu ka sha, gamu gadagau da lafiyar mu, wallahi daga nan zan iya zuwa har Azare da bala'in gudu, tsabar lafiya, kuma ba'a taɓa kai zuriyar gidanmu asibiti ba, a kanki baki isa a soma ba, uwar iya. Dan haka na gargajiya zaki yi. Kice ciwon ma gado ne." Yana kaiwa nan ya wanke hannunshi, ya haye maulidi. Nafi kwatan dare a zaune a wajan ina dubka da warwara, maganganun da Yawale ya yaɓa mun sai yawo suke a kaina. Ƙunzugun jikina ya jiƙe sharab har tsungulata yake yi. Sake ƙunzugun nayi, wanda na cire kuma nasa a bokitin da nake wanke kayan ƙunzugun Ƙasimu, na tura a ƙarƙashin maulidi, na jawo matashin kai na yar a ƙasa. Na jima banyi bacci ba. Ina ganin lokacin da Yawale yake zuwa zance gidanmu a idanuna. Da irin kalamai tausasan da yake jifana dashi. Ko a gida aka ɓata mun rai, da zaran Yawale yazo zance, zai yaye mun dukkannin damuwa, saiya tabbatar ya sani farin ciki. Ashe yaudarace kawai. Yau gani a cikin halin da nake buƙatar tsantsar kulawa daga wajan Yawale, amma yayi kwanciyarshi yayi burus dani, sai munshari yake ja. Tunda na Auri Yawale muka gama cin amarcinmu salamun_salamun, ban kuma samun farin cikin daya haura mako ba. Kullum a cikin taraddadi gami da taka tsan_tsan nake, dan ɗan motsi kaɗan zakayi, saiya zama gagarumin laifi, a wajan miji, ko iyayenshi.



MRS BUKHARI


INA MIƘA GODIYA TA DA DUKKAN MASOYA WANNAN LITTAFI NAWA. HAƘIƘA YAU NAGA RUWAN SOYAYYA. NA AMSA WAYA TAFI SAU GOMA, ANA TAMBAYATA YAU BANYI POSTING BA. NAGODE DA SOYAYYA.
AKWAI WATA BAIWAR ALLAH DATA SAKA MUN SAƘO A MOTA DAGA NIGER ZUWA INDA NAKE RIVERS STATE. DUK AKAN WANNAN LITTAFI. NAGODE SOSAI. DAMA DANA BUƊE INGA.....🤣


Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent, sannan idanuwansa suna kan ƴammata saboda ya samu sarauniyar girki, kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.

Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin👇🏻👇🏻

07068606171
08104335144
08179523215

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

*🤟GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARA TA 2023🤟*
*_Ina kuke masoyan gawurtattu uku ga su ssun dawo muku da wasu sabbin labaransu a wannan sabuwar shekarar, wannan karon salon gawurtacce ne, ku hanzarto kar ku sake ayi babu ku._*
_Sun shirya tsaf a wannan karon don kawo muku labaran da zakuyi fahari da su, tafiyar mai zafi ce sannan ta musamman._

*_Haziƙai kuma gawurtattu ukun sun shirya ne domin kawo muku gwarazan labaran da zaku yi alfahari da su._*

*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_


*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_


*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_


_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_


1 500
2 700
3 1000

_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank

_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._


_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171

*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*

0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171


*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023 SABON SALO SABON TAKU.*


_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_
MATA IYAYEN GIJI

BADI'AT IBRAHIM (MRS BUKHARI)
( GAWURTATTU UKU)

*_🔥GAWURTATTU UKU🤟2023_*

*_TALLAH TALLAH TALLA🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️_*

_A HAYYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃💃🏻💃🏻_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894

*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._*
*_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA KUDIN KI IYA SHAGALINKI🤝_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU, INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN ZO 👏👏👏👏👏_*



SAMFOTI


LAMBA TA SHIDA



Da ƙyar ɓarawon bacci wahalalle ya kwashe ni.
Kamar a mafarki naji ana tokarata da ƙafa ana shureni. Da sauri na farka tare da saurin zama. Yawale na gani a tsaye a kaina, hancinshi a toshe.
"Kinji kunya wallahi Musina, fitsarin kwance da girmanki, jibi yanda fitsarinki ya fita har waje yana gudana. Da sakel gaskiya." Tsaki yaja ya tsallakeni ya tafi sallar asubahi. Cikin hanzari na miƙe, kayan fitsarin na haɗa dana jiya du na wawwanke na shanya. Ruwa na samu na wanke ɗakin tasa na goge, turare ɗan goma na yayyafa a ɗakin. Sannan nayo wanka da ruwa mai ɗari. Ina idar da Sallah, Ƙasimu ya farka da kuka. Nima hawayen nake ta zubarwa. Nono na zura mishi a baki. Babu ko sallama Yawale ya shigo. A kaina ya tsaya ƙiƙam kamar ɗan doka, sai toshe hancinshi yake yi, yana mun muzurai.
Ina kwana Yawale?
Baice dani komai ba, ban daddara ba nace.
Zuwa ƙarfe nawa zamu tafi can ruggan?" Ananne na fusata shi ainun, dama mai neman kukane aka jefeshi da kashin awakai.
"A haka zamu je rugga muna tafe kina fitsari kamar wata tunkiya kenan? Allah ya tsari gatarina da saran shuka. Ke bari kiji abunda nake so dake shine. Ki shirya tsab ki tafi gida, ayi miki magani a can ala bashi in kika warke sumul sai in je in ɗakko ku. Bazan iyaba, kinji zarnin da ku ke yi daga ke har yaron kuwa?" Yana kaiwa nan ya wuce wajan kwalla inda anan kayanshi na sawa suke. Kaya ya sake ya fice. Baima kalleni ba balle ya tausaya mun. Murmushi kawai nayi. Na jima da fahimtar halin maza, lafiyar mace da ƙuruciyarta kawai suka iya cinyewa. Da zaran ciwo ko girma ya saukar mata, shikenan a wajansu ta zama bola, daga wannan lokacin zasu iya wanko budurwa tsarar jikarsu ma su aura, tunda su tsufa bai fiye shafarsu kamar mu mata ba. Barinma mazan ƙauye, wanda ƙashinsu ya ginu da tuwon dawa, da zogala, da yaɗiya. Ƙasimu na saɓa a bayana, na fita tsakar gidan. Kai tsaye shiyyar su Baba Hauwa na nufa. Bayan na gaisheta ne, na shiga yi mata aikace_akace kamar yadda yake bisa al'ada da tarbiyya irinta malam bahaushe. Na gyare mata ɗakinta tass. Na fito da wankin kayanta kala uku na wanke mata tas. Sannan na koma ɗaki na sake ƙunzugu, na wanke wanda na cire na shanya. Madafi na nufa wajan facalolina. Bayan mun gaggaisa kuma sai muka shiga aikin ɗunamen tuwo da dama ruwan kokko. A'i tace.
"Musina sai kika ji tafiya ta kama su Yawale da jamilu ko?" Tsabar takaici E kawai nace mata naci gaba da abinda zai fishsheni. Damuwar dake gabana ma tafi ƙarfina, dan haka bazan ɗaura damuwar Yawale a raina ba. Rana fatse_fatse ina shirin kulle ɗakina zan tafi gida. Sai kawai na jiyo ihun yara a waje, ana cewa.
"Ga almajirai sunzo ganin gida, ayi noma a koma makaranta, dan damuna tana dab da tsaiwa, harma munje munyi sharar gona. A guje suka shigo gidan tuɗuɗu. Ina gani su A'i suka rungumi yaransu, amma irinsu Laure dani masu na fari ba damar ko kallo ka yawanta yi. Yanzu sai ace kayi fitsara, kai da ɗanka, sai a iya zazzaginka ma, a gaban yaran. Shi yasa yaranma suke tasowa basa ganin girman mu, yaro a ƙauye uwarshi zata iya cewa yayi mata abu, ko yaje mata aika, kakarshi wato uwar miji tace bazashi ba, a gabanshi kuma. Da sun girma kuwa sai abinda iyayensu maza suka ce dasu, shawara ma yaro bazai naima a wajan uwarshi ba. Banyi aune ba Idi ya tawo a guje ya ruƙunƙunemun zane yana dariya. Kallonshi nayi da kyau, yaro ɗan shekara Shida, wanda bai wuci inyi mishi wanka, da wankin kashi ba, shine ɗawainiyar kula da kanshi ta rataya a wuyanshi, kaico. Hannunshi na jaye na ɗan tureshi gefe badan raina yaso hakan ba, sai dan gudun matsalar da kaje kazo tai sanadin auren nawa baki ɗaya ma. A guje yayi cikin gidan yana kwaɗama Baba Hauwa kira, dama a ɗakin yake. Inba dai idanuna basu suna mun dai_dai ba, sai naga Idi kamar ɗingisa ƙafafunshi yake yi. Kulle ɗakina nayi na wuce shiyyar su Baba Hauwa.
Sallamu Alaikum, sannu Baba." Da harara ta bini.
"Lafiya da dawowar yaro zaki shiga yi mun sunturi a ɗaki, menene to rasa kunya ɓeran danga? Wallahi ki kiyayeni Musina, inba haka ba kina dab da barin gidanma baki ɗaya" Kai na sauke ƙasa kawai, inason kallon Idi ko zanji daɗi amma babu wannan damar.
Gida zani shine nace bara inzo inyi muku sallama "
"To ki gaida magabata" Tuwo ta tura ma Idi a kwanon samira. Tashi nayi na fita. Naje naima Baba Huwaila sallama, sannan na kama hanyar zuwa tashar bodi. Ina tafe harna kusan isa tashar, sai kawai naji an riƙe mun mayafina ta baya. Juyowar da zanyi muka haɗa idanu da Idi. Murmushi muka sakarma juna dukkanmu, hannunshi naja zuwa gefe can.
Yaya karatun kana taɓawa ko, kuma kana maida hankali a karatun dai ko?" Hawaye ya soma sharewa, gefe da gefen bakinshi duk ya fashe, ga wani ƙaton makero a kanshi sai ci yake. Tsugunnawa nayi nace.
Ya'isa me yasa kake kukan to?"
"Baba kice ma Baba ya cireni a makarantar, kullum da duka da ruwan sanyi ake tashinmu, kullum bana samun abinci inci da daddare. Malam Zulƙe kuma yaita samu a mari, ƙafata ciwo take yi, in ranar labara bamu bada kuɗin laraba ba, saiya samu a ɗakin duhu mu kwana." Hankalina naji ya tashi ainun, da rai na yarona yana kwana da yunwa, ya kwana a mari, da ɗakin duhu. Inna ci gaba da zura idanu inaga kamar banyi ma shi kanshi Idin adalci ba. Tuno da zafi da azabar dake cikin naƙuda nayi. A lokacin dana Haifi Idi saida na kwana biyu cir jiri na ɗibata bana iya gane kowa. Amma yau dubi halin da mahaifinshi ya sashi a ciki. Ƙafarshi ya nuna mun, ƙarfen mari duk ya fasa mai idanun sawu.
Kayi haƙuri zan roƙeshi ya barka a gida, yanzu ka koma gida kaji, gidanmu zanje. Bari in baka nera uku ka sai marau_marau nasan kana so." Abunka da yaro sai kuma ya washe baki, ina bashi ya kwasa a guje yana jujjuya kai irinna murnar yarinta. Murmushi nayi, tare da share hawayen daya gangaro a kuncina. Munyi tafiya sosai, sai wajajen la'asar na isa Azare. Gida na wuce, na riga na jiƙe sharab ruwan fitsari sai wanke mun ƙafafu yake yi. Ina shiga na zube a gaban iyayena mata.
"Lafiya Musina zaki shigo da kuka meke faruwa?" Cewar abokiyar zaman mahaifiyata, Innata tana zaune a turmi tana yanka kuɓewa zata shanya. Kallona kawai tayi, tana ganina tasan ina cikin matsala, amma sai cemun tayi.
"Ana miki magana kin tusa mutane a gaba kina kuka, ki sakko da goyon, ɗan baɗo yayi miki fitsari a baya." Ana cikin haka mahaifina ya shigo, shima ya tambayeni ko lafiya?"
Baba ciwon yoyyon fitsari ne ya kamani, kuma na roƙi Yawale ya kawo ni asibiti yace baida kuɗi, daga baya kuma yace in dawo gida, in ku kai mun magani na warke zai zo ya ɗaukeni." Inna Lami kishiyar mahaifiyata ta dubi mahaifiyata wacce suke kiranta Tarana tace.
"Tarana yau nake jin ɗan gatan uwa, wato mu nema mata lafiya, sai yazo ya ɗauki abunshi ko? Haka fa mijin Hanne yai mana sanadin mutuwarta." Inna dai bata ce komai ba sai haɗiyan ƙududu take. Malam Dauda mahaifina yace.
"Yawale baiyi laifiba ko a musulunci, da lafiya ya aureta, amman ku sani in wata lalura ta sameta yaji bazai iya zama da'ita, zai iya sauwaƙe mata. Lo kuma yaji bazai iya nema mata lafiya ba, zai iya turota wajanmu mu saimu nema mata lafiya, inta warke kuma yazo ya tafi da matarshi. Ku mata kun cika kacancana zancen da bai kai ya kawo ba. Ke Lami ɗauketa kuje asibiti muji me zasu ce, da kun gama ki wuce ki

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment