Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jere a ɗakikin ba? Ki kaɗar dashi ki samu na magani, amma ni in ba wajan maganin Hausa za'ajeba. Ficikata Kwarankwatsa ba zatai ciwon kai ba." Murmushin takaici nayi na dubeshi nace.
"Umarnin zama a gida nake son ka bani kawai, domun bani da ikon fita ƙofar gida ba tare da izininka ba. Ficikarka bana buƙata."
"Umma ta gai da Asha, Allah raka taki gona, can dasu gada. Dama jarabarki ce tasa kika dawo gidan ma. Aini cewa nayi sai kin warke kya dawo." Da dai na riga naji abinda nake son ji. Ban jira ya haɗiye yawu ba nayi ficewata a ɗakin, zuchiyata sai suya take yi.

Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent, sannan idanuwansa suna kan ƴammata saboda ya samu sarauniyar girki, kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.

Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin👇🏻👇🏻

07068606171
08104335144
08179523215

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

*🤟GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARA TA 2023🤟*
*_Ina kuke masoyan gawurtattu uku ga su ssun dawo muku da wasu sabbin labaransu a wannan sabuwar shekarar, wannan karon salon gawurtacce ne, ku hanzarto kar ku sake ayi babu ku._*
_Sun shirya tsaf a wannan karon don kawo muku labaran da zakuyi fahari da su, tafiyar mai zafi ce sannan ta musamman._

*_Haziƙai kuma gawurtattu ukun sun shirya ne domin kawo muku gwarazan labaran da zaku yi alfahari da su._*

*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_


*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_


*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_


_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_


1 500
2 700
3 1000

_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank

_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._


_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171

*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*

0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171


*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023 SABON SALO SABON TAKU.*


_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_





MRS BUKHARI
MATA IYAYEN GIJI

BADI'AT IBRAHIM ( MRS BUKHARI)

( GAWURTATTU UKU)


INA MIƘA SAƘON GODIYATA GA HAƊAKAR MARUBUTAN NAJERIYA BISA SHAIDAR KARRAMAWA DA SUKA BANI, AKAN LITTAFINA MAI SUNA ( UNGULU DA KAN ZABO) NAGODE MATUƘA ALLAH YA SAKA DA ALKHAIRI. INA MIƘA GODIYATA GA SHUWAGABANNIN HAƊAKAR MARUBUTA, DA ALƘALAN DA SU KAI ALƘALANCI.



*_🔥GAWURTATTU UKU🤟2023_*

*_TALLAH TALLAH TALLA🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️_*

_A HAYYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃💃🏻💃🏻_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894

*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._*
*_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA KUDIN KI IYA SHAGALINKI🤝_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU, INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN ZO 👏👏👏👏👏_*

SAMFOTI


LAMBA TA TAKWAS



BAKORI:
Da isar Shehu Bakori bai zarce ko inaba, sai ƴar kasuwa wajan mahaifin Laila malam Zangina. Inda anan yake kasuwancin sai da musullar ƙarfe, da musullar da ake cirewa a jikin bushiya da matajin kai na katako, da wuƙaƙe masu ƙota. Wannan itace sana'ar mahaifin Laila, taburin dake kusa da nashi kuma teburin wan Laila ne Jibirila. Shi kuma yana siyar da, kayan aikin gona. Garma, ƙota, cebur, da sauransu. Haka Shehu ya ratso kasuwar nan yazo wajan mahaifin Laila afujajan.
"Shehu kaine tafe afujajan haka? kar dai almurar yarinyar nan ta kuma tawowa ne? Ka haifi yarone baka haifi halinsa ba, amma zanje gidan in bata kashi yanzu." Shehu da yake duk a burkice, dan ana tafe a hanya yana tunano mata mazan da Laila ta haifa mishi, wannan wacce iriyar ƙaddarace haka? Yace.
"Ba kuma fitowa tayi ba. Ta samu kaine"
"A masha Allah, tana dai lafiya ita da abunda aka samu ko?"
"A'a gaskiya, ita da jaririn duk ba lafiya, Laila bata san wanda yake ma kanta ba, jini ne ya ɓalle mata wallahi, saida aka jiƙa mata manda tasha. Jaririn kuma mata maza ta haifa " wani zumm mahaifin Laila yaji a jikinshi, yayi shiru yana nazari irin nasu na manya, ya tausaya ma ɗiyar tashi gaya, kafin daga bisani yace
" Hmmmm Allah ya bata lafiya, shi kuma yaro Allah ya raya shi da imani. Muje gidan in sanar ma da mata, in yaso sai a samu mata su bika ko?"
"Toh" kawai Shehu yace, dan hatta mahaifin Laila Shehu haushinshi yake ji.
"Malam tsalha ga kayana kayi mun jira, yanzu zan dawo" malam Tsalha abokin malam Zangina ne sosai. Zungui_zungui suke tafiya kowanne cikinsu da abinda yake magana akai a cikin zuchiyarshi, Malam Zangina sai tunani yake yi, gami da taraddadin halin da iyayen Laila mata zasu shiga, in sunji halin da take ciki, da kuma abunda ta haifa, dan a wannan zamani mata maza tamkar mayu, ko aljanu aka ɗaukesu, gidan da akwai mata maza ma, ba'a aiken yara gidan, kuma an camfa cewar iyaye suna shiga halin fatara da shiga iftila'i kala_kala da zaran sun haifi mata maza. Har suka iso gida, malam Zangina tunani yake yi, hankali, da nutsuwa, basu da gurbi a jikinshi tsabar kaɗuwa. Tare suka shiga gidan da Shehu. Malam Zangina shi ya Faɗama su Ta asibi da Daddo halin da Laila take ciki da abinda ta haifa kuma. Take Ta Asibi ta soma zubarma da ɗiyarta hawaye. Dan tasan mutanenmu na ƙauye zasu camfa Laila da yaronta, ƙila ma a ɗaura musu karan tsana. Gabaki ɗaya suka tashi hankulansu, Shehu sai kallonsu yake yi, yana jin wani mugun haushinsu na ɗarsuwa a ranshi Daddo cikin murya mai cike da karaya tace.
"Malam to yanzu yaya za'ayi maganar tafiyar?"
"Ke da Laraba saiku je, amma ke dubota zaki yi ki dawo, ita Laraba saita zauna da'ita zuwa kafin su tawo wanka. Shehu ka shiga ka sha ruwa, zanje Fada in tambayi mai gari mijin ƙanwar tawa izini, sai mu tawo ku wuce." Fitarshi da mintuna talatin, sai gashi shi da Laraba ƙanwarshi, itama a kiɗimen take sosai.
"Daddo fito ku tafi, zan aiki wannan yaron yaje ya sanar da ƙannenshi batun haihuwar, ranar suna sai su ɗunguma suje." Daddo ta fito da ƙunshin kayanta a ƙunshe a ɗankwali, Ta Asibiti ta fito da ƙunshin yajin daddawa, da soyayyen man shanu, da yajin gauta, ta miƙama Laraba.
"Kuje Laraba Allah ya bata lafiya. Laraba tace.
"Amma Yaya itama Daddon ka barmu muyi zaman mu a can, ita saita kula da Laila, ni kuma inji da aikace_aikace koya kace Yaya, sabida Laila tana buƙatar kulawa kasan haihuwar fari ce?" Malam Zangina ya gyaɗa kai yace.
"Babu komai Laraba kuje ɗin." Kama hanya suka yi, Shehu na biye dasu a baya sai wani cin magani yake yi. A haka har suka isa Saleri yana zabga uban fishi da dana sanin auren Lailan ma baki ɗaya.
"Ahuwanku dai masu gidan" inji Laraba kenan. Matar malam wacce fitowarta kenan daga ɗakin Laila tace."
"Laraba sannunku da hanya, kun shawo rana, ku shiga ba insa a kawo muku ruwa." Da sallama su Laraba suka shiga ɗakin. Amman ganin irin halin da Laila ke ciki ya sake ɗaga hankalinsu sosai. Matar malam ce ta shigo da sallama, Baba mai riga na biye da'ita da kaskon wuta. A kusa da gadon Laila ta ajjiye kaskon, ta zuba tazargade a cikin kaskon. Jaririn ta ɗakko ta dinga busa mishi hayaƙin tazardagennan maganin mayo ne wanda ake amfani dashi a ƙasashen Hausa dan korar maye, kuma ana yima wanda ake zargin Mayu sun shafeshi.
"Mai riga ni ina ganin bai dace ace an bar yarinyar nan a gida ba, kamata yayi a tafi da'ita asibiti." Inji Laraba kenan. Matar malam tace.
"Ana ƙoƙari akan lafiyar tata, kinga kofin rubutu yanzu malam ya aiko, aka shafe mata jikinta dashi. Baban yara kuwa ya shiga jeji zai tsinko mata magani, ya farauto mata naman gashi, kar a raina ƙoƙarin Laraba ayi haƙuri" Baba mai riga tace.
"Kinsan ƴan birni duk inda suka kai suka kawo sai sun raina baƙauye. In banda raini Fulani Laraba, ina ke ina maganar asibiti a nan gidan na mafarauta, ƴan na gada ba ƴan haye ba. Daga nan cikin gida Shehu zai iya kiran zomo ko gada, kuma dolenta tazo, harmu za'aima zancan banza?" Laraba ta buɗe baki zata mayar ma da Baba mai riga martani. Daddo ta haneta ta hanyar girgiza mata kai, sannan tace.
"Mai riga ayi haƙuri kinsan sha'anin yara. Fatanmu Allah ya bata lafiya." Shehu ne yai sallama ya shigo.
"Matar malam, malam yace a bada jaririn, wanzami yazo zai dubashi ko da maganin da zai bayar." Laraba tasa hannu ta ɗakko jaririn taba Shehu. A mugun wulaƙance ya karɓi yaron, yana wani huhhura hancinshi, ala dole waishi an cuceshi."


Shehu:
Fita yayi da Jaririn zuwa ƙofar gida. Akan taburmar kaba ya samu Malam da wanzan.
"Miƙa mishi yaron Shehu, meye haka ka riƙo yaro sheƙeƙe? Wallahi ka kiyayeni shin me ruwa ukun banza (shashashan banza) Inji Malam.
Shehu baice komai ba, ya miƙa ma wanzan jaririn. A hankali ya sunce ƙunzugun jikin yaron. Halittarshi ta bayyana ta mace da namiji, na mazan a sama, na matan a ƙasa. Allah sarkin girma, mai yin yanda yaso da bawanshi, a lokacin da yaso. Sarkin da babu irinshi, sarkin daya haɗa ma wannan jariri al'aura biyu a jikinshi. Tsarki ya tabbata ga wannan ubangiji.
Wanzan ya juya yaron, ya juya, yace da malam.
"Babu wani magani da za'a bama yaronnan da sunan maganin kashe halitta ɗaya ta jikinshi. Ni abunda nake gani kawai malam, kayi mai rubutun tsari yasha, ƙila mayu ne suka shafeshi ko aljanu. Riƙeshi Shehu a mayar ma da mata shi sabida sanyi. Ranar suna zanzo inyi mai aski a cire mishi beli. Shehu jikinshi a mugun mace mus ya mayar da yaron ya dawo ya zauna a gaban malam.
"Nayi ma jaririn huɗuba da Ɗahiru domun tunawa da ɗan uwanmu. Kai kuma kayi haƙuri, ka ga uwar yaronnan? Nayi imani saita fika shiga damuwa, dan duk wata tsangwama da za'aima yaronnan inya girma, ita zaifi taɓawa. Kuma ba'ita taba kanta wannan yaro ba, Allah shiya bamu. Kai dai kaci gaba da shirinka na shiga jeji dan zaɓen fidda gwani. Akwai rubutu gora biyu da zaka ƙarashe sha. Fatanmu ace kai ka zama sarkin mafarautan Unguwar Alƙali. Nasan kai jarumine, sai dai fa jejin da zaku shiga yana da haɗari sosai, ko a mutu ko ayi rai ne. Shi yasa ma in har mutum ya kwana bakwai a cikin jejin ya fito sumul ake naɗashi sarkin mafarauta. Kuma Lauwali ya shirya tsab shima dan baka wasu layi da guru na layar zana ba wanda muka saba amfani dashi ba. Yanzu haka Baban yara akwai wani gashi da zaima shima laƙanine. Ka mayar da kanka akan sarautar dake tunkaroka karka watsar da darajar gidannan, mu da muka gaji farauta tun kakanninmu." Godiya Shehu yayi ma Malam. Amma gani yake yi, kamar ya faɗi akan zaɓen fidda gwani da za'ayi, dan fidda sarkin mafarauta. A tunaninshi sabida Laila ta haifa mishi mata maza.
Mrs Bukhari ce

Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent, sannan idanuwansa suna kan ƴammata saboda ya samu sarauniyar girki, kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.

Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin👇🏻👇🏻

07068606171
08104335144
08179523215

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

*🤟GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARA TA 2023🤟*
*_Ina kuke masoyan gawurtattu uku ga su ssun dawo muku da wasu sabbin labaransu a wannan sabuwar shekarar, wannan karon salon gawurtacce ne, ku hanzarto kar ku sake ayi babu ku._*
_Sun shirya tsaf a wannan karon don kawo muku labaran da zakuyi fahari da su, tafiyar mai zafi ce sannan ta musamman._

*_Haziƙai kuma gawurtattu ukun sun shirya ne domin kawo muku gwarazan labaran da zaku yi alfahari da su._*

*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_


*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_


*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_


_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_


1 500
2 700
3 1000

_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank

_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._


_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171

*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*

0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171


*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023 SABON SALO SABON TAKU.*


_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_
MATA IYAYEN GIJI

BADI'AT IBRAHIM ( MRS BUKHARI)
(GAWURTATTU UKU)

*_🔥GAWURTATTU UKU🤟2023_*

*_TALLAH TALLAH TALLA🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️_*

_A HAYYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃💃🏻💃🏻_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894

*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._*
*_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA KUDIN KI IYA SHAGALINKI🤝_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU, INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN ZO 👏👏👏👏👏_*

SAMFOTI

LAMBA TA TARA



KADUNA. KURMIN MASHI:
anguwace ta talakawa futuk, duk wanda ka gani a cikin unguwar mai fafutukar neman na sawa a bakin salatine, hakan yasa gidajen wajan yawancinsu na haya ne. Wani gida na hango da wata mata a tsakar gidan da tsohon cikinta. Yarane a gabanta mace da namiji. Ƙuɗi ta sunce a hannun zanenta, nera biyar ta miƙa ma babban, da gani shine babba.
"Maza Zulƙifulu ka kama hannun Hadiza kuje makaranta, ga kuɗin laraba nan." Baban yarannanne ya dirƙo ta katanga, sai gashi tik a tsakar gidan yana haki."
"Subuhanallahi Ɗahiru meye haka kuma, ko dai tsiyar ka kuma yowa ne?" Cikin masifa yace.
"Dallah rabu dani, wace tsiya zan kuma yowa. Bashi ya cika mun hanjina yana shirin halakani. Labari naji fa Rabe yaje kira mun ƴan doka akan kuɗinshi." Tani tace.
"Ni kaina duk tsukukunnan bashi suke bina Ɗahiru, fita wannan ta gagareni, yanzu meye abunyi to?"
"Garin zamu bari Tani, bazan yi sake ƴan doka su kamani ba"
"Me kace Ɗahiru, to in mun bar garin ina muka nufa?" Ɗahiru yace.
"Saleri zamu koma Tani na riga na samu sana'a. Ɗan Audu ya koya mun duba, da yanda ake dukan ƙasa tayi magana, malumta zan soma da mun isa ƙauyen Saleri. Dama kuma kinsan nasan wasu laƙanin abubbuwa da dama, yawon almajirci da farauta wanne irine bamu yi ba, baduniye ne ni cikakke. Sako mayafinki mu wuce, dan tsaiwa ɗiban tsumma zai iya tona mana asiri." Tani ta riƙe ƙugu tace.
"Ɗahiru ka mance tsiyar daka tabka a Saleri, ko ka manta da yanda muka fito daga ƙyauyen? Munfa tafi mun bar baya da ƙura, muna jiyo ihun matasa suna shirin ƙone gidanku, shine yanzu zamu kwashi jiki mu koma ƙauye?"
"Ai Tani duk abinda ya koro ɓera daga rami kika ga ya faɗa wuta. To abunda yake cikin ramin yafi wutar bala'i."
"Bikinka daya rage saura sati biyu fa, za'a ɗaura mu tafi da matar ƙauyene?
"Kinci ubanki ƴar gatan uwa kai" Dariya Tani tayi. Mayafi ta ɗakko ta fito.
"Ku same ni a titin baya, dan tafiyata daku bazai yiwu ba." Yana kaiwa ƙarshen maganarshi ya zuba da gudu." Tani taja hannun yara suka nufi titi. A tsaye suka samu Ɗahiru, suna isowa suka tari abun hawa zuwa tasha. Tafiyar awa biyar ce ta kaisu Bauchi. Daga Bauchi suka hau motar Azare, daga nan suka shiga bodi. Tani ta galaiba iyakar galabaita.


Saleri:
Laila.
A hankali na buɗe idanuna da Goggo Laraba na soma haɗa idanu, idanuna sai ruwa_ruwa suke yi.
"Alhamdulillah Daddo Laila ta farka. Sannu Laila kinji, yaya kike ji a jikin naki" Cikin ƙarfin hali da tawakkali nace.
Bana jin komai sai rashin ƙarfi" Daddo tace.
"Sannu ƴannan Allah ya ƙara sauƙi."
Yunwa nake ji Goggo."
Da sauri Goggo Laraba ta fita, bata jima ba ta dawo da tuwo mai zafi yana ta turiri. Yaji ta baɗa mun da man shanu. Jikina har yana rawa, duk yawan tuwon sai da na cinye shi tas. Saina soma jin sanyi_sanyi na shigata. Jaririna nake ta kallo a hannun Daddo tana bashi ruwa. Matar malam ce ta shigo.
"A abun yayi kyau. Sannu Laila, yaya jikin kuma, ta farka kenan?"
Da sauƙi matar Malam.
Zuchiyata sai tunano mun wannan magen dana gani take yi. Amma nasan jaririn dana haifa mayu basu shafe shi ba. Dan ɗan gidan mafarauta ne, a zauren shigowa zauren gidannan akwai kafin Mayu a sagale a jikin azara, kusa da inda tsetsewalu suke guje_gujensu. ( Irin ƴan ƙananun tsuntsayennan da suke karakaina a zaurukan ƙasar Hausa ada) Adda'a nayi akan Allah yai mun tsari da dukkan abunda zai zama sharri a gareni.
"Ungo Laila ɗan sa mishi nonon ya ɗan dinga zuƙa. A haka har ruwan zai kawo. Hanuna har rawa yake yi dana karɓeshi. Tausayi da ƙaunar jaririn sai ƙara burunƙasa yake a zuchiyata. Lumshe idanu nayi, hawaye suka surnano mun. Nonon na zura mishi a baki, carab ya soma tsotsa, a fakaice na dubeshi, kamanninshi ya fito sak da Shehu. Matar malam tace
"Ki shirya ayi wanka, duk da magriba ta kunno, amman baza kiji daɗin jikin naki ba." Fita tayi, bata jima ba ta dawo.
"Laila maza fito muje kar ruwan ya huce." Kwantar da yaron nayi, na yafa fallen zane na fita. Muna shiga sakaki matar malam ta tura mun wani kwaɓaɓɓen magani a gabana tace.
"Mayar da ɗan durus ɗinki" mayarwa nayi. Ruwannan da mugun zafi haka matar malam ta dinga yaɓamun tana zaneni da ganyen darbejiya. Ta dinga zuba mun ganyen darbejiyannan a tudun cikina. Jini kuwa ya dinga fita, ina jin daɗi, jikina sai warwarewa yake yi. Hannu matar malam ta saka ta kwakwule maganin data cusamun. Ta bani ƙatuwar butar ƙarfe cike da itatuwa tace in wanke gabana. Na dinga wankewa a hankali, ina gamawa matar Malam ta rufeni da zani. Gudu gudu na koma ɗaki. Gaushi ya gama ɗumame ɗakin sai naji ni sawai iska mai daɗi na busani. Tsakin magani matar Malam ta zuba a wuta tace.
"Maza tsugunna Laila yanzu ƙarin da akayi miki zai haɗe." Tsugunnawa nayi maganinnan yana shigata ina mugun jin zafi da raɗaɗi,jini sai ɗiga yake yi a cikin garwashin, saida na haɗa zufa sharab sannan matar Malam ta ɗagani, na samu na sake kaya nayi ƙunzugu. Bacci nannauya ne ya kwasheni.


Daddo:
"Laraba yarinyar nan fa da ganinta tana cikin damuwa mai yawa. Jiya da daddare uban ya korota tayo yaji. Wallahi haka muka rasa sukuni ni da Ta Asibi a cikin gidannan. Tunda akayi auren Laila bata taɓa zuwa ganin gida ba. Jiyan da zata fita sai naga tana ɗingishi, amman na ɗauka nauyin cikine. Sai naga abun kamar fa ba hakan bane Laraba. Kuma tunda muka zo gidannan babu wata facala data shigo ɗakinnan da sunan dubiya. Sai Iyami da matar Malam kawai suke suntiri. Shehun ma sai ciccika yake yi. Ni jikina bai bani ba Laraba." Goggo Laraba tace.
"Nima naga hakan Daddo, amma ni zan rutsata ta faɗi abunda ke damunta ko zata samu sassauci a zuchiyarta. Ni tausayi take bani. Wannan yaro data haifa nina tabbatar sanadinshi matsalolin gidan aure zasu matsa ma Laila lamba.

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment