Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwance yake babu abinda ke damunta, tasamu wata me aiki Jummai, batayi komai sede taci tasha, takara kyau, tayi kiba, ta maida Alh, saniyar tatsa, har dukiyarshi tafarayin kasa, sabodayawan kudin dayake bama Zarah, sosai ta tara kudi a account dinta. Bata da wata damuwa sena rashin dawowar Jidda, wata rana har kuka takeyi, takasa fadama kowa se Jalila, itama dataji haka seda tayi kuka, dan tasanyawon duniya kawai Jidda ta tafi, kullum cikin yimata addua, take.

Al,amin kuwa yana gama Umarah yakira abokinshi yace gashinan, ze taho, jirgin karfe 8 yabi yawuce London yana me addu,ar samun nasara akan Joseph.

Urs.
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[6/6, 3:30 PM] Nabeela lady: 🙋🏻😭😭🙋🏻 AGOLAH !!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@( H,O,N,A)

Part 95..... 100

Al,amin yana sauka london suka hadu da abokinshin yana jiranshi a air pot. Direct gidan shi suka wuce, bayan yayi wanka yayi sallah, yaci abinci. Anan suka fara tsara yanda zasu dauko Jidda. Duk da abokin Al,amin ba musulmi bane amma yana da riko da addininsu, kuma yanada gaskiya, sunanshi Daniel, kum makwabcin Joseph ne, sede halinsu kwata kwata badaya bane. Kwanan Al,amin 2 suna lura da duk wani shige da ficen Joseph. Jiran lokaci kawai sukeyi su shiga gidan, ko so daya bega Jidda ba, hakan ya tabbatar mashi baya barinta fita.

Ginin su Sameer har ankusa gamawa, fenti kawai akeyi, Sameer beda lokaci kullum yana plaza ko gurin masu gini. Falak tayi kyau sosai, idan kaganta baza kace Falak din daka sani bace, takara girma, kyawunta yakara fitowa. Yanzu babu abinda kedamunta, se tunanin Dadynsu Jalila, kullum cikin yimashi addu,a take.

Kuma Baba mairo tace kada suje gidan se nan dawani lokaci. Zamansu da Sameer zamane na mutunta juna, suna bala,in son junansu, Sameer bayasan ganin bacin ran Falak, itama haka, kasancewarta mace me hakuri kuma tasamu miji me hakuri. Haryanzu akwai sauran kudinta a account, ko naira Sameer yafitar seyayi mata bayanin abinda akai da ita, har fushi tayi mashi akan abinda yake mata amma yaki bari, yace haka shine gaskiya. Dole tahakura badan taso ba.

Ajikin gidansu yasa akayi shaguna guda biyu, yace na Falak ne ze zub mata kaya asamu me tsare mata, musamman da unguwar basuda irin shagon saida kayayyaki haka.
Baba mairo da Umman Sameer hankalinsu kwance suke sana,arsu cike da girmama juna, dan Baba mairo ta girmi Halima sosai, dan ita Halima bawani tsufa tayi ba, kawai de halin rayuwa ne yamaidata babba, amma yanzu da kwanciyar hankali tafara zuwa masu tuni tafara maida jikinta. Duk wata shawara dazasuyi Baba mairo suke kawo ma ita, idan kuma abun yafi karfinsu, Kawun Sameer suke kaima ita.

Zarah ce zaune adakin Asabe, bayan sungama gaisawa, tace waini Inna haryanzu shiru babu Jidda, nifa hankalina yafara tashi, kawai ina cikin kwanciyar hankali yarinyar nan zata sani cikin damuwa, aduniyar nan babu abinda ke damuna se rashin sanin inda Jidda take, tun Alh, yana tambayata ina mashi karya har nafara gajiya.

Jiya yake cemun zezo har nan yatafi da ita, kuma idan har bata fitar da mijin aure ba, duk wanda yasamu zebama ita. Shine nazo dan Allah kirakani gurin boka yaduba mun inda take, kotana raye, kuma arufema Alh, baki yadena maganarta, kota dawo kada yatambayeta inda taje.

Asabe tace gaskiya ni kaina abun yana damuna, kuma kinga idan haryagane bata gidan nan muze zarga, gara muje arufe mashi baki kawai. Ita kuma nasan duk inda take zata dawo. Malam dayake bakin kofa yana jinsu yashigo, ya kalli, Asabe, duk da yanajin tsoronta, amm wannan karon seda yayi magana.

Yanzu ke Asabe kina ganin abinda kikesa yarinyar nan tanayi dede ne? Na dade ina jin duk wani abu da kukeyi akan bawan Allan nan, wai seyaushe zaku tuba kudena abinda kukeyi? Kadafa ku manta akwai wata rayuwa bayan an mutu, kum kowa ze tsaya agaban Allah yafadi abinda yayi, wanda aranar baki baze iya magana ba, saboda shima makaryaci ne. Ke kuma Zarah abinda nakeso dake kiji tsoron Allah, kina ganide tun aduniya yafara nuna maki ishara, akan diyarki, yanzu Allah kadai yasan inda take, kuma duk inda take, ba halin kwarai take aikatawa ba.

Nasha ganinta da manyan mutane suna sauketa kofar gidan nan, amma dayake baku daukeni abakin komai ba, bakwajin maganata, yaude nafada maku iya gaskiyata, idan harkunji to, idan kuma bakuji ba, wlh inaji maku tsoron ranar danasani, ranar da babu lokacin gyara barnar da kukayi.

Zarah ta zunburo baki tace wai kai Baba mekaga munyi? Nifa wlh banason takura, dama naga duk sanda nazo gidan nan labe kake mana, kuma kana nufin Inna Asabe ita zata cuceni ne, ko gorin haihuwa zaka mata? Kuma ni nasan babu abinda Jiddata take aikatawa se alheri, kawai de kanamun bakin cikin yanda na auri me kudi, itama tasamu. Kuma mekaji munce zamuyima Alh?

Inna Asabe tace ai gara ke dayake diyarshi ce kifada mashi, wato Malam yanzu duk irin rikon danayima Zarah beyi maka ba? Lallai nayarda da,akace namiji ba dan goyo bane, to ai kadeji da kunnanka, abinda diyar taka tace. Kuma wlh wannan shine karo na karshe da zakaji muna magana kashigo kasa mana baki. Wuce kabani guri, namiji da akai kana halin mata. Allah yabaki hakuri ammade Zarah kiji tsoron duniya, kuma ni kike fadama magana. Kije duniyace ta isheki komai, wanda bezo bama jiranshi takeyi.

Dallan can kawuce kabamu guri, fita yayi yana matsar kwalla, wai yau diyar daya haiface take fadamashi magana. Asabe tace aikinyi mun dede, maza zuma ne, dole seda wuta. Shiyasa nace kada ki saurarama mijinki, kina ganinde duk irin biyayyar danakema Babanki amma yau yayimun gori. Kukan munafurci tasa, anan Zarah tashiga bata hakuri. Asabe tace tashi muje inrakaki dan Dije bata nan tayi tafiya. Tashi sukayi suka wuce gurin boka.

Tundaga ranar da Zarah tasama Alh, magani a abinci bekara maganar Jidda ba, shiyasa hankalin Zarah yadan kwanta, duk itama bata bacci sosai, dan tanason Jidda, tamafi sonta akan Jalila, dan halinsu daya da Jidda. Saukinta daya boka yace mata Jidda tana raye kuma yakusa dawowa gida.

Yau Jalila tagama final exam dinta, kuma ayau tagama shirya kayanta domin tafiya gida, driver take jira. Yana zuwa yadauketa, seda tafara biyawa cikin kasuwa inda kakansu yake. Dan ita bata zuwa gidansu, kwata kwata jininta be hadu dana Asabe ba, shiyasa tunda tafara karatu so 1 taje gidan.

Abakin shagon dayake zama tasameshi, tasowa yayi yana fara,a ganin Jalila, dan yana sonta sosai, tana temaka mashi, da yan kudi duk sadda tazo gurinshi, har bakin motar yakaraso, bayan motar yashig, bayan sungaisa da driver, Jalila tace ma driver yadan jirasu awaje. Gaisawa sukayi take fada mashi batun tafiyarta yau, dan tagama karatu, sosai yayi mata murna, sede beji dadin tafiyar taba zedena ganinta, dan itace abokiyar shawararshi. Jalila tace ai kaka kona tafi zanrika zuwa, kuma baga waya nan nabaka ba, zamu rika gaisawa, idan akwai wani abu seka fadamun tanan, idan yakama inzo senazo, ai babu nisa daga Kaduna zuwa Zariya.

Goge kwallan data zubo mashi yayi, Jalila tace kaka akwai abunda ke damunka, bantaba ganinka cikin damuwa haka ba. Murmushi yayi yace Jalila akwai abunda kedamuna sosai ma, kuma akan mahaifinki ne, da kuma Zarah,,,,,,,, anan yafada mata duk irin firar dayaji su Asabe sunayi da irin cin mutuncin da Zarah tayi mashi.

Seda Jalila tayi kuka, jin irin abinda Umminta keyi, hakuri tayi ta bashi, tace Kaka nima nasan akwai abubuwa da dama wanda Ummi takeyi, kuma bakowa bane yake zugata se su Inna Asabe da Dije. Amma Ummi tayi mani kashedi babba akan idan taji ina shiga maganar da babu ruwana aciki, har cewa tayi zata tsinemun, hakan yasa ma tunda nataho karatu ban koma gida ba, Dady ne kuma yanazuwa muna gaisawa.

Addu,a kawai nake masu, amma Kaka yaya Jidda tayi nisa batajin kira sede addu,a. Yace kikara hakuri insha Allah wata rana gaskiya zata fito, mucigaba dayi masu addu,a, kuma kamar yanda Zarah tafada maki, banason kishiga abinda babu ruwanki. Allah yayi maki albarka, kuma dan Allah Jalila kinga kingama karatu, kada kitsaya ruwan ido, kifitar da miji kiyi aure, banason zamanki agidan nan, kinga Falak tayi aurenta tahuta,kema Allaj yabaki miji nagari. Haka sukayi sallama takawo kudi tabashi, suka tafi.


Ayau Al,amin suka shirya yanda zasu dauko Jidda, Daniel yace kabari zan shiga gidan tunda yau munci sa,a shidaya yadawo, zanje muyi fira, zan bashi wiky nahada mashi da maganin bacci, dayayi zankiraka seka taho. Al,amin yace to amma megadin gidanfa? Daniel yace kabari nasan yanda zanyi dashi, kaide kazama cikin shiri, kadauki visa dinku da kayanka, nayima me taxi magana yanzu zezo yajiraka kuna fitowa kushiga yawuce daku. Godiya sosai Al,amin yayi mashi kuma yayi mashi alkawarin idan yasamu dama zezo surika gaisawa.

Zaune ya iske Joseph afalo yana kallo, bayan sungaisa Daniel yace joseph kaboye yanzu kaja kaya ko. Murmushi Joseph yayi yace haba ogana kaine bana ganinka, ya labari? Daniel yace lafiya lau, wata sabuwar whisky nakawo maka jiya wani abokina yabani ita, amma kasan bana shan irinta, shine nakawo maka. Katabar kwalbar Joseph yayi yace wow amma nagode, budewa yayi yafara sha, Daniel yace yauwa bama gateman dinka yasiyomun, irin whisky danake sha acan bakin titi.

Karbar kudin joseph yayi yafita yana tangadi yafita, bayan ya aiki megadi yadawo yacigaba da shan whisky dinshi suna fira, cikin lokaci kadan yafada bisa kujera bacci yadaukeshi.

Cikin sauri Daniel yadaukeshi yakaishi daki, yakira Al,amin. Jidda tana kwance adaki tasha giya da kwaya summata yawa tana bacci, Al,amin be tsaya bata lokaci ba yadauketa daga ita se riga da dogon wondo, kanta babu dankwali yasha tsohon kitson attache, fita sukayi ko tsyawa daukar jakarta beyi ba, ga uban kudin da Jidda ta tara aciki haka yabarsu suka fita, me taxi suka samu dan nan suka shige yadaga ma Daniel hannu suka nufi air pot, shima Daniel yafita. Tun acikin mota Al,amin yaciro jallabiyar daya siyowama Jidda yasa mata, yakama gyalen yadaura mata, sede duk abinda akeyi bacci take.
Suna zuwa ya sallami me mota suka jira aka kira sunansu yakamata suka shiga, ko acikin jirgin kwantar da ita yayi bisa cinyarshi tacigaba da baccinta. Suna isa yayima wani abokinshi waya yazo yadaukesu suka nufi gidanshi.


Ayau su Falak suka tare. Asabon gidansu daya keru, yayi kyau sosai, duk da bawani ginin karya akayi ba, amma yayi kyau, duk wanda yashiga ciki seya burgeshi, anzuba kaya masu kyau, dakin Falak yasha kaya masu kyau, kitchen dinta kamar nawata diyar me kudi.

Kwance Falak take akan cinyar Sameer suna fira, wayarta ce tayi kara, dauka tayi tace habawa Jalila nikam nayi fushi, yau satinki nawa da dawowa, amma kinkasa zuwa kiganni. Jalila tace dan Allah kiyi hakuri wlh banaso Ummi tasan gidanki zanzo, amma yanzu kiran danayi maki ma kwatancen gidan nakeso kimun ganinan ina shiryawa.

Falak tace to Allah yasoki, bara inturo maki da address din yanzu. Jalila tace Allah sa de mijinki baya nan dan wlh tsoran masu shaye shaye nake. Dariya Falak tayi tace ai babu abinda zemaki, kuma bayama nan, Jalila tace Allah Falak dande kinmatsamun inzo banason zuwa inga halin dakike ciki. Falak tace nide banason wani dogon surutu sekinzo. Kashe wayar tayi tana dariya, ta tura mata da address din.

Sameer yace keda Jalila ne hala? Tace emana, kasan metace, yace a,a wai cewa tayi Allah sa baka nan tsoron yan shaye shaye take. Dariya yayi yace ai zanso inga irin mamakin da Jalila zatayi idan tagammu amatsayin ma,aurata.

Au, kinga namanta tundazu inaso infada maki, dana fita shago nahadu dawani babban abokina Saleem, tare mukayi Zariya dashi amma shi yasamu aiki, awani kamfani na babanshi. Dama kuma bussiness yakaranta, nikuma nayi Pharmacy. Yarigani gamawa da shekara 1 danmu shekara 5 ne sukuma 4.

Bayan mungaisa yake tambayata menakeyi anan, nace mashi ai shago nane, shine yace meyasa ban bude chemist ba, natsaya bude shago, shine nace mashi kasan bude chemist ba sauki bane dole sekana da hanya shiyasa kawai na bude plaza.

Yace mun bana aiki ne, nace mashi wlh na nema harnagaji bansamuba, shiyasa kawai na hakura. Shine yace anjima da dare zezo yasameni ashago muzo nan gida ze amshi takarduna ya bama babanshi yanemamun aiki, kinsan babanshi babbane dan a Abuja ma yake aiki.

Falak tace kai amma gaskiya naji dadi sosai. Allah yasa asamu, yace Ameen. Tace bara intashi inshiryama Jalila abinci kafin tazo, yace to nide ina daki bacci zanyi idan tazo kitadani.

Jalila tafito cikin shirinta tace ma Zarah Ummi nagama shiryawa, zantafi. Zarah tace kijira driver yazo ya kaiki mana, yanzu zedawo. Jalila tace a,a Ummi kawai kibarshi zantafi sauri nakeyi kuma kawata tana tajirana. Kudi tamika mata tace gashi nan sarkin sauri, kigaisheta, amma kada kiyi dare fa. Tace to Ummi nagode.

Fita tayi tahau taxi tayi mashi kwatancen inda ze kaita, yace yagane gurin. Tafiya suke tana tunanin halin dazata iske Falak aciki. Dede wani hadaddan gida suka tsaya yace mata hajiya mun iso seki kirata kiji wane gidanne aciki. Jalila tace malam anya nanne unguwar kuwa, nifa duk cikin gidajen nan babu wanda yayi kama da irin gidan da,aka cemun Falak tana ciki. Yace tonide sauka kibani kudina ki kirata mana idan bata fitoba seki nemi wani ko. Sauka tayi tabashi kudinshi taciro wayarta takira Falak.

Urs,
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[6/12, 3:25 PM] Nabeela lady: 🙆🏻😭😭🙆🏻 AGOLAH !!!Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@( H,O,N,A)

Part 100.....105

Lekawa kofar gida Falak tayi domin ganin inda Jalila take, tana fita suka hada ido kasancewar akusa da gidan take tsaye. Mamaki ne yakama Jalila ganin daga inda Falak ta fito, kallo daya tamata tagano kyawun datayi.

Falak tace tokishigo kosena daukoki? Murmushi tayi tanufo gidan, fuskarta dauke da mamaki. Suna shiga, mamakinta yakara yawa ganin irin yanda cikin gidan ya tsaru. Falak tace bismilla mana. Jalila tace Falak bazaki kasheni da mamaki ba, zo zauna ki amsa mun tarun tambayoyina, kafin ayi komai.

Dariya Falak tayi tace a,a zauna inkawo maki abun sha idan muka gaisa zan amsa maki. Bata jira mezata ceba tawuce kitchen, da kallo Jalila tabita, tana mejin farin cikin ganin halin data isketa. Hamdala kawai takeyi acikin zuciyarta.

Bayan takawo mata kayan motsa baki, tazuba mata zobo a cup, tace ina zuwa, kai tsaye dakin Sameer tawuce, tsaye tasameshi yana shiryawa, da alama daga wanka yafito, amsar man tayi tacigaba da shafa mashi tana murmushi.

Sameer yace daga ganin wannan fara,ar nasan Jalila ta iso, Falak tace tanama falo, nace bara inzo inkiraka ta idasa cika da mamaki kafin inbata labari nafiso kana zaune agurin. Kayanshi tamika mashi, ya amsa yasa yace nima zanso inga fuskar Jalila ai. Turare yafesa yace muje ko, hannunta yakama suka fita.

Jalila dake zaune afalo tana cin abinci, se kalle kalle takeyi, duk da gidansu yana da kyau amma tsarin falon Falak ya burgeta. Zumbur tamike ganin abinda batayi zatoba. Malam Sameer, Jalila tafada cike da mamaki. Murmushi yayi yajawo Falak suka zauna akujera, zamewa tayi daga jikinshi ta zauna sosai.

Sameer yace Jalila kizauna mana kada kuda yashige maki baki, zama tayi tana kallon Falak. Dan Allah kufitar dani aduhu, duk da na dade dasanin kana son Falak amma banyi zaton kaine zansama amatsayin mijinta ba, kuma ni Ummi ba irin auren da tace tama Falak bane, nagani agidanta.

Sameer yace to Jalila sede muce Alhamdulillahi, kuma inaso kamar yanda nasanki me gaskiya kici gaba da zama ahaka, kuma inaso infada maki ba,ayima Uwa biyayya inde gurin sabon Allah ne, kuma hakan bayana nufin kamata rashin kunya ba, duk yanda mahaifiyarka takai ga aikata sabo, tana nan amatsayin Uwa agareka, sede kayita nema mata shiriya agurin Allah.

Tabbas nasan Umminki tana aikata abubuwa dayawa marasa kyau, amma adalilinki da kuma Dadynki yasa dole muma mubata darajar Uwa, kuma inaso duk abinda zakiji kiyi kokarin barinshi amatsayin sirri, kamar yanda mukayi, nan da wanj lokaci komai ze zama dede bara infada maki yanda akayi nazamo mijin Falak..............


Sautin kukan Jalila kawai akeji falon, Falak kam hawayene keta zubo mata. Da kyar Jalila tayi shiru, goge idonta tayi ta matso kusa da Falak, har kasa ta duka tace Falak tabbas nasa Ummi na bata cancanci afuwa agareki ba, amma duk da haka iname baki hkr akan irin abubuwan da tayi maki. Insha Allah wata rana zata gane gaskiya, nide kam banyi sa,ar uw..... dasauri Falak tarufe mata baki tana girgiza mata kai.

Sameer yace a,a Jalila kada inkara jin wata kalma me muni akan Umminki, laifi nede ta aikatashi, abinda yarage agareki, addu,a zakiyi mata, Allah shine maji rokon bayinsa, idan yasota da rahama seya shiryar da ita, amma kada kikara cewa zaki aibanta ta.

Jalila tace nagode Malam, kuma insha Allah nazan kara fadar haka ba, kuma kusani bazan taba fadin wani sirri naku ba, nime kaunar kuce, ina daukar Falak tamkar Jidda agurina, Falak takamata takoma bisa kujera ta zauna, Falak tace to ya isa haka, yanzunde komai yawuce, inafatan yanzu bakijin tsoron mijina ya iskeki agida ko? Dariya suka su duka. Sameer yace toni bara infita munyi alkawari da Saleem zamu hadu a plaza, Jalila kijira indawo ba dadewa zanyi ba, tace to ammade kayi sauri Ummi tace kada inyi dare. Haka sukayita fira da Falak.

Har cikin gate din Al,amin abokinshi yashiga dasu, bayan yayi packing Al,amin yafito yana tallafe da Jidda, wadda haryanzu bata ida dawowa hayyacinta ba, jakarshi yadauka yayima abokinshi godiya, sukayi sallama yashiga gida. Afalo ya kwantar da ita, yawuce daki, toilet yafada domin wanka dan duk jikinshi warin giya yakeyi, bayan yafito yasaka jallabiya yayi sallolin da beyi ba, sannan yafito falo, azaune ya iske Jidda tana ta yan kalle kalle, sede haryanzu idonta ba dede yake ba. Kitchen yawuce yadauko madara pick yazubota akofi, yazo kusa da ita yamika mata, amsa tayi takafa kai seda ta shanye tas tabashi kofin.

Yace Jidda kinaji na? Kai tadaga mashi, yace tashi kije kiyi wanka nasan zakiji karfin jikinki, sekidawo muyi magana, da kyar ta tashi amma seta koma tazauna, ganin haka yasa yakamata suka nufi daki, har toilet yakaita sannan yafito, kitchen yakoma yadora masu indomie, cikin minti 20 yagama hada masu komai, yazauna jiranta.

Da karfi Jidda tabanko kofar dakin tafito, cak ta tsaya ganin Al,amin afalo, kara kallon falon tayi, hawaye suna fita a idonta tace Al,amin ina muke nan? Tasowa yayi yace Jidda ki kwantar da hankalinki a nigeria muke, kinsan nayi maki alkawari zan daukoki. Ya isa haka. Meyasa zakamun haka, kuma ina jakar kayana naduba banganta ba. Al,amin yace Jidda nida name kokarin cetoki daga halaka ina zan tsaya daukar wata jakar kayanki, wadda nasan kayan ciki ma bana mutunci bane.....tasssssss yaji tadaukeshi da mari.

Cike da mamaki yadafe fuska yana kallonta. Wani irin kuka tasa tare da rike mashi kwalar riga. Kacuceni Al,amin, kasan irin walahar dana sha kafin intara kudadena dasuke cikin jakata. Wlh nasan ko zaka saida duka kadarorinka bazasu kai yawan kudin da Joseph yabani ba, harma da wadanda na daukar mashi bada saninshi ba. Sannan ace duk irin azabar dana sha ace nayita abanza. Ina ruwanka da rayuwata, kaine Uwata ko Ubana?...... Kuka yaci karfinta tazube akasa.

Tausayi Jidda tabashi, dukawa yayi yace Jidda kiyi hkr, nasan bankyauta maki ba, amma hakan danayi maki wlh shine gata, kuma kudi bazasu taba biya maki wata bukata agidan Joseph ba, sede ya illataki daga karshe ma Ya kasheki abanza. Ni nasan waye Joseph, kiyarda dani bazan taba cutarki ba, kozaki cemun haryanzu Joseph yana zama dake acikin mutunci?

Kiyi hakuri ki koma gida kema kituba zuwa ga Allah kisake sabuwar rayuwa kamar kowa, haryanzu kinada sauran lokaci tunda Allah be amshi ranki ba. Tashi yayi yadauko abinci yazauna yazuba mata yace dauka kici nasan kinajin yunwa, lemu yazuba mata akofi. Ba musu tadauki abincin tafara ci dan yunwa takeji sosai, kallonta yakeyi tanaci tana kwalla. Shima zubawa yayi yafaraci.

Lemu tadauka tasha, sede kagaba daya test dinshi beyi mata ba, kallonshi tayi tace Al,amin bakada whisky ne, gaskiya bazan iya shan wannan kemun ba. Mamaki ne yakamashi jin abinda Jidda tace, girgiza kai yayi yace Jidda yau kuma kece kike shan giya? Amma ai kinfi kowa sanin bana shanta, asalima bana zama tare da meshanta, saboda haka hakuri zakiyi tunda kindawo gida ki aje duk wata dabi,a da kika dauko acan kicigaba da rayuwarki kamar da. Kinsan gara mutum ya aikata kowane laifi ze iyayin daraja agurin mutane da ace yazama mashayin giya, aduk lokacin dakika shata bakisan da wanda zaki haduba, zaki fita daga cikin hankalinki,saboda haka iname shawartar ki tunda de nasan baki dade dafara shanta ba, kiyi hakuri kidena.

Kuka tasaka mashi tace bazan iya ba, Al,amin, Giya tazama tamkar ruwan shana bana iya minti 5 batare dana shata ba, katemaka mun dan Allah. Tausayinta yakamashi yatashi yadauko mata Lime drink a kitchen, karba tayi tafara sha, duk da bataji dede ba amma garashi da dayan.

Bayan sungama suka koma bisa kujera, tasowa tayi daniyar fadawa jikinshi yayi saurin matsawa, Jidda lafiyarki kuwa? Nifa yanzu rayuwata ta canza ba Al,amin din da bane yanzu, duk da ban fada maki ba, amma yanzu haka daga saudiya nadawo shine nawuce london domin daukoki. Wlh Jidda yanzu natuba m, nakoma ga Allah, babu abinda na tsana kamar Zina. Ke duk wani laifi na sabon Allah nadenashi, saboda haka kema ina rokonki daki tuba kizo muyi aure, amma kafin nan inaso kibani labarin yanda zamanki da Joseph yacigaba datafiya.

Kuka tasaka mashi, anan takwashe komai tafada mashi, sosai yaji tausayinta, duk da hada laifinta, da sin kudinta suka jamata. Girgiza kai yayi yace Lallai Jidda kinga rayuwa, sede agaskiya naso in aureki, tun abaya amma kika gwada a,a ko alokacin da nayi maki waya zanzo indaukeki nayi niyar muna dawowa in aureki, amma kikamun rashi, mutunci. Gaskiya Jidda bazan boye maki ba, bazan iya kara hada shimfida dake ba ahalin dakike yanzu, saboda Joseph yagama cutarki yayi amfani dake ta ko ina dayaga dama, bashi kadai bama harda wasu kazamai, wadda gaskiya ina tsananin kyamarsu, da ace Joseph ne kadai yayi amfani dake, zan iya aurenki, saboda nasan halinshi. Amma kincemun tunda yakawo abokanshi suka fara lalata dake yadena kusantarki. Hakan yanuna cewar akwai muguntar daya shirya maki.

Kiyi hakuri da abinda zanfada maki, kidaure kije asibiti ayi maki duk wani test daya kamata, domin tabbatar da lafiyarki, ni kaina nasan naje asibiti da yawa, ke har saudiya naje anduba ni. Kuma Alhamdulillahi banida cuta ajikina, kinga dole inji tsoron aurenki.
Jidda tayi murmushi tace nima haka babu abinda kedamuna, saboda haka babu wani asibiti dazanje, kuma dama ai nafada maka nafi karfin na aureka, dan bakada kudin dazaka rikeni, shiriya kuma ai ta Allah ce, kamar yanda yashiryaka nima nasan watarana tawa tana nan zuwa. Murmushi yayi yace Jidda....... Hannu tadaga mashi tace ya isa, kabar wa,azinka banaso, idan kashirya kazo kamaidani gida. Kai ya girgiza yatashi yaname cike da tausayinta.

Doguwar rigar datasaka dazu ita tamaida, gaba daya ta rame, se uban hasken bleaching dayayi mata yawa, duk ta fita hayyacinta. Haka yafita yadauko mota yaja suka tafi. Adede kofar gidansu ya ajeta, kudi yadauko masu yawa yamika mata yaceto Jidda ina maki fatan alkhairi, nide daga yau bazaki kara ganina ba, se ince Allah yasadamu da Alkhairi, abu na 2 kuma ina rokonki daki yafemun, nasan nabada gudummuwa gurin lalacewar tarbiyarki, dan Allah kiyafemun. Murmushi tayi ta amshi kudin tace bakomai Al,amin nayafe maka, Allah ya yafe mana baki daya. Idonshi suka ciko da kwalla, yayi saurin dauke fuskarshi daga kallonta, yanaji tafita tana fadin bye, amma ya kasa kallonta, tabbas yasan Jidda tayi nisa batajin kira, sede addu,a. Haka yaja motarshi yatafi.

Bata shiga gidan ba seda takoma wani chemist tasiyo wasu kwayoyi sannan tawuce gida. Megadi da driver tagani zaune suna fira, wuce su tayi, megadi yace baiwar Allah daga ina zakizo kiwuce mu ko sallama babu, wani kallo tayi mashi tace ina ba gidan ubanka bane bare kadamu da rashin sallamata, driver yace tofa meyakawo nazagi kuma, amma naga kamar Jidda ko? Oho koma wacece badamuwarka bace tunda inda gado agidan, mamaki yakamasu sukayi shiru sukallonta hartawuce. Driver yace ikon Allah, wai yaushema tadawo? Megadi yace yanda kaganta haka naganta, tagaji dayawon duniyar ne. Amma insha Allah zataga bacin rana yanda ta iya bude baki tazageni. Driver yace kayi hkr Baba, Allah yashirya.

Zarah tana zaune afalo tana kallo, taji sallama saurin tashi tayijin kamar maganar Jidda, cak ta tsaya ganin Jidda cikin wani irin kama. Jidda tace Ummi yanaga kintsaya kamar baki farin ciki da ganina ba. Zarah tace Jidda lafiyarki kuwa? Wucewa tayi tazauna tace lafiya lau

Please Login or Register in order to submit comment