Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rakata ɗakinta, bata da wajan zama anan, nina haifeta bazan ƙi nema mata lafiya ba, amma bazata zauna mun a gida ba, hakkin cinta, shanta, makwancinta a wuyan Yawale kaɗai ya rataya." Inna Lami tace.
"Amma Malam ayi haka kuwa?
"Amma yi Lami, ga wannan jaka ɗaya ce ku tafi ku ga likita, ke kuma Musina ga muttala biyu ki riƙe, sai haƙuri. Ina kuka nace.
Baba dan Allah ka barni in zauna anan ɗin inna warke sai in koma" dubana yayi yace.
"Uwata in badan kinci darajar mai sunanki ba, dana baki kashi a gidannan ƴar jakar uba, ana nuna muku hanya kuna bauɗewa. Banyi zuchiya ba nace.
Baba wannan yaron ya dawo yau daga birni, amma yunwa tana damunshi, kuma idanun sahunshi du sun fashe sabida sashi a mari da akeyi a makaranta. Dan Allah ko zaka yi ma Yawalen magana yai haƙuri ya barshi a gida ya ƙara tasawa.
"Ke uwata tashi ki tafi. Yawale shi ke da cikakken iko a kanki da yaranki, ta yaro kyau take bata ƙarko, ke ashe in da kinsan wuyar da muka sha a almajirci zaki ɗauka baza muyi rai bane ko kiyi tunanin iyayenmu basa ƙaunarmu ne. Gatan da za'a nuna mishi kenan, ita rayuwa ƴar gwagwarmaya ce. Mu gashi yanzu mun gama tuni, kuma muna cin gajiyar almajirci. Lami ɗagata ku tafi. Abincinshi ya karɓa ya fice. Mahaifita ce ta bani kaya na sake, na sake ƙunzugu. Muna tafe ina kuka har muka isa asibitin, inna Lami sai rarrashina take yi, tana bani magana. Bamu samu likitan ƴan yoyyon fitsari ba, ranar Laraba kaɗai ake zuwa. Haka Inna Lami ta sani a gaba har gida. Bamu muka isa ba sai bayan magriba. Ɗakin Baba Huwaila ta kaini sabida tsabar kara irin ta iyayenmu. Sai Baba Huwaila ce tasa akayi kiran Baba Hauwa tazo.
"Ga Musina na dawo da'ita mahaifinta yace aba Yawale haƙuri ya barta ta zauna, zamu nema mata lafiya in sha Allah, daga asibitin ma muka wuto nan, sai ran laraba zamu koma dan bamu samu malaman kiwon lafiyar ba." Baba Huwaila tace.
"Musinan ce ba lafiya Lami? Ai mu bamu da masaniya, kinga Yanzu Yawalen ya bar nan ɗakin dawowarsu daga tafiya kenan shi da wanshi." Cike da mamaki Inna Lami ta dubeni. Labarta musu lalurar dake damuna tayi. Nan suka shiga sallallami, buɗar bakin Baba Hauwa tace.
"Ni ko ina da shawara Lami. Da kun bar Musina a gida tayi jinya, nake ganin kamar zata fi samun kulawa a can. Yawalen ma bikinshi shingin mako ɗaya zai auri ƴar aminiyata a can rugar malam harɗo can hayi, yau ɗinnan wanshi ya rakashi aka tsaida ranar, ga can lefen ma. Wasu sababbin Kumbuna na gani masu hawa uku, da babba da mabi da babba, da ƙaramin na saman sai walƙiya suke yi. Muƙut na haɗiye kibiyar kishi, idanuna suka cika tab da hawaye, ita kanta Inna Lami jikinta ya mace, tace.
"Ayya Allah ya sanya alkhairi, wannan amarya tako yi goshi. Baba Hauwa tace.
"Ku buɗa kuga kayan ciki mana."
Inna lami ta buɗa kumbunannan, kayan alfarma Yawale ya zuba ma amaryarshi, su atamfa mai ɗawisu, goji, banbalasta, leshi, karen miski, ɗankwali mai geza, ɗan duros, fatari, rigar mama, jan baki, gazal, sarkar murjani, da tsakiya, agogo, da takalma masu tsini, da mayafai. Kaya rigijibjib dai, dan banma gama kalloba, Inna Lami sai ɗaga kayan take tana mamakin irin uwar dukiyar da Yawale ya narka, amma ya kasa nema mun lafiyata. Inna Lami tace. "Amma Hauwa yarinyar nan a barta a ɗakinta ta zauna, zan dinga zuwa dubata, biki kuma da Yawale zai ƙara Allah ya sanya alkhairi."
"To tunda hakan kika ce ai saita zauna." Har ɗaki Inna Lami ta rakani. Sannan ta dawo ɗakin Baba Huwaila ta kwana. Ni kuwa ina kwance a ƙasa Yawale ya turo ƙofar ya shigo. Kuka ya samu inayi.
"Baki ji abinda bace miki bane shine kika wani dawo ko? To ga ɗakinnan ki zauna na bar miki. Fuu ya fice a ɗakin, kwanan damuwa da baƙin ciki nayi dare yayi mun tsayi sosai. Washe gari da sassafe Inna Lami tayi mana sallama ta kama hanya. Ni kuwa da wankin kayan fitsari na tashi. Labarin lalurata ya bazu har maƙobta, sai jaje aketa yi mini, Baba Hauwa tace in dena zuwa madafi aiki har saina warke. Ina dai zuwa inyi mata gyara, akan po nake zama a koda yaushe, sai zuwa dare kuma sai inyi ƙunzugu, kafin gari ya waye fitsari har gudu yake.
Yau Laraba, yau zan koma asibiti, amma na ƙudiri niyyar kai tsaye asibitin zani, gidan ma bazan shiga ba tunda ba ƙaunata suke yi ba. Ina gama aiki na nufi shiyyar su Baba Hauwa, na gyara mata ɗaki. A tsakar gida naci karo da Idi, murya ƙasa ƙasa nace dashi.
Ka sameni a bayan gonar mai gari yanzu, karka faɗama kowa" Fita nayi a gidan na nufi bayan gari. Zama nayi a kan wani kututture ina jiran zuwan Idi"


Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent, sannan idanuwansa suna kan ƴammata saboda ya samu sarauniyar girki, kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.

Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin👇🏻👇🏻

07068606171
08104335144
08179523215

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

*🤟GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARA TA 2023🤟*
*_Ina kuke masoyan gawurtattu uku ga su ssun dawo muku da wasu sabbin labaransu a wannan sabuwar shekarar, wannan karon salon gawurtacce ne, ku hanzarto kar ku sake ayi babu ku._*
_Sun shirya tsaf a wannan karon don kawo muku labaran da zakuyi fahari da su, tafiyar mai zafi ce sannan ta musamman._

*_Haziƙai kuma gawurtattu ukun sun shirya ne domin kawo muku gwarazan labaran da zaku yi alfahari da su._*

*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_


*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_


*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_


_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_


1 500
2 700
3 1000

_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank

_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._


_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171

*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*

0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171


*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023 SABON SALO SABON TAKU.*


_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_



MRS BUKHARI
MATA IYAYEN GIJI


BADI'AT IBRAHIM ( MRS BUKHARI)
( GAWURTATTU UKU)




*_🔥GAWURTATTU UKU🤟2023_*

*_TALLAH TALLAH TALLA🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️_*

_A HAYYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃💃🏻💃🏻_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894

*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._*
*_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA KUDIN KI IYA SHAGALINKI🤝_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU, INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN ZO 👏👏👏👏👏_*

SAMFOTI

LAMBA TA BAKWAI



Na ɗan jima a zaune a wajan.
"Baba! Baba!!"
Na jiyo muryarshi yana kirana cike da yarinta. Ko dana hangoshi gudu yake yi sosai, yana isowa ya faɗa jikina. Tsam na tiƙeshi fata nake dama mu dauwama a haka.
"Inna kinyi ma Baba magana bazan sake tafiya in barki ba ko?" Kanshi na shafa, nace.
Haba ɗannan ai wannan karatun da kake yi shine gatanka, kuma kayi haƙuri da duk abinda malaminku yake yi maka, gyaran tarbiyya yake yi muku. Kul na kuma jin kace bazaka koma ba, ka zamto mai bin umarnin mahaifinka a koda yaushe." Badan inaso ba na bashi haƙuri, nayi hakanne dan in kore mishi damuwa, gami da ƙarfafashi, ga ƙafafunshi duk raunin ƙarfen mari, ga datti da tsagewar fata har wani ɗoyi_ɗoyi yake yi. Ga ɗakin duhu da malaminsu ke rufesu a ciki, ni tsorona ma kar yarona ya rasa idanunshi, dan Mahaifinmu ya taɓa bamu labarin wani abokinsu ada lokacin suna wajan almajirci ya kasance mai yawan yin laifin da yasa kusan kullum sai an sashi a ɗakin duhu, daga ƙarshe wannan ɗakin shi yai sanadiyyar makancewarshi, sai gida aka mayar ma da iyayenshi shi. Babu wani mataki da aka ɗauka na shari'a shikenan an cuci iyayenshi. Na jima ina yi ma Idi nasiha, ina kuma kwatanta mishi rayuwa, mun jima sosai a wajan, daga baya mu kai sallama ni na nufi tashar Bodi, shi kuma ya nufi dandali.
Kafin in isa Azare na jiƙe sharab da fitsari. Hakanne ya tilasta mun zuwa gida dan in gyara kaina. Kayana dana bari rannan shi mahaifiyata ta ɗakko mun na saka nayi ƙunzugu, sannan tace.
"Naji cewar wai Yawale zai ƙara aure ko? Karma ki sake kice zaki ta da hankalinki a karon banza. Tunda kika taso kika tarad damu mu biyu da Lami a gidannan, kuma mun cakuɗe yaranmu ta yanda mu kaɗai muke iya banbancewa. Ki sanya salama a zuchiyarki, kici gaba da bin Yawale sawu da ƙafa. Zaki ci ribar yin haƙuri, Allah ya raya miki yaranku SU KULA DAKE." Inna Lami ce tayo sallama ta shirya tsab.
"Tarana na fito, Musina tawo mu tafi maza, harma fa nasa tun safe Yayanku yaje ya kama mana layi." Jiki ba ƙarfi na fito muka wuce."
In baka zuwa asibiti bazaka gane cewar ana ciwo ba. Nayi zaton masu yoyyon fitsari basu da yawa, amma abun mamaki sai naga a ɓangarenmu munfi mata hamsin. Harda ƙananun yara da basu wuce shekaru goma ba. Ashe nawa nafila ne, dan naga mata da dama da suke zaune amma fitsari na gudu a ƙasa daga jikinsu. Gun duk zarni. Ƴar nutsuwa na samu. Muna zaune ba'a soma ganin likita ba, kamar ma likitan baya nan. Sai muka ga wasu mata manya sun shigo. Sai nuna musu mu akeyi, sunata mana sannu da jiki. Basu jima da tafiya ba Likita ta iso. Nan kuma aka shiga bin layin shiga ganin likita. Duk wacce ta shiga sai in ganta ta fito da takadda. Har layi yazo kaina na tashi jiki ba kwari, Ƙasimu yana hannun Inna Lami. Tare muka shiga ɗakin ganawa da likita.
"Bismilla zauna" waje ta nuna mana.
"Musina ko zaki iya bani labarin sauyin yanayin da kika samu a jikinki kamun wannan lalurar ta ɓullo miki?" Hawaye na soma zubarwa, nama kasa bata amsa. Likitannan ta dubi Inna Lami tace.
"Baba tare kuke da mai gidan nata ne?"
"O'o ƴannan mu kaɗaine, ni uwarta ce, sai yaronta na goye. A Saleri take ba anan ba.
"Amma ina mai gidanta? Ai ya kamata ace shi zai rakota. Wai me yasa maza suke gudunmu da zaran laruri ya samemu, kuma duk yawancin lalurin sune suke zama sanadiyyar ɗaura mana, sai su dinga gudunmu in matsala ta samu. Nayi imani da shine wannan lalurar ta sameshi, ƙarshenta ita zata rakoshi asibiti, kuma taita ƙarfafa mishi guiwa. Baba Lokacin da tazo haihuwa a gida ta haihu ko asibiti?
"Ƴannan a gida ta haihu, bata taɓa zuwa asibiti ba dai_dai da sunan awo, sanadiyyar wannan lalurinne yasa muka zo." Ɗan rubuce_rubuce tayi sannan tace.
"Musina kinyi doguwar naƙudane a lokacin da kika haifi jaririnki, sannan watanshi nawa ne? Ki saki jiki kiyi mun bayani asibiti ana zuwane dan a samu mafita, ba'a ɓoye komai. Baki ga tarin mata masu yoyyon fitsari a waje ba? Wasu ma aiki za'ayi musu, ga wasu tari da yawa suna kwance a cikin asibitinnan an basu gado." Daurewa nayi nace.
Nayi naƙuda ta kusan kwana biyu, kuma iyayen mijina sun hana a kawoni asibiti, dan alokacin mai gidan yaso a kawoni. Ko dana haihu har akayi suna ban dawo dai_dai ba. Yanzu wata huɗu da haihuwar tawa. Kwana takwas yau da faruwar abun."
"Okey jikin naki ma da sauƙi kuma kinyi kyan kai sosai da kika zo asibiti, ba wajan maganin gargajiya ba. Zan ɗauraki kan wata shawara Musina mu gwada na tsawon sati biyu mu gani. In kika koma gida kita shan ruwa kawai, ko da ƙishi ko babu, fitsarin da kike yi zai ƙaru amma karki damu da hakan. In anyi sati biyu saiki dawo asibiti. Sannan in ba dai dare bane ya rufa ba, ki dena saka ƙunzugu, ki dinga barin wurin yana samun iska dan gudun wari da kuma gujema ƙwayoyin cuta masu cinye al'aurar mata wato Infection sanyi kenan a hausance. Sannan akwai wata gidauniya data ajjiye mana forms guda hamsin, kuma ga mata masu lalurar fitsari kawai suka bada umarnin a raba. Wannan gidauniyar zata ɗebi mata masu lalurar fitsarine ta horar dasu kan sana'a irinsu ɗinki, haɗa mandula, da sabulun soda, da omo na gari, da man shafawa. Kuma a kyauta zata horar daku, sannan ta raba jari gareku in zata yaye ku. Ga Form nera nera biyar zaki bayar a baki form. Za'a gudanar da aikinnan a filin firamare tamu, ina fatan zaki zama ɗaya daga cikin waɗanda za'a horar ko Musina? Bana fatan mijinki ya hanaki wannan abun kiyi ƙoƙarin kasancewa ɗaya daga ciki, dan zai taimaka miki ki tsaya da ƙafafunki." Ajjiyar zuchiya na sauke, jakata na buɗa na ciro nera biyar kamar yadda tace. A gabanta ta ajjiye Form ɗin tace.
"Bari in cike miki, sannan ɓangaren wacce sana'a kika zaɓa?.
Likita aina iya karatu da rubutu, na ajimi da hausar boko nayi firamare a makarantar gwamnati ta Azare." Murna naga wannan likitan nayi tace.
"Amma iyayenki sunyi ƙoƙari sosai Musina. To ga form ɗinki sai ki cike, nan da sati biyu za'a soma horas daku, shima horarswar zata kai sati biyu ana yinta. Sai kuma a yayeku,a ɗan baku jari da zaku dinga jujjuyawa." Godiya Inna Lami tayi ma likitannan sosai. Mu kai mata sallama muka fito. Har saida Inna Lami taga bodin mu ta tashi, sannan ta nufi gida.
Zuchiyata cike dake fal da fargaba. Dan nasan ko ina shure shuren mutuwa dafara na fitowa a bakina Yawale bazai amince da wannan ƙungiya dana karɓi form ba. Ko ya amince nayi imani Baba Hauwa bazata taɓa amincewa ba. A zahirin gaskiya inason koyan sana'ar haɗa mandula, dan mandula in zamu saye, sai dai muyi sallahu a tawo mana dashi daga Azare, amma mu bamu dashi a ƙauyenmu. Zanso im koya ko dan in dogara da kaina, in kula da yarana. Dan nasan Yawale bazai kula dasu ba. Gashi ina da buri akan yarana mata in Allah ya bani, ina da burin ganin sunyi ilimin boko mai zurfi. Dan inason karatun boko sosai. Inna tsaya akan sana'a sai in kula da karatunsu ai. Da waɗannan saƙe saƙen muka iso madakata. Koda na shiga gidan babu wanda ma ya amsa sallamata, sai tottoshe hanci suke faman yi. Kai kawai na gyaɗa nayi shigewata ɗaki. A jiƙe na dawo sharab, kayan jikina na cire, na ɗaura zani a ƙirjina na fita tsakar gidan. Kayan Fitsarin na wanke, sannan na shika sakaki na ɗauraye jikina, na fito tsakar gida na ɗaura alwala na koma cikin ɗakina.
Rayuwa haka tai ta garawa, har gida ya cika daf da jama'ar biki. Ranar likinin aka soma bikin bisa ga al'adar ƙauyen Saleri. Ranar litinin: In dare yayi Babannin Amarya zasu tafi gidan uwar dakinta, a kamo ta dakyar qawaye sun ɓoyeta, a fisgota, a sa mata lalle wanda aka kwaɓa da turare, sai a shafa mata suyi ta kuka ita da qawayenta."
Ranar talata: za a yini a nata qunshi amarya da qawayanta, Haka laraba da yamma, babbar qawar Amarya, da mabi da babbar ƙawar Amarya, za su sai lalle a taru a dekashi adama da ruwa , su fito qofar gida kowacce ta daura tsohon zani, ba riga, mamunansu a bayyane, ayita zubawa juna duk su jiqe, a hakan za'a tafi gun angwaye ayi ciniki su biya, a dawo gidan da amarya take wato gidan uwar dakina . Da yawan samarin ƙauyan Saleri, a rana irinta yau, suke zaɓen matan aure, sabida mamansu a buɗe suke zuwa, mai so saiya zaɓi wacce mamanta yayi dai_dai da ra'ayinshi. Bayan sun koma gidan uwar ɗakin Amarya, sai su yi wanka. To in dare yayi kuma, gidansu ango zasu zo su kawo kayan sakun lalle, zasu kawo dakakken lalle, turmin zani biyu, sabulu, man shafa, turare, takalmi, gazal, jambaki, duk kowanne guda bibbiyu, da bokiti, baho, moda, kofi, se goro da minti za'a bara goro a faranti kowa ya dauki minti goro ɗaya, minti biyu "
Ranar laraba: Asuba nayi baza ayi salla ba za'a zagaye garin baki ɗaya a nata waqoqin amarya iri _iri sai a wuce gidan wali nanma a yita waqa shima seya biya kudi tukunna ayi sallah a karya kumallo. Yamma nayi se kokuwar tsifa ɗaya bayan ɗaya za'a riqa yi amarya tana dokawa, ƙawayen amarya sai su taru a kadata ɗaya ta zauna tana tsefe mata kai, saura kuma suna waqa har agama. kowacce za ta duqa amarya ta zage tayi mata dundu abaya sau biyu, sai su tafi gun angwaye a biya su. Daga nan sai su wuce gidan amarya. Rufar qofa kafin akawo amarya, za su rufe ɗaki nanma sai angwaye sun biya sannan su bude a saka amarya.
Ingari yawaye za'a sami budurwar da tsawanta yayi dede dana amarya se tasa kayan amarya a zagaye gidan dangin miji, ana waqa wannan su bada taro wancan su bada sisi da haka har su gama a dawo. In dare yayi ko wacce zata dafo abincinta, sunan abin alibidi a yi taci a dakin amarya, samari su cika kowa da budurwarsa yaci abinci ya bata kudi juma'a. kafin hakan da safe zuwa dare dangi za su yita kawo gudummowarsu atara kaya a fitar da tsaraba kaya Lodi_ Lodi akai gidan su ango"
Asabar: Yinin gidansu ango, za'a yanka tunkiya abawa "yan matan amarya wuya dashi za suyi abinci suci idan anzo cin abincin, sai asa zobe aqasan abincin aboye ana cikin cin abinci wacce ta zaro zobe ita za'ayita tsokana"
Lahadi: kashe wuta, za,a kawo ma amarya sauran kayanta a wanke tukunyar da'aka,aro, baqi kowa ya tafi biki ya qare. Haka al'adar bikin aure a Saleri yake, har gobe, amma bamu san dame jibi zata zo ba.
Haka ne ya gudana a bikin Yawale. Ni kuma inata faman jinyar kaina, na zama abun ƙyama babu mai raɓata, aka yi ta mun waƙe_waƙe a tsakar gida. Yawale kuwa bana ma jin ɗuriyarshi sam tunda ya tare a ɗakin amaryarshi. Sai a bakin matan gida nake jin sunan Amaryar Yawale wai sunanta Kumatu. Amarci Yawale yake ragargaza shi da Amaryarshi Kumatu, dan ina jiyo labarin yadda suke gudanar da amarcinsu a bakin matan gida. Ni dai ina ɗaki ina jinyar kaina, da zuchiyata, dan in nace bana kishi ma, na yaudari duk wanda zai karanta labarina. Ana washe gari sati biyu da zuwa na asibiti, na fito da zummar zuwa ɗakin amarya dan inyi magana da Yawale, ganinshi ma ai yafi ƙarfina a yanzu. Gabana sai faɗuwa yake yi, dan bansan yanda zamu kwashe da Yawale ba. Amma na shirya duk abunda zance mai, dan dai ya barni inje koyon sana'arnan.
Assalamu alaikum' Assalamu alaikum" daga ciki na jiyo muryar kumatu tana cewa.
"Wata sabuwar alaranmiya muka samu ne a gidan? Koma waye in zai shigo ya shigo. Yawale yace
"Musina ce, uwar iyayi ake faɗa miki"
Da ba dan ba dan ba da yau anyi badan, dan ji nake kamar in shiga in shaƙo wuyan Yawale inta jibgar matsiyaci har sai naga ya dena motsawa. Jiki a mace nasa kai na shiga ɗakin.
Yawale yana shingiɗe a ƙasa anyi mishi shinfiɗa irinta sarakai. Yana kan faifan tum_tum, guiwar hannunshi dafe da tum_tum. Ga gashsshen zabo a gabansu suna ci, harda lemun lamurje a gabansu, Kumatu sai wani fifita take yi mishi, harda yi mai sannu, kamar wanda jaki ya ka dashi.
Ɗakin nabi da kallo, caɓi lallai duk inda akayi Kumatu Mahaifinta tahirine dan an zuba mata dukiya a ɗaki. Gado biyu ne a ɗakin, maulidi da bono. Ga kwaba bango guda mai ƙofofin glass, can saman kwabar ma tangaran aka jera mata, cikin kwabar kuwa harda samira mai kala. Ga kwalla hawa kusan goma, ga fanteku suma hawa hawa, haka kumbo ma hawa hawa. Bango guda kuma akai mata jeren tasoshi sama da seti sittin. Ga tum_tum guda uku tare da faifain shi. Ga ƙore a rataye a ragaya fin goma, ga shinfiɗa mai taushi a ɗaki, sai ƙamshin turaren binta sudan ke tashi. Ita kuma Kumatu sai ƙamshin turaren jan miski take yi. Ajjiyar zuchiya na sauke, inajin nunfashina na bazaranar ɗaukewa.
"Musina ya kamata ki faɗi abunda ya kawo ki ko? Sabida kar kiyi ma Kumatu fitsari a ɗaki." Cewar Yawale kenan. Buɗar bakin Kumatu tace.
"Ga fitsarin manya da mugun zarni" Dauriya na aro na yafa ma kaina. Na cije nace.
"Dama gobe ne ranar komawa asibiti. Kuma ita likitan tace daga gobe kullum zanje asibiti harna tsawon sati biyu..."
"Bani da ko ficika Musina, ba kina da kayan

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment