Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ummi. Kusa da ita Zarah tazauna tace a,a ba lafiya ba, naga kindawo kamar wadda aka koro, ko jakar hannu banganki da ita ba se bakar leda, bare jakar kaya. Jidda tace kede Ummi kawai ki godema Allah nadawo lafiya, bakiji ankasheni ba. Zarah tace Jidda kisa kuma meyafaru? Tace Ummi kwanan mu 10 agidan yan fashi, babu abinci me kyau, se wahala dasuke bamu, intakaita maki ma, kawata damukaje london tare sunkasheta, nima da kyar wani yaji tausayina yafito dani yabani wannan kudin ya sakoni motar kaduna, amma sun kwace mana komai, bakiga ko dan kunnena na zinari babu ba. Gaskiya munsha wahala, gashi bamusan garin da,a kaimu ba. Lokacin damuka taho daga air pot dayake da dare muka sauka ashe me taxi din barawone, yafesa mana wani abu, bamu kara sanin inda muke ba, amma nasan ba,a kaduna muke ba, dan kafin na iso nan munyi tafiya me nisa.

Kuka Zarah tasa tace shikenan yanzu baki samo komai ba, duk irin zaman dakikayi haka suka rabaki da komai? Amma de Allah ya isa wlh, ina nan ina jiran samun kusi masu yawa amma wasu sunfini so. Jidda tace wlh kuwa Ummi dana dawo da jakata, dakeda talauci har abada. Zarah tace Allah ya isa wlh bamu yafe ba. Jidda tace Ummi Ina Jalila fa? Taje gidan kawarta, kinsan ai tadawo tagama karatunta. Jidda tace lallai kam tayi kokari, ina fatan de bata barinki cikin rashin kudi? Zarah tace wannan yarinyar idan da ace ita zata rika ciyar dani ai dana mutu, babu inda take zuwa, ko saurayi bantaba jin yayi sallama da ita ba. Duk yanda akayi tagogo kashin tsiya agurin waccan AGOLAR. Dariya Jidda tayi tace ni wlh Ummi harna manta da ita, ashe tana duniyar. Kince tayi aure ko? Emana, takusa fitowa ma. Jidda tace haba keko Ummi tunda de kinmata aure kawai kibarta tayi zamanta agidan mijinta, idan yagaji yasaketa, amma yanzu mezatayi maki idan tadawo? Babu komai, kotadawo ma korarta zanyi, to kingani ai babu amfani mugunta ko,,,, ke tashi kibani guri banason wannan shirmen surutun naki. Dariya Jidda tayi tace nide nawuce daki bacci zanyi kuma kada atadani.

Zaune suke bayan sunyi sallar magriba sun gama cin abinci. Jalila tace wlh Falak tafiya zanyi banason mijinki yajamun fadan ummi, damma Dady baya gari. Falak tace yanzu zedawo kiyi hkr,,, sallama sukaji, Sameer ne, yashigo yana fadin afuwan Jalila wlh Saleem ne ya tsaidani yanzu hakama tare muke. Jalila tace aiko yanzu nake cema Falak zantafi. Sameer yace Dear dauko hijabinki ga Saleem nan zeshigo kugaisa, tashi tayi tashige daki shi kuma yafita.

Atare suka shigo da sallama, Falak ta amsa, tana fadin manyan baki garemu yau ashe, Saleem yace gaskiya kam, kuma masu laifi ba, tunda gashi seyau muke zuwa ganin amarya. Zama yayi bayan sungaisa Falak tace Jalila kawo masu ruwan mana, Jalila tafito dauke da tray tayi sallama tashigo. Tunda tashigo Saleem yakafeta da idanu harta aje tray din ta gaidashi amma bemasan tanayi ba. Dariya Sameer yayi yabugi kafadarshi yace abokina ina katafi ne ana ta gaidaka kayi shiru. Murmushi yayi yace lafiya lau Jalila ya gidan?

Jalila tayi murmushi tace lafiya lau, Sameer yace to kode.... amma de bari inyi shiru. Falak tace a,a kadeyi shiru zamuji koma menene, Jalila tace Uhm nide zanwuce. Saleem yace tonimade tafiya zanyi tunda mungaisa. Sameer yace ina yunwar ta tafi kuma? Kai ya sosa yace ai nakoshi ma, idan naje gida nasha tea. Muje sena saukeki ko tunda nima fita zanyi. Sameer yace kamade yi magana, idan kadawo nasan dole kabiyo tanan sekaci abincin.

Jalila tace a,a kabarshi nagode, sameer yace a,a kanwata ai abokinane bakomai kije ya kaiki, kinsan mu bamuda mota ammade tana hanya zuwa jibi zata iso. Dariya sukayi, tace to Allah yakawota, daki Falak taje tadauko mata turaruka , har kofar mota suka rakasu, Sameer yaciro 5k yabama Falak yace tasaka mata ajaka, kama jakarta tayi tace gashi inji megidan yace abaki. Jalila tace haba dan Allah kubarshi, Sameer yace ashe dama kanwa tana kin karbar kyauta daga yayanta? Murmushi tayi tace a,a nagode, to. Haka suka tafi suna tayima Saleem tsiya.

Dije ce da Asabe zaune adaki suna fira, Asabe tace waini Dije kina ganin yanzu Zarah tafara juya mana baya, wlh jiya 500 takaina banida ita, yanzu ko awaya nakirata bata cika dauka ba, gashi tadena zuwa gurin boka bare musami rabon mu. Dije tace ai dole musake dabara, ammafa idan zaki iya, Asabe tace haba Dije, kode kin manta ko wacece Asabe ne? Tunda na iya kashe rai saboda abin duniya babu abinda bazan iya ba, kawai fadi shawararki. To asabe nafarko de dole kibar mijinki, dan garin zamu bari. Mtswwww Asabe taja tsaki tace danna bar mijina shine wani abu, kema kinsan dayana da maiko da tuni yazama gawa nakara gaba, amma tunda zamuci tajikin diyarshi ya huta, yakikeso ayi?

Urs,
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[6/15, 3:15 PM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ»AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@ (H,O,N,A)

Part 105..... 110

Dije tace Asabe, agaskiya munyima Zarah hidima, kuma tasamu duniya fiye da yadda baki zato, amma acikin kudin datasamu, babu wani abun arziki data yimaki bare kumani. Dan haka lokaci yayi dazamu nuna mata asalin halinmu, kinga damun samu sa,a kawai semubar garin, munufi lagos.

Akwai wata kawata datake zaune acan, zata bamu masauki, kinga semu kama sana,a me kyau, muma mushigo gari. Asabe tace gaskiya kawata kinkawo shawara me kyau, kibari zuwa sati mezuwa zanje kadunan, kibar sauran aikin ahannuna.

Bayan Saleem ya,aje Jalila agida sukayi sallama ya amshi numberta, dan tun ahanya yagabatar mata da abinda yake ranshi, itama agurinta hakan yake, dan tunda taganshi ita taji ya kwanta mata, babu bata lokaci ta amshi tayinshi, dan itama ta kosa tabar gidan, dubu 20 yabata, da kyar ta amsa, sannan yawuce.

Tana shiga gidan tagaishe da megadi tawuce ciki, adaki tasamu Zarah tafito daga wanka, tace Ummi sannu da gida, yauwa Jalila harkin dawo? Tace wlh kam. Zarah tace to albishirinki, tace Ummi goro, Jidda tadawo dazu fa. Kai Ummi da gaske? Emana, tana dakinta bacci takeyi dan kosallar magrib batayiba, tace kada atadata, batajin dadi.

Kai amma naji dadi wlh, Allah sa kada Yaya Jidda takara tafiya tabarmu, ai itama tace babu inda zata kara zuwa, domin tsautsayine asamesu, har kawarta dasuka tafi ankasheta..........
Anan tabama Jalila labarin da Jidda tabata, Jalila harda kwallanta, sede akasan zuciyarta bata yarda da labarin ba. Wayyo Ummi yaya jidda taci wuya, Allah yakara tsarewa. Kudin da Saleem yabata tamika ma Zarah, washe baki tayi tace Jalila wannan kudinfa daga ina? Ummi agidan kawata danaje gurin dawowa muka hadu dawani Saleem, shine yadauko ni yamaidoni gida, shine yabani kudi.

Kai amma naji dadi wlh, motarshi ce yadaukoki ko? E Ummi tashi ce, to aikin meyakeyi haka? Shine manager a kamfanin babanshi. Toshi baban nashi aikin meyakeyi? Eto yacemun yana aiki aAbuja kuma yana cikin manyan gwamnati.

Kai amma wannan yarinya Allah yayi maki albarka, gaskiya yau kinfaranta mani rai sosai, daam nace inde ina raye ,ya,yana bazasu auri talaka ba. Sosai Jalila taji dadin addu,ar da Zarah tayi mata, dan rabon da tasa mata albarka harta manta, godiya tayima Allah dayasa Saleem yafito daga gidan masu kudi, duk da ita ba burinta kenan ba, amma gashi ta dalilinshi Umminta tana saka mata albarka.

Idan yakara zuwa, ai seki kawoshi mugaisa ko, idan Dadynku ma yadawo zanyi mashi maganar, bazamu tsaya sanya ba, tunda dama kingama karatunki kawai yafito ayi bawani daukar lokaci za,ayi ba. Dama nakosa nima inga nayi biki agidana, tunda waccan sakarar yayar taki taki maida hankali tafiddo miji ai gara kiyi ki kyaleta. Murmushi Jalila tayi jin yadda kudi suka sa Umminsu saurin juyama Jidda baya. Ummi bara inje inyi isha,i idan ta tashi semu gaisa. To Jalilata idan kingama akwai abinci akitchen idan kuma bakisonshi se indafa maki wani. A,a Ummi naci abinci ma. Fita tayi tana mamakin hali irin na Umminsu.

Har tagama sallah tayi duk abinda zatayi, takara fita domin dubo Jidda amma haryanzu bata farka ba, harzata fita taga wani magani abisa side drawer zuwa tayi tadauka, mamaki ne yasauka akan fuskarta ganin sunan kwayar dake jikin maganin. Wasu irin zafafan hawayene suka rika sauko mata, kara kallon Jidda tayi, se anan taga irin ramar datayi da kuma wani irin haske, daukar kwayar tayi tafita da ita, ballesu tayi duka tazuba amasai ta yarda ledar maganin abolar waje. Zama tayi tana ta tunani, can wayarta tayi kara, murmushi tayi ganin wanda ke kira, kwanciya tayi suka shiga firarsu ta sababbin masoya.

Bayan kwana 2 soyayya me karfi dashiga tsakanin Saleem da Jalila, duk wani tarihi na gidansu Jalila babu abinda Sameer da Falak basu fada ma Saleem ba, kuma hada goyon bayan Jalila dan aganinta be kamata taboye mashi wani abu daga gidansu ba, dan tasan wata rana dole zeji.

Sosai Saleem ya tausaya ma Jalila ganin irin uwar da Allah yabata amma gata ita daban acikin gidansu, jin labarinta be rage komai na sonta aranshi ba, sema karuwa dayayi, kuma yasan baze samu matsala agurin Abbanshi ba, dan Mamanshi tarasu.

Har gida yaje yagaida Ummin Jalila kuma sanin halinta nasan kudi yasa yayi mata kyauta me tsoka, sosai taji dadin zuwanshi, Jidda kuwa tunda taganshi takasa dauke idonta akanshi, sede sanin yafi karfinta, yasa ta maida kwadayinta ciki, sede takasa fita su gaisa sema fita datayi tabar gidan. Zarah tace ma Saleem nan da kwana 2 idan Alh yadawo zatayi mashi maganarsu seyadawo sugaisa.

Jidda abin duniya yafara isarta, babu abinda takeso kamar namiji, gashi bata da no saurayinta ko daya, kullum seta yi wanka tafita kozata samu dan hannu sede haryanzu bata daceba, har gidan su kawarta Ameera taje amma tayi rashin sa,a akace mata suntashi daga unguwar, gashi kuma bata da no dinta. Ahanyarta ta dawowa ce tahadu dawani dan bayan unguwarsu, irin yan iskan unguwane, mashayine na karshe, waishi Viju, saboda tsabar bin mata abokanshi suka samashi Viju.

Kamar da wasa yayi mata magana babu bata lokaci Jidda ta amince dashi, anan sukayi exchanging no tawuce gida tana murna. Tun daga ranar suka fara soyayya, da farko be nuna mata dan hannu bane, amma ganin dayayi idan harsuna fira batajin kunyar kama hannunshi tayi ta wasa dashi hakan yasa yayi mata tayin zuwa shagonshi, babu bata lokaci ta amince.

Daga ranar suka fara aikata masha,a sosai sukejin dadin junansu , tunda Viju yasamu Jidda yadena kula kowace mace, dan Jidda tana gamsar dashi sosai, kuma tanuna mashi yayi amfani da ita ta ko ina, dan Joseph ya saba mata da hakan, shima Viju tunda yafarayi yaji dadi daganan shima yacigaba duk ta inda yaga dama, wani lokacin har kwana jidda takeyi adakinshi, sede babu wanda yasan bata kwana agida se Jalila, kuma tayi shiru bata fadama Zarah ba. Gashi yakara koya mata shaye shaye hardasu Sigari takesha, sede bata sha agidansu, gashi taba bashi kudi sosai, dan idan batada kudi na Zarah take sata, dayake itama Zarah kanta batasan yawan kudin ba, hakan yasa bata gane ana diba.

Aranar da Alh, yadawo da dare Zarah tayi mashi maganar saurayin Jalila, sosai shima yaji dadin maganar, kuma yace tafada mashi gobe yazo yanason ganinshi, koda yadawo Jidda ba,a gida ta kwana ba, hakan yasa basu haduba. Jalila tafada ma Saleem, yace mata to zasu zo shida Sameer.

Washe gari sukazo, har cikin falo suka shiga, bayan sun gaisa da Alh da Zarah, ta tashi tabasu guri, anan Sameer yayima Alh bayanin Saleem, ashema yasan Babanshi abokinshine, nan take yakirashi awaya suka gaisa yayi mashi bayanin komai, shima yaji dadi sosai, jin yarainyar da danshi yafada mashi ze aura yar abokinshi ce. Anan yace cikin week end zasu shigo domin atsaida magana. Sosai Saleem yaji dadi yakusa mallakar Jalilanshi, daga haka sukayi masu sallama, anan Zarah tafito sukayimata sallama suka ajemata bandir din kudi.

Zaune suke agidansu Baba mairo, Falak se cin kwadon zogala takeyi suna labari, Baba mairo tace lallai wannan jikan nawa yana da kwadayi, waiko Sameer kunje asibiti kuwa? Sosai kai yayi yace munje Baba, to wata nawa ne, cikin? Watanshi 5. A lallai Allah yaraba lafiya. Murmushi Halima tayi tace ameen.

Falak tace Baba dan Allah inaso inje ingaida Dady nide kobaze amsa ba, wlh inason ganinshi, kwana 2 ina yawan mafarkin Umma tanacemun meyasa nabar Dady kibarni naje naganshi, koda hakan yana nufin Ummi zata dauki mataki akan aurena. Ta goge kwallan data zubo mata.

Baba mairo tace kinyi gaskiya Falak, nima nayi wannan tunanin bakomai, gobe zaku iya zuwa keda mijinki. Sameer yace Baba sede mubari ranar lahadi, domin gobe Zanje inter view kinsan nafada maku Abban Saleem ya bada takarduna toshine ake nemanmu gobe anan genaral hospital, kuma ranar asabar iyayen Saleem zasuje neman aure gidansu Jalila, shiyasa nace mubari se ranar lahadi.

Baba Mairo tace to Allah yakaimu ko kuwa Halima? Tace hakane Baba duk abinda kikace yayi, Allah de ya tona asirin wannan mata. Baba mairo tace Ameen. Sameer yace nizan tafi shago Baba mairo tace zoka dauki matarka kutafi, Falak tace kai Baba mairo tsakani da Allah fa yanzu mukazo, kuma yace seda dare zamu koma. Dariya yayi yace kema de kinsan halin Baba mairo, yizamanki tunda inada mota anjima zanzo indaukeki. Baba mairo tace ohode tunda bazaka iya barinta ta kwana ba, dariya yayi yafita.

Jalila ce da Jidda zaune afalon Umminsu, Jalila tanayima Jidda kitso, Jidda tace waini Ummi ina Mairo tunda nadawo banganta ba? Uhmm wama yasan inda take kota raye kota mutu, tunda tacemun zataje ganin gida bankarajin labarinta, amma Ummi ai da kinsa an tambayo maki ko lafiya ko, kai dalla can rabu dani, daga temako se intsaya ina nemanta, ita tasani idan bata dawo ba, har bikin Jalila wata kwai zandauka, dama na daga mata kafane kozata dawo, amma tunda bata dawoba shikenan. Murmushi Jalila tayi batace komai ba.

Zarah tace Jidda kinga kema dakin fiddo miji da se ahada bikinku tare dana Jalila. Jidda tace nifa Ummi banaso kinamun wani maganar aure, itama data samu mijin ai ba rawa tayima Allah yabata ba, nima kuma zansamu. Tsaki tayi tace ke Jalila tashi muje daki ki karasamun kitsona. Zarah tace E lallai Jidda kingirma, yanzu ni kikema tsaki? Ke kika sani wlh kije duniya ce zak...... saurin toshe mata baki Jalila tayi tana kwalla tace haba Ummi, dan Allah kidena saurin yima Yaya Jidda baki, addu,a yakamata kiyi mata. Hannun Jidda Jalila taja suka bar dakin. Zarah tace aikin banza, kawai kizo kizaunamun agida baki anfana mani da komai, ni narasa wane irin abu akayi mata ma, ada yarinya ta taso da farin jini, amma yanzu kamar wadda akama asiri, gaba daya samarinta sun dauke kafa, dole inje gurin boka kema kisamu kiyi aure.

Aranar asabar iyayen Saleem sukazo, kuma an tsaida rana wata 1, kudin neman aure suka bada naira dubu 100, Zarah kamar zata zuba ruwa akasa tasha, saboda farin ciki, bayan suntafi tace ma Alh, yabata kudi taje dubai tahado ma Jalila kayan daki. Alh yace amma ai dakin bari an siyamata anan ina ganin zefi. Zarah tace to matsolo wlh baka isaba, kawai bikin diyar tawa zakace wai anan za,a mata kayan daki, da kudinka da komai, ko waccan AGOLAR BANZAR FALAK dazatayi aure nawa kabada. Kanshi yadafe jin abinda Zarah tafada, kallonta yayi yace wane suna naji kinfada yanzu. Dif Zarah tayi jin irin katobarar datayi, dan bata manta kashedin boka ba, yace kada takira sunan Falak agabanshi, idan tana kiran sunanta ze iya tunawa da ita, bare kuma su hada ido da ita.
Cikin sauri tace ina nufin ko sadaka akazo nema agurinkana kayan aure ai yakamata kabada kudi masu yawa bare ace auran diyarka na farko. Tonaji, yanzude kamar nawa kike ganin zasu isa? Murmushi tayi tace Eto kagade gidan masu kudi Jalila zatayi aure, idab bamu zuba mata kaya masu tsada ba, kaima kasan rainamu za,ayi kawai kabada million 6 ina ganin zasu isa. Shiru yayi bece komai ba. Cike da tsawa tace kobaka jini ba? A,a najiki waida inaga kamar sunyi yawa ne, dan duka million 10 ce a account dina kuma wasu kaya nakeso insiyo. To wlh seka badasu, idan yaso kasiyo kayan dasauran kudin. To to naji yanzu check zanrubuta maki ko kuwa transfer zan maki? A,a kamun transfer kawai, kuma yanzu zakamun tavwayarka tunda gobe babu aiki. Anan take yatura mata million 6, sosai taji dadi dan ta aiyana aranta 2 zata raba tadauki rabi.

Washe gari Asabe ta dira gidan Zarah, a yamutse ta karbeta, sewani shan kamshi take mata da kyar ma ta amsa gaisuwarta, Jalila cema ta kawo mata ruwa da abinci. Asabe tace waini kam hajiya kinajin labarin Falak? Yamutsa fuska tayi tace niharna manta ma da ita amma de ai batayi shekara da aure ba ko? E gaskiya batayi ba, yauwa, dan ina jiran lokaci yayi, kinsan Itama Jalila ankawo kudin aurenta.
Asabe tace kai amma naji dadi, amma ina fatan gidan maiko ne ko? Se alokacin Zarah tayi murmushi tafara sakin jiki suka fara magana, anan tafadi mata komai, cikin kissa Asabe tasaka ta tafada mata hada yawan kudin da Alh, yabata. Tunda taji yawan kudin tace lallai muma wahalarmu takusa zuwa karshe.

Haka sukayita fira har la,asar Zarah tace Inna yakamata kitashi kitafi kada dare yayi maki, sakin baki Asabe tayi tana kallonta, dan ita da shirin kwana tazo, hadiye bacin ranta tayi tace toshikenan hajiya bara intafi. Dubu 1 tabata tace tahau mota, atare suka fito waje, dede lokacin megadi yana bude gate, Asabe tace ko Alh, ne yadawo ma, Zarah tace bashi bane, dan yacemun seda dare zedawo, kuma bema da irin wannan motar. Tsayawa sukayi suna kallon motar harta tsaya, ganin wasu kyawawa sunfito daga motar yasa Zarah tace kai yau kuma wane irin yan gayun baki ne mukayi haka, har suka iso kusa dasu basu sani ba.

Falak tace Assalamu Alaikum sannunku da gida, Zarah tace yauwa sannunku, mushiga daga ciki mana, Asabe tace tonima bara muje mugaisa ko, Zarah tace to shigo. Bayan sungaisa, Zarah ta kalli Falak da sameer tace sede bangane kuba. Sameer yayi murmushi yace Hajiya dasauri haka ko shekara ba,ayi ba, kice baki ganemu ba, aiko ita yakamata ki ganeta.

Zarah tace idan da naganeku ai bazan tambaya ba. Sameer yace hakane, to sirikinki ne, Sameer, wato Asid, da matarshi Falak....... zunbur Zarah da mairo suka mike tsaye jin kalaman Sameer.

Urs,
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[6/16, 12:55 PM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ» AGOLAH !!!Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@(H,O,N,A)
Part 110..... 115

Cike datashin hankali Zarah tace Asid yaushe ka koma haka? Dama ba dan iska bane kai? Meyasa Mairo ta munafunceni? Zubewa kasa tayi tana kuka, Murmushin mugunta Asabe tayi, sannan tadauki kayanta tace tofa, Allah ya kyauta, nizan wuce hajiya kada dare yayi mun.

Saurin kamota Zarah tayi tace haba Inna kibari ki kwana mana, ai yanzu yamma tayi. Komawa tayi tazauna tana dariya aciki ciki, Sameer yace Ummi kiyi hakuri Baba mairo bata munafunceki ba, tayi abunda yadace ne, domin kinkasa rike marainiyar Allah shiyasa tayi kokarin kubutar da ita daga sharrinki.

Anan Sameer yafadama Zarah komai, kuka kawai takeyi. Falak tace Ummi dady bayanan ne? Dadyn Ubanki, ke awa dazaki tambayeshi? To wlh tunkafin inkirga 3 kubacemun daga gidan nan, cuta ce kun cuceni, bakomai amma wlh duk ranar da kika bari kafarki takara taka gidan nan sede adau gawarki.

Kuma duk ranar dakika zo neman mijina Allah ya isa, dan idan har ina raye bazan barki ki kara hada ido dashi ba. Kutashi kubarmun gidana, kai kuma nabaka daga yau zuwa gobe kamaidomun kudina dakasan nabaka, idan bahaka ba, wlh kotu zata rabamu.

Murmushi Sameer yayi yace haba Ummi meyayi zafi haka? Ni dama can bantaba kashe ko kwandalarki ba, wata jaka yadauko agefenshi yamika mata yace wannan kudinki ne, tundaga dubu 10 da kika fara bama Baba mairo har kudin sadakin da kika bani, babu kwabonki dayayi ciwo. Hannun Falak yakama wadda take ta kuka, suka fita, abakin kofar falon suka hadu da Jidda wadda tundazu take tsaye tana sauraronsu.

Da kallo tabisu harsuka wuce, mamaki kawai takeyi wai Falak ce da mijinta, harma ga alamar ciki ajikinta. Baki ta tabe takalli Umminsu datake ta kuka ta kalli jakar kudin dake gabanta tayi murmushi tajuya tayi waje.

Asabe tace hajiya kitashi mukoma daki kada Alh yazo ya iske ki haka, muje inada mafita cikin sauki. Jakar kudin tadauka suka wuce daki. Seda Zarah tagama kirga kudin tsaf taga sun cika, sannan tasakasu cikin drawer tadawo tazauna.

Inna kenake saurare, banida sauran wata dabara, dolene muje gurin boka babu bata lokaci kashe Falak zanyi, shi kuma mijinta da Mairo wlh bazan kyalesu ba, tunda suka munafunceni, haba dama biri yayi kama da mutum.

Nayi mamakin yanda Mairo tayi saurin canzawa daga son datakema Falak zuwa tsana, duk yanda akayi aranar da mukayi waya dake aranar taji duk wani plan dina, saboda inagama wayar babu dadewa tashigo tana kukan munafurci. Kuma gashi bayan bikin Falak babu dadewa itama tace zataje ganin gida, gashi haryanzu bata dawoba.

Asabe tayi dariya tace aini dama nayi zargin wani abu agame da Mairo, kawaide nayi shirune. Toyanzu duk ki kyale wannan maganar, akwai mafita sede tana da wahala, na manta danazo ban fada maki ba, Boka ya mutu.... zunbur Zarah tayi ta mike taname dafe kirjinta, tace nashiga 3 ni Zarah, boka yazakamun haka seda bukatar nemanka tayi sannan zaka mutu.

Asabe tace kwantar da hankalinki wannan badamuwa bace, duka shekaranjiya Dije tadawo daga tafiyar danace maki tayi, dama ban fada maki bane, kasar yarbawa taje wata mata ta aiketa gurin wani babban boka, domin bakaramin hatsabibi bane, yashafe bokan dakika sani, dan aikinshi alokacin dakika fadi bukatarki alokacin take biya, kuma shi aikinshi beda makari.
Sede bakananan mutane yakema aiki ba, daga matan gwabnoni shugaban kasa, sarakuna se manyan yan kasuwa da yan siyasa, sabida aikinshi ba dubunnai yake amsa ba, miliyoyi ne. Ko Dije Matar sarkin Zariya ce ta aiketa.

Zarah tazauna tace yauwa Inna wlh harnaji dadi, yanzu yaushe za,aje? Asabe tace kina ganin zaki iya harka dashi, kinsan fa bawasu kudi gareki ba, kada yayi maki aiki ki kasa biyanshi aiki yadawo kanki.
Zarah tace wlh Inna kozanyi yawo tsirara bazan bari Falak tacigaba da rayuwar jindadi aduniya ba,( wa iyazubillah). Zankashe konawa ne domin ganin burina yacika akanta, kuma aikin ba ita kadai za,ayi mawa ba, hada Alh, inaso ta karbomun maganin mallakar zuciya tayanda beda makari, kuma bazanji shayin suhadu da ita ba.

Asabe tace kinga kudi sunkaru tunda aikin mutum 2 ne, kawai hotonsu zaki bada atafi dashi sekuma kudi, amma bari inkira Dije ince takirashi taji yawan kudin. Amma hajiya inazaki samu kudi masu yawa haka? Uhm kede bari Inna, kinsan Allah yana temakona aduk lokacin danashiga matsala, jiya Alh yabani million 6 na kayan auren Jalila, dama niyata inkashe mata million 3 indau 3, kuma gashi yanzu wani aiki yashigo, inaganin kawai zanyi mata siyayyarta anan kinsan Alhjn atafin hannuna yake bawani abu zece ba.

Asabe tace hakama yayi, inaganin kisiya mata na million 2 kirike 4 kinga kome aka bukata bakida sauran damuwa. Zarah tace haka za,ayi Inna shiyasa nake sonki nasan idan har kina raye, Allah yabarmunke.

Bara inje insa Jalila tadora abinci ki kira Dijen kiji konawane nafison ayi komai cikin sauri. Tana fita Asabe takira Dije tafada mata komai, nan take Dije tafada mata yanda zata ce.
Bayan Zarah tashigo Asabe tace uhm, aiki game kareka, kinsan Dije da mutane, muna gama waya takira bokan harsungama magana, tafadi mashi matsalarki, harya yanke mugun hukuncin dazeyima Falak, danshima yanajin haushin masu cin amana. Dariya Zarah tayi tace kai amma naji dadi, gaskiya Dije kawace tagari. Nawa yace kudin aikin?

Uhm aini hajiya abunne naji dayawa, kodayake biyan bukata yafi dogon buri, boka yace maganin dazeyima Alh, zaki mallakeshi, dayanda shine zerika aiki amma kudi suna gurinki, ko naira 1 baze iya kashewa ba, seda izininki, daya samu kudi kece ze kawomawa. Kara washe baki Zarah tayi tace kai, kice nazama babbar Hajiya, kawai fadimun kudin konawa ne, nasan nan da dan lokaci zanmaida mafiyansu.

Uhm na Falak de yace kibada million 2, na Alh kuma 1 da rabi, se kuma kudin da Dije zatayi kudin mota dasu dubu 50 sena abinci dan kwana 2 zatayi. Zarah tace kai kudinma babu yawa tunda acikin million 4 ina da saura, bakomai zan bata dubu 100 gaba daya nasan zasu isheta, gashi ku kuma

Please Login or Register in order to submit comment