Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kinsan maza basu cika tawakkali ba."


Ɗahiru:
A tashar bodi aka sauke su, sai jan yaran yake, Tani kuwa ahankali take jan ƙafafunta, dan ji take uwa zata haife abunda ke cikintane yanzu tsabar wahala. A haka har suka iso gida, Ɗahiru sai zazzare idanu yake yi.
"Tani mu shiga can shiyyar su Yaya, ki daure sai rakin tsiya moi dalla." Ɗaga ƙafa ta shiga yi har zuwa shiyyar su Baba mai riga. Matar Malam ce ta soma ganinsu, fitowarta daga turakar malam kenan zata ɗebo mishi ruwa.
"Wa nake gani kamar Ɗahiru da Tani? Mai riga, mai riga, malam,Baban Yara ku fito ga Ɗahiru." Ba iyakar waɗanda Matar Malam ta ambaci sunansu bane kaɗai suka fito ba. Kusan rabin matan gidan sun fito, cikin al'ajabi da almara. Malam yace.
"Ɗahiru, Tani. Kune kuka dawo a cikin darennan?" Ɗahiru yayi dariya yace.
"Yaya ka manta sanda zamu bar garinnanma da daddare muka barshi, ta katanga ma bata ƙofa ba?" Ajjiyar zuchiya Malam ya sauke. Baban Yara yace"
"A tafiyarku baya haihuwa tayi ta tara tulin yara masu ƙiriniya sosai. Ɗahiru sai nake ganin kamar ka tabka babban kuskure da kayi tunanin waiwayar gida. Mai riga ki shiga da Tani da yara ɗaki. Tani wannan du yaranku ne? Ku da kuka tafi ku biyu, amma gashi kun dawo ku huɗu, da guxirin na biyar a ciki" Tani wacce take a galabaice tace.
"Ke dai Yaya Mai riga bari. Mun wahala a bariki sosai, duk da nasan dawowarmu tamkar wasa da rayukanmu ne." Matar malam da Baba mai riga suka shiga ciki da Tani da yaransu. Baban yara ya dubi Shehu yace.
"Kuje da Ɗahiru ɗakin zaure ku kwana tare Shehu." Ɗahiru yace.
"Au Shehu bai aure ba har yanzu? Naga ya zama babban mutun. Ina Lauwali ne?" Malam yayi dariya yace.
"Lauwali yana wajan tukuba yana gashi. Ga Iyami matarshi ita kaɗai nake tunanin ka sani a cikin surukan gidan. Lauwali yanzu ai da babban ɗanshi Jafaru suke shiga dawa farauta, kuma da gani zaifi ubanshi zamani. Shehu matarshi ce ta haihu, ƴan uwanta suna tare da'ita shi yasa ya koma ɗakin zaure." Ɗahiru yayi dariya. Nan surukan gidan suka shiga gaisheshi tare da wucewa ɗakin Mai riga dan gaishe da Tani. Shehu kuma suka wuce ciki da Ɗahiru.
"Zauna kawu bari insa Iyami ta kawo maka abinci da ruwa." Dariya Ɗahiru yayi yace.
"Shehu jarumin dawa, ka gagari kowa a dawa." Dariya Shehu yayi kawai ya fita.


Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent, sannan idanuwansa suna kan ƴammata saboda ya samu sarauniyar girki, kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.

Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin👇🏻👇🏻

07068606171
08104335144
08179523215

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

*🤟GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARA TA 2023🤟*
*_Ina kuke masoyan gawurtattu uku ga su ssun dawo muku da wasu sabbin labaransu a wannan sabuwar shekarar, wannan karon salon gawurtacce ne, ku hanzarto kar ku sake ayi babu ku._*
_Sun shirya tsaf a wannan karon don kawo muku labaran da zakuyi fahari da su, tafiyar mai zafi ce sannan ta musamman._

*_Haziƙai kuma gawurtattu ukun sun shirya ne domin kawo muku gwarazan labaran da zaku yi alfahari da su._*

*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_


*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_


*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_


_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_


1 500
2 700
3 1000

_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank

_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._


_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171

*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*

0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171


*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023 SABON SALO SABON TAKU.*


_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_



MRS BUKHARI
MALLAKIN BADI'AT IBRAHIM
( MRS BUKHARI)
(GAWURTATTU UKU)2023


INA TAYAKI MURNAR ZAGAYOWAR RANAR HAIHUWARKI. KIYI HAƘURI NAYI LATTI. ALLAH YA SAKE MA RAYUWA ALBARKA. KI DAƊE KIYI ƘARKO ( LAILA ALI OTHMAN) FARAR MACE ALKYABBAR MATA, SUKARI BAKIYI FARIN BANZA BA. 🤍🤍🤍💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻


*_🔥GAWURTATTU UKU🤟2023_*

*_TALLAH TALLAH TALLA🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️_*

_A HAYYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃💃🏻💃🏻_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894

*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._*
*_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA KUDIN KI IYA SHAGALINKI🤝_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU, INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN ZO 👏👏👏👏👏_*


SAMFOTI

LAMBA TA GOMA


Lauwali ne ya shiga ɗakin da Ɗahiru yake ciki da sallama. Yana ganin Ɗahiru ya shiga washe baki.
"Kawu ashe dai da gasken kune a tafe? Sannunku da zuwa."
"Lauwali sarkin gashi, a gasa zomo, a gasa maciji, a gasa, akuya, a gasa tunkiya da ƴaƴan cikinta. Ya farauta kuma, naji labarin Jafaru na wajanka yana nema ya gajeka." Dariya Lauwali yayi.
"Kawu ga gashashshen naman maciji na ƙunso maka." Ɗahiru yace
"Kamar kasan kuwa ina kewa. Kai kowa yabar gida, gida ya barshi. Meye a bariki in ba hawala ba. Komai nasu tsada, abun ba'a magana. Bani labarin dawa." Naman macijin ya soma ci. Iyami ce tayi sallama ta shigo, hannunta riƙe da langar tuwo da miya, Shehu na biye da'ita da sassanyar ruwan tulu a kwanon sha. A gabanshi ta dire, suka kuma gaisawa sannan ta fice. Lauwali yace.
"Ai Kawu Shehu za'a tambaya labarin dawa, dan yana daga cikin samarin da aka ware za'a gwada jarumtarsu dan a naɗasu sarautar sarkin mafarauta na ƙauyannan. Jibi ma zasu tafi gwajin ƙarshe a cikin dajin kankia, daji mai haɗari da ƙwanƙwamai. Amma anata dai girka shi, malam yana ta taimakawa da rubutu shima, duk wani kauci da sassaƙen daya dace yasha, ya gama Kawu." Dariya Ɗahiru ya saka har yana buga ƙafafu dan Ɗahiru baduniye ne sosai.
"Kai kace gara da Allah yasa na dawo, ina gida za'ayi naɗinnan naka Shehu. Abun yayi mun daɗi, kaji shaƙiyyyin yaro mu ba'ai mana tayin sarauta ba sai kai. Wato sarkin mafarauta ya mutu?" Shehu yace.
"Yayi doguwar jinya sosai kafin ya mutu. Aljanune suka shafeshi suka sabauta mishi lafiyarsu. Wai wani mai sarauta ya taɓa a cikinsu." Ɗahiru yace.
"Hmmm mahaifinshi ma daya mutu, aljanune suka taɓashi, hauka yayi tuburan yana yawo da kamfai. Yawancin sarakan mafarauta ƙarshe da aljanu suke fafatawa wanda yaci nasara ya hallaka abokin gabanshi. Shehu me aka samu ne mace ko namiji ance matarka ta haihu?" Wani baƙin cikine ya turniƙe Shehu dan baya ƙaunar a dangantashi da Laila ma balle yaronta. Kasa magana yayi, Lauwali yace.
"Namiji ne, Kawu sunanka ma yaron yaci. Amma mai lalurace ta mata maza. Tunda akayi haihuwarnan Shehu yake cikin tashin hankali, sai saƙe saƙe yake yi".
"Mata maza, kuma dai nasan mayu basa iya raɓar zuriyar gidanmu, ko dai abokan hamayya ne suka sabautaka Shehu, dan kar yayi nasara? Kasan dai bazai haifi mata maza yayi tunanin cin nasara ba. Inma fa zaici nasarar saiya tashi tsaye yayi da gasken gaske tukunna. Wannan mata anya alkhairi ce a gareka kuwa, daga haihuwar ɗan fari? Wa yasan wanne jarabar zata haifo nan gaba. Ni ina ganin ka saketa kawai ta ɗauki ɗanta ta kama gabanta. Dan wulaƙanci a rasa wanda za'aimun magaji dashi sai mata maza? Yarinyarnan karfa ka bari ta taɓama mihibbarka, ina ganin haɗin naku babu alkairi duk yanda akayi mai farar ƙafa ce." Hannu yasa ya soma cin tuwon da Iyami ta kawo mishi. Lauwali yace.
"Kawu bari in koma tukuba na bar Jafaru a wajan shi kaɗai." Tuwo cike da bakinshi yace.
"To gobe zamu haɗu, dana gama zan kwanta."
Shehu dai yana zaune yana ta jujjuya zancan Ɗahiru a ranshi, duk da shima yana tunanin ko ya rabu da Laila ne kawai? Amma kuma akwai wani buri da yake son cinmmawa, kuma yana tunanin in Laila tana ƙarƙashin inuwar aurenshi, burin nashi zaifi saurin cimmuwa, in yaso daga baya saiya cika ma rigarta iska.
"Shehu, ince dai da daddare babu wanda yake fitowa tsakar gida ko? Dan akwai sunan wani aljani da zan kira biyun dare, zaimun aiki ne, kuma ance ba'ason kowa ya ganni a lokacin da zan kirawo shi." Shehu ya dubi Ɗahiru yace.
"Babu mai fitowa, inma sun fito sai in zasu sakaki, kuma kaga a bayan gida can nesa yake."
"To sai ka kula duk abinda zaka ji inayi, karka kuskura ka juyo dan zaka iya halaka." Shehu ya haɗe hannayenshi biyu suka daki idanun hannunwanshi duka biyu irinna ƙauraye yace.
"Caw badai mutum ba, ba dai aljanba sai dai Allah. Nasha tabara, nasha yasin babu wani aljani da zai iya ja dani. Kawu wuya a jeji, wuya a kasuwa fa " Dariya suka saka dukkansu.

Ta ɓangaren Malam, da Baban yara kuwa, bacci ya gagara ɗaukarsu suna tsoron mai gobe zata haifar. Dan sun tabbatar yanzu haka shigowar su Ɗahiru an samu mai gari an sanar mishi. Gashi bayan tafiyarshi abubbuwa da yawa nashi sun ɓullo, ƙila ma a ƙone musu gidan nasu a wannan karon."

Tani:
"Ai Yaya mai riga, faɗar wahalar dake cikin bariki ba'a magana wallahi."
"Tani kun tafi kunbar baya da ƙura, dan wallahi guguwace ta tashi mai mugun ƙarfi, wanda mu kanmu saida ta kusan halaka mana rayuwa. Rikici anyi shi, dan Malam ma aka so a kama, wai kotun birni suke son a shiga. Ke Malam fa saida ya dena bacci, kullum sallah da sadakar zazzafan ƙosai. To sai maganar ta mutu. Mahaifanki ma, suka zo suka tada zaune tsaye a gidannan, akan ada tilas sai mun fito musu da ƴarsu. Sanadiyyar hakan ɗan zumuncin dake tsakani ya rushe. Wancan yaron ma yaso ya Auri ƴar gidan Iyatu, amma mahaifinki daya daka tsalle ya duro, dole muka janye. Ke abu dai babu daɗi." Inji Baba mai riga kenan. Matar malam tace.
"Ai nasan gobe fada zata cika, ke mai garinma da kanshi zai taso babu mamaki." Haka sukaita tattaunawa dai, daga baya suka kwanta bacci. Dama yaran sun jima dayin nasu baccin.


Ɗahiru.
Ƙarfe biyun dare ya fito tsakar gida tsirara haihuwar uwarshi da ubanshi, da wani turare na kiran aljanin da aka bashi sunanshi.
"Kayanasu, kayanasu, kayanasu"
Taku Ɗahiru ya soma ji dib dib a bayanshi. Take tsoro ya rufeshi, wani irin hayaƙine ya ya makanta ganin Ɗahiru. Magana ya soma ji kamar raɗa a kunnenshi.
"Labari ya iso mun. Ka samu duniya, zaka zama daga cikin shahararrun bokayen duniya. Gari, gari za'a dinga zancanka. Amma aikin da zamu baka da wuya. Muna buƙatar mahaifar da ƴarka take kwance a ciki. Dan haka gobe za'a haife yarinyar, sannan zamu ajjiye maka ƙoƙo da zaka taran mana jinin haihuwar matarka. Sannan muna buƙatar zabi guda ashirin, ka kalli yamma ka murɗe musu wuya ɗaya bayan ɗaya, ka tsotse jininsu tas ka shanye. Ayi sadaka da naman bayan an soya. Sannan ka samo jaki ka yanka a dokar daji a darennan, ka tona rami jinin ya tsiyaye a rami, saika ciro harshenshi da idanunshi ka ajjiye mana. Kana yin wannan aikin ka hau mataki na farko, kuma babu mai ja da kai, musu wannan babu mai yi da kai. Wannan shine mataki na farko, kuma karka sake a ganka yayin da zaka aikata komai." Ɗib ya daina jin maganar, a hankali Ɗahiru ya soma ganin gabanshi. Juyawa yayi ya koma ɗakin zaure. Wando da rigarshi ya mayar. Ya shiga tashin Shehu.
"Kai Shehu, ana kiwon jakai a gidannan ne?" Cikin jin bacci Shehu yace.
"A'a Kawu bamu da jaki ko ɗaya. Kasan ai gidan ɗan fulani maƙocinmu shine mai jakai" Shiru Ɗahiru yayi. Wuƙa ya zara, ya ɗauki layar zanan Shehu ya fice a gidan."


Tafe yake yana jan jaki har zuwa dokar daji, garin shiru kowa na bacci. Rami Ɗahiru ya shiga tonawa, sai zufa yake ta faman yi. Yana gama tona raminnan ya yanka jakinnan, bayan sun sha turka_turka. Ya ciri abunda aljani yace ya cira. Ya bar gawar jakinnan a yashe a wajan. Ya nufo hanyar dawowa. Yana fitowa daga dajin ana kiran sallar asuba. Hanyar kasuwar ƙauyen dake maƙwabtaka dasu ya nufa, dan yau ake cin kasuwa a ƙauyen. Ya shiga ƙauyen kasuwa bata ma soma ci ba. Sallar asuba yayi a ƙauyan, yana zaune aka soma cin kasuwar. Ɓangaren masu kaji ya duba. Yako samo zabin cikin rahusa jaka ɗaɗɗiyq ya sane su. Buhu ya siya, ya kama hanya. A wani lungu ya tsaya, ya dinga murɗe wuyan zabinnan yana zuƙe musu jini, a haka_haka har ya gama ya ɗuresu a buhu. Yana tafe yana murmushi, burinshi ya zama shahararren gaske ta yanda labarin bokancinshi zai kewaye ƙasarshi Najeria kab. Yaga irin nasara da tarin dukiyar da abokinshi Ɗan Audu ya tara, duk ta sanadiyyar bokanci. Da kiɗan gambara yake yi a bakin kasuwa. Amma a halin yanzu ya tamfatsa gida a kurmin mashi, yana hawa mota, ga malum_malum na shadda, taji aikin aska tara, ya samu sukuni har kumatu da tumbi ya ajjiye. Ɗan Audu abokin Ɗahiru ne, Ɗahiru yaji sha'awar ya zama mai sukuni kamar Ɗan Audu. Sabida tun tasowarshi ya taso da mugun son abun duniya. Tun yana yawon bara yake ƴan sace_sace ƙananu. A hannun Malam ya girma dan tun bayan rasuwar mahaifiyarsu, riƙon Ɗahiru ya dawo hannun malam a lokacin Ɗahiru na da shekara goma da haihuwa. Ya taso da rashin ji da muguwar ƙeta, dan ko kaza inta bashi haushi, yana iya kasheta ya huta. Ya taɓa farke ma wata akuyarsu mai ciki, cikin nata da aska."


Gidan mai Gari:



MRS BUKHARI.

Anan na kawo ƙarshen free page. Wato samfoti. Mai son kasancewa da wannan littafin mai ɗumbun darasi, mai cike da abun mamaki saiya tuntuɓi gawurtattu uku. Karku mance wannan labarin ya faru a gaske, ba ƙirƙira akayi ba. Ku nuna mana soyayya masoyanmu na faɗin duniya baki ɗaya.



Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent, sannan idanuwansa suna kan ƴammata saboda ya samu sarauniyar girki, kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.

Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin👇🏻👇🏻

07068606171
08104335144
08179523215

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

*🤟GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARA TA 2023🤟*
*_Ina kuke masoyan gawurtattu uku ga su ssun dawo muku da wasu sabbin labaransu a wannan sabuwar shekarar, wannan karon salon gawurtacce ne, ku hanzarto kar ku sake ayi babu ku._*
_Sun shirya tsaf a wannan karon don kawo muku labaran da zakuyi fahari da su, tafiyar mai zafi ce sannan ta musamman._

*_Haziƙai kuma gawurtattu ukun sun shirya ne domin kawo muku gwarazan labaran da zaku yi alfahari da su._*

*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_


*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_


*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_


_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_


1 500
2 700
3 1000

_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank

_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._


_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171

*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*

0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171


*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023 SABON SALO SABON TAKU.*


_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment